Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 9
lalle a Rasa ya tafi don ba zai ari dokin wani ba ga nasa. Kafin a jima kofar Sarki fa ta cika da dawakai. Sannan Sarki ya fito gun masu dawakai, ya ce su rabu hudu kowa, ne rabo ya nufi jaha guda, su bi inda duk Galadima ya tafi su maido shi. Mazaje suka fantsama cikin karkara da daji, aka yi ta neman Galadima har Allah ya gajishe su, wanda ya ga Galadima ma basu gani ba. Wasu da dare suka dawo wasu ko can suka kwana gun nemansa. Murna gun Ubandawaki ba sai an fada ba, ga shi zai auri matar da ya ke so. Jama'a duk da suka tafi neman Galadima suka dawo suka ba Sarki labarin dai ba su same shi ba, kuma duk sun tambaya ko wanda ya ganshi ba su gani ba. San nan Sarki ya sa aka rubuta takardu gun Sarakuna na kusa da na nesa, ya aike masu cigiyar Galadimansa. Duk aka bada cigiya ko'ina dai,.amma shiru ka ke ji. 'Diyar Sarki ko matar Galadima sai aka kwaso 'yan kayanta ta komo gidan Sarki kafin a sami Galadima. Galadima ko da shi da macijiya da asuba ta yi sai, suka miKa, macijiya ta yi alkawali ba inda za su tsaya daga nan sai inda duwatsun nan suke, suka yi ta yi, ko da ya ke Galadima da hawan bayanta ya rufe idonsa bai san yadda suke tafiya ba. Su ka yini suna tafiya su ka kwana, misalin azaharin fari, sai M.'Danye ya ji macijiya ta tsaya, da bude idonsa sai ya ga wuri maras lema ga duwatsu nan sun jera, ashe wurin ne. Macijiya ta ce masa sai ka sauko, Allah ya kawo mu wurin da muke nema, kuma Allah ya biya mana bukatar abinda ya tafo da mu M. Danye ya sauko, suka nemi inuwar gindin wani dutse suka sauka don su huta kafin su san abin da za su aikata. Macijiya ta sake yin kamar yadda ta yi da sai ga abinci ya fito, suka ci suka sha har suka Roshi, san nan kuma butar ruwa ta fito suka sha, ta ce ma M.'Danye, to sai mu yi dan barci don mu huta, san nan ka shiga aikin abin da ya kawo mu. Suka yi barci har gari ya waye, san nan suka falka. Macijiya ta sake fiddo masu abinci suka ci suka sha. San nan M.'Danye ya shiga shirin zuwa gun tsohon nan wanda za'shiryad da shi kafin ya shiga duwatsun nan. --- **Page 63** M. 'Danye ya i e gun dutsen nan na yamma tamkar yanda Faira'atu ta fada masa ya kutsa kai ya shiga. Ya wuce wannan kogo, ya wuce wancan, har-can Rarshe ya iske tsohon nan. gashi ya rufe jikinsa, yana tsugunne a cikin kogo na can Rarshen dutsen. Ko da tsoho ya ji tafiya, sai ya daga kansa, ya kore gashin fuskarsa, ya ce da M. 'Danye kai mutum ko Aljan?" M.'Danye ya amsa masa. "Mutum ne". Tsoho ya ce masa, "Ya- ya ka yi ka zo nan, kuma wa ya nuna maka wannan dutse da nake ciki?" M. 'Danye ya ce masa, "Labarin ka na ji tun da- ga Rasar mu, yau ko shekara ta goma rabo na da Rasarmu don kai, ba bu irin wahala da jin dadin da ban sadu da shi ba don gurin in zo in gan ka, ina ko fata zaka amshe ni da idon rahama, ka biya mani duk bukata wadda ta raba ni da iyalina wannan yawan lokaci." Tsoho ya ce da M.'Danye, "In Allah ya so zan biya ma bukatar, in kuma ka kiyaye alkawali don ko ka sani alkawali nauyi gare shi." M. 'Danye ya ce masa, "In Allah ya so ni mai daukar duk irin alkawalin da ka aza mani ne." San- nan 'tsohon ya ce, "To, je ka, ka yi yawa ka huta, sai bayan kwana biyu ka zo gare ni zan biya ma bukatarka." M. 'Danye ya fito ya koma gun Macijiya ya bata labarin duk irin abin da suka yi da wannan tsoho, kuma jibi bukatarsu za ta biya. M. 'Danye da macijiya suna zaune gindin dutse su duba haka yamma da su sai suka hangi mutum yana tafe, yana waRe wa- ke yana riRe da wata Ratuwar umara. M. 