to ayi shi tun akan lokaci". Ta се
"Gaskiya ne
Kashe gari bayan sun karya sai ya kira Faruk waje
daya ya tambayeshi abinda ya ke ciki, wai nan ta ke ya
fada ma sa, ya ce "To ita fa ta na sonka?" Ya ce
"Gaskiya Abba wai wani ta ke so!" Ya ce "Ba wani ba
ne, bashir ne, shi kuma mahaifinsa ya ce ba ya son hadin
zumunci, don haka ba zai amince ba, yanzu abinda za'a
yi sai in sanarwa shi Abban nata mu ji abinda zai ce ko?"
Cikin dokin jin abinda mahaifinsa ya fada game da
Bashir ya amsa da "To Daddy". Sannan ya ce "To tashi
ka je, sai anjima zan sake kiranka inji abinda ya ce.
Sun dan juma su na hira da Alhaji Usaini ta waya,
kafin ya furata masa makasudin yin wayar, ya na gama
furta masan, Alhaji Usaini ya yi farin ciki matuka, ya се
"Ai dama wani hanin ga Allah baiwa ne, yanzu ba gashi
Allah ya musanya ma ta da alherinsa ba, ni yanzu abinda
na ke so da kai kawai ya sanar ma ta in yaso abinda suka
yi sai a fada mun, in ma ta ki ai aure ba fashi, yo don
15
Kwadayı harijana'- Ammna Abdullahı Sharada
ıyayenta haka za ta yi ta zama babu aure? Sai ayi komai
anan ba sai kun dawo nan din ba, domin in ta ga anan ne
sai ta fi bijirewa". Ya ce "To shikenan sai ka kuma ji
na". Suka yi sallama ya kashe wayar.
Babu abinda bai sanarwa Faruk ba. Faruk ya yi
murna sosai cikin doki ya tashi ya shiga dakin maryam a
sameta a zaune, gefen gado ya yi ma ta sallama ta amsa
gami da dubansa, sannan ya samu wuri ya zauna, ya
dubeta "Maryam !" Ta ce "Na'am". Ya ce "A gaskıya ba
zan boye miki halin da na shiga game da ke ba wallahi
Maryam ina kaunarki sosai, kuna ina tunanin in na gaya
miki ba zaki amince da ni ba, duk da haka sai na gaya
mikin". Kallo daya ya yi ma ta ya fauke ido, domîn ya
san bai samu karbuwa ba, amma duk da haka, ya yi shiru
ya ji irin amsar da za ta bashi, cikin sheshshekar kuka ta
mike tsaye "Yaya sanin kanka ne dai bani da wanda na
ke kauna fiye da Yaya bashir, domin Yaya bashir shi
kadai ne wanda na fara sawa a cikin zuciyata, kuma ba
zan iya canza shi da wani ba saboda haka ka hakura kar
ma wani ya san wannan magana don Allah ka taimakeni
Yaya!"
Shiru kawai ya yi, ya na tunani, lallai ne duk abinda
ta ce ya yi, zai yi to amma banda wannan bukatar domin
ba zai iya bin umarninta ya cuci kansa ba, don haka ya
dago kai ya kalleta yayinda ita kuma ta tattara hankalinta
don ta ji irin amsar da zai ba ta. "Maryam Allah ya sani
ina matukar kaunarki, a gaskiya da za ki farka zuciyata
da kin tabbatar da abinda na fada miki, sai dai ina ganin
tunda son Bashir ya ri ga ya mamaye miki ta ki zuciyar
ba zaki gani ba, ni na san a maimakon haka ma duk
abinda zan miki na farantawa a tsana zai kare a wurinki,
16
Kwadayı barjana!- Anina Abdullahı Sharada
to amma ina so ki sani Bashir mahaifinsa ba zai amince
ya aureki ba, because shi wani irin mutum ne mai
tsattsauran ra'ayi, ni kaina da na ji irin abinda ya faru na
yi bakin ciki sosai.
Domin ke kin riga ya kin bada ta ki kaunar gareshi,
amma iyayensa sun ki amincewa, kuma ina mai
tattabatar miki ba zai amince din ba domin kuwa shi
kaifi daya ne, in ya so ya so, in ya ki ya ki don haka ki
bar kaunar Bashir ki so ni, zaki same ni mai rike miki
alkawarai kuma mai cikakken kaunarki”.
