Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
nan sai kurum ka ci shi yadda ka so kuma." Dabo ya ce, "Ni dai bar ni in fare ba ku labarin rabuwar mu da kai, haka ma da na yi ai ya kyautu ka yaba mani." Sai Macijiya ta ce, "Amma ko ni abin ya ba ni mamaki, don ina ga ba halittar da tafi mutum hankali, amma ga shi kai da Sarki irin yadda ku ka yi, ko ni maciji ai ba ni saran mutum sai in na ga alamar zai halaka ni, shi Sarki na son cutar wani, ya gamu da wanda ya fi shi cuta, ya zama shi aka cuta." Dabo ya ce, "Abar binciken komi cikin sha'anin mu na mutane, ai mun fi ko wace irin halitta cuta ga junammu, kuma mun fi kowace halitta taimako ga junammu, don Allah ya ba mu hankali da wayo fiye da kowa ce halitta, ya kuma bamu hanyar koyon abubuwa na gari ta littattafai. Bari in karasa ma ku labarina." Bayan kwana uku na gama shiri, sai zakara ya ba ni sa'a ko mai masaukina ban yi ma sallama ba. Na kama hanya na yi --- **Page 70** gabas bisa dokina, a cikin yinin nan na shiga wani babban daji na yi ta yi, wata na bakwai ina tafiya amma ban taba ganin ko sawum mutum ba, kuma tun da na ke ban taba ganin daji irin wannan ba a cikin yawace yawacemmu. A cikin wata na takwas ne na zo wani wurin babban rami ba bu komi cikinsa sai kasu- suwa, na ga to lalle ida wanda ya kawo su nan, in duba haka arewa da ni sai na ga wata yar hanyar, sai kurum na bita. ban yi tafiya mai nisa ba sai na iske wani babban gida, an gira shi da azurfa da zinare, sai walkiya ya ke, sai tsoro ya kama ni, amma na dake na sabko daga kan dokina, na daure shi na koma kofar gidan na harde sai ka ce gidana. Ina nan har magariba ta yi ban ga mutum ya fito ba, ban ga wani ya shiga ba sai na ga gidan a haske kamar rana, wani abu kamar dutse 'yan kanana a jikin bangon duk ya haske gidan. Kyan gidan ko daga ciki, ya sa na yi zaton ko aljannar da na ji ana cewa kanana a jikin bangon duk ya haske gidan. Kyan gidan ko daga ciki, ya sa na yi zaton ko aljannar da na ji ana cewa akwai ta a duniya ce, na ga kuma an ya tsarkina ya isa in ga aljannar nan da idona tun kafin in mutu. Sai na shiga duduba dakunan gidan in ga yadda su ke. In shiga wannan daki, in koma wannan, don babban gida ne, har can na iske wani katon daki, na kutsa kai na shiga, sai na iske wata mace a kwance a kan gado, 'yan mata biyu na mata murza a kafafunta. Ko da ta ganni sai ta yi zunbur ta tashi zaune. Na dube ta da kyau, na ga duk inda mace ta kai ga kyau to ita ta fi haka, in na ce in tsaya in ba ku labarin kyawunta, sai ku zaci fanya ne, don kuma komin iya bayanin mutum, ba zai iya bayyana kyawun matar nan ba har a ce wani ya gane, don tilas ya rage wani abu. Kuma duk matan da muka gani ba wadda ta kama kafarta, ganin kuma ma ya karfafa mani zuciya da wannan gidan ko Aljannan ce, wannan ko yarinya, cikin 'yan matan Aljanna ne da ni ke jin labarinsu." Ta tashi zaune kan gado, ta ce mani, "Kai mutum, ko aljan ?" Na ce mata "Mutum ne." Ta ce, ""Ya ya ka yi ka zo nan, daga ina ka fito, mai ya kawo ka nan, don me ba ka yi mana sallama ba, don me