'Danye a ya ce da ma- cijiya wannan ai mutum ne, bari in tarye shi in tambaye shi abin da ya kawo shi, kuma ko zaunnan nan ne. Ya tarbi mutum da fara'a yana kira, har mutumin ya farga ya nufo M. 'Danye, ko da mutumin ya kusato sai M. 'Danye ya ga ashe Dabo ne yaronsa mamaki ya kama shi, amma Dabo bai gane ko wane ne ba, don yana zaton M. 'Danye ya rasu a hadarin da ya raba su. Da Dabo ya matso kusa ya ga M. 'Danye ne sai ya rungume shi suka fadi Rasa don murna, suka tashi M. 'Danye ya shiga gaba suka nufi wurin macijiya, da suka isa Dabo ya toge da ya ga abu himi guda, sai da M. 'Danye ya lallashe shi san nan ya yarda ya isa. M. 'Danye ya ba macijiya labarin Dabo, ta yi murna da Allah ya 'hada su da M. 'Danye har itu ma ta sanshi. --- **Page 64** San nan Dabo ya ce bari in ba ku labarin abin da ya afku kaina bayan rabuwar mu da M.‘Danye. Dabo ya ce, “Yayin da jirgi ya yi karo ya fashe, sai Allah ya mani gamo da katar, na samu guntun allon jirgi na mal'aye kwana na hudu ina yawo bisa ruwa, na yi gab da mutuwa a rana ta hudu, sai Allah ya kawo wani babban iska ba don shi ba da na hallaka, ya turo guntun allon da na ke bisa zuwa bakin gaba, na kama reshen wata itaciya wadda rabinta a ruwa rabi a waje, na sauka kan Rasa. Na dube gabas da yamma kudu da arewa ban ga kowa ba, sabo da haka sai na Ri barin gabar kogin, don kada in tafi ga rashin Rarfin jiki in hallaka don yun- wa ma da Rishirwa. Na riRa yin su ina samun kifi ina ci. Kwana na bakwai na ga dai jikina ya yi kwari, sai na yi shawara kan zan koma tun da na rabu da ubangida na, na ga dai kuma komawa gida gare ni ba sassauRan abu bane, tun da ya ke gashi mun rabu da abokin neman abin da ya fiddo mu, to gara ni in mutu garin nema. Wannan shawara ita ta Rarfafa mani zuciyata na ci gaba da neman abin da ya fiddo mu. Daga bakin kogi sai na yi gabas kwana na bakwai ina tafiya ban gamu da mutum ba, sai na tsinkayi wani Raton birni, sai na doshe shi. Da na zo bakin kofar birnin na sami wani saurayi, na tambaye shi sunan wan- nan birni, ya ce mani wannan Birnin Kutama ne, mai sarau- tar garin ko sunan shi Birgizau. Na tambaye shi sunan babban Malamin Garin ya ce mani Mallam Lukumanu, amma tsoho ne Rwarai, don ya shekara kamar dari da saba'in a duniya. Da na ji wannan bayani sai na kutse kai na shiga, na tambayi gidan M. Lukumanu aka nuna mani, na je na yi sallama aka ce in shiga. Na shiga na tarad da shi bisa buzun zaki na yi masa sallama ya amsa mani, ya umurce ni in zauna, na zauna. Ga litattafai sun kewaye shi, ba abin da ya ke sai karatu, duk tsufan wai bai hana shi karatu ba, kuma duk abin- da ya karanta dä bai ishe shi, lalle tsufa ba ya hana neman ilmi, kuma ilmi baya Rarewa. Ba mu gaisa ba sai da ya sa aka kawo mani abinci da ruwan sha, kamar ya san abin da na ke so ko nan, na ce gafarta Malam lalle ka san abinci na ke so, shi ya sa ko gaisawa ba mu yi ba sai da ka kawo shi, ya ce mani, ‘Aa’, ai abin da ya kyautu a fara ma baRo ke nan.” Wannan magana ta ilmi ta Rara shere ni, na ce kai lalle ilmi zan koya, in bukatata --- **Page 65** ba ta biya ba. Na ci abinci na sha ruwa na tunbatsa san nan muka gaisa, na kwashe labarina duk na fada masa, na ce, "Ni almajiri ne" Ya ko yi murna da zuwana gidansa. Ya sa aka kai ni masauki, wani gida ba kowa a ciki sai ni, ga shi kya- kykyawa. Abin da ya sa na sauka gidan Malamin nan don in shiga hanyar tusbbu, don na ga lalle ita kurum zan bi in samu abin guzuri. Ko da na