Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 9
suka zo ma- raka suka Kwace 'yar dukiyarsu, suka bar su nan suka oe ko namun dafi ko wani abu in ya same ku mu ba ruwammu, mun --- **Page 54** dai kawo ku inda Sarki ya ce. Suka rofe su su ba su dan abin da za su yi guzuri ma, suka fi, suka zunzungure su suka ce yanzu ma mu kashe ku, ko don Sarki ya yi muku adaki. Suka yi shiru. Maraka suka dawo. Kashegari da safe maraka, suka zo suka ba Sarki labarin sun dawo, kuna sun kai su har bakin kasarsa. Sarki ya aika aka kira M.'Danye ya sanad da shi ya sa an kai su bakin kasarsa, wadan- nan ma su suka raka su, ga su har sun dawo, kuma sai ya yi ha- kuri ya zauna. M.'Danye ya ce shi kam ba shi da damar tsayawa. Sarki ya lallashe shi, ya ce, "To, shi ke nan ya yarda zai zauna". Da fadan haka Sarki bai jira wani abu ba, sai ya ce a tara masa hakimai da manyan fadawa da jama'ar gari. Da aka taru Sarki ya ce, to, don in sanad da ku zan nada M.'Danye hakimi yanzu. Madawaki ya tashi, aka kawo riga da rawani da alkyabba aka nada shi Galadimain Kurna. Sarki ya nada wani babbam mafadansa amintaccensa, ana ce da shi Kahiru Wazirin Galadima. San nan ya sa a kai Galadima gidansa. Duk manyan fadawa da hakimai suka rufe masa baya. Makada kowa sai fadin abin da ya fito daga bakinsa ya ke. Sarkin Kiran Sarki sai zuga Galadima ya ke, yana cewa : Babba Galadima abokin Mahiru, Allah ya ba ka mai nukura duk sai ya mutu. Ga uban Sarkin fada, aminin Mahiru. Mai hattara uban Kahiru, GinshiKi babban Jarumi, Saukarka Kurna munafukai sun gudu. Jama'a ku taya ni shewa, Galadima ya zo gare mu don shirya, A fada ma mutanen Gabas da Birnin Kurna, Ko su yi ladab ko su mutu. Na Mahiru mutanen arewa sun kawo caffa don duniya, Manya na Kahiru allurar dunkin duniya. Nan da nan sai kan M.'Danye ya yi gungurum, yana zareido, wai shi zaton shi ba ya shi duk duniya makada sun ruda shi. Bayan an kai shi gida jama'a duk suka yi mubayi'a, aka fita aka bar shi don ya huta, sai kuma azahar. Ya shiga gida kangá- meme wanda Sarki ya ba shi, amma ko karya ba bu a gidan, ga shi Galadima guda, amma gwauro, sai fa abin duniya duk ya rufe masa, tum ba main ya tuna wakar da makada ke yi masa. --- **Page 55** Yana tunani shi kadai, sai ya tuna da fa shi gawurtaccen bara- wo ne, shi da mai mulki ba amana, ya ga yau wai shi M. Danye shi ne har hakimi, kuma Galadima ma. Ya gode ma Allah da Ma'aikinsa. Da azaharaka kawo masa abinci daga gidan Mahiru, ya tashi ya ci abincin mulki ya tunbatsa. Ya je ya yi wanka ya yi sallah, san nan ya shiga kayan ado, dama ka san ba iya kwanciya aka fi kare ba, sai dai rashin abin rufa. Ya gama shiri ke nan, sai ga Wazirinsa Kahiru ya shigo, ya fadi, ya ce, "Allah ya ba ka nasara, jama'a sun taru, sai kai a ke jira don fadancin azahar". M. Danye ya yi shiru, yana jin abin kamar tatsuniya, wai amma da gaske a ke. Ya tashi, Waziri na biye dashi suka doso kofar gida. Nan ko soron da ya ke zai zauna cikinsa, an zuba kilisai da ku- jeru na zinari da dai sauran kayan alatu, in ka zo sai ka ce aljan- na duniya ce. Da zuwansa kofar gida, sai hayaniya ta kaure, ma- roka kowa na