sani cewa ba zasu cinyeku ba farat daya, a duk Inda suka kama ku sai sun tafi daku izuwa ga mahaifinsu MUGULUS. Da zarar sun Kai ku za a sanyaku a cikin wani kejin ice a kulle, zaku zauna anan har tsawon kwana uku. Ba don komai za a ajiye ku wannan wuri ba, sai don zaman jiran yajin da Matar MUGULUS zata dafa. Wanda da wannan yajin ne MUGULUS zayyi Amfani wajen cinyeku. Idan har Kuna so ku ku6uta daga haka sai Kun kiyaye dokoki bakwai.
*Doka ta farko ita ce Kar ku kuskura ku ce zaku yaki wadannan dodanni.
*Doka ta biyu yayinda kuka fada hannunsu kada dayanku ya sake yin magana da dan uwansa.
*Doka ta uku ita ce tsawon kwana ukun da zakuyi a cikin keji Kar kuci ko kusha duk abinda suka kawo maku Koda kuwa kunajin kamar yunwa da kishirwa zasu kashe ku.
*Doka ta hudu ita ce kada ku jarraba aiki da tsafi.
*Doka ta biyar duk sa'adda dodannin nan suka zo suna kallon ku, to ku sunkui da kawunanku Kasa Kar ku dinga hada idanu da su.
*Doka ta shida ita ce, akwai wata bishiyar Zinari a kofar gidan MUGULUS daf da inda kejin da za a sanyaku yake. Kullum da safe kuyi sujjada ga wannan bishiya tsawon kwanaki ukun.
*Doka ta bakwai ranar da za a fito daku daga cikin kejin nan domin a cinyeku kada kuyi gardamar fita. Da zarar anzo giftawa daku ta gaban bishiyar Zinarin nan, gaba dayanku ku daga Kai sama ku Kalli bishiyar. Kuna yin hakan ganyayen zasu zuzzubo Kasa ba adadi iyakar ganin mutum. Da faruwar hakan gaba dayan dodannin nan zasu zama gumaka har uban nasu MUGULUS da iyalansa. To a wannan lokaci ne zaku kunna Kai cikin gidan MUGULUS. Ku shiga izuwa cikin gidan Kai tsaye batare da Jin tsoron komai ba, zaku wuce dakuna Dari uku da Sha biyu wannan na bin wannan ku ratsa ta cikinsu har izuwa daki na karshe. A cikin wannan daki ne zaku iske kokunan kawunan bil'adama birjik ba adadi. Wadannan su ne iyakar kokunan kawunan bil'adaman da dodo MUGULUS yaci a duniya. A wannan lokacin zakuyi duba izuwa bangon gabas din dakin daga sama, zaku ga takobin SARJUS a sakale a jikin bango a jikin wata kusa. Wannan takobi anyita ne da zallan kashin bil'adama, Kuma tsawonta bai wuce kamu biyu ba. Kuma tana da matukar nauyi, inda za a Tara karti dari ba zasu iya daukarta ba, Amma idan suka dauki kokon Kai guda daga cikin kokunan kawunan bil'adaman da ke dakin kuka jefi takobin da shi, shikenan Kun karya alkadarin nauyinta kowa daga cikin ku zai iya daukarta.
Kuna daukar takobin sai ku hanzarta fita daga cikin dajin kuyi ta tafiya da kafafunku batare da Kun gogi Koda Gunki guda ba daga cikin gumakan dajin, har tsawon sa'a guda. Sannan ku haye bisa Aljani NARGAS ya tashi daku sama ku bar wannan jejin na KALKIM. Ku sani cewa idan kukayi kuskure kuka bugi Gunki guda daga cikin gumakan nan har ya fadi Kasa, take zasu tashi gaba daya su kama ku su dasa maku Wawa. Wani ma ko digon jinin ba zai samu ba.
Sa'adda Boka JISHEN yazo nan a zancensa sai hankalin YALISA ya tashi, ta dubi JAFARU ta ce," Abokina Kaji fa irin hadarin dake cikin jejin KALKIM Yaya zaka iya zuwa? JAFARU yayi murmushi ya ce," ai Koda hadarin ya ninka haka sau goma ba zan sauya ra'ayina ba. Ya Kai wannan Boka kayi sani cewa na fito da shirina ba gudu ba ja da baya. Kai nake Jira kawai, ke Kuma qawata idan Kin karaya da wannan tafiya kiyi zamanki na hutassheki, Amma nayi maki alkawarin cewa lallai zan dawo gareki bayan na kammala hada kubar nan ta Miftahuzzarbil. Da Jin wannan batu sai YALISA taji kamar an cire mata dukkanin tsoron wani Abu dake doron Kasa, kawai sai ta ce lallai maganganunka sun Kara min kwarin gwiwa. Babu makawa da ni za ayi wannan tafiya. Tana gama fadin hakan ta juya ta dubi mahaifina ta ce ya Kai Abbana gamu gareka sallamarmu mu kama gabanmu.
DOKA TA TAKWAS ITA CE DOLE NE KU YAWAITA COMMENTS DA LIKES DA SHARE MUDDIN KUNA SON A RINKA KAWO MAKU WANNAN KAYATACCEN LABARI ✍️🪖🪖
Mu hadu a Kundin tsatsuba na daya part I don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi da debe kewa...
Wanda ni Najibullah Muhammad ke kawo maku shi, nake cewa ku huta lafiya 🙏🥰❤️♥️**KUNDIN TSATSUBA**
LITTAFI NA DAYA 1 ♥️♥️
PART I ✍️💯
NA:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👮👮
TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷🥷
COMMENTS DA LIKES DA SHARE NA DA MATUKAR MUHIMMANCI ✍️✋✋
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...
Boka JISHEN ya bushe da dariya ya ce," haka nake so naga Yara da dakakkiyar zuciya irinta manya, domin nan gaba ku zama ababan tsoro. Nan take JISHEN ya kwallawa Aljani NARGAS kira sau uku, ya bayyana a gabansa. Ya risina cikin girmamawa ya kwashi gaisuwa. BOKA JISHEN ya dube shi ya ce," yau ne ranar tafiyarku izuwa jejin KALKIM. Inaso kayiwa su YALISA rakiya. Duk sa'adda kaga Aljani GULZUM ya tafi, sai ka dauke su gaba daya har shi kuci gaba da tafiya. Ka sani cewa daga nan zuwa jejin KALKIM tafiya ce ta shekaru goma Sha bakwai. Amma idan kukayi hanzari zaku iya Isa cikin kwanaki Tara. Kamar yadda Kasan dokokin shiga jejin KALKIM su ma sun sani don na sanar da su. Haka Kuma Umarnin nan da na baka, lallai Kar ka manta dashi. Koda Jin haka sai YALISA ta dubi mahaifinta cikin alamun rashin yadda ta ce, ya Abbana wane Umarni ne Kuma ka baiwa NARGAS wanda mu bamu sanshi ba? JISHEN yayi murmushi ya ce, wannan Kuma wani Abu ne Kuma Wanda Bai shafeku ba. Yake 'yata don me Zaki damu alhalin Kinsan cewa bazan iya Cutar da ke ba. YALISA ta gyada Kai Bata ce komai ba. Nan take Boka JISHEN ya yiwa Aljanun nan biyu izinin tashi.
