An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
TASTAR TSAFIABDULAZIZ SANI M/GINI
Taskar Tsufl Ahdul'azit Sant M/iini
TASKAR TSAFI
kimanin shekaru dubu daya da dari K
daya kafin zamanin Sarki lamarudu
na birnin KUSA an yi wata
mashahuriyar sarauniya kuma babbar matsahfiya
j'yar ta'addanci mai suna ABIDATUL AZMAL.
Abidatul Azmal ta kasance kyakkyawar
buqurwa 'yar shckara ashirin da biyar kuma ta gají
sarauta ne da tsafi a wajen mahaifinta Sarki Azmal
bin Taufid wanda a zamaninsa babu wani sarki a
duniya mai karfin mayaka da karfin sihiri kamarsa.
Sai dja ya zamana gaba dayan sarakunan duniya da
matsafa na matukar tsoronsa.
A lokacin sarki Azmal bashi da wani buri
wanda ya fi ya mulki duniya gaba dayanta don haka
sai da ya-ci manyan kasashen duniya da yaki guda
dari bakwai da tamanin, wannan dalili ne ya sa
sarakuna da dama suka dinga gudu daga cikin
birancnsu suna buya a cikin dazuzzuka saboda idan
Sarki Azmal ya riskesu a cikin kasarsu yana yi
musu kisan gilla tarc da duk iyalansu. Sarki Azmal
na kan wannan sharafi nasa ne Allah ya jarrabeshi
daj wata irin cuta mai muni, ya zamana naman
jikinsa na rubewa da kadan-kadan, har sai da ya
zamo abin gudu ga dukkanin iyalansa da hadiman
sa domin kuwa jikinsa doyi yake, fuskarsa ma sai
da ta zagwanye ta yi muni abin firgitarwa, magani
3
Taskur Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
babu irin wanda ba a yi ba amma a banza.
A gaba dayan iyalan Sarki Azmal Abidatu ce kadai ba ta gujeshi ba saboda tsananin kaunar da take masa amma mahaifiyar ta ma gudu ta yi ta bar shi sai da ya zamana darc da rana kullum Abidatu
na zaunc a gaban Sarki Azmal tana rusa kuka kuma ita cc ke yi masa komai.
Wata rana Abidatu na tare da Sarknal
tana dura madsa abinci a baki tana zub daaye kamar yadda ta saba kawai sai ta ga ya dubeta ya kama murmushi. Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki kenan, ta share hawayenta ta ce "Ya kai Abbana ina dalilin wannan murmushi nake alhalin
yau watanka uku kcnan rabonka da yin murmushi? Sarki Azmal ya sake yin murmushi a garcta a karo
na biyu sannan ya bude baki da kyar ya cc "Ya ke 'yata ki yi sani ccwa ba komai ne ya sani wannan murmushi ba face na hango cewa ke ce za ki gajeni, lallai za ki yi shuhura a duniya kamar yadda na yi kuma za ki dade akan karagar mulki har ki tsufa har zuwa ajalinki. Hakika ke kadai cc ki ka nuna mini so da kauna fiyc da kowa tunda ba ki gujeni ba a
sa'adda kowa ya gujeni haka kuma ba ki kyamace ni ba a lokacin da kowa ya kyamace ni." Sarki Azmal ya daga hannunsa da kyar ya yi nuni izuwa wata bakar akwati sannan da Abidatu "Je ki ki dafa saman akwatin can da tafin
4
Tuskur Tvafl Abdul'azi: Sani M/Gint
hannunki."
Cikin sanyin jiki da rashin fahimta Abidatu
ta mike ta je ta dafa akwatin, ba zato ba tsammani
sai ta ga akwatin ta rikide ta zama kofar wani katon
kogo, mai duhün gaskc wata irin iska mai karfi na
fitowa daga ciki tana kokarin zukcta. Ta kc iskar ta
haddasa mikewar gashin kan Abidatu, rigar dake
jikinta kuwa ta dinga kadawa kamar za ta fita daga
jikinta, ba don Abidatu ta tokare kofar kogon da
kafafunta ba da hannayenta da tuni iskar ta zuketa
izuwa ciki.