ka shigo ba ka nemi izni ba ?" Na fadi Rasa da ladabi da girmamawa na ce mata ""Ni mai dimauta ne, na fito daga Damas ne, ni mutum ne, na yo niyyar zuwa Duwatsun Samardala ne, ina mai neman taimako da ga gare ki, ya uwarqijiya ta, ki dube ni da idon rahama." San nan ta ce mani "Ko ka san wannan gida ?" Na ce mata --- **Page 71** “A’a ban sani ba.” Ta ce, “Wannan gidan’Dan Sarkin Aljan- nun duniya ne, ni ko matarsa ce, dukkammu nan aljannu ne, amma sabo da ladabinka ba za mu cuce ka ba, kuma zan biya ma bukata in Allah ya so.” Na ce, “Ranki ya dafe ni bukata ta in ganni a Samardala.” Ta ce, “Mu aljannu bamu ikon zuwa gun Duwatsun Samardala, amma zan sa a kai ka kusa da duwatsun, je ka ga daki can ka shiga ka kwanta, gobe ya wannan kana Samardala, yanzu mijina zai zo zan sanad da shi.” Na shiga na yi kwance. Ashe tun da daren nan da mijinta ya zo ta ba shi labari, har ya zo ina barci ya ganni, kuma ya ga doki na a kofar a gida. Da gari ya waye na tashi na yi sallah, sai na shiga na iske ta da mijinta da aljannu sun kewaye su, ana fadanci. Na fadi na yi gaisuwa, mijin ya amsa da fara’a, sauran aljannu sai duba na su ke, sun ga nama, na koma gefe guda na zauna. Sai na ga an kira wani RaKarfan aljani, mijin ya ce masa,” Ka dauki wannan mutum ka kai shi kusa da duwatsun Samardala yanzu ka dawo, ka kai shi lafiya.” Na tashi na yi godiya tun kafin a yi mani magana, don na matsu in bar gun, na ce ma su na ba su dokina. Aljani ya sunkuya na hau bayansa, ya ce, “Runtse idonka.” Na runtse, ni dai daga nan ban san abin da a ke ba, sai kurum na ganni a Rasa, Aljanin nan a gaba na. Ya ce mani “To nan ne bakin inda zan iya kai ka, kuma sai ka iyar a Rasa.” Na gode masa, na kama hanya, shi kuma ya bace. Ina tafi ya shi ne banci rabin zango ba sai na hadu da kai. To, kun ji irin abin da ya afku gare ni bayan rabuwarmu da kai. M.’Danye da macijiya suka yi mamaki yadda kowa ya gamu da yadda tafiyarsa ta zama mai sauki, aka hadu kuma lokaci daya. San nan M. ‘Danye ya ba Dabo labarin abin da ya afku gare shi bayan rabuwarsu, da yadda suka hadu da wannan macijiyar. Dabo yai mamaki ya gode ma Allah da ya sake tara su gun biyan bukata. Kashegari wa’adin da tsoho ya yi ma M.’Danye ya cika, sai ya ce da Dabo, ya shirya su je don ya gabatadda shi gun tsoho. Su ka dunguma, su ka je su ka yi ma tsoho sallama, ya amsa masu. Tsoho ya ce da M. ‘Danye, “Samari ka dawo kan ma- ganar da mu ka yi ?” M. ‘Danye ya ce, “Na dawo Baba, amma har da abokin tafi ya ta muka zo.” Tsoho ya yi murna, san nan ya ce, “To abin da zan gaya ma ku, zan ba ku iznin shiga --- **Page 72** dutse biyu rak, idan kun shiga dutse na farko kun fito lafiya, to na biyu ba wani abin tsoro. Shiga wannan duwatsu ko a gareku, ya ishe ku, ga duk bukatunku na duniya, san nan ba za ku mutu ba har abada, sai ranar tashin Riyama duk ba wanda ya taba shiga duwatsun nan, sai ko ku. Sai ku je dutse na Karshen gabas, ku je gabas da shi, ku ce 'Iftih ya Jabalu, bi iznin-lahi, za ka ga ya bude. To ku shiga, za ka fara iske mu- tane a tsraitsaye suna