Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 12
ya hadu. Falon shi ya sa su a tsakiya 6angaren, shigo sai ka ratsa falon sannan za ka kowane a girke da kuma anan falo daga gefe dinning table ya ke kujerunsa abin dai gwanin ban sha'awa. cewa dai Kowa ya fashe an bar Amarya da Angonta, duk da ana Angwanci, Angon bai shigo ba, ya na can tare da abokansa dakin Amaryarsa, kusan sau goma suka taho rako Ango domin garin ya fara nuna alamun hadari zai taso, ana ta faman walkiya da ya ke damuna ne. bakinsa, Sunyi anyiwa raha sosai da sosai kowa ya fadi albarkacin zaman lafiya, daga Ango da Amarya addu'a ta neman nan kowa ya kama gabansa saboda hadarin da ya taso, shi kuma Bashir ya raka su ya rufo kofa ya komo, a lokacin nan Sameera ta na nan zaune, ban da fargaba ba abinda ta ke yi, don Bashir ba ya sonta aka yi wannan auren har kawo yau da aka gama biki bai ce ma ta kala ba yanzu ma da ya shigo fangarensa ya shige abinsa. Ta na jira ko zai fito, kusan awa biyu bai fito ba har ta fara bacciba ta san shi tuni ya yi baccinsa ba ma, 42 Kwadayı barı jana!- Auna Abdullahı Sharada bangaren dakinta ta tafi ita ma ta kwanta ba tare da ta rufe kofar da key ba, nan ta ke bacci ya yi awon gaba da ita, don ta gaji sosai. Kashe gari tunda wuri ta tashi, ta yi sallah, bayan ta idar ta fito falo, ta shiga kitchen don ta hada musu abin karyawa ba ta fito ba sai bakwai saura, ta same shi a falo ya na zaune ya kunnan kallo har kasa ta durkusa ta gaishe shi, amma ko kallon inda ta ke bai yi ba, cikin sanyin jiki ta shige dakinta, yayinda hawaye ya zubo ma ta, ta ce "Yau na shiga uku, ya zanyi? Bashir ba ya so na da gaske!" Fitowa ta kuma yi, ta shiga kitchen ta hada musu break fast ta kawo bisa dinning table ta shirya sannan ta komo ta durkusa ta ce ma sa "Yaya na gama shirya mana break ka zo muje mu karya". Ta na maganar ne gabanta na faduwa. Ko kallonta bai yi ba, nan ma sai ta koma gefe daya ta zauna, ta yi tagumi hannu biyu, jarida ma ya dauka ya na karatu abinsa, bai ko kalleta ba, can kuma sai ya ajiye jaridar ya haura takalmansa ya fice abinsa. Ta bishi da kallo har ya kule, wasu sabbin hawaye masu dumi suka zubo ma ta. Nan ta ke tunanin iyayenta da 'yan uwanta ya fado ma ta a rai, duk da cewa suna nan basu koma ba, amma ai gobe za su tafi, ya za ta yi in sun ta fi? Gashi wanda ta ke so din ta zauna domin shi ba ya kaunarta? Hawaye ya sake zubo ma ta a fuska, ta na cikin gogewa, sai gashi ya shigo ya na dauke da wata kula, ashe abin karyawa ya je ya sayo a wani restaurant da ke nan ku sa da su, nan ma ran ta ya sosu, ta hana idonta bacci ta yi don ta burge shi amma ya je ya sayo a wani wuri, kuma abinda ya sayo din ma bai kai dadin 43 Kwadayi barijana'- Auna Abdullahu Sharada nata da tsafta ba. Don ita ko abinda ta zuba musu abin karyawar ma abin sha'awa ne, ga wani ado da ta sshirya musu kun san turawa da adonta abinci, kamar daurawa za'ayi ba ci bа, tashi ta yi ta nufi inda aka girke musu kayan kallo ta ciro wani faifan sidi na audio wakar Ramla