ya zo don su gaisa. Bayan sun gama gaisuwa, ya tambaye su sunansu, M. ‘Danye ya ce shi sunansa ‘Birnin-rai’, wannan ko ‘Birnin-lun-fashi’. Malami ya yi ta mamakin irin wannan sunaye, ya tamba-ye su ko mai ya sa ake kiransu da wannan sunaye. M. ‘Danye ya ce masa duk ran wanda ya mutu a lahira a hannunsa ya ke, in ya ga dama sai ya maida wa mutum. wan nan ko lunfashi a hannunsa ya ke, shi ya sa a ke kiransu da wan nan sunaye. Ya ce abin da ya sa muka zo garinku, don ku Malamai ne, in kuna son wata karuwa sai mu kara ku.
Da Malami ya ji haka bai tsaya ba sai gun Sarki, ya ba shi labarin irin baŗin da ya yi. Da Sarki ya ji haka, sai ya ce ya je ya zo da su. Malami ya zo gida ya fada ma M.‘Danye Sarki na nemansu. M.‘Danye ya ce, “Ai sai dai in je, don Birnin lunfashi in ya je gun Sarki sai Sarki ya mutu.’
Da jin haka sai Malami ya ce to ai sai dai mu tafi da kai, tun da ya ke haka ne. Da Malami da M. ‘Danye suka dunguma sai gun Sarki. Sarki ya yi ma M. ‘Danye maraba, suka gaisa, san nan ya ce, ‘Wannan Malami ya bani labarinku shi ya sa na kira ku. Ina dan uwanka ?” M.‘Danye ya ce, “I, dama abin da ya sa na ce shi ya zauna gida don in ya je gun Sarki, Sarkin baya kwana uku sai ya mutu, don zai đauke lunfashinsa.”. Ko da Sarki ya ji haka, sai ya ce, “I, gaskiyarka, gara ya yi zamanshi.
Sarki ya ce da M.‘Danye dana ne ya rasu, ni ke so ka taimake ni ka maida masa ransa. M.‘Danye ya ce, “Inji dai bai yi tsami ba,” Sarki ya ce, “Ai yau ne ya rasu.”’ M.‘Danye ya ce to sai ka gama ni da wani amintaccenka mu je gun kabarin in tafo ma da shi.
---
**Page 30**
Sarki ya gama M. Danye da wani amintaccen yaronsa suka tafi. Da suka je inda aka binne yaro, wato wurin da ake binne Sarakunan garin da ’ya’yansu, sai M. Danye ya ga wani babban kabari kusa da sabon kabari na yaron nan. Ya tambayi yaron Sarki, wancan babban kabarin fa. Yaron Sarki ya ce, “Na uban Sarki ne, wato kakan wannan yaro da zaka tasa yanzu”, M. Danye ya ce, “To”.
Da suka isa gun kabarin yaro, sai M. Danye ya zo wajen kan yaro, ya ture kasar ya sunkuyar da kansa, ya rika cewa, “Ya ya muke, lafiya lau,” can kuma sai ya fara cewa, “To,” da an jima kuma sai ya ce “To”, can sai yaron Sarki ya ji M. Danye na cewa, “Haba haka ai ba za ta yiwu ba, ni ai ba a ce mani ba” Sai ya ga ya maida kasa da sauri ya rufe, ya tashi da fushi ya ce da yaron Sarki mu tafi.
Da suka isa yaron Sarki ya shiga gun Sarki ya fada masa sun dawo. Sarki ya ce kun tafo da shi, yaronsa ya ce, “A’a.” Sarki ya ce, “To ya ya aka yi?” Yaro ya ce, “Na ji yana cewa ba zata yiwu ba na ii kuma suna magana da yaron.” Da jin haka sai Sarki ya yo waje. M. Danye ya shigo. Sarki ya ce ya ya. M. Danve ya ce, “Na je, har zamu tafo da shi, ashe akwai wani kakansa da ya mutu.” Sarki ya ce, “I, ai ubana ne.” M. Danye ya ce, “To tare na iske su suna fira, kakan ya zo yana masa barka da zuwa, yana tambayarsa labarinku.” Da muka gaisa na fada masa ka roke ni arziki, kan in maida masa ransa mu tafo tare sai kuma shi ma kakan ya ce wai ba na bar shi ba, to shi ya sa na ce, ni ba zan tafo da shi ba sai na zo na fada, don ko suna tare da yaro, da na ce yaron ya fito shi zai ma riga shi fitowa. Kuma yanzu abin da ka ce, shi zan koma in aikata. Idan kana so su duka a kawo su, to mu koma yanzu a tafo da su. Sarki ya ce to bari in yi shawara.