Cikin hanzari YALISA da JAFARU suka dare bayan GULZUM, KUNDIN TSATSUBA na makale a hammatar JAFARU, GULZUM ya Bude fuka-fukansa yayi sama. NARGAS yabi bayansu, suka ratsa ta cikin Saman rufin dakin kamar yadda haske ke gauraye wuri suka fice. Bayan sun Samu kamar rabin sa'a suna tafiya a cikin gajimare, sai Aljani NARGAS ya matsa kusa da Aljani GULZUM Wanda ke dauke da JAFARU da YALISA ya ce," Kai GULZUM Kasan wani abu kuwa? GULZUM yace Ina fa? Sai ka fada. Tun sa'adda muka fara tafiyar nan nakejin kamshin Dan uwanmu Aljani a bayanmu. Amma na waiga iya waige Banga komai ba. GULZUM yace Ashe ba ni kadai nake ji ba. Kawai dai ka rigani fada ne, lallai Ina zargin cewa wani na biye da mu. Yanzu menene abinyi? Caraf JAFARU ya tari numfashin su yace to menene abun damuwa don wani na biye damu? Koma waye ai bai cika jarumi ba, tunda har yaji tsoro ya boye Kansa. In ya Isa ya fito Fili mana. Kunga ku kwantar da hankalinku, koma wanene yaci gaba da binmu din. Abinda na sani shine babu Wanda ya Isa ya rabamu da littafin KUNDIN TSATSUBA ko Kuma kubar nan ta Miftahuzzarbil Idan mun samo. Ba wani bane 6oyayyen Aljanin dake biye da su JAFARU ba, face Aljani DURFAS. Wanda ke dauke da Gimbiya sima tare da guntun wazirinta Qaddaru. Duk hirar dake wakana a tsakanin JAFARU da Abokan tafiyar sa sunaji. Har ma Ala'marin ya baiwa Gimbiya sima dariya, ta dubi Qaddaru ta ce, Kaji kuri irin na Yaron nan, wai har cewa yake ba a Isa a rabashi da kundin tsatsuba ba. Imba don Muna Kan Umarnin Boka SULBAINI ba, ai da mun ganar da shi kuskurensa. Qaddaru yayi dariya yace," kedai rabu da shi. Idan kare na yawo zomo na yawo watarana za a hadu."
Duk da cewa su Qaddaru suna daf da su JAFARU Amma Basu ji wannan hira tasu ba, saboda karfin sihirinsu. Lallai tsafi kogi ne, idan Mutum ya shige shi sai dai ya debo iya rabonsa ya bar saura. Haka dai tafiya taci gaba da wakana har tsawon kwanaki uku. A Rana ta ukun ne da la'asar JAFARU ya dubi YALISA yace ke qawata a Gaskiya na gaji sosai, Ina da bukatar Hutu. Koda Jin haka sai YALISA ta yiwa GULZUM Umarnin sauka Kasa. Nan take yabi Umarni, Shima NARGAS ya bishi a baya sukayi Kasa. Ala'marin su Gimbiya sima kuwa, Ashe itama ta gama gajiya tilis, Koda taji ance a sauko Kasa a huta sai murna ta kama ta. Batare da Bata lokaci ba Shima Aljani DURFAS ya sauko Kasa. Ya dira bisa turba baya kadan da Inda su JAFARU suke. Gimbiya sima da Qaddaru suka sauka daga Kan DURFAS sannan ta dube shi ta ce," zamu Dan taka sawayenmu don Muji dadin jikinmu, lallai ka tsaya nan kana lura da su JAFARU kada su shammace mu su tafi bamu sani ba. DURFAS ya ce,_ an gama ranki shi dade. Amma fa ku kula da Kanku sosai, don babu mamaki a samu mugayen Aljanu ko dodanni a wannan jejin. Sima tayi murmushi ta ce," Kar ka damu zan iya karemu daga sharrinsu.
Batare da Bata lokaci ba sima ta wuce gaba Qaddaru na biye da ita a baya, yana tafiya dugul-dugul Kai kace Aljani ne ba mutum ba saboda tsabar gajartar sa. A bangarensu YALISA kuwa JAFARU ne ya ce, Kai ya kamata mu tashi mu dan kewaya dajin nan. Kinsan ance zama wuri Daya tsautsayi ne Inji kifi. YALISA tace hakane, Amma Kuma ai karambanin akuya ke Kaita ramin Kura. Baka San zama waje daya. Garin yawace-yawacenka Kar Kasa mu fada mugun hannu. Kedai matsoraciya ce, in bazaki ba ni ki kyaleni na tafi. A dawo lafiya Nikam Ina nan tare da su NARGAS. Shawarar da zan baka, idan kaga hallaka ka kwallah ihu mu kawo maka dauki. JAFARU yayi murmushi ya ce," Haba, nifa namiji ne ai ba asan Maza da ragwanta ba. Bana gudu don wuya, sai dai idan kukaji shiru Kuna iya bin baya. JAFARU na gama fadin hakan yayi gaba ya nausa cikin jejin batare da sanin inda ya nufa ba. Gimbiya sima da waziri Qaddaru kuwa, Basu dade suna tafiya a cikin jejin ba sai kawai suka ga wani kerarran gida guda Daya tal a gefe guda. Ala'marin da yayi matukar Basu mamaki kenan, suka tsaya cak suna kallon gidan. Suka dubi junansu, sima ta ce dubi wannan abun Al'ajabi. Wanene Kuma yazo ya dandasa kyakkyawan gida a tsakiyar jeji? Lallai sai munje ga wannan gida, ko don naga mamallakinsa.
