da
bakin naci tamkar talauci.
19
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
Bayan Hasilatul Kurbas ta shafe sa'a uku
tana gudu bisa dokinta a cikin wannan dare sai ta iso daf dainda take iya hango wannan tsibiri, inda kurkukun Ukubatul dukkan yake daga can nesa kai
kace dan mitsitsin dutsene aka azashi bisa tsibirin,
wannan wuri inda Hasilatul Kurbas ta iso dajine fatal mai dauke da wadansu irin manya-manyan bishiyoi.
Ba tare da bata wnai lokacin ba Hasilatul
Kurbas ta sauko daga kan dokinta ta daureshi a jikin wata bishiya sannan ta fara nazarin dajin, koda ta dubi wata makekeyar bishiya sai ta daka tsalle sama
ta doketa da kafa daya, abinda da basadaukiya,
wadda tayi gadon sadaukantaka take bishiyar ta fadi
ta tsuguna sannan ta fiddo wani zabgegeb gatarinta
ta kama sassaka bishiyar. Har sai da gari yawe rana
ta kwalle tana wannan aiki sanna ta hattama kera
kwale-kwalen nan. Bayan ta kimtsa cikinta sannan
ta bude jakarta ta fiddo abin kalaci ta kimtsa cikinta
sannan ta haye kan wata doguwar bishiya ta kama aikin rago domin ta rama bashin barcinta na daren
jiya, amma kafin ta hau kan bishiyar sai da ta kwance dokinta domin ya sami damar tafiya kiwo
don ya ciyar da kansa.
Sa'adda Hasilatul Kurbas ta sami kimanin
sa'o'i hudu tana barci ne wasu dakaru masu tsaron
kurkukun Ukubatul Dukkan sun kan kimanin su
20
1
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
dari suka shigo kwalc-kwale guda hamsin suka haye wannan kogi suka iso wannan daji inda Hasilatul Kurbas taya da zango.
Dama a ka'ida kullum da safc sai sun zo
wannan wuri don a tabbatar da tsaro a nahiyar
saboda kada a kawo farmakin sumame. Ai kuwa wadan nan dakaru na zuwa sukayi arba da kwale kwalen nan wanda Hasilatul Kurbas ta kera, koda ganinsa sai suka fara tafiyar sanda da lebe labe kuma suka rarrabu don sun tabbatar da cewa akwai
wadansu bakin dake a dajin masu shirin zuwa can kurkukun.
Sai da wadan nan dakaru suka shafe kusan
rabin sa'a a cikin dajin suna dubc-dube amma basu
ga kowa ba face dokin Hasilatul Kurbas wanda ya je
bakin wata korama ya kafa bakinsa yana shan ruwa.
Lokacin guda dakarun su duka suka yi wa dokin
kawanya suka zusa idanu kawai, shugaban dakarun
wani barde da ake kira Uzaima ya dubesu gaba daya
yace lallai muna da bako a cikin dajin nan kuma
tabbas shine mai wannan doki kuma shine ya
sassaka wancan jirgin ruwa. Abin da za muyi kawai
mu kashc wannan doki tunda ba muga mai shi ba in
yaso muci gaba da neman mamallakinsa, koda gama
fadin hakan sai Uzaima ya dubi wani barde cikin in
kiya. Barden ya zare mashinsa ya ja da baya sannan
ya saita dokin Hasilatul Kurbas da mashin, koda ya
21
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
tabe hannunsa da nufin ya cilla mashin izuwa ga dokin kawai sai aka ga kibiya ta zo ta nutse a cikin
makogwaronsa, take barden ya saki mashin dake
hannunsa suka sulale kasa tareshi da mashin cikin
firgici su duka dakarun suka waigo baya suna duban
inda kibiyar ta fito, kawai sai sukayi arba da jaruma Hasilatul Kurbas ta durfafosu cikin tafiyar takama
tana ruke da sharbebiyar takobinta, nan fa suka fara
yi mata lugudan kibiyoyi, kawai sai tasa takobinta
ta dunga kakkabe kibiyoyin cikin zafin nama ko
daya bata samu damar shiga jikinta ba. Al'amarin da
ya firgita dakarun kenan suka tabbatar da cewa
lallai sun gamu da gamowa amma saboda sun
kasance marasa tsoro sai suka ci gaba da cillo mata
masu. Nan ma tayi ta kadesu da takobinta suna
kakkacyewa da zubewa kasa. Ya yinda suka ga tya
kusa cimmasu sai duk suka zare takubbansu suka yi
ca akanta da niyar yi mata rubdugu. Wogogo, nan
fa ta shiga ragargazarsu, sai dai kaga kafafu da
hannaye suna tsinkewa daga cikin gangar jikin bil
adama, kawuna kuwa suka rinka shawagi a sararin
sama tamkar yara na wasan tamola, cikin kankanin
lokaci jaruma Hasilatul Kurbas ta kashesu gaba
daya ya rage saura shugaba Uzaima- shi kadai a
tsayc a gabanta jikinsa na kyarma shi bai gudu ba
kuma bai tunkareta ba sai kallan kallo suke kawai,
duk jikinta ya baci da jinin maza kuma ko kwarzane
22
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
daya ba'ayi maya ba.