Duk wannan maganganun jinsa ta ke tamkar ya na
ma ta kade-kade aka domin sun dameta Allah-Allah ta
ke ya gama ya fita, ya ma za'ayi ban da son kai ya ce
wani ta ki Bashir ta so shi? To a wane dalili ma ita ya ma
daina shigo ma ta daki kawai saboda shi ma za ta dinga
kulle dakinta, ya ma daina shigo ma ta aikin banza
kawai.
Shi kuma shiru ya yi ya na sauraren abinda za ta ce
ganin ba ta bashi amsa ba, ya yi zaton ko ta amince ne,
don haka ya mike, kar ma ya yi wata magana ta ce ta
fasa, cikin hanzari ya nufi falon Babansa ya same su
zaune su an hira da Mama, cikin doki ya ce "Dad ta
amince fa". Ya ce "Da me?" Ya ce "Da ni, kuma ka
kirata ka ji". Ya ce "To kirawota".
Ya na shiga ya sameta zaune ta na tunanin wai ita
ya za ta yi da rayuwarta ne, yanzu in ya je kuma ya
gayawa iyayensa da wane idon za ta kallesu? A gaskiya
ita sam ba ta san me za ta yi ba, ita dai kam ta shiga uku,
wannan wane irin abu ne?....
"Salamu alaikum". Ya ce lokacin da ya ke kokarin
shigowa cikin dakin. "Wa'alaika salamu". Ta amsa
17
mishi
Kwadayz Nanan hullaht harada
Ya shigo ya ce "Ki zo mji Dad" Ta zaro ido cikin
fargaba "Me ka ce musu ne Yaya?" Ya ce "Ke dai ki zo
mana?
Cıkin fargaba ta mike ta fita ba tare da ta ko kalle
shi ba, shima ya bıyo bayanta har cıkın falon Daddy
kanta a sunkuye ta durkusa ta na sauraran abinda zai ce,
yayın da shuma ya durkusa din ya na sauraren me zai
biyo baya, amma idonsa kirr akan Maryam.
"Na ji sakonki" Gabanta ya fadi ta ce a ranta "To
me ya ce musu kuma?"
Ya katse ma ta tunani da cewa "Tunda kin amince
zan yiwa Alhajı waya ya zo ayi abinda za'ayi domin a
bar ya huce shi kewo rabon wani". Ta dai ji cewa zai
gayawa Abbanta ta amince wanda sakamakon hakan ne
ya janyo ma ta rudfewar da ba ta gani sosai sabo da tsabar kidima.
Da hasashen hanya ta bar dakin yayinda ta lalubi dakinta, shi ma kuma laruk ya fuskanci halinda ta shiga
don haka ya mike ya bi bayanta, shi ko Alhaji Gambo sai murna ya ke yi don ta amince.
Nan da nan ya kira Alhaji Usaini a waya, ya sanar da shi abinda ake ciki, ya ce "Kuma ya kamata ya zo ayi abinda za'ayi".
Alhaji Usaini ya ce "Ai da shirina zan zo don in na zo bikin za'ayi kawai, za kuma mu zo da su Hajiya da
"Watannan
Halima". Ya ce "To shikenan, yaushe za ka zo?" Ya ce zamu zo insha Allahu". Ya ce "To sai kun
sai
zo".
mu
Ya aje wayar, ya dubi Husna ya ce "Kinga shikenan
"To
fara shirin biki don in sun zo za'a yi bikın. Ta ce yanzu Alhaji ina za su zauna ke nan?" Ya ce "Gidan
18
Kwadayı barıjana!- Amina Ahdullahı Sharada
nan ba sama da kasa ba ne, gashi mayalwaci? Ai sai su zauna a saman kawai ba ruwansu da kowa" Ta се "Shikenan Allah ya bada zaman lafiya". Ya ce "Amin". Ya na ta murna.
"Na shiga uku Yaya, na shiga uku, yanzu ya zanyi da raina, ka san sarai da wanda na ke so amma ka je ka
ce musu kai na ke so? Yau ya zanyi, ni da na mutu ma na huta da 6acin ran nan wallahi da ya fi mun".
