Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
ya huta, ai sai barci ya share shi don gajiyar tafiya, ko da ya ke sabon shi ce. M. 'Danye bai farka ba har rana ta fito. Can wajen hantsin gwauro sai wadansu, 'yan hari bisa rafuma, suka zo suka tarad da shi yana barci. Bubbansu ya durkusad da ra- Ruminsa ya sauka, ya d'auke duk kayan M. 'Danye har da 'yar laya da Sarkin Aljannu ya ba shi, sannan ya ta da shi. M.'Danye ya tashi firgigi a tsorace, ya wawuri kaya babu, ba wani makami, sai ya yi turus, suka tisa shi gaba har Rauyensu Da fa M.'Danye ya ga ya zo hannu ya ga ya zama bawa, sai ya fara tunanin yadda zai ya fita daga wannan hali. Can dabara ta zo masa, ya ga lalle abin da ya fi Karfinka, sai lallashi, ya ga kuma don ya lallashi ubangidansa kan ya bar shi ya tafi, wan- nan bata yi wo, sabo da haka sai ya shiga fadanci yadda za a yarda da shi har ya samu ya gudu. Sabo da haka kullum in suna fira da ubangidansa, sai ya rika cewa, "Ni dai Allah ya ba ni sa'ar fitowa da ka kamo ni, da ma ba ka kamo ni ba, da na biyo ka, ga shi ni bani wata wahala, in ci abinci irin wanda na ke so, wallahi har ba ni son in ko fita yawa, haka duk al'adarku ta ke, ku jiya wa bayinku dadi? Ubangida ya ji an yaba shi, sai ya ce, "Ai duk garin nan ba mai yi wa bawa, yadda na ke wa na- wa, nan gaba ma in idonka ya fara budewa da mutane zan fara tura ka kasuwoyi kana sayar mani da alkama da shinkafa, don lalle in nuna ma na yarda da kai". Da M.'Danye ya ji an masa susa inda ke masa RaiRayi ya ga kuma har zai sami guzuri, sai ya ce, "Haba Maigida ai wanian wahala ce, ni dai ba ni so gara kullum ina tare da kai, ko da ya ke dai in ka sani zan yi don faranta ma rai, kuma ka kara ganin gaskiya ta, ya kaikaici idonsa ya yi masa gwalo. Jin haka sai ya sa Ubangidansa ya himmantu da ya tura shi --- **Page 13** kasuwoyi, sabo da haka ya labta wa rakuma biyu kayan alkama da na shinkafa ya kira M.‘Danye ya gama shi da fatake. M.‘Danye suka miŘa tare da fatake. Suna tafiya sai tamta- yarsu hanyoyi ya ke, har ya dace ya ga hanya mai zuwa Langeri. Da magariba ta yi suka sauke, inda za su kwana, suka ci abinci, suka yi yar fira, sabo da gajiyar tafiyar nan da nan suka yi barci, amma M.‘Danye idonsa biyu, ya yi kamar ya yi tardi. Can da dare sai ya tashi ya yi labtu, ya hau rakumi guda ya yi baya, ya dire hanyar Langeri ya yi ta yi. Da asuba suka tashi, suka duta, ba M.‘Danye, suka yi tsam- mani ko har ya yi gaba. Sabo da haka suka ci gaba wai ko sun tarad da shi, ina, har suka isa kasuwa ba bu M.‘Danye. M.‘Danye da isa wani dan kauye sai ya sayar da alkama da shinkafa da rakumi guda, ya sami isashen guzuri ya ci gaba da tafiyarsa. M.‘Danye yana cikin tafiya sai ya ji wani ya ce, “Ta’ nan ya bi”. Sai ya zaci ko Ubangidansa ne ya biyo shi, sai ya ce, “Wal- lahi hanya ta bace mani har suka barni”. Da mutanen nan suka ji haka sai suka ce, “Ai ba mu yarda ba, sai mun tafi da kai gun Sarki, don sun tabbata ba shi da gaskiya”. Da ya ga da gaske su ke, sai ya ba su duk kudin alkama da kudin rakumin, don yana tsoron kada su tafi da shi, har ubangidansa ya tarad da shi, sa’annan suka bar shi. Yana tafe yana cewa su dai kayan zalunci ba su da albarka. Ashe su mutanen nan jakinsu ne ya bace, su ke cewa, ta nan ya bi, shi kuma M.