ransa "A
gaškiya babu abinda ya fi yara dadi ina ma nine da
wadannan yaran ai da duk inda zani muna tare da su,
lallai ma na yarda da rahama ne".
Yana komowa gida yana so ya yi ma Sakina zancen
yaran da ya gani suka burge shi, yana tsoro kar ta tada
balli ta ce ita ma haihuwar take so, ashe bai sani ba ita ta
gano a wani wurin sun burgeta tana so ta sanar masa,
yana nan zaune sai ta ce "Jamil ka ga kuwa 'yan biyun
Yaya Sa'id?" Ya ce "Ina zan gansu?" Ta ce "Ai suna nan
sun yi bul-6ul kamar ba 'yan biyu ba, wallahi gwanin ban
sha'awa". Ya yi murmushi kawai don ma ya kawar da
106
Kwadayı bar ana Aа Abdullalu Sharada
zancen sai ya ce "Wai yaushe kıka ce ana sa ranar
kanwarki Ni'ima ne?" Ta ee "Sat jibi". Ya ce "To Allah
ya kaımu jıbın"
Kwance yake yana ta faman tunani a ransa yana
cewa shi yanzu ina zai sami da, ga shi shi kadai ne wurin
mahaifansa ba shi da wa ba shi da kani bare in sun haihu
ya dauki 'ya'yansu, ga shi su kuma ba kara samun da zai
yi ba, yau ya zai yi da ransa A gaskiya ya yi kuskure babba da ya lalata kwayayen haihuwarsa, ai da ace ya
san haka ne gara ya hakura yanzu shi ya zai ya sami da? Ga shi ya yiwa kansa. Wannan tunani shi ne yake
damunsa a kowane lokaci, yana cikinsa da zarar ya ga
yara ko kuma iyaye da 'ya'yansu ana ta raha sai ya dinga jin shaukin abin. A takaice dai tsananin son da ya kamashi ya yin da kuma tsananin nadama ta mamaye shi
na abinda ya aikata.
"Jamil ya kamata ace munje an duba lafiyarmu domin yau shekara biyu kenan da aurenmu babu ko
fatan wata". Kawai ya ji saukar muryar matar tashi a
dodon kunnensa, ya dube ta "To maye kuma na wannan
maganar ana zaune lafiya?" Inji Jamilu, yayin da ya hantaro mata "To wai ma har yaushe aka yi auran da zaki
damu sai an wani haihu? Na ga ana samun shekara biyar
da aure babu haihu ba sai daga baya, to ni ba na son irin
wannan, ai wannan ma rashin godiyar Allah ne da nuna
gazawa akan hakuri".
Ta ce "To shikenan ka yi hakuri in ka ji haushi, ni
bana fada ne don ranka ya baci ba". Ya ce "Ai ke ce kika
ban haushi, kar ki kara yi min irin wannan maganar". Та
ce "To na ji insha Allahu ba za a kara ba".
Tun daga wannan rana Sakina bata kara cewa
107
Kwadayı harijanal- Auna Abdullahu Sharada
komai ba, to amma fa duk yadda Sakina ta ke son ta
haihu ba kamar Jamil ba, ba ya so ne ta san matsalarsa
domin in ta sani zata iya guje masa kamar sauran matan
shi ne ya ke mata wannan kandagarkin.
A zaune ya ke bisa gadonsa yayin da ya yaye
tattausan bargonsa ya maida shi rabin jikinsa ya yi
tagumi yana tunanin halin da ya ke ciki, wannan ba shi
ne karo na farko ba da ya fara wannan zaman tunanin ba,
wato ya tashi cikin talatainin dare ya yi zaune yana sakar
zuci ba, ya saka wannan ya kwance ya saka wancan ya
kwance, yana nan zaune yana tunani ya dubi Sakina
wacce ta ke kwance tana sharar bacci ya dai zuba mata
ido na 'yan muntuna, sannan ya kauda kai ya ce
"Shirman banza har da cewa Jamilu muje likita ya duba
mu". Ya kwaikwayi maganar ta cikin gatse sannan ya се
"Kin damu da son haihuwa, har kya sami idon bacci? Ni
da na damu ba gani a zaune ina tunanin mafita ba?" Ya
yi tsaki yayin da ya komo cikin tunaninsa da har kusan
asuba bai hango mafita ba don haka ya kishingida domin
ya d'an rurruma kafin ayi assalatu.
