Ya ce "Mama wallahi na koma
gidan ne sai na ji gidan babu dadi ni kadai shi ne na zo
na tafi da ita" Suka kwashe da dariya sannan Hajıya
Jamila ta ce "Sam ba inda za ta sai da dare kwa tafi".
Ashe Alhaji Usaini ya na nan ya na jin abinda ake cewa
sai ko ya fito ya ce da Bashir "Kai dauki matarka ku tafi,
ma za wai ku Hajiya me ya sa ku ke irin wannan ne sai
kace wasu yara? Tunda ya ce zai tafi da matarsa ai ba
kwa haan ba, ina laifi da ya akwo ta ma? Ai kuna so nan
gaba ya kara kawo ta tazo, ni ba an son rashin hankalı"
Nan dai Bashir ya ja matarsa suka kama hanya.
Hajiya Jamila ta cewa Halima "Ai dama na san in Alhaji
ya na nan sai ya yi magaan kina gani ke mai mai ya hana
Maryam zuwa garin nan duk haihuwar nan biyu da kika
yi ta bai bari ta zo ba, wai ba ya so su sami sabani da
mijinta". Halima ta ce "Aiko haka ya fi ma da ace kullum
ana hanya kamar wasu bitalman ai zaman gidan mijinka
ya fi maka komai a rayuwa". Nan dai suka yi ta hira har
wani lokaci.
82
Kwadayı barıjana'- Amina Abdullahu Sharada
***
Z
ama ya yi matukar dadi tsakanin Maryam da
laruk domin a yanzu soyayya ta ginu mai karfin gaske, a kullum sai zubawa juna so suke kara yi, ga cikin Maryam yaznu ya kara tsufa sai faman
shagwaba ta ke zuba masa, shi kuma ya na ta faman aikin rarrashinta a kullum suna manne da juna a yanzu haka ma ba sa son ko fitowa falon Mum sabanin da da а
kullum sai ta koresu, malana in Maryam ce ta zo sai ta yi faam da ita akan ta je ta kula da mijinta, sai dakyar ta ke
-zuwa, to amma a yanzu sai kusan goma ake saukowa a
gaida ita, don Daddy ma ba ya samun gaisuwar tunda shi da wuri ya ke fita.
Yau ma suna manne da juna har kusan goma na safe basu ma fito ba bare su sauko a gaisa, ta na zaune a
gefen gado yayinda shi kuma Faruk ya ke ta sharar bacci.
Ta juya ta kara juyawa jikinta cikin rashin jin dadi, sai
kawai ta mike domin ta je ta yi wanka, ta shiga bathroom
din da ke falon ta yo wanka ta fito, ciwo ya sarketa a
wurin, ciwon ma kuwa mai karfi, ai nan da nan ta
durkushe ta na matagugu ta ma ka sa magana saboda
zafin ciwo, ta fara kiran "Wayyo Allah Faruk! Wayyo
zan mutu! Faruk ka taimake ni! Ka tashi zan mutu!"
Cikin bacci ya ji kamar ana kiran sunansa, ya bude ido
ya kasa kunne ai ko ya ji tabbas Maryam ce ke kiransa,
ya ko diro daga gadon a rude ya na neman inda ta ke,
ashe ma ta na gaban wardrop dinshi. Ta na murkususu,
83
t
1
C
C
S
Kwadayıhan jana - Anuna Abdullahı Sharaри
cikin saurı ya karasa ında ta ke ya na tambayar me ya
sameta?
Da kyar ta ce "Faruk ina jin haihuwa ce". Ya yi
sauri ya kıra Mum, sannan ya koma Mum ta biyo
bayansa ita ma suka taitayeta sai hospital nan da nan aka
karbcta. bai fi minti ashirin da zuwansu ba sai ga wata
nurse ta fito cikin fara'a baki daya suka mike suna
tambayarta ya ya? Ta ce "Ai ta haihu lafiya danta
namiji". Ai nan da nan suka fara murna, suna mika
godiyarsu ga Allah, to dama shi Daddy ya an can office
dinsa da ya ke asibitinsu aka kaita, nan da nan Mum ta
tafi fada masa, shi kuma Faruk ya shige dakin da aka kai
Maryam domin ta huta, ya sameta kwance da jaririnta a
gabanta, dama sai da aka hada musu komai na haihuwa
sannan aka shiga da ita. Sai gashi nan da nan sun gama
gyarata kun san abu namu wato mahaifinsa shi ne babba
a asibitin kowa ya riga ya san su don haak ba jira.
