Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 11
tsatsuba a hannun JAFARU sai ya rena Kansa. Nan take ya fara tuba yana Mai rokon alfarma akan a tafi dashi izuwa jejin KALKIM da fadar Sarki LU'UMANU. Kuma ya ce ya amince sai bayan an kammala Karanta kundin tsatsuba sannan a bashi ya tafi birnin MASJUR domin ya dauki FANSA akan Sarki ZURKILU. Yayinda JAFARU yaga Boka HAFSUL HABAL ya saduda sai ya bushe da dariya ya ce," lallai idan kaga Qi guda to sa gudu ne Bai zo ba. JAFARU ya juya ya fuskanci Gimbiya sima ya ce," yake sarauniyar kyawawa sanar damu dalilin dayawa kuke biye damu sau da kafa. Batare da wata gardama ba, sima ta kwashe labarinta tun daga lokacin da ta aika aka kira waziri Qaddaru kawo izuwa lokacin da Boka SULBAINI ya hada su da Aljani DURFAS sukayi wannan tafiya. Bayan ta kare wannan bayani, sai sukayi shiru suna jinjina Ala'marin. Daga can sai JAFARU ya daga KUNDIN TSATSUBA sama yace yanzu dai na fuskanci duk rigimar duniya akan wannan littafi ake yinta. Gaba dayanmu nan akan Abu guda muke, saboda haka mu hada kanmu mu zama tsintsiya madaurinki guda. Inason yanzu mu dunguma mu tafi izuwa jejin KALKIM mu dauko takobin SARJUS sannan mu wuce birnin TEHRAN mu shiga kurkukun Sarki LU'UMANU mu sato Aljani MARKAHUSSABUS. Ku sani cewa wannan Aljani ne kadai zai iya zuwa bangwayen duniya ya dauko mana kubar miftahuzzarbil wacce da ita ce kadai zamu iya Bude kundin tsatsuba har mu samu damar Karanta shi. Shin Kun amince da wannan shawara ko kuwa akwai Mai korafi? gaba dayansu sukayi shiru aka rasa Wanda zai ce wani abu. Kawai sai JAFARU ya kama hannun YALISA suka dane bayan GULZUM shi Kuma GULZUM ya haye bayan NARGAS. Koda ganin sun yunkura zasu tashi sama, sai Boka HAFSUL HABAL yayi ihu yace kuyi min Rai ku kwance ni. Ina Mai rokonku da ku dorani bisa aljaninku ku tafi dani. Koda Jin haka sai gaba dayansu suka bushe da dariya. ALJANI NARGAS ya zuro Dan yatsansa guda ya tsittsinke igiyar tsafin da ta daddaure HAFSUL HABAL. Sannan ya sure shi da Dan yatsansa guda ya Dora shi a bayansa. Nan take NARGAS ya Bude fuka-fukansa yayi sama. Cikin hanzari Gimbiya sima da Qaddaru suka haye bayan DURFAS Shima yayi sama yabi su NARGAS a baya cikin 'yan dakiku kadan suka shige cikin gajimare. Yanzu dai tafiya ta zama ta mutum biyar da Aljanu uku wato.. JAFARU da YALISA da SIMA da QADDARU da HAFSUL HABAL. a bangaren Aljanu kuwa akwai NARGAS, DURFAS da Kuma GULZUM. Yayinda suka samu kwana Daya da yini guda suna tafiya sai Aljani NARGAS ya dubi JAFARU ya ce," ya Shugabana Ina Mai tunatar daku cewa nan da kwana uku da rabi zamu shiga jejin KALKIM. Saboda haka Ina son kafin mu shiga ka kara tuna mana dokokin nan guda bakwai, wadanda in muka sa6a su zamu halaka gaba Daya. JAFARU yace Kwarai kuwa NARGAS kazo da magana Abar dubawa. Yanzu dai abinda nake so da Kai shi ne kaci gaba da tafiya damu babu Batun yada zango balle hutawa, kowa sai yayi hakuri ya jure gajiyarsa domin yada zango a wani wuri na iya sa mu bata lokaci mai yawa. Koda Jin haka sai suka aminta. Haka dai sukaci gaba da tafiya ba dare ba rana har yaxamana saura yini daya tak a shiga jejin KALKIM. Sannan ne JAFARU ya ce, to ku saurara dakyau zan tunatar