Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
kirawo ta, ya ce, "Zo ki gaida wani wanki." Yarinya ta zo ta gaida M. Danve. Da M. Danve ya koma gida sai ya sa aka kira masa babbam mafadan Sarkin wanda komi ya ce kansa za a tsaya, ana kiransa Fada. Da Fada ya zo, M. Danve ya fada masa yana son 'yar Sarki da aure. Fada ya ce, "Ranka ya dade, wannan ai ba abu ba ne mai wuya M. Danve ya kawo fam hamsin ya ba shi ya kai wa Sarki, ya kuma ba shi fam biyar nasa. Fada ya Runshe kudi ya fita, bai zame ko ina ba sai gidan Sarki. Ya isa gun Sarki, ka san shi ba sai an yi masa iso ba, ya kai masa kudi, ya ba shi labarin bukatar M. Danve, sa'an nan ya shiga gyara maganar. Sarki ya yarda, amma zai shawarci uwar yarinya. Fada ya koma ya sanad da M. Danve, Sarki ya yarda amma, zai shawarci uwar yarinya da yarinya. M. Danve ya ce, "Bai yarda ba ke nan, da ya yarda ai ba sauran shawara, tun da su duka mulkinsa ne." Sai ya sake kawo fam ashirin ya ce a kai wa Sarki fam goma, uwar yarinya fam goma. Fada ya amshi kudi ya koma. Ya sanad da Sarki, ga kuma abin da M. Danve ya ce, ga kuma abin da ya bayar. Ko da Sarki ya ga kudi fam ashirin ga waccan fam hamsin ka san a zamanin nan fam ham- sin daidai ta ke da jaka hamsin a yau, ya ga kuma M. Danve dan Sarki ne, ga shi da halin karama, sai ya ce da Fada, "Ai ba abin da zai hana tun da ya ce yana so, amma za a tura ta --- **Page 21** hausabook.com --- **Page 22** wata rana sai ka huce, idan ko ba ni zuwa, kullum kana nan da fushina, ba abin da ka ke mani na fucewa." Sarki ya ce da Fada, "So ka ke kullum da safe in zageka, ba ka tsoron kada wata masifa ta same ka ?" Fada ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ba komi, ni dai bukata ta ke nan." Sarki tsammanin wata masifa zata afkawa Fada idan yana zaginsa kullum sai ya ce, "Na yi ma." Nan ko cikin gari magana ta bazu an kori Fada, duk inda ya nufa ba mai ko son ya ganshi bare ya yi masa magana. Gidansa, da kullum a'cike ya ke, da baRi da mutanen gari, masu neman abin tuwo da masu shari'a, amma da wannan ta afku ko kare bai Rara gani ba daga shi sai matansa da 'ya'yansa. Fada ya ce, "Ko da su mutanen duniya haka su ke, sai ana yi da kai a ke son ka". Bugu da Rari, sai Fada ya yi ta ji a gari ana ta fadin laifukan da bai ji bai gani ba, ana cewa duk shi ya yi,'abin duni- ya duk ya rude masa, ya maida abin ga Allah, don dai ya tab- bata, ba wani abu da ya yi mugu, wanda har ya sa a ke yi masa wannan maganganu. Kashegari Majalisa ta cika maRil, sai Fada ya tafo, kamar yadda ya roRi Sarki arziki aka yi masa. Mutane sai kallonsa su ke suna cewa, "Kai wannan mutum kuma ko so ya ke a daure shi." Ba wanda ya kalle shi balle magana. Da ko inya tafo mutane na biye da shi di, sai a tarye shi ana gaida shi, kafin ya shiga Majalisa gun Sarki. Fada ya shiga ya yi gaisuwa, ba wanda ya ce ci kanka, sai ya tashi ya je kusa da Sarki ya sunkuya kamar Sarki zai fada masa wata magana, Sarki ya tuna maganarsu ta jiya, sai ya riRa ce masa, "Allah wadanka," Shi ko yana cewa, "To, Allah ya baka nasara." Sarki ya zazzage shi, ko da aka gama zaginsa, sai ya yiwO waje da