Idonta a rufe ya sameta cikin dokin ganinta ya kira
sunanta, ta bude a hankali ya ce "Ya jikin?" Ta ce "Ai na
warke". Ya ce "To Allah ya karo sauki". Sannan ya
dauki Babby ya na kallo, ya dubeta ya ce "Maryam tashi
ki gani yaron nan da wa suka yi kama?" Ta ce "Da ni".
Ya yi murmushi ya ce "Wallahi kuwa da ke yake kama
domin kamar taku ma har ta yi yawa, kamar an tsaga
kara". Ta yi murmushi ta ce "Amma dai ni ma ai
kyakkyawa ce?" Ya ce "Sosai ma, ai wallahi Maryam
duk gidanku babu mai kyan ki, inda kika san ba 'yar
gidan ba don babu wanda kuka yi kama a gidan sai ka се
Balarabiya, kin fi kama da Larabawa". Ta yi murmushi
kawai, ta ce "Wannan kyau nawa ai baiwa ce daga Allah,
ni ma sau da yawa ina wannan tunanin, na kan ce ni
84
Kwadayı barıjana!- Amına Abdullahı Sharada
kadai Allah ya zabe ya yi min kyakkyawar sura a gidan".
Ya yi murmushi ya ce "Ai ni Allah ya yiwa gata domin,
ya yi ki ne don ni". Ta yi dariya marar fitar da sauti ta ce
"Son kai kuma ya tashi ke nan?" Ya ce "Ai gaskiya
ne...." Suna cikin wannan hirar ne su Mum suka shigo,
suna ganinsu Faruk ya mike ya na cewa "Dad zo ka ga
yaron kyakkyawa dashi kamar uwarsa".
Mum ta ce "To marar kunya, ka kyale mu mu fada
mana sai kai?" Ya sunkuyar da kanshi ya na sosa keya,
daga nan sai ga su Zainab da Ibrahim sun shigho, suma
suka karbi yaron su na yaba kyawunshi, nan dai aka yi ta
hira har wani lokaci, sannan Alhaji Gambo ya ce su tafi
gida baki daya, har mai jegon domin tunda lafiyaria
kalau ba ta zauna ba, dama sun sanar amsa cewa za ta
haihu da ba sai sunzo ba, sai ya tura musu likitocin har
gida su karbi haihuwar acan gidan. Nan suka hada
komatsansu sai gida, suna zuwa kuwa suka yi ta buga
waya suna fadar haihuwar, tunda ga kan 'yan uwansu
Mum har 'yan uwan Alhaji Gambon babu wanda basu
sanarwa a ranar ba.
Sameera na fama da laulayin ciki aka sanar mata
haihuwar Maryam, ta dinga murna don za ta je suna,
Bashir na dawowa ta sanar masa, ya ce ba zai yiwu ta je
ba, ai nan da nan sai hawaye, don ta na son ta ga
Mamanta, da 'yan uwanta amma ya ce wai ba zaat je ba,
sai kawai ya ficce abinsa. Hakan shi ya sa ta shiga cikin
tsananin 6acin rai, bai ma dawo gidan ba sai can dare
don kar ta sake yi masa maganar, ya dawo ya lallabа уа
kwanta ba ta sani ba, sai da safe sannan ta ganshi ya na
shirin Kara fita.