"Maryam ji ma na? Ji nan Maryam ki kwantar da hankalinki wallahi ina Kaunarki kuma wallahi na fi
Bashir sonki don da ace ni ne haka ta faru kaina wallahi
sai anyi auren, amma Bashir ya kyale, ke ma kin san bai damu da ke sosai ba. Maryam ki daure ki so ni, wallahi ni mai kaunarki ne.
"Bana sonka! Ba na kaunarka! Wallahi ga ra in
mutu da in aure ka Faruk, ka janye maganar auren nan don babu alheri a cikinsa....."
Shi ma ya katse ta "Me ye na rashin alherin? To ni
na amince in aureki ki kashe ni in har ke ki ka zama ajalina ba zanyi bakin ciki ba don ina tsantsar kaunarki” Shiru kawai ta yi ta na kuka "Yau na shiga uku, yau ya zanyi da raina, wallahi gara ma na mutu, wayyo Allah Bashir!" Sa fuskarshi ya yi ya na sauraren abinda ta ke fada kawai, don shi wannan kalaman ma dadi suke masa
in har anyi auren zance ya kare, domin zata so shi ne yau da gobe, shi dai aikinsa kawai hakuri, shi hakuri ya kama dole ne kuma ya yi shi duk abinda za ta yi ya dauke kai kar ma wani ya ji.
Tun daga wannan rana shikenan Maryam ta zama abin tausayi ko abinci ba ta iya ci, don kar iyayen su gane halinda ta ke ciki, Faruk ya ce a dinga ba shi 19
Kwalayı barijana Amuna Abfullahı Sharadа
abincınta ya na kai ma ta, a kullum shi zai kai ma ta
abinci, kuma sai ya yi fama da ita kafin ta ci wani
lokacin ma sai dai ta kl ci, haka zai hakura ya dawo
dashi amma shi ma ya na cikin damuwa domin yawan
tunani ya dameshi, shigar Maryam cikin wannan halin
shiga sanya Faruk ya shiga cikin damuwa ko abinci ba ya
iya ci shi ma duk ya rame kamar yadda Maryam din ta
rame, kuma ba ya bacci sosai, don haka sai ya fara
tunanin da ma ayi sauri ayi auren kawai in har an ri ga
anyi ya san zai samu nasarar shawo kanta in ta na kusa
da shi.
***
l'amarin Yalwa kam, sai da tsufa ya zaike Ama ta sannan ta fara ganin rashin amfanin
sangartar yara domin duk 'ya'yanta babu mai tsayawa ya
taimaka ma ta, dama shi Malam Usman sunyi sallama da
yaransa domin shi duk abinda suka kawo ba ya karba in
ma sun kawo din domin sai su shafe wata uku basu basu
komai ba, mai dan dama-daman ma shi ne Auwalu amma
Lawan ai abin ba sakainan doba domin shi ko gidan ma
bai faye waiwaya ba, in har ka ganshi a gida to sai dai in
zuwa ya yi ya rori wani abin ya sayar ba shi da kudl shi
ne zai dawo gashi yau su yi fada da wannan, gobe su yi
fada da wancan, jibi su yi da wannan.
Yau Baba Abu ce ta je gidan Yalwa don sa da
zumuncinta da yaranta biyu wato Safiyya da Saudat,
dama ta saba in zata zo sai ta sako su a gaba su zo tare
domin halin dan yau in tace su zo su kaďai kowacce ta na
sabgarta ba mai zuwa akan lokaci.
20
Kwadayı barjana'- Anuna Abdullahi Sharadn
Ita kuma Yalwa ta tsufa ba ta ma yawaita fita mai
nisa sosai ba. Baba Abu ta ce "Wai ni ko Yalwa har yau Asabe shiru babu ko labari ko?"
Ta ce "Ina? Asabe ai ko duriyarta ma ba a ji, ko ta
na ina? Oho!"