Sarki ya aika a kira masa Waziri da Liman don su yi shawara. To kafin mutuwar wancan Sarki, shi wannan Sarkin shi ne Waziri. Shi kuma Waziri Bafade ne ku'um, ba ma wanda ya giga ba.
Waziri da Liman suka iso. Sarki ya kwashe labari ya basu, ya ce kuma mai suka gani. Waziri ya ce, “Allah ya ba Sarki nasara, idan kana son tshonka ya dawo duniya, mu ba mu ce ma, kada ya komo ba, amma kun san dai tilas ka koma Waziri ba Sarki ba, ni ko na koma fadanci na kamar da.” Liman ya ce,” Wannan magana ta Waziri gaskiya ce.” Ko da Sarki ya ji
---
**Page 31**
haka, sai ya ce da M. Danye, "Mun yi dai hakuri, har shi yaron duk a bar su, mu in mun mutu, wa zai yi mana irin wannan Rokarin." Kuma shi baba ai ya ci rabonsa, ya ya, ya ke so kuma ya dawo ya ci rabon wani." M. Danye ya ce, "To zan je mu tafo da Birnin lunfashi don ka sallame mu." Ko da Sarki ya ga abin da M. Danye ke so, ya sa shi ma ya mutu, sai ya ce, "A'a fadi duk irin abin da ku ke so yanzu in yi maku, amma kada birnin lunfashi ya zo." M. Danye ya yanka dukiya mai yawa Sarki ya kawo ya bashi har aka gama shi da masu daukan masa.
Da M. Danye ya isa masauki, da Dabo ya ga dukiyar da ya samo, sai mamaki ya kama shi, ya ce, "Lalle M. Danye sai a barka." M. Danye ya bashi labarin yadda suka yi da Sarki. Ya ce da Dabo, "Amma ina jin tsoron kada a kure mu don garin nan fa Malamai ne." Dabo ya ce haba, "Ai ni komi ka yi, gaba na ba ya faduw a, na san dubarunka ba su kare ba har a kureka". M. Danye ya ji an yabe shi sai ya ce, "Kai dai bari mana."
Labari ko ya cika gari kan wasu baki sun zo, wanda za su iya raya wanda ya mutu. Da Malaman gari suka ji sai suka ce, ba abin da ya fi da mu tsaya muna ja in ja kan sha'anin addini, gara mu je gun bakin nan, su fahintar da mu wadanda ke kan hanya ta gaskiya.
Sai suka taru su duka da wanda ake jayayya, suka tafi masau- kin su M. Danye. Da suka isa Dabo ya fito ya tambaye su ko lafiya. Suka safnad dashi abin da ya ke tafeda su. Dabo ya shiga ya ba M. Danye labari, yau fa karyarsu ta kare, ga Malaman gari sun zo kan a yaye masu jahala kan sha'anin addini. M.
Danye ya ce, "Ba komi ce su shigo."
Malamai suka shigo suka gaida M. Danye don ladabi kamar su nutse kasa, wai sun zo gun mutanen Allah. M. Danye ya amsa, ya tambaye su, "Ko minene da'awarsu?" Malamai su ka ba shi labari kan kansu ba hade ya ke ba kan sha'anin addini, wadannan na zargi wadan nan kan yadda suke tafiyar da addi- ninsu ba daidai ba ne.
Ko da M. Danye ya ji maganar su, sai ya ce, ashe ku da duk jahilai ne, ni ina zaton ku Malamai ne, shi ya sa har na zo gun- ku ashe ma ba ku san yadda za ku bauta ma Allah ba.