Ta tashi cikin sauri ta ce masa "Yaya Bashir ina
85
1
1
1
1
1
Kwadayı barijana Amina Abdullahı Staradа
zaka kuma" Ya daure ma ta fuska ta ce "To ina da
magana da kaı, amma ka jita ni inyı sallah tukunnan" Ya
ce "Jeki ina jirankı" Ta je ta yı sallah ta idar sannan la
komo ta sameshı a falon Bayan ta gaishe shi ne ta samu
wun ta zauna ta dubeshı ido cikin ido ta ce masa "Y aya
Bashir amma dai ina tunanın har yanzu baka hakura da
Maryam ba?" Ya ce "Saboda me ki ke min wannan
tambayar?" Та се "Ai wasu lokacin ne ta ke takenka suna
nuna min hakan" Ya yi murmushi kawai, bai ce komai
ba, ranta ya kara baci ta dubeshi ta ce masa "Yaya bashır
ina so ka fada min gaskiyar abinda ke zuciyarka in har ka
na kaunar maryam ka fada min, wallahi in har ka san
baka so na Maryam ak ke so to ni na yi maka alkawani
zan hakura domin bai kamata in dinga zama da abinda ba
ya kaunata ba!" Cikin mamakin jin wannan magana mai
kaam da saukar bindiga ya dago kai ya kalleta ido cikin
ido ya ce "Samecra wai wacce irin magana ki ke fada
min ne" Ta ce "Ai ga ra in san matsayina a wurinka, in
ina da shi, in babu in san abinda na kama domin ba zan
zauna ina shukar dusa ba". Ya ce cikin wani sabon
mamakın "Waı Sameera shakkar kaunar da nake yi miki
ki ke yi ne har yau?" Ta ce "Ai ba wai shakka ba ce, gani
na yi in ba haka me zai sa ka ki barnina inje sunan
Maryam?"
Ya yi murmushi ya ce "Ashe wai dama duk
wadannan maganganun saboda ban amince ki je suna
Maryam ba ne?" Ta ce "Saboda haka ne". ya ce "To ki
kwantar da hankalinki wallahi ba don komai na hanaki
ba sai don ganin baki da lafiya, kuma wurin nan ba ma
kasar nan ba ne shi ya sa". Ta ce "To in dai haak ne ai
can inda zanin ma gida ne". Y ace "To in haka ne na ji ki
86
Kwadayı bar jana Amuna Abdullahu Sharada
je ai ban san irın zargın da kıke yi min ba, ashe gani kı ke
har yau ina son Maryam To ai ni tunda Allah ya dasa
min sonki a rai na daina ko tunanin Maryam ma".
Ta yi murmushin jin dadin maganarshi ta ce "Ai
wallahi da ni na saka tsanar Maryam a rai na saboda kai
amma yanzu na zare". Ya ce "Ai gara ki cire domin a
yanzu ba wata a gabana sai ke Sameera!"
Gidan Alhaji Usaini ana ta faman shirye-shiryen
zuwa suna, haka ma gidan Alhaji hassan tuni Hajiya Rukayya ta kammala na ta shirin musamman Alhaji
Gambo ya turo musu kudi ta account din Alhaji Usainı
cewa su rage kudin jirgi. Bayan ya karbo ya ce "Ai
wannan ya fi karfin ragewa sai dai a biya baki faya".
Nan dai ya kaşa ya kaiwa Alhaji Hassan na shi kason,
sannan suka shirya abinda zasu saya su tafi musu da shi domin tsaraba.
Hajiya Jamila na zaune shirim a falo, sai ga Halima
'ta shigo ita ma ta zauna. Hajiya Jamila ta kalletą ta ce
"Wai ke Dubu da 'ya'yan zaki tafi baki daya ne?" Tа се
"To Aunty wa zan barwa? In har za'a dani ai ya zama
dole in tafi da yarana". Ta ce "Lallai kam, wa ya ga
yuya?" Ta ce "Ai ni ban ga yawansu ba ma, yaran uku en
fa kacal?" ta ce "ai sai ki yi ta zuwa da su!" Ta mike ta
shige cikin daki abinta ta bar lHalima nan zaune, to dama
Halima ta saba da irin wannan halaye na Hajiya Jamila
don haka ba ta damu ba, ya ci ace sun daidita a junansu,
amma duk yawan shekarun nan har yau ba sa wani
jituwa shi kansa Alhajin ya yi ya gaji kuma laifin na
Hajiya Jamila ne ko kadan ba ta kaunar Halima da
yaranta don dai kawai Alhajin ya na tsaye a gidansa en
shi ya sa ake samun saukin lamarin.