Cikin murya mai. rawa Uzaima ya dubi Hasilatul Kurbas ya ce "Ya kai wannan gawurtaccen sadauki wanene kai? kuma menene manufarka na son zuwa Ukubatul Dukkan?"
Koda jin wannan tambaya sai Hasilatul Kurbas ta mai da takobinta cikin kufe sannan ta
cire hular karfen dake kanta Uzaima yai arba da fuskarta. Al'amarin da ya matukar razanashi kenan, bai san sa'adda ya tsuguna kasa ba yana tuba da
neman afuwa.
Hasilatul Kurbas ta daka masa tsawa ta ce
"Ya kai Uzaima na sanka tun kana matsayin
sauriyin bawa a gidanmu, ina so ka koma Ukubatul
Dukkan ka sanar da Babban shugabanku sadauki
Muhukur Azbalu cewa gani nan tafe don fitar dfa
mijina yarioma Himal, ko dai ku bani shi cikin
ruwan sanyi ko kuma takobina tashi jininku gaba
daya, ka gaya masa cewa ba zan iso ba sai gobe da
hantsi domin ku sami damar yin. duk irin shirin da
kuke son kuyi, maza kaje ka isar da wannan sakо,
kuma ka gaya masa cewa ko tsuntsune na gani zai
giffa ta wannan dajin da nufin zuwa cikin birnin
Babila sai na mai dashi gawa."
Koda gama fadin haka sai Uzaima ya mike
zumbur ya juya da gudu har ya isa bakin kogi inda
jiragensu suke, nan da nan ya shiga kwalo-kwalc
23
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
guda ya nufi tsibirin da kurkukun Ukubatul Dukkan yake. Ita kuwa Hasilatul Kurbas sai ta sake komawa kan bishiyar nan da take barci tasake kwanciya don ta Karasa barcinta ashc dama tun sa'adda dakaru suka shigo dajin wani tsuntsu ta tasheta sakamakon digomata kashinsa a kofar hancinta. Ai kuwa tana farkawarne taji motsin tafiyar laben dakarun ta farga dasu, wannan shine abin da ya faru tsakanin jaruma Hasilatul Kurbas da dakaru bayanta baro
cikin
cikin birnin Babila don kubutar da mijinta daga kurkukun Ukubatul Dukkaa.