Abidatu ta rusa ihu ta waigo ta dubi
mahaifinta fuskarta cike da tsoro ta ce "Ya kai
Abbana yanzu ba ka ceceni ba kana gani zan hallaka?"
Azmal ya ce "Ya ke 'yata ashe duk tsawon
zamana dake ba kı amince dani ba. Saki jikinki ki
kwantar da hankalınkı ki bari wannan iska ta zukeki
domin za ta kai ki ne inda za ki samu irin matsayin
da na samu kuma za ta kai ki inda wani mahaluki
bai taba zuwa ba, kuma daga ke har izuwa mutumin
karshe na duniya wani ba zai je ba."
Koda Abidatu ta ji wannan batu sai hankalinta ya kwanta ta saki jikinta wannan iska ta zuketa izuwa cikin kogon. Take kogon ya rikide ya
zama wannan bakar akwati, Sarki Azmal ya kurawa
akwatin idanu har tsawon rabin sa'a sannan akwatin
5
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
ta sake rikidewa ta zama kogo, sai ga Abidatu ta fito
daga ciki fuskarta cike da annuri wani irin haske ya
baibaye jikinta gaba daya. Tana fitowa daga cikin
kogon sai kogon ya zama bakar akwatin a daidai
lokacin ne Sarki Azmal ya fara wani irin kakarin
mutuwa. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin
Abidatu kenan ta ruga izuwa kan gado da Sarki
Azmal ke kwance, ta zaunc daf da shi ta kura masa
idanu tana kwalla ta ce "Ina ma'anar wannan kakari
naka?"
Azmal ya ce "Ya ke 'yata ki yi sani cewa
lokaci ya yi da zamu yi bankwana. A halin yanzu
kin ziyarci inda gaba dayan sirrikan tsafin duniya
yakc,w anda ni kadai na mallakesu kuma yanzu sun
barni sun koma gareki. Wannan wuri da ki ka je shi
ake kira TASKAR TSAFI. Shin za ki iya bani
labarin abubuwan da ki ka gano a cikin Taskar
Tsafi?"
Abidatul Azmal ta kada kai ta ce "Ya kai
Babana ka yi sani cewa harshe ba zai iya bayanin
abin da na gani ba, idanu ba su isa su ga abin da na
gani ba, abin da zan iya cewa kawai shi ne na je
inda babu irinsa a duk fadin duniyar nan kuma na ji wani sirri a cikin jinin jikina, Kashina, bargona da fatar jikina irin wanda ban taba ji ba. Ka yi sani ccwa
azata
bisa
ina ji kamar zan iya daukar duniyar nan na tafin hannuna."
6
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
Ko da jin haka sai Sarki Azmal ya yi guntun murmushi cikin karfin hali a lokaci guda kuma ya hadiyi miyau na karshe. Take idanunsa suka kafe, gaba daya gangar jikinsa ta sandare komai ya daina motsi, koda ganin haka sai Abidatul Azmal ta
rungumc gawar Sarki Azmal ta fashc da matsanancin kuka har da ihu al'amarin da ya
haddasa durowar gaba dayan dakarun gin sarautar
izuwa cikin turakar Sarki Azmal. Duk wanda ya shigo ya ga Abidatu rungume da gawa sai jikinsa ya yi sanyi ya kame kawai.
Cikin kankanin lokaci labari ya bazu izuwa
sauran kasashe dake makwabtaka da birnin kusan
cewar Sarki Azmal ya mutu, ai kuwa nan fa jama'a
suka cika da farin ciki domin sun san cewa sun huta
dulkin zaluncin da ake yi musu sun manta da
cewa an kashe maciji ne ba a sare kansa ba, domin
akwai magajin Sarki Azmal wato 'yarsa Abidatul
Azmal.
A yammacin birain Kusa akwai wani babban
gari da ake kira Babila. Sarkin dake mulki a Babila
sunansa Asmaru bin Ufila.
Kafin Sarki Asmaru ya hau kan karaga Sarki
Zuwadu ne ke mulki amma sai Sarki Azmal ya
kaudashi da karfin tsiya ya dora Asmaru.