Tunanin bacin rai, damuwa, rashin bacci, zancen
zuci, babu wanda Jamil baya yi akan matsalar da take
addabarsa wacce kuma shi yasa ya tada hankalinsa, ganin
duk kudinsa ya kasa magancewa kanshi matsalar da ke
takura shi, kuma neman rabuwa da ita, abin ya gagara ga
shi yanzu ko abinci ba ya iya ci sosai tun ya nai a boye
har Sakina ta sani, amma bata fahimci me yake damunsa
ba in ma ta tambaye shi sai ya ce mata ba komai, a yanzu
haka suke ita ma kuma ta damu da halin da yake ciki,
domi sau da yawa in ta ganshi a irin wannan halin sai ta
yi ta kuka don a zatonta ko wani abu ne yake shirin
108
Kwadayı barijana'- Amına Abdullahı Sharada
zancen sai ya ce "Wai yaushe kıka ce ana sa ranar
kanwarki Ni'ima ne?" Ta ce "Sar jıbi". Ya ce "To Allah
ya kaımu jıbin".
Kwance yake yana ta ſaman tunani a ransa yana
cewa shi yanzu ina zai sami da, ga shi shi kadai ne wurin
mahaifansa ba shi da wa ba shi da kani bare in sun haihu
ya dauki 'ya'yansu, ga shi su kuma ba kara samun da zai
yi ba, yau ya zai yi da ransa? A gaskiya ya yi kuskure
babba da ya lalata kwayayen haihuwarsa, ai da ace ya
san haka ne gara ya hakura yanzu shi ya zai ya sami da?
Ga shi ya yiwa kansa. Wannan tunani shi ne yake
damunsa a kowane lokaci, yana cikinsa da zarar ya ga
yara ko kuma iyaye da 'ya'yansu ana ta raha sai ya dinga
jin shaukin abin. A takaice dai tsananin son da ya kamashi ya yin da kuma tsananin nadama ta mamaye shi
na abinda ya aikata.
"Jamil ya kamata ace munje an duba lafiyarmu
domin yau shekara biyu kenan da aurenmu babu ko
batan wata". Kawai ya ji saukar muryar matar tashi а
dodon kunnensa, ya dube ta "To maye kuma na wannan
maganar ana zaune lafiya?" Inji Jamilu, yayin da ya
hantaro mata "To wai ma har yaushe aka yi auran da zaki
damu sai an wani haihu? Na ga ana samun shekara biyar
da aure babu haihu ba sai daga baya, to ni ba na son irin
wannan, ai wannan ma rashin godiyar Allah ne da nuna
gazawa akan hakuri".
Ta ce "To shikenan ka yi hakuri in ka ji haushi, ni
bana faďa ne don ranka ya baci ba". Ya ce "Ai ke ce kika
ban haushi, kar ki kara yi min irin wannan maganar". Та
ce "To na ji insha Allahu ba za a kara ba".
Tun daga wannan rana Sakina bata kara cewa
107
Kwadayı barijana'- Amına Abdullahi Sharada
komai ba, to amma fa duk yadda Sakina ta ke son ta
haihu ba kamar Jamil ba, ba ya so ne ta san matsalarsa
domin in ta sani zata iya guje masa kamar sauran matan
shi ne ya ke mata wannan kandagarkin.
A zaune ya ke bisa gadonsa yayin da ya yaye
lattausan bargonsa ya maida shi rabin jikinsa ya yi
tagumi yana tunanin halin da ya ke ciki, wannan ba shi
ne karo na farko ba da ya fara wannan zaman tunanin ba,
wato ya tashi cikin talatainin dare ya yi zaune yana sakar
zuci ba, ya saka wannan ya kwance ya saka wancan ya
kwance, yana nan zaune yana tunani ya dubi Sakina
wacce ta ke kwance tana sharar bacci ya dai zuba mata
ido na 'yan muntuna, sannan ya kauda kai ya cе
"Shirman banza har da cewa Jamilu muje likita ya duba
mu". Ya kwaikwayi maganar ta cikin gatse sannan ya се
"Kin damu da son haihuwa, har kya sami idon bacci? Ni
da na damu ba gani a zaune ina tunanin mafita ba?" Ya
yi tsaki yayin da ya komo cikin tunaninsa da har kusan
asuba bai hango mafita ba don haka ya kishingida domin
ya dan rurruma kafin ayi assalatu.