87
Kwadayı han jana'- Amina Abdullahu Sharada
Yau sauran kwana biyu ayi tafiyar Alhaji na
dakinsa a zaune, wato Alhaji Usaini, lajiya Jamila n
gefensa ta kawo masa abincin dare da ya ke ita ta y
girkin, ya na ci ta na zaune suna hira, a hankali ta takul
maganar tafiya domin ta haan ayi da Halima, ta dubi
Alhaji ta ce "Alhaji Halima ba ta jin shawara". Ya се
"Kamar ta me fa?" Ta ce "Wai dazu ne na ce ma ta dama
ta hakura da tafiyar nan tunda babu inda za ta kai yaran
nan shi ne ta ke ta faman gaigaya min maganganu har da
su gore-goren haihuwa". Alhaji ya ce "To ke don em za
ki ce ta hakura bayan ta na doki ta je?" ta ce "To ai gani
nayi yanzu ba wai fata ake ba, wannan tafiyar Allah ya
kiyaye a samu wani hadari akan hanya ka ga duk 'ya'yan
aka kwashe aka tafi dasu ba a rage ko daya ba, ya kamata
in za'a dinga tafiya in yaran mutum biyar ne ya debi biyu
ya bar uku, to amma tunda ita babu inda za ta kai su ai
sai ta hakura in yaso in mun dawo taje tunda zuwan ya
zame ma ta dole!" Ya ce "Eh to maganarki kam akwai
kamshin gaskiya kin san ita Halima ta faye taurin kai ina
ta ke, kira min ita yanzu ma". Ta ce "To". Ta mike cikin
doki ta nufi dakin Halima, ta na zuwa ta sameta ita da
'yan yaranta har sun kwanta ta ce "Ki zo inji Alhaji".
"To". Ta се ma ta, ta taso yayinda ita kuma ta juya. Ta na
shiga ta durkusa ta ce "Ga ni Alhaji". ya ce "Yauwa
dama kiranki na yi in gaya miki wannan tafiya an fasata
da ke, ki yi zamanki ki kula da yaranki tunda kin taba zuwa".
Ta na jin abinda ya ce, ta yi sak, don ta san ba
makircin kowa ba ne sai Hajiya Jamila, ba tare da ko
musu ba ta ce "Shikenan Alhaji ai ka san ba na ketare
umarninka, duk abinda ka ce inyi dai-dai ne". Ya ce
88
Awadyr bartjana!- Auna Abdullahı Sharada
"Yauwa na gode mi ki Allah ya yi miki albarka".
"Amin". Ta ce mishi, ta mike, ta ficce daga dakin, ta
koma kan gado ta na ta faman tunanin abinda Hajiyа
jamila ta ke ma ta, inda sabo ma ya ci ace ta saba.
Tunda safe suke shiri domin tafiya suka gama
shirinsu suna haramar tafiya, Auwal ya makalewa Alhaji
Usaini, wai sai ya bi su, shi ko ya ce da Halima hado
masa kayansa ma za mu tafi". nan da nan ta tashi cikin
murna, ta san ko ba komai dole ran Haljiya Jamila ya
sosu, ta ahdo masa kayansa a 'yar jakarsa ta mika wa
Alhaji Usaini, ya karba ya ce musu "Ku muje". Tunda
aka ce za'a tafi da Auwal Hajiya Jamila ta yi dif da ita,
babu walwala har suka fila. Halima na musu adawo
lafiya, Alhaji ne kawai mai amsawa, ya an yiwa Zainab
wasa ya an cewa "Ko ke ma zaki ne?" Halima ta ce
"Haba Alhaji ai sai su yi muku yawa". Murmushi ya yi
ya ce da direba ya ja motar su je gidan Alhaji Hassan
sannan su tafi tare.
Can kuma bangaren masu jego ana ta shiryeshiryen suna da tarbar baki ko da ya ke sunan can ba irin
na nan bane domin lamari ne na jajayen fata, to amma
tunda lamarine na musulunci to an sami banbanci a
wajen taron da wanda suka saba yi domin iyayen
musulmai ne, suka rada sunan da ranar sunan ta zo, aka
radawa yaro suna Abubakar Saddik, kowa sai sa masa
albarka ya ke yi, nan aka yi ta shagali har dare.