ta labbaika rasulullah ta sanya, wakar na tashi a hankali ta koma ta kwanta bayan ta rage rediyon ta na sauraron wakar. Zuciyarta cike da shaukin bege na manzon Allah (S.W.A), shi kuma ya na gama cin abinci ya yi waje abisa, ya bar kular a wurin. Tsam! Ta mike ta je ta duba, ashe ma har ya cinye, ta dauki kular ta wanke, sannan ta komo da ita ta ajiye ma sa can sai gashi ya zo dauka, ya na budawa ya ga an wanke, amma duk da haka bai yi magana ba ya ficce kawai abinsa. Murmushi ta yi ta ce "Duk lalacewar zuciyata na san mai kyautata ma ta". Ya na ta faman sauri ya shirya zai ficce ya fito da wankinsa daga daki, zai tafi da su ya kai wanki, ya zube a falo ya fice ya manta su don ya na ta sauri, kuma har ya ficce bai tuna cewar ya mance wankin ba, nan da nan ta kwaso bahunna ta zagaya can famfon baya ta dauki wankin da sabulu, ta wanek ma sa su tas. Set takwas ne ban da gajerun wanduna da best da kuma hankici kala biyar a cikin aljihunnan wandon ne ta sami takardu da 'yan tsirarin canji da dan abinda ba'a rasa ba, ta kwashe ta kai ma sa daki ta ajiye don ba ya nan, har wankin ya bushe bai dawo ba, ta kwaso ta zo ta zube ta fara guga gashi kuma kayan sun fi ta kal. Ta gama gugar ta ciro zani daga cikin zannuwanta Kwadayı barı jana'- Anuna Abdullahi Sharada ta nade gugar nan ta ajiye a inda ya ajiye kafin ya fi ta, sannan ta dora musu abinci duk da cewa ba ci zai yi ba, to amma dai in bai ci ba na sa rabon ta ke ci da daddare in ta abshi da daren ma ya ki ci. Bai dawo ba sai ku san takwas na dare, to ta na jin ya shigo ta mike ta nufi inda ya ke, ta yi masa sannu da zuwa, ko kallon inda ta ke bai yi ba, ya wuce inda ya ajiye wankinsa, don bai tuna ya mance ba sai da ya yi nisa sannan ya tuna ya bar wankinsa, to amma gobe ya kai. a Duk da ba haka ya so ba, ya fi son a wanke su yau din nan don akwai wata shadda da ya ke son sa ta gobe, ya na shirin dauka ya ga zanin mace an nade su, ya ware zanin ya ga kayanshi a wanke, a goge, a tsaftace, gashi an gaam shirya su kamar yadda ya kamata, layin gajerun wandunansa daban, layin hankicinsa daban, ga wani kamshi mai dadi ya na tashi, a jikin kayan, ashe turaranta ta fesa musu. Cikin sauri ya waiwaya inda ta ke, ya ga ashe ba ta wurin ma, sai zuwa can ya ga ta fito ta nufo inda ya ke, ta durkusa ta mika masa canjinsa da ta tsinta a aljihun wando, kuma ta abshi sauran takardun ta ce ma sa "Yaya da ina yi maka wanki ne na gansu a aljihun wandonka, shine na dauke na ajiye ma ka". Shiru kawai ya yi gami da mika hannu ta bashi, ya cire zanin da ta yi masa wankin ya ajiye, sannan ya shige dakinsa abinsa, ya rufe kofa ya barta anan a tsaye, dama ba ta sa ran zai kula ta ba, don haka sai ta juya abinta ta shige dakinta. 