‘Danye yana zaton da shi su ke, ganin ko almar rashin gaskiyarsa shi ya sa suka turza, su da suka sami wannan kudisin yi ta jaki, ai sai gida. Mutanen nan da suka shiga garinsu, sai suka nufi fada don neman fadanci, suka kwashe labarin M. ‘Danye suka ba Sarkin garinsu kan lalle wani gawurtaccen barawa ne, akwai kudimasu yawa gun shi, don mu ma har ya ba mu. Sarki da ya ji haka, mai nema a duhu ya samu a sarari, sai ya tura dogarai kan dawak, suka bi M. ‘Danye. M. ‘Danye bai san abin da baya ke ciki ba, yana cikin tafiya, sai kurum ya ga mutane sun kewaye shi, shi ga zato ce ya ke Maigidansa ne da mutanensa, sai kuma ya fara tuba. Haba, ya gamu da mutanen Sarki, ga shi’kuma har ya nuna masu rashin gaskiya, ai kafin haka sun bugo shi da ga kan rakumi ya fado, suka daure shi kamar goro, aka kai shi gun Sarki. Da zuwa Sarki bai wata wata ba, sai ya kwace sauran rakumi, ya ce a kai shi kurkuku. --- **Page 14** Ga shi an Rwace raRumi da du kudinsa da 'yan kayansa, ga kurkuku, sai kuma ya zamana, ba a nuna masa komi sai baRar azaba.. Kullum da safe bulala dari, da yamma dari. Har dai ta kai yana cewa a zuciyarsa, da na sani da ban d'auko wa kaina wannan wahala ba, ga shi ina murna na kuButa daga hannun Maigidana, amma kuButar ta zaman mani wahala don ko rashin gaskiya kurum amma tun da na d'auko alkawali neman yarinyar nan, gara a kashe ni ina cikin KoKarina domin girman alkawali. M.'Danye duk ya rame, ba ya komi sai doyi, ga rashin abinci isassshe, ga azaba. Bugu da Rari sai kuMa Sarki ya yi umurni ya riKa kwashe kashin kasuwa wai don ya fiddo da kudi. Da M. 'Danye ya ga abin so a ke a kashe shi ta hanyar wa- ha'a, sai ya ce a kai shi gun Sarki yana da magana. Aka kai shi, ya yi gaisuwa ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ina so ka taimake ni ka kashe ni, don in huta da azaba". Da Sarki ya ji haka, sai ya ce, "Idan na kashe ka na taimake ka, kuma ka huta da azaba?" M. 'Danya ya ce, "Ko dai ban huta ba gara Allah ya yi mani azaba, don watakila tashi ta fi taka rangwame, kuma wannan lalle taimako ne, don ko baka kashe ni ba yanzu, azabarka za ta kashe ni gaba, shi ya sa na ga in- an kashe'n'i yanzu an taimake ni". Da Sarki ya ji haka sai ya bushe da dariya ya ce a sake shi. Da aka saki M. 'Danye bai kwana a garin ba, sai ya rarrafa ya bar garin. Kwanansa uku yana tafiya, sai ya isa wani babban birni. Ya sami gidan wata tsohuwa ya sauka ya yi ta jiyya. Tsohuwar da M. 'Danye ya sauka gidanta irin matsolon tso- ffin nan ne, sana'arta sayar da daddawa, amma duk abin da ta samu ba ta ci ba ta sha, sai ta zuba a tukunya, da dare ta shiga bara. Duk halin da ta ke ciki M. 