Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 11
zata iya tantance ainihin siffarsa ba. Koda ta kare kallon sai ta cika da mamaki, ta dubi JAFARU ta ce lallai Kam yau kazo min da babban Ala'mari abun Al'ajabi. Tunda haka ne sai ki cire min takunkumin Azaba daga yau. JAFARU ya fada a cikin murna da murmushi. YALISA ta mayar Masa da martanin murmushin ta ce na amince, Kuma ka sani lallai a daren yau zamu dauko KUNDIN TSATSUBA. Sai dai bansan yadda zamuyi ba dangane da Batun dauko kubar miftahuzzarbil. Ina ganin dole sai mun Furta wannan Ala'mari ga mahaifina. Amma Ina tsoron yin hakan, don kada yayi mana fin karfi ya rabamu da 'kundin tsatsuba ' yayinda JAFARU yaji haka sai yace Kinga masu iya magana sun ce samu yafi iyawa. Mu fara mallakar wannan littafi, inyaso daga baya sai muyi binciken yadda zamu iya budeshi. YALISA ta ce kwarai kazo da shawara Mai kyau, yakai Abokina. To kayi sani cewa daga yau Ka zamo Abokin shawara ba na fada ba. Nan take ta Mika Masa hannu tana Mai murmushi Shima ya Mika mata nasa, sukayi musabaha a karo na farko tun haduwarsu da juna. Lallai ba zan taba mata mantawa da yau ba, ranar da ni da ke mukayi musabaha. YALISA tayi dariya ta ce, ni kaina wannan ranar ta shiga cikin KUNDIN tarihin rayuwata. Ba zan mance da ita ba. Kafin JAFARU ya Kara fadin wani Abu, sai ta ja shi izuwa cikin wannan babban gida. Su kuwa masu tsaron kofar sai suka Bude masu cikin biyayya. JAFARU da YALISA suka kutsa Kai ciki suna annashuwa, Kai kace sun Dade suna zumunci da abokantaka tsawon shekaru. Wannan shi ne abinda ya faru da hatsabibin Yaro da hatsabibiyar yarinya wato JAFARU Bin RUZYAL ma'abocin hikima da YALISA 'yar BOKA JISHEN shugaban Bokayen birnin Sin. A can wani 6angare na kudancin duniya kuwa, akwai wata Kasa da ake kira LAHARIM. Laharim babban birni ne Wanda ya tara manyan attajirai da sarakai da bokaye. Sarkin wannan Kasa ya rasu yabar 'ya guda daya wata kyakkyawar budurwa 'yar shekaru goma Sha takwas, wadda masana suka tabbatar da cewa a duniya a wannan Zamani babu wata kyakkyawa kamarta. Ana kiranta da suna SIMA. Sima ta hau karagar mulki tun tana da shekaru bakwai a duniya, tun daga wannan lokaci kawo i'yanzu ita ke mulkin Kasar LAHARIM. Tana da waziri wani guntun wada Wanda tsawonsa Bai wuce kamu biyu ba, ana kiransa Qaddaru. Duk abinda Gimbiya sima zatayi sai tayi shawara da Qaddaru, Kuma duk Inda zata tana tare da shi. Ta amince dashi matuka domin ta gaje shi ne a wajen kakanta. Ma'ana Qaddaru ne wazirin mahaifin ubanta tun Asali. A halin yanxu shekarun Qaddaru sun Kai Dari da Ashirin da biyu. Amma idan ka dubi fuskarsa sai kayi zaton Yaro ne Dan shekaru goma Sha. Ba don siffar ga6o6in jikinsa ba sai ka ce Yaro ne. Yana da baiwa ta rashin gashi da yanayin tsufa. Kuma har yanzu ya kasance kakkarfa ga koshin lafiya. A tarihin rayuwarsa Bai taba yin rashin lafiya ba, Koda kuwa