Sarki Asmaru na da da guda daya wani
kyakkyawan saurayi kuma jarumin gaske mai suna
7
Himal.
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
Himal ya kasance adalin mutum kuma ga tausayi da jin kan talakawa. Wadannan halayc na sanc suka sa bai shaku da mahaifinsa ba Sarki Asmaru domin shi Asmaru ya kasance cikakken azzalumi, makctaci. A ragowar Sarki Asmaru babu
abin da ya ke so sama da cin zali, kisa da kwatar
dukiya ko macc mai kyau. Ita kanta mahaifiyar
Himal asalinta matar wazirin Sarki Asmaru ce. A
ranar da Sarki Asmaru ya kyallara idanu ya ganta ya
jc har gidan Wazirin nasa ya yi masa kisan gilla ya
daukota da karfin tsiya ya aurcta bisa dolc.,
Wannan abu ya faru ne kimanin shekaru ashirin da
biyar baya kuma har yanzu Yarima Himal bai taba
jin wannan labari ba, domin mahaifiyarsa ba ta bari
ya sani ba.
Sa'adda Yarima Himal ya fuskanci cewa
ra'ayinsa da na mahaifinsa sun bambanta sai ya ja
da baya ja cikin harkokin sarauta ya zama kamar ba
dan Sarki ba. Kullum ba shi da tunanin hanyar da
zai bi ya hana zalunci a doron kasa to amma fa ya
san cewa bai isa ba, domin ko ba komai Sarkin
yawa ya fi sarkin karfi. Tabbas idan ya ce zai shiga
cikin irin harkokin mahaifinsa na hanashi aiwatar da
zalunci, mahaifin nasa zai iya sawa a hallaka shi,
tunda dai babu wata kauna da kyakkyawar alaka a
tsakaninsu.
8
Tuskar Tsafl Abdul'aziz Sani M/Gini
Akwai wani lokaci da Yarima Himal ya kama wani dan gari ya yi masa dukan tsiya har ya
sumar da shi bisa laifin yiwa wata makauniya fyade, koda Sarki Asmaru ya sami labarin abinda ya faru
sai ya tura dakaru hamsin don su kamo Himal su kaishi kurkuku. A wannan lokaci HImal na can
bayan gari shi kadai yana baiwa kansa horon yaki, koda dakarunj hamsin suka afka masa da niyyar su
cafkeshi sai ya hau su da duka, cikin dakiku kadan
ya sumar da mutum arba'in, mutum goma kuwa
suka cika wandonsu da iska. Yayin da dakaru
goman suka kaiwa Sarki labarin 6arnar da Yarima
Himal ya yi sai aka sake tura wadansu dakarun guda
dari, suma duk a kakkarye suka dawo, al'amarin da
ya fusata Sarki Asmaru kenan ya dubi Sarkin
yakinsa Kurbas ibni Hamzil ba tare da ya ce dashi
komai ba. Nan take Kurbas ya mike ya tafi gidansa
ya yi shigar yaki sannan ya kama dokinsa ya hau
yua nufi bayan gari shi kadai, hakika komai
jarumtakar Sadauki idan ya ga Kurbas a cikin irin
wannan shiga da ya yi dole ne ya razana.
Sadauki Kurbas ya kasance garjejen kato, ya
tsawo kuma ga kauri. Yana da karfin tsiya fiye da
kwatancen mai kwatance domiun idan ransa nya
baci, komai girman bishiya idan ya nausheta sai
hannunsa ya nutse a cikinta. Idan kuwa ya doke ta
da kafarsa sai ta jijjigo jijiyoyinta daga karkashin
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
kasa ta fadi kasa, in dai tsagwaron karfi ake
magana babu kamarsa a wannan zamani, a harkar
tsafi ne su Sarki Asmaru suka sha gaban sa yake
musu biyayya bisa dole.