sanye da riguna da rawuna a kansu, ku gaisa da su, san nan ku sunbance su, ku wuce gaba, za ku samu yaro ma'abucin Runshi kafa da hannu to shi ma ku sunbance shi, ku wuce gaba za ka samu mace da danta ya na riRe da ma- manta ku sunbunce ta ita ma ku wuce, za ku ga mutum goma sha biyu bisa wani gado na baKin Rarfe a kwance, to ku kwanta cikinsu dan lokaci kadan san nan ku tashi ku yi gaba za ku ishe wata Korama tana gudana, ku debi ruwanta, ku sha ku yi wanka. To in kun aikata haka sai ku fito, to lokacin da zaku fito za ku ji dutsen kamar ya kife da hayaniya, ana cewa a kama su, ka da ku ji tsoro kada ku waiwaya, ku fito a hankali, don duk wanda ya firgita ba da shi ba, don mutanen nan da ku ka gani matattu ne, ba mai rai duk cikinsu. Idan kun fito daga wannan dutse, ku kirga duwatsu uku to na hudu shi zaku shiga, zaku ga wuta na cinsa, amima ba komi, muddin kun aikata yadda na fada maku a dutse na farko. In kun je sai ku ce, 'iftin ya Jabalu nari bi izninlahi', idan kuka shiga, zaku ga tsuntsuwa a cikin kogo kan sheka, ku kama ta, ku yanka ku dau kitsen ku shafa a jikinku. To in har ku ka aikata haka kada ku ji tsoron komi duniyar nan". Suka yi sallama da tsoho suka fito suka doshi dutse na kar- shen gabas, da suka zo gabas da shi M. 'Danye ya yi karatun da tsoho ya fada masu sai ya ga dutse ya bude, suka shiga suka aikata duk yadda tsoho ya fada masu da juyo zasu fito sai suka ji hargowa ana kiransu, suka yi kamar su koma, amma suka tuna gargadin da tsoho ya yi masu, suka daure dai suka fito lafiya. Ko da suka fito sai suka ga dutse ya koma ya rufe kamar ba wata Rofa, san nan suka Rirga dutse hudu, suka yi karatu, dutse ya bude, suka ga dutsen ba abin da ke cikinsa sai wuta. M. 'Danye ya ce da Dabo ya fara shiga, Dabo ya ce, sai M. 'Danye ya fara shiga don shi ne babba. M. 'Danye ya yi Ruru ya fada, amma Dabo tsoro ya hana shi, ya ga wuta --- **Page 73** ras. M. 'Danye ya iske tsuntsuwa, ya yanka ta. ya aikata yadda tsoho ya ce masa, amma bai ga Dabo ya shigo ha shiru. Dabo na nan bakin kofa yana jira ya ga M. 'Danye zai fito ko ya mutu ke nan, sai ya ga M. 'Danye ya fito dutse ya koma ya rufe. Dabo ya ji haushi, amma da ya ke ya shiga wancan dutse bai damu ba, kuma tunda M. 'Danye ya gama yadda aka so a yi duka. 'Suka tafo gun tsoho, suka shiga suka yi godiya, sannan suka yi sallama, suka dawo gun macijiya suka sanatta sun gama abinda za su yi kuma bukatarsu ta biya. Macijiya ta ce. "To sai mu kwana gobe da asuba. in daukc ku duk in kai ku inda kuke so." Kashegari M. 'Danye ya ce, "To ba inda muke so ki kai mu sai gidan sarkin Jafila." Macijiya ta daukc su la'asar na yi sai ga su kofar gidan Sarkin Jafila wato inda Jamilatul-uhura ta ke. Suka iske Sarki ba ya nan, amma har an gane su. Mutanen gida na zato irin zuwansu wancan ne. Kan a ce haka sun nufo M. 'Danye da maraba, shi kuma sai kurum ya gama masu aiki da duk masu gadi suka kwanta dama. Sauran Jamilatul uhura, ya ce mata ke matata ce, don tsoron ka da ya kasheta ta yarda, tana zaton in Sarki mijinta ya zo, zai kashe su. Kwaram sai ga Sarki da jama'arsa da kafe-kafe da bushe-bushe da zuwa Sarki ya ga alamar ba kowa a gidan, ya shiga a fusace, sai ya tarad da gawar mutane, da M. 