fadin abin da ya fito bakinsa, makada ko wani baya jin kidin wani. Can Mahiru da Malami abokin Mahiru suka doso gidan Galadima da jama'arsu, wuri nan da nan ya cika sai ka ce, ranar sallah. Aka shiga fa shagali tun daga wan- nan lokaci har magariba, riguna da kudi wanda Mahiru ya kashe da sauran abokan arzuka in aka ce, a tsaya a fada, sai a yi wani dan littafi karam. Aka watse aka ce kuma sai dare za a komo. Galadima ya ce, shi abin da ya gani gara, a bar wannan sha'ani sai ranar wankan sarauta, in mako ya kewayo, don ba a shirya ba. Sabo da haka Mahiru ya sa aka yi shela cewa 'Duk jama'ar gari mace da namiji wadanda ke jin kansu su shirya in rana ta kewa- yo akwai shagali kofar Galadima masu molo da masu goge za su zo da sauran makada! Sarki da ya ga Galdima gwauro ne, sai ya shirya za a ba shi kanwar Mahiru da aure, ita ko yarinya ce don ma ba ta isa aure ba, sabo da shi aka tsiri auren. Mahiru ya fada ma Sarki sai a yi biki ranar wankan sarauta don bikin ya fi armashi. Kafin haka, aka aika ma hakimai na waje takardu su taru don bukin diyar Sarki Baira'atu kanwar Mahiru. Aka kuma sanad da jama'a cewa dai kuma bayan wankan sarauta akwai kuma buki a ranar nan da Galadima da Baira'atu. To, Sarkin Kurna yana da wani mugun hakimi bawansa ma'- abucin sharri, wanda baya son kowa da alheri sai sharri, kai ko --- **Page 56** uwar da ta haife shi ma bai bar ta ba kan sharri bare wani, ana ce masa Ubandawaki. Ubandawaki shi ke neman Baira'atu da aure, kai abin ma kamar dai a ce an ba shi. Wannan abu da Sarki ya yi fa duk ya sha masa kai, ya rasa yadda zai yi, ya yi ma M. 'Danye sharri, don ya san da ya ke tauraronshi ke tsaye, kome ya ce zai yi masa na banza ne, sai ma ya komo kansa. To, amma duk da haka yana nan yana sa'ar zuci kullum kan yadda zai yi da M. 'Danye watau Galadima. Jama'ar gari ko, kowa ya tashi tsaye kan saye saye na kaya yadda ranar wanka sarauta za a ce ba ya shi. Da ya ke zamani ne tun na da, babu las da su karanmiski da kaya irin na yau, zamani ne da dunhu, da saRi, da kamayanke da kudi ke alRadari, mace ko wacce ka gani sai ka ga wannan da saRi' dan ubansa, ta lumko ta nufi gida, wannan kamayanke wannan dunhu wata zanen ku-di. Wajen sha'anin shuni ko, tun da a ke a Kurna ba a taBa ci-nikin shuni irin na wannan mako ba duk gidan da ka shiga sai ka iske kayansa tuli. Mata ko wace ta yi kitso an sa mata doka, sai ka ga an yaBe kan da shuni, kan yana walkiya, abin ba a ma-gana, ta ci fure bakin baRi Ririn, in ta yi dariya ba ka so ta rufe bakin ba. Zannuwa sai fesa musu ruwa a ke ana labta musu shuni, kai abin ya fi a rubuta. Jiya ba yau ba, ka san ba yau-aka fara yin karuwai ba, da ya ke karuwai ko a wane irin lokaci sun dan banbanta da matan aure, sa ko nuna wata 'yar hanya ta su wai wadanda suka ci gaba ne, to, ba su yaBe kansu da shuni ba, sai burbure, watau a kwaBa shuni da man shanu, a shafe kai bayan an yi kitso, su kuma sai ka ga kai na naso, ka dai san sha'anin mai in ya sha rana, bare ma an gama shi da wa-i abu. Lalle mazan baya sun yi irin nasu sha'anin. Wajen Runshi ko wasu matan torami har cinya don kakale, amma da ya