Baba Abu ta ce "To wai su wadannan yaran haka
za a sa musu ido su yi ta abinda suka ga dama?" Yalwa
ta ce "To Abu ya zan yi? In na yi musu fadan ma ba sa ji,
yanzu ki duba ki ga yaran nan Lawan in banda aikin
dauko magana ba ya komai, kinga fa jiya suka yi fada da
wani mutum ko abonkinsa ne oho wai ya sare shi aka, shi
ma aka yi kararsa yanzu ya na can a tsare, sun ce beli
dubu uku, to yanzu ni da dubu ukun wa ya ajiye wani?"
Abu ta ce "Kai wannan amsifa Allah ya tsareta,
yanzu to me ake ciki?" Ta ce "Ya na can dai a tsaren sai
yadda ta yiwu". Baba Abu ta ce "Halima ta sani?" Yalwa
ta ce "Ba ta sani ba, abinda jiya-jiya aka yi abin?" Та се
"Wai shin ta na zuwa gidan nan kuwa?" Yalwa ta ce "Ai
tunda Halima ta yi aure ba ta faye zuwa ba, wai ba ta son
mijinta ya zo ya ga irin abinda ya ke faruwa a gidan
nan".
Baba Abu ta ce "Amma ko ba ta kyauta ba, ai
hannunka ba ya rubewa ka yanke ka yar, dole ne ta dinga
taimaka muku, amma ba ri zanje in sameta ni sai na ji
raina ya ma baci wallahi, ba ra dai inje yanzu, ina fita
can zan zarce, wannan ai rashin hankaline, iyayenka ai
iyayenka ne komai lalacewa".
Nan ta mike suka yi sallama ita ta tafi gidan Raba
Abu su kuma su Saudat kowa ya kama hanyar zuwa
gidan mijinsa.
Sallamar Baba Abu ce ta sa Haj. Jamila da ke da kc 21
Kwadavı ban jana- Amına Abdullahu Sharada
aune a falo bude ido ta yi saurin tashi "Au Baba
sannunku da zuwa, ku shiga ta na cikı". Suka tsaya
domin su gaisa, ta ce "Ku shiga zan zo ne mu gaisa". Ta
ce To"
Ta shiga, ta samu Halima zaune da Walid a hannu
ya na wasansa, ganınta ya sa ta yı saurin tashi ta tare ta
da murnarta ta na tambayar "Baba daga ina haka?" Ta се
"Daga gidan Yalwa na ke". Ta ce "Ince ko da lafiya?" Ta
ce "Lafiya kalau” Sannan ta zauna.
Halima ta mika ma ta Walid, ta dauko ma ta ruwa
da lemo sannan ta zuba ma ta abinci, ta na zama Hajiya
Jamila ta shigo suka gaisa sosai sannan ta fita.
Bayan Baba Abu ta gama cin abincin ne ta dubi
Halima ta ce "halima wai ko kina zuwa gidanku?"
Halima ta ce "Ina zuwa baba, amma ba sosai ba". Ta ce
"To me ya sa?" Ta ce "Baba ina bakin cikin inje gidan
nan in dinga ganin 6acin rai”. Ta ce "Au ko me za ki
gani ya zama dole ki je domin gidanku ne ba ki da inda
ya fi shi, sannan wadancan tsofaffin su Yalwa da malam
yakamata a yadda Allah ya buda miki din nan ki dinga
taimaka musu domin a yanzu ne ya kamata ki dinga
samun albarkarsu, muddin kina taimakonsu ba za ki tab
tabewa ba, iyaye ba abin yarwa ba ne.
Kuma kinga yanzu kina ganin su ki na kin yi musu
in har sun mutu sai kinyi da kin sani, domin ba kya
ganinsu, a da dai ki na ganinsu ki na kin kyautata musu
sai bayan babu su ki zo kina son ganin su ki yi musu,
sabo da haka yanzu ke ce farin cikinsu ke ya kamata ki
dinga kyautata musu ki samu albarkarsu ki wanke musu
zuciya bisa ga bakin cikin sauran 'ya'yan da suke cusa
musu kinji ko?"