'Danye na lura da ita. Da dai ya gane ma'ajiyar tsohuwa sosi, ai kurum da ta fita, sai ya je ya bude tukunya ya kwaso kudi. Da safe in tsohuwa zata tafi kasuwa sai ya kawo kudi ya ba ta ta kwaso nama da kayan girki. Tun da azahar tsohuwa na rawar jiki, sai ta komo ta shiga hidimar girki, ba ta san ashe kudinta ne ta ke ci ba. Kafin a ce haka tsohuwa ta yi bulbul har ta bar bara. Mutane sai mama'xi su ke yi suna cewa tsohuwar nan ta yi sa'a, ta sami wani ba'ora falke, sai gara ya ke kasho masu, dubi duk ta can- za nan da nan. --- **Page 15** Suna cikin haka da M. Danye duk ya murmur, har ya soma ajiye teba da kudin tsohuwa, sai rannan tsohuwa ta ga safiya ta yi M. Danye bai ba da kudin girki ba, ta ce masa, “Maigida yau lafiya, na ga ko kudin girki ba ka ba da ba ?” Sai gogan ya ce, “Ai kudin namu sun fare”. Sai tsohuwa ta sha jinin jikinta. Ta tafi daki ta duba tukunya sai ta ga ko kwabo babu. Sai tso- huwa ta fasa kuka da kururuwa, nan da nan gida ya cika maRil. Aka tambaye ta dalili, ta ce “Kudina bako ya dauk”. Mutane da suka ji haka, sai suka riRa yi mata dariya suna cewa, “Ai gara haka, kin tara kudi, kin Ri ci, kin Ri sha, kin damu mutane da bara, to ga shi Allah ya kawo macyjinsu”. Ko da gogan ya ga tsohuwa na neman ta maida shi kurkuku, sai ya garzaya gun Sarki. Aka yi masa iso, ya shiga ya yi gai- suwa, ya ce da Sarki, “Kara na ke yi”. Aka ce, “fadi Karanka”. Ya ce, “Wata tsohuwa ce mai saida daddawa, na zo ba ni lafiya, na sauka a gidanta, na kawo kudi na bata ta ajiye, na ce ta riRa yi mana abinci, to yanzu na sami lafiya na yi shiri zan wuce, to sabo da ban zo na gaida ka ba, mu ko bisa al’adarmu, mutum kamar ni bai kamata ya zo garin Sarki kamar ka ba, bai je ya gaida shi ba. Sabo da haka na ce ta kawo fam hamsin don in zo in gaida ka, sai ta fasa kururuwa da kuka, ta ce bata san wannan magana ba”. Ko da fadawa suka ji haka, kafin Sarki ya yi magana, sai suka ce “Ta aika”. To da shi ne dalili yanzu ko bara ba ta yi. Da Sarki ya ji maganar fadawa da maganar fam hamsin, sai ya ce a je a kamo ta. Kafin haka an taso keyarta, tana kuka. Da zuwanta, Sarki ya ce, “Ke manufika, kukan me ki ke, ina kudi?” Tsohuwa ba ta san cikin magana ba, ta ce, “Wallahi duk shi ya debe mini kudin”. Sarki ya ce, munaflka, ki fiddo su duk inda ki ka sa su”. Aka kai tsohuwa kurkuku aka jefa. Sarki ya ce da M. Danye, “Je ka na neme ka in ta nuna inda su ke.” Da M.‘Danye ya ga ya fita lafiya, sai fa ya yi tunanin ya gudu ya bar garin. Sabo da haka zakara ya ba shi sa’a, ya bar tsohu- wa cikin wahala ya san dai ba abin da za’a samu. Yana cikin tafi ya sai ya yi aune da wani Raton Bar awo. Da bar awo ya ga M. Danye, sai ya ce, “Kai mai tafi ya, tsaya nan!” M. Danye ya ce, “Af, abin da mu ke wa wadansu, yau mu a ke wa, lalle in kana da rai ba irin canjin da ba za ka gani ba”. --- **Page 16** Ko da baraw o ya ji muryar M. 'Danye, sai ya ce, "Ko Malam 'Danye ne ?" M. 'Danye ya ce, "I, ai ni ne." Ashe wannan baraw o yaronsa ne da a ke kira Dabo. Dabo ya ce, "Ai, ni ne Dabo." M. 'Danye ya ce, "To tun da na same ka ba zan barka ba, sai mu tafi don ka ji abin da ya fito da ni". Ya kwashe labari duk ya gaya masa da irin wahalar da ya sha. M. 'Danye ya shiga tsubbu. Da M. 'Danye da Dabo suka runkuta har suka isa wani kauye mai kuraye. Da suka isa, sai M. 'Danye ya ce da Dabo," To wannan sana'a ta mu, sai mu ajiye ta, don lalle in mun ce, za mu yi ta sai ta hana mu samun biyan bukata, don kada a kama mu a daure, ko da ya ke dai dubarun yin sata suna da yawa, am- ma dai kai sa mini ido" Dabo ya ce, "To." A wannan kauye sai M. 