An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
WADAVIBARI JANA2
Amina Abdullahi Sharada
(Mrs Ahmad Yusuf Hadejia)
Kwadayi bari jana!- Amına Abdullahi Sharada
KWADAYI BARI JANA
2
Na
Amina Abdullahi Sharada
(Mrs Ahmad Yusuf Hadeja)
1
GODIYA
Kwadayı ban jana' Amuna Abdullahı Sharada
Godiya ta ga Allah Subhanahu wata'ala da ya bani
damar rubuta wannan littafi mai suna KWADAYI BARI JA
NA!, Allah ka kara tsira da aminci ga shugabanmu
Muhammad (S.A.W)
GODIYA TA MUSAMMAN GA
Yakubu Usman Ubangari
Da Family dinsa.
TUNATARWA
Wannan littafi KWADAYI BARI JA NA! Ba'ayi shi
don kowa ko wata ba, kagaggen labari en saboda haka in kunji
hali ya zo dai-dai da naku to arashi ne ba'ayo shi don a ci
fuska ba anyi shi ne don fadakar wa da nishadantarwa.
MUSAMMAN NA YI SIII DON
Masoyana kamar su:-
Binta Umar Sani Gombe
Maimuna Isma'il Sokoto
Amina A Bobbo (Mrs Rabi'u Sanka)
Amina 1H. Sokoto
Amina Ahmad Tukur Bauchin Yakubu
Hassana M. dan Sarari Ajiyan Kano
Amina Aliyu (Nanaye) Mrs Muh'd Wawata Kaduna
Amina Bauchi Unguwar CGwabba
Asma'u Abdullahi Niger Minna
Lubabatu Usman dan madami (Mrs Ibrahim dan Maliki)
2
Kwadayı barıjana'- Amına Abdullalu Sharada
KWADAYI BARI JANA-2
A
Ihaji Usaini ya yi tsaye ya na tunanin abinda
zai biyo baya, bayan tafiyarsu domin za
tilaswa Maryam ne ta bi su, kuma in ta bisu bai san inn
zaman da za ta yi a can ba, kila ta ki kwantar da
hankalinta, to amma ya na ganin bin nasu shi ya dace,
kuma shi ne kwanciyar hankalinsa don haka sai ya dubi
Alhaji Gambo ya ce "Na amince ta bi ku din kawai, sai
dai abínda na ke tunani in ta biku maganar aure fa?" Ya
ce "Kar ka ji komai maganar aure za ta yi aure, amma a
bari wannan rigimar ta lafa tukunna". Ya ce "To shike
nan Allah ya zaba abinda ya fi alheri". Ya ce "Amin".
Faruk ne kwance ya yi shiru in banda tunanin
Maryam babu abinda ya ke yi "A agskiya Maryam ta
haďu karshe sai ka ce ba 'yar nigeria ba, ince ko da ma
ruwa biyu ce ne? A gaskiya duk yadda aka yi Mamanta
wato Hajiya Jamila ba 'yar Nigeria ba ce, kuma wani
ikon Allah sai ta kama da kakaninta na wajen uwa, eh to
kakaninta na wajen uwa mana domin dai sam ba ta kama
da danginmu na uba, kuma ba sa kama da Haj. Jamila, ita
kamaninta daban sai ka ce ba 'yar gidan ba, amma dai sai
na tambayi Dadina ince ni ko Maryam da wa su ke kama
in our family, wallahi ta na burge ni sosai, ta hadu, ga
kyau, ga kyan gani fuskar nan abin sha'awa kai....." Ya yi
ajiyar zuciya da ya tuna cewa ko kula shi ma ba ta yi ba
duk da irin kyansa da haďuwarsa kuwa, nan ta ke ya ji
tunanin ya ki ma sa dadi sabo da wannan tunanin da ya
yi cikin sauri ya kawar da wannan tunanin domin ya na
kawo masa dacin rai.
"Salamu alaikum".
"Wa'alaiki salam". Ya amsa, ba ya bukatar daga kai
4
Kwadayı harı jana'- Amuna Abdullahı Sharada
don ya ri ga ya san mai sallamar kanwarshi ce karamar
wato Zainab, ta durkusa "Yaya wai ka zo inji Daddy, ya
na can bangaren Uncle". Ya ce "To gani nan, ina zuwa".