Yarima Himal na zaune shi kadai a dokar
daji bisa wani dutse ya cake takobinsa cikin kasa a
gabansa ya kura mata idanu kawai. Kai da ganinsa
kasan yayi nisa a cikin kogin tunani, kwatsam sai ya
jiyo sukuwar doki a gabansa. Koda ya dago kai yayi
arba da Kurbas cikin shigar yaki sai ya razana ya
mike tsaye zumbur yana shawarar tsayawa
koguduwa, tabbas yarima Himal ya san cewa
Kurbas ya fi karfinsa nesa ba kusa ba domin ruwa
ba sa'an kwando bane to amma da yake koda wasa
basu taba jarraba fada da juna ba kowa na baiwa kowa kimarsa.
Sadauki Kurbas ya iso har gaban yarima Himal bisa dokinsa. Dokin ya daga kafafunsa sama kamar zai banke Himal yana haniniya amma ko gizau Himal baiyiba. Al'amarin da ya baiwa Kurbas mamaki kenan, kawai sai ya sauko daga kan dokin
nasa ya dubi Himal ido da ido ya ce "Na zo bisa umarnin sarki don na tafi dakai izuwa kurkuku, ina mai shawartarka daka bani hadin kai cikin ruwan sanyi ko kuma na tafi da kai ta tsiya tsiya." Koda jin wannan batu sai Himal yayi murmushi ya ce "Ai kuwa sai dai ka tafi dani ta
10
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gint
tsiya tsiya don bazan taßa baka hadin kai ba." kafin
Himal ya gama rufe bakinsa tuni Kurbas ya kawo
masa wawar cafka ya daga shi sama da niyar ya
fyadashi da kasa domin ya suma ya tafi dashi a
saukake.
Cikin zafin nama da nuna kwarewa da
bajinta Himal yayi wata irin katantanwa a sama ya
zulle daga hannun Kurbas ya duro a bayansa bisa duga dugansa kuma ya hankada Kurbas gaba ya tafi
taga-taga kamar zai fadi amma sai ya noke ya juyo
yana mai yiwa Himal tafi domin yayi mamakin
wannan bajinta da ya nuna. Kurbas ya ci gaba da
yiwa Himal tafi yana murmushi a gareshi.
Shi kuwa Himal sai ya murtuke fuska ya zare
takobinsa daga cikin kasa ya ce "Ya kai Kurbas
kayi sani cewa ko ta wane hali bazan bari ba ka
kaini hannun sarki ba, sai dai ka kai gawata."
Ko da jin haka sai Kurbas ya bushe da dariya
ya ce "Ai a raye akace na kai ka don ayi maka
hukunci bisa laifin da ka aikata don haka kowa a
rayen zan kaika. Yaro ka yi kuskure da kake tunanin
har zaka iya yakata ko iya rufcewa daga hannuna."
Gama fadin hakan ke da wuya sai Kurbas ya
zare takobinsa shima ya kaiwa Himal mugun sara.
Himal ya kare saran da takobinsa, amma saboda
karfın saran sai daya tsugunna kasa bisa
gwiwoyinsa ya ji kamar an dora masa dutse mai
11
girma; nan fa suka ci gaba da dauki ba dadi a hakan
wato Kurbas na tsaye shi kuma Himal na tsugunne. Kurbas na ta kawo masa sara da suka yana kokarin
karewa amma ya kasa mai da martani domin fifikon
a baiyane yake, ya yinda aka dan jima kadan a haka
ya zamana Kurbas bai yiwa Himal rauni ba ko sau
daya shi kuma Himal ya kasa mai da martani, sai
duk suka gaji kowannansu ya rinka daga
makaminsa sama da kyar. Koda Kurbas ya ga
wankin hula zai kaishi dare sai ya fusata yai jifa da
takobinsa ya sake rarumar Himal da nufin yai masa
mugun kaye ya take amma sai Himal ya sakle
murguda jikinsa tamkar sifirin yayi katantanwa har
sau bakwai a sama sannan ya fado kasa, Kurbas ya
kai masa cafka, shi kuma ya fice fit ta tsakankanin
kafafunsa. Hanfa suka kasa tsere tamkar kyanwa ta
biyo 6cra, kuskuren da Himal yayi kena domin bai
san ccwa ko da zaki Kurbas ya kasa tere sai ya
cimmasa saboda Allah ya hore masa azababben
gudu kuma ga baiwar rashin gajiya.
