Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
11 / 11
suka dira. A wannan lokaci kishirwa ta kamasu su duka. Nanfa suka shiga Neman ruwa. Inda suka kewaya gaba Daya dajin basu ga wata fadama ko korama ba. Nanfa hankalinsu ya dugunzuma aka tsaya ana shawarar abinda ya kamata ayi. Bayan kowa ya gabatar da tasa shawarar ba a aminta da ita ba, sai JAFARU ya gabatar da tasa. Ina da shawara Mafi Alheri a garemu. Kai DURFAS Kasan cewa gaba dayanmu ka fimu karfi, sihiri da wayau da DABARA. Saboda haka zamu bar ajiyar kundin tsatsuba a hannunka. Ka hada wannan battar karfen mu Kuma zamu tafi Neman ruwan da zamusha. Dabararmu anan ita ce karmu tafi da KUNDIN TSATSUBA wani tsautsayi ya hau Kansa. Amma idan Yana hannunka munsan ya tsira, haka Kuma munsan ka fimu gajiya da Jin kishirwa Bai kamata a tafi wannan yawo da Kai ba.. Sa'adda DURFAS yaji haka sai murna ta kama shi,ya tabbatar da cewa shi keda iKon komai don haka sai ya amince da wannan shawara. Batare da Bata lokaci ba JAFARU YALISA da GULZUM suka haye bayan NARGAS suka tafi Neman ruwa. Suka bar Aljani DURFAS Yana gadin kundin tsatsuba rike da battar karfe. Bayan su JAFARU sun shafe sa'a biyu suna Neman ruwa sai suka dace suka Isa bakin wata korama. Nan take suka sauka a gefenta kowa yasha ya koshi harma su JAFARU da YALISA sukayi Wanka. Bayan sun natsu sai JAFARU ya dubesu gaba daya ya ce, abinda nake so da ku shi ne duk abinda kukaga nayi ku zura min Ido kawai Kar ku tambayeni dalili. Ina tabbatar maku da cewa zan nema mana mafita Mafi Alkhairi tsakaninmu da wancan azzalumin. Da Jin haka su duka suka ce min yarda da dukkan shirinka. Take Aljani NARGAS ya cika wata Katuwar battar fata da ruwa, JAFARU ya zura hannu a cikin aljihun rigarsa ya dauko wata 'yar Karamar akwatu ya fito da wata farar kwalba 'yar mitsitsiya Mai dauke da wani farin gari. JAFARU ya dauki wannan kwalbar ya zazzaga farin garin nan a cikin ruwan da aka debarw DURFAS. Koda ganin haka sai Aljani NARGAS yayi murmushi yace hakika sai yanzu na Gane nufin ka. Kai wannan Yaro ka cika hatsabibi, ya akayi ka samo banjun Aljanu? YALISA ta bushe da dariya ta ce ka dena mamaki na rantse da gemun mahaifina ban taba ganin hatsabibin mutum ba kamar JAFARU, domin zai iya yin abinda kaf Bokayen duniya ba zasu iya ba. Nan take suka bar wannan wuri suka koma can jejin da suka baro Aljani DURFAS. Da zuwansu DURFAS ya Mike zumbur ya taryesu da murna. Abinka da mabukaci Yana ganin ruwa a hannun Aljani NARGAS sai ya karba ya Kafa bakinsa ya kwankwade ruwan Nan, harda yin wata irin gyatsa me warin gaske. Gama Shan ruwan DURFAS keda wuya sai yaji jikinsa ya mutu, kawai sai ya koma gefe guda ya zauna, aka cigaba da fira. Ana cikin firarne kawai sai yaji idanuwansa sun fara lumshewa, ya rinka gani dishi-dishi. Cikin tsoro da damuwa yace Kai ku tsaya wane irin ruwa ku ka bani nasha? Anya kuwa Baku shirya min wani makirci ba? Caraf sai JAFARU ya Amsa ya ce Kai bakin mugu Ashe kwakwalwarka na ja, nayi zaton ba ka da kwanya. Hakane mun zuba banju a ruwan da ka Sha. Kuma ko kaqi ko kaso sai mun tafi da kundin tsatsuba da battar karfe mun barka anan, tunda baka da wani zabi Wanda yafi kayita sharar barci har tsawon lokaci Mai yawa. Yayinda DURFAS yaji wannan Batu sai ya harzuka zuciyarsa tayi baki-kirin ya yunkura da nufin ya kaiwa JAFARU duka, Amma sai yaji ya Kasa motsi. Nanfa ya kama Layi kamar Wanda ya bugu da giya. Kafin a jima tuni ya 6ingire ya kama barci harda minshari me kama da saukar aradu. JAFARU ya bambare kundin tsatsuba daga hannunsa da Kuma battar karfe.... Tom Nima a dai-dai nan ne naji na gaji ainun. Sai mu hadu a KUNDIN TSATSUBA part O don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi da debe kewa πŸ₯°β™₯️β™₯️ Wanda ni Najibullah Muhammad nake kawo maku shi, da fatan kunji dadin wannan labari. 