45 Vma am sane, duns Ahhilbahı Sharnda Amaday AnC une odullahı Shaada *** A Famarin su Maryam kuma, abin ba magana domin faruk ya shiga tsaka mai wuya game da Maryam, sam zama ya ki dadi, duk abinda ya kamata ya yi don a zauna laliya ya yi, amma bai samu nasarar shawo kanta ba. Gashı iyayensa sun dauki laifi sun fora mishi saboda sharrin da ta ke-masa, wai cutar ta ya ke, dukanta ya ke, kuma ya shiga neman mata, wannan sharri shi ya janyo wata matsala a wurin iyayensa domin sun yi fushi da shi sosai, su a ganınsu wulakanta matarsa ya ke, fargabarsu daya kar ta sanarwa iyayenta domin abin ba zai musu dadi ba, ga gari ba kusa ba, har ta kai yanzu daga Mum har Abba da sauran kannan Faruk wato Ibrahim da Zainab ba ya jin dadinsu, zaune ya ke a gidan kowa ya tsane shi, amma ita Maryam ko a jikinta, yadda abın ko ya fara, shi ne:- Lokacin da suka tafi bikin Samecra gida ya rage daga Faruk sai Maryam, to ga laifin Bashir zai auri kuma Kanwar Faruk zai aura sai ta kara hasala, ta kuma dora masa karan tsana shi kuma ganin su kadai ne a gidan sai ya zamana duk lokacin da ya bukace ta sai ya ida bukatarsa komai ihunta, hakan ne ya kara rura wutar Kiyayya a tsakaninsu, ya zamana ba ta ko son ta dube shi, bare ta saurare shi, gashi har yau ba ta jin dadin jıkinta ba, bayan sun dawo ne suka samu duk ta rame, suke tambayarta ko har yanzu jikin nata ne?" Ta сe "Ba komai, ita ba ta san abinda Faruk ya ke yi ba, sai ya dinga kawo mata gidan, ta yi masa magaan 46 hwadayı hanjana' Amuna Abdullalu Sharada ya yı ma ta duka" Ai jin abinda ta fada ya harzuka Zuciyar su Mum suka kira shı, ran Abba a bace suka yi masa lada sosar, to tunda nan sar Mum ta tambaye ta ko ya daına balinsa?" Sai ta ce "Bai daina ba". To fa nan suka kafa masa karan-tsana ko ya gaischsu ba sa amsawa, yayi-yayi lyayen su fahimta ba su fahimta ba, don haka sai kawai ya kyale su ya zuba musu ido kawai ya na kallonsu don shi ya san wannan duk hadin na Maryam ne ba wani ba. Yawan tunani da zancen zucin da sauran su su suka haddasawa Paruk shiga bacın rai da sauransu, har ya dinga jin babu dadi a 'ransa, a kullum shi ke nan yawan tunani da abin ya yi tsananı ma sai ya dinga jm rashin dadi a jikinsa, yau a lafiya, gobe babu, amma babu wanda ya san halin da ya ke cıki, sai shi daya, sannusannu har ciwo ya fara damunsa, tun ya na kokari akan wannan har ya zamana ba ya iya aıkin komai, yawan kwanciya da yawan tunani wannan lamari ya sa iyayensa sun hassala domin su na zaton ko halayya ya sauya. Yau ma ba inda ya je, don jikin nasa na matsa masa, ga ciwon kirji da ciwon kai duk ya bi ya rame, ya na nan a kwance sai ga Mama wato Mum ta shigo, ranta a bace ta sameshi akwance ta ce "Wai kai me ka ke nufi ne?" Cikın karlin hali ya taso ya ce "Me na yi kuma Mum?" Ta ce "Ban sani ba, ka ga in baka san yarinyar nan ka saketa kawai shi ya ti sauki". Y ace "Mum me ta ce kuma na yı ma ta?" Ta ce "ban sani ba, ai komai ka ke yi ma ta ka xani ba sai an fada ba, ka fi kowa sani"/ Ya ce "Mum wallahi ni ban san abinda na yiwa Maryam ba, kuma ina onta, ba zan iya rabuwa da ita ba....." 47 Amon Kwadayr harra A Arhillahı haraня "Kai tafi can marar mutuncı, yanzu da ka ganni ba? Ai wallahı ka banı mamaki, ban taba zaton zaka kunyata mu ba, kai fa ka ce ka na son yarınyar nan, amma daga baya ka zo ka ke