sauri, kamar wanda aka fada wa wani asiri, ya je ya aikata. Ko da mutane suka ga haka sai suka yi zaton an huce da shi, har ga shi an yi maganar asiri da shi kamar da. Kafin a ce haka gidan Fada ya cika maRil abin har ya fi da, kuma kowa na fadfin ta bakinsa, duk gari ya dauka ai an maida Fada, mutane sai duruwa su ke gidansa, ana yi masa barka, shi ko, tun da ya san gobe ma za shi a zage shi sai amsawa ya le. Da Sarki ya gane dabarar da Fada ya yi, sai ya sa aka kira shi, ya ce, "To, na ji gidanka ya cika, ana yi ma barka wai na maida ka, wa ya ce na maida ka ?" Fada ya ce, "Allah ya ba Sarki na- sara, zaginka da ka ce in ka yi mini masifa zata auka mini, to --- **Page 23** ita ce yanzu, ta auka mini, tun da mutane don izgili sun ga ka zage, sun ce ka maida ni, ko da ya ke dai ba su san zagina ka yi ba, abin da ya sa suka zo yi mini barka, don ka ce na yi ma Rarya ne kurum, kuma zuciyarka ta Rara baci, to mai sonka ya bata ma rai ne ?” Da Sarki ya ji haka sai ya ce, “To, tun da ya ke an yi ma ne don ba’a, to shi ke nan, na maida ka, kuma su je su yi ba’ar mu gani”. Fada ya koma kamar da, ya gode wa Allah da Ma’aikinsa da haka ta faru, don ya Rara sanin yadda zai zauna da mutane. Da Fada ya ga sabo da M.’Danye haka ta auku gare shi, sai kuma ya yi kamun Rafa ga M. ’Danye, kullum wurinsa za shi hira. Ta haka M. ’Danye ya san asirin Rasar kaf. Da fa M. ’Danye ya ga garin ya zama nasa, sai abin da ya ce, ga shi kuma ya san abin da duk ke ckin fadar Sarki, sai fa ya shiga cikin sha’anin mulki sosi ya yi ta tara abin duniya, gama shi da ya ke abin duniya ya ke so kurum, to ko Sarkin ba ya sa-nun abin da ya ke samu. Tabarin yarinya kuma soyayya sai gaba ta ke har ya zama dare da rana tana gun sa. To, da fa M. ’Danye ya ga ya tara abin du-niya ya ga kuma in ya sake zai bata lokacinsa a wannan gari, sai ya bar yi wa yarinya ko maganar aure, ta-ga duk dai ya, canza mata hali. Yarinya fa hankalinta ya ta shi, har ta fada wa uban, ita gara a yi, a yi bikinsu. Ganin hankalin yarinya ya tashi, sai Sarki ya aika wa M. ’Danye a fada masa ya kamata ya yi shiri a yi biki. M. ’Danye dame ya cire kan bawo, ya sami hanyar gudu cikin arziki da su-tura, sai ya aika a fada wa Sarki, shi yanzu kam ba shi da sukuni, amma yana so Sarki ya ba shi lokaci ya koma gida ya shiryo don bikin zai fi armashi. Kuma ga shi ubansa ya sani. Sarki jin haka sai ya ce gaskiyar M. ’Danye, ya ce, “To, sai ka shirya na ba ka wata shida, ka tafi ka shiryo ka dawo”. Sarki ya yi masa kyauta mai yawa, ya kawo doki taka ka hau ya ba shi. M. ’Danye ya shirya ya tafi shi da Dabo. Labarin Zulkaratu ko, tana can ita da Yarima soyayya sai abin da ya yi gaba, sun daidaita ba abin da a ke jira sai biki kurum. Masoya ko, abin ba a magana, daga ko ina sarakuna sai a: kowa su ke, wadansu jin ba za a ba su ba, suna ta shirin su zo su ci Langeri, su amshe ta. An Yi Bikin ZulRaratu Da Yarima Ganin irin aike da kullum Nakowa ke samu kan ana son Zul- --- **Page 24** Karatu sai ya ba Sarki uban Yarima shawara ya kamata a yi musu biki, ko ya huta da maganar mutane, kada wani tashin hankali ya same su, ko