A can tsibirin Ukubatul Dukkan kuwa tunda aka shigar da yarima Himal cikin wani daki mai duhu bai sake ganin koda tafin hannun saba har sai da ya kwana ya yinnni, kuma ko ruwa ba'a bashi ba bare ayi maganar abinci, koda Himal y tuna cewa shifa dan sarkine amma kuma gashi anyi masa irin
wannan wulakanci sai takaici ya kamashi gami da tsananin bakin ciki wanda ya haddasa fitowar kwalla a cikin idanunsa. Yana cikin wannan tunani
ne shugaban kurkukun Hukunul Azbalu tare da
wasu barade biye dashi şuka zo kofar dakin ruke da fitila a hannu da kuma wata tsohuwar tasa. Koda
Himal ya ji motsin tafioyarsu sai ya yunkura ya mike tsaye, da zuwa suka tsaya a gaban kofar dakin
wacce ta kasance ta sandunan karafa suna iya
shima haka. Bayan sun dallare fuskarsa da ganinsa
24
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
hasken fitila sai Muhukul Azbalu ya bushe da
mahaukaciyar dariya sannan ya ce "Ya kai Himal
shin zaka iya tunowa da wannan fuska tawa?"
Himal ya dubi Muhukul Azbalu da kyau kawai sai
ya gyada kai cikin alamun karayar zuci.
Muhukul Azbalu ya sake bushewa da dariya
ya cc "A she dai zaka gane ni duk da cewar yau
shckara goma sha biyar kenan rabon da muga juna,
ni ne dai wannan wanda ka taba yiwa dukan kawo
wuka sa'adda na yiwa wata yarinya fyde a bayan gari, in ba don sirikinka sadauki Kurbas ya kawo
mini dauki ba a wannan lokaci da tuni ka sheka
dani barzahu, yau fa gaka a hannuna ya kai yarima, daga yanzu na zama sarkinka ka zama bawana, na
rantse da darajar gemun ubana shekaru uku nan da
zakayi anan sai na gana maka azaba irin wacce ba'a
taba yiwa wani ba a gidan nan."
Koda gama fadin hakan sai Muhukul Azbalu
ya karbi wannan tsohowar tasa daga hannun wani badakare ya mikawa Hamil ya ce "Wannan shine
daddadan abincinmu anan gidan wanda yafi kowanne dadi, a matsayinka na dan sarki naga ya
dace mu fara yi maka marhaban da shi. Nasan kana jin yunwa sai ka hanzarta cika cikinka don kada
cutar yunwa tayi maka lahani."
Yayinda Himal ya karbi tasar ya duba abin
dake ciki sai yaga ashewasu irin kananan tsutsotsine
25
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
a ciki har suna wani irin mugunyar doyi, cikin fushi
Himal ya watsowa Muhukul Azbalu tsutsotsin a
fuskarsa ya ce "Ku barni na mutu da yunwa ba zanci
abin cin ku ba."
Faruwar hakan ce ta fusata Hukumul Azbalu,
nan take yasa aka bude kofar dakin ya shiga ya rufe
Himal da duka da wani shirgegen kulki har sai da ya
kaishi kas. Bai gushe ba yana dukansa sai da yaga
ya suma sannan ya kyaleshi. Tabbas in ba don cewa
hannayen Himal da kafafunsa a daure suke ba cikin
sarkoki da hakan bata faru ba.
Bayan Hukumul Azbalu ya ga cewar Himal
ya suma sai yasa aka ciccibeshi aka fito dashi waje
izuwa tsakiyar wani babban fil a harabar kurkukun
aka sake bankareshi ajikin wani katako mai gwafa
biyu aka daureshi tamau da wasu manyan sarkokin
karfen sanna aka kwara masa ruwa ya farfado.
Bude idanunsa ke da wuya ya yi arba da Hukumul
Azbalu zaune a gabansa bisa wata kujera an hura
wuta yana gasa wadansu tsitakoki guda biyu acikin
wutar har sunyi jajawur. Hukumul Azbalu ya zaro
tsitakokin daga cikin wutar ya nufo Himal gadan
gadan yana murmushin mugunta da nufin ya gakasu
a jikinsa, al'amarin. da ya duguzuma hankalin
yarima Himal kenan don yasan cewa in dai ya caka
masa tsitakokin ba karamin lahani zai yi masa ba.
Sai da ya rage saura taku biyu ya iso gabansa kawai
26
Taskar Tsafi Abdul'áziz Sani M/Gini
sai yaji an kira sunansa a baya, cikin fushi Hukumul
Azbalu ya waigo. Take ya yi arba da Uzaima
durkushe bisa guiwoyinsa yana faman haki.
Hukumul Azbalu ya yarda tsitakokin dake hannunsa
ya rugo wajen Uzaima yana mai tambayarsa cikin
firgici, ina abokan nan aikinka? me ya faru gareku?
Nan take Uzaima ya kwashe labarin
gamonsu da Hasjlatul Kurbas ya zaiyane har da
sakon da ta bashi cewar gatanan tafe gobe da hantsi
don karbar mijinta. Ko dajin wannan batu sai
yarima Himal ya bushe da dariyar farin ciki shi
kuwa Hukumul Azbalu sai hankalinsa ya duguzuma
ya rasa abin da zai yi. Nan take yasa aka dauke
Himal aka kaishi can cikin wani daki dake
karkashin kasa aka kulle sannan ya tara dukkanin
dakarun gidan aka fara shawarar yadda za'a bullowa
wannan gagarumar basadaukiya mai zuwa gobe.
A can cikin birnin Babila kuwa sarki Asmaru
na zaune bisa karagar mulki ana tsakiyar fadanci sai.
ga wani shahonsa na tsafi ya dira a gabansa. Shahon
ya yi wani irin kuka mai ta da hankali, sannan ya
bude fukafukanshi ya tashi sama, ya fice daga cikin
fadar. Ko da faruwar hakan sai sarki Amsaru ya
mike zumbur ya nufi cikin gida da sauri-sauri,
gudu-gudu. Al'amarin da ya razana sauran
fadawansa kenan da sauran mutanen gari, domin
bisa al'ada duk sa'adda wannan shaho ya zo ya yi
27
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
irin wannan kuka tabbas wani mugun abu ne zai
faru.
Luhura mahaifiyar yarima Himal na zaune a
harabar gidan sarautar kuyangi sun kewaycta, ana yị mata hidima, kawai sai ta ga sarki ya zo ya wuce da sauri cikin tsananin damuwa. Ai kuwa sai ta mike zumbir ta bishi a guje, don ta taushe shi kamar yadda ta saba, a duk lokacin da taga ransa ya baci. Sarki Asmaru dai bai dangane da ko'ina ba, sai cikin turakarsa. Da zuwa ya bude wata karamar akwatu
ya dauko, madubinsa na tsafi.
A daidai lokacin ne Luhura ta iso daf da shi
ta tsaya a bayansa. Asmaru ya shafi madubin tsafin
da tafin hannunsa, take ya ga duk abin da ya faru tsakanin Hasilatul Kurbas da dakarun nan dari, wato.
su Uzaima, sannan ya ga yadda hankalin su
Hukumul Azbalu ya dungunzuma, a can kurkukun
Ukubatu Dukkan. Nan take zuciyar sarki Asmaru ta
kama tafarfasa, ya jiyo a fusace ya dubi Luhura ya
ce, "Tabbas wannan karon sai na kashe dan nan
naki."
Koda jin haka sai Luhura ta fashe da kuka,
sannan ta durukusa bisa gwiwuyinta, ta kama kafar
sarki Asmaru tana mai rokonsa ta ce, "Ya kai sarkin
sarakai ka tuna cewa ni ce matarka mafi soyuwa à
ranka, fiye da dukkanin matanka. Na sani cewa na
rokeka wannan alfarma sau biyu a baya kuma ka yi
28
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Ginİ
mini. Ina mai dada rokonka a karo na uku da kada ka kashe mini dana, domin ina sonsa fiye da komai
na rayuwata. Idan ka kashe shi tamkar ka yanke mini farin cikin duniya ne. Na sani cewa Himal ba jinin ka ba ne, domin da cikinsa na zo gidan nan, wazirinka mijina na da wanda ka kashe, shi ne mahaifinsa. Ka sani cewa kai ne ka umarce ni da na 6oye wannan sirri ga kowa, kuma na bi umarninka.