wulakantata, wallahı muddın ba ka sake hali ba sai dai ka saketa don ba zaka zo ka kunyatamu ba abin zumunci". Shiru kawai ya yi ya na sauraronta, don ya rasa ta cewa, hankalinsa aa tashe, tuni ta ficce ta na ta faman fada shi ma sai ya tashi tsam ya nufi dakin Maryam, ya sameta zaune bisa gefen gado, shi ma ya shiga ta na ganinsa kawai ta mike da sauri cikin razana ta dauka ırın abinda ya saba yi mata ne ya kawo shi, wato ya bukaceta bisa dole. y1 Maryam bai kamata in ba kya sona ba ki dunga min sharri ba, don Annabi (S.A.W) Ya ce in zaka yi so ka yi shi domin Allahi, in zaka yi ki ma ka yi shi don Allah, to ke babu abinda ki ke yi don Allah, wai shin ke ba ki koyi da wannan hadisin? Ni na san ce wa bakya kaunata, to wai me ya sa zaki dinga hadani da iyayena? wai ke ba kya tsoron Allah ne?" Ya ci gaba da "Maryam ina so ki sani wannan wata daam ce kike da ita game da ni ina jiye miki kar ki yi sake damar ta wuce ki, shi wanda kike so din ya yi aure, kuma su na zamansu lafiya da matarsa, tuni ya ma manta ki amma ke kina nan ki na kwasar zunubi saboda shi, kuma wani abin haushin ma ko da ace mun rabu da ke aure ya haramta tsakaninku domin na ri ga ya na aureki shi kuma kin san dai auren kanwata ya ke, kina ganin wannan kwadon zai yiwu? Saboda haka ya kamata ki san nasihata me kike yi, ki bar bugun taki ga jaki, wannan shi ne ta karshe daga cikin dumbin nasihohin da nake 48 Kwadayı bari jana!-Amina Abdullahi Sharada yawan yi miki". Ya na gama wannan bayanin ya tashi ya ficce ya barta. Shiru kawai ta yi ta na tunani, jikinta a sanyaye ta ce "Lallai na yarda da maganarsa gaskiya ce, don ga shi tunda aka yi bikin Sameera da Bashir shiru zamansu, su na can su na shan shagalin amarcinsu, kai jama'a lallai na yarda namiji bashi da alkawari!" Faruk kam tunda ya yiwa Maryam wannan nasiha bai sake sauraranta ba, don shi mutum in ya dauki nasihar da akai masa ai ankance za'a gani, to babu abinda ya sauya shi ya sa ya ce har yau Allah bai kawo iyakar wahalar ba. Maryma ma ba lafiyar ce da ita ba, yau fari gobe tsumma, kuma ta Ki ta je asibiti in Mum ta ce ta zo akai ta sai ta ce ta warke, haka Mum za ta hakura ta kyale ta. Yau ma jikin ya tashi ta na falo kwance ta na lissafin yau kwanan Faruk biyu bai fito daga daki ba, ko dai ba ya nan ne? Don duk inda zashi ba ya fada ma ta. Ta na fito ya na nan ta na wannan tunani, Faruk ya hada hanya, duk ya rame ya kode. Ya na zuwa dai-dai inda ta ke amai ya kamashi, ina? Kafin ya yi wani yunkuri sai ya fito gami da tari, nan da nan ya fadi bakinsa a bude ya na kiran Maryam da kyar, ko kallon inda ya ke bata yi ba bare ta san halin da ya ke ciki, a maimakon haka ma sai ta mike za ta koma daki, ta daka masa harara, ai ko hararar da ta daka masa sai ta koma kallon abin mamaki, domin aman da ya ke yi aman jini ne. Cikin rudani ta yi saurin zuwa inda ya ke, shi kam a halin yanzu bai san inda ya ke ba, ta yi saurin juyo shi, ai ko bakin idanun nasa ya juye ya koma fari, ganin haka 49 Kwadayı bar jana!