fadi haka sai M. Danye ya fashe da dari- riya, ya tuna tusbubmumu na baya, yana zaton ba zan iya yin yadda za ta fishshe ni ba. Washegari na fita don in ga gari, na kewaya har kofar Fada. Fadar Sarki ta cika tab, ban yi wa kowa magana ba, ni kuma ba wanda ya yi mani magana. Na gama kallace kallace na, na komo gidan Malam muka yi hira, na komo gidan da aka sau- kan. Ashe bayan na tafo daga Fada, Sarki ya tambaya ni ko wanene, aka fada masa baRon Malami ne, a gidan M. Luku- manu ya ke. Jin haka fa ya sa Sarki ya dauke ni da girma kan lalle ni wani babban Malami ne. Ka san shi bakon Malami komin rashin saninsa sai ka ga mutanen gari sun yarda da shi fye da na garinsu wadanda suka san asalinsu, wannan shi ya sa cutarsu ba ta da wata wuya, sai dai in Malamin bai san han- yar cutar ba. Dare na yi sai ga manzon Sarki in zo Sarki na kira na. Manzo ya shiga gaba ina binsa har cikin gidan Sarki, na iske Sarki a wani shirayi bisa kujera ya na hutawa, shi kadai. Aka yi mani iso, Sarki ya ce, "In shigo." Na shiga na yi gaisuwa, Sarki ya amsa da girmamawa, daga nan na san ya tabbata Jahili sai in yanka shi duk yadda na so? Ya tambaye ni sunana na ce masa Malam Dabo ni ke, na ce Malam don ya Rara girmamani, sai macijiya ta ce; "Ai ko lalle Sarkin Jahilai ne, ai malamin kirki ba ya cewa kansa Malam ba, sai dai wasu su kira shi da haka." Na ce mata yo ba sha'anin jahilcin ba ke nan, in ni jahili ne to shi da bai gane haka ba, ai ya fi ni jahilci, kuma masu Raramin ilmi ma kan ce ma kan su malam, ni kai na na san ba ladabi ba ne mutum ya kira kansa da sunan girma. Sarki ya ce mani, "Abin da ya sa na kira ka, ina neman taimako gare ka, don akwai wani Sarki nan arewa da ni da ya fitine ni kowace shekara yana kawo mani yaRi, ya haddasa asarar rayuka da yawa da dukiya mai yawa. Kodanajihaka sai na ce da Sarki, ai wannan abu mai sauRi ne Allah ya baka nasara, amma zan kaika ga --- **Page 66** aljana za ta iya yi ma'duk yadda ka ke so a yi da shi kai ba shi ba ko wani ma in ya dame ka, ka fada mata za ta yi ma magani. Sarki ya ce mani, "To nan za ka kira ta ne, ko kuwa mu zamu wurinta." Jin haka ya Rara sawa na tabbata dai Sarkin nan duk inda jahili ya kai ya kai, duk fa maganata ban sa Allah ba, bai sani shi kansa aljanin bawa ne daga cikin bayin Allah, to dama ko na fadi haka don in san in wannan hanya za ta yiwu na ga ko zata yi. Ka san dai fadin aljan ba zai tasiri ba ga mutu- min da ke da cikakken imani da Allah ba. Na cema sa haba Allah ya ba ka nasara ai sai dai mu mu je ni da kai gunta, amma ba za ta zo ba, ma so dan tsuntsu shi ka bi shi da jifa. Sarki ya ce, "Yaushe za mu je ke nan ?" Na ce masa" Ran daren Jumma'a, a ran nan ko Lahadi ce, na fadi haka ko don in samu lokacin in shirya yadda zan yi da wannan Sarki. Mu ka yi sallama da Sarki na komo masauki. A wannan dare na kasa barci ina tunanin abin da zan yi in yi samu gun Sarki, kuma in fita daga Raryar da na shirya masa, ko da shi ke wannan ba wuya don in abin ya yi tsamari sai in gudu, na ko tabbata ba za a bi ni ba don ban ci ba ban sha ba, ko da shi ke na san mutane sun yi imani da masu duba har sun amince su iya fada masu cutar da ba su ji a jikinsu, amma su yar- da, duk su sakankance su na cuta da Malam mai duba ya ce. Wannan tunani ya sa dabara ta zo mani. Safiya na yi sai na fita daji na samo kaba. Na zo gida na shirya rigar kaba, da hula na sami irin jijiyar nan da ke fita daga itaciyar cediya; na zo bisa hu- lar na zuba kamar dai gashi, ga shi ya zuba