Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 11
izuwa cikin Kogo. Qaddaru da galadima ma suka bi bayansu. Sai Boka SULBAINI ya juyo ya dubi galadima ya ce, koma da baya bama bukatarka. Cikin alamun kunya galadima ya koma da baya. Yayinda Boka SULBAINI da su sima suka shiga ciki, sai Kogon ya koma ya rufe kamar an rufe littafi. Kai kace tun fil-azal Dutsen Bai taba budewa ba, Kuma babu wata Halitta da ta taba shigarsa. Sa'adda suka shiga a cikin Kogon RUHIM sai Gimbiya sima da Qaddaru suka ga kamar sun shigo cikin wata sabuwar duniya. Domin hatta irin iskar da suke shaka a wajen, Mai Dan Karen dadi ce. Yanayin wajen Kuma madaidaici ne, ma'ana babu sanyi Kuma babu zafi. Komai Dake wajen daban yake da abinda Ido ya Saba gani. Ko'ina ka duba abubuwan Al'ajabi ne birjik a zuzzube. Halittu ko gasu Nan iri-iri. A wajen ne suka mace mai nono hudu, sannan suka ga Jaki Mai kawuna uku. A can gefe guda Kuma sai sukaga wani kyakkyawan saurayi Wanda rabin jikinsa na Doki ne, daga cibiyarsa zuwa Kansa yake bil'adama. Amma Gangar jikinsa da kafafuwansa duk na Doki ne. An daure shi a jikin turke sai Harbin iska yake. A can gefe guda Kuma wadansu kyawawan 'yan mata ne guda hudu, rabin tsagin jikinsu na bil'adama ne, rabi Kuma na doddani ne. Haka Kuma acan bisa wani dutse sai sukaga wani jibgegen hankaka, Mai Kan bil'adama har Yana da dogon gemu Mai sharar Kasa. Kuma Yana rera wata Waka Mai Zakin gaske, da dadin sauraro kamar haka:- *Duniya da yawa take. *Haka ma abun cikinta yake. *Komai sammakonka wani a tafe ya kwana. *Ina Gwanin wani ga nawa. *SULBAINI Kai ne gwarzo dodon gwarzaye. *Ya masanin sirrin boye. *Kai ga mai duniya ya iso. *Kai Kasan dukkanin tsatson da ke cikinta. *Kai Kasan abinda aka haifa yau, Kuma Kai ne Kasan Wanda za a haifa gobe. *Ina Mai Neman labari, yazo ga littafin da shafukansa basu kirguwa. *SULBAINI Kai ne haske Mai kewaye duniya kaf a dakika guda. *Ya masanin sirrin halittun duniya, Kai ne farin wata Mai Sanyaya koramai. *Kai ne rana Mai yada zufa. Haka dai wannan tsuntsu Mai Kan bil'adama yaci gaba da yiwa Boka SULBAINI kirari a cikin wake. Bai gushe ba Yana yi har yakai su Gimbiya sima bisa Katuwar karagarsa ta mulki yana mai yi masu nu ni da su zauna. Zamansu keda wuya kayan marmari suka bayyana a gabansu, bisa wani farantin Zinari. Sannan Kuma sai ga tulunan ababan Sha iri-iri, tare da kofuna na Zinari. Duk abinda mutum ke so, da ya Kai hannu sai abun ya taso ya dira a hannunsa. Haka dai Gimbiya sima da waziri Qaddaru suka ci suka Sha sukayi hani'an. Bayan sun natsu sai Boka SULBAINI ya dube su ya ce, ya ku wadannan manyan Baki, ku sani cewa yau kwana Ashirin kenan da fara halwata ta tsafi. Wanda bani da nufin tsayawa sai na cika kwanaki arba'in. Inda Kun hakura zuwa gareni sai bayan na kammala halwar, da Kuna zuwa zan Baku abinda ku ka fito nema. To Amma yanzu Kun tarwatsa komai, ba zan iya mallakar abinda nake so ba sai na sake shiga wata halwar ta shekara hudu a maimakon kwana arba'in. In ku ka sake zuwar min kafin cikar shekara hudun komai ya dagule, sai na sake shiga ta shekara dari hudu. Na sani cewa kunzo gareni ne ba don komai ba, sai don kusan inda zaku riski KUNDIN