daku dokokin nan guda bakwai wadanda zamu kiyaye yayinda muka shiga jejin KALKIM. Doka ta farko shi ne," kada dayanmu ya kuskura ya ce zai yaki dodannin Nan. Doka ta biyu shi ne yayinda suka kama mu, kowa ya tsuke bakinsa kada ayi magana har su kaimu inda zasu kaimu. Doka ta uku ita ce, idan an sakamu a cikin kejin icce, duk abinda zasu kawo mana kada muci Kuma kada musha komai, har tsawon kwanaki uku Koda kuwa zamuji yunwa da kishirwa zasu kashe mu. Doka ta hudu ita ce kada wani yace zai jarraba aiki da tsafi. Doka ta biyar duk sa'adda dodannin nan suka zo suna kallonmu kowa ya sunkuyar da Kansa Kasa Kar mu rinka hada idanu da su. Doka ta shida ita ce dole ne mu rinka yin sujjada ga wata bishiyar Zinari dake kofar gidan MUGULUS uban dodanni. Doka ta bakwai ita ce," duk ranar da aka zo za'a fiddamu don a cinyemu, kada dayanmu yayi gardama ko taurin Kai. Da zarar anzo giftawa damu ta gaban bishiyar Zinarin nan gaba dayanmu mu daga kawunanmu sama mu Kalli ganyayen take ganyayen zasu zubo Kasa ba adadi iyakar ganin mutum. Haka na faruwa gaba dayan dodannin nan zasu kame su zama gumaka har uban nasu MUGULUS kuwa. A sannan ne zamu samu damar shiga gidan MUGULUS mu dauko takobin SARJUS. A lokacin da JAFARU yazo Nan a zancensa sai ya dubesu daya bayan daya yace," Ina fatan duk mun haddace abinda na fada. Lallai ku sani cewa ko mantuwa ga dayanmu na nufin halakarmu gaba daya. Wanda duk yasan ba zai iya kiyayewa ba tun yanzu yayi bayani mu sauka Kasa mu ajiye shi kafin mu Isa jejin KALKIM. Gaba dayansu sukayi tsit ba a samu Wanda ya nuna gazawa ba. YALISA tayi murmushi ta ce," ah toh! Rai dai guda Daya ne duk Wanda yayi ganganci ya rasa nasa shikenan. Ni dama ban damu ba, don ance mutuwar yawa kaka ce. JAFARU ya bushe da dariya sannan ya ce, ai kema bakisan dacin mutuwa ba. Inda Kinsan dacin mutuwa da Zaki fadi haka ba. Sannu wanda ya san mutuwa ai sai ka fada mana lokacin da ka dandana ta. JAFARU yayi murmushi ya ce," Ashe har kin mance lokacin da HAFSUL HABAL yayi min 6arin makauniya? Ai a wannan lokaci idanuwa na ne suka dena gani ba rinka ganin wadansu taurari na yawo a sama daga sannan ne Kuma ji da ganina suka dauke gaba Daya. Tabbas wannan Hali da na shiga dai-dai yake da dandanon mutuwa. YALISA ta bushe da dariya ta ce dakyau tsoho Mai ran karfe. Kai ne maganin Mai karambani, gaba dayansu dariya ta kwace masu. Sukayi ta kyakyatawa musamman Aljani NARGAS da Aljani DURFAS Kai kace ba zasu dena dariyar ba iya tsawon rayuwarsu. Oh! Aljanu da keta ku ke, wannan muguwar dariya fa kamar an baku tallan auduga? Ba shiri kowa ya tsuke bakinsa sakamkon abinda suka hango a gabansu. Ba komai bane sai jejin KALKIM. Daga sama suna iya hango jejin ko'ina dodanni ne birjik ba adadi. Dodannin sun kasance manya-manya Kuma masu mummunar siffa. Duk irin taurin kan mutum idan ya hada Ido dasu sai ya razana. Yayinda Aljani NARGAS da Aljani DURFAS suka Kara kusantar wannan jeji sai sukaji basa iya motsa fuka-fukansu sosai. Karfin gudunsu yaci gaba da raguwa akai-akai. Nanfa cikin kowa ya duri ruwa. Ba zato ba tsammani sai sukaji sunyi Kasa luu kamar an janyosu da kugiya. Caraf suka fada hannun dodannin nan su duka. Dodanni suka hau