22
Kwadayi barijana!- Amuna Abdullahı Sharada
Halima cikin hawaye ta ce "To Baba insha Allahu zan yi musu da ma ni wallahi abun da ya ke ban bakın ciki shi ne inje gidan nan inga abinda yaran nan suke yi,
sai inji sam na tsani gidan, rannan fa munje da Alhaji gaida Baba sai muka samu Lawan da Auwalu su na fada, wai Lawan ya sayar wa da Auwalu rediyo don haka ba
zai yarda ba sai ya biya shi, wallahi Baba fada suke sosai
har da yanke-yanke suka yiwa kansu jina-jina. Baba Yalwa na waje sai faman kururuwa ta ke azo a taimaka
ma ta kar su kashe kansu, amma babu wanda ya kula ta
sai ma zaginta da ake a boye, wai wa zai shiga fadan
'yan daba su je su sara shi, wallahi Baba ana cikin
wannan abin sai ga mu ni da Alhaji da har Aunty Jamila
ta ce za ta bi mu ta gaishe shi, sai Alhaji ya ce kar a bar
gıdan ba kowa sannan ta hakura ke da ta zo ai da na
shiga uku da gori.
Shi yasa fa har yanzu su Lawan har Asaben ban
bari sun nan gidana ba". Та се "Тo ki na gaya min ya
akai?" ta ci gaba da "Alhajin ya zo ya ga halin da ake
ciki, sai ya tsaya ya raba fadan da kyar Lawan ya na
zaginsa, haka ya biya Auwalu kudin rediyon sannan aka
zauna lafiya. Wallahi Baba ba ki ga kunyar da an ji ba,
har ce wa na yi na daina zuwa gidan domin tsananin
bacin rai, amma a raina na fada ban gayawa kowa ba
Ta ce "To ya za'ayi ai dole ne zuwanki gıdan
domin gidanku ne, iyayenki ne kuma suna nan da ransu
dole zuwa ya kamaki in ma ba kya so Alhaji ya je ya ga
wanı abin bakin cikin sai ki daina bari ya na kai ki, sai ki
hau motar haya ki je ko ya sa direbansa ya kai ki", Ta ce
"Ai Alhaji ya na da mugun kishi shi ya sa ba ya bari ana
zuwa unguwa ba tare da shi ba, bai ma yarda direba ya
23
Kwadayı barijana!- Amina Abdullalu Sharada
kai mu ba sai bi sa lalura, babu yadda za'ayi". Ta cсе
"IHaka dai za ki dinga zuwa shi kuma ai dole ya gani ya
kl gani, ya ji ya kl ji"
Та се "То, ya za kı yi, sai dai hakuri da ma". Haka
suka ci gaba da hira har wani lokaci sannan ta yi musu
sallama ta koma gida.
Shi kuma Bashir tunda aka tafi da Maryam can
Jamus bai sani ba, ba shi da labari sai gani ya yi Abbansa
ya ce ma sa "To yanzu ka na da damar da zaka je ko ina
ne domin wacce na ke gudun kar ku hadu din ma ba ta
nan". Jin haka mamaki ya kamashi ya ce a ransa "Ba ta
nan, kamar ya ya? Tafiya unguwa suka yi, ko kuwa gudu
ta yi? Ai ko in har unguwa suka tafi za ta komo, amma in
gudu ta yi babu magana".
Cikin dai tunani ya fito ya na ta Allah-Allah ya јe
gidan ya san abinda ake ciki, bayan ya je ne ya sami
Hajiya Jamila ya tambayeta "Ina Maryam ta tafi?" Shi ne
ta yi masa cikakken bayani, nan da nan hankalinshi ya
tashi, ya ce "Yanzu wai me ya ke damun Abbana ne?
sabo da Allah kai kadai ne babba a cikinsu, amma ba za
ka tsaya ka ja 'yan uwanka a jiki ku yi ta zumuncinku ba,
sai faman abu iri-iri?"
Hajiya ta ce "To ya za ayi, ai sai hakuri, ita dai
Maryam ta na can ma shi wanda ya ke kaunarta da
gaskiya ai ya amince za a bawa dansa". Cikin tsananin
tashin hankali ya mike tsaye ya ce "Umma wa za ta
aura?" ta ce "Faruk mana". Nan da nan ya dafe kai, ya
koma ya zube bisa kujera, ya ce "Wayyo Allah Umma,
ki yi hakuri a dawo min da Maryam, wallahi Umma ba
laifina ba ne, laifin Abbana ne, Umma ki yi hakuri ki
Tadawa Abba ya yi hakuri, wayyo Allah Maryam wallahi
24
Kwadayı barijana
Amina Abdullahu Sharada
ina sonta ina kaunarta, babu wacce na ke so kamar ta
Hajiya Jamıla ta fara bashi hakurı, amma ina saı kuka ya
ke, shi dai a dawo mishi da Maryam dinsa.
Suna cikin haka sai ga Abba ya dawo shi da
Sameera, dama tare suka fita. Abba na ganin Bashir
durkushe ya na ta faman kuka wurjajan ya ce “lafiya?"
Hajiya Jamila ta ce "Wai lallai sai an dawo masa ad
Maryam
Alhaji ya tashe shi, cikin tausayawa ya ja shi
falonsa, sannan ya fara yi masa nasiha don hankalinsa ya
kwanta, amma ina ya dai yi shiru da kukan, amma babu
wata walwala, haka ya tashi ya sauko kasa ya na cewa
"Wallahi ko za a kashe ni ba zan koma gidan ba, anan
36
zan zauna
Alhaji ya biyo shi ya bude masa daki ya na
rarrashinsa, ya ce "Ai nan gidanku ne Bashir, yi zamanka
ni ma ban goyi da bayan ka koma ba, ga daki nan ka yi
zamanka ka ji ban ce ka koma ba”.
To fa Sameera tunda ta kyalla ido ta ga Bashir
shikenan ta kwallafa shi a ranta, nan ta ke ta ji nan
duniya ban da shi babu wanda ta ke so a rayuwarta don
haka sai ya zamana komai ita ta take yiwa Bashir don ta
samu shiga kamar su sharar dakinsa, kai ma sa abinci,
kuma ta kan je haka kawai ma ta zauna, wai ta taya shi
hira duk da cewa ba ya ko kulata sai dai ta kara cсі
zamanta ta ficce wannan hali na ko inkula ya na damun
Sameera, wani lokacin har kuka ta ke ma sa, amma ko
sauraronta ba ya yi.
Yau ma abinci ta kai masa, ya na kwance da hoton
Maryam a hannu ya zuba ma ta ido kawai ya na kallonta,
ya na ayyano irin dunbin asarar da ya tafka na rashinta
25
Kwadayı harı jana Anına Abdullaln Shanda
Maryam kam ta hadu karshe, babu namijin da zai
mallaki Maryam ya so ta kubee ma sa, shi kam gashi ya
na t va na pani ta fi Karfinsa sakamakon taurin kan
mahaitinsa, hawaye ya gangaro ma sa sabhoda bakin ciki
bai san Sameera na tsaye ba, ya fara sambatu "Maryam
ki dawo gare m. Maryam kar ki amince da kowa in ba ni
ba. Maryam rashinki cuta ne gare ni Maryam ki yi
hakuri kı dawo min wallahi ba ni da kamarki! Haba
Maryam ki tuna irin son da na ke yi miki, yanzu duk
wannan dumbin son da muke yiwa juna ya tashi na
banza ke nan? Wayc zai maye min gurbinki?...."
"Ni zan maye ma ka Yaya in har ka amince Ina
Kaunarka bil-hakk! don haka kar ka ji komai, ni zan
zame ma ka madadin Maryam daga yau
Cikin fushı ya daga kai ya dubi Sameera ya сс "bа
na sonki! Ba na kaunarki! Me zanyi da ke? Ni kar ki kara shigo min daki in ba haka ba wallahi sat na ci mikı
mutunci, banza kawai!"
ta
ta
Duk da cewa ranta ya baci sai ta kanne ba
bayyana ba, ta dai danyi murmushi ta ficce daga dakin
na mai tunanin yadda za ta bullo ma sa, ta san cewa so
abu ne mai tsanani shauki da dama zuciya in har an rasa abin da ake nema.
dakin Halima ta wuce kai tsaye ta sameta zaune da
yaranta a hannu, ta ce ma ta "Aunty Halima a gaskiya ina
son in gaya miki wata magana ki fadawa Abba". Ta ce "To wace magana ce?"