Kurbas na iya shafe yini guda yana gudu a
cikin daji ba tare da ya tsaya ba don ya huta.
Shi kuwa Himal gudune dashi natsiya tsiya
amma bashi da daguwar juriya.
Yayin da suka sami sa'a kacal suna tseren guda duk da cewar Himal ya baiwa Kurbas ta zara
mai yawa sai gashi HImal ya fara sarewa yana gudu
12
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
yana tangadi kamar zai fadi. Shi kuwa Kurbas sai
ya zami kamar sannan ne ma ya fara gudun, ai kuwa
kamar kiftawar ido ya cimma Himal har ma sai da
sha gabansa. Koda Himal ya ga Kurbas. a gabansa
sai gwiwoyinsa suka yi sanyi ya yanke jiki ya fadi
gaban Kurbas yana haki, ba tarc da bata wani lokaci
ba Kurbas ya kama Himal a ruwan sanyi yai masa
daurin huhun goro ya azashi bisa doki ya tafi da shi.
Bai zame ko'ina da shi ba sai gaban sarki Asmaru,
da zuwa sarki ya yankewa Himal hukuncin dauri na
shekaru uku a gidan maza, nan take Kurbas ya tafi
da Himal kurkuku sai da tabbatar da cewa an sashi
cikin daki an kulle sannan ya tafi.
Lokacin da labari ya riski Hasilatul Kurbas
wato matar Himal kuma 'ya ga sadauki Kurbas sai
ranta ya baci, kuma hankalinta ya dugunzuma tayi
rantsuwa da girman mahaifinta cewa sai ta fitar da
mijinta daga cikin kurkuku a wannan darc.
Hasilatul Kurbas ta kasance gagarumar
jaruma kuma basadaukiya, saboda tsananin karfinta
da jarumtakarta ne ake ganin ma kamar tafi
mahaifinta jarumta. Hasilatul Kurbas ta kasance
kyakykyawar gaske domin a fagen kyau ana ganin
cewa ita da Abidatul Azamal 'yar sarki Azmal za su
iya zama kunnen doki ko kuma daya tafi daya da
kadan. Abin da yasa ba'a tantance ba shine basu
taba haduwa ba a waje guda. Matsalar Hasilatul
13
Taskar Tsufi Abdul'aziz Sani M/Gini
Kurbas daya ce wato rashin iya tsafi kuma bata nuna jarumtakarta da karfinta sai a filin yaki domin sau tari ma ita ce take zuwa ta wakilci mahaifinta
duk sa'adda za'a tafi babban yaki wanda ake matukar shakkar abokan gaba, shi kansa sadauki
Kurbas yana alfahari da Hasilatun Kurbas kuma ya yarda har a cikin ransa cewa 'yarsa tafishi karfi da jarumta.
A halin yanzu Himal da Hasilatul kurbas sun
haifi 'ya'yan biyu mace da namiji. Macen itace babba, yarinya ce 'yar kimanin shekaru tara mai
suna Izaima, shi kuwa namijin shekararsa biyar ana
kiransa Uhairu.
Kafin Himal da Hasilatul Kurbas suyi aure
sai da suka yi gagarumar soyayya irin wacce ba'a
tabayi baa tarihin Kasar domin ansha
gwagwarmaya sabodatarin yawan masoyan
Hasilatul Kurbas. Sai da aka sa wata babbar gasa
mai matukar wuya a tsakanin masoyannata mutum
dubu daya.
Yanayin wannan gasa shine an debi
wadannan masoya na Hasilatul Kurbas su dubu
daya izuwa tsakiyar wani daji wanda babu komai a
cikinsa face dusar kankara sai kuma wasu irin
muggan dabbobi masu rayuwa a cikin kankara wadanda ke da matukar girma da karfi, su dai dabbobin sun kasahce masu siffa irin ta Bauna, suna
14
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
da farata manya-manya masu tsini da kaifi tamkar
na takobi.