TSATSUBA. Domin Gimbiya ta Karanta shi ta sadu da Abokin rayuwar da ya dace da ita, ko ba haka bane? Qaddaru ya risina ya ce haka yake ya Shugaban Bokayen duniya. Hakika kunzo da babban Ala'mari Amma shi ne, Mafi sauki idan har zaku kiyaye da abinda zan shaida maku. A halin yanzu shi wannan littafi wato KUNDIN TSATSUBA Yana hannun wadansu hatsabiban Yara a birnin Sin. Ana kiransu daya JAFARU dayar kuwa YALISA. Sun kasance mace da namiji. KUNDIN TSATSUBA ba zai Karantu ba domin, babu Mai iya Bude shi sai da wata kuba da ake kira MIFTAHUZZARBIL. Ita ko wannan kuba an raba ta gida uku. Kaso guda an kaishi bangon karshen duniya dake Gabas, Daya kason an kaishi bangon kudu, dayan kuwa an kaishi bangon Arewa ne. Daga ko'ina cikin wadannan wurare tafiya ce ta shekara hamsin-hamsin ga SADAUKIN Aljani Mai tashen balaga. Amma kuyi sani cewa akwai wani Aljani Wanda zai iya yin wannan tafiyar a cikin kwanaki hamsin-hamsin. Ana kiransa MARKAHUSSABUS. Inda akayi rashin dace shi wannan Aljani a yanzu haka Yana can a tsare cikin kurkukun Sarki LU'UMANU na birnin TEHRAN dake karkashin Kasa. Kuyi sani cewa an Saka MARKAHUSSABUS a cikin wani bakin akwatin karfe, an kulle da Katon kwado Wanda bashi da makulli sai dai a sareshi da wata takobi ta musamman da ake kira SARJUS. Ita ko wannan takobi mallakar wani kasurgumin Aljani ne da ake kira MUGULUS da ke jejin KALKIM. Jejin da babu wata Halitta da ta Isa ta keta shi ta fita, batare da ta kiyaye wasu tsauraran dokoki ba masu wuyar sha'ani. Sa'adda Boka SULBAINI yazo Nan a zancensa sai Gimbiya sima da ta Qaddaru ta karaya. Suka fitar da Rai ga samun biyan bukata. Koda Boka SULBAINI ya fuskanci hakan, sai ya dube su ya kyalkyale da dariya ya ce," haba 'yayan Zamani Kar ku bani kunya mana. Ba kuji an ce Yaro 6ata hankalin dare kayi suna ba? Ai matsoraci bashi zama gwani. Inda ni matsoraci ne da bansan abinda na sani ba yau. Lallai ku karfafa zukatanku ni ko na taimaka maku ku Kai ga samun nasara. Yayinda suka ji haka sai Gimbiya sima ta ce, ya Kai Sarkin Bokaye hakika wannan kalami naka ya Kara min kwarin gwiwa. Don haka na rantse da darajar karagar gidanmu, daga yau na sallama rayuwata domin samun biyan bukatata. Fada mana abinyi mu ko mu kasance masu biyayyar su sau da kafa. Boka SULBAINI ya tuntsire da mahaukaciyar dariya a karo na biyu, ya ce haka nake so naga mace da zuciyar Maza. Na umarceku da kuyi duba izuwa ga wancan allon tsafin. SULBAINI ya nuna wani farin kyalle da sandarsa ta tsafi. Sai ga JAFARU da YALISA bisa Aljani GULZUM sun dira a kofar gidan Boka JISHEN. Dirarsu keda wuya masu tsaron kofar suka Basu hanya. YALISA ta kama hannun JAFARU suka wuce cikin gidan, suka bar Aljani GULZUM zaune Yana jiransu. Bayan 'yar doguwar tafiya ta kimanin dakika dari biyar sai gashi sun iso cikin wata Katuwar fada Mai tarin kayan alatu. Acan Saman wani gini Mai Tudu aka ajiye wata karagar mulki. Wadda aka kera da yakutu, bisa Kan karagar Boka JISHEN ne sanye da bakaken kaya, bakin rawani da bakin takalmi Wanda akayi shi da fatar damisa. A 'yantsunsa na hannun hagu da dama akwai zobbuna guda shida-shida. Bisa wata farar shimfida dake gabansa wani murgujejen Zaki ne rayayye