Ina son na ci albarkacin bin wannan umarnin naka
ka janyc hukuncin kisa akan yarima Himal." Yayin da Luhura ta zo nan a jawabinta, saі jikin sarki Asmaru ya yi dan sanyi, amma har yanzu fuskarsa a murtuke takc, babu alamar tausayi ko imani. Cikin kunan rai ya cakumo kwalar rigar
Luhura ya tasheta tsayc. Ya dube ta da kakkausar
murya yа сс,
"Na ji zan yi miki wannan alfarma, amma ita
ce ta karshc, kuma duk da haka sai na yi wa dan ki azaba mai radadi, tare da matarsa Hasilatul Kurbas,
sannan zan huce takaicin da nake ciki."
Yana gama fadin hakan ne ya bangajс
Lahura ta fadi kasa, sannan ya fice daga cikin turakar da sauri. Koda sarki Asmaru ya isa fada sai ya tura a kira masa sarkin yaki sadauki Kurbas. Cikin kankanin lokaci kuwa ya bayyana gabansa. Asmaru ya dubi Kurbas fuskarsa cike da yanayin
fushi ya ce, "Sarkin yaki ka yi sani cewa 'yarka a
29
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
halin yanzu ta kusan isa kurkukun mu na Ukubatul
Dukkan, domin kubutar da mijinta wato dan mu
yarima Himal, har ma ta kashe mini dakaru casa'in
da tara, masu tsaron kurkukun. Hakika wannan abu
ya matukar kona mini rai, don haka na umarce ka
da ka hanzarta ka je ka riske ta, kafin ta sami
nasarar fito da shi kuma ka zo mini da ita nan a
raye, domin na yi mata hukunci daidai da abin da ta
aikata."
Sa'adda sarki Asmaru ya zo nan a zancensa,
sai hankalin sadauki Kurbas ya dungunzuma, ba dan
komai ba sai don tsananinn kaunar da yake yi wa
'yarsa, Hasilatul Kurbas. Tabbas inda ya san za ta
aikata wannan mummunan aiki da ya hanata. Yanzu
ga shi da hannunsa zai je ya kamota a yi mata
hukunci. Tabbas ya san cewa hukuncin bai zai wuce
na azaba ba, da kuma dauri. Ba tare da nuna
damuwa ba, cikin karfin hali sai sadauki Kurbas ya
risina ya ce da sarki.
"Ya shugabana hakika ina goyon bayanka
bisa hakan, domin yarinya ta aikata babban laifi,
lallai ta cancanci horo sai dai ya kamata ka ba ni
taimako yadda zan risketa akan lokaci, kafin ta isa
can tsiburin Ukubatul Dukkan."
Koda sarki Asmaru uya ji wannan batu, sai
ya tuntsure da dariya ya ce, "Kada ka damu ya
sarkin yaki, za mu hadaka da daya daga cikin
30
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
dakarun mu, wanda zai kai ka a cikin yini daya."
Nan take sarki Asmaru ya yi nuni da
hannunsa a cikin dan yatsansa ta tsaga kasa. Wani
murgujejen aljani mai mummunar siffa ya fito ta
cikin karkashin kasar ya risina a gaban sarki ya
kwashi gaisuwa, a lokacin da kasar ta koma ta hade tamkar ba ta taba tsagewa ba. Sarki Asmaru ya dubi
aljanin mai siffar mikiya ya ce, "Ya kai Kaiduzil
Azman ka yi sani cewa ban kira ka ba, don komai
sai domin ka dauki sarkin yakina ka kai shi izuwa jejin tsibirin Ukubatul Dukkan, domin ya kamo
'yarsa, jaruma Hasilatul Kurbas, ku zo mini da ita
nan a cikin abin da bai wuce kwana daya ba."
Aljani Kalduzil Azman ya yi murmushi ya
ce, 'An gama ya shugabana tabbas, shan ruwa ya fi
wannan aiki wahala a gareni."
Koda jin haka sai sarki Asmaru ya dubi sadauki Kurbas, shi kuma sai ya daka tsalle ya dane bayan Kalduzul Azman. Ba tare da bata lokaci ba aljani Kalduzil Azman, ya bude fukafukinsa ya btashi sama, cikin 'yan dakiku kadan ya kule a cikin
sararin samaniya. t
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin sarki
Asmaru da sarkin yaki sadauki Kurbas, a can cikin birnin Babila.