har Rasa, na sami danRo na curashi kamar idanu, ka san danRo baRi'ne sabo da haka na sami jar garura na sa a tsakiyar wai nufi na aljani ba shi da wani fari a cikin idanunsa sai ja kurum kuma don dai jan zai fi bada tsoro, na dai yi siffar riga da kai yadda in mutum ya gani an sa ba zai ce mutum ba ne, bare ka san akwai ban gaskiya cikin zuciyar Sarkin, ta RaRa zai iya kawowa zan shirya haka, ga shi kuma na yi maganar zan yi wuridi, Da la'asar sai na fita daji da kayan nan, ina yawa har na zo gindin wata Ratuwar tsamiya mai wani kogo Rato, yau wa wurin dabo ya samu sosi. Na share gindinta, na kawo rigar nan ta kaba da sauran kaya na zuba, na komo gida. Da dare sai na kirawo wani yaro da ake kira Kodago, wannan yaro na san duk yadda na shirya da shi ba kuskure ga ba shi da tsoro, ga dabara kamar ya fi ni. Na fada masa kan ran alhamis idan magariba ta yi ina so ya zo zan --- **Page 67** kai shi wuri kaza, na dai bayyana masa kan in ya je wurin to zamu ni da Sarkinsu, abin da Sarki ke so ka kashe masa Sarkin nan da ya dame shi da yaRi, don na fada ma Sarki kai aljani ne sabo da haka duk abin da za ka yi kan kai aljani ne da magana da komi, na kuma fada masa yadda zai yi da kayan nan, wato ka da ya damu da ba ya gani wajen sa dankon nan a ido, a'a tun da ba wani wuri zai je ba, kuma in an gama zai fitar ya tafo kada ya damu. Su kuma kayan saura sawa zai yi. Irin abin da za ka fada don ni da kai mu yi samu, shi ne Sarki ya kawo kudi jaka biyar da dawakai goma da riga asharin, kuma a daren nan zai kawo, in ya kawo ka fada masa duk ka ba ni, kada ko ya kuskura wani ya san abin da a ka yi, in ko wani ya sani, shi zaka kashe ba wancan Sarkin ba. Da safiya ta yi sai na kai shi gu tsamiyar ya gani don ka da ran alhamis ya tsaya jira na, to dama shi kamar shedanin yaro ne, don ba inda bai sani ba cikin daji, ko kwatance na yi masa zai san wurin. Ya sa kayan nan na gani, kai mutum abin tsoro ne, wallahi sai ka ce aljanin da rana ma bare a ce da dare ne. Abin mamaki yanzu haka a na iya yin haka a cuci mutane. Sarki ko daga ran nan ba abin da ake kawo mani sai dabge in an kawo irin wannan abinci da safe, da rana ba irin shi ba za'a kawo, wai ina cikin wuridi, ko da ya ke ganin haka fa ba ka raba ni da casbi, amma ina wuridi ga wanda ya cika ciki da dabge sai barci, amma ko yaushe Jakadun Sarkin suka zo sai a yi sa'a na sa gabana gabas, ina riRe da casbi kamar dai wuridin na ke, ko magana ba su yi mani wai a na yi ma Sarki aiki, nan ko ba bu abin da na ke sai saRe saRen zuci, duk ba abin da ke zuciya ta irin dukiyar da na shirya mu samu, ko daya ban damu da abin da zai afku ba, bayan mun samu dukiyar, ko da ya ke na tabbata ba komi. Ran alhamis da magariba Kodago ya zo ta gida na, na ce masa maza ka tafi, gamu nan muna zuwa yanzu. Fitar Kodago ke da wuya sai ga Jakadan Sarki in zo. Jakada ya shiga gaba ina bi, da na je ran nan kafin mu gaisa sai da na yi addu'a ga Sarki ko da ya ke wai a zuci na ke karatu, to ka san fa ni duk in da jahili ya kai na kai, ko da ya ke mai masauki na watakila ya gane haka, don wata ran muna fira sai ya ce mani, M. Dabo, na ce gafarta Malam. Ya ce, 'Ai ka san baRara ko ?' Sai na ce masa, 'Matar wa ke nan ?' Ya ce, 'BaRara ta cikin Kura'ani ?" --- **Page 68** San nan na san wai yana nufin gandun mu ne ya shiga, sai na ce, 'To, da gaske, ai cikin Kura'ani ba inda ban ratsa ba'. Don ka da tone tonen ya yi zurfi ya gane ni sosai sai na yi sallama. San nan Sarki ya ce to ai sai mu yi harama. Na