sai gurnani yake kamar yaci babu. Koda JAFARU yaga wannan Zakin sai jikinsa ya hau 6ari, ya rukunkume YALISA saboda tsananin tsorata. YALISA ta daka Masa tsawa ta ce Amma ka bani kunya. Yanzu duk rashin tsoron nan naka da na sani ace Zaki ya baka tsoro? To ka saki jikinka ko Kuma ya turmushe ka ya cinye. Da fadin haka sai JAFARU ya natsu ya dena rawar Dari. Amma sai ya dena kallon idanun Zakin domin baya yi Masa kama da komai sai garwashin wuta. Tun sa'adda JAFARU da YALISA suka shigo wannan fada Boka JISHEN ya bisu da kallo kawai Yana Mai yin murmushi. Kai tsaye YALISA ta je ta zauna daf da shi ta ce ya Kai Abbana. Ni ce kadai 'ya a gareka a duk fadin duniyar nan. Haka Kuma nasan kana matukar Sona so ba na wasa ba. Tun tasowa ta duk abinda na bukata daga gareka kana yi min komai wahalarsa. Ka sani yau nazo gareka da wata babbar bukata wacce ban taba zuwar maka da irinta ba, Ina fatan zaka taimake ni ka biya min ita. Yayinda Boka JISHEN yaji haka sai ya kyalkyale da dariya Kuma yayita yin dariyar har sai da kwallah ta cika Masa idanu, ya fado Kasa daga Kan karagarsa. Ala'marin da yayi matukar baiwa YALISA da JAFARU mamaki kenan. Sukayi Kasake suna kallonsa kawai. Daga can sai YALISA ta sake matsawa kusa da shi ta hade Rai ta ce Ina dalilin wannan dariya taka? Boka JISHEN ya murtuke Fuska sannan ya ce ya ke 'yata kiyi sani cewa ba komai bane ya sani dariya, sai ganin yadda ku ke son kuyi aikin manya a matsayinku na Yara. Ni a tawa shawarar ku bani KUNDIN TSATSUBA kubar komai a hannuna....... Tom mu hadu a part H don Jin cigaban littafin KUNDIN TSATSUBA na Daya Wanda ni Najibullah Muhammad nake maku typing din shi. Ina fatan kunajin dadin wannan littafin, Ina yiwa kowa fatan Alkhairi tare da cewa sai mun sake saduwa✍️✍️✍️👆👆👆🙏🙏♥️♥️♥️🙏🙏🙏 **KUNDIN TSATSUBA** LITTAFI NA DAYA 1 ♥️ PART H 🤝🤝 MARUBUCI:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👮👮 TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷🥷 08112778656 ( Whatsapp ) Kar a manta da comments da likes da share ✍️✍️✋🥰 Marubucin yaci gaba da cewa.... Ni a tawa shawarar ku bani KUNDIN TSATSUBA kubar komai a hannuna. Daga nan zan aika aje a kawo min kubar miftahuzzarbil a cikin kwanaki kadan. A gaban idanunku zan bude wannan littafin na Karanta shi tare da ku. Sa'adda Boka JISHEN yazo nan a zancensa sai YALISA ta bushe da dariya ta ce," haba Abbana, nasan Kai ka haifeni Amma ka sani cewa ba fa zaka iya yimin wayau ba a yanzu. Domin kaina ya waye fiye da yadda baka zato. Mu yanzu abinda muke so da Kai shi ne, ka sanar da mu dokokin da zamu kiyaye yayinda muka shiga jejin KALKIM don dauko takobin MUGULUS. In kayi mana wannan ka gama biya mana bukata, sauran wahalar ka barmu da ita. Sa'adda Boka JISHEN yaji haka sai yayi shiru Yana tunani a zuciyarsa, yace," gaskiya abun kunya ne na kwace KUNDIN TSATSUBA daga hannun yaran nan. Tunda bansan yadda akayi suka samo shi ba. Kuma idan nayi haka kima ta zata ragu a idanun 'yata. Shikenan na yadda zan sanar daku dokokin da zaku bi, yayinda kuka shiga jejin KALKIM. Amma bisa sharadi guda, sharadin shi ne zan hada ku da wani bawana ya tafi tare daku. Ba wani bane wannan bawa sai Aljani NARGAS. Kuyi sani