Al'amarin jaruma Hasilatul Kurbas kuwa tun bayan rabuwarta da Uzaima sai ta fara tunani, mai
31
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
zurfi inda ta gano kuskurenta na shaidawa Uzaima
lokacin da za ta iso tsibirin Ukubatul Dukkan.
Tabbas ta san cewa za su iya daukar kyakkyawan mataki, wata kila ma su dana mata wani mugun tarkon da za ta kasa hayewa duk da cewa ta yarda da jarumatakarta. Koda Hasibatul Kurbas ta zo nan
a tunaninta sai ta sauya shawara. Nan take ta mike tsayc ta kwashi duk makaman ta na yaki, ta daura a
jikinta, sannan ta gyara damararta. Kawai sai ta je ta ja kwalekwalenta izuwa cikin kogin nan ta shiga ciki ta kama tafiya a cikin kogin ta nufi tsibirin Ukubatul Dukkan kai tsaye ba tare da shakkar komai ba.
A can tsibirin Ukubatul Dukkan kuwa, su Hukumul Azbalu na ta shirye-shiryen makaman yaki, da kuma dana tərkuna iri-iri da raba mayaka
rukuni-rukuni a kowanne sashi, na katangun
kurkukun. Kuma gaba daya kofofin gidan da
tagoginsa sai da aka rufe su ruf. Babu wata kafa
wadda ko sauro zai iya shiga cikin gidan kurkukun.
Ba zato, ba tsammani sai kawai aka hango
kwalekwalen jaruma Hasilatul Kurbas ya ci rabin
tafiya, a cikin kogin wato saura bai fi tafiyar rabin
sa'a ba, ta iso tsibirin. Nan fa hankalin hukumul
Azbalu ya dungunzuma, kawai sai ya raba
dakarunsa kaso biyu, ya tura kaso guda cikin
kwalekwale da umarnin su tari Hasilatul Kubas su
32
Taskur Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
kashc ta ta kowannc hali, lallai kar so barta ta iso
tsibirin.
Tun daea nesa Hasibatul Kurbas ta hango
kwalckwale kimanin guda Cyu sut adinaro ta.
Ko da ta hango su sai ta yi murmushi, don ta san
cewa ita aka kawowa farmaki. Hasilatul Kurbas ta
kara tuka kwalekwalenta da sauri tana jan marar da
hanzari, har tana jin kamar ta yi fiffike ta riski
wadannan abokan gaba. Suma dakarun sai suka
kara azama don su riske ta, suna kwarara uban ihu
mai tabbatar da cewa ana daf da fara azababben
yaki.
Ai kuwa nan da nan aka yi mugun gamo.
Wohoho! Hakika mai karfi sai Allah ya isa. Nan fa
Hasilatul Kurbas ta nuna tsagwaron jarumtaka,
bajinta da kwarcwa, domin sai da ta zamo kəmar
tsuntsuwa mai tashi sama. Sai dai ka ga ta daka
tsalle sama ta ci kasuwar kawunann dakarun. Duk
kwalelen da ta dira a cikin dakiku uku take gamawa
da dakarun ciki, duk da cewa wasu na kawo mata
sara da suka. Kai wasu ma har da ka tsalle suke su
duro kanta, amma sai dai ka ga ta tarwatsasu tamkar
tana faskara itace. Nan da nan jini ya dinga malala
akan koginb yana gudu, kai da bala'i ya yi bala'i sai
Hasilatul Kurbus ta ga cewar jikin dakarunma ya yi
mata kadan don haka har jiragen na suma ta hada ta
dinga ragargazarsu sai da ta yi filla-filla da jiragen
33
Tuskur Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
da kuma sassan jikin dakarun.