Ta fita sannan ya mike ya ficce shi ma durkusawa
ya yi a gabansa yayin da kansa ya ke sunkuye ya na
sauraren abinda ya ke cewa "Ka na ji na ko, zamu ta fi
wannan satin, don haka sai ka fadawa sauran kannanka
su shirya kayansu domin ba na son sai anzo tafiya a
dinga an mance kaza da kaza".
Ya ce "To Daddy, amma to ai da ka ce zan dan
zauna sai bayan an kwana biyu na koma?" Ya ce "Na fa
sa duk za mu tafi don banga abinda zaka yi anan din ba".
Cikin rashin jin dadīn maganar ya mike domin dai shi fa
so ya yi abar shi, to amma ya ki ya barshi why? Shi
kuma uban wato Alh. Gambo sai ya yi kiran Sameera ta
zo ta durkusa "Gani Dad".
Ya ce "Yauwa Sameera dama wani tunani na yi
Alhaji ya ce a kyaleki anan ki dan zauna, to da na ce a'a
sai yanzu na ga ya dace in amince shi ne na ce ki zauna
ki yi ko irin two months din nan sai ki koma gida ko?"
Тa сe "To Dad, dama ina son zaman nan din wallahi don
dai ina tsoro ko ba za ka barni ba ne".
"A me zai hana in barki Sameera ke da gidan
iyayenki?"
Ta yi murmushi "To zan zauna".
"Shikenan je ki".
Alh. Usaini na zaune shi da Alh. Gambo suna hira
sai ya kira Maryam ta zo ta durkusa ta gaishe su, sannan
ta ce "Gani Abba". Ya ce "Yauwa Maryam da ma Uncle
din ki ne ya ce ko za ki bi su ki yi ko wata guda ma...."
Nan da nan gabanta ya fadi ras! Har sai da suka ga
5
Awaday hnаnя Aиnа Abdullatu Maиа
alamar razanar, amma sat ya yi kamar hai lura ba yуa
gaba "Shi zumunci a kafa ya ke, Maryam ki na sane da ni
da Alh Gambo uwa daya uba daya mu ke amma
'ya'yanmu basu san mahallinmu ba, ma'ana ke haki san
gidan Uncle dinki ba, su ma 'ya'yansa basu sanku bha, to
sai yaushe za'ayi zumuncin ke nan? Saboda haka
Sameera za ta zauna anan ke ma kuma za ki bi su in har
na isa da ke to zan sa ki ki amince, in ko kin ki to kin
nuna min ban isa da ke ba kenan...."
Alh. Gambo ya yi farat ya tari numfashinsa "Haba
Alhaji me ne na wannap magana ai ba za ta ki ba ta ma
amince ko Maryam?" Ta gyada kai alamar "Eh". Тo
amma a zuciyarta ba haka ba ne, don ranta bai so wannan
tafiyar ba, ta tashi ta ficce, faki ta koma ta zauna a gefen
gado ta na ta faman tunani a zuciyarta "Yau na shiga
uku, yanzu shikenan rabuwata da Bashir ke nan? Na san
ba don komai aka ce in bi su ba sai don a raba ni da
Bashir ne, inko haka ne ai ni da aure har abadan domin
banga wanda zan so tamkar Bashir ba"
Zaune ya ke a falo gashi falon ba kowa sai shi daya
ya na karatun wata mujalla ta turanci wato darly trust sai
ga Maryam nan, ta fito sanye da wata riga da sikeri na
atamfa dinkin mai sharp ne, ya yi mata kyau sosai tamfar
kalar ruwan kwai ce, super holland ta yi mata bala'in
kyau, kanta babu dankwali ta yi gyaran gashi domin
tafiyar da zasu yi, an yafa mata kananan kitso ya zubo
ma ta har baya, takalmin da ta sakawa kafarta mai tsada
ne sosai, kalar atamfar ne shi ma ya karbe ta duk da cewa
Maryam ba ta cikin walwala amma ta yi kyau sosar, cikin
sannu ta ke takun yayinda ta daga idanunta sai suka yi
ido hudu da Faruk, ya zubo ma ta ido kirr ya na kallonta,
6
Kwadayı barıjana'- Amına Abdullalu Sharada
ta sunkuyar da kanta kawai, ita ma ta zo za ta gittashı ya
ce "kanwata babu gaisuwa ne?" Ta juyo ta danyi ma sa
murmushi kana ta ce "Sannu da hutawa". Ya ce "Yauwa
sannunki, ina zaki ne?" Ta ce "Ba ko ina"
Ya ce "Zo ki taya ni hira mana?"