'Danye da matarsa suna tare, ya tasamma M. 'Danye, amma kan a ce taro, ya kashe shi, fadawa suna kofar gida. M. 'Danye ya ce da fadawa da ku Allah ya gama mu ya kashe na kashcwa ya kama na kamawa. Ya nada Dabo ya zama Sarkin Jafila. M. 'Danye da Jamilatul'uhura da Dabo da sauran fadawa da da ba a kashe ba, suka dunguma zuwa Jafila don a yi wa Dabo mubayi'a. Aka bisu da kafe-kafe, amma kafin su zo an kai labari. Da fari mutanen garin suka tarye su da yaKi, amma da su ka ga ba dama suka watsar su ka bi. M. 'Danye ya sa a ka tara jama'a ya nada Dabo ya zama Sarki suka kwana bakwai, sannan aka yi wakili kafin Dabo ya dawo daga raka M. 'Danye. Da M. 'Danye da Dabo da Jamailatul'uhura suka dunguma da 'yan fadawa suka nufi inda Faira'atu ta ke. Kwanci tashi har suka isa. Suka hau dutsen da take, watau matar Aljanan nan da ta ba su labarin Samardala, su ka yi sallama ta fito da ganinsu sai ta shaida su, suka shiga gida, suka bata labari bukatarsu ta biya sun je duwatsun nan na Samardala, ta yi --- **Page 74** hausabook.com --- **Page 75** ya mutu, har an nada sabo. M. 'Danye ya ba Sarki labarin tafiyar shi daga farko har Karshe, da yadda ya kamo Zulkaratu, san nan ya sa aka kira Zulkaratu ya danka ta ga Sarki. Ko da Sarki ya ji labarin M. 'Danye, ya kuma ji dama labarin yakin Langeri, amma ba ya zaton su M. 'Danye ne, sai ya ce, "Ai sai ka zama Sarkin Sarakuna, kuma ka zauna nan garin, ni kuma in zama Wazirinka. M. 'Danye ya ce dama haka na yi niyya. Labarin Nakowa ko, ko da ya ji inda diyarsa ta ke, sai ya kwantar da ransa, ya rungumi jikansa yana ba shi shawara, don yaro ne, ya zama kamar shi ne Sarkin. Wannan ya sa Na kowa ya yi tunanin lokacin da ya yi ta rokon Allah ya ba shi da namiji, da ya samu mace, ya zaci rokonsa bai amsu ba, ashe Ubangiji ya amshi rokonsa, ta hanya mafi alheri gare shi, ga shi ba sha'anin attajiranci ba, ya zama kamar shi ne Sarki a Langeri, a Damas kuma dansa mijin diyar shi Wazirin Sarkin Sarakuna. Ya gode ma Allah, ya tabbatar Allah shi ya fi sanin abin da zai zamanwa mutum alheri. M. 'Danye ko ya sa aka gina masa tabkeken gida, ya zama shi ne Sarkin Sarakunan Hamada. Dabo kuma ya koma Jafila ya kama ta shi cin duniya, ko da ya ke ya so ya zama Wazirin M. 'Danye, amma haka ma da ta same shi ba ta raba su ba, idan ya yi nishadi sai ya tafo Damas gun M. 'Danye su yi 'yan Kwanaki suna fira suna tuna wuyar da suka sha, da kuma irin muraminsu a da, da na yanzu, su gode ma Allah da Annabinsa, da ya shiryad da su, ya kuma kawo duniya ingattaciya ya ba su. Haka su ke ta cin duniyar su har gobe, don ba su mutuwa, yanzu haka in ka je Damas sai ka iske su. Macijiya kuma tana zuwa gunsu ko wane mako. Idan wannan littafi ya Rayatar za mu bada na biyunsa mulkin M. 'Danye. --- **Page 76** hausabook.com --- 如果还需要进一步处理(如分段整理、翻译、总结等),请告诉我。 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9