23/12/2025πŸ‘†πŸ‘†βœοΈβœοΈβœοΈβœοΈ**KUNDIN TSATSUBA** LITTAFI NA DAYA 1 β™₯️ PART O βœοΈπŸ”œ MARUBUCI :- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI πŸͺ– TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING:- Najibullah Muhammad πŸ₯·πŸ₯· Note:- Comments da likes da share sun zama wajibi ga masu karatuπŸ‘†βœοΈ 08112778656 ( Whatsapp ) LAST CHAPTER IN BOOK ONEβœοΈβœοΈπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA.... Nan take ya dora battar karfen nan akan wani Dutse, ya je kusa da ita ya ce," ya kai MARKAHUSSABUS kayi sani cewa yau shekararka hamsin da bakwai a cikin wannan battar karfen batare da ka shaqi iskar duniyar nan ba me dan Karen dadi. Idan ka amince da bukatarmu zamu Bude wannan batta ka fito. Koda gama fadin hakan sai suka ji an kyalkyale da dariya, sannan aka ce ya Kai me wannan magana fadi kowace irin bukata, na yadda zan biya maku ita idan har kuka budeni na fito. To Amma menene sakamakona ? Kun sani cewa na shekara hamsin da bakwai a cikin kuncin rayuwa, domin an rabani da masoyiyata FATISA. Kuma a halin yanzu FATISA ta mutu. Ina amfanin rayuwata a doron Kasa, me zaku bani ya dauke min kewar FATISA? JAFARU ya ce kwantar da hankalinka zamu baka wata kyakkyawar mace wadda tafi FATISA kyau sau Dari. Kuma da zarar ka fito zamu nuna maka ita. Abinda muke so da Kai kawai shi ne, kayi mana rantsuwa cewa zaka cika mana alkawarinmu batare da ka yaudaremu ba. Koda Jin haka sai Aljani MARKAHUSSABUS yayi shiru tsawon lokaci Bai ce komai ba, daga can sai yayi ajiyar zuciya ya ce Amma fa Kun daure ni da jijiyata, dole ne na kasance me cika alkawari. Nan take MARKAHUSSABUS yayi rantsuwa da darajar soyayyarsa da FATISA cewa ba zai ci amanarsu ba. Yana gama yin rantsuwar JAFARU ya kwance igiyar da aka daure bakin wannan battar karfen. Budewarta keda wuya wani yalon Hayaki yayi fitar burtu daga cikinta, yayi tsiri izuwa sararin samaniya kamar zai tokare da hadari. Sannu a hankali hayakin ya rikide ya zama wata jibgegiyar halitta ta wani kyakkyawan Aljani Mai doguwar siffa. MARKAHUSSABUS yayi Mika gami da doguwar hamma sannan ya dubi su Aljani Aljani NARGAS wadanda ke gabansa tamkar kiyashi. Sai ya cika da mamaki yace oh! Yanzu wadannan Kananan halittun ne suka ceto rayuwata daga hannun Sarki LU'UMANU? Lallai na yadda cewa me Nisan kwana shi zai Sha kallo a duniya. Tabbas Kun cika hatsabibai. MARKAHUSSABUS na gama fadin hakan sai ya sake rikida girmansa ya kankance ya dawo girma daya da na bil'adama. Sannan ya dubi JAFARU ya ce Yaro fadi bukatarku naji. Muna so kaje bangon karshen duniya dake Gabas kudu da Arewa ka dauko mana sassan kubar miftahuzzarbil domin mu Bude littafin KUNDIN TSATSUBA. Koda Jin wannan batu sai MARKAHUSSABUS ya tuntsire da dariya ya ce ai bukatar taku ma me sauki ce. Na rantse da darajar soyayyata ga FATISA zan iya gama