ke irin matan da ba su sami isassun takalma ba, da wuya ka ga mace ba ta da faso-fason duk daBirinsa yai baRi Ririn don Runshi. Ko da ya ke mutumin yau sai ya ji wannan abu kamar duk ba wani abin sha'awa amma da yana cikin mazan baya, ba abin da ya ke so da gani irinsa, ko wane zamani da irin na shi al'amarin, lalle mazan baya sun ji irin nasu jin dadin. Maza ko, kowa ya duka baRa da fara-ta-gaske, da banten kudi ga ratayen layu ya shirya, an duba saRi na kirki an d'unka masu wani hula habar kada, wasu ko dado miya, ba abin da ake jira sai ranar shagali. --- **Page 57** Da ranar ta zo, sai aka shirya sha'anin buki na aure, a yi shi da safe, sha'anin wankan sarauta ko sai da azahar. Da safe fa tsakanin gidan Sarki da gidan Galadima ba abin da a ke sai shigi da fici. Aka daura aure tun da safe, aka shiga sha'anin kai goro, don amarya sai da dare za'a kawo ta. Bayan fa rana ta daga kadan sai duk mutane suka shiga gidajensu, suka shiga shirin bukin wankan sarauta. Azahar na yi, don wada'su ko ma sallah ba su yi ba, sha'anin buki ya ci masu rai, sai mata da samari suka fara fitowa zuwa kofar Galadima. Ko wace rariya ka duba, sai ka ga mace, ta fito tana rangashi, Malam zanen nan ya sha shuni, kan na wal- kiya, a hannunta ko ga wani dan kasko ba komi ciki sai fure, ga madubin ta a rike a hannunta. Ko wacce ta zo sai ta girka kujerarta, ta kame ta rika kara cin fure, kafin sha'ani ya kak- kama. Can sai ga mai goge da molo, karuwai sun danne masu baya, ka san sha'nin su karuwa, da ban yake, suna tafiyar kasai- ta, Magajiya na gaba sai kirari ake bata, wanda bai sani ba, sai ya zaci wata mutuniyar kirki ce, wannan suna Magajiya ko wani sunan sarauta ne, ba'a san sunan sarautar lalata ba ne. Ko wace ta zo ta kama wuri ta harde. Makada ko da 'yan kira, sai zuga su suke. Can sai fa maza suka fara barkowa daga gari, ka san su manyan al'amari ba da wuri su kan zo ba, sai abu ya fara kan- kama; kowa ka duba, ya sha baka da fara, ga hula ta saki ta sha shuni, ya ci goro, ya yi kumurya sai kukan kasa ya ke, ga bante na kirki, ga ratayen layu, Malam abin, abin ban sha'awa. Masu goge da molo, suka fara dan tabawa, watau irin wannan kafin abu ya kankama. Malam ka san namiji Rwazo gare shi in ya ga mace, nan da nan, wannan in ta yi ma mutumin ta fari, sai a jawo jaka, don lokacin nan ba a yarda a yi ajiye a ko'ina sai a zuba a jaka a Rulle, jakar ma ta fata ce, a jawo taro ko kwabo, wato aninai fa, a soma watsawa makada, shagali fa ya fara kankama, amma saraki ba su fito ba tukun. Can fa sai aka fara fiddo kujeru na zinarid a azurfa, ana gir- kawa, aka soma zuba kilisai da kayan shinfida iri iri, Malam nan da nan wurin ya gamu da kaya masu tsada. Da ya ke ka san M. Danye dan duniya ne, ya buga ko'ina ya san duniya, ya ga irin ci gabar wurare da yawa, nan ya sa an dora adursu don yi ma jama'a shayi, sabo da haka kafin ya fito duk an fiddo --- **Page 58** shayi cikin masuka, an aza moda kamar biyar cikin kowa ne masaki. Ka san fa lokacin ba kwano bare su kap, to na saraki ko aka zuba luduna, zanannu da wuta, Malam shagali fa in ba kai ban wuri. Can fa sai Galadima