ciwon Kai ne. Watarana da sassafe Gimbiya sima ta aika aka kira Qaddaru, da yake ba ayi Masa iso gareta, sai ya wuce izuwa cikin kuryar turakarta inda ya isketa a cikin bahon wanka Mai cike da kumfar sabulu kunyagi na cudata. Koda ganinta cikin wannan Hali sai ya sunkuyar da Kansa kas, cikin sauri yace kaicona da cin amanar gidan nan, lallai ba zan iya kallon tsiraicinki ba, ranki ya dade ki gafarceni. Koda Jin haka sai Gimbiya sima tayi murmushi sannan ta ce, ya Kai Qaddaru kayi sani cewa ban kira ka Nan ba, sai don idanunka su ga kyakkyawar surar jikina a bisa wani dalili guda Daya. Don haka Ina Mai umartar ka da ka dago kanka ka kalleni sama da kasa. Bayan haka zanyi maka wata tambaya, wadda yanzu take zaka bani amsarta. Na rantse da kabarin mahaifina idan kaqi bin umarnina zan kashe kaina, Kuma na Dora alhakin Raina a kanka. Kayi sani cewa tuni na gama Shirya komai tare da wadannan kuyangi. Sima na gama fadin hakan sai Qaddaru yaga wadansu kuyangi guda goma Sha daya sun firfito daga inda suka boye, sun kukkule kofofin fita daga wannan turaka guda goma Sha daya. Cikin tsananin razana Qaddaru ya dago Kai ya Kalli Gimbiya sima jikinsa na karkarwa. A wannan lokaci ta Mike tsaye daga cikin bahon wanka kumfar sabulu na mammane a jikinta. Take wata kuyanga tasa wani farin kyalle ta goge kumfar dake jikinta. Nanfa surar jikin sima ta bayyana karara a Fili. Ta kasance tum6ur babu wani hijabi, gashin kanta baki-kirin Mai kyalkyali ya zuba har Kasan mararta. Cikinta a shafe yake kamar bata ta6a cin komai ba. Kugunta kuwa a tsuke yake, daga baya ya fashe yayi doro kamar a dora kofin lemo akai ya zauna. Fatar jikinta jaa ce sumul-sumul ko digon kwarzane babu a ko'ina. Tana da siririn wuya kamar na barewa. Sima doguwa ce mai madai-dacin kaurin jiki. Tana da manya-manyan cinyoyi da zara-zaran 'yan yatsun hannu da Kafa. Batun Ido Hanci da baki kuwa kamar kwararren Mai Zane ne ya zana su bisa takarda dai-dai yadda ake bukata. Idan tayi murmushi mutum na iya ji kamar an zare masa Cutar ajali wadda aka shafa Masa shekara da shekaru. Yayinda waziri Qaddaru yayi arba da wannan kyakkyawar sura, sai yaja dogon gwauron numfashi sannan ya ce,' ranki ya dade na rantse da girman abun bautarmu ban taba ganin wani Abu Mai kyau ba a doron Kasa tamkarki. Inda nasan haka kike, da tuni na mutu wajen Neman kyakkyawan mijin da ya dace da ke. Domin sai na nemo maki namijin da babu mai kyawunsa a duniya. Koda Jin wannan lafazi sai sima ta kyalkyale da dariya ta c," ka fara hawa Kan turbar da nake so. Ya Kai Qaddaru kayi sani cewa a rayuwata ta duniya babu abinda nake so face tafiye-tafiye don ganin abubuwan Al'ajabi da ke cikin duniya. Ka sani cewa Ina da kyau mulki da dukiya ba abinda na nema na rasa face Abokin rayuwa Wanda ya dace Dani. Ni sima na rantse da darajar tsafin da na gada a wurin iyaye da kakanni ba zan Auri wani da