Ta ce "dakin Aunty zanje".
"To tsaya mu tafi tare mana".
Ranta bai so ba, ta ce "To" kawai.
Shi ma ya san ranta bai so ba, amma ya nuna bai
kula ba tare suka shiga dakin suka samu Halima na
sanyawa jaririnta wanda zuwansu Faruk suka rada masa
suna Walid kuma Walid din ta bishi, yanzu haka kowa
da Walid din ya ke kiranshi, ta na sanya masa kaya,
Maryam ta karbeshi ta ce "Kawo shi in sanya masa". Та
mika ma ta shi.
Ta karasa sa masa kayan, sannan ta rike shi ta nai
masa wasa, a duk lokacin da ta dago kai idon Faruk ya
na wajenta, ganin haka ya sa ta mike da Walid a hannu
ta ficce, shi ma dai bai zauna ba, to amma ya makara
domin bai san inda ta shiga ba, ita ko dakinta ta koma ta
kulle kofa zuciyarta cike da jin haushin laruk, da tsanar
shi, ta tsani mutum mai kallo sam fita ranta ya ke yi, ta yi
tsakı "Ni sh: yasa ba na son haduwa da shi, sabo da ba na
son ko hada hanya da Faruk wallahi"
*** ***
Yau ee ranar tafiyarsu, don haka duk wani shiryeshirye an gama shi har ma an fiddo kaya domin sanyawa
a mota, sannan bayan an gama zuba su a motar suka fito
don tafiya, su Haj. Jamila sun fita har Halima don y
musu sallama, za a tafi kuma, tunda Faruk ya ji cewa da
7
Kwadayı barı jana'- Amına Abdullalu Sharada
Maryam za a yi wannan tafiyar ya jı kamar anyı mas gafara, murna kamar me, cıkın doki ya dauk
jakunkunnan ta ya sanya a mota, sannan ya koma kiranta
don har wannan lokaci ba ta fito ba, ya na shiga dakinta
ya sameta, ta kifa kai ta na ta faman kuka "Maryam!" Ya
kirayi sunanta, ta dago kai ta dube shi ido ya yi ful
saboda kuka, ya ce cikin sanyin murya "Ta so mu tafi ke
ake jira".
Ta mike ba magana ta sanya takalminta ta zo ta
gitta shi, ya bi ta da kallo har ta kule, sannan ya janyo
kofar shi ma ya fito, babu wanda ya yi ma ta magana
domin an san ba ta son tafiyar, haka ta shiga motar,
Abban ta ya leko cikin motar ya ce "To Maryam sai an
dawo kо?"
Ta kalleshi idanunta cike da hawaye, ya yi saurin
dauke nasa idon, domin ba ya son ganinta cikin wannan
hali, tunda ya ke da ita ba ta taba kukan minti guda ba
ma sai yanzu da ta isa munzalin aure.
Nan ta ke wani 6acin rai ya zo masa ya ce a ransa
"Amma Alhaji Hassan bai kyauta ba, domin duk shi ya
janyo wannan matsalar da kamar ya hakura da tuni anyi
aurensu, amma ba komai Allah ya hada kowa da
rabonsa".
Cikin wannan tunani ne ya ji ana cewa "To Abba
sai wata-ran". Faruk ne mai fadar hakan wanda wurin
zamansu daya a kujerar baya da Maryam, gaba kuma
direbane kawai. dayar motar kuwa Alhaji Gambo ne da
'ya'yansa Ibrahim da Zainab sai direba, ita Sameera an ce
za ta dan kwana biyu sannan ta komo, sai murna ta ke
babu abinda ya dame ta, mota ta ja suka danna, ana daga
musu hannu sai airport.
8
Kwadayı harı jana'- Amına Abdullahu Sharada
A cıkin jirgı sai da laruk ya ga inda Maryam ta
zauna, sannan shi ma ya zauna kusa da ita, hankalinsa
akanta, banda hawaye babu abinda ta ke yi, ya yi rarrashin dunıya amma ta ki yin shiru, sai kawai ya zuba
ma ta ido, can sai aka kawo musu dan abin motsa baki,
wani icc-cream ne mai dankaren dadi, ya mika ma ta na
ta, da ya ke biyu aka dire, shi daya ita daya, ta ki ko kallonsa, har fargabar yi ma ta magana ya ke yi, domin
bai san ta inda za ta bashi amsar ba.