wani irin gurnani Wanda idan Mai ciki zata ji shi take zatayi 6ari. Kuma sai suka rinka dalalar da yawu saboda tsabar kwadayi. Nanfa sai aka fara yiwa su JAFARU daukar makara wadannan su Mikawa wadancan, wadancan su Mikawa wadannan. Akayi ta tafiya dasu gaba-gaba su dai su JAFARU sukayu lakwas babu Wanda yace kala. Bayan anyi doguwar tafiya dasu a haka, sai aka Isa kofar gidan MUGULUS uban dodanni. Da zuwa aka iske shi tsaye kikam Yana jiran isowarsu. Dama tuni labari ya isar Masa cewa yau an kamo wadansu bil'adama. Yayinda aka gurfanar da su JAFARU gaban MUGULUS sukayi arba da shi, sai kowannensu cikinsu ya duri ruwa. Saboda firgicewar da sukayi sakamakon ganin siffar halittarsa. MUGULUS dogo ne, saboda tsananin tsayinsa idan Mutum ya daga Kai sai ya rinka hango fuskarsa tamkar tsuntsu a kololuwar sama. Fadin kirjinsa ko kamu tamanin da uku ne. Kaurin duga-duginsa sunyi kama da murtukekiyar bishiyar kuka. Idan ya daga kafarsa guda zai iya talitse 'yayansa dari a lokaci daya, duk da cewa su ma ba kanana bane girman kowane daya ya ninka na Gimbiya sima sau biyar. MUGULUS yayi nuni da a Sanya su a cikin wani kejin icce. Nan da nan 'yayan nasa suka cika Umarni aka jefasu ciki aka kulle, tamkar an jefa Kaji a akurki daga nan kowa ya watse suka kama gabansu. ALJANI DURFAS ya hada Kai da gwiwa cikin takaici, sannan ya dago Kai ya Kalli NARGAS ya ce," Kai duk Wanda bayyi yawo a duniya ba Bai Sha kallo ba. Yanzu ka dubi duk irin girman nan nawa da karfin nan nawa da Kuma karfin tsafina, wai yau ni ne a cikin kejin icce a kulle. Kuma a hannun wasu halittu daban ba Aljanu ba, hatsabibancinsu ya fi namu. NARGAS ya ce," uhm ai Ni ba wannan bane yafi bani mamaki sai uban dodannin nan. Ka dubi tsananin girmansa sai kace tsauni. Ai ni sa'adda na hango kofofin hancinsa daga nesa, na dauka Kogon duwatsu ne manya-manya. Shi ko GULZUM ya ce," ni ko da na hango idanuwansa nayi zaton rana da wata ne zasuyi karo a sararin samaniya. Koda Jin wannan batu sai su JAFARU suka bushe da dariya, JAFARU ya ce" lallai Kai ka ma fi kowa rudewa. Ina ka taba ganin rana da wata sun hadu? Ai Abu ne Wanda ba zai taba yiwuwa ba, in ko sun hadu dole ne daya ya narkar da daya. 08112778656 ( Whatsapp ) Najibullah Muhammad ✍️✍️ Gimbiya sima ta ce lallai ku hankalinku a kwance yake. Ashe yanzu har Kun mance halin da muke ciki, Kun bude shafin fira? Ku tuna fa rayuwarmu na cikin kila wa kala ne, zai fi kyau mu tsuke bakinmu ko mun samu natsuwa mu kiyaye dokokin dajin nan, Kun San dai yin shiru na daga ciki. JAFARU ya ce Gaskiyane Amma ai tunda dodannin nan basa kusa zamu iya yin surutanmu. Firar ma ai rahma ce a garemu domin zata rage mana fargaba da zullumi. Don wannan ya tuna min da labarin wasu 'yayan Sarki su uku da suka bazama Neman kayan yakin mahaifinsu Wanda ya 6ace a duniya aka neme shi aka rasa. Koda Jin haka sai YALISA ta ce Kai JAFARU, wannan Kuma wane irin labari ne? Bamu kanu musha.. JAFARU yayi gyaran murya gami da saisaita makogwaronsa ya ce," Asalin wannan labari na samo shi ne a cikin wani littafin tarihi da ake kira KARON BATTA. A wani Zamani can baya anyi wani shahararren Sarki da ake kira JAMNASH Wanda a zamaninsa yaci kasashe da