namiji ba, face Wanda ya fini kyau mulki da dukiya. Nayi bincike akan madubin tsafina na gano cewa akwai wani littafi da ake kira KUNDIN TSATSUBA, wannan littafi ya kunshi manyan sirrikan Al'ajabi guda dubu. Lallai idan na mallakeshi na samu Damar Karanta shi, zanyi daukakar da babu wani mahaluki da ya taba yi Walau yanxu ko daa ko nan gaba. Nayi iya kokarin akan na gano inda wannan littafi yake Amma na Kasa. Yakai Qaddaru kayi sani cewa bincikena ya nuna min cewa ba zan taba haduwa da namijin da ya dace Dani ba, har sai na Karanta wani shafi daga cikin shafukan KUNDIN TSATSUBA. Yanzu Ina Neman shawara a gareka. 08112778656 ( Whatsapp) Lokacin da Gimbiya sima ta zo Nan a zancenta sai hankalin Qaddaru ya dugunzuma ya Kasa cewa komai, yayi shiru Yana tunani. Wata kuyanga tazo da wani babban shudin mayafi ta lullubawa sima. Sima ta matsa kusa da Qaddaru ta Kai hannu don dafa kafadarsa, sai yayi sauri ya matsa baya. Cikin firgici ta dube shi ta ce lafiya me ya faru gareka? Qaddaru ya numfasa ya ce," ranki ya dade ai Ina kishi ne ace wannan hannu naki ya ta6a jikin wani daa namijin da bai dace da ke ba. Na rantse da darajar gidan nan a iya sanina tun daga ranar da mahaifiyarki ta haifeki kawo i'yanzu namiji bai ta6a-ta6a jikinki ba har shi Kansa mahaifin naki kuwa. Shi ne da Kansa ya Kafa Dokar duk namijin da ya ta6a jikinki a sare Kansa, ba don komai yasa wannan doka ba sai don tsananin kyawunki har yau wannan doka na aiki, Kuma muna kiyayewa da ita. Sima tayi murmushi ta ce, to naji batunka Nima saurari nawa. Qaddaru ya zauna nesa kadan da ita ya sunkuyar da Kansa Yana Mai sauraro cikin biyayya. Abinda nake so da Kai shi ne, ka Kaini wajen Bokan da yafi kowane Boka Isa a Kasar nan. Domin ya bincika min inda KUNDIN TSATSUBA ya ke. Kuma ya taimaka min na Isa wajen har na mallakeshi. Yayinda Qaddaru yaji haka sai ya sake yin shiru tsawon 'yan dakiku sannan ya dago Kai ya dubi sima ya ce," ranki ya dade ai kaf Kasar nan babu Wanda zai iya wannan aiki fa ce BOKA SULBAINI IBN BARZUK. Kiyi sani cewa a halin yanxu yana can jejin FALWAS ya shiga Kogon RUHIM don shiga doguwar halwar tsafi ta kwana arba'in da daya, saboda wata muhimmiyar bukata tashi. Ina Jin tsoron mu je mu katse Masa aiki fushinsa ya tabbata a gareni. Yayinda Gimbiya sima taji haka sai ta daka Masa tsawa ta ce," Kai waziri Qaddaru ai sawun giwa ya take na rakumi, bukatarsa ce a Saman tamu ko kuwa bukatar mu ce a saman tasa? Ashe ba ni ke mulkin Kasar LAHARIM ba? Duk mahalukin da yake zaune a wannan kasa Yana zaune a karkashin iKona ne. Lallai Boka SULBAINI bawanmu ne, Ubansa ma yayi Bauta a gidan nan, dole ne ya bi Umarnin mu. Haka yake ranki ya dade, zancenki Dutse ki gafarceni. Da jin haka sai Gimbiya sima tayi murmushi ta ce, na umarceka dakayi Maza ka koma gida don kayin sallama da iyalanka, ka dawo nan bayan magriba yau din nan zamu tafi dajin