Malamai suka ce, "A'a, ai mun san yadda ake addini, don muna salla muna azumi, muna zakka, har wasu cikin mu masu
---
**Page 32**
hali kanje hajji, tamkar yanda aka ce a yi cikin Kura'ani da Hadisin Annabi Mai tsira da Aminci da na Halifansa Rashidai.
M.'Danye ya ce, “Af da kun san haka, ku ke jayayya, to kan me kuma ?” Malamai suka ce, “Rikicin kan maganar Shehuna ce, wadanda ke bin wadannan.”
M.'Danye ya ce masu, “To mine ne ya wajibta kan mutum ya yi ?” Suka ce, “Ya yi farillai da aka aza masa, kuma ya bi sunnar Annabi, sai kuma abubuwa wadanda suke abin so ga mutum ya yi su, sune wadanda muke rikici.kansu.”
Da M.'Danye yajiinda duk suka nufa,'kuma su da kansu, sun bashi amsa, sai yace, to ku duka Allah ku ke bauta ma, kuma Annabi guda shi ku ke bi, kan Musulinci, suma ko Shehu- namanyan haka ne, kuma daza ku iya bin yadda shehuna suka bi kuma sai ku zama kamar su, to kuma kan me, har za ku yi jayayya. Ku tuna fa ba farilla ba ku ka bari ba, ba sunna ba, to duk wanda ya ke bada farilla yana bin sunna mai zai sa a zarge shi. Suka ce, “Lalle gaskiya ne ba’a zarge shi ba.”
Duk suka ji magana#M.'Danye suka bi, ba su kara jayayya da junansu ba. Amma amsa da M.'Danye ya basu, ba wata amsa ba ce ta ilmi, domin su ya tambaya suka ba kansu amsa, amma don sun yarda da shi mai sani ne, ba su gane ba.
Amma Sarkin garin shi hankalinsa duk a tashe ya ke, don kada ya hadu da Birnin lunfashi. Sabo da haka Sarki ya sake aikowa da dukiya mai yawa a kawo wa su M.'Danye sallamarsu don su tafi. Da M.'Danye ya amshi dukiya, sai ya ce, “A fada ma Sarki za mu zo mu yi godiya. Sarki ya ce, “A fada masu, shi ke nan ka da su zo ya hutad da su.” Amma M.'Danye don ya burge Sarki sai ya Ki.
Fada ta cika sai. M.'Danye da Dabo suka shirya suka doso fada. Da Sarki ya hango su fa, sai aka ga ya tsallake Karaga ya yi cikin gida da gudu. Mata suka ga Sarki a guje ya shigo gida kowacce sai ta shiga daktinta ta rufe. Ko wane daki Sarki ya nufa sai ya ga a rufe, jin tsoron kada su shigo, sai ya buda runbu ya shiga.
Su M.'Danye sai suka koma gida suka shirya suka bar garin. Amma fadawa ba su san dalilin da ya sa Sarki ya shiga gida a guje ba. Sabo da haka suka bi Sarki har cikin gida, aka taras gida ba kowa fakuna duk a rurrufe. Suka yi ta bugawa, mata na zaton abin da ya koro Sarki ne ya zo ya ke buga kofa, sai
---
**Page 33**
kowacce ta yi shiru kamar ta mutu. Fadawa na dubawa haka sai suka ga kan Sarki daga runbu ya leko. Suka ruga suka dau- ke murfin runbu. Ko da Sarki ya ga haka, sai ya fara tuba yana zaton su Birnin lunfashi ne, san nan fadawa suka jawo shi aka lallashi shi ya fito, da ya tabbata ba su nan. Da Sarki ya fito sai ya aika 'yan rahoto suga ko su M. 'Danye su na nan. Aka je aka taras sun tashi, san nan hankalinsa ya kwanta.