Kwanan su Hajiya Jamila biyar suka komo gida,
aka bar Maryam da kyakkyawon jaririnta Saddik, suka
rabu akan in ta yi arba'in zata zo ta ga gida. maryam ta yi
ta murna domin rabonta da gida yau ku san shekararta
guda da rabi kenan. Ita kuwa Sameera ba ta komo a
89
Kwadayı bari jana'- Amina Abdullahı Shara da
wannan lokaci ba, don su Alhaji cewa suka yi ta zauna
sai ta kara ganin gida ta koma, ran Bashir bai so ba, to
amma haka ya hakura don jin kunyar iyayensa da har ya
fara murna Alhaji Gambo ya ce ba za ta zauna ba, to sai
kuma murna ta koma ciki, don Alhaji Hassan da Alhaji
Usaini sun dage akan ya kyaleta sai ta gaam gaisawa da
'yan uwanta. Haka ya hakura ya kyaleta akan dole, don
gani ya ke kamar ba a kular masa da ita ba, saboda cikin
da ke jikinta har Hajiya Rukayya ya samu a gefe daya ya
ce ma ta "Mama don Allah ki sa baki a bani Sameera mu
tafi, kinga ba ta da lafiya, ciki gare ta a kullum sai faman
amai ta ke yi". Hajiya Rukayya ta ce "Au sannu gwani,
wato nan ba za'a iya kula da ita ba kenan ko? Sai kai
wato uwarta ma da ta raine ta har ta girma har ka samu
ka aura ka fi ta iya kula da ita ko?" Cikin jin kunya ya
zame ya tsere ya na sosa keya.
Tunda suka komo gida Bashir ya zamo tamkar
wani maraya, don gidan sai ya yi masa fadi, hakika
yanzu kam ya na bala'in kaunar Sameera don shi a yanzu
ba ya ko son ya ga Maryam ko don yanzu muharramarsa
ce? Oho! Da suka je suna ma ya yi mamakin abinda ta yi
masa a da ya dauka zata kulashi kamar da, sai kawai ya
ga ta wani dauke masa kai kamar ab ta san ma daga inda
ya ke ba, Allah Sarki bai san irin yakin da Faruk ya sha
ba kafin ya shawo kanta ta so shi ba, wannan zuwan ma
sai da ya ji fargabar kar ta ganshi ta kara rikice masa, sai
gashi abin mamaki duk abin da yake zato babu wanda ya
samu sai ma wani tsana-tsana da take d'an nunawa Bashir
din, to sun dai tafi kuma ya na zaune lafiya da matarsa da dansa Saddik tsakanin Sameera da Maryam kuwa sai
wasa da dariya in sun haďu suna hira sai su kai sha biyun
90
Kwadayı barı jana!- Amına Abdullahı Sharada
dare, Maryam ta na tambayarta game da gida, da ya ke
bata samu damar zama sunyi hira da su Hajiya ba, har
suka koma gida, amma ta ce ta na yin arba'in zata je
ganin gida.
Faruk ne zaune ya dauki jaririnta Saddik ya na
masa wasa kamar wani mai wayo. Ita kuma Maryam na
can gefe daya ta an kishingide ta nai masa hira, wata ya
amsa, wata kuma ba ya ji, hankalinsa na wajen Saddik
har dai Maryam ta gaji ta ce "Ni ko Faruk ina tsoron
ranar da zanyi magana ka ki dauka Saddik ya yi ka
karba". Ya juyo ya kalleta ya ce "Kamar ya ya?" Та се
"To gani na yi ko hira na ke ma ka baka saurarona in
azaton dai wala rana ma sai na yi kamun kafa da Saddik
sannan zan tambayi abu a wurinka". Ya yi dariya "Ke
kuma kina kishin haka ko?" Та сс "A'a ba kishi na ke
ba". Ya ce "Kishi ne mana, lallai ma Maryam to kina
kishin dan ki ina ga kuma in karo aure?" Ta yi saurin
mikewa zaune "Aure Faruk?" Ya ce "A'a to haramun
ne?" ta ce "A'a, ba zancen wasa ba da gaske aure zaka
yo?" Ya ce "In Allah ya kaddara ai sai inyin...." "Kaikai-kai don Allah daina fada kar 'yan amin su amsa,
wallahi ka fadar min da gaba, a gaskiya yau ban san irin
baccin da zanyi ba". Ya ce "Bare kuma ace yau ga shi na
yo ta ba?" Ta ce "to ka yo mana har da wani nanatawa,
wallahi ta na shigowa ni kuma ina barin gidan". Ya се
cikin dariya "Ina zaki je?" Ta ce "In koma inda na fito
mana". Ya yi murmushi "Ina ne inda kika fito?" "Oho!"