FALWAS don mu sadu da Boka SULBAINI. Cikin biyayya kaddaru yayi sujjada ga sima sannan yayi Mata sallama. Nan da nan ya fice daga wannan turaka zuciyarsa cike da damuwa domin Bai San abinda kan iya faruwa ba da rayuwarsa. Tabbas yasan cewa Gimbiya ta tsokano abinda bazai taba yiwuwa ba. Domin ya ta6a Jin labarin KUNDIN TSATSUBA a wajen Boka SULBAINI Kuma ya gaya Masa cewa babu Wanda yasan inda yake, balle a San Wanda ke da mallakinsa. A can birnin SIN kuwa cikin sulusainin dare RUZYAL na kwance cikin dakinsa Yana barci kawai sai ya Farka a firgice sakamakon wata irin Kara da yaji Mai kama da saukar aradu. Nan take ya ruga zumbur izuwa tagar dakin ya Bude cikin tsananin tsoro, tartsatsin hasken tsawa ne ya daki fuskarsa yaja da baya a tsorace. Cikin karfin hali ya sake lekawa wannan karon bai ga tsawar ba sai acan nesa kadan yake hangota. RUZYAL ya dubi sararin samaniya dakyau yaga babu alamun hadari sai kirjinsa ya fara dakan uku-uku. Don ya tabbatar ba lafiya ba. Take zuciyarsa ta fara wasu-wasin shin Anya ba Aljanin Nan bane ya sake dawowa? Tabbas daga 6angaren rijiyar nan ne yake hango kyallin walkiyar. Batare da 6ata ba RUZYAL ya dauki rigarsa ya sa, sannan ya bude Kofa ya fito tsakar gida gadan-gadan, da zuwansa bakin rijiyar sai ya iske an dauke wannan Katon murfin an ajiye gefe guda. Cikin tsananin tsoro RUZYAL ya leka cikin rijiyar, yin hakan keda wuya yaji wani Abu yayi fitar burtu ya bugi fuskarsa sai ga RUZYAL yayi tsalle sama ya fado Kasa Koda ya dago Kai sama sai yayi arba da shi. Ba wani bane face dansa JAFARU bisa wani Aljani Mai siffar tsuntsu hannayensa biyu na rungume da littafin KUNDIN TSATSUBA a kirjinsa. Koda sukayi arba sai JAFARU yayi murmushi ga RUZYAL sannan ya ce, ya Kai Abbana ai dama na gaya maka cewa sai na dauko wannan littafin gashi kuwa lallai Rana Bata karya. Cikin tsoro da matukar mamaki da damuwa, RUZYAL ya Mike tsaye yace ya Kai dana ka rufa min asiri ka rufawa kanka ka mayar da wannan littafin inda yake, idan ko kaqi, zaka tsokano masifar da ajali ya fi ta dadi. Mu hadu a 'KUNDIN TSATSUBA' na daya part C don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️ ♥️ 🥰 🥰 ♥️**KUNDIN TSATSUBA** LITTAFI NA DAYA 1 ♥️ PART C ✍️✍️ AUTHOR:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👮 TYPING & POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️🥷🥷 08112778656 ( Whatsapp) Toh idan baku manta ba a baya mun tsaya ne a inda JAFARU da YALISA suka samu nasarar dauko KUNDIN TSATSUBA daga cikin tsohuwar rijiyar nan, harma suka tsaya suna cacar baki da RUZYAL akan Yana rokonsu da su mayar da littafin. To a halin yanxu zamuci gaba...... Koda Jin haka sai JAFARU ya bushe da dariya sannan ya ce," Abba ka manta ko ni waye? Ni ne fa hatsabibi uban hatsabibai, ni ne likitan kasada mai binciko bala'i duk Inda yake, ni ne Guguwar fitina mai tada duniya tsaye. Ni dai burina