Kawai dai sai ya yi shiru har ya gama shan na sa
ice-cream din ba ta dauki na ta ba, anan ne ya ce ma ta
"Maryam dauki mana ki sha, kya dan rage yunwa kafin
mu je gida". Ta yi masa banza a ta ki ce da shi komai,
har suka sauka ba ta sha ba, anan ta tashi ta barshi.
Suna isa gida Mamansu ta tura Direba ya dauko su daga airport 'in, sannan ya akwo su gida. Suna zuwa
Maman ta fito cikin sauri da murnarta, ta tare su anan ta
rungume Maryam ta na muma.
Kallo daya Maryam ta yi ma ta, ta gane cewar ita
Faruk ya yo kama da ita, komai da koma, haka ma
Zainab amma Ibrahim da Sameera Daddynsu suka yo kama, sai dai su ma farare ne sun dauki launin uwarsu,
amma tsantsar kamanninta suna wurin Faruk kamar an
tsaga kara.
Tunda suka sauka Maryam ta ke ganin garin abin gwanin ban sha'awa domin garin ya tsaru haka ma da
suka zo gidan ta yi mamakin irin tsarin gidan nasu kamar gidan wani shugaban kasa, duk wani abu na jin dadin rayuwa akwai a gidan duk da haduwa irin ta gidansu sai ta ga kamar a kauye ta ke akan wannan gidan, ta ga ma karfin hali irın na 'ya'yan da har suka zauna ku san sati
Kwadayı barı jana'- Anuna Abdullahı Sharada
uku acan, ai ba ta yi tsammanın haka suka hadu ba, lalla
sun hadu da yawa, Mamansu sai faman haba-haba ta ke
ma ta, kamar ta lashe ta don so.
Hakan ne ma ya dan rage ma ta radadin rahuwa da
gıda, kuma iyayenta da masoyinta Bashir wanda a halin
yanzu bai ma san sun taho nan din ba.
lFaruk fa ya fada cikin wani hali na tsaka mai wuya,
halin ko shi ne na kaunar Maryam, a gaskiya ya
tsunduma dumu-dumu a ciki, amma ya rasa ta yadda zai
bullo ma ta domin babu fuska, kullum sai tunaninta ne ya
ke nukurkusars a ko wane lokaci ya kan so ya yi ma ta
magana, to amma ya na fargaba, ganin har yanzu ba ta
kwantar da hankalinta ba, duk kuwa da cewar ana nuna
ma ta gata sosai a gidan.
Mama madece mai fara'a sosai, amma ba ta son
raini, za ka ga gashi ta nai wa yaranta wasa, to amma ba
raini domin ta na da fada wani lokacin, shi ya sa yaran su
na shakkar ta sosaj har lFaruk din ma. Shi ya sa sau tari
ya na son ya yiwa Maryam magana ya na tsoron kar
ranta ya baci Mama ta sani, in har ta sani to lallai za ta ci
ma sa mutunci, kuma ba ta shakkar a gaban sauran "yan
uwansa ta figa masa rashin mutunci shi ya sa har yanzu
tsakaninsa da Maryam sai dai gaisuwa kawai domin ko
wane lokaci ta na gaishe shi, in kuma ya je wani wuri ya
dawo za ta yi masa sannu da zuwa domin ganin
Mamansa.
Yau ma ya hallara a hadadden Isantararran falonsu
ana ta hira, suna ta bata labarin Nigeria, da wuraren da
suka ziyarta a lokacin da suka je, ta na ta saurarensu, ta
na cewa "Ina ma ni ma inje?" Ibrahim va ce "Ai ke ma
Daddy ya ce za ki je" Ta ce "To shikenan zan je
10
Kwadayı han jana'- Anuna Abdullalu Sharuda
Duk wannan hıra da turanci suke yin ta domın
hausar tata ba ta gama kwarewa ba, in ta san wani abin,
wani bata sanı ba, domın ba za ta ıya hıra ta cıkakken
mınti biyar da hausa ba, sai dai ta san dan wani abin maı
saukin fada, duk hırar da suke yı laruk na jinsu kawaı ya
yı shiru ba ya wanı walwala, don bai ga Maryam a wurin ba ya san kila ta na can ta na ta faman kuka, don sau tarı
in bata falon to in ka je ka same ta a daki, kuka take yi, don haka ya mike tsaye tsam!
Ya shiga dakin nata, ya same ta a kwance bisa gado
ta kifa kai da matashin kai pillow, ta na ta faman kuka.