Cikin alamun tsoro Qaddaru yace a,a sarauniyar duniya Kar muje wajen can. Babu mamaki tarko ne na mugayen Aljanu. Inda kamar ma Muna tare da Aljani DURFAS ne babu matsala, domin zai iya karemu daga sharrinsu. Ni ko dadina da Kai ka cika tsoro. Wai an gaya maka cewa ni kyalle ce? Ina tabbatar maka da cewa Ina da cikakken sihiri ba karamin Aljani bane zai iya Cutar Dani. Hakane ranki ya dade ba musu nake dake ba, Amma Kinsan ance hanyar lafiya a bita da shekara. Koda Jin haka sai Gimbiya sima ta dakawa Qaddaru tsawa ta ce," na umarceka da ka biyoni izuwa cikin gidan can. Idan ko kaqi na rantse da darajar sarauta ta sai na sa an maka azaba Mai radadi. Tuba nake ranki ya dade tabbas zan biki Koda zan rasa rayuwata. Bin umarninki shi ne ibada ta. Kai tsaye Gimbiya sima da Qaddaru suka durfafi kofar wannan gida. Da zuwansu suka iske kofar shiga a kulle garam. Sukayi -sukayi su Bude Abu ya gagara. Har sun hakura sun juya da baya da nufin komawa inda suka fito, sai kofar ta bude da kanta. Cikin sauri suka waigo Amma Basu ga kowa a bakin kofar ba. Batare da Jin tsoron komai ba, sima ta juya da nufin shiga gidan. Qaddaru na biye da ita a baya cikin tsananin tsoro. Sai waige-waige yake kamar ace kyat ya tsere. Har suka kunna Kai cikin gidan jikin Qaddaru Bai dena karkarwa ba. A koyaushe Yana waigen wannan kofar ta shiga. Don Yana tsammanin zata iya rufe kanta. Wani abun mamaki babu komai a cikin gidan. Sai tarin dukiya da tsubin zinare da lu'u-lu'u da jauhari da sauransu. A cikin wadansu irin manyan tukwane na Kasa. Saboda dadewa duk yana ta lullube su. Koda ganin wannan dukiya sai idanun Qaddaru suka zazzaro farin ciki ya lullube shi yace ranki ya dade, ai ni ko daga nan na tsaya da wannan tafiya na gama rabauta.
Na tabbata jikokina da tatta6a kunnena ma ba zasuyi talauci ba a doron Kasa. Kawai sai ya Kai hannunsa cikin tukunya guda da nufin ya kwashi dukiya, sima ta daka Masa tsawa, ta janye hannunsa da sauri. Ta ce na hore ka da kada ka kuskura ka taba komai a cikin gidan nan. Ka sani cewa ba mu baro gidanmu don wannan bukata ba. Wannan dukiyar tamkar qura ce daga cikin irin dukiyata. Kayi hakuri indai muka koma LAHARIM cikin biyan bukatata zan baka ninkin ba ninkin dinta. Sima na gama fadin haka ta hango wani allon karfe karfe bisa wani farantin Zinari. Cikin sauri ta Isa wajen, ta dubi rubutun da ke jikinsa cikin natsuwa. Ta ga bayani kamar haka:-
Ya Kai bakon wannan gida kayi duba izuwa bangon Arewa zaka ga mabudin shiga ainihin taskar gidan nan, ka Bude ka shiga duk abinda kake nema a rayuwarka zaka samu a ciki. Koda Gimbiya sima ta gama wannan karatu sai ta juya ta dubi bangon Arewa. Ai ko sai tayi arba da wani zagayayyen karfe maƙale a jikin bango Wanda da gani Kasan wana shi akeyi Yana zagayawa tamkar Dutsen niqan tsaba, Wanda dawaki ko shanu ke sarrafawa. Kai tsaye sima ta je ga wannan mabudi ta fara kokarin wana shi. Amma sai ta jishi da karfi sosai. Kawai sai ta kwallawa Qaddaru kira ya ruga gareta suka hada karfi suka wana shi ya rinka juyawa a hankali- a hankali.