Gaba daya wadannan masoya na Hasilatul
Kurbas su dubu daya an ajiyesu ne acikin wannan
dajin babu mai makami ko guda kuma babu wata
sutura a jikinsu face bante na fata, saboda haka ana
zubesu acikin dajin suka kama makyarkyatar sanyi.
Kafin ma muggan dabbobin dajin su farmusu sanyi
ya fara hallaka wasu daga cikinsu. Daga nan kuma
sai dabbobin suka dunga faso kankara daga kasa
suna fitowa sama suna wani irin gurnani mai ban
tsoro wanda ya dinga firgita jarumai dubun. Nan fa
dabbobin suka rinka walima da sassan jikin
bil'adama, kafin wani lokaci sun cinye jarumai dari
tara da casa'in da tara saura mutum daya kacal
kuma ba kowa bane face jarumi Himal, shima in ba
don ya cire farcen daya daga cikinsu ba da karfin
tsiya ya rukeshi a matsayin makami ba datuni sun
hallaka. Nan fa aka fara mugum artabu tsakanin
jarumi Himal da wadannan dabbobi kuma a lokacin
ne sanyin wajen ya fara yi masa illah. Koda yaga
masifa tai masifa saı ya sunkuci gawar daya daga
cikin dabbobin wadda ya kashc da hannunsa ya
runtuma da azababben gudu, dabbobin kuwa suka
tasam masa a guje suna neman kure masa gudu.
Matacciyar dabbar na ruke a hannunsa tamkar ya
dauki silan kara duk da kasancewar girman ta da
15
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
dake hannunsa yana kan wanna hali na gudu, a haka
nauyinta ya wuce kima sai ya shige fedeta da farce
ya sami nasarar kammala fedeta ya yiwa kansa riga
da fatar jikin dabbar wadda ya fede, nan take ya
daina jin sanyi jikinsa ya daina karkarwar dari.
Koda jin hakan sai ya tsaya cak ya waigo yai arba
da dabbobin sa'adda bai wuce taku daya ba
tsakaninsa da su, kamar a mafarki sai suma
dabbobin suka tsaya kyma aka fara kallan kallo tsakaninsu dashi. Jarumi Himal ya kwarara uban ihu
irin wanda ke razana barade a filin daga, a lokaci guda ya afkawa dabbobin da sara da wannan farce
irin na jikinsu, nanfa yaita ragargazarsu suka dunga zubewa kasa matattu. Ya yinda dabbobin suka
fuskanci cewa lallai baza su iya dashi ba sai suka juya da baya suka fara gudun ceton rayukansu.
Lallai gaskiyar masu magana da suka ce idan kaji ki gudu sa gudune bai zoba, ai kuwa jarumi Himal bai
ragawa dabbobin ba sai da ya kare musu gudu daya bayan daya yana zare musu ruhin numfashi. Kai
wasu ma har karkashin ruwa ya dunga binsa yana
kashe su sai da ya tabbatar da cewa ya kashesu gaba daya sannan hankalinsa ya kwanta. A sannan
ne ya gasa daya daga cikin dabbobin ya ci ya koshi,
bayan ya sha ruwa kuma ya huta sai yayi guzurin
naman da ya gasa mai yawa tare da ruwa sannan ya
kama hanya yayi ta tafiya a cikin dusar Kankarar.
16
Tasker Tsafi Abdulaziz Sani M/Gini
Ya kwana nan ya tashì can sai da ya kwana goma
sha daya a cikin wannan mugun daji yana tafiya
sannan ya fita daga cikinsa, bayan ya sake shafe
kwana tara ne ya iso birnin Babila.