'Danye ya ce da Dabo, "To zan zama Malami, zan rika yin duba." Abinka da wanda ya iya bakinsa ga shi wajen lalata ko Ja'iru na "Magana Jari ce" ya san da shi. Kafin a ce haka duk gari ya gama wani babban Malami ya sauka kusa da bayan gari wanda ba abin da bai sani ba. Kafin a ce haka gidan da ya sauka dare da rana cike ya ke da mutane masu son a yi masu duba, da masu neman taimako. Ran nan da dare, sai wata mace ta zo, ta ce, "Gafarta Malam, mijina ne ya mutu tun shekara bakwai, amma na rasa manemi, ina so ka bani laya ta samin bazawari, in ya samu ko wane iri ne zan baka fam ashirin". M. 'Danye ya dauki alkalami da takarda da tawada yana rubutun karya, sai ga wani Kure kisim-kisim ya biyo ta kusa da gidansu, yai tsaye ya yi kuka, wuu-wuu. Sai kurum M. 'Danye ya ajiye alkalami ya ce, "Ai sai biya, don kin ce ko wane irin bazawari, to wannan kukan da ya yi cewa ya yi, ina bazawarar ga shi." Mace ta ga M. 'Danye da gaske ya ya ke, sai ta ce, "Allah gafata Malam rabu da wancan bazawari, ni yi mani layar in samu in je gida lafiya". M. 'Danye ya ce, "Na fa rabu da shi, na yi maki aiki ya ko ci, ba ki biya ba" Mace ta ce, "Ai sai ka yi mani layar komawa gida lafiya tukuna" Da M. 'Danye ya ji ta samu, ya ce, "To ai sai ki biya ni, sa'an nan in shiga sabon aiki." Bazawara, don tsoron kada ya bar ta da Kure, ta biya shi fam ashirin chif. Sa'an nan ya ce, "To nawa za ki biya ni, in taimake ki, ki koma gida lafiya?" Suka yi tsada fam goma, ta biya. Sai ya ce da ita ta tsaya, ya shiga bukkarsu, dama akwai wata katuwar ganga, sai ya buga, gan- --- **Page 17** gan-gan-gan-gan. Ko da Kure ya ji karar ganga, sai ya zabura a guje, ya tsere. Bazawara ta samu ta tsere. Ran nan wani Bafilatani ya zo gun su M.'Danye, ya ce, "Ga- farta Malam "Na zo ka taimake ni, ka ba ni magani in yi shanu'. M. 'Danye ya ce, "Waiya, wannan ai babbar magana ce, sai munga Sarkin Aljannu". Ya tambayi Bafilatani yaushe za ka zo, muje mu gan shi. Bafilace ya ce "Ai gafarta Malam ni ko yanzu ka ce mu tafi sai mu tafi". M.'Danye ya ce, "To ka zo ne da gaisuwar Sarkin Aljannu, don ba a ganinsa, sai da jaka". Bafilatani ya ce, yanzu bani da jaka, amma zan je in saida shanu in kawo jibi." Suka yi sallama sai jibi. Da Bafilatani ya fita, sai M. 'Danye ya kira Dabo ya ce, "To jibi idan Bafilatanin nan ya dawo, za mu bayan gari, gun tabkin nan, da ma akwai wâni tabki gabas da gari. Kâi za ka shiga sagagin ciyawa na bâkin tabkin, idan na ce, "Yo Sarkin Aljan- nu, ka rika yin wata irin magana wanda ba za a fahinta ba". Komi dai na ce kai dai rika maganar da ba za a fahinta ba". Dabo ya ce, "To,". Bayan kwana biyu Bafilatani ya zo da jaka guda. M.'Danye ya amshi jaka ya adana, sa'annan ya đauko wata jakar dabam ya saka dutse, sa'annan ya ce da Bafilatani, "To tafiya, sai fa dare ya yi don ba a ganin Sarkin Aljannu sai da dare". Bafi- latani ya ce, "To." Da suka ci abinci, sai Dabo ya fara tafiya. Bayan an jima can sai M.'Danye da Bafilatani suka bi shi. Da suka isa sai M. 'Danye ya ce da Bafilatani, "To dakata can, zan je in jefa masa kudin, in yi masa sallama. Bafilatani ya dakata, M. 