dama yaki, har ya bar duniya ba a ta6a cin kasarsa da yaki ba. Kuma sai da ya shekara casa'in yana mulki a Kasar LAHAMUS. Dare daya aka wayi gari bashi ba alamunsa. Sarki JAMNASH Yana da 'yaya Maza guda uku SAHAL, FAZMAL DA HUZMAL. Dukkaninsu jarumai ne na hakika, domin su ke jagoranci a duk sa'adda za'a fita yaki. Kowannensu mahaifiyarsa daban Kuma ko kadan basa jituwa a tsakaninsu sakamakon bakin kishin da ke addabar iyayensu mata. Domin kowace tafi so ace danta ne ya gaji karagar mulki. Bayan shekaru hudu da 6acewar Sarki JAMNASH sai gidan sarautar ya rikice da rigingimu akan Wanda ya dace ya hau karagar mulki. Bisa wannan dalili ne majalisa ta zauna aka kira SAHAL FAZMAL DA HUZMAL. Waziri MARKAS ya dube su yace kuyi sani cewa a halin yanxu dole ne biyu daga cikinsu su hakura aba gudanku sauratar garin nan. To Amma gashi gaba dayanku Kunqi amincewa da haka. A bisa wannan dalili ne muka zauna mukayi tunani sannan muka Yanke shawara akan abinda ya kamata ayi don a raba wannan gardama. Boka RAKABU yayi bincike ya gano cewa mahaifinku ya mutu, amma takobinsa na yaki tare da garkuwarsa da damararsa suna Nan a cikin duniyar Nan. Kuma babu Wanda yasan inda suke. Kun sani cewa mahaifin nan naku cikakken matsafi ne Kuma jarumi ne. Lallai abinda yasa ya rabu da kayan yakinsa ba karamin bala'i bane, Kuma wannan Abu ne ya zama sanadiyyar ajalinsa. Saboda haka duk Wanda yake so ya zama ya gaje shi a cikinku dole ne yayi shiri ya shiga duniya neman wadannan abubuwan guda uku. Kun sani mun sani Abubuwan nan uku daban suke, babu Mai irinsu a cikin fadin duniya. Wanda duk ya dawo da wadannan kayan yaki daga cikinku to shine ya kamata ya hau karagar mulki. Yaya Kun amince da wannan sharadi? Cikin hadin Baki SAHAL FAZMAL DA HUZMAL suka ce sun amince. Kashe gari kuwa su duka ukun suka dau guzuri kowa ya hau dokinsa suka nausa cikin jejin. Yayinda suka zo wajen wata mararrabar hanya guda uku sai suka tsaya sukayi cirko-cirko. SAHAL yace anan zamu rabu kowa yabi hanyar da tayi Masa ko mun samo abinda muka tafi bida, ko bamu samo ba mu hadu anan cikin kwanaki sittin. Yana gama fadin hakan ya kada linzamin dokinsa ya nufi hanyar da tayi Gabas, FAZMAL kuwa sai yabi hanyar da ta nufi yamma, HUZMAL kuwa sai yabi wadda tayi kudu. Yana tafe Yana tunani da bakin cikin wannan Hali da suka tsinci kansu na tsananin rashin jituwa da qin juna saboda kawai kwadayin mulki. Sa'adda JAFARU yazo nan a zancensa sai waziri Qaddaru ya tari numfashinsa ya ce," kaga dakata haka yanzu menene amfanin wannan labarin, Ina hikima a cikinsa? JAFARU yayi tsaki ya ce," ai Kaji irinta halin Dan Adam kenan rashin hakuri. Inda ka bini a Sannu ai zakaga inda ma'anar labarin take, Amma tunda ka katseni ba zan ci gaba ba sai wani lokacin idan an samu dama irin wannan. JAFARU yayi shiru Bai sake cewa komai ba, dama a wannan lokaci dare ya soma saboda haka duk sai suka saduda kowa ya kama barci. Kashe gari kuwa da safe aka kawowa su JAFARU wani irin ruwa mai wari a cikin wani Katon kasko gami da wasu kananan duwatsu a matsayin abinci. Yadda aka ajiye ruwan da duwatsun haka aka dawo aka daukesu, domin babu Wanda ya dubi inda suke balle yaci. Sa'adda rana ta fito sai