Dama tuni an zuba dakaru a bayan gari
wadanda za su taryi jarumin da ya sami nasarar
wannan gasa. Koda suka hango jarunmi Himal sanye
da fatar wadan nan dabbobi na dajin kankara sai
suka ruga gareshi suna shewa tarc da yi masa
jinjina, nan take suka dagashi sama suka tafi dashi
izuwa cikin gari. A wannan-rana aka daura auren
Himal da Hasilatul Kurbas domin an yarda da
jarumtakarsa an san cewa ya dace da ita. Wannan
shine takaitaccen tarihin soyayyar yarima Himal da
Hasilatul Kurbas.•
Lokacin da bakin ciki ya yiwa Hasilatul
Kurbas yawa sakamakon samun labarin daure
mijinta a kurkuku har tsawon shekaru ukar zuciyarta
ta kama tafarfasa. Izaima da Uhairu kuwa sai suka
kama kuka, koda Hasilatul Kurbas taga yadda
'ya'yanta suka shiga matsananci damuwa sai ta shiga
rarrashinsu sannan ta kira wata baiwarta mai suna
Kasirat wadda dama itace tayi renonsu tun suna
jarirai, tace da ita "Gasunan ta kula dasu sosai
domin ita yanzu zata fita ne kuma bata sani ba ko
zata dawo a raye."
Ko dajin wannan batu sai hankalin Kasirat ya
17
Taskar Tvafi Abdul'aziz Sani M/Gini
dugunzuwa ta ce "Ya shugabata ke kuwa ina ne inda zaki je haka har da kike tunanin ba zaki dawo a
raye ba?"
Hasilatul Kurbas tayi murmushi sannan ta dafa kafadar Kasirat cikin yanayin yake ta ce "kar ki damu da inda zanje ke dai kawai ki kula da -"yayana, ki rakestf amana koda a bayan raina ne."
Ta na gama fadin hakan sai ta juya ta shiga cikin turakarta ta bar Kasirat nan a tsaye a tsakar gida cikin tsananin damuwa da fargaba.
Hasilatul Kurbat bata fito ba daga cikin turakarta sai da dare ya raba, sanye cikin shigar yaki
ta fito, ta sanya farin sulke da hular karfe a kanta,
ba'a ganin komai a fuskarta face idanunta, hancinta
da bakinta sannan kuma ta ratayo wata zabgegiyar
takobi a bayanta. A kuibin cinyoyinta dama da hagu
kuwa wadansu zabga zabgan wukakene acikin
kufensu guda biyu, koda fitowarta sai ta ruga inda Bargar dawaki yake ta kwance wani ingarma farin
dokinta ta daura masa siddi da sauri wannan-ta haye
kansa ta zabureshi da gudu. Tana isa kofar gidan
tadakawa masu gadi tsawa tana mai umartarsu dasu
gaggauta bude mata kofa, in ba don sun dauki
muryartaba da baza su bude kofarba domin tuni sun
razana jikinsu ya kama karkarwa tun sa'adda suka
hangota ta durfafosu sun a tsammanin cewa wani
sarkin barayinne ya kawo musu mamaya, nan da
18
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
nan maso gadin suka budewa Hasilatul Kurbat kofa
ta fice sukwane, so kowa suka mai da kofa suka
rufe.
Kai tsaye Hasilatul Kurbat ta durfafi
kurkukun garin ba tare da shayin komai ba duk da
kuwa tasan cewa akwai gagarumin tsaro a cikin
kurkun wanda aka yiwa lakabi Ukubatul dukkan.
Shi dai Ukubatul dukkan kurkuku ne wanda
yai kaurin suna a duniya saboda tsananin azabar da
ake yiwa fursunonin cikinsa da kuma mugun tsaron
da aka yi masa, shi dai wannan kurkuku an gina
shine akan wani tsibiri wanda wani makeken kogi
ya zagayeshi. Dole sai mutum ya shiga kwale kwale
yayi tafiya yini guda acikin kogin sannan zai isa
wannan kurkuku, shi kuwa ginin gidan kurkukun
anyi shine da zallan duwatsun wuta, kofofin gidan
kuwa da tagoginsu anyi sune da murtuka murtakan
karafa masu tsananin kwari wadanda sai makeri ya
shafe sa'a uku kafin ya iya yankasu.
Dakarun dake tsaron wannan kurkuku
mutum dubu dari uku ne da sittin da uku. Gaba
dayansu suna sanye da jajayan tufafi kuma ruke da
muggan makaman yaki, dukkanninsu sun kasance
zakwakumai a fagen yaki wadanda basu san tsoro
ba kuma idan bala'i yai bala'i basa ja da baya don
ganin mutuwa sai dai su kara tun kararta gasu