wannan aiki a cikin kwanaki dari da hamsin. JAFARU ya ce mun San da haka, Amma Muna so kayi tafiyar nan ne tare damu. Domin Muna tsoron kada Aljani DURFAS ya Farka daga barcin kwana arba'in ya halaka mu. MARKAHUSSABUS ya bushe da dariya a karo na biyu ya ce ba matsala zan tafi da ku. Kuma muddin kuna tare dani, to babu wani tsautsayi da zai hau Kanku. Yanzu Ina alkawarinmu da ku? Ina so ku nuna min kyakkyawar budurwar da kuka ce tafi masoyiyata FATISA kyau. Nan take JAFARU ya dauki madubin tsafinsa ya shafe shi da hannun hagu, sai ga hoton Gimbiya sima kwance a Kasa cikin kurkukun Sarki LU'UMANU har yanzu bata farfado daga dogon Suman da tayi ba. Sakamakon mangarewar da Aljani DURFAS yayi Mata. A kusa da ita Kuma jarumi Hubairu da waziri Qaddaru ne a sume. Yayinda Aljani MARKAHUSSABUS yayi arba da sima sai kyawunta ya bugi zuciyarsa nan take ya rude ya dimauce, ya ce tabbas wannan tafi masoyiyata FATISA kyau. Maza ku hau bayana mu tafi izuwa wannan aiki, ko na dawo na mallaki wannan sarauniyar kyau ta Karar min da bakin cikin shekara da shekaru. Take MARKAHUSSABUS ya sake rikida ya zama babbar Halitta. Cikin zafin nama ya Suri JAFARU da YALISA GULZUM da NARGAS ya azasu a bayansa. Yana Bude fuka-fukansa ya luluka da su cikin sararin samaniya, Yana mai keto hazo cikin tsananin gudun da yafi na tauraruwa me wutsiya. Kamar yadda yayi alkawari haka Ala'marin ya kasance. Wato cikin kwanaki hamsin-hamsin MARKAHUSSABUS ya kewaye bangwayen duniya guda uku da su JAFARU Kuma ya dauki masu sassan kubar miftahuzzarbil. Daga nan suka dunguma izuwa kurkukun Sarki LU'UMANU suka iske su jarumi Hubairu a kwance har yanxu Basu Farka daga barci ba. Nan take JAFARU yayiwa MARKAHUSSABUS izinin daukar Gimbiya sima. Cikin tsananin farin ciki ya dauketa ya tafi da ita abinsa. Su ko su JAFARU sai suka tafi suka bar su jarumi Hubairu da waziri Qaddaru kwance a wajen. Bayan sunyi Nisa ne sai YALISA ta dubi JAFARU ta ce Wai shin yaushe ne su jarumi Hubairu zasu farfado daga wannan dogon barcin da suke? JAFARU ya kyalkyale da dariya ya ce ba zasu Farka ba, har sai ranar da Aljani DURFAS ya Farka daga barcinsa. Wannan ranar kuwa zata zo dai-dai da ranar da zamu kammala Karanta littafin KUNDIN TSATSUBA. Koda Jin haka sai suka bushe da dariya gaba Daya. Bayan 'yar gajeriyar tafiya sai suka sauko Kasa cikin wani jeji me kyawun gaske. Ko'ina ka duba furanni ne da shuke-shuke. Wata irin iska Mai dadi na kadawa a hankali a wannan wuri. Nan take JAFARU, YALISA NARGAS da GULZUM suka zauna don a bude KUNDIN TSATSUBA. Zamansu keda wuya sai YALISA ta faki idanun NARGAS ta maka Masa igiyar tsafinta a ka, take Kan nasa ya rabe gida biyu. Sai ga kwakwalwarsa tana kwaranya, Nan ya fadi Kasa matacce. JAFARU da GULZUM suka kyalkyale da dariya, kinyi mana maganin munafiki me kwanton 6auna Yana so ya cucemu be san cewa Muna sane da shi ba. YALISA tayi murmushi ai ba don na shammace shi ba, da tuni yayi mana yadda mukayiwa Aljani DURFAS. Kai be kamata mu tsaya 6ata lokaci ba. Maza Bude mana littafin nan musha kallo. Take JAFARU ya fito da kubar nan ta Miftahuzzarbil ya zurata a cikin kafarta Dake jikin littafin ya murda hannun hagu, sai ko sukaji Kara alamar cewa ta bude. Kawai sai ya zare kubar sannan ya daga bangon kundin tsatsuba a hankali cikin tsoro-tsoro. Yana buduewa sukayi arba da