Tunanin bacin rai, damuwa, rashin bacci, zancen
zuci, babu wanda Jamil baya yi akan matsalar da take
addabarsa wacce kuma shi yasa ya tada hankalinsa, ganin
duk kudinsa ya kasa magancewa kanshi matsalar da ke
takura shi, kuma neman rabuwa da ita, abin ya gagara ga
shi yanzu ko abinci ba ya iya ci sosai tun ya nai a boye
har Sakina ta sani, amma bata fahimci me yake damunsa
ba in ma ta tambaye shi sai ya ce mata ba komai, a yanzu
haka suke ita ma kuma ta damu da halin da yake ciki,
domi sau da yawa in ta ganshi a irin wannan halin sai ta
yi ta kuka don a zatonta ko wani abu ne yake shirin
108
faruwa.
Kwadayı barijana'- Amına Abdullalu Sharada
Tsaye ya ke ya rataye hannunsa a makarin bene ya
zubawa wata bishiya ido kirr, yana kallonta idonsa cike
da hawaye domin zafin tunani, Allah ya jarabce shi da
son da wannan zamu iya daukarsa a matsayin sakamako
ne dangane da abinda ya aikata a baya. Ya fi minti biyar
bai dauke ido daga kan bishiyar da yake kallo ba, sai can
kamar wanda aka mintsila ko aka zubawa bulala ya
zabura cikin gaggawa gami da cewa a fili "Hakika na bar
Halima da ciki a wancan lokacin ina cikin ina Hliman ina
take? Mc ta haifa?" Cikin sauri ya sauko daga saman
gami da shiga matarsa Sakina na cewa "Jamilu ina zuwa
haka?" Ya daga mata hannu "Ina zuwa".
Har ya kai unguwar su Halima yana kiyasta abinda
zai ce da Yalwa in ya je domin hakika Yalwa ba kanwar
lasa ba ce, ya san bala'inta sarai bare ga yadda suka rabu.
Yana shiga unguwar sai ya yi tsai yana tunanin layin da
suke, domin rabonsa da garin yau kimanin shekara goma
sha takwas da watanni sai ya ga duk wurin ya sauya
masa, don haka ya yanke shawarar ya yi tambaya, nan ya
fara tambayar jama'a a gefen hanya har ya sami wadansu
suka ce sun san gidan Yalwa suk sa shi a hanya. Ya na
zuwa da bishiyar mangwaro a kofar gidan ya gane ya
tsaya ya fito ya jingina da motarsa, yana tunanin yadda
zai tunkari Yalwa, domin ance tana nan bata mutu ba har
ma Babansu wato Malam Usman yana nan da ransa.
Wani tunani ne ya fado masa ai ko akwai wata
mata makotansu mai suna Gwaggo Hanne, ina ma ace
tana nan da a gunta zai fi samun cikakken bayani, can ya
dosa domin a gane gidan, saboda katangarsu guda, har
yau kuwa haka ne.
109
Kwadayı barijana'- Amına Abdullahı Sharada
Yana zuwa ya sa aka yi masa sallama da ita, jim
kadan ta lito tana dogara sanda abın ya bashi mamaki ya
ce "Lallai tsufa labari, ashe har ta tsufa haka? Koda yake
ai abin ba na yau ba ne". Bayan sun gaisa ne Gwaggo
hanne ta ce "Samari ban fishshenka ba, daga ina?" Ya ce
"Gwaggo na san ba zaki gane ni ba, ni ne Jamilu". Ta ce
"Jamilu? Wanne Jamilun fa?" Ya yi murmushí ya ce
"Saurayin Haliman gidansu Yalwa?" Ta ce "Af, to to
Jamilu kai ne haka?" "Yau wallahi ni ne Gwaggo". Та се
"Allah sarki Jamilu ka je ka buya shiru ba amo ba
labari?"
Ya yi murmushi ya ce "Gwaggo lamarin ne sai
hankali dama yanzun ma zuwa na yi in gaishe ku in
wuce". Ta ce "Allah sarki ince ko dai kun gaisa da
Yalwan, hata jin dadin jikin ma tun kwanaki". Ya ce "A'a
ban shiga ba, ai gani nake yi kamar in na shiga zata kore
ni". Ta yi dariya ta ce "Haba sai ka ce wani yaro?"