'Banye ya tafi bakin tabki ya ga inda Dabo ya ke cikin sagagin haku- kuwan bakin tabki, sai ya saka jaka cikin ruwa, abin nauyin dutse, saiji ka ke kundum. Sa'an nan ya komo gun Bafilatani ya ce, "To matso". Bafilatani ya matsa. M.'Danye ya ce, "Ka ji na ba shi kudin?" Bafilatani, yana rawar jiki duk tsoro ya kama shi zai ga Sarkin Aljannu, ya ce, "E, na ji fađawarsu". Sa'an nan M.'Danye ya ce, "To saurara", Bafilatani ya yi shiru kamar wanda ya mutu ko motsi ba ya yi, ya rura wa M.'Danye idanu. Sai M.'Danye ya ce, "Yo Sarkin Aljannu!" Sai Bafilatani ya ji an ce 'Mo', M.'Danye ya ce, "Ranka ya dađe, baRi mai sarautar duniya, wanda ka so da arziki ya samu, wanda ko ka Ri ya lalace, ka ga jaka guda ta kuđi?" Sai Bafilatani ya ji hausaboq.com --- **Page 18** an ce, “Bo, nako fato waja kudi”. Sai M. ‘Danye ya ce, “Ya ce a gaya ma ya ga kudi, ya kuma gode, ka kuma fadi wai bu katarka ko wace iri ce a duniyar nan”. Bafilatani da rawar jiki, ya ce “Shanu ni ke so ya taimake ni in samu”. M. ‘Danye ya ce, “Ran Sarki ya dade, yana so ka taimake shi da shanu daga taskarka ta shanu”. Sai Bafilatani ya ji an ce daga cikin tabki, “Kaliyori fem ma juma’a wakawari Kurunzun-zum” M. ‘Danye ya ce da Bafilatani ranar Juma’a in an fito daga Masallaci ya ce ka je yamma da kasuwa ka rika cewa Kurunzun-zum, za ka ga shanu sun kewaye ka, sai ka kora ka tafi, don sai ran Juma’a a ke bude taskarsa ta shanu, ya kuma ce a fada ma komi yawansu ya ba ka, kada ka ga yawansu ka debi kadan. To ran Juma’a ko kasuwar ke ci. Ka san Bafilatanin daji da shanu da jin an ce masa komi yawansu nasa ne, kada ya bar wadansu, sai ya c: da M. ‘Danye, “Ka fada masa komi yawansu, a sako su duk na iya kore su.” M. ‘Danye ya ce,” Ai dama ba za’a koro yadda za su yi ma kadan ba.” Bafilatani ya ce”, to na gode, amma yanzu ba ni da goron da zam baka.” M. ‘Danye ya ce, “Ai ni ba komi, sai lokacin da shanun suka zo hannunka, ka sallame ni”. Suka yi sallama a nan suka rabu. Bayan M. ‘Danye ya zo gida kadan sai ga Dabo. Dabo ya ce da M. ‘Danye, “To ai sai mu gudu don kada a gane mu”. M. ‘Danye ya ce, “Haba Dabo, ai Bafilatanin nan ko yana tsafi da bakar jaka, ya rabu da kudin nan, ba ko abin da zai same mu, shin kai ba ka iya duba ba, ai dama tilas ne, mai yin irin wannan kada ya yi fargaba, ya ko shiry i bakinsa, ai sai mu jira mu ga abin da zai faru ran Juma’a”. Ran Juma’a Bafilatani don doki, tun da hantsi ya yi ya je yamma da kasuwa ya zauna. Masayar shanu ko a kasuwar, yamma da kasuwar ta ke, sabo da haka sai gani ya ke shanu na wucewa, shi duk zato ya ke nashi ne suka fara zuwa, in ya ga mai Riba sai ya ce yauwa, irin wadannan na ke so a rika ka- wow a, in ya ga, ramamniya’sai ya yi tsaki, ‘Mhts. Yana nan ya Ki ko cin abinci don murna, har aka fito daga Masallaci. Ko da gogan ya yi sin fito daga Masallaci, sai ya tashi ya zabi fili babba wai doh kadi wakansu su rasa wurin tsayawa. Sai ya fara fadi, ‘kiuotzaii-ih, kiirun eumzum, kununzum-um ya yi ta fadi, ko kahobariya yanulo shiba, ya yi zaton ko bahaji bahasi ya yi la fadi da Riba, hik yanfazagaji ya, shiru ka kejiio Da Bafilatani --- **Page 19** ya ga haka, sai ya tafi masayar shanu, yana cewa, “Kai ku koro mini su nan, ku shanu ba ku ji ina kiranku, ko so ku ke in fada wa Sarkin Aljannu”. Mutane da suka ga haka sai suka zata taŵuwa ya yi, sabo da haka ba wanda ya kula da shi. Yana nan, in za a tafi da shanu, sai ya tsare, ya ce, “Ina zaku kai mini.’ A ture shi har ya fadi, a wuce, har magariba aka watse aka bar shi a masayar shanu, ba bu sanuwa ko daya. Da iyalinsa suka ga shiru suka biyo shi, suka same shi a ma- sayar shanu yana hauka, suka lallaße shi suka kai shi gida. Abu dai ya kai Baflatani ga turu, ga shi ya tabbata lafiyarsa lau, amma mutane har da iyalinsa sun ce shi mahaukaci ne. Da ya ga wahalar turu ga ba kudi ba shanu, sai ya ga gara ya bar zan- cen shanu, ko ya sami lafiyar turu. Sabo da haka ya yi shiru, aka ce ya warke, aka fitar da shi, ya haŵura. Da M.‘Danye ya sami labarin abin da ya faru ga Baflatani, sai ya ce da Dabo, “Da ma na gaya ma, ka ce wai mu gudu, to kan me, ba mu kai shi gun Sarkin Aljannu ba, bai ga an jefa kudin shi a tabki ba, bai kuma ji maganar Sarkin Aljannu ba, to mi nene laifinmu ciki, ko kana zato ya san kai ne ka ke magana ba Sarkin Aljan- nu ba ?” Dabo ya ce, “Wallahi gaskiyarka”. Sa’an nan suka yi shiri suka bar wannan gari. ## M.‘Danya Ya Shiga Neman Auren, Yar Sarki Bayan zakara ya ba su sa’a sun bar wannan gari da suka yi samu mai yawa, sai suka kama wata hanya ba su san inda za su ba. Suna cikin tafiya, Dabo ya ce da M.‘Danye, “Ashe dai hanyar sata yawa gare ta, da a banza mu ke bin dare, ka ga ta hanyar tsubbu, har gida, mu sace mutum ya kuma rika yi mana godiya, wai mun taimake shi.” M.‘Danye ya ce, “Ko da ya ke akwai abin da ya fiddo ni daga gida, amma duk da haka, kafin mu samu biyan bukata zan koya ma hanyoyi masu yawa wanda zaka ci abinci.” Dabo ya ga sun sami dukiya mai yawa kan hanyar tsubbu, sai ya ce, “Ai hanyar nan ta tsubbu ta fi ko wace.” M.‘Danye ya ce “Kai dai ita ka gani, sa ido mana, ka kuma yi aiki da abin da na ce maka.” A kwana a tashi rannan suka isa wani babbam bimni wanda ya fi duk birnin da suka wuce. Da suka shiga garin ba su zame ko ima ba sai fada. Aka yi masu iso gum Sarkin suka shiga. Bayan sun gaida Sarki aka tambaye su ko daga ina suka fida. M. Danye ya ce shi dan Sarkin Damas ne ya ji labatinsa ya tafo --- **Page 20** 3 don ya gan sa su yi zumunci. Da Sarki ya ji haka ya ce," Don me ka tafo a kasa ?" M. Danve ya ce rakuminsa a hanya ya mutu. Sarki ya amshe su da mumna, ya sa aka kaisu masauki. M. Danve ya ce da Dabo, "Kai dai in za ka shiga yaw o irin wannan, kada ka yarda ka rabu da sutura mai kyau, to ko Ina ka shiga duk karyar da ka yi da hannu biyu za a amsa, ka yi samu mai yawa, duk ko albarkar sutura mai kyau ce." Sarki ya sa aka yi ta kai kayan sauka iri-iri, sai ka ce wani gawurtaccen Sarki ya sauka. Gogan naka komi aka kai masu in ya tashi ba da tukuici, sai ya ba da fiye da abin da aka kai. Sarki ya ce, "Af, haka ba kon ke yi, ashe abin na yi ne." Aka yi ta kashe masu gara abin ba a magana. M. Danve ya samu shiga gun Sarki sosi, har ya zama da dare tare su ke hira, su biyu, Dabo na can bakin kofar gida yana rike da takalman M. Danve. Ran nan suna hira da dare, sai M. Danve ya ga 'yar Sarki ta fito, ya cewa Sarki, "Wannan fa ?" Sarki ya ce, "Af, baka santa ba, ai 'yata ce." Sarki ya

Chapter 2 of 9