Nan ta ke ya ji zuciyarsa kamar ta fashe don rashin jin dadl, ya karasa ya zaunā ya ce ckin sanyin murya "Maryam me aka yi miki?” Ta yi shiru ba ta yi magana ba, ya ce "Maryam ki yi hakuri ki daina kukan, ba na son ínga ki na cikin damuwa"
Ta yi ma sa banza, nan ya zauna ya na ta faman
rarrashinta, amma ko ta kalleshi, haka ya gaji ya hakura
ya fita ranshi bai so ba, ya koma dakinsa ya kwanta ya na tunanin wannan wane irin abu ne Allah ya jarabce shi da
shi? Yarinyar nan ba ma ta yarda ta zauna a inda ya ke
zaune ba, amma shi a kullum zuciyarsa kara masa
kaunarta ya ke yi, yau shi dai kam ya bani, ya zai yi da rayuwarsa?
Suna zaune da Mama a falo ta na ta yi ma ta fada,
lallai ta saki jikinta domin nan gidan su ne, kamar can,
ubm kawai Maryam ta ce, don ita abinda ya daem ta daban ne, da ya ke Mamansu Zainab ba ta san abında ke
faruwa a gida ba, ta dauka Maryam har yanzu bakunta ce ta ke damunta.
Shi ko Alhaji ya sani amma bai gaya ma kowa ba,
11
华
Kwadayı barıjana'- Amına Abdullalu Sharada
don ko Faruk bai san abinda ya ke damun Maryam ha zatonsa kawai ba ta son zuwa ne, kuma da ya sake lunan
sai ya ga ai acan gidan su ma haka take yi, to wai me y
sa? Ya ga ai da a lokacin in sun yo waya a cikin farа
suke gaisawa, amma yanzu kamar ba ta sansu ba, why
A kullum wannan tunani shi ke damun l'aruk.
Ta na zaune ita kadai a harabar gidan, ta yi lagum
kawai ta na tunani, can ciki kuma lFaruk ne ya shig
dakinta ya samu ba kowa, har ya juyo zai fita sai idons
ya kai kan wani dan kati a dab da filo, ya koma у
dauka, sai ya ga an rubuta 'You are only one in my hcari'
Nan da nan gabanshi ya yi wani mummunan
faduwa, ya yi saurin juya bayan katin ya ga ashe hoton
Bashir ne tare da Maryam din, suna dari cikin nishadi.
Nan da nan ya ji gaba daya garin ya yi masa zafi
duniyar ta yi masa duhu wani tukukin bakin ciki ya taso
masa, ya ce a ransa "Kar dai ace Maryam saboda Bashit
ta ke cikin wannan halin? In ko haka ne to ni ya ya zanyı
da raina? Gashi na afka cikin kogin begenta?
Lallai in har Maryam ta na son Bashir kuma su
Daddy sun sani to lallai ba zasu bari in aureta ba", Ya yi
saurin kawar da wannan tunanin don ba ya son yinsa m
ya ajiye hoton kamar yadda ya ganshi.
Ya fito cikin sauri ya na tunanin ta wacce siga zai
bullo ma ta ya san gaskiyar lamarin?
A zaune ya sameta, ya yi ma ta sallama, ta amsa ma
sa gami da sake kawar da kanta gefe daya, ya samu wun
ya zauna, ya na fuskantarta "Maryam!" Ya kira sunanta a
ciki. Ta amsa ma sa, ta na fisge kai, bai damu ba, ya ce
"dazu Bashir ya yo mun waya ya na tambayarki....."
12
6
Kwadayı barı jana'- Amına Abdullatu Sharada
3Me ya ce?" Ya yi murmushin karfin hali don kar ta
Cikin sauri ta juyo ta kalleshi, fuskarta a sake ta ce
gane, ya ce "Ce wa ya yi kina ina?" Ta ce "Bani shi don Allah!"
Ya ce "Ai na bar wayar a daki, zo mu je in ba ki,
amma kar ki ce masa na fada miki ke dai ki kirashi
kawai”. Ta ce "To". Cikin doki ta karbi wayar ta kirashi.
Shi ko banda kallonta babu abinda ya ke yi, bai
ankaraba ya ji ta na cewa "Haba My own ya zaka ce ban damu ba, ka san ko a cikin halin da na ke ciki kuwa?