ita yarinyar. Sarki ya yarda aka sa ranar biki ashirin ga wata. Sarki ya sa aka rubuta takardu duk aka aikewa Hakiman kasarsa, da kuma Sarakunan da su ke abin arziki, kan su halarci bikin. Kafin ranar bikin ta zo da kwana bakwai Langeri ta cika ma- rii. Raran biki da ta zo mutane tilas wafansu sai bayan gari suka sauka, don dai Sarkin dansa ke nan Yarima, balle kuma Nakowa. Shagalin da aka yi a Langeri, abin ya wuce a rubuta. Bayan an yi sallar azahar, sai aka hangi fura daga kudu kamar hadari. Sarki na zatou wani Sarki ne ya tafo gun biki, ya aika 'yan tarye, ashe wani Sarki ne da ya ke wa Zulkaratu mugun so, Nakowa ya Ri ba shi, ya ji ranar daurin aure ya tafo ya ci garin, ya Rwace ta da Farfi. 'Yan tarye da suka tafi ba wanda ya dawo Sarkin nan ya kama su duk. Sarkin Langeri ba shi da asirin komi, kafin a ce haka Sarkin nan ya kewaye Langeri da dawakai da rafuma, babu shiga.babu fita. Duk mutanen da ke bayan' gari sun dade a hannu. Nan da nan da Sarkin Langeri ya ji yafi ne, ya sa aka yi gangami, duk dakaru suka shiga damara suka hawo. Da Nakowa ya ji gan- gami, sai ya kasa hafuri, ya san dai wannan biki ya jawo ko mene- ne, ya nufi fada a Rasa, ya iske Sarkiya ce, "Ko lafiya?" Sarkiya ce, "Ina lafiya, yafi ne ya zo mana daga kudu". Ko da Nakowa ya ji ya san abin da ya faru, Sarkin nan ne ya zo ya amshi Zul- Faratu. Sai ya koma gida da sauri ya shirya ya dauki takobinsa da abokinsa Aljani ya ba shi, ya hau doki ya doshi inda yafi ya ke. Ya iske mutanensa ba wanda ya iso. Bai yi wata wata ba, sai ya fada rundunar nansi daiya, in ya yi dauki gabas na yamma su biyo shi, ya juya ya ce da ku Allah ya gama mu, su dare, inda duk ya nufa sai ka ga mutane falas Rasa. Kafin a ce haka ya fara ba maza kashi, can mutanensa suka iso. Da zuwan mutanen Langeri, suka iske irin barnar da Nakowa ya yi, sai fa jikinsu ya yi Farfi, suka fada fage da murna sun tabbata za su yi nasara. Kafin a ce haka mutanen waccan Sarki duk Nakowa ya shanya manyan dakarun a Rasa. Sarkin ko yana gindin wata itaciya an girka masa karaga ya harde, dakaru sun kewaye shi. Sarkin Langeri ko zuwa bai yi ba, sai Yarima ango ya wakilce shi. --- **Page 25** 3arkin nan yana gindin itaciya, ana yi masa fita bai san ba yaRi ya bace masu, sai ya ga Nakowa ya nufo su. Dakaru suka zabu- ra suka tarye shi, kowa suka gamu da Nakowa sai dai a sake hai- huwar wani. Kafin a ce haka sai Sarki ya ga Nakowa ya nufoshi gadan-gadan da takobi tsirara, Sarki ya zabura daga karaga, ya ramci ta kare a Rasa, Nakowa ya bi shi ya banke ya kama shi da ya ke baya son kashe shi. Ya daure shi da asawalin dokinsa, ya tuso shi gaba, yana cewa kai zaka riRa wankewa ZulKaratu aku- sa, shi ya sa na Ri kashe ka. Da Sarki ya zo hannu, sai yaRi ya tsaya. Aka kama mutanen Sarkin nan da dawakansu da duk dukiyar da suka zo da ita. Mutanen gari ko da duk baRin ciki ya rufe su, sai kuma cewa suke wannan amarya da sa'a take, ban da ganimar yaRi, har ta sami Sarkin duniya zai riRa wanke mata akusa. Kashégari Sarki ya tara duk hakimai da manyan fadawansa a Majalisarsa, ya ce, "To, kun ga ni na tsufa, ga shi kuma na ga