Ta ce "Ni dai ina kaunar Bashir, amma shi ba ya
son ma inyi ma sa magana". Halima ta yi murmushi ta ce
"Sameera kin ga har yanzu akwai bacin ran rashın
Maryam a zuciyarsa, shi ya sa ba zai saurare ki ba, to
26
Kwadayı han jana'- Amna Abdullah Sharada
amma zan ladawa shi Alhajin kila ya shawo kansa ya
amince". Ta ce "To shikenan, ina sauraro".
Hakika Alhaji ya yı na'am da wannan magana,
domin kuwa shi ma da ya ayyana ko ma don su shirya da
dan uwansa don haka ya na jin cewa Samcera na son
Bashir sai kawaı ya kira Bashir din don ya ji ra'ayinsa, ai
ko ta ke ya nuna ma sa cewa shi ba ya sonta sam. Alhaji
Usaini bai ji dadin wannan magaan ba ya ce masa
"Bashir ina ganinka yaro mai hankali bai kamata ka
dinga kawo min abinda zai sani bacin rai ba, wannan
yarinyar 'yar uwa ce a wurinka, a ganina da ka je ka auro
bare ga ra ka aureta ko ba komai zumuncin mu zai kara
kulluwa, saboda haka kar in kara jin kalmar ba ka so din
nan ka ji ko?"
Tilas ya amsawa Abba ba don son ransa ba, sai don
kar ya zamo mai saba umarninsa, amma ko kadan
Sameera ba ta ransa. Abban ne ya katse masa tunaninsa
da cewa "Sai ka je ka sameta domin ku fahimci juna
ko?"
Ya ce cikin bacin rai "Abba ba ma sai na je ba
kawai duk abinda ya dace ayi, to ayı kawai. Ya ce
"Amma ai inka je za ku li fahimtar junanku". Ya ce Ba
komai ni zan sameta", Ya ce "Yauwa dana Allah ya yı
ma ka albarka". Ya ce "Amin".
***
uni har an tsaida ranar daurin auren Maryam da Tl'aruk, amma har kawo yau Faruk bai sami nasarar
shawo kanta ba, sai ma kara nuna masa ki take yi, amma
27
Kwadayı barıjana'- Amına Abdullahu Sharada
a boye domin a gaban iyayenshı ta nuna ta na son auren,
amma in bayan idonsu ne sai ta nuna ma sa tsana karara,
don haka ne ma ya ke son a zauna hira bakı daya domin
ya fi samın kulawarta.
Yau dai ita ce ranar da su Alhaji Usaini da iyalansa
za su zo domın shagalin bikin Maryam da Faruk, tuni har
sun fara shirye-shiryen taryar bakl, Ango kam abin ba
dama, domin da ka ganshi ka san ya na cikin tsananin
farin ciki na wannan aure, yayin da Amarya kuma farin
cikinta daya shi ne ganin iyayenta, tuni har an gama
shirya ma ta komai su ake jira.
Can kusan yamma sai gashi sun yo wayo sun zZO
filin jirgi (Airport) su na jin haka suka shirya domin
taryar su, nan da nan kuwa suka je suka same su ba tare
da wani bata lokaci ba suka taho gida suna ta faman
murna. Maryam kamar ta koma cikin Hajiya jamila
domin murna har Halima ta na tsokanarta "Wai Maryam
ciki za ki koma ne?" Hajiya Jamila ta ce "Ku kyale min
abata ta ji dumina domin daga wannan za'a shiga
kwaryar manya, shikenan sai dai ta shagwaba 'yarta ko
"danta יי
Maryam ta ce "Umma ai dai ba za ki daina riritani
ba ko?" Ta ce "Ai duk sarda kika zo gida sai kin hau
cinya, abincin ki a baki". Ta yi murmushin jin dadl
sannan suka karasa don duk wannan hirar a mota suke
yinta.
Suna zuwa gida Hajiya Husna wato Mum ta taso a
guje ta rungume su ta na ta faman murna kamar ta san su
suma murnar suke ta yi.
Bayan kwana biyu da zuwan su ne, aka sa ranar
daurin aure da ranar ta zo sai aka fara ruguntsumi, a wani
28
Kwadayi hanjana!- Aina Abdullalu Shumda
masallacin juma'a na kaxar aka daura auren akan sadakı
dubu hamsin, sannan suka yi shagalinsu na biki, ta
hanyar yin walima
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 12