Shi ma dariyar ya yi ya sa hannu aljihu ya ciro kudi
masu yawa ya bata, ta yi ta godiya sannan ya ce "Wai ni
Gwaggo ina Halima kuwa?" Tana jin wannan tambayar
sai ta tabe masa baki "Halima ta na can ta auri wani mai
kudi sai faman sakar musu kudi yake, suna washe wa".
Ya ce "Wai ni ko ya ta yi da cikin nan na jikinta? ta
haihu kuwa ko sun zubar da shi'?" Та се "Таa haihu wai ya
mace......" Cikin doki ya katse mata maganar da take yi
"Ina 'yar?" Ta ce "Ta yadda ita". "Ta yar?" Ya bukata a
dan razane, "Eh, wai tana haihuwa sai Yalwa ta ce ta
yadda 'yar ina ga ma a kwararo ta haife ta ta yar". nan da
nan kamanninsa suka sauya "Ina Haliman ta ke auren?"
"Ka ji ka ko? Ni dai kar ka je ka ce ni na haďa ka da ita,
na gaya maka komai". Ya ce "Haba (Gwaggo ai babu
110
a
Kwadayı barı jana!- Amina Abdullahi Sharada
wanda ya san na zo bare a zargi wani abu". Ta ce "A to
koda an tambaye ka wa ya gaya maka kar ka be ni ce".
Ya ce "Ba ma wani mai tambayata, yanzu a ina ta ke
auren?" nan ta ke ta yi masa kwatance, ya gane sannan
suka yi sallama akan zai komo bayan kwana biyu. Bai ko
kalli gidan Yalwa ba domin ba nan dama ya yi niyyar
zuwa ba.
***
Y
au ce ranar sunan Sameera don haka jama'a
an taru makil ko ina mutanen jamus an
hallara baki dayansu, Saddik ya zama kato yana rarrafe
ko ina abinsa gwanin ban sha'awa ga su Žainab ma an zo
da su ibrahim yana ta doki zai ga matar da zai aura a fili, gidan su Alhaji usaini ya cika da baki har Baba Abu ma
ta zo a takaice dai an hallara sosai da ya ke Bashir kulle
gidan suka yi suka komo gidan Alhaji Usaini wai ayi
taron sunan anan don kar a bata musu gida shi yasa baki
dayan jama'ar suna gidan hatta harabar gidan ma jama'a
ce su kansu gidan su Bashir din wato gidan Hajiya Rukayya nan suka dungumo.
Ana cikin tsaka da suna su Halima na ta faman
kawowa da komowa ana harabar gidan ana rabon abinci
don haka kowa ya nutsu sai cin abinci ake ga abin cin
nan iri-iri sai wanda ranka ya zaba, kuma kome ka ce sai
an saki maka rabin kazar nan soyayya da tsire mai dadin
gaske, ga lemuka nan iri-iri birjik sai wanda ka zaba, ban
da na bature na kwali 'yan waje ga na gida nan kuma
wanda aka hada da kai kamar su lemon kwakwa da na
abarba da dai sauransu wadanda aka dauko masu yi
111
kwaday han jana'- Amına Ahdullaly Sharаdи
musamman dama an saha duk sa'anın su sai an barar da
kudi shi yasa ma in har sha'anin su ya zo zaka ga jama'a
kamar kara turo su aka yi ga kuma kayan rabo nan da za
a raba a jibge kala-kala masu rabo na jira a gama sannan
a hau rabo
Wata bakar motace ta tsaya jeep mai dubun gilasai
yayın da sauran 'yan suna su kai mata kallo daya sai
kowa ya dauke kansa domin a zatonsu wadansu 'yan
sunan ne suka zo sai ga wani farin mutum kyakkyawa ya
fito daga motar yana sanye da manyan kaya na alfarma,
sai kamshi ke tashi a jikinsa, yayın da ya fito sai ya sami
wanı yaro wanda yana daya daga cıkin yaran da aka zo
da su sannan ya kkra shi yaro ya ıso da gudu ya durkusa
ya ce "Gani". Ya ce masa "Ko ka san wata Halima anan
gidan?" Yaron ya ce "Aunty halima?" Ya ce "Eh". Ya ce
"Na santa ka ganta can ma waccen mai blue din atamfar
wacce ta dauko plate din can ita ce". Ya ce "Yauwa to ka
ce ta zo ta yi bako". Yaro ya ruga da gudu yana kiran
"Aunty Halima wai kizo kinyi bako" Cıkin tsananin
mamaki ta waigo ta kalli yaron tana nanata kalmar bako
a bakinta, ta ce da shi "Wanne inin bako kuma?" Ya ce
"Wani farin mutum ne". Ya ce "Wai ki zo kin ganshi
can". Ya nuna inda mutumın ya ke, Ilalıma bata shaida
ko wayc ba, sai ga lHajiya Jamila ta zo ta ce "Wa ye
kuma yake kiranki?" Ta ce "Wallahi ban san ko waye
ba". Ta ce "To muje mana mu ganı?" Halima ta ce "To".