dodannin nan suka rinka fitowa sahu-sahu suna kallon wadannan fursunoni na cikin kejin icce. Suko fursunonin sai suka rinka sunkuyar da kawunansu Kasa suka Qi yarda su rinka hada Ido da dodannin. Da rana tayi tsaka sai aka sake kawowa fursunonin wani nau'in abincin aka ajiye masu Shima sukaqi ci. Sa'adda magriba tayi aka kawo wani abincin iri daban Shima sukaqi ci. Haka dai akaci gaba da wannan Ala'marin har tsawon kwanaki uku. Fursunonin nan suka galabaita da matukar yunwa da kishirwa kamar ba zasu rayu ba. Kullum da safe sai su JAFARU sunyi duba izuwa bishiyar Zinarin nan sunyi mata sujjada. A yammacin rana ta uku ne aka fito da wadannan fursunonin daga cikin kejin icce, aka tasa keyarsu gaba. Koda aka zo giftawa da su ta gaban wannan bishiyar Zinarin sai gaba dayansu suka daga kawunansu sama suka dubi bishiyar. Yin hakan keda sai gaba dayan sukayi ta zubowa Kasa fululu suka cika ko'ina. Faruwar hakan keda wuya sai gaba dayan dodannin nan suka kame suka zama gumaka. Koda ganin hakan sai murna ta kama su JAFARU. Kai tsaye suka wuce cikin gidan MUGULUS uban dodanni. Sukayi ta ratsawa ta cikin dodanni har suka shiga cikin kuryar dakin. Da shiga suka ga kokunan kawunan bil'adama birjik a zube, sannan Kuma suka hango takobin SARJUS rataye a jikin bango, JAFARU ya sunkuya ya dauki kokon Kai guda ya jefi takobin SARJUS da shi. Take takobin ya fado Kasa shi ko ya ruga ya dauka. Yana dauka ya kama hanyar fitowa kowa yabi bayansa, duk Inda JAFARU ya dauke sawunsa nan su Aljani DURFAS da su Gimbiya sima ke sa nasu. Har dai sukayi tafiya ta kimanin sa'a guda. JAFARU ya tsaya ya dubi Aljani DURFAS da Aljani NARGAS ya ce," Maza ku dauke mu ku bar jejin nan da mu. Cikin hanzari Aljanun biyu suka sunkuya Kasa.... Tom mu hadu a KUNDIN TSATSUBA na daya part L don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi da debe kewa 🥰♥️ Anan ni Najibullah Muhammad nake cewa ku huta lafiya 🙏🥰**KUNDIN TSATSUBA** LITTAFI NA DAYA 1 ♥️ PART L ✍️🔜 MARUBUCI:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👮👮 TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING:- Najibullah Muhammad 🥷🥷 Note:- Yin comments da likes da share ya zama wajibi ga wanda ke son cigaban wannan labari✍️👇👇 08112778656 ( Whatsapp ) MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA... Cikin hanzari Aljanun biyu suka rankwafa Kasa, GULZUM, JAFARU da YALISA suka haye bayan NARGAS. Gimbiya sima, Qaddaru da Boka HAFSUL HABAL suka haye bayan DURFAS. A lokaci guda Aljanun suka Bude fuka-fukansu suka yunkura bisa mamaki sai sukaji sunyi sama, karfin jikinsu ya dawo har ma sukaji yafi na daa. Koda ganin cewa sun kubuta sai HAFSUL HABAL ya leko Kasa ya kutunmawa dodannin zagi harda jeho masu wani Dutse. Koda Dutsen nan ya dira Kan dodo Daya sai ruhinsa ya dawo jikinsa. Cikin zafin nama dodon nan ya dago kansa sama da hannunsa guda, kawai sai hannun nan nasa yayita yin sama yana kara tsawo, sululu cikin abinda bai wuce dakika uku ba hannun nan ya damko HAFSUL HABAL ya jefa shi a bakin dodon nan yayi Loma guda dashi ya taune. A wannan lokaci tuni Aljani NARGAS da Aljani DURFAS sunyi Nisa da barin jejin KALKIM. YALISA ta dubi JAFARU ta ce lallai sau tari mutum