kallo ba, domin karfi ne, ya hadu da karfi, sadaukantaka, juriya da bajinta suka yi karon batta. Sai da suka shafe sa'a shida suna gumurzuwa tsakanin 'ya da uban, ya zamana sun galabaita sun zube kasa sumammu, a tare lokaci guda. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin yarima Himal kenan, ya kama duru-duru a kansu ya rasa abin da zai yi.
38
Tuskar T'safi Abdul'aziz Sani M/Gini
Duk wannan abu da ke faruwa sarki Asmaru
na gani a cikin madubin tsafinsa, don haka sai ya
fusata ya kira wadansu manyan baraden aljanu guda
bakwai, masu tsananin karfin damtse da karfin
sihiri, wadanda yake matukar takama da su, ya tura
su izuwa tsibirin Ukubatul Dukkan da umarnin su
ballaka Himal da matarsa har dama shi kansa
sadauki Kurbas din.
Ai kuwa a cikin dakiku dari da ashirin suka
dirga akan tsibirin suka yi wa su Himal Kawanya. A
daidai lokacin ne Himal ya yayyafawa Hasilat da
Kurbas ruwa, suka farfado. Faruwar hakan ke da
wuya aljanun bakwai suka tasam musu gaba daya
da nufin su hallaka su. Ba zato, ba tsammani, sai ga
wani kyakkyawan aljani mai kirar jarumtaka ya
bayyana. Kamar walkiya ya sure su Himal su ukun
ya yi sama da su. Nan fa aka kasa tsere tsakaninsa
da aljanu bakwai na sarki Asmaru. Koda bakon
aljaninn ya ga aljanu bakwan sun kusan cim masa
sai ya fara wani irin karatu. Nan take kuwa уа баce
bata, tare da su Himal suka neme shi suka rasa.
Sa'adda sarki Asmaru ya ga wannan al'amari
a cikin madubin tsafinsa sai ya kurma ihu cikin
tsananin takaici da bakin ciki, kuma ya fashe da
kuka. Daga can sai ya dago kai ya shafi madubin
tsafinsa, sai ga fuskar sauraniya Abidatul Azmal ta
bayyana akai tana kyakyata dariya. Asmaru ya bude
39
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gimi
baki da niyar ya yi magana, sai ta daga masa hannu
ta ce, "Ai na san matsalarka. Tabbas wannan fada
ya fi karfinka, ai babban goro sai magogin karfe.Duk abin da ya faru tsakanin dakarunka da su
Hasilatul Kurbas na gani a nan fada ta. Kar ka damu
ni da kaina yanzu zan yi shiri na bi aljanin da ya
sace su na kamo su gaba daya."
WANENE WANNAN ALJANI DA YA
CI RAYUWAR SU HASILATUL KURBAS
DAGA SHARRIN ALJANU BAKWAI? WANE
IRIN GUMURZU ZA'A YI IDAN ABIDATUL AZMAL TA HADU DA JARUMA HASILATUL KURBAS? SHIN SADAUKI KURBAS ZAI YIWA SARKI ASMARU TAWAYE? WANE IRIN MULKIN ZALUNCI DA TA'ADDANCI SARAUNIYA ABIDATUL AZMAL KE.YI A
KASARTA DA SAURAN KASASHEN DUNIYA? MU HADU A 'TASKAR TSAFI' LITTAFI NA BIYU.
40
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels