ba na son ka kuma janyo wani rikici a tsakaninku, ka
ga zaman aure zaam ne na din-din din, ba wai yau azo
gobe a koma ba, dama ina so in same ka in yi maka
wannan nasihar na ga dukkanku babu wanda ya ke
daukar abinda muhimmanci, na fuskanci akwai wani abu
da ya ke faruwa a tsakaninku.
68
Kwadayı barıjana!- Amina Abdullalu Sharadn
Faruk kai ne babba, kai ne mai hankali kar ka
dakata tata ka biye ma ta ku zo kuna zaman doya da
manja, kai ak kawo don haka kai hakuri ya kaam dole ne
ka dinga hakuri da abinda zaka gani, don samun ci
gabanka, ka ga yanzu nan gaba za ka fara samun yara in
har kuna irin wannan a tsakanínku za ku dinga raba
kawunnan yaranku, kuma in har kuna da mace a ciki ta
na girma ta na ganin abinda ya ke faruwa, za ta dinga
koya ita ma ta na yiwa mijinıta. Ka ga babu ci gaba
kenan? Kuma babu tarbiya saboda haka ba don komai
ake son zaman lafiya da kwanciyar hankali magıdanta ba
sai don kar su barwa aransu abin gadon abin fada, domin
muddin suna irin wannan to tarbiyar yaransu za ta yi
fata-fata har mazan ma don shi da namiji abinda ya ga
mahaifinsa na yiwa ta sa nmahaifiyar haka zai yiwa
matarsa kamar yadda 'ya mace za ta kwaikwayi halayyar
mahaifiyarta ta dinga yiwa na ta mijin. Ka ga ba ki
dayansu tarbiyarsu ta lalace kenan?"
Cikin sanyin jiki ya ce "Na ji abinda ki ka ce
Mum, kuma na gamsu na gode Allah ya saka muku da
gidan Aljanna Firdausi". Ta coe "Amin summa amin".
Daga nan ya mike ya tafi can ya samu Maryam ta gama
aman ta komo falo, ta na kwanc'e ta sa hannunta ta kare
fuskarta idonta a lumshe, ya tsay a a gabanat cikin sanyin
murya ya ce "Maryam me ya k damunki ne?" Ji ta yi
maganar kamar a mafarki, ta yi saurin bude ido ta
kalleshi ta ce "Ai ni babu abinda ya ke damuna". Ya ce
"Amma na ga kina amai?"
Ta na jin haka ta yi murm ushi kawai ta ce ma sa
"Dama na saba ai kullum ne wan nan aman". Ya се "То
me ya sa ba ki sanar min ba?" Tia ce "Yaya ga ni na yi
69
Kwadayı barı jana!- Amına Abdullahi Sharada
kamar baka so in yi maka magana shi yasa ni kuma na ka
sa gaya maka domin gani na ke in na gaya maka ba zaka
dauki abinda muhimmanci ba". Ya ce "Saboda me? Ai
ya zama dole a matsayina na mai gidanki in saurari
uzurinki, kuma in jibanci lamarinki". Ta yi murmushi
"Dama ba wani abu ne ya ke damuna ba wallahi sai....."
Shiru ta yi ta ka sa fada, shi kuma ya na jin haka
sai kawai ya yi shiru ya na kallonta, don ya san kunya ce
ta dameta, a zuciyarsa ya na godewa Allah don a yanzu
ya san cewa Maryam ta na kaunarsa kuma ta yi zurfi,
kallonta ya yi bayan ya matso kusa da ita ya janyota
jikinsa gami da runguma ya ce "Bara in duba ajiyata ko
ita ce ta janyo wannan amaye-amayen?" Hannu ta sa ta
rufe fuskarta cikin jin kunya ta na murmushi yayinda
yanayin kamshin jikinsa ya kara am ta sonshi, hannu ya
sa ya fara shafa cikinta, ya ji shi da dan tudu kamar ta
kifa karamin koko, ya yi murmushi ya ce "Amma
Maryam ba ki kyauta min ba". Ta yi saurin kallonsa a
shagwabe ta ce "Me kuma na yi'?" Ya ce "Saboda me
zaki samu ciki amma ba zaki sanar min ba? ki yi ta amn
dakonsa ke kadai gashi har ya girma".
Kanta ta boye a kirjinsa sannan ta ce "Kai
yakamata ka fara bincikensa domin dai ka san da kunya
in sanar ma ka". Ya ce "To me ye abin kunyar? Wallahi
duk ke ki ka janyo mana gashi shi kansa cikin ba a cikin nutsuwa a ka sameshi ba, ni kaina ban zaci akwai shi ba".
Та се "То ai yanzu komai ya yi dai-dai sai ayi min afuwa". Ya ce doki "Da gaske Maryam kina kaunata?"
Ta lumshe manyan fararen idonta ta ce "Ina kaunarka
Yaya, ai da ni na so in bar jaki in doki taki, a yanzu ne na san cewa na yi sa'ar miji, ga hakuri, ga kyau, ga... Kai ka
70
Kwadayı barnıjana!- Anına Abdullalu Sharada
hada komai da komai ma wallahi!" Ya ce "Kai amma ba
na tunanin na taba samun sa'ar da ta kai ta yau a
rayuwata ba, lallai kam an godewa Allah Maryam ina
kaunarki wallahi kaunarki ce ta kusa hallakani, to amma
na godewa Allah da ya akwo mu lokacin da har ke ki ke
furta min kalmar so da bakinki".
Saukar numfashinta a dai-dai fuskarsa shi ya kara
rudashi da kidimashi har ya fara kidima ya na sakin layi,
ta na ganin haka ta fara bayyanar masa wasu abubuwa da
zasu kara jan hankalinsa, ai ko nan da nan ta hargitsa shi,
rude suka koma bedroom dinsa, daga nan suke rufe
kofa, sauran bayanan kuma sirrine.
a
***
A
l'amarin gidan Yalwa mahaifiyar Halima
kuwa, yanzu abin sai dai ayi addu'a, gashi dai
Yalwa ta saduda to amma ta rasa yadda zata bullowa
yaranta su koma kan hanya, ga tsufa ya kamata har shi
Malam Usman shi ma dai ya kara tsufa sosai, don har ta
kai baya zuwa ko ina sai masallaci, amma abin Allah da
bakinsa da idonsa da kuma kunnensa, kafa ce kawai ke
bashi matsala domin baya iya tafiya mai nisa, haka ma
Yalwa ta ke fama da kafa ita ma, amma ita tana tafiya ko
ina nan mako ta da nan cikin unguwa duk tana zuwa.
Kuma IHalima ta na iya kokarinta wajen taimaka
musu don daga kan abinci har wajen abin sawa suna
samu. Alhaji Usaini ya na taimaka musu domin ita
Halima ba ta sana'ar komai kullum ta na gida, gashi
yanzu haihuwarta uku a gidan wato Auwal sai
71
S
Kwadayı barıjana'- Amuna Abdullahu Sharada
Kamaluddin wanda suke kira da kamal sai kuma macen
mai sunan Baba Abu wato Zainab ake kiranta da
Shahida, shi yasa yanzu Halıma ta zama 'yar gaban
goshin Alhaji Usaini, kuma game da Alhaji Hassan ya
kama yaran nan ya rike sosai, ya na matukar son su
domin 'ya'yan dan uwansa ne na hakika a kullum da
abinda zai sayowa yaran nan koma ya dauki Auwal ya yi
kwanaki a gidansa, tarkacen kayan wasansa da ya ke
kawowa yaransa ma ga wasu dunkunan da yake musu na
musamma. A takaice dai sun dawo tamkar da, shi da ma
Maryam ce baya so don haka aka samu sabani, to a
yanzu haka zumuncinsu ya fi na da ma domin suna
matukar son junansu.
Yau Alhaji ya komo daga kasuwa ya wuce kai
tsaye dakin Halima don itace da girki, a lokacin su
Auwal da Kamal sun tafi makaranta. Bashir ne mai
dauko su kullum ko shi ko direba, to direban suna tare da
Alhajin don haka sai shi zai dauko su, ya na shiga dakin
ya sameta ta na ta faman kuka, yarinyarta Zainab na
kwance kusa da ita. Ganin haka ya yi saurin shiga ya na
tambayarta "Lafiya? Me ya same ki?" Ta yi shiru ba ta ce
ma sa komai ba, ya zauna gefen gadon ya ce ma ta "Na
fuskanci tun lokacin da ki ka je gidanku kika dawo ban
sake ganin walwalarki ba, ina so ki sanar min me ya ke
faruwa?" Shiru ba ta ce komai ba, ya sake tambayarta
"Wai me ya ke faruwa ne?"
Ta yi shiru don ita bata so ya sameta ta na kukan
ba, ba ta so ya san halin da suke ciki, ba ta son zancen
duniya baya buya ba, shi tuni ya san cewa an kaam su
Auwalu babba, wato dan gidan Yalwa kaninta, da Lawan
sun karyawa wani mai shago kofar kanti sun debar masa
72
Kwadayı barı jana Amına Abdullalu Sharada
kaya za su gudu aka kaamsu, bayan dan karamın duka da
suka ci aka kai su police-station sannan kwana bıyu aka
mika su kotu aka yanke musu hukuncın dauri na wata
bıyar da tara ta dubu ashirin
Ya gyara zama bayan ya yi wannan tunanin ya ce
"Halima ki fada min abında ya ke damunki, kin san bana
son ganinki cikin wannan bakin cikin, kuma ma to in ba
kı fada min me ya ke damunki ba wa za ki fadawa? kin
san dai ba ki da wanda ya fi ni inba iyayenki ba ko?"
Cikin kuka ta dago kai ta ce "Suma din ai basu fi
ka ba, don kai muke tare yanzu". Ya ce "To wai me ya ke
faruwa ne?" Ta ce "wallahi idan na tuna al'amarin
gidanmu wato gidan Yalwa sai inji komai ya sauya min,
wallahi na rasa jin addi. Alhaji duk 'yan uwa sun kewaye
mana tsinke babu sauran mai Kaunarmu sai Baba Abu
saboda halayyar yarannan gashi yanzu ma su na daure ga
su Yalwa ba sa samun abinci sai dai wai yalwa ta yi bara
in wasu sun ba ta wasu su hanata wannan abin ne ya ke
ba ni haushi wallahi, ya ke sa ni bakin ciki da ace ni
namiji ce da ba abinda za su yi zan dinga nemowa ina kai
musu". Ya ce "Kar ki damu in don abinda za su ci ne, to
ni zan yi kokari inga ina basu har ma da suturar da zasu
daura don ina ga in har na dauke musu wannan abin zai
komo da sauki ko?" Ta ce "A'a ai shikenan dama ni iya
abinda ya ke damuna kenan, tunda ni ba wani kudi gare
ni ba da zan dinga yi musu ba". Ya ce "Ki bar wannan
zance ai ya wuce".
To wannan shi ne abinda ya faru da Halima har ya
zama Alhaji Usaini ya na taimakonsu don Halima ta
zama wani bangare na jikinsa, 'ya'ya har uku wasa ne?
maza biyu mace daya ai an zama daya ko? Kuma alakar
73
a
7
1
S
Kwadayı barijana'- Amumn Abdullalu Sharadи
yaran nan ta sa ya na matukar son Halima ita kanta
Ilapya Jamila ta yi ta gaji ta kyale su, amma sam ba ta
kaunar zaman Ifalima a gidan, Halima har cewa ta yi in
ta yaye Zainab za ta bata ita ta rike tunda ita ta aurar da
lata 'yar har yanzun ta ba ta san cewa Maryam ba 'yarta
ba ce, kai wannan fa-shine hautsini, ku dai kar ku gaji ku
biyo ni ku ji me zai faru akan Maryam nan gaba kadan?
Asabe ce aka zo gida, amma wannan karon duk ta
bi ta rame duk da man da ta ke faman shafawa na
bleachingbai sa ta tayi hasken sosai ba, don duk ta yi
baki sosai ta na shigowa da kayan akwatinta aka ta sami
Yalwa a zaune ta na korar kaji ta shanya waken da
lalima ta kawo ma ta, ta barshi ya an leda har ya fara
kwari, ta na ganin Asabe ta mike cikin murna ta na cewa
"Asabe daga ina?" Ta ce "Wallahi Yalwa daag Legos na
ke, ai na dawo gida gaba daya".
Cikin tsananin murna Yalwa ta ce "Kai amma na
godewa Allah da ya kawo mu wannan lokaci da na ga
nutsuwarki tun kafin in mutu yadda ki ka shiryu Allah ya
sa 'yan uwan naki su ma su shiryu haka". Ta ce "Yauwa".
Yalwa ta kai jakar daki sannan ta koma wurin Yalwan ta
zauna ta dube ta "Yalwa aure zanyi!" Cikin doki ta
kalleta "Haba dai 'yan nan, kin samu wanda za ki aura
din ne?" Ta ce "A'a ban samu ba, amma dai na san zan
samu insha Allahu, an zo da kudi da yawa ina so insa
Malamai su kawo min mijin da zan aura ta hanyar rokon
Allah ina son mutum mai hankali nutsattse". Ta се "То
Allah ya kawo, je ki ki sanarwa Babanki ya na ciki". Ta
ce "To".
Ta shiga dakin Malam Usman ta sameshi kwance
ta gaishe da shi, sannan ta ce ma sa "Baba na zo na sanar
74
Awadayı harijana Aına Ahdullalu Sharada
maka na komo gıda bakı daya, aure zanyi". Ya ce "To
madallah kai amma na ji dadin wannan lamari Allah ya
kara shurya ku amın". Ita ma ta amsa, sannan ta tashi.
Yau kusan watan Asabe biyu da komowa gida, don haak ta na ta faman zuwa wurin Malamai wai ta samu
mijin aure, suna ta faman ba ta maganin farin jini da
kwarjini a haka har ta dace mutane su na yi mata magana
har ma wasu su na tambayarta ko ta na da bukatar yin
aure, daga cikin masu zuwa wurinta akwai wani mutum
magidanci ne mai suna Alhajı Rabi'u, matansa uku, 'ya'ya
goma sha biyar har na goye ya an da hali dai-dai
gwargwado domin ya na da gidan sa tafkeke da motarsa
da kuma sana'arsa ta kasuwanci, shi ne ya ce ya na son
ya auri Asabe, to kasan zancen duniya ba ya boyu don
haka sai aka samu wasu munafukai suka je suka sanarwa Iyalinsa cewa zai auri wata cikakkiyar kasuwa wacce ba
ta dade da komowa daag yawon banzan ta ba, gashi gidan su ba tarbiya Yayarta ma sai da ta haihu a gida ta yi aure, 'yan uwanta duk 6arayi ne gasu 'yan daba, mashaya, don haka su saurari daukar mataki akai, kar a
shigo musu da masifa.
Suna jin wannan magaanr hankalinsu ya yi matukar
tashi suka rasa ya zasu bullowa zancen sai uwargidan ta
oc musu "Yanzu abinda ya kamata muyi shi ne mu kyale
shi sai in ya zo mana da maganar sannan mu san abinda
zamu sanar masa, amma yanzu in munyi ma sa maganar
zai iya dauka wani matakin akan mu, ko dai ya sanar da iyayenmu, ko kuma ya bullo da wani abin daban". Suka
ce "Eh, haak ne ya yi wannan shawarar da ki ka yanke ta yi".
Kwanci atshi magaanr aure ta mika tsakanin Alhaji
75
Kwadayı barı jana'- Amına Abdullalu Sharada
Rabi'u da Asabe har ma ya kai komai, an sa rana, ana
maganar daurin aure, ya tara iyalansa wato matansa ranar
wata juma'a da dare ya ce musu "Ni fa aure na ek son yi".
Suka ce "Kai amma muna yi ma ka murna a ina ne?" Ya
kwatanta musu Asabe, suka tabbatar ita ce wacce aka
kawo musu tseguminta, sai suka ce "Munji mun amince,
to amma muna ba ka shawara a matsayinmu an wadanda
suka zama daya kafin ka yi wannan auren ka fara zuwa a
gwada jinku, don kar ka ce ita kadai ta je ta ha'ince ka,
sai kuyi tare in an gwada ka ga sakamako mai kyau ne to
shikenan sai ka komo ka yi binciken tarbiyya in ko ba a
dace da sakamako mai kyau ba sai ka kyaleta ka samu
wata mu ba ma bakin ciki da aurenka don Karuwa се
babu wanda zai ce ba ya son karuwa", Inji Uwargidan
don ita ta ke bayanin "Ka ga duk gidannan akan idona
aka tarasu kuma ga su sun yadu munyi yawa, ina jin
dadin zama da su ta wajen wannan ma ga shi har sun tara
zuri'a a gidan mu ya kara yawa, to amma ka ga a loakcin
da ka auro su zamani bai rikice kamar yanzu ba, amma in
ka ga wannan shawarar ba ta yi ma ka ba zaka iya
canzawa".
Ya nisa ya ce "Kunyi gaskiya domin yanzu lokacin
nan na yanzu sai da bincike kuma insha Allahu gobe
zamu je a dauki jininmu da ita baki daya, kinga a san me
ye abin yi in an same ta da wani abu in kuma ta na lafiyа
shikenan sai ayi kawai". Ta ce "Yauwa Alhaji haka ya
kamata ayin".
Kashe gari tunda safe ya yiwa wani mutum Likita
abokinsa waya cewa yau zai zo oflice dinsa ya na son ya
dauki jininsu shi da Amaryar da zai aura, ya ce to
shikenan ya na saurarensu.
76
Kwadayı barıjana!- Amina Abdullahi Sharada
Gidansu Asabe ya wuce kai tsaye ya sameta ya ce
ta shirya za su unguwa, ta ce "To". Ba wani musu, ta
shirya tsaf ya dauke ta sai wannan asibiti. Bayan sun isa
office din ne ya karbesu hannu bibiyu, dama shi aikinshi
ke nan daukar jinin masu cutar kanjamau din. Bayan
wani dan dogon bayani aka fahimtar da Asabe abinda
ake son yi, ta kuma amince har aka gama gwajin. Suna
zaune to fa ai wurin fidda sakamako nan aka sha banban
domin shi Alhaji Rabi'u jinsa garau ya ke, ita ko Asabe
an sameta da kwayar cutar har ma ta fi ta daga matsayin
H.I.B ta koma S wato Aids, abin ba karamin razana
Alhaji Rabi'u ya yi ba, ita ko ma Asabe ai sai kawai ta
sulale kasa ta fadi, sai wani daddan farin ciki ya kama,
ya ringa murna, don a ganinsa Uwargidansa ec ta janyo
masa wannan lamari da yanzu ya janyo musu bala'i har
wani doki ya ke ya je ya samesu ya sanar da su kudin
mota ya baiwa likitan ya ce ya ajiyewa Asabe, in ta farka
ya bata shi ya yi gaba. Ya cc "To ya za'ayi haka?"
"Ka san dai ni yanzu ba abinda zai sa in aure ta, to
me kuma zan jira inyi ma ta? Kai na tafi kawai, in ta
farka ta ga bana nan ai ba sai na tsaya dogon bayani ba ta
san na fasa". Kawai murmushi Likitan ya yi ya ce "To ai
shikenan na ji". Ya na zuwa gida ya tara matansa baki
daya ya sanar musu abinda ya faru, kuma ya gode wa
Uwargidansa da ta zamo silar gano wannan abu, da
yanzu ya zuba musu alakakai, da yanzu ya zamo saandin
gano wannan abu. Ta сe "To Alhaji ai ka zama ni na
zama kai in har wani abu zai faru yakamata mu bincika
ko a boye ne kuma mu sanar ma ka ba tare da hankali ya
tashi ba". Ya ce "Ai ke dai na gode Allah ya bar maan ke
amin".