cewa shi NARGAS SADAUKI ne na gaske, Kuma zai zama kariya a gareku daga sharrin mugayen Aljanu. Kuma ya kasance Yana da matukar sauri fiye da naku Aljanin wato GULZUM. Haka Kuma idan GULZUM ya gaji da tafiya, to NARGAS zai iya daukarku duka har shi GULZUM din kuci gaba da tafiya. Bayan da JAFARU da YALISA suka ji wannan batu sai suka dubi juna sukayi shiru. Daga can sai JAFARU ya dubi Boka JISHEN cikin biyayya ya ce," ya shugabana munji sharadinka Kuma mun amince, Amma Muna so kayi mana uzuri zuwa gobe domin muyi shawara. Boka JISHEN yayi dariya ya ce," shikenan na amince ku tafi sai gobe war haka ku dawo min da shawarar da kuka Yanke. Nan take JAFARU da YALISA suka mike suka fita daga cikin fadar rike da KUNDIN TSATSUBA. Fitar su keda wuya Boka JISHEN ya kira sunan Aljani NARGAS sau uku, nan take ya bayyana gabansa ya risina cikin girmamawa. Ya ce," gani gareka ya Shugabana me kake bukata Dani? ALJANI NARGAS Katon gaske ne, domin ko girmansa ya ninka na Aljani GULZUM sau goma. Kakkarfan gaske ne, Kuma a halin yanzu Yana Kan ganiyar karfinsa na samartaka. Boka JISHEN ya dubi NARGAS cikin natsuwa ya ce," ban kira ka don komai ba, sai don kayi shiri Ina son zan hada ka da 'yata tare da JAFARU Dan RUZYAL, ku tafi izuwa jejin KALKIM don ku dauki takobin SARJUS mallakar MUGULUS. Ka sani cewa zakuyi wannan tafiya tare da GULZUM. Na hore ka da ka taimaka masu a duk lokacin da bukatar taimakon ta taso. Bayan Kun samu nasarar dauko takobin zaku wuce izuwa birnin TEHRAN ku shiga kurkukun Sarki LU'UMANU dake karkashin Kasa ku sare kwadon da aka kulle Aljani MARKAHUSSABUS a ciki. Lallai da wannan takobi na SARJUS zaku sare kwadon, da zarar Kun Bude akwatin zaku iske wata battar karfe a ciki, kada ku kuskura ku ce zaku Bude wannan batta. Lallai ku xo min da ita a rufe. Idan ko kukayi gangancin bude ta, to nan take Aljani MARKAHUSSABUS zai fito ya hallaka ku gaba Daya. Yayinda Aljani NARGAS yaji wannan bayani na ubangidansa, sai ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya ce,_ ya shugabana ka sani cewa bansan dokokin da za'a bi a shiga jejin KALKIM har a fita lafiya ba. Haka Kuma shiga birnin TEHRAN ba na karamin shiryayye bane. Balle ma har mu samu iKon shiga kurkukun Sarki LU'UMANU da ke karkashin Kasa. Koda Jin wannan batu sai Boka JISHEN ya bushe da dariya sannan ya ce," Kar ka damu zan sanar daku komai kamar yanzu war haka. Yanzu na sallameka kaje sai goben ka dawo a dai-dai irin wannan lokaci. ALJANI NARGAS ya risina ya ce an gama ya Shugabana, nan take ya 6ace. Shi Kuma JISHEN sai ya murza daya daga cikin zubunan hannunsa, take Shima ya 6ace. A dai-dai nan ne Boka SULBAINI ya sake nuna farin kyalle da sandan nan da ke hannunsa sai komai ya washe. Su Gimbiya sima suka dena ganin hoton komai. To yanzu kunga komai da idanunku ko? Saboda haka babu abinda ya kamace ku sai dai kubi bayan wadannan Yara. Duk inda zasuje Kuma ku je, Kuma duk abinda zasuyi suyi a gabanku. Da zarar kunga sun mallaki kubar miftahuzzarbil sai ku yake su ku kwace KUNDIN TSATSUBA da miftahuzzarbil din a lokaci guda. Sa'adda Boka SULBAINI yazo Nan a zancensa sai waziri Qaddaru yace ya Shugaban ka sani cewa daga Nan zuwa