hoton wata Katuwar rijiya bisa shafin farko, a Saman rijiyar anyi rubutu Layi hudu. JAFARU ya dubi YALISA da GULZUM ya ce a cikinku waye zai Karanta mana wannan littafin? YALISA ta ce ai babu Wanda ya cancanci ya Karanta sai Kai, tunda dai duk ka fimu rashin tsoro. Ni Kam tun yanzu har jikina ya fara 6ari. Shi ko GULZUM sai yace ni Kam Ina daga baya-baya da naji kayya-kayya zan cika wandona da iska. JAFARU Karanta Muga abinda zai faru. Batare da fargabar komai ba JAFARU ya fara karatu kamar haka:- Wannan rijiya, rijiya ce ta bala'i da masifa. An Gina ta kimanin shekaru dubu dari uku baya. Mai karatu shigo ciki ka ganewa idanunka. JAFARU na gama wannan karatu sai wata irin iska Mai tsananin karfin tsiya ta fito daga cikin kundin tsatsuba gaba daya duniya ta hau tangal-tangal. Kafin su JAFARU su ankara tuni iskar nan ta zuke su sun zama 'yan kanana mini-mini sun shige cikin wannan littafi. Kawai sai gani sukayi sun fada cikin wata rijiya Mai zurfin gaske, a cikin wata nahiyar duniya. JAFARU YALISA da GULZUM sukayi ta tafiya a cikin rijiyar nan sululu tafiya taqi karewa. Sai da sukayi tafiyar kwana uku suna shigewa cikin rijiyar nan sannan suka riski karshenta. Wani abun mamaki karshen rijiyar turba ce ko kadan babu ruwa a ciki. Saboda tsananin iskar da suka Sha kafin su iso karshen wannan rijiya, gaba dayansu a sume suka fado. Basu farfado ba sai bayan awa Ashirin da hudu. Koda suka Farka sai sukaga wata Kofa wacce zata iya fitar da su daga cikin wannan rijiya. Nan fa suka tsaya suna kallon juna, kowa idanunsa ya zaro kamar ace kyat ya fita da gudu don tsoro. YALISA ta dubi JAFARU ta ce Wai shin nan a Ina muke ne? JAFARU ya Bata Rai sannan ya ce ya Zaki tambayi kaza hanyar Rafi? Sai ki nemi agwagwa Kisha labari. GULZUM yace uhm, duk jinku nake. Ai anan babu agwagwa Kuma babu rafin balle a samu labarin. Ko Kunsan kau a cikin wata duniyar daban muke? Na rantse da girman tsafi wannan duniyar ba irin tamu bace, don komai nata daban ne da irin namu. To yanzu menene abinyi? YALISA ce ta sake tambaya. Abinyi kawai mu tashi mu bude wannan kofar mu fita. Inyaso sai Muga inda zata kaimu. Karambaninmu ne dai ya janyo a cikin masifar da bamu San farkonta ba, ballantana karshenta. Kawai sai JAFARU yaje ya bude wannan Kofa, gaba dayansu suka leka waje. Rashin sani yafi dare duhu, inda su JAFARU sun San abinda zasu gani a wajen wannan Kofa da Basu Bude ba. Ba komai bane sai ruwan teku. Iya hangensu gabas da yamma kudu da Arewa ruwa ne. Ita kanta wannan rijiyar da suke ciki a tsakiyar teku take bisa wani Dan mitsisin tsubiri. Nan fa hankalinsu ya tashi suka rasa abinda ke masu dadi. JAFARU ya dubi GULZUM ya ce ai Kai Aljani ne, kana da fuka-fukai me zai hana ka dauke mu ka ketare tekun nan da mu? GULZUM yace tabdijammmm inda zan iya aiki da fuka-fukan nan ai da tuni nayi Amfani da su tun sa'adda fado cikin rijiyar nan. 08112778656 ( Whatsapp ) Najibullah Muhammad KATSINA❀️❀️✍️✍️ NA GAYA maku wannan duniyar ba irin tamu bace. Ba abinda zamu iya yi da kanmu. Kunga ku dubi sararin samaniya ba irin na duniyar mu bane. Cikin sauri YALISA da JAFARU suka daga kawunansu sama, sukaga taurari manya-manya kamar duwatsu. GA su Nan birjik kamar duwatsu. Nanfa Ido ya rena fata suka gasgata maganar Aljani GULZUM. Kunga zama ba namu bane. Kuzo mu afka tekun nan, kome zai same