da sauran saraki suka yo waje gun da ake wannan bidi'a, kowa ya zo ya zauna a mahalinsa. Jama'a aka taso kowa ya yi gaisuwa. San nan Magajiya ta taso mata suka rufe mata baya, 'yan Rira ko sai kirari suke bata, suna cewa : 'Malka tafi da ruwa ta Waziriya, maganin kishirwar baRo, mai tafiya da girgijen ruwa 'yar Shehu.' Ta isa ta yi gai- suwa da sauran mata, san nan suka shiga fage suka yi ta tamba- yo kudi, su yi rawa in sun yi rangaji sai ka ji wani saurayi can ya ce a bata zane ta goge Rura, wadda ta gaji, ta koma ta kam. kan kujera Galadima ya sa, a dau moda daya. ta shayi a bata. Samari kuma kowa in mutuniyarsa ta shiga rawa, ta zabe shi, sai ya shiga ya kashe kudi, wasu ma har yar rawa sukan taka tare da wadda ta zabo shi, kai shagali dai har asuba. Da asuba san nan Galadima ya shiga rabon riguna da rawana ga marora da makada, afalla kowa ne makadi da maroRi ya samu abinda zai ci har wata a wankan sarautar Galadima, don dai ba'a taba shagali irin wannan ba tun da ake a Rasar Kurna, don nadin Galadima har ya fi nadin Sarki. Bayan an gama rabo, sai Gala- dima ya tashi ya yi ma jama'a godiya, wadanda suka zo don taya shi murna da wadanda suka yo aike da kuma wadanda ba- su sami damar zuwa ba, san nan ya sallame su. Fadar Galadima gun Sarki, abin har sai a ce ya fi Mahiru, ga diya an ba shi, ya kuma zama ba shi da gefe a gidan Sarki a ko wane lokaci. (To wannan fa ya sa sauran hakimai baKin ciki, ga shi baRo ya zo nan da nan har ya fi su mutunci gun Sarki, har an dau diya an ba shi ban da sarauta, ko da ya ke fa duk abin nan Mahiru aka yi ma in an lura. Ka san inda abin duniya ya taru babu halin gazawa, sai ko dama in ya zama mutum da- bi'arsa ce, ka san sha'anin karama gun Galadima ana yi ma a banza da wofi bare ga shi zai yi da tushe, duk wanda ya leRa soron ko bai shiga ba, ya maido kanshi waje yana godiya. Allah kada ka kashe mu sai mun ci duniya, mun dama yanda muke so. Hakimai al’amarin Galadima ba sassauRan abu bane, bare Ubandawaki, dama Sarkin sharri bare an taba shi. Ganin haka sai sauran hakimai suka ce a bar shi da Ubandawaki --- **Page 59** ishe shi. Ubandawaki fa ya shiga sharrinsa, in yau ya yi wan- nan ya ga bai ci ba, gobe sai ya yi wan can, ya rasa yadda zai yi da Galadima. Ran nan Galadima ya hau kilisa da marece, shi daya tak, yana yaw o cikin daji kusa da gari, sai ya zo kusa da wata babbar tsamya inda wata sanannyar macijiya take, duk mu- tanen garin babba da yaro ba wanda bai san ta ba, amma da ya ke Galadima baño ne, bai san ta ba. Ya saurara sai ya ji nishi daga cikin tsamiyar kamar na mutum wanda baya lafiya. Ya karya linzami ya zo gindin tsamiya sai ya ga wani kogo, ya leña haka sai ya ga macijiya girmanta ya yi na mutum ta nana de cikin kogo, ga wani Raton itace an feke shi an soka mata a tsakiyar jikinta, ashe ita ce mai wannan nishi. Da Galadima ya ga haka sai ya sabko daga kan doki ya zo ya cire mata itacen nan ; macijiya ta daga ido ta dube shi san nan ta maida kanta. Galadima ya hau ya koma gida ya nemo danyan nama ya sake sulalewa ya kawo mata. Haka ya yi ta yi ma macijiyar nan, kullum sai ya kawo mata danyan nama. Batun Ubandawaki ko ya na nan ya na ma M. 