ce masa, "To abin da na ke so da kai, na farko ka da ka ji tsoro, don in ka fìrgita kashe ka za ta yi, kuma ka yi mata ladabi, ka da ka kuskura ka yi mata gardama, don yanzu haka duk abin da mu ke ciki fa ta sani har wannan magana da mu ke yi da kai duk ta sani, ta kan zo gidanka yawo don haka ta fada mani jiya, ba abin da bata sani ba naka. A lokacin da mu ke wannan magana da Sarki na tabbata Kodago ya dade da isa, ya kuma shirya sai mu kurum ya ke jira. Sarki ya tashi ya shiga gida ya shirya don ba zai tafi ba da kamar da an ganshi za'a gane shi ba. Sarki ya shiryo ya fito daga ni sai shi muka kama hanya har bayan gari. Muka kama hanya mai zuwa gindin tsamiyar nan. Ga mu nan, har kusa da gindin tsamiyar, don ka san ba mu je gab da ita ba. San nan na ce sai mu tsaya nan. Na share wuri na samo hakukuwa na hura wuta, san nan na yi addu'a ga shi wuri duk ya haske fau da hasken wutar nan. In duba haka sai na ga Kodago ya fiddo daga cibiyarsa zuwa kansa daga cikin kogo, sai na fadi na yi gaisuwa. Ko da Sarki ya ga haka sai ya fìrgita zai ruga, na rike shi, na ce in ka kuskura ka ruga za ta kashe ka, fadi ka yi gaisuwa maza, Sarki ya fadi yana rawar jiki duk tsoro ya kama. San nan na ce da Kodago ranki ya dade muna tare da Sarki ne, ya na neman taimako, sabo da wani Sarki nan arewa da shi ya fitine shi da hallakar da rayuka da haddasa musu barna ko wace shekara, ko dai ki kashe masa shi, ko kuma in ya zo ya ki ka da ya samu nasara. Ko da Sarki ya ji haka sai ya ce, "A'a, a dai kashe shi duniya ta huta da wannan masifa. Sai Kodago ya ce," To shi ke nan, amma Sarki ya ba da jaka biyar da doki goma da riga asharin yanzu yanzu na ke so in gansu, kuma ya kawo sa don a yanka mani in sha jinin. Sai na ce ma Sarki, "To ka ji abin da ta ce, sai ka yi sauri maza ka kawo yanzu." Sarki ya koma gida, kafin a ce haka har ya zo da duk- kan abubuwan da aka fada masa. Ya zo ya ce da ni, "Ga duk abin da aka ce in kawo na kawo". Na tashi kaimar da gaske na kira aljana, ta amsa kamar zuwammu na fari, na ce ga kaya nan da ki ka ce Sarki ya kawo. Kodago, wato aljana, ya ce, "Sai a --- **Page 69** yanka mani san in sha jujin, da naman da sauran kaya ko duk na ba ka iMalam". Sai na zube kasa, ina cewa godiya ni ke ranki ya dadc, l.odiya ni ke, Allah ya sa ki mallaki aljannun duniyar nan. San nan kuma ta ce, "Ka fada ma Sarki kada in ji ko da wasa ya fada ma wani abin nan da mu ka yi da shi, daga nan ko zuwa kwana goma sha hudu zan biya masa bukatarsa". Na ce, "To ka ji Sarki". Sai ya ce, "Wane ni, ai wannan magana ba wanda zai ji ta". San nan mu ka yi sallama ni da Sarki gunta. Sarki ya sa a ka kai mani duk kayan nan masauki na. Can bayan na yi sallama da Sarki, na zo gida har na huta sai ga Kodago. Na ce, to mai ka ke so ?" Ya ce, "Ai ni ba abin da za ka ba ni sai kudi." Na kawo jaka biyu na ba shi, sauran kaya ko duk sai na ba mai masaukina su, na dauki doki daya ingar- ma, da dan abin da zan yi guzuri, don ba hali in tsaya kwana sha hudu ta matso ban yi nisa daga garin ba. Daga nan sai M.'Danye ya ce, "Ashe ba ka kware da tsubbun na damfara ba, ai ba abin da zai hana ka yi kwana sha hudu a garin, don Sarkin fa ya tabbata aljana ce ta yi masa wannan ba Kodago ba, to ai kwana goma kurum za'a yi sai in koma gun Sarki in ce, ai aljana ta ce wai kai za ta kashe, don ta bincika taga kai azzalumi ne, na yi ta ba ta hakuri, amma har yanzu ta na cikin hushi. To, lalle cikin Sarki da jin wannan magana zai yi kuka, daga

Chapter 8 of 9