mu ai gwara ma ya samemu mu huta da fargaba. Kawai sai JAFARU ya fita ta cikin kofar nan ya fada cikin tekun ya fara iyo. YALISA da GULZUM suka bi bayansa. Koda sukayi nitso cikin ruwan sai sukaga wani Katon rami wawakeke Mai tsananin duhu. Kai kuzo mu shiga cikin wannan ramin, watakila hanya ce ta fita daga cikin ruwan Nan. JAFARU ne yayi wannan furuci Kuma ya shige gaba Suma suka bi bayansa. Abinda Basu sani ba shi ne, bakin wani Katon ne suka shige. Suna shiga kifin ya rufe bakinsa ya cigaba da sha'anin gabansa. A Kalla sai da su JAFARU suka wuce kwana Ashirin da biyu cikin-cikin kifin Nan suna rayuwa ta kunci wuya da Azaba. Gaba dayan jikinsu yayi lugub-lugub saboda tsananin zafin cikin kifin Nan. Ba su da abinci sai Kananan kifaye Wanda kifin ya hadiya. Tsawon wadannan kwanaki wannan Katon kifi Yana ta tafiya ne a karkashin teku. A Rana ta Ashirin da biyu ne ya Isa gabar tekun, yaje ya amayar da su JAFARU suka fado a cikin cikinsa a matukar galabaice. Sai da iskar waje ta buge su sosai sannan fatar jikinsu ta bushe ta dawo kamar yadda take daa. Sannan suka mike suka dubi Gabas da yamma kudu da sukaga iya hangensu daji ne. Kawai sai suka kunna Kai cikin dajin batare da sanin inda suka dosa ba. Suna cikin tafiya ne suka rinka Jin wani irin huci Wanda Basu taba Jin irinsa ba. Hucin na zuwa ne da wata irin iska me zafi. Nanfa suka tsaya suna waige-waige domin sun Kasa gano daga inda hucin ke tahowa. Ba zato ba tsammani sai sukaga wata irin Katuwar macijiya, wadda idan ta Mike saboda tsananin tsayinta sai suga kamar kanta zai tabo manyan taurarin nan da ke sararin samaniya. Macijiyar ta Kura masu idanu ta cigaba da hucinta tana furzar da dafi daga bakinta. Nanfa jikin su JAFARU ya kama karkarwa gudu ya gagara tsayiwa ta gagara. Koda macijiyar ta rankwafa kanta Kasa, sukaga zata danne su da wannan rafkeken kan nata. Sai suka ranta a na kare, Nan fa suka Kasa tsere suna gudu iyakar ransu, Amma duk da haka macijiyar nan Bata fasa binsu ba. Sai da suka wuni suna gudu sannan suka dena ganinta. Nan fa suka zube a Kasa suna haki numfashinsu na fita dakyar. Haka dai su JAFARU suka rinka haduwa da mugayen dabbobi iri-iri har kala dubu. Kowace dabba sai tayi kamar zata halaka su, sai kaga sun kubuta dakyar. Yayinda dabbar karshe ta hadiyesu sai suka tsinci kansu a cikin rijiyar nan wadda suka fado cikinta sa'adda suka fara Karanta littafin Kundin tsatsuba. Sai iskar nan me karfi ta ratso cikin rijiyar ta kwashesu tayi sama da su, sai gashi sun fito ta cikin KUNDIN TSATSUBA sun dawo duniya da suke da. Har yanxu Kundin tsatsuba na ajiye a inda suka barshi, Kuma shafin farko ne a Bude. JAFARU YALISA da GULZUM suka dubi juna sukayi tsuru-tsuru da idanu. Sai wannan ya dubi wancan, wancan ya dubi wannan. Daga can sai JAFARU ya ce to yanzu munga masifar Dake cikin shafi na farko, don haka sai mu bude shafi na biyu don Muga abinda ke ciki. Koda Jin wannan batu sai YALISA da GULZUM suka koma gefe guda suka tsaya. YALISA ta ce Kai takadari shugaban hatsabibai ba dai damu ba, sai da ka bude ka gani Kai kadai. Mu Muna daga nan inka dawo ka bamu labari, wahalar da muka Sha ma ta ishemu. JAFARU ya bushe da dariya ya ce ai ihu ku ke Yi bayan hari, tunda aka fara da ku dole sai an kare da Ku. Ka'idar wannan littafin kenan. Inda zaku gudu kuyi tafiyar shekara dubu