Yarima ya kawo hankali, ina tsammani zai đauki haŧurin zama da ku, ina so zan huta shi ya zama Sarkinku, ko da ya ke dai muna tare, don in na ga ya yi ba daidai ba, zan riŧa ba shi sha- wara ina nuna masa hanya mai kyau ta riŧe jama'a. Jama'a duk suka yarda. Aka shirya sai kashegari za a nađa sarauta. Ga irin taron biki ba a fashe ba, wannan dare duk mutumin da ke Lan- geri ba wanda ya yi barci. Gidan su Zulŧaratu ko sai shiga da fita a ke. Sarkin nan kamamme yana can an ajiye shi a Kurkuku ba wanda ya ŧarŧa komawa ta kansa. Kashegari fada ta cika mutane abin ba a magana. Sarki ya sa aka girka karđga a waje, hakimai duk sun kewaye wurin. Sa'an nan Sarki ya taşhi ya yi jawabi, kan yau ne ya ke so zai bar sarau- ta don tsufa ya kama shi, Yarima ya kama, ko da ya ke yana tare da Yarima, zai kuma riŧa ba shi shawara kan duk al'amura da ya ga ya kamata. Duka jama'a suka amsa sun yarda. Sai Wazi- rin Sarkin ya tashi, ya kama Yarima ya đora kan karaga. Shagalifa ko ba a fađa ba ka saninda aka ce an nađa sabon Sarki ba a magana. Bayan an natsa, sai Sarki ya sa aka kawo Sarkin nan da ya kawo masa yaŗi, don matarsa. Da Sarkin ya zo, sabon Sarki ya ce, "Na yi murna da ya zamana ka iske ni, ina muŝa- min Sarki, kuma ina Sarki, zan yi ma abin da duk da na so" Ka sani, ba mu taka ma ba ba mu zubar ma ba, kurum sabo da ya- rinya ka taso ka haddasa ŝarnar rayuka masu yawa, suka ŝalla- ka, to, da na yi niyya, in kashe ka, to, amma yanzu, zan barka da --- **Page 26** haRin da ke bisa kanka, in kuma fora ma fansa, ka biya in mai- da ka garinka, don ina fata wannan ya zamamma ishara, ka kuma Rara ilmin yadda za ka tafi da jama'arka nan gaba". Sar- kin ya yi godiya. Aka fora masa fansa, ya ce, "To, a gama ni da mutane in sun kai ni garina zan ba su biya". Aka gama shi da mutane cikin karama tamkar yana cikin sarauta ba a ci shi ba. Kwanci tashi har Allah ya kai su kusa da Birnin garin da ya ke sarauta. Da Sarkin ya ga sun zo kusa da birninsa, sai ya sauka tare da 'yan rakiyarsa, ya aiki mutum a sanad da mutanen gari ga shi ya dawo, su hawo a zo a taryensa. To, ka san labari ya dade da isa kan an kama shi kuma ba a shakka an kashe shi, sabo da haka har an nada babban dansa ya zama Sarki. Sabo da haka da labari ya isa kan a zo a tarye shi, ka san abin sarauta, sai dansa, watau sabon Sarki, ya fara cewa wannan ai zancen banza ne, wani ya tafa mutuwa ya dawo har a ce za a je taryen gawa, fadawa suka ce koko fatalwa ya ke dai, aka dai Ri zuwa a tarye shi. Ko da Sarki ya ga shiru ba wanda ya zo, sai ya fahinta da abin da ya auku, watau an nada sabon Sarki, sabo da haka sai ya tafi shi da 'yan rakiyarsa suka shiga birnin. Da shigarsu, mutane sai kallonsu su ke suna mamaki, kowa kuma ya nufi fada ya ga abin da zai auku. Shi ko da ya shiga gari, bai zame ko ina ba sai fada watau gidansa na da, ana ko cikin fadanci. Da dai dansa wato sabon Sarki nan ya ganshi, sai ya ce, "Ashe maganar nan gaskiya ce, wato baba fatalwa ya ke, to ai ba zan Rara jin kunya ba, ka mutu, amma zuciyarka har yanzu tana duniya." Sai ya tambayi Waziri maganin fatalwa, Waziri ya ce, "Maganinta ai