birnin Sin tafiya ce ta shekara dari da goma, batare da yada zango ba. Yanzu tayaya zamu tafi izuwa wannan gari kafin su YALISA su tafi jejin KALKIM? Kuma tayaya zamubi sawunsu sau da kafa? Koda Jin wannan tambaya sai Boka SULBAINI ya tuntsire da dariya sannan ya ce," ai wannan Mai sauki ne. Yanzu zan hadaku da wani Aljani daga cikin Aljanu na Wanda nake matukar takama da shi, sunan wannan Aljani DURFAS. kuyi sani cewa DURFAS ya ninka Aljani NARGAS sau arba'in a komai. Haka Kuma Yana da wani sihiri na musamman Wanda in yaso Yana iya 6acewa Ko Dan uwansa ALJANI Bai Isa ya iya ganinsa ba. Duk yake bisansa ma zai iya 6acewa tare da shi. Kuma idanun bil'adama ko na aljan ba zasu iya ganinsa ba. Yana da tsananin gudu yayin tafiya a cikin sararin samaniya kamar tauraruwa mai wutsiya. ALJANI MARKAHUSSABUS ne kadai ya fishi gudu. Kafin Gimbiya sima da Qaddaru su Kara fadin wani Abu tuni Boka SULBAINI ya shafi wani bakin dutse na tsafi. Sai ga wani NARKEKEN Aljani ya ratso ta cikin Dutsen Kogon ya keto cikin Kasa. Sai ga Aljanin ya durkusa bisa gwiwowinsa a gaban SULBAINI ya ce," gani ya Shugabana fadi kowace irin bukata yanzun nan na aiwatar da ita. Boka SULBAINI yayi murmushi sannan ya ce," Maza ka dauki Gimbiya sima tare da wazirinta ka kaisu birnin Sin. Don kubi bayansu Aljani NARGAS izuwa jejin KALKIM. Ina so ka kasance tare dasu har izuwa lokacin da za a mallaki kubar nan ta Miftahuzzarbil. Da zarar hakan ta faru sai ka yaki su Aljani NARGAS ku kwato KUNDIN TSATSUBA da kubar miftahuzzarbil ku taho min da su nan wurina." Koda Jin wannan Umarni sai Aljani DURFAS yasa hannu guda ya Suri Gimbiya sima da Qaddaru ya azasu a bayansa. Sannan ya yunkura da niyyar tashi, sai sima ta ce," ka dakata Sarkin hanzari akwai sakon da zan baiwa jama'ata dake waje. Koda Jin haka sai Boka SULBAINI ya ce," Kar ki damu ya Shugabata tuni munsan sakon naki. Kinaso ne kibar amanar kasarki a hannun galadima. Ki tafi abinki zamu isar da wannan Sako Kuma Muma zamu zuba Ido akan harkar mulkin don kada ayi wani Abu ba dai-dai ba yayinda baku Nan. SULBAINI na gama rufe Baki DURFAS ya Bude fuka-fukansa ya zama haske. Su ma su Gimbiya sima da ke zaune a Kansa sai suka zama hasken. Take hasken ya ratsa ta Saman Dutsen Kogon ya fice izuwa sararin samaniya ya 6ace. Ala'marin YALISA da JAFARU kuwa bayan sun bar Boka JISHEN sai GULZUM ya daukesu izuwa kogon nan dake can bayan gari, Inda Kogon YALISA yake. Da zuwansu sai suka shiga cikin Kogon tunani daga can sai JAFARU ya dubi YALISA ya ce," Anya kuwa bakya tsammanin mahaifinki ya Shirya mana tuggun da zai kwace mana KUNDIN TSATSUBA? Nikam hankalina Bai kwanta ba da Batun wannan Aljani nasa da zai hada mu da shi." YALISA tayi ajiyar zuciya ta ce," Abokina ni kaina ban yadda dashi ba, to Amma Kasan cewa bamu da wani zabi Wanda yafi mubi Umarninsa. Hakane Amma ai DABARA Bata karewa Mai nema. Karki damu tuni nayi wani shiri a zuciyata. Lallai babu Wanda ya Isa ya rabamu da kundin tsatsuba har sai mun gama karanceshi kaf daga farkonsa zuwa karshe. Koda Jin haka sai YALISA ta dubi JAFARU ta ce," Kai kuwa wane irin shiri ne kayi mana, Wanda tunanina da hikimata Basu Kai Kansa ba? JAFARU yayi