Ta ce mishi cikin nuna alamar fushi, ya kuwa kwashe da
dariya ya ce "Kinga hakan da kika yi har kin tuna min
wani wasa da na gani a can nigeria na su dan ibro wai
sai abokin tafiyar tasa suna cikin tafiya su biyu
91
ya ce
Kwadayı han jana'- Amına Abdullahı Sharada
"yanzu dai muna cikin tafiyar nan mu tsinci kudi". Sai
ibro ya ce "Da sai mu raba". Dayan ya ce "Ai anwa sai
ya fi naak yawa". sai kuwa Ibro ya ce "Don me naka zai
fi nawa ba tare muka tsinta ba?" Ya ce "Aiko ba za'a raba
dai-dai ba." Nan fa fada ya sarke har da kwabe riga aka
fara dakuwa tun kafin a tsinci kudin, to yau sai kike
gwada min". Maryam ta yi ta dariya ta ce "Ai su su Ibro
nasu mai sauki ne ni fa kishiya ka ce? Tabdijan Allah ya
tsare ni da ita". Ya ce "To wai saboda me ba kya son ayo
miki kishiya ne?" ta ce "Saboda na fi son in mallakeka ni
kadai ba na son mu dinga musayarka da wata". yayi
dariya "To ni kuma in na gano wata ina so fa?" Ta cе
"yanzu saboda Allah duk kyautata ma kan da nake yi har
sha'awar aure ka ke yi?" Ya ce "No wannan daban, kin
san sunna ce kuma wata rana zan zamo mai sha'awar yin
hakan don haka na ke so ki saba da zancen tun kafin
lokacin ya zo".
Ta ce "lallai faruk ni dai to ba na son zancen". Ya
ce "To an daina shikenan?" Ta yi murmushi ya ce "Wai
ni Faruk na ga tasku a da lallai so so wani abu ne, duk
irin kayar nan da ki ka dinga yi min ba na gani". Ta ce
"to me kuma ya akwo wannan zancen?" Ya ce "Tuna
baya!" Ta ce "Ka fara ba? Ni ka ga ma baccina zanyi". ya
ce "ai wallahi ba ki isa ba, sai kin tashi mun yi hirar". ta
ce "To wai ba ka rama ba? To kuma me ka ke so ayi?"
Ya ce "Bai ramu ba". Ta ce "Kamar ya ya bai ramu ba?"
Ya ce "Wancan karon kin sa mun samu Saddik ba ta
hanyar nutsuwa ba, to wannan karon zamu samu kaninsa
ta cikin nutsuwa". Ta na jin ya fadi haka ta yi saurin
mikewa tsaye ta na cewa "Faruk yau fa kwanana talatin
da biyu, amma ka ke min wannan batu?" Ya janyo
92
Kwadayı ban jana!- Amına Abdullahı Sharada
hannunta ya ce "Ina zaki je?" Ta ce "Ni dai cikani?" Ya
ce "to ai a dakinki muke, ina kuma za ki?" Tа се "Ка
cika ni mana ka ga inda za ni?" ya ce "Na ki, wayon ki
gudu ne". ya janyo ta jikinsa ta na kokarin kwacewa ya
maida bakinsa a nata, shikenan sai jikin ya mutu ab ta
san lokacin ad shaukin so da kauna ya sa ta mai da masa
martani ba.