Domin ta ji kwarin zuwa tunda ga Hajiya Jamila, sunje
tare ba a ce da alhaji Usaini wanı ya zo ya yi sallama da
ita taje ba, don haka sai suka tali babu wanda hankalinsa
ya ke kansu kowa nata hidimar gabansa.
Suna isa wurin mai kıran Halıma ta tsaya cak tana
112
Kwadayı barıjana'- Amina Abdullahı Sharada
dafe da kirji cikin tsananin kaduwa ta ce masa "JAMILU
me ya kawo ka gidana kuma bayan ka san cewa ina da
aure?" Murmushi ya yi ya ce "Haba lalima ai kya bari
mu gaisa tukunna kuma ai na san kina da aure zuwa na yi
ki bani 'ya ta da kika haifa!" Wannan magana ta zo wa
Halima tamkar harbin bindiga domin saboda razana sai
da ta yi baya taga-taga, Hajiya jamila ce at taro ta tana
cewa "Wacce 'yar zaki ba shi kuma? ko Zainab?" Da
kyar Halima ta girgiza kai ta ce "Ba ita ba ce". Sannan ta
dubi Jamilu ta ce "Haba jamilu wannan wacce irin
magana ce kuma? ko so kake ka tona min asiri shi yasa
ka zo?" Ya ce "No ba nufina ke nan ba, Halima kuma
tonon asiri ma ai ke zaki tonawa kanki domin wannan
matar da kuka zo tare ai tare an ganku ban san
matsayinta a wurinki ba shi yasa". Ta share hawayen da
ya gangaro mata ba zato ta ce "Ni dai don Allah ka tafi
ka bani wuri, kar Alhaji ya zo ya same ka a nan". Ya ce
wanne irin in tafi bayan ga abinda na ce miki?" Ta се "Ai
kai kace baka so ni yanzu a ina an samo ta?" Ya ce "to
yanzu ina so don haka na baki nan da kwana uku ku
gama taron zan komo ku bani 'ya ta don naji ance mace
kika haifa". Cikin tsananin fargaa ta dubi Hajiya Jamila,
ita kuma Hajiya jamilar ta tabe baki ta juya abinta ta
shiga cikin 'yan suna tana ta faman kwazawa jama'a
"Kinga wannan mutumin wai wurin Halima ya zo karbar
'yar sa, ko dai dama duk 'ya'yan da halima ta ke haifa
bana Alhaji ba ne? To gashi dai ya zo ta bashi 'yar sa duk
ta rude ta na cewa wai wani kar ya tona mata asiri".
Wasu suka ce "To zancen yaushe ai asiri ya tonu". Ta ce
"Ku gane min hanya wai makaho ya so tsegumi". Nan da
nan sai zance ya baza gida kaf! 'Yan sunan da baki da
113
Kwadayı barijana- Amina Abdullalu Sharada
'yan gıda babu wanda bai ji wannan magana ba, sai
mazan da basu nan kawai.