sai a raba ta biyu da takobi, to ba zata Rara komowa ba." Sarkin da ya ji haka, sai ya fara rantse- rantse, kan wallahi dama shi bai mutu ba, balle ma a ce yana fatalwa. Haba duk rantse-rantsensa bai fitad da shi ba, kafin a ce haka tuni ya kwana lahira. Da fa 'yan rakiya suka ga abinda ya faru ga Sarki, sai in bakai ban wuri, wasu suka tsira da kyar, wasu aka kame su aka kashe, ana cewa abokansa ne fatalwoyi. Duk abin nan an fahinta fa Sarkin nan shi ne ba wata fatalwa ba, aka Ri da gangam don sha'anin duniya kurum. Sauran 'yan rakiya da suka sami kansu, suka kai Langeri da Ryar. Sarkin Langeri bayan sun huta, ya aika aka kirawo su don su bada abin da Sarki ya bayar na fansa, da kuma irin alheri da ya yi dan kansa. Da suka zo Sarki ya tambaye su ko sun kai --- **Page 27** shi gida lafiya, suka ce, “I, mun kai shi har cikin birnin shi lafiya amma ga abin da dansa ya aikata gare shi wai shi fatalwa ne, kuma wasu cikin mutanemmu sun kwanta dama tare da shi. Da fa Sarki ya ji haka sai hankalinsa ya tashi, tum ma da ya ji dansa ne ya aikata masa haka don sha’anin duniya kurum. Fadawa da ke nan sai suka ce, “Ai ba abin da ya fi Allah ya ba Sarki nasara, sai ka je ka yaRe su, ka cinye shi, ka kama shi ka sa a tsire shi a kasuwar garinsu”. Wannan shawara ta shiga zuciyar Sarki, sabo da haka ya sanad da da ubansa abin da ya ke son aikatawa. Uban ya ce, “Kada ka tsire shi ko ka ci shi, kai dai ka kamo shi ka tafo da shi, ka nada masu sabon Sarki” Sai fa Sarki ya sanad da dakura su shiga shiri zai kai ma Sarkin nan yaŝi, dakaru suka yi ta shiri. Bayan sun gama shiri ya fita. Kwanci tashi har Allah ya kai su birnin Sarkin. Sarki ba shi da labarin ’yan yaŝi, sai ya ji su bayan gari su yi ma garin zoŝe. Nan da nan ya sa aka yi gangami aka fita. To yan yaŝinsa, tun a yaŝin Langeri Jarumawa da yawa sun kwanta dama. Ya fita haka nan duk jikinsa ya yi masa sanyi, da fara gwabzawa sai ga shi ya zo hannu ko wani ŝauki ba daŝi babu. Sarkin Langeri ya shiga birnin ya sauka, duk jama’arsa suka shiga, amma sabo da garin ya yi masu kadaŝan wasu su ka sauka bayan gari. Bayan Sarkin Langeri ya huta, sai ya sa aka kawo dan Sarkin nan babban, ko da ya ke dai yaro ne, don bai wuce slckara ashirin ba ya nada shi Sarki. San nan ya ce da kamanman Sarki, kai kuma kai ne fansar ubanka, ga kuma taka ta kanka. Dansa, wato sabon Sarki ya yi, ya yi da Sarkin Laugeri ya ba shi fansa, ya ŝi, ya ce, “Da shi zan tafi, kuma tun da ya sa aka ka- she wancan Sarki, shi ma kashe shi zan yi.” Sarkin Langeri ya shirya ya taso daga birnin nan da ganima mai yawa, ’yan yaŝinsa sai murma su ke sun yi sa’a, kowa sai annashuwa ya ke irin wadda ta dace da shi a kan hanya, kam- mamman Sarki yana tare da su. Kwanci tashi, har Allah ya kai su Langeri. \Da suka shiga cikin garin Langeri, sai aka kai Sarkin nan Kurkuku. Bayan Sarki ya huta ya je don ya gaida ubansa, kuma ya ba shi labarin abin da ya afku. Ya je ya sanad da shi kan, har sun zo da Sarkin nan, amma ya aika shi Kur- kuku. Sai uban ya ba shi shawara kada ya kashe shi, ya bar shi har shekara guda, san nan ya sake shi ya tura shi