dariya ya ce," karki damu kawata kiyi sani cewa ku gadon tsafi kuka fini Amma ba gadon hikima ba. Domin Kinsan cewa mahaifina cikakken masani ne Kuma mai cikakkiyar basira. Kedai kawai ki zuba Ido Kisha kallo. Shin kin manta da kirarina ne? Ni ne fa hatsabibin Yaro Mai ta'adin tsiya, mugun tsuntsu nake mai sheka hudu, ni da tsoro mun raba gari." Da Jin haka YALISA ta kyalkyale da dariya ta ce," ah gyara maganarka ai akan Batun tsoro kayi karya, Ashe ba kaine kayi arba da Zakin mahaifina ka firgice ba? JAFARU yayi murmushi ya ce ai Jin tsoro take ba tsoro bane, abinda nake nufi anan shine bana Jin tsoron abinda ban gani ba. Kin sani cewa Koda za a gaya min cewa akwai mutuwa a cikin rijiya, ba fa zanji tsoron shiga ba sai dai idan na shiga na ganta sannan. YALISA tayi murmushi ta ce kwarai Nima na shaida da wannan Jarumtaka taka. Bari Nima nayi maka nawa kirarin. Sannu JAFARU gogan YALISA. Kura kake ga tsoro ga ban tsoro. A fagen daga baka San gudu ba. Gaisheka hatsabibi na hatsabibiya. Hannu biyu maganin kazamar miya. Koda YALISA ta zo Nan a wannan kirari sai dadi ya kama JAFARU ya dube ta ya ce," dakata kawata, bar zugani haka Kar kaina ya fashe. Tunda ai ance yaba kyauta tukuici, Nima yakamata ki saurari nawa. Gaisheki karama Mai babban aiki. Kece tsafi Kuma Kinsha tsafi a nono. Kyalkyali kike Mai dadin kallo daga nesa, da zarar kin matso kusa sai ki zama wuta Mai Quna. Gaba Kadan Zaki zamo tauraruwa mai haskaka duniya, Sannu da fama 'yar matsafa. Sa'adda YALISA taji wannan kirari da JAFARU yayi Mata, sai ta bushe da dariya sannan ta ce," lallai na yadda ka gaji hikima. Sai dai ka Sanyani a duhu, me kake nufi da nice tauraruwa da zan haskaka duniya a nan gaba? Yayinda JAFARU yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar zuciya ya ce," yake qawata hakika kinyi min tambayar da bazan iya amsawa ba a yanzu, kiyi hakuri idan lokaci yayi zakiga Amsar da idanunki. Shikenan zan Jira izuwa lokacin. Yanzu me muka Yanke dangane da wannan tafiya tamu? JAFARU yayi murmushi ya ce," ai mun gama magana gobe zamu koma ga mahaifinki mu sanar da shi mun amince ya hadamu da bawansa NARGAS mu tafi izuwa jejin KALKIM. Sauran Ala'marin kibar komai gareni, tabbas zan kubutar damu daga dukkanin tarko. Nasan zaka iya Abokina. YALISA ta fada tare da mike hannayenta biyu sai ga abinci birjik sun bayyana bisa wata shimfida dake gabansu. YALISA ta dubi JAFARU ta ce ai sai kuzo muci abinci ko? Batare da Bata lokaci ba suka zauna tare suka wanke hannayensu da ruwa, nan suka hau abinci da ci. Suna cikin hakane idanun YALISA suka cika da kwallah, ta fara zubar da hawaye. Ala'marin da yayi matukar tayar da hankalin JAFARU kenan. Ya dube ta cikin alamun tausayi ya ce yake qawata Ina dalilin wannan kuka naki? YALISA ta sa hannu ta share hawayenta, tace ba wani Abu bane ya sani kuka face tunowa da mahaifiyata wacce ta rasu tun banfi shekara shida ba a duniya. A kokarinta na hada wani tsafi Mai hadari. Yakai Abokina kayi sani cewa har yau Ina iya tunowa da lokutan da nake zama tare da ita muci abinci. Hakika ta nuna min matukar soyayya. Kai duk sihirin tsafin da na samu ma daga gareta ne. Ban ta6a samun sihiri guda ba daga wurin