Sameera kam sai da ta samu cikakkun wata biyu
sannan ta koma, shi ma din Bashir ne ya daemsu da
waya gashi dai ba zai iya cewa ya na so ta komo ba, to
amma fa sai faman kiransu ya ke a waya yau in ya kira
wannan, gobe sai ya kira wancan har dai Dad ya gaji ya
če da Mum "Wannan yaron Bashir na san fa abinda ya ke
yiwa yawan waya, so ya ek matarsa ta koma, saboda
haka a wannan satin za ta tafi". Mum ta ce "Ni ma ina da
niyyar gaya maka haka, ai gara ta koma gidan ai ta
zaunu". Ya ce "Yauwa ai gara ta koma yanzu me za'a
shirya mata na komawa?" ta ce "Ba abinda zata tafi da
shi sai dai a tura musu kudi a banki kawai". Ya ce "to
shikenan".
Kwana uku da wannan maganar sai kawai suka fara
hadawa sameera kayan ta, don kashe gari za ta wuce,
haka ko aka yi da ranar ta zo, suka sa ta a jirgi sai
nigeria Bashir na gida a zaune bai fita ko ina ba, ya ji
sallamar Sameera cikin mamaki ya ce "Yaushe kika zo?"
Ta ce "Saukar kenan". ya ce "Wa ye ya dauko ki daga
airport?" Ta ce "Motar haya na hawo". Ya ce "To me ya
sa ba ki yo min waya ba?" Ta ce "To ai ban san uzurin da
ke gabanka ba shi yasa ya ce karka kara yin irin
wannan". "Ai ko ni baki yo min ba sai kijewa su Abba
dasu Abban gidan su Maryam". Ta ce "To ni dai wallahi
93
win ha LAAitalu Sharnf
ban kira kowa" Ya ce "To ya su Mum da Uncle?" Ta
"Suna nan lafiya, ka san kuwa Dad ne ya ce lallai in t
bo Ya ce "Aı ya kyauta kına can kin barni da kewarki
Ta ce "Dama ai sarda na ayyana". Ya ce "Yanzu ke da
basu ce ki taho ba, ba zaki taho ba kenan ko?" Tа y
murmushi "Haba Bashir mahaifa fa aka ce ma?" Ya ce
"A'a lallai, ai ko baki fada ba na sani"
Tayi murmushi "Ashe na mance na bar dan tasi da
kaya a mota, zo muje ka taya ni daukowa". Ya ce "A
ina mai gadi, baya nan ne?" Ta ce "Ban ganshi ba". Ya
ce "To muje Haruna mai wanki na san shi ya na nan don
yanzun nan ya gama guga".
Nan dai duk ta yi wa su Hajiya Jamila waya a
komo da su Hajiya Rukayya, wato mahaifiyar Bashir
kenan, sannan shi kuma ya sanarwa su Abbansu, nan dai
suka yi ta bugowa sunai mata sannu da zuwa, kuma ta yi
wa can gidan nasu waya cewa ta sauka lafiya, ta samu
kowa lafiya
Bayan kamar wata guda da dawowar Sameсrа
Maryam ta yo waya cewa ita ma ga ta nan zuwa, nan aka
yı ta shurin taryar ta, cikin doki da murna.
Kwana biyu kuwa da yin wannan maganar sai ga
shi ta yo waya cewa ta iso, ta kuma bukaci Abba ya aika
a dauko ta, dai-dai misalin hudu na yamma Abba ya
amsa mata da to.
Lokacin na cika da kansa ya tafi daukota ya ko yi
sa'a saukarsu ke nan taan hango shi ta rugo da gudu tana
murnar ganinsa, ya amshi jinjirin ya rungume ya na
faman murna har dai wani lokaci sannan ya dauki kayan
nasu ya sanya a boot suka taho gida suna ta faman murna
da farin ciki.
94
Kwadayı barı jana!- Amına Abdullahı Sharada
hannunta ya ce "Ina zaki je?" Ta ce "Ni dai cikani?" Ya
ce "to ai a dakinki muke, ina kuma za ki?" Ta се "Ка
cika ni mana ka ga inda za ni?" ya ce "Na ki, wayon ki
gudu ne". ya janyo ta jikinsa ta na kokarin kwacewa ya
maida bakinsa a nata, shikenan sai jikin ya mutu ab ta
san lokacin ad shaukin so da kauna ya sa ta mai da masa
martani ba.
Sameera kam sai da ta samu cikakkun wata biyu
sannan ta koma, shi ma din Bashir ne ya daemsu da
waya gashi dai ba zai iya cewa ya na so ta komo ba, to
amma fa sai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 12