## Su M. 'Danye Sun Yi 'Batan Kai
Da su M. 'Danye suka fito daga Surbadu, sai suka yi kudu ba su san inda suka dosa ba. Suna cikin tafiya sai suka fara ganin itatuwa manya manya, da ganin haka sai M. 'Danye ya ce da Dabo, "Na tabbata mun bata don wannan wuri ba shi kama da kasarmu, bare a ce ma a samu hanyar Langeri". Dabo ya ce masa, "Amma sai mu je, mu samu gida ko gari a gaba, to sai mu tambaya hanya". M. 'Danye ya ce, "Haka ne".
Suna cikin tafiya sai suka shiga wani babban daji. Suka yini suna tafiya ba su kure dajin ba, kuma ko sawun mutum ba su gani ba bare gida. M. 'Danye ya ce da Dabo gara mu yi ta tafiya a komin dare ko mun fita daga dajin, don in mun ce mu tsaya sabo da dare sai wani hadari ya same mu, domin daji irin wan- nan abin tsoro ne, ko namun daji ko wani abu sai ya hallaka mutum. Suna cikin tafiya sai suka hangi wuta cikin daji can. Dabo ya ce da M. 'Danye, "Gara mu je gun wutar can, don lalle mutane ne". Sai suka nufi inda wuta take. Da suka isa sai suka ga wani dan gida bisa wani dutse. M. 'Danye ya ce, "Ai sai mu hau". Suka hau suka zo kofar gidan suka yi sallama, shiru, suka yi ta sallama, can sai ga wata kwalwar yarinya, wadda do- min kyawunta suka ce lalle wannan aljana ce. M. 'Danye da ga- ninta yana rawar jiki, ga zatonsa, lalle in ba aljana ba ce, to Zulkaratu ce, watau ya sadu da biyan bukata ba tare da zato ba. Ya ce da Dabo kai lalle wannan Zulkaratu ce, aljannu suka dau- ko ta suka kawo ta nan. M. 'Danye da Dabo suka fadi kasa suka gaishe ta. Yarinya ta ce, "Ku mutane ko aljannu ?" M. 'Danye ya ce, "Mutane ne". Yarinya ta tambaye su dalilin zuwansu nan. M. 'Danye ya ba ta labarin cewa diyar ubangidansu ce, ana ce da ita Zulkaratu ta ba ce suka fito nemanta, ya fadi haka don zaton wai ko ta ce ai ni ce. Sai yarinya ta ce ai ko ni ma na ji la- barinta gun mijina. M. 'Danye ya tambaye ta ko wane ne mijinta.
---
**Page 34**
Ta ce, ai aliani ne. Ko da suka ji haka sai suka dauki makyal- kyata. Ta ce ka da ku ji tsoro don ni mutum ce kamarku.
Ta ce, ni diyar Sarkin Gadangama ce, ubana babban Sarki ne a Rasar Gabas can wajen Rarshen duniya, ya mulki dukiyar da ba a zaton akwai Sarkin da ya taba mallakarta ba. Wata rana ne, na kwanta barci a gidan ubana a bayan gari, da na farka sai na ganni cikin wannan gida, wani aljani ya rungume ni, na zabu- ra a frigice, sai ya ce da ni, kada in ji tsoro. Na tashi zaune na dube shi na fasa kuka. Ya ce mini, “Ban dauko ki ba don in cuce ki, sai don ina son ki, kuma zan rika kawo maki duk abin da ki ke bukata, kuma zan kai ki yawo duk inda ki ke so, amma banda Raskru”. To, da fari duk na rude ma sa ya rasa abin da ke masada di amma daga baya da na ga babu Sarki sai Allah, sai na yi hafuri, muka fara fira da annashuwa. Ashe wannan aljani dan Sarkin aljannu ne. Yau ko shekara ta uku a nan, sunana ko Faira’atu.