Cikin sanyin jiki da kidimewa Halima ta shige sai
la ga anai mata wani irin kallo kamar wadda ta yi
gagarumin abu, sai ta wuce cikin gida ta shige dakinta ta
rufe kofa ta afka kan agdo tana ta faman kuka, ta ji a
rayuwarta dama ta mutu ta huta da wannan bakin cikin
ashe Baba Abu bata tafi ba, taan can tana jin yadda gidan
sunan ya dauki dumin zancen kowa na fadin albarkacin
bakinsa sai ta higa dakin Haliman ta kwankwasa can sai
ta taso ta bude, Baba Abu ta tambaye ta "Me yake
faruwa ne?" Ta sanar mata cewa "Jamilu ne ya zo wai in
bašhi 'yar sa". ta ce "Wa ye kuma Jamilu?" Ta ce
"Wannan wanda..." Sai ta kasa fada, Baba Abu ta ce
"Kar dai wanda ya yi miki cikin nan?" Ta gyada kai
cikin kuka. Baba Abu ta yi salati ta ce "Wannan zuwa ya
yi ya tona miki asiri ba zuwa ya yi domin 'yar shi ba, shi
da ya ce ba ya so?" Ta ce "To ai ya tona min domin dubu
wadannan taron al'umma yadda suka yo caa akan
maganar kowa na fadin albarkacin bakinsa". Baba Abu ta
ce "to yanzu ya za'ayi?" Ta ce "Z.uwan Alhaji zan jira inji
irin hukuncin da zai yanke domin ni na san zamana kuma
ya zo karshe a gidan nan don da kyar za a fadi masa iya
abinda aka yi sai an yi kari, ta yadda zai ji ya tsane ni!"
Ta ce "ki kwantar da hankalinki zama da rashi na Allah
ne...." Halima ta katse Baba Abu "Baba kina ganin ko na
ci gaba da zama anan zan sami daraja irin ta da?" Ta cе
"A gaskiya babu, kai amma wannan yaron ya yi mana
rashin mutunci, to Allah dai ya saka miki Halima".
Dare ya yi duk 'yan suna an fashe kowa ya tafi da
wannan magana a baki, haka ma mai jego mijinta ya zo
114
Kwadayı barı jana'- Amına Abdullahı Sharada
ya dauke matars da bind aka tara musu na suna, sun tafi
Baba Abu ma sai magruba ta tafi, saboda jimamin abin
nan ta yi ta faman kwantar mata da hankali domin
hankalın Halima ya yi matukar tashi, can kuma gidan
Sameera bayan sun koma sai Sameera ta ke tseguntawa
Bashir abinda ya faru yau, ta ce "Yaya bashir ka san me
ya faru?"Ya сс "A'а". Та сe "Wai wani ne yau ya zo ya
ce wai Aunty Halima ta bashi 'yar sa". Bashir ya kara
gyara zama "wacce irin 'ya kuma zata bashi?" "Oho wasu
dai suna ta tsegumin wai ko Zainab ba 'yar Abbansu
Maryam ba ce". Ya ce "kai haba ai kowa ya ga Zainab ya
ga Alhaji har duk sauran 'ya'yan ta ma". Ta ce "A to
maye na rudewar da ta ganshi in ta san sharri ya ke
mara?" Ya ce "in ma dai akwai wani abu daban to ba
maganarsu Zainab ba ce sai dai in akwai abinda ya hada
su can daban". Ta ce "Ka san wani abu?" Ya ce "A'a". Та
ce "wallahi mutumin suna bala'in kaam da Saddik dan
gidan Maryam". Ya yi dariya "Au nan kuma kika
koma?" Ta ce "wallahi bani kadai ba kowa ma ya fada".
Ya ce "Da Allah ki sake wata hirar daban ni bama na son
jin wannan hirar". Ta ja baki ta tsuke kawai.
Maryam na tafa hannu a dakinta na gidansu Hajiya
Jamila ta dubi mijin yayin da ya ke ta faman yiwa Saddik
wasa akan gado ta ce "Faruk ka san abinda ya faru?" Bai
ji ba domin suna ta kyalkyalar dariya da Saddik ta dan
daka masa duka ya waiwayo yana dariya, ta ce "kai ina
son in gaya ma zance kana wasa da da?" Ya ce "Me aka
yi?" ta ce "Yau wani mutum ne ya zo wai Aunty Halima
ta bashi 'yarsa". Ya ce "Wacce kuma 'ya? Bashi da
hankali ne?" Ta ce "wanne irin bashi da hankali?