shi ke jefa Kansa cikin halaka. Ka dubi shirme irinna Boka HAFSUL HABAL, gaba dayanmu mun gama kubuta. Amma saboda wauta irin tasa sai da ya tsokano dodannin nan. Gashi yanxu sun cinyeshi. Shikenan yanzu ya mutu a banza batare da ya cika burin rayuwarsa ba, tunda bai dauki FANSA ba akan Sarki ZURKILU. JAFARU yace Kwarai kuwa ai dama ance da hakuri da rashinsa tazararsu 'yar kadan ce. Yanzu dai sai muyi barka tunda mun samu nasarar dauko takobin SARJUS. Yanzu sai mu tafi birnin TEHRAN don sato Aljani MARKAHUSSABUS a cikin kurkukun karkashin Kasa. Shin ko a cikinmu nan akwai Wanda yasan sirrin fadar Sarki LU'UMANU, don mu San matakan da zamubi mu samu nasara? Sa'adda JAFARU yazo nan a zancensa sai kowa yayi shiru aka rasa Wanda zai ce wani abu. Daga can sai Aljani DURFAS ya ce idan babu Wanda ya sani a cikinku ni zanyi bayani. Amma kuyi hakuri sai mun samu wuri Mai kyau mun yada zango kowa ya samu abinci yaci mun kore yunwa da kishirwa da Kuma wannan wahalar da muka Sha ta kwana uku. Da Jin haka sai Gimbiya sima tace kazo da magana Mai kyau, domin bayani baya shiga sai da natsuwa. Daga Nan kowa yayi shiru ba a Kara cewa uffan ba. Suna cikin tafiya sai suka iso wani daji Mai yawan itatuwa da koramai. Cikin hanzari suka sauka wannan jeji. Da saukarsu Aljani GULZUM ya sauka yaje ya samo masu abinci daga 'yayan itatuwa. Bayan kowa ya samu natsuwa sai Aljani DURFAS yayi gyaran murya yace" to sai kowa ya bani Aron kunnensa Kuma ku bani dukkanin natsuwarku domin kuji labarin masifun da ke cikin fadar Sarki LU'UMANU. Da Kuma hanyoyin da zamubi don mu kubuta daga sharrinsa. Nima ban taba zuwa wannan wuri ba. Amma na samu labari ne daga bakin Shugabana Boka SULBAINI. Da farko zan fara yi maku bayani akan Shirin Sarki LU'UMANU da Kuma karfin tsafinsa, da Kuma yadda akayi ya gagara anan duniya. SARKI LU'UMANU Mutum ne Wanda tun yana Yaro karami dan shekara shida yake Bauta da hidima a wajen wani shahararren Boka da zamaninsa ya shude ana kiransa ABUL-FASU. Sarki LU'UMANU yasha bakar wahala a wajen boka ABUL-FASU. Domin duk sa'adda aka bashi wani aiki yayi kuskure sai an gana Masa Azaba kala dari. Tun LU'UMANU na Jin tsoron azabar da ake masa, har ma ya zamana yayi sabo da ita. Boka ABUL-FASU na da 'yaya hudu, Amma gaba dayansu babu Wanda ya samu sirrikan tsafi a hannunsa. Shima LU'UMANU da yake yi Masa biyayya da Bauta mara misaltuwa bai samo komai a wajensa ba. Amma har kullum bai taba nuna gajiyawarsa ba ga cigaba da yin bauta, duk da cewa yana matukar abzabtar dashi. Yana nan a cikin wannan hali, sai aka wayi gari Boka ABUL-FASU ya kwanta ciwon ajali, yayinda 'yayansa suka tabbatar da cewa wannan ciwon ba na tashi bane Kuma suka fahimci cewa Basu karu da komai ba na daga sirrikan tsafi sai suka sace dukiyarsa gaba daya suka rabeta a tsakaninsu kowa ya kama gabansu. Yayinda ABUL-FASU ya fahimci abinda ya faru, sai ya kadaita da LU'UMANU cikin dakinsa inda ya dubeshi yace" ya Kai LU'UMANU kayi sani cewa kayi Bauta a gareni shekara da shekaru. Kuma na azabtar da kai azabar da ban taba yiwa wanina ba. Amma hakan batasa ka gujeni ba. A matsayinka na almajirina Mai Neman sirrinkan tsafi har yanzu baka karu Dani da sihiri daya