- Amina Abdullalu Sharai ba mai Karamin razanarwa, tsorata ta ya yi ba, sai kuwa ta kwala kara su Mum su na falo dasu Ibrahım da Z.ainab da Abbansu ana ta hira suka ji karar Maryam. Mum ta ce "To Alhaji gashi can zai kashe musu yarinya, ma za je ka". Baki dayansu suka runtuma da gudu su na rige-rige, ai ko suna isa suka yi turus suka tsaya kallon ikon Allah don ganinsa suka yi kwance cikin jini kamar ba rai. Ibrahim ne ya ce "Me ki ka caka ma sa haka? Cikin kuka ta ce "Ba komai, amai ya ke yi na jini". Mum ta ce "Alhaji ai sai ayi gaggawar kai shi asibiti." Shi dai Alhaji saboda rudewa sai ya ce "Yo me za'a kai asibiti bayan ya mutu?" Ibrahim ya ce "Daddy bai mutu ba, suma ya yi". Zainab kam sai kuka ta ke yi ta ka sa zaune ta kasa tsaye, nan dai Alhaji da Ibrahim suka taitaye shi zuwa mota, jikinsu duk ya baci da jinin aman da ya yi, Alhaji ya ja motar sai asibiti. Da zuwansu, nana da nan aka karbe su, aka sanya masa wannan robar a hanci don jan numfashi aka yi dakin da ya dace ayi treat dinshi, su kuma su Mum sun yi tsaye su na faman saſa da marwa, su na jimamin abinda ya faru, kuma ya haddasa ma sa wannan lamari wanda in ba ayi hankali ba zai iya sanadin ransa cikin lokaci kalilan, jim kadan sai ga shi su Daddy sun fito da shi sun tura shi zuwa wani daki, bayan sun bashi gado ne sai da ya karaso inda suke "In baku manta ba shi Daddy fa babban likita ne, abinda ya sa aka kawo shi asibitin ma don ya fi fahimtar me ya ke damunsa, kuma asibitin da ya ke aiki nan aka kawo shi Daddy ya zare safar da ke hannunshi ya dubi Mum wacce a halin yanzu duk jikinta ya yi sanyi, ya ce "Ilusna 50 Kwadayı barı jana'- Amına Abdullahı Sharaрв wai me ya ke damun yaron nan ne?" Ta ce "Ai kai zan tambaya domin ku ne likitoci". Ya ce "No ba wannan ba, ina nufin wane tension na rayuwa ya shiga haka har ya samu wannan ciwon?" Cikin damuwa ta ce "Alhaji wane irin ciwo ne ya same shi?" Ya yi tsaki "Wallahi ya kamu da ciwon zuciya ne". Ba ma ita ba hatta su Ibrahim sai da suka razana, ita kuwa Mum rawar sanyi ta kama yi a wurin don fargaba, ya ci gaba "Yanzu dai munyi kokarin gano abinda ke damunshi sauran kuma mu bashi maganin da zai samu lafiya insha Allahu, amma akwai magana sai mun koma gidi. Ya kamata a san me ke faruwa tsakaninsa da Matarsa, la gaya mana gaskiyar lamari kar ta boye mana domin ya zama dole a san me ye ke damunsa har ya samu wannan ciwo haka". Nan dai suka yanke shawarar ita Zainab ta zauna a wurinsa domin ba'a san abinda ke damunsa ba, game da zamansu da matarsa ba a sa ta yi jinyarsa ba, nan dai suka dan zauna a wurinsu, su Mum suka wuce gida don dauko abinda za su bukata. Tunda Faruk ya samu rashin lafiyar nan aka kai shi asibiti har yau din nan kwana biyu Maryam ba ta je ba, ta na gida, yanzu ma a kwance ta ke ta na ta faman tunani hankalinta a tashe, tayi shiru ta na ayyana abinda ta yi kam 'Lallai ba ta kyauta ba, wai to me ma ya ke janyo hakan? Anya kuwa abinda ta kewa faruk kiyayya се? Emana ita ce mana, in ko ita ce lallai ya ci ace ta saurara masa