bana so a zauna lafiya. Ni da tsoro mun raba gari. Da a bani labari gwara ni na bayar, Abba kayi hakuri nikam nayi gaba sai watarana idan da rabon zamu sake saduwa zan dawo gida, idan Kuma babu shikenan, wannan gani ya zamo na karshe a tsakaninmu. JAFARU na gama fadin hakan ya zunguri cikin Aljanin da kafafunsa, kawai sai Aljanin ya Kara yin sama ya luluka a cikin gajimare. Shi kuwa RUZYAL sai ya daga Kai sama Yana Mai kallonsa cikin tsananin fargaba da damuwa, hawayen takaici ya zubo Masa ya ce a ransa, duk da dai JAFARU ne kadai dana a duniya da shi gwara babu, domin yanzu gashi ya janyo min masifar da babu Wanda ya Isa ya kare ni. Tafiyar dakika sittin sukayi a sararin samaniya, suka iso wani jeji da ke bayan gari. Aljanin ya sauko Kasa gaban wani kogon dutse. Saukarsu ke da wuya, YALISA ta fito daga cikin Kogon. Koda taga KUNDIN TSATSUBA a hannun JAFARU sai fuskarta ta cika da annuri. Ta dubi wannan Aljani da ya kawo JAFARU ta ce, an gaisheka ya GULZUM, yau kayi aiki Mai girma. Cikin fara'a ta karbi KUNDIN TSATSUBA ta dube shi dakyau duba na tsanaki, sannan ta gyada Kai ta ce," barkanmu da samun wannan littafin. Yanzu sai ku biyoni zuwa cikin Kogon nan, don mu zauna muyi binciken hanyar da zamubi mu samo kubar da zata bude shi. Tana gama fadin haka ta juya ta nufi cikin Kogon. JAFARU da GULZUM suka bi ta a baya. Bayan 'yar gajeriyar tafiya ne a cikin Kogon suka iso wani Fili Mai fadin gaske Wanda aka kawata shi da ginina lu'u-lu'u. Wajen a haskeke yake da wani irin haske Wanda Ido Bai Isa yaga ta inda ya samu ba. Wajen ya kasance wata 'yar Karamar fada ce. Amma babu komai a wajen sai tarkacen kayan tsatsuba iri-iri. Babban abinda ya baiwa JAFARU mamaki shi ne, farko sa'adda zasu shiga cikin wannan Kogon, Yana ta laluben wajen, Kai kace fiye da shekaru arba'in baya ba wata Halitta da ta shiga wajen. Koda suka tunkari wajen sai yanar ta yayi da kanta kamar labule. Ta Basu wuri suka wuce. Su na wucewa sai ta dawo ta rufe hanya. Kai tsaye YALISA ta wuce izuwa gaban wani dogon tebur faffada na bakin karfe Mai dauke da kayan tarkacen tsafi iri-iri. Da zuwa sai YALISA ta ajiye KUNDIN TSATSUBA bisa wannan tebur. JAFARU da GULZUM suka tsaya bayan YALISA, suna kallon abinda zai faru. YALISA ta rufe idanunta ta dora hannayenta biyu bisa wani dutsen tsafi, ta fara surutai irin na tsafi. Bayan kamar dakika dari uku da Ashirin, sai ga wata karamar Guguwa ta bayyana akan wannan tebur, tana katantawa. Jim kadan sai Guguwar ta rikide ta zama wani siririn Aljani Wanda kaurin jikinsa Bai wuce na silin Kara ba. Dogo ne zarkalale kamar igiya, domin Kansa na tabo Dutsen Saman Kogon. YALISA ta dube shi ta ce," ya Kai LUHUMAS me ka sani dangane da wannan littafi? Tayaya zamu iya samo kubar miftahuzzarbil mu Bude shi? Najibullah Muhammad ✍️♥️ 08112778656..... ************************ Koda Jin wannan tambayar sai LUHUMAS ya runtuma da Kasa, yayi tsalle ya kwallara ihu Sannan ya dago Kai ya dubi YALISA cikin damuwa ya ce," kaicona ya Shugabata. Kiyi sani cewa yau kinyi min tambayar da nake tsoron amsawa. Duk duniya babu wata kuba da zata iya bude KUNDIN TSATSUBA face kubar miftahuzzarbil. Ita kuwa miftahuzzarbil kuba ce da aka gina daga sassa uku. Kowane sashe guda an tafi dashi izuwa bangon karshen duniya. 