ba. Lallai kayi hakuri Mai yawa yau gashi 'yayana na cikina sun gujeni. Kuma sun sace dukiyata gaba daya sun gudu, amma har yanxu kana nan manne dani. To ka sani wannan hakuri da kayi shi zai sa na taimakeka ka cimma wani babban matsayi. Wanda sai ka shahara ko'ina cikin duniya. Zaka mallaki dukiya mai dimbin yawa, Kuma zaka mallaki macen da babu Mai kyawunta a duniya. Zaka zama Sarki Mai mulkin Katuwar Kasa, haka Kuma zan hadaka da wasu Aljanu wadanda sun kasance manyan sadaukan da babu kamarsu daga cikin Zuriyyar Aljanu. Wadannan Aljanu guda dubu hudu ne da arba'in da hudu. Muddin kana tare da su babu Wanda ya isa ya cika da yaki. Sa'adda ABUL-FASU yazo nan a zancensa sai tari ya turnuke shi, dakyar ya samu tarin nan ya lafa. Sannan ya LU'UMANU ya ce ya Kai LU'UMANU Mike tsaye ka bude waccan randar, ba ruwansha ne a ciki ba. Zaka iske wani kambun tsafi a ciki. Na umarceka da ka dauki wannan kambu ka daura shi a damtsenka na hagu. Koda Jin haka sai LU'UMANU ya Mike zumbur yaje ya bude wannan randa. Ai kuwa sai yayi arba da kambun. Cikin sauri ya dauki kambun yasa a damtsensa na hagu kamar yadda ABUL-FASU ya umarceshi. Sanya kambun keda wuya LU'UMANU yaji wani irin karfi na shigarsa mara misaltuwa. Sannan Kuma da ya dubi waje ta tagar dakin sai yaga Yana iya hango abinda ke can waje kamar tafiyar sa'a arba'in. Haka Kuma in yayi tafiyar taku daya sai yaga ya Kai wajen da sai yayi taku goma a da. ABUL-FASU ya dube shi ya ce, ya Kaji yanzu a jikinka? LU'UMANU ya ce Ina ji yanxu kamar zan iya tashin duniyar nan gaba dayanta. Kuma Ina Jin kamar komai nisan tafiya zan iya ta batare da na gaji ba. Kuma Ina Jin kamar zan iya fin tauraruwa karfin gudu. Sa'adda Boka ABUL-FASU yaji haka sai yayi murmushin karfin hali gami da hadiyar yawu yace, jeka abinda LU'UMANU duk garin da ya baka sha'awa ka kashe sarkinsu ka hau karagarsa, duk macen da ka gani kana so ka kwaceta ko matar waye. Lallai kana tare da bayinmu guda dubu hudu da arba'in da hudu wadanda zasu kare ka daga dukkan hadari. Gargadina a gareka shi ne, duk wuya duk rintsi Kar ka kuskura ka cire wannan kambun tsafi dake hannunka. Nan take ABUL-FASU yayi bankwana da LU'UMANU ya sunkuya ya sumbaci goshinsa yana Mai zubda hawaye saboda sabo. Nan take Shima LU'UMANU ya zubda hawaye, ya kama hannunsa ya kankame a kirjinsa yana sumbata a haka rai yayi halinsa. Sa'adda LU'UMANU ya fuskanci cewa ABUL-FASU ya mutu, sai ya janye hannunsa daga jikinsa ya koma gefe guda yana kuka. Ba zato Kuma sai yaga Gawar ABUL-FASU ta murmushe ta zama Kasa, wata irin iska ta shigo cikin dakin ta kwashe Kasar gaba daya tayi sama da ita, suka bace da ita a sararin samaniya. Manyan Bokaye mutuwarsu ma abun Al'ajabi ce, LU'UMANU yayi wannan furuci. Yana gama fadin hakan sai ya juya ya fice daga cikin gidan gaba daya. Fitarsa keda sai gidan gaba daya ya nutse a karkashin Kasa kamar an jefa Dutse a karkashin teku. LU'UMANU ya waigo ya Kalli filin wajen, yaga babu komai tamkar wani Abu Bai taba wanzuwa ba a wajen. Kawai sai ya jinjina Kai yaci gaba da tafiyarsa. Bayan 'yar gajeriyar tafiya sai kawai LU'UMANU yaga Gungun wadansu manyan bakaken Aljanu sun bayyana a gabansa. Cikin

Chapter 8 of 11