Nan fa saman ruwan ya cika da kananan
sassan jiki marasa nauyi kamar irin su kunnuwa,
idanuwa da sauransu. Amma kamar kawuna, kafafuwa da hannuwa kuwa nutsewa suka yi a
karkashin kogin, cikin abin da bai wuce rabin sa'a
ba komai ya bajc akan kogin babu komai face jaruma Hasilatul Kurbas da kwalc-kwalenta kacal.
A daidai wannan lokaci ne aljani Kalduzil
Azman ya sauko kasa a can dajin nan na baya inda
Hasilatul Kurbas ta yada zango har ta kera kwale- kwalcnta. Aljani Kalduzil Azman ya shaki kamshin
bil adama ya dubi sadauki Kurbas ya ce "Tabbas
jaruma Hasilatul Kurfas ta shigo dajin nan sai mu
hanzarta nemanta."
Sadauki Kurbas ya gyada kai ya ce "Gaskiya
ne nima na ji kamshin wani turare-nata wanda ni ne
na ba ta shi kuma duk duniya babu mai irinsa face
ni." Yana gama fadin baka ne idanunsa suka ciko ds
kwalla, al'amarin da ya baiwa aljani Kalduzi)
Azman mamaki kenan, ya so ya tambayi Kurbas
dalilin zubar da hawayen amma da yake babu lokaci
sai ya yi shiru bai ce komai ba. Nan dai suka
bazama a cikin dajin suna neman Hasilatul Kurbas.
A can tsaunin Ukubatul Dukkan kuwa duk
abin da ya faru a cikin kogin nan tsakanin jaruma
Hasilatul Kurbas da rabin dakarun nan, Hukumul
34
Taskar Tsaji Abdul’aziz Sani M/Gini
Azbalu ya gani a cikin abin hangen nesa don haka
sai ya kwarara uban ihu ya zare takobinsa, suma
ragowar dakarun nasa sai suka yi yadda ya yi suka
yi cirko-cirko suna sauraren isowar Hasilatul
Kurbas.
Shi kuwa Yarima Himal dake can cikin
dakin karkashin kasa a kulle koda ya jiyo ihun
dakarun gidan sai ya cika da farin ciki don ya san
cewa matarsa ce ta iso tabbas lokacin fitarsa daga
cikin wannan kurkuku ya zo.
Ai kuwa bai dade ba da jin wannan ihu na
farko sai ya ji na biyu wanda ya fi na farko karfi,
kai har ma wani irin rugugi ya rinka ji wanda ya
haddasa girgizar gidan kurkuku gaba daya. Ashe kuwa a wannan lokaci tuni Hasilatul
Kurbas ta iso har ta afkawa dakarun gidan kan mai
uwa da wabi. Duk tarkunan da aka kafa mata sai
suka zamo a banza tamkar dama ta san dasu domin
kafin ta je kansu ma ta lalatasu. Nan fa ta bude kasuwar daukar rayuka, duk inda ta sa gabanta sai dai ka ga maza na zubewa kasa kamar tana sassabe
a gona. Kuma duk wanda ya zo gabanta ta ke yake
zama gawa.
Hukumul Azbalu nc kadai yakc iya dan kokari shima kuma ya ki yarda ya tsaya su kafsa
sosai da ya sha wuya sai ya gudu, sannan ya sakc
sumamowa ya dawo. Koda ganin yadda Hukumul
35 از
Taskar Trafi Abdul'aziz Sani M/ini
Azbalu ke yi sai Hasilatul Kurbas ta fusata ta kara
himma wajen kashe dakarun don ta karar dasu da
wuri. Ai kuwa ana samun sa'a guda sai ta gama da
kaso biyu cikin uku al'amarin da ya firgita dakarun
kenan suka rinka gudu suna neman табоya.
Shi kuwa Hukumul Azbalu sai ya fusata ya cire dukkan tsoro ya tareta gaba da gaba suka fara kafsawa, hakika Hukumul Azabatul ya yi matukar kokari, domin yana fadan ne iyakar karfinsa, da kwarewarsa don ceton ransa da cika umarnin sarki.
Sai da suka bata dan lokaci bai samu nasarar yi mata komai ba, ita ma haka.