duk Inda ku ke sai iskar nan ta zuko ku. JAFARU na gama fadin hakan sai ya bude shafin gaba, sai yaga hoton wata jibgegiyar bishiya, a samanta anyi wani rubutu kamar haka... Wannan bishiya. Bishiya ce ta masifu da bala'i Kuma an shuka ta ne kimanin shekaru dubu dari shida baya. Mai karatu hayo kasha kallo. Ai ko yana gama karantawa iska ta ratso wajen ta cika wajen ta zuke shi sannan ta zuke su YALISA wadanda ke can gefe guda. Sannan ta mayar da su 'yan kanana mini-mini kawai sai tsintar kansu sukayi a cikin wadansu dakuna. Dakuna ne a jere kimanin guda dubu. Da shigarsu suka kunna Kai cikin dakin farko. Da shigarsu suka iske babu komai a ciki sai wasu manyan dodanni sun daddaure bil'adama ciki suna Zane su da bulalar wuta. Aljanun nan na ganinsu su JAFARU sukayi wuf suka kamosu suka shiga Zane su da wannan bulalar wuta, sai da aka kwana goma ana masu wannan Azaba sannan aka jeho su cikin daki na biyu. Nan ma akayi masu wata kalar azabar daban. Kai a takaice dai sai da aka shigar da su JAFARU dakuna dubu, Kuma duk Inda aka shigar da su sai anyi masu Azaba kala daban da ta baya. Bayan an gama yimasu azabar karshe ne aka Watso sh a cikin duniyarsu. Wannan karon sai da sukayi jinyar kwana arba'in sannan suka warke daga raunikan da ke jikinsu. Suna warkewa JAFARU ya Bude shafi na uku daga cikin shafukan KUNDIN TSATSUBA, inda yaga hoton wuta. A kasanta anyi rubutu kamar haka:- Wannan wuta ce ta bala'i da masifa, an hada ta ne shekaru ba adadi baya. Me karatu shigo cikinta kasha kallo. Nan take iska ta zuko su JAFARU ta watsa su cikin wata duniya daban. Sai gasu cikin wata irin wuta Mai tsananin zafi, nan take suka babbake. Kasusuwansu ma sai da suka farfashe suka narke Amma daga karshe, aka sake tashinsu aka jefa su a cikin wata wutar da tafi ta wannan zafi. Haka dai akayi ta sauya masu wuta, har sai da aka sauya masu wuta kalau dubu. Kowace suka shiga sai suji tafi ta baya zafi, daga karshe aka Watso su waje izuwa duniyar su ta Asali. A wannan lokacin NE su duka ukun suka fashe da kuka suna masu nadamar Nemo wannan littafi da har suka bude shi. Gashi ya zame masu alakakai.. wannan karon sai JAFARU yaki bude shafin gaba, ya tsaya kawai Yana kallon littafin hawaye na zuba daga idanunsa. Koda aka samu dakika sittin a haka sai shafin ya Bude Kansa izuwa shafi na hudu. Take sukayi arba da hoton wata kankara a samanta anyi rubutu Layi hudu kamar haka... Wannan kankara. Kankara ce ta bala'i da masifa, Kuma an Samar da ita ne kimanin shekaru dubu saba'in baya, mai karatu shigo cikinta kasha kallo.. muryan nayi shiru sai iskar nan ta fito daga cikin kundin tsatsuba ta zuke JAFARU da YALISA da GULZUM suka zan 'yan kanana suka shige cikin wannan littafin Tom Alhmdllh Ala kullu halin.. Nan wannan littafi KUNDIN TSATSUBA na daya ya zo karshe. Marubucin yace mu hadu a KUNDIN TSATSUBA littafi na biyu. Ina fatan masu karatu Kunji dadin wannan littafin. Idan har Kuna son na kawo maku cigaban wannan littafin da wuri, to ya zama dole kuyi comments da likes Mai yawa domin nuna farin cikinku.. Bari mugani ko Kuna son littafin nan sosai πŸ’―πŸ’―πŸ’―πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜… Anan Nan nake cewa mu hadu a KUNDIN TSATSUBA na BIYUβœοΈβœοΈπŸ™πŸ™πŸ™ 31/12/2025. Last day in 2025 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 11 of 11