haka, ko fa dubashi bata je ba, yanzu ko ba za ta ji nauyin kowa ba. ai ta ji na iyayensa wadanda suke matukar nuna ma ta so. Lallai kan ya kamata ta je ta duba shi don ta wanke 51 Kwadayı barijana'- Amına Abdullalu Sharada kanta wurin iyayensa". Nan da nan ta fara shiri ta na ta faman kokarin tafiya sai dai kash! Ba ta san asibitin ba, wai ina ne ma? Wa ya kamata ta tambaya? Ta dauko mayafinta ta sauko falon kasa don ko za ta samu wanda zai ma ta kwatancen wurin. Ta kuwa yi sa'ar samun Ibrahim, ta na ganinsa ta ce ma sa "Yauwa Ibrahim don Allah ko zaka kai ni can asibitin da Yaya ya ke a kwance?" Ya ce "Ba zan samu dama ba". Ta ce "Kai Ibrahim don Allah ka taimaka". Ya ce "Na gaya miki ni ba zanje yanzu ba, ki bari sai na samu lokaci na je". Ta yi turus sannan bayan ya tafi ta bishi ta na cewa "To don Allah yi min kwatance sai inje" Ya ce "Da cần me ya hana ki binsu sanda za'a je? Ni ma ban sani ba". Cikin tsabar kidima ta ce "Haba Ibrahim ka daure ka fada min mana, na san za ku yi fushi, to amma ku yi hakuri". Ya ce "Oo ni meye nawa a ciki? Kinga in kin san wuri ki tafi kawai, amma ni ba zan kai ki ba". Ta ce "to ya jikin na sa?" Ya ce "Yana nan sai abinda hali ya yi, don in ance ya mutu ma babu mamaki". Ba ta san sa'in da ta rike masa hannu ba ta na girgizawa "Ibrahim me ya ke damunsa?" Ya ce "Ciwon zuciya ne" Ta ce "Na shiga uku". Ta cika masa hannun ta dafe kanta cikin tsananin fargaba ta koma sama ta shiga dakinsa, kamar me neman wani abu da ya ke tunda aka kawo ta bata taba shiga dakin ba sai yau, shi yasa ya zame ma ta bako, tsayawa ta yi a tsakiyar dakin ta na dube-dube, kamar wacce za ta ganshi, ya ci ace tsaruwar dakin da haduwarsa ya burgeta, to amma da ya ke hankalinta ba ya jikinta ba ta lura da wannan ba, ita kanta ba ta san me ya kawo ta dakin ba. 52 Kwadayı barı jana!- Amına Abdullahi Sharada Wani zazzafan hawaye ne ya zubo ma ta daga ido ta alka bisa gadonsa ta fara kukan da ba ta san dalilin yinsa ba "Wayyo Allah Faruk kar ka mutu! Ka dawo Faruk na saba maka, Faruk ya zanyi da dumbin hakkinka in na rasa ka?" Wani tafkeken hotonsa ne lamination, a jikin bangon dakin ya ke kallonta, ya na murmushi, can kusa dashi kuma na ta hoton ne da Mama ta bashi, wato Hajiya Jamila, ta dauka da wata doguwar riga mai kyau kalar blue ta sanya hijabi shima bulun, ta sa hannayenta biyu ta kwantar da kanta bisa hannun ta na murmushi, ta yi bala'in kyau, kallo daya ta yiwa hoton ta dauke ido ta mai dashi ga kallon hoton Faruk wanda duk da haduwar nata, to na Faruk ya fi nata, a hoto kenan ma, amma a zahiri Faruk ya fi haka ahďuwa don ita kanta ta san ya yagawa Bashir nesa ba kusa ba a komai da komai, to amma why da ta tsane shi? Har ta ke son kashe wannan santalelen yaro haka? Ba amsa sai kawai ta mike ta dauko horon ta nufi hanyar fita, sai da ta kai karshen kofa sannan ta juyo ta kalli dakin wanda kamshin dakin da kamshin jikin Faruk iri daya ne, wato kamshi ne mai dadin shaka. Hoton ta rike a kirjinta ta komo ta janyo kofar ta na rufewa, sai