'Danye wato Galadima kulle kulle ka san halinsa dama sharri bare ta yi dalili wato an kasa shi. To a bisa al'ada tun da aka nada M. 'Danye Galadima in an tashi daga fadanci, sai a tafo gidan Galadima har da Mahiru, a zo a girka sabon fadanci. Wannan fa ya sa Ubandawaki samun kofa, ya shiga kullen wai Galadima yana so ne ya zama Sarki. Yau in ya fadi wannan gobe sai ya fadi wancan, tun Sarki da Mahiru basu dauka, ka san yau da gobe mai kare garin tsohuwa har ya zama sun fara dauka. Ka san ko itace da a kan sare shi da gatari, ba da an sara ba sau daya ko biyu sai ya fadi, a'a sai an sha sara, wato girman itace, yawan sara, haka kuma tsananin soyayya, tsawon sara. Wannan dada wa da Ubandawaki ya yi yana saran Galadima ya sa Sarki da Mahiru suka fara juya masa idon uban wani, sarauta guba ce, in ji hausawa. Galadima fa ganin haka sai ya fara shawarar ya yi tafiyarsa neman abin da ya fiddo shi. Batun macijiya ko kullum Galadima bai fasa kai mata danyen nama ba. An ce maciji baya tabo, amma wannan macijiyar Allah da ikonsa sai ta warke sarai wurin ya zama tabo. Rannan Galadima ya kawo mata nama, sai ya ji ta ce masa kai ko wane ne. Galadima ya bata labarin shi daga farko har --- **Page 60** Farshe, da kuma irin halin da ya ke ciki. Macijiya ta ce masa ta yi masa alkawali za ta taimake shi ya sami biyan bukata in Allah ya so. Ta ba shi labari cewa shekarunta dubu a wannan wuri, ba wanda ya taba cutarta, ita kuma bata cutar wani ba, duk ko mutane Rasar ba wanda bai santa ba. Wannan ko wanda ya soka mata itacen nan, ba shi ba, ko irin shi ma ba zai rayu ba, shi ko M. 'Danye da ya yi mata haka daga lokacin har zuwa Farshen zuriyarsa ba wanda maciji zai cuta. Ta kuma fada masa ita ma za ta tashi daga wannan Rasa. Ta umurce shi ya je ya shiryo gobe ya zo wurinta. San nan Galadima ya bata labari cewa shi ma yana son ya tafi ne neman abin da ya rabo shi daga gida, don ya ga mutanen sun sauya masa hali, kuma hankalinsa ya tashi, in ba abin da ya fiddo shi ya samu ba. Ta ce to gobe ka yo shirin tafiya ka zo da asuba. Galadima ya komagida ya fara debar kayan da zai yi guzuri na ci da na sawa. Sauran dukiyarsa ya ba matarsa, ya gargadeta kan shi zai yi tafiya amma Allah ya bata haKuri, in ta ga zata iya jiransa to ta jira shi, in ko ba za ta iya ba, to, ya bata hanya ta yi aure. Matar ta fasa kuka ta ce ita bata yarda ba ya tafi ya barta, duk inda zai shiga sai dai su shiga tare. M. 'Danye ya lallashe ta, ya fada mata cewa ba ya na nufin ya barta bane, zai tafi, amma sabo da ita zai dawo in Allah ya so. Ya dai bata magana har ta yarda. Amma duk al'amarin nan Sarki da Mahiru ba su san abin da a ke ciki ba. Asalatun fari M. 'Danye ya fita matar na barci, ya tafi gun macijiya, ya tarar ta shirya sai shi take jira ta fito daga cikin kogo. Macijiya ta ce masa wadannan duwatsu da ka ke nema ba inda za'a same su sai gabas can wajen karshen duniya a Samardala, sabo da haka sai mu nufi gabas in raka ka, lalle ba zan rabu da kai ba sai na ga bukatarka ta biya. M. 