M. ‘Danye ya tambaye ta dalilin da ya sa ta san ZulRaratu. Ta ce dalilin ko da ya sa na ji labarinta, wata rana ya dawo daga yawo, ya ke ba ni labarin ya ga matar da ta fi ni kyau, ya ce ba don kada ya yi mini butulci ba, da ya dauko ta. Ya kuma bani labarin tana.da masoya da yawa. Har ma ya ce mini akwai wani Sarki da ya neme ta amma uban ya ce ba zai ba shi ba, amma Sarkin ya shirya a sato ta, to amma ba za ta satu ba, sai dai a sha wahala a banza, ko wadanda za su sato ta, ko sun sato ta, za a kama su a kashe a banza. Ta ce, wannan shi ne dalilin da ya sa na yi mamakin yadda aka yi aka sato ta. Kuma mijina ya ce ubanta yana da wani takobi wanda duk duniyar nan ba mai irinsa, wanda ko da Sarkin aljannu sai su gwabsa, wannan ma yana cikin dalilin da ya sa bai sato ta ba, ni ga zato na. Na ko tabbata in har an sace ta, to ubangidanku yana can yana hallaka rayuka, don na sa ita kurum ya mallaka, ga shi attajiri jarumi kuma, kuma mijinta wanda na ji ya zama Sarkin duniya bayan an yi bikin shi ma ya dinga yaRi, ko ku an aikoku ku riRa rahoto ne. M. ‘Danye ya ce, “Mu kam mun tafo in mun same ta mu tafi da ita, in ko abin ya fi Rafimmu, to mu koma mu fada, a zo a amshe ta, ko a kashe iyaven gidammu wurin amsar.
Sa’an nan Faira’atu ta ce musu, “Amma wata ran muna labari da mijina ya fada mini, da mutanen nan da za su sace ta, sa iya zuwa Rasar Samardala, gun wasu duwatsu goma sha biyu, a
---
**Page 35**
hausabook.com
---
**Page 36**
wannan tsoho na iya muku hanyar da za ku same ta”.
Da suka gama wannan magana da Faira'atu ta shiga ta kawo musu abinci suka ci, suka tunbatsa. San nan M.'Danye ya ce, "Suna so su kwana da safe su wuce". Ta ce musu, "Idan Mai- gidana ya iske ku nan duk zai hallaka ku, amma zan kai ku wani wuri can, ku kwana da safe ku wuce". Da M.'Danye ya ga dogu- war tafiya ta same su, sai ya ba ta duk dukiyarsu, ya ce ta ajiye musu sai sun dawo. Ta amsa, san nan ta kai su wurin kwana.
Bayan sun shiga 'yar bukkar da ta kai su su kwanta, sai M 'Danye ya ce da Dabo, "Yaya za mu yi, mu tafi gun duwatsun nan ko mu nemi hanyar Langeri mu tafi". Dabo ya ce, "Ai gara mu mutu gun neman wadannan duwatsu, tun da dai za mu samu abubuwa k'amar yadda ta zana, ai sai mu zama sarakuna, in mun samu Zul'karatu ko kai ai sai ka aure ta, daman ai kai ma kana so, don dai an ce abin da ba ka samu ba gama shi da bana so". M.'Danye ya ji Dabo ya kanbama shi, sai ya ce, "Wallahi Dabo gaskiyarka".
Kashegari suka tashi, suka je gidanta don su yi mata sallama. Ta fito suka gaishe ta, suka ce, “To zamu tafi neman duwatsun nan, sai dai mu mutu a,nema.” Ta ce, “To na hore ku, kada wani abin duniya ya tsaida ku, kuma akwai wani Sarki kan hanya da zai kama ku ya daure, to hanyar da za ku bi ku ku buta, akwai ranar da shafon Sarkin zai kamo kifi ya kawo, ku ce kada Sarki ya ci kifin don samantacce ne, da kuma wani zai ci sai ya mutu nan take. Kuma komin fadar da kuka samu ga Sarki, kada ku tsaya a gari, ku tafi neman abin nan. Kuma kada ku auri mace bazawara, kada ku yi abuta da mafadan Sarki, ko attajirin da bai tafa gadon arziki ba daga sama ya same shi.” Suka ce, “To,” Suka dur kusa suka yi godiya suka kama hanya.