Wallahi rashinka ya sani shiga cikin wani hali wanda ban saba samun kaina a ciki ba, yanzu wane mataki ka daukar mana kan wannan lamari? lya abinda lFaruk ya ji kenan, ya nemi wuri ya zauna, don ji ya yi jiri na neman
kada shi, lallai yanzu ya san komai, shin wai yanzu wane mataki zai dauka? In ya ce zai yi kishi da Bashir.
Bashir dai dan uwansa ne, shi kuma gaskiya komai kunci ba zai jure jin suna wayar nan ba, ya mike tsaye
"in kin gama kya sameni a garden ina jiranki". Ta cе "To". Cikin fara’a ya juya ya tafi jiki ba karfi.
Ya na nan zaune, ya yi tagumi ya rasa abinda ke
ma sa dadi, sai ga Maryam ta nufo wurinshi "Yaya ga
wayar, na gode". "To". Kawai ya ce, ya karba ya sa aljihu, sannan ya yi jigum da shi, ta dube shi "Yaya lafiya?"
Ya yi murmushi "Ba komai".
Ta ce "Gani na yi ka yi jigum ka na tunani?"
a
Ya ce "Ai dole ne wannan tunanin". Daga nan sai
ta bar wannan tambayar ta shiga yi masa hira wanda a da
ko kallo bai isheta ba, nan ya dinga tayata hirar har wani lokaci sannan suka koma ciki ta shiga kitchen domin taya
13
Kwadayı harıjana
mna thullahı hara
Mama da /aınab aikı saboda ta same su sun shırya abıner
a kitchen din ta shiga kitchen din da gudu ta na murna
Mama ta dubeta cikin fara'a ta ce "A'a 'yata farin
cıkı ake yı ai gara ki saki jikinki, amma bakunta kamar
wata 'yar goye?"
Maryam ta yi dariya "Mama kenan ai daga yau na
zama 'yar gida". Ta ce "Ai dama ke 'yar gida ce don ba
ki saki ranki ba ne". Ta ce "To yau na sa ki
"Faruk wai me yake damunka ne, na ga ka rame
haka? Kuma walwalarka ta ragu ba sosai ba?" Inji
Mamansa ta ke tambayarsa, bayan ta kai shi inda babu
kowa sannan ta ke tambayarsa.
Ya sunkuyar da kai "Ba komai Mama". Та се "Ка
ga ni mahaifiyarka ce bai cancanta ka boye mun
damuwarka ba, domin ba ka da wanda zaka gayawa in ba
mahaifinka ba, don haka ina so ka sanar da ni abinda ke
damunka in na magani ne abin zan yi a take, in kuma ma
ba shi ba ne zanyi maka addu'a, kuma da shawara ta
gan".
Ya ce "Mama dama ba wani abu ba ne, a gaskiya
tunda na dora idona akan yarinyar nan Maryam na ji ina
kaunarta, na ka sa sukuni, amma kuma sai na ga ila
akwai wanda ta ke so, shi ne abin ya ke damuna
Ta na jin haka ta ce "Shikenan sai ka saurara ba
Dadinka ya komo sai in sanar masa, abinda ya ce da shi
zaka yi aiki, in ya ce ya amince shikenan, in kuma ya се
a'a sai ka yi hakuri Allah ya zaba ma ka ta gari, don haka
ka kwantar da hankalinka". Ya ce "To shikenan Mama
Allah dai ya sa ya amince don a gaskiya dai son Maryam
ya girma a zuciyata". Ta ce "To dai iya abinda ya kamata ayi ke nan".
14
Kwadayı barıjana'- Amına Abdullahı Sharada
Suna zaune da Alhajı Gambo suna hira daga shi sai matarshi, a lokacin dare ne, kowa ya isa wurin
kwanciyarsa, Mama ta dube shi "Ka san abinda ya ke
faruwa kuwa?" Ya yı saurin dago kai ya dube ta ya ce
"A'a me ya faru ne?" Ta ce "Wai Faruk shi dai babbu
wacce ya ke so sai Maryam!"
Ya na jin haka ya yi murmushi "To me ye? Ai
shıkenan Allah ya tabbatar mana da alheri, wallahi na ji
dadin wannan abu, ba ra gobe sai in yiwa Alhajin waya
in sanar masa abinda ake ciki". Ta се "Паkа da saurі
Alhaji?" Ya ce "Ai da zali-zafi kan bugi karfe, kuma a
bari ya huce shi ke kawo rabon wani, don haka gara
abinda za'ayin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 12