6angaren Gabas kudu da Arewa. Yau saura kwana arba'in cif sashen karshe ya Isa bangon Arewa. Ya Shugabata kiyi sani cewa babu wani mahaluki daga cikin Aljanu ko bil'adama da ya Isa yaje wadannan wurare a cikin lokaci kadan, sai wani Aljani guda daya da ake kira MARKAHUSSABUS. YANXU haka shi wannan Aljani na can a tsare a cikin fadar Sarki LU'UMANU na birin TEHRAN a cikin wani kurkuku da ke karkashin Kasa. A daddaure da sarkar tsafi a cikin wata battar farin karfe, ita kuwa battar farin karfen an sanyata a cikin akwattin bakin karfe, akwatin bakin karfen Kuma an kulleta da wani kwado da bashi da makulli sai dai a sareshi da wata takobi da ake kira SARJUS. Ya Shugabata kiyi sani cewa ita kuwa takobin SARJUS mallakar wani tsohon dodon Aljani ne dake cikin karshen jejin KALKIM. Jejin da saboda tsananin masifar wannan Aljani da akewa lakabi da MUGULUS. Masana tarihi sun kyasta shekarun MUGULUS da cewa a kalla zasu Kai Dari uku da Talatin da uku. Duk shekara Yana haihuwar 'yaya dubu uku. A halin yanzu jejin KALKIM a cike yake da iyalansa. Ko'ina su ne babu masaka tsinke. Duk duniya babu Wanda yasan yadda za a iya kiyaye dokokin shiga jejin KALKIM sai mahaifinki Boka JISHEN. Saboda haka Ina Mai shawartarku da ku mika wannan bukata ga mahaifinki. Shi kadai ne zai iya taimakawa ku mallaki ALJANI MARKAHUSSABUS. Koda LUHUMAS yazo nan a zancensa sai YALISA da JAFARU suka kawo gwauron numfashi suka ajiye. YALISA ta Kara dubansa ta ce ya Kai LUHUMAS Ina son ka gaya min dalilin dayasa aka kulle Aljani MARKAHUSSABUS a cikin akwatin karfe. Koda Jin wannan tambaya sai LUHUMAS ya Nisa ya ce ya Shugabata kinyi min tambayar labari mai tsawo. To Amma zanyi kokari na gajarce maki labarin a cikin Koda sa'a biyar ne. Sai ku saurara don kuji wannan labari Mai cike da Al'ajabi. NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️ 🙏 🥰 ❤️ 08112778656 SARKI LU'UMANU 🥷🥷 fiye da shekaru goma Sha biyar baya Sarki LU'UMANU na birnin TEHRAN na da wata zabgegiyar kyakkyawar mace da ake kira FATISA. Saboda tsananin kyawunta ake ganin cewa ba mutum bace zalla, wasu sun ce ruwa biyu ce. Ana zaton ubanta mutum ne uwarta aljanah. Wasu Kuma sun ce a,a ubanta ne Aljani uwarta mutum. Har yau dai babu Wanda ya tabbatar da gaskiyar Ala'marin. Bayan Sarki LU'UMANU ya Suri FATISA tsawon shekaru hudu Basu samu haihuwa ba, sai Ala'marin duniya suka ca6e Masa. Domin bashi da burin da yafi ya samu Magaji. Yayinda tunani da bakin ciki sukayi Masa yawa, sai ya Tara