ga Ibrahim ya shiga, ta ce cikin sauri "Ibrahim in zo ka kaini?" Ya ce "A'a ni da abinda zan dauka in fita". Ya shige dakin, ita kuma ta koma dakinta, ta sa hoton gaba ta na ta kallo, zuciyarta a yanzu ta yi tankade da rauraya duk bakin ilahirin son da takewa Bashir in ma da kari to ya koma kan laruk don in banda tunanin irin abinda ya faru a baya ba abinda take yi, anan ta fahimci ce wa lallai Faruk ya na matsanancin sonta, to amma me 53 Kwadayı barава Аnиа Abdullalu Sharnda ya dace ta yi in Allah ya abshi lafiya? Banda ma haka so ta kamar da kuwa? Bare ya na ganin ga abinda faru? To wannan amsar dai sai in Allah ya bashi laliyw tukunna ma gani. Ya na kwance bisa gadon asibiti ya yi tagumi ya n tunani, can ya daga kai ya dubi Mum da ke zaune gel daya ta na jan carbi bayan ta idar ad sallar la'asar, gash dai Mum da ba asalin musulma ba ce kirista ce,Alhaj Gambo ya musuluntar da ita ya aureta sai gashi a yanzu haka har ta fi wanda aka haifa cikin musuluncin riko da addini a koda yaushe za a same ta tana faman lazımi ko kuma yawan azumi, kamar an ranar litinin da alhamis. Gashi ta san abubuwa da dama fiye da wani wandy ya girma a musuluncin don ta na koya kuma ta na bayarwa a sayo mata littattafan addini na turanci, gashi ta na yawan sauraran laccar manyan Malamai irin su Shaik Ahmad Didat da sauransu, shi yasa a kullum za ka ganta cikin nutsuwa ga yawan ibada haka ma yaranta mazan da matan suke. "Mum!" laruk ya kirayi sunanta, ta amsa gami da dago kai "laruk me ka ke so?" Ya ce "Ba komai Mum, wai har yanzu Maryam ba ta zo asibitin nan ba?" Mum ta ce "Ta zo kana bacci shi ne ta ce kar a tashe ka". Ya girgiza kai "Ki yi hakuri Mum kar ki ce na Karyata ki, amma na san Maryam ba zata zo wurina ba ko da ace zan mutu, na san maryam ba ta so na Mum". Ta yi murmushi "Ta na sonka mana ka san Maryam yarinya ce mai tsananin kunya shi yasa ka ga bata nuna maka a fili ba". Shiru kawai ya yi don zuciyarsa ba ta taba amince wa wai maryam ta na kaunarsa ba, "Mum bani ruwa mai 54 Kwadayı bar jana'- Amına Abdullahı Sharada sanyi insha". Та се "To". Ta mika masa cup daya ya shanye, sannan ta ce "Ga abincin in dan zubo maka maan ka ci ko ya ya ne?" Ya ce "Na koshi Mum". Ta ce "Me ka ci, za ka koshi? Ai gara ka ci ko ya ya ne?" Ba ta jira ya sake magana ba ta bude kular abincin ta fara zuba masa a plate sannan ta sanya cokali ta mika masa. Ci kawai ya ke amma bakin babu dadi, ya dubi Mum ya ce "Na koshi". Ta ce "Haba Faruk me ka ci kenan cokali biyu fa ka yi? A'a ya kamata ka kara". Ya ce "Ba na ci ba?" ta ce "To shikenan ajiye ai an samu da da baka ci kuma fa?" Ya ajiye ya dauki ruwan ya kara, sannan ya sha magani ya kwanta ya na tunanin abinda ke faruwa, ya ga dai ana nuña masa kulawa ina ma ace yadda ya ke samun kulawar nan haka zai samu kulawar Maryam? Ai shi da ya zama dan gata a rayuwarshi, shi kam yanzu ya gama sadakar cewa ba za ta taba sonsa ba, to amma ya zuba ma ta ido sai abinda ta yi. Maryam na zaune kallo daya zaka yi ma ta

Chapter 4 of 12