Nan take zuciyar Hasilatul Kurbas ta harzuko ta sauya salon fada, inda ta yi jifa da takobinta ta rugo kan Hukumul Azbalu. Koda ya ga haka sai murna ta kama shi don yana zaton tabbas, zai samu nasara akan ta, tun da babu makami a
hannunta. Koda ta iso daf da shi, sai ya kawo mata
wawan sara, cikin zafin nama ta goce, takobin ta bugi iska. Kafin ya yi wani yunkuri ta yi masa barin makauniya a fuska ya ga taurarin mutuwa. Kawai
sai ta kama wuyansa ta murde da karfin tsiya ta yi jifa da gawarsa. Nan take ta sake ja da baya ta ruga inda kofar kurkukun take ta dokita, da kafa daya. Saboda karfin naushin kafar tata sai da kofar ta jijjige daga cikin gini, ta fadi kasa rikica. Hasilatu ta
kunna kai cikin kurkukun ta dunga balle kofofin
36
Tuskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
dakunan tana fito da fursunoni, tana kwalawa Himal
kira, amma shiru ba ta ji ya amsa ba. Al'amarin da
ya dugunzuma hankalinta kenan ta fara tunanin ko
an kashe shi ne, don haka sai ta fara kuka. Su kuwa
fursunonin nan sai suka kama murna, suka yi ta
guje-guje suna neman kwalckwalen da za su shiga
su fita daga wannan tsibiri.
Hasilatul Kurbas ta ci gaba da kuka tana
kwalawa Himal kira, tana kara kutsawa cikin gidan.
Ba zato, ba tsammani sai ta ji muryar Himal yana
amsa kiran. Nan fa murna ta kama ta, ta yi ta bin
sautin muryar har ta gano cewa a cikin gidan kasa
yake. Nan take ta ga wata kofa mai matattakala
izuwa kasa. Cikin hanzari ta ruga ciki har ta iso
dakin da Himal yake ciki. Da isarta ta bake kofar ta
shige ciki ta ciccißo Himal ta goyo shi a bayanta ta
fito da shi har waje, sanna suka rungume juna suna
kukan farin ciki. Har a lokacin hannayen Himal da
Kafafunsa a daddaure suke da sarkoki.
Suna manne da juna cikin tsananin farin
cikin ne, kawai suka ji wata irin iska mai karfi a
samansu cikin razani suka daga kawunansu sama,
suka yi arba da su. Ba wani ba ne face sadauki
Kurbas, bisa aljani Kalduzil Azman.
Kalduzil Azman ya sauko kasa-kasa daidai
tsawon su Hasilatul Kurbas, aka fara katlan-kallo
tsakanin sadauki Kurbas da su Himal. Cikin
37
Taskar Tsafi Ahdul'aziz Sani M/Gini
tsananin fuskata Kurbas ya dubi Hasilat ya ce, "Ya
ke 'yata don me za ki aikata wannan danyen
hukuncin? To ki sani ccwa yanbzu sarki ya aiko ni
na tafi da ke garc shi, kuma ba makawa sai na je da kc."
Ko da ya zo nan a jawabinsa, sai hawaye ya subuto masa. Ita ma Hasilat sai idanunta suka ciko
da kwalla, ta ce, "Ya kai Abbana ka yi sani cewa wajibi ne a gareni na ceci rayuwar mijina, kuma kai
ma wajibi ne a gareka ka cika umarnin sarkinka, domin idan ka ki hallaka ka zai yi. Abin da nake so da kai shi ne kowa dabararsa ta kwace shi. Ni kam daga yau na zama 'yar tawaye ga sarki Asmaru kai
ma ina shawartarka da ka yi masa tawayen....."
Kafin Hasilatul Kurbas ta gama rufe bakinta, tuni Kurbas ya kawo mata wawan naushi a fuska. In ba don ta sunkuya ba, cikin zafin nama da tuni ta sume. Nan fa suka fara azababben fada, suka wanzu
suna kai wa juna naushi kafa da hannu. Hakika duk wanda bai ga wannan fadan ba, bai more