Mutumin lafiyayye ras da shi". Ya ce "to ya akai ya san
115
Kwadayı barıjana!- Amına Abdullahı Sharada
ta? Ko dai don 4.1.9 ne?" Ta ce "Anya kuwa? Ai ita ma
ta san shi". Ya ce "To kila mijinta ne na baya, ba ance ta
taba yin aure ba?" Ta ce "Au ch haka ne kuwa, amma
baka ji yadda gidan sunan nan ya dauka ba, wai kila ma
duk 'ya'yan Abba ba nasa ba ne, na wancan mutumin ne,
wallahi sai da tausayin Aunty ya sani kuka domin kana
ganinta dole ka tausaya mata". Ya ce "Ina ma mun same
shi mu ci abu ta kazar ubansa don rainin hankali zai zo
har gidan mijinta ya ce wani ta bashi 'yar sa?" Та се
"wallahi kuwa, wannan rainin hankali ne". Faruk wallahi
mutumin nan ya ban mamaki da na leka sai naga suna
kama da Saddik". Ya ce "Wanne Saddik kuma?" Та се
"Saddik dinmu". Ya ce "Kin faye shirme da yawa".
Hajiya Jamila ce zaune a tsakiyar su Hajiya Husna
da IHajiya Rukayya da 'yan tsirarun kawayenta, ana ta
hira, Hajiya Jamila ce ke ta zuba zance ai kanta ake
jiyowa, "Yo in ban da ma Alhaji waye zai yi aure bai yi
wani bincike ba? Wallahi Hajiya Husna kannan Halima
duk 'yan daba ne, ai ita Hajiya Rukayya munej da ita ta
gani. Halima ma bata sani ba, na ja ta muka tafi don ta
ganewa idonta, duk sanda kaje gidan nan sai ka tarar da
wani abin husuma". Hajiya Husna wato mahaifiyarsu
Faruk kenan ta ce "Amman ko in haka ne Halima ta bata
wayonta ina ganinta kamar me hankali ashe wayon banza
ne da ita?"
"Uhum! In na gaya muku ai sai ku ga kamar sharri
nake mata, tun da kishiya ta ce". Hajiya Rukayya ta ce
"Ai ni dama tuni naji labarinta har cikin shege ta taba yi
ko zubar wa aka yi ne oho? Shi ne dalilin da ta koma
gidan wannan kanwar uwar tata ta Gwale". Hajiya Jamila
ta ce "Ammashi ne ko ki sanar min?" Ta ce "to ai in kaji
116
Kwadayı harı jana'- Anına Abdullahu Sharada
irin wannan baka lada lajiya Jamila kın san dai irin son
da Alhajı yake mata in ya ji ba lallai ne ya yarda ba". Tа
сc "Hakika ba ya son laifin ta bara ki ga yanzun ma ba
lallai ne ya yarda ba, in ma ya tan yaushe za'a taushe
bakinsa da malamai". Inji Hajiya Jamila "Ai wannan son
da yake mata bana Allah ba ne". Nan dai suka yi ta
faman hirar har kusan goma na dare, sannan Alhaji
Usainı ya komo, Hajiya Jamila ta tafi dakinsa domin ita
ce da girki a wannan ranar.
Kusan sha biyun dare kowa ya yi bacci, amma
Halima na kwance idonta biyu duk ya kumbura, saboda
kuka ga yaranta nan a kwance suna ta bacci kusan ukun
ita kuma ta hada kai da gwiwa sai ta ji an turo kofa a
hankali an shigo. Cikin sauri ta dago kai ta ga Alhaji
Usaini ya shigo, daga shi sai singileti da gajeran wando
ya sami gefen gadon ya zauna yayin da ita kuma hantar
cikinta ta ci gaba da kadawa domin razanar ganinsa da
tayi ta fara rawar sanyi dama kuma zazzabi ne a jikinta,
saboda kukan da ta sha. "Hajiya Sadiya ance yau kinyi
bako ko?" Nan take gabanta ya kara faduwa ta rasa ya
ma zata amsa masa wannan tambayar, sai hawaye kawai
ke zuba, ya ce "Da ke nake fa?" Ta dago kai ta kalle shi
ta ce cikin shesshekar kuka "I na yi".
"To me ya zo yi?"
"Wai cewa ya yi in bashi 'yarshi?" Saı ta karashe
zancen cikin kuka, ya ce "Wacce 'ya ya ke da ita a
wajenki?" Ta ce "Ai ba yanzu ba ne zancen ya jima". Ya
ce "Tun yaushe ne?" Ta ce "tun
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 12