dukkanin bokayensa ya sanar da su halin da ake ciki. Kuma ya Nemi da su share Masa hawaye. Gaba Daya Bokayen aka rasa Wanda zai ce wani abu har wani dan lokaci. Daga can Sarkin Bokayen ya ce ya Sarkin duniya, " hakika ka zo mana da babban Ala'mari, Amma abinda nake so da Kai shi ne, ka bamu kwanaki uku muje muyi nazari, lallai ba zamu dawo Nan ba sai da hanyar biyan bukata." Koda Jin haka sai fuskar Sarki LU'UMANU ta fadada da murmushi ya ce ," to shikenan ku tafi na sallameku. Zan kasance Mai sauraronku Nan da kwana uku. Nan take suka watse suka bar Sarki shi kadai zaune a turakarsa, Yana nazarin Ala'marin a ransa. Da kwanaki uku suka cika sai Sarkin Bokayen da tawagarsa suka dawo, bayan sun kwashi gaisuwa sai Sarkin Bokayen ya ce," ya Mai duniya gaba dayanmu mun dukufa wajen bincike domin samun biyan bukatarka Amma bamu samo komai ba sai Abu guda. Sarki LU'UMANU ya gyara zama ya ce Ina sauraro, menene Abu gudan? Idan har kana so ka samu biyan bukata, to dole ne sai anje KOGON ZUHURUM an debo tsumin DODO KIRYANU ka Sha sannan matarka zata samu juna biyu. Ya Kai wannan Sarki ka sani cewa daga Nan zuwa Kogon ZUHURUM tafiya ce ta shekara dari da goma Sha biyu ga basamuden gwarzon saurayin Aljani Mai takama da karfi da sadaukantaka. Haka Kuma ka sani cewa shi dodo KIRYANU shiryayye ne, babu wani sihiri ko karfi da zai tasiri a Kansa face hikima da dabaru. A iya bincikenmu duk duniyar nan Aljani Daya ne zai iya gajarce tafiyar nan a maimakon shekaru dari da goma Sha biyu izuwa kwanaki dari da goma Sha biyu.. Ba wani bane sai Aljani MARKAHUSSABUS. Shi wannan Aljani shi ne Mafi kyawu daga cikin samarin Aljanun duniya, a halin yanxu Yana Kan tsakiyar balagarsa domin shekarunsa na haihuwa Basu wuce dari shida da arba'in ba. Saboda karfinsa da hikimarsa ake Masa lakabi da abul hikima, wato Baban hikima. A tarihin rayuwarsa Bai ta6a sa bukata a gabansa ba ta gagareshi, yakai wannan Sarki kayi sani cewa na tuntu6i wannan Aljani Kuma ya amince zai je Kogon ZUHURUM ya debo maka tsumin DODO KIRYANU Amma bisa sharadi guda. Sharadin kuwa shi ne, ba Zai fadi ladansa ba har sai yazo da wannan tsumin. Koda Sarkin Bokayen yazo Nan a zancensa. Sai Sarki LU'UMANU yayi shiru Bai ce komai ba, ya shiga Kogon tunani. Daga can sai ya dubi Sarkin Bokayen ya ce," Nima na amince Amma sai idan MARKAHUSSABUS ba zai Nemi Raina ko mulkina ba. Amma ko me yake so zan bashi. Kuma Ina so in gargade shi da cewa idan ya kuskura ya sa6a da umarnina zan sa shi a cikin kurkukun da bazai taba fitowa ba har karshen rayuwarsa kuwa. Sarkin Bokayen da tawagarsa Na Jin haka, sai sukayi zugum cikin jinjina Ala'marin. Daga can Sarkin Bokayen ya ce ya Mai duniya ai masu iya magana sun ce Waka a bakin Mai ita tafi dadi. Bari na kira MARKAHUSSABUS don kuyi yarjejeniya a tsakaninku. Kayi dai-dai Sarkin Bokaye. Sarki LU'UMANU ya fada Yana Mai yin murmushin