mahaifina. Kayi sani cewa duk lokacin da na zauna zan ci abinci sai na tuno da ita. Shiyasa kaga Ina kuka. Sa'adda YALISA tazo Nan a zancenta sai ta dago Kai ta dubi JAFARU bisa mamaki sai taga Shima Yana zubar da hawaye. Abokina menene dalilin naka kukan? JAFARU yayi ajiyar zuciya sannan ya ce, " wani Abu ne ya bani mamaki, kusan komai naki irin nawa ne. Ki sani cewa sunan mahaifiyata Zuhura Kuma yau shekara guda kenan da rasuwarta. Lokacin da mahaifiyata ke Raye babu irin gatan da Bata nuna min ba, saboda tsananin son da take min yasa take ziyartar matsafa don su bincika mata irin rayuwar da zan kasance. Duk wajen Bokan da mukaje sai yace da ita, danki zai shahara a duniya Kuma zai karbi wani bakon Addini Wanda zai kawar da dukkan sauran addinai a doron Kasa. Amma ki sani cewa ba Zaki riski wannan lokacin ba, domin ajalinki ya kusa. Sai da mukaje wurin Bokaye arba'in suna fadin haka, bayanin dayansu Bai sa6a da na Dan uwansa ba. To tun daga wannan rana hankalin mahaifiyata ya dugunzuma ta shiga bincike domin ta gano irin Addinin da aka ce zan karba. Har ajalinta yazo Bata gano ba. Nima yanzu da nake maki maganar ban gano ba. Kuma lallai zan ci gaba da bincike da Kuma tambaya har sai na gano wannan Addini. 08112778656 ( Whatsapp) Najibullah Muhammad ✍️✍️ Tabbas nasan inada babban aiki a gabana, Amma sai mun samu nasarar Bude kundin tsatsuba sannan zan mayar da hankalina Kansa. Haka dai JAFARU da YALISA suka ci gaba da fira har dare ya raba sosai barci ya sace su. Da ranar tafiya jejin KALKIM tazo. Boka JISHEN yasa JAFARU da YALISA a gaba Yana karanto masu dokokin da zasu kiyaye don samun nasarar dauko takobin SARJUS. Inda ya fara da cewa... Inaso ku natsu ku saurareni dakyau, domin idan kuka mance Abu Daya daga cikin abubuwan da zan lissafa maku tamkar Kun hallaka ne. Kafin na sanar da ku dokoki bakwai na shiga jejin KALKIM zan fara maku bayani akan jejin KALKIM da Kuma MUGULUS halayyarsa da ta iyalansa. Shidai jejin KALKIM ya kasance Mai tsananin girma tsawo da fadi, domin daga farkonsa zuwa karshensa tafiya ce ta kwana arba'in bisa Aljani NARGAS. A duk shekara MUGULUS na haihuwar 'yaya dubu uku. Saboda wannan dalili ne jejin ya cika ya batse da 'yayansa ko'ina ka duba su ne babu masaka tsinke. Tarihi ya nuna cewa fiye da shekaru dubu baya babu wani mahaluki da ya Isa ya keta cikin wannan jeji. Walau ta sama ko ta Kasa, batare da ya zama abincin MUGULUS ko iyalansa ba. Kai sai da ta Kai ta kawo cewa MUGULUS da iyalansa sun cinye dabbobin dajin Dake cikin dukkanin dazuzzukan Dake kewaye da su. Hatta Kananan Tsuntsaye Basu bari ba. Yayinda sukaga babu sauran namomin daji, sai suka hau bishiyoyin dajin da ci har suka Karar da su. A halin yanzu ta Kai cewa Basu da abinci sai duwatsu da tur6aya don kada yunwa ta kashesu. Wani babban abin mamaki shi ne Basu da ikon barin kewayen da suke. Domin da zarar sun bar muhallin nasu sai iskar wurin ta zame musu guba, sai kaga jikinsa na tsattsagewa Yana rushewa kamar mutu tuni da aka gina da yum6u. Kuyi sani cewa tsafi ko karfi baya tasiri akan wadannan dodanni. Babu yadda za'ayi ku shiga jejin KALKIM batare da Kun fada hannunsu ba, Amma ku

Chapter 5 of 11