'Danye ya ce mai bani labari ma Samardala ya ce mani suke. Ta ce haka na yi zato, don na taba jin labarinsu. Ta ce, to ya hau hayanta ya runtse idonsa, ya hau ya runtse idonsa, daga nan M. 'Danye bai san abin da ake ciki ba, a duniya ya ke a lahira ya ke, oho, shi dai sai iska ya ke ji sha. Can sai ya ji ta tsaya, idon shi ya bude, gari tangaran ya duba taka sai ya ga sun zo wani wuri mai koramu, ga tsuntsaye iri iri, wurin ya cika ni'ima, amma ba mutum, ba namun daji sai' tsuntsaye kurum. Ya tambayi macijiya, "Wannan ko wace irin --- **Page 61** Rasa ce mai yalwa haka ba mutane ba alamun namun daji ? Ta ce, "Wannan Rasa haka Allah ya ha'icce ta ba mu mutane cikinta ba bu ko namun daji gata da ni'ima, amma ban da tsuntsayen nan Allah bai ba wani ikon zama cikinta ba". Tace masa ka ga daga wannan Rasar sai mu shiga Rasar da duwatsun da muke nema ta ke in Allah ya so, wato Samardala, wannan ko Rasar ba Rasar da ta fita ni'ima cikin duniya, mutum ko Aljan ba wanda ya tafa zuwa nan ya fita lafiya." M. 'Danye da ya ji haka sai duk tsoro ya kama shi, ya ce mata, "To ai gara mu yimu bar wannan Rasa tunda haka ta ke." Ta ce masa, "Kada kaji tsoron komi, ba bu abinda zai same mu in Allah ya so, ka san da abin da na taka tunda na sani haka ne, amma na zo cikinta, kwantar da ranka, mu je lafiya mu dawolafiya". Suna zauhe sai M. 'Danye ya ga Rasa ta tsage, sai ga wata jaka babba ta fito, macijiya ta sa bakinta ta jawo ta budc. Sai M. 'Danye ya ga tana jawo abinci iri iri. Suka ci har suka tunbatsa, san nan ta jawo butar ruwa suka sha. Ta ce da M. Danye sai ka yi barci ka huta don in mun tashi daga nan ba inda zamu tsaya sai gun duwatsun nan. M. 'Danye ya kwanta ya yi ta barci. Abin da ya afku a Kurna ko, matar Galadima diyar Sarki wadda itace kurum ta san Galadima zai tafi, tun da barci ya share ta bata falka ba, ba ma ta san har ya tafi ba, har gari ya waye rana ta fito tana barci don dare yai nisa bata runtsa ba don tafiyar mijinta. Har Sarki ya fito hakimai duk suka taru Galadima bai zo ba. Da ya ke an soma gajiya da shi don zugar Ubandawaki, sai Sarki ya ce a ci gaba da fadanci ya zo koyau- she, jama'a da yawa ba za su jira mutum daya ba. Majalisa ta ci gaba da sha'aninta har aka kusa tashi ba Galadima. Sai Sarki ya tura Mahiru ya je ya gano ko lafiya. Mahiru ya tafi ya iske gida a rufe, nan da nan ya nemo Ratti mabuga kare, suka gigibe Ryauran. Mahiru ya shiga ya buga kofar daki, san nan Kanwarsa ta ji, ta taso ta zo ta bud? Rofa, sai ta ga wanta. Mahiru ya tambaye ta, "Ina Galadima?" Yarinya bata yi magana ba, sai ta fashe da kuka. Mahiru ya tambaye ta, "Ko ya mutu ne?" Bata ce masa kanzil ba. Sai ya shiga daki bai ga Galadima ba, ya fito ya duba duk dakanun gidan ba Galadima ba mafarin shi. Ya sake zuwa gun yarinya ya tambaye ta, sannan ta ba shi labarin abin da Galadima ya fada mata jiya, amma ita ma ba ta san lokacin da ya tafi'ba. --- **Page 62** Mahiru ya kqmo ya ba Sarki labari, sai hankalin Sarki ya tuma ya ce, a je a buga gangami a hau duk inda ya nufa a maido shi kada a bari ya tafi. Sarki ya tambayi Mahiru ko bisa doki ya tafi, Mahiru ya ce, ba ya zato don duk dawakanshi suna nan,

Chapter 7 of 9