Kwanan su bakwai suna tafiya cikin dajin nan, san nan suka shiga karkara. Suka kwana uku suna tafiya cikin karkara, san- nan suka iske wani babban birni, suka taras amma babu mai shiga ko mai fita daga cikin birni, abin ya ba su mamaki, M. 'Danye ya ce, ai sai mu shiga. Da shigar su sai suka iske cikin birnin babu daki ko daya, mutanen cikin birnin ga su nan a fili tiRa tiRa, don kowanne mutum ya fi giwa girma, wajen tsaw kowanne bai fi zira'i uku ba. Ashe girmansu ya hana su yin dakuna bare fita daga garin. Duk mutanen garin kowa yana
---
**Page 37**
da shafo, wanda ya ke masu farauta tsuntsaye, su ne abincinsu, abin mamaki shafunan kuma sun saba, da sun kamo tsuntsu ba za su nufi kowa ba sai ubangidansu, kuma ba za su ci ba. Ko da suka ga su M. 'Danye sai suka yo ca kansu, su zatonsu sun sami wani nama ne. Suka kama su suka kai gun Sarkinsu. Sarkin ya sa aka zuba su cikin wani keji da ya ke zuba tsuntsa- yen da aka farauto masa kafin a yanka.
Ran nan Sarl in yana zaune sai kurciya ta zo ta dira, da ga- ninta sai ya saki shafons , shafo ya kai mata sura, ta tashi bai same ta ba, ya bita sama, da ya dawo sai aka ga shafo da kif. Sarki ya yi al'ajabi, ya ce ba zai ci ba, sai ya tambayi Malamai. Aka tara Malaman gari Sarki ya basu labarin wannan kifi, ya tambaye su ko a ci, Mallamai duk suka ce mai zai hana a ci. M. Danye daga cikin keji ya ce ai ba'a ci ba. Da Sarki ya ji maganar dabba ta cikin keji ya ce a kawö' kejin. A ka kawo su M. 'Danye da tsuntsaye da suke tare Sarki ya tambayi M. 'Danye dalilin da ya sa ya ce kada ya ci wan nan kifi. M. 'Danye ya ce, "Don idan har ka ci wannan kifi zaka mutu nan take don samantaccen kifi ne, in kana so ka jarraba, a sami wani wanda kisa ya kama a bashi ya ci, zai mutu." Sarki ya sa aka kawo wanda kisa ya kama aka bashi kifi, ya ci. Koda ya ci sai ya fara makyalkyata, nan take ya mutu.
Da Sarki fa ya ga haka nan da nan ya sa aka fitar da su M. 'Danye daga keji, ya zauna tare da su cikin jin dadi irin nasu. Komi zai yi sai ya yi shawara da su M. 'Danye, ya zama dai ba abin da za'a yi a garin sai da yardar M. 'Danye.
Suna cikin wannan hali na cin daula gawrgwadon iko, sai suka ga za su bata lokacinsu a wannan gari, sabo da haka suka yi shawara su yi ma Sarki sallama su ci gaba. Suka sanad da Sarkiza su ci gaba, Sarki ya ri, suka nace har ya yarda, ya basu guzuri mai dama suka yi sallama suka bar garin.
## SUN· SHIGA GIDAN SARKIN JAFILA
Kwanci tashi suka shiga wani daji mai yawan namun daji, a nan suka ga wata irin dabba mai kafafu sha biyu, wannan ya sa su zaton ko sun kusa kawo ga duwatsun nan. Suna cikin tafiya sai suka kawo ga wata korama, suka yi wanka, abin da suka dade ba su yi ba. San nan suka Retare koramar. Da Retare ta, sai suka ga wani gida mai benaye yana walkiya tamkar an gina
---
**Page 38**
shi da lu’ulu’u, ashe wannan gida na gindin korama shi ne karshen dajin.
Da ganin gida, M. Danye ya ce da Dabo, “Ai sai mu je wan- nan gida muga abin da ke ciki, watakila mu yi sa’ar tamu.” Dabo ya ce, “To”, ko dayakeshi yana tsoron irin wadannan gida. Suka je gida suka yi sallama shiru, suka yi ta sallama. Zuwa can sai ga wasu tsofin mata irin na Fada, suk. fito suna fada. M. Danye ya ce masu, “Iyayena ko mun samu wurin kwana mu matafiya ne, da safe mu wuce.” Wata tsohuwa wadda take babbaru, ta ce, “Kai kuwa wane irin mutum ne, ba ka san wurin