samun natsuwa. Nan take Sarkin Bokayen ya fito da wani Dan karamin kaskon tsafi, yasa itatuwan turare a ciki ya kunna masu wuta wani irin Jan hayaki ya fara tashi, kawai ya shiga Kiran sunan Aljani MARKAHUSSABUS Yana Mai yi masa kirari da cewa ya SADAUKIN Aljanun duniya. Kai ne jarumi uban jarumai. Kai ne abul hikima. Mai biyan dukkan bukata. Ya Kai ruwan teku Mai girgiza duniya. Ya balbalin wuta Mai kone jeji. Kai ne girgije Mai Sanya inuwa ga mabukaci. Fito da izzarka da kwarjininka gaban Sarkin duniya. Sarkin Bokayen na gama fadin hakan sai garin gaba Daya ya sauya launi, hadari ya gangamo aka fara walkiya da tsawa Kai kace ruwan sama ne zai kece. Daga can sai akaga Kasa ta tsage a tsakiyar fadar Sarki LU'UMANU wani gabjejen Aljani Mai cikar sura da kwarjini ya bayyana. Bambancinsa da bil'adama Abu biyu ne kawai, Yana da fuka-fukai a kuibin cikinsa hagu da dama, sannan Yana da doguwar jela wadda saboda tsawonta har sharar Kasa ta ke idan Yana tafiya bisa turba. Aljanin ya dubi Sarki LU'UMANU ya risina ya kwashi gaisuwa, sannan ya juya ga Sarkin Bokayen ya ce," gani na Amsa kira, akan me ake nema na a yanxu? Sarkin Bokayen ya Mike tsaye ya ce," ya Kai MARKAHUSSABUS kayi sani cewa ban kirawo ka Nan ba, sai domin bukatar Nan ta sarkinmu da na shaida maka. Sarki ya amince da sharadin da ka gindaya bisa Abu biyu. Ya ce," idan har bazaka Nemi ransa ko mulkinsa ba ko me kake so zai baka. Amma idan ka bijirewa Umarninsa zai sanyaka cikin kurkukun da har abada babu Mai iya fito da Kai. Koda Jin wannan batu sai MARKAHUSSABUS ya tuntsire da mahaukaciyar dariya wadda ta sa fadar gaba Daya ta hau girgiza har sai da yayi shiru sannan wurin ya tsaya cak. Ashe har akwai wani bil'adama da yake tunanin zai iya kama ni ya tsare? Ya Kai wannan Sarki hakika kayi babban kuskure. Domin ni ne gagarau uban kangararru, gaba dayan sarakunan Aljanu ma sun rasa yadda zasuyi dani ma balle sarakunan bil'adama. Abinda nake so da Kai ya wannan Sarki kawai mu tsaya bisa alkawari Banda tunanin nuna Isa ko iKo....... Tom a dai-dai Nan ne na gaji da rubutu ainun. Mu hadu a part D don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi da debe kewa 🥰♥️ Najibullah Muhammad ✍️✍️🙏 ke cewa ku Huta lafiya🙏🙏🙏**KUNDIN TSATSUBA** LITTAFI NA DAYA 1 ♥️ PART D ✍️✍️ MARUBUCI:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👮 TYPING & POSTING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ CIGABAN LABARIN... Koda Jin wannan batu sai MARKAHUSSABUS ya tuntsire da mahaukaciyar dariya wadda tasa fadar gaba daya ta hau girgiza. Har sai da yayi shiru sannan wurin ya tsaya cak. Ashe har akwai wani bil'adama da yake tunanin zai iya kamani ya tsare? Ya Kai wannan Sarki hakika kayi babban kuskure domin ni ne gagarau uban kangararru. Gaba dayan sarakunan Aljanu ma sun rasa yadda zasuyi dani balle na bil'adama. Abinda nake so da Kai

Chapter 2 of 11