77
Kwadayı barıjana!- Amına Abdullahı Sharada
Bayan Asabe ta farka ta fara zunduma ihu ta na
kukan bakin ciki. Zuciyarta cike da tsananin tarin
nadama mai yawan gaske ta mike ko sallama ba ta yiwa
Likitan ba ta ficce ta samu dan acaba ta ſada masa inda
zai kai ta, wato unguwarsu bai yi birki ba sai kofar gidan,
ya na tsayawa ta sauka ta shiga gida ta karbo ma sa
kudinsa ta bashi. Ku duba ku ga yadda Asabe ta ke
bala'in son kudi wanda hakan ne ya kai ta ga halaka
KWADAYI YA JA TA! Ta afka cikin gurbatacciyar
rayuwa, gashi yanzu lokaci daya kudin sun fita daga ran
ta sakamakon tiket din da ta ke ganin ta yanka na tafiya
lahira wato aids, sai kawai ta barwa Likitan kudin da
Alhaji Rabi'u ya bāta don ta hau mota, abin mamaki sai
gashi ta shiga wurin Yalwa ta na kuka, ta na kiran
"Yalwa kin cuce ni kin janyo min bala'i, yanzu ya zanyi
da raina?"
Yalwa ta ce "Me ya faru Asabe?" Та се "Kе сe kika
turamu a wannan amsifar ba kince mu nemo miki kudi
ko ta halin ya ya ba? Gashi nan yanzu na je na dauko
cutar da za ta kai ni kushewa!" Cikin tsananin kidima
Yalwa na kwance ta mike ta na cewa "Asabe me ya
sameki?"
Cikin jin dacin maganar ta yi shiru, can ta се "Ва
'zan fada din ba, ai ke ce ki ka janyo min duk halin da na
shiga ciki wallahi fadanki bai amfana mana komai ba, sai
wahala, yanzu ga shi kannanmu sun zama 'yan daba, duk
don sakacinki ga tarbiyarsu, yanzu gashi na zaam abin
tausayi, karshe zan mutu ba wan ba kanin, ni dai na
shiga uku! Wallahi ban san yadda zan tubarwa
ubangijina bisa wannan sabawa da na yi ma sa ba!" Ta
kuma fashewa da kuka, tana cikin wannan maganganun
78
Kwadayı banjana!- Amına Abdullahı Sharada
ne Babansu wato Malam Usman ya leko ya ce "%o nan
Asabe". Ta ce "To Baba".
Ta je ta zauna ta ce "Ga ni". Ya ce "Kar in kara jin
kin gayawa Yalwa wannan maganar don mahaifiyarki ce,
duk abinda ta yi don kanta amma in kina irin wannan zа
ki kara dorawa kanki wani bala'in, saboda haka ki guji
kona ma ta rai, kuam duk abinda ya samu bawa kaddara
ce, laifinki daya da kika biyewa son zuciyarki
KWADAYI YA JA KI ki ka botsarewa mahaliccinki, ai
ko shaidan ma ana neman tsari da shi a wurin Allah ba re
mutum don haak kar ki kara ga ya ma ta wata magana
domin ke ma kina da laifi.
`Kuma na ji kina cewa wai ya za.ki yi ki tuba, to
babu maganar ya zaki yi don duk mutumin da ya ke da
wani laifi babu wanda ya canenci ya dosa sai Allah, shi
ne mai yafiya yanzu tunda kin gane gaskiya sai ki yi
istigifari har Allah ya gafarta miki, kuma mai halayya
irin taki ma ya ci ace sun tuba tunda wuri tun kafin Allah
ya kama su, domin ko wannan masifar da kika daukarwa
kanki ta ciwon nan ita ma kadai wani sakamakon abinda
ki ka yiwa Allah ne, don ba ta inda ba ya kama bawansa,
kinga ita 'yar uwarki Halima ta huta ta na gidan mijinta
haihuwarta ta uku kenan, ta na zamanta lafiya, ga shi ko
da yaushe sai sa ma ta albarka na ke yi". Ta ce "Ai ni ma
sai ka sa mun albarkar