garinsu. --- **Page 28** Bayan shekara guda sai Sarki ya sa aka kawo daurarren Sarki. Ya ce masa, to zan sake ka, wannan ya isa ladabi, amma bance zan maida ma sarauta ba, in danka ya yarda, to ya bar ma, in bai yarda ba ko shi ke nan, wannan abu tsakaninku n^; tun da ya ke danka ne. Sarki ya sallame shi ya bashi kayan ka- rama, amma ya ce ba zan gama ka da 'yan rakiya ba. Sarkin ya roki Sarki, da ya fara rubuta takarda ya sanad da dansa kan ya sake shi kuma ga shi nan zuwa, Sarkin Langeri ya ce, ba za ya rubuta ba. Sarkin nan ya ce, "To shi ke nan, adalci da ka yi mani ai ya na da yawa," Ya yi godiya ya fita. Sarkin nan ya yi shiri ya tafi. Ran nan Allah ya kai shi garinsa ya ko isa da hantsi fada ta cika ta batse, ta yi makil, dansa ya mi ke kafa sai mulki ya ke shinfidawa, ka san abu ga sarautar yaro, shagali kullum ne. Da ya shiga gari sai ya nufi fada, duk inda ya wuce mutane sai kallon shi suke suna mamaki, suna cewa a'a Sarkin nan fatalwa ya ke ba, har dal ya isa fada. Ko dadansa Sarki ya kyalla ido ya ganshi, sai ya ce, "Kash!" Abin nan da kakana ya yi, wato ubana shi ma shi ne ya yi, shin jama'a ko ana gadon yin fatalwa ne? Waziri ya ce, "Allah ya ba Sarki nasara, ai wani lokacin a kan yi." Sarki ya ce, "Shin mine ne maganinta?" Waziri ya ce, "Takobi." Ko da Sarkin ya ji Waziri ya bada irin shawarar da ya tafa ba shi, sai ya ce, "Wallahi ni ba fatalwa ba ce, ni ne ubanka Sarki, kada ka kashe ni, ka yi mani rai." Sarki ya ce, "Haba baban da muka wa sadaka tun tuni, zaka ce, wai kai ne fatalwa dai, bar cewa ka haife ni." Shi kuwa sai ya ce, "Wallahi ni ba fatalwa ba ne, kuma in ka yi mani rai ni ba sarauta ba ni ke so, ku dai barni da raina." Sannan Liman ya ce, "Tun da yana sa Allah cikin ma- ganarsa ai sai a kyale shi, har kwana uku, in fatalwa ce a gani." aka yarda aka kyale shi dai, koda ya ke dama an sani shi ne. ya zauna a garin ga shi ya kashe ubansa don sarauta, ya koma ba sarautar, shi ma na shi ran da kyar ya samu ga zaman ta- lauci, koda ya ke dansa yana dan taimaka masa. ## M. DANYE YA ISA GARIN MALAMAI Labarin M.'Danye ko, bayan ya yi sallama da Sarki, suka yo gaba shida Dabo, ba su san inda suka dosa ba, da duk dukiyar da suka samu. Kwanci tashi har Allah ya kai su wani birni ana kiransa Surbadu, ya samu shi ma babban birni ne. Da suka shiga garin sai suka sauka gidan wani babban Malami mai --- **Page 29** almajiräi masu yawa. Ashe wannan garin akasarin mutanen garin duk Malamai ne. Sabo da haka M.‘Danye ya ce da Dabo, to wannan gari ba za mu ji dafinsa ba sai ta hanyar makaranta, amma in mun ce mu shiga tsubbu, nan da nan za’a kure mu, amma ina so idan aka tambaye ka sunanka ka ce, sunanka ‘Birnin-lunfashi’ ni ko sunana ‘Birnin-rai’. Kara rikicewar abin sai ya zama garin kansu ba game ya ke ba, sun rraraba a kan sha’anin addini, wannan share suna zargi wafancan, su kuma wadan nan suna zargin wadan can. A ran da su M.‘Danye suka isa garin ran nan dan Sarkin gari.1 wanda ake ma mugun so ya rasu, sabo da haka garin sai ya zamana ba wata harka, sai baŗin ciki’ake yi. Malamin nan mai masaukinsu, bayan ya kintsa,

Chapter 3 of 9