Ba zato Kuma sai suka ga wata kofa na Budewa a kasansu. Yayinda suka kure mawanin sai kofar ta bude dai-dai yadda mutum zai iya shiga. Koda suka leka sai sukaga Ashe wani gida ne a karkashin Kasa. Batare da Bata lokaci ba sima ta kama hannun Qaddaru ta wuce dashi cikin wannan Kofa. Suna masu bin wata matattakala har suka kule a ciki. A dai-dai wannan lokaci ne JAFARU ya shigo wannan gida, inda aka zube dukiya ta farko wadda su sima suka fara gani. Sa'adda JAFARU yaga wannan dukiya sai Shima ya cika da mamaki. Bai ta6a komai ba har ya hango wannan Kofa ta karkashin Kasa. Kawai sai ya kunna Kai ciki kamar yadda su Gimbiya sima sukayi. Bayan Gimbiya sima da Qaddaru sunyi 'yar doguwar tafiya kadan kawai sai suka riski kansu a cikin wata fada Mai dauke da dukkanin wani kayan alatu na duniya. A gefe guda Kuma ga kyawawan samari da 'yan mata cikin Kayataccen ado, Wanda idanu bai ta6a ganin irinsu ba. Wani irin kamshi Mai dadin gaske na tashi a wurin. Dangane da abinci da abin Sha kuwa babu irin nau'in da babu a wannan wuri. Sima ta tsaya ta karewa samarin wajen kallo tsaf, sai ta Kasa Gane Wanda yafi wani kyawu. Tabbas duk Wanda ta samu daga cikinsu a matsayin mijin aure ta gama morewa. Nan fa ta tsaya tana duru-duru da tunanin Wanda ya kamata ta aura.
Shi ko waziri Qaddaru Koda yaga wadannan kyawawan 'yan mata sai ya rude ya dimauce ya fara ayyanawa a ransa cewa shikam sai dai ya tafi dasu gaba daya ya zuba su a gidansa na LAHARIM. Ko kallonsu kadai yakeyi bazai Kara bakin ciki a rayuwarsa ba. Sima ta nufi inda kyawawan samarin suke tana mai kallonsu daya bayan daya kowanne nayi Mata murmushi gami da mika mata hannu da nufin ta za6e shi..
Shima Qaddaru kawai sai ya nufi inda zika-zikan 'yan mata suka rinka yimasa yanda samarin suka yiwa sima. Koda sima ta kama hannun daya daga cikinsu sai dukkaninsu suka rikide suka zama wadansu irin dodanni, masu mummunar kama. Sukayi mata kama-kama tana ihu suka daddaure ta a jikin wani dogon karfe. Sannan suka ja da baya sukayi cirko-cirko, kowannensu na tande harshe. Kamar yadda abun ya faru da Gimbiya sima haka ya faru da Qaddaru. Shima wadannan kyawawan 'yan mata sun rikide sun zama dodanni, Kuma sun daure shi tamau a jikin dogon karfe, sun tsaya cak kamar masu jiran Umarni. Ba zato sai kawai suka fara Jin wani irin gurnani Wanda Basu taba Jin irinsa ba. Gurnanin yaci gaba da karuwa har ya gauraye fadar gaba Daya. Sai ga wani jibgegen dodo irin wadannan Amma girmansa ya ninka nasu sau goma. Baya iya ganin komai Dake wajen sai ya sunkuyo da Kansa Kasa. Yayinda Gimbiya sima da Qaddaru suka yi arba da sai suka razana ainun. Dodon ya kyalkyale da dariya wacce tasa suka Kara hargitsewa. Dodon yayo kansu da baya, Nan fa sima ta fara kokarin ceton kansu da karfin tsafi. Domin tsafin yaki yayi tasiri akan dodannin Nan. Kai tsaye dodannin sukayi caa akan sima da Qaddaru don su yagalgala su. Ba zato sai akaji wani ihu ya ratso cikin fadar da gudu.
08112778656 ( Whatsapp )
Najibullah Muhammad ✍️♥️
Dodannin suka bar su sima suka waigo baya sai sukayi arba da JAFARU. Koda sukaga wannan 'yar Karamar Halitta ya nufo su a guje sai gaba dayansu suka juyo Kansa. Sai suka ruga gareshi tamkar an Bude garken shanu. Yayinda JAFARU yaga wadannan dodanni sunyi caa akansa sai ya razana ya juya da baya ya Kara runtumawa da gudu. Gudu yake iya karfinsa don ya fice daga gidan, Amma sai yaga kamar a waje daya yake. Ala'marin da ya Kara razana kenan, Kuma da zarar ya waiga baya sai yaga tsakaninsa da dodannin nan Bai wuce kamu biyu ba. A koyaushe dayansu na iya cafko shi, Karar sawayensu da gurnaninsu ya addabeshi. Ba zato sai JAFARU yaji an danko rigarsa ta baya anyi sama da shi. Da yake Yana maƙale da kundin tsatsuba a hammatarsa. Sai ya juyo cikin zafin nama yayi nuni da kundin tsatsuba yayi nuni ga wadannan dodanni. Bisa mamaki sai yaga wani haske ya fito daga cikin KUNDIN TSATSUBA ya buge su. Nan take suka rinka kamawa da wuta suna kumbura suna farfashewa tamkar mushen da yakai kwana da kwanaki ba a binne ba. Nan fa na baya-baya suka juya a guje don kada wannan haske ya riske su. Koda ganin haka sai JAFARU ya tasa su a guje yayita Karar da su da wannan haske. Shi kanshi Shugaban nasu sai da ya take da kafarsa Yana Neman maboya. Amma wannan haske Bai bari ya kubuta ba, dukkaninsu sai da suka zamo gawa dayansu Bai kubuta ba. Bayan JAFARU ya gama da wadannan dodanni sai ya sake duban kundin tsatsuba dakyau ya rungume sa a kirjinsa, cikin tsananin farin ciki yace a ransa Ashema ni Ina tare da maganin mugaye ban sani ba? Yana gama fadin haka ne ya daga Kai ya dubi inda Gimbiya sima da Qaddaru ke daure. Kawai sai ya ruga garesu ya fara kokarin kwance igiyar da aka daure sima da ita. Nan fa Abu ya gagara domin bashi da karfin da zai kwance murtukekiyar igiyar, JAFARU ya tsaya ya duba kowace kusurwa Dake wajen yaga babu wani makami da zai iya Amfani da shi ya Yanke igiyar. Kawai sai yayi nuni da igiyar ga KUNDIN TSATSUBA take wani Jan siririn haske ya fito ya tsittsinka igiyoyin sima ta fado Kasa sannan ya sake nuna igiyar da ta daure Qaddaru itama ta tsittsinke. Gimbiya sima na fadowa Kasa suka dubi juna ita da JAFARU, Koda yaga tsananin kyawunta sai ya rude idanunsa suka Kafe ko kiftawa bayayi bakinsa ya kulle. Har sai da ta dafa kafadarsa tace dakyau JAFARU Bin RUZYAL lallai Kam ka ceci rayuwata bazan manta dakai ba. Cikin tsananin mamaki JAFARU yace wacece ke? Ya akayi kika Sanni, Kuma menene dalilin zuwanki Nan? Gimbiya sima tayi murmushi ta ce ni ce Gimbiya sima Mai mulkin Kasar LAHARIM. Na sanka ne ta hanyar ganinka a cikin allon tsafin Boka SULBAINI. Dangane da abinda ya kawo ni nan Kuma, bazan iya baka Amsa ba a halin yanxu sai dai nan gaba idan damar hakan ta samu. Kafin JAFARU ya Kara cewa wani Abu tuni sima ta dafa Qaddaru Wanda ke kwance a Kasa sun bace gaba Daya. JAFARU yayita dube -dube Amma ko duriyarsu Bai gani ba. Ala'marin da ya Kara bashi mamaki kenan. Kawai sai ya fice daga gidan ya koma inda ya baro YALISA da su Aljani NARGAS. Da zuwa ya dubi YALISA yace tashi mu tafi, ko gardama batayi ba ta dane bayan GULZUM Shima haka. GULZUM yayi sama da sh, NARGAS na take masu baya. Abinda Basu sani ba shi ne Aljani DURFAS na nan biye dasu dauke da su Gimbiya sima da Qaddaru wadanda suka kusan rasa rayukansu a birnin dodanni. Tafiya taci gaba ya zama ba a Kara yada zango ba sai bayan kwana hudu sannan YALISA ta bukaci da a sauko Kasa a huta. Koda Jin haka sai JAFARU ya bushe da dariya yace Ina zaton Zaki iya hakuri har cikon kwanaki Tara don Kinsan jiya da Shekaranjiya Aljani NARGAS ne ya dauke mu gaba Daya na tabbatar yanxu Muna daf da shiga jejin KALKIM. YALISA tayi murmushi ta ce Amma dai ka sani cewa nayi karfin hali tunda na jure zaman kwana hudu akan wannan Aljanin Wanda ko'ina a jikinsa tauri ne kamar ice.
Inba don ma mun Sha magunguna ba da tunin mun kamu da mugun ciwon basir. Koda Jin haka sai Aljani DURFAS da GULZUM suka bushe da dariya, shi koNARGAS sai zuciyarsa tayi baki-kirin yace a ransa, kuyi min jafa'i son ranku. Da Sannu zan kuntata maku abun bakin cikin da har abada bazaku taba manta dashi ba. Ni nasan wahalar banza zakusha. Kura da Shan bugu gardi da kwashe kudi.
Gaba Daya wannan hira ta wakana ne yayinda suke kokarin saukowa Kasa. Suna dira bisa turba sai ta sauka daga Kan Aljani GULZUM ta dubi JAFARU ta ce ni zan Dan Mike Kafa sai na dawo. Cikin hanzari shima JAFARU ya ce dakata YALISA bari nazo nayi maki rakiya.
Koda Jin haka sai ta waigo ta dube shi cikin mamaki a lokacin da tuni ya iso gabanta. A wancan Karo da muka yada zango Kai kadai ka tafi yawon Mike Kafa banyi maka rakiya ba, saboda me yanxu Kai zaka yimin rakiya? JAFARU yace saboda a wancan lokacin Nima da kyar na kwaci rayuwata. Ina tsoron kada abinda ya faru gareni kema ya sameki. Ashe wani Abu ya sameka Amma baka bani labari ba? Haka ne Kinsan komai sai da hali, to halin hakan ne ban samu ba. Amma yanxu muje gaba zan sanar dake abubuwan Al'ajabin da na gani da Kuma hadarin da na shiga. Batare da wata gardama ba YALISA ta amince suka juya suka nufi cikin jejin. Inda suka bar Aljani GULZUM da Aljani NARGAS su ma suka Bude nasu shafin firar. NARGAS ya fara da cewa Kai Amma fa aikin da ke gabanmu ba karami bane. Yanzu fa Kaga gaba dayanmu ba lallai bane mu tsira da rayukanmu yayinda muka shiga jejin KALKIM. Kafin mu samu nasarar dauko takobin SARJUS sai munsha bakar wahala daga nan Kuma sai mu wuce fadar Sarki LU'UMANU mu shiga kurkukunsa dake karkashin Kasa mu sato Aljani MARKAHUSSABUS. Ko ka San cewa bakaken Aljanun da ke gadin wannan kurkukun duk duniya babu wasu Aljanu masu karfi da taurin Kai kamar su? Nikam Banga hanyar da zamubi ba mu kubuta daga sharrinsu. Yayinda Aljani GULZUM yaji wannan bayani sai yayi ajiyar zuciya ya ce, a Gaskiya mu Aljanu girmanmu da karfin mu duk ya zamo na banza. Tunda gashi har kullum bayi muke da bil'adama. Ka dubi duk irin hadurran da muke shiga don kawai mu biya masu bukatunsu Wanda a Koda yaushe zamu iya rasa rayuwarmu. Amma daga karshe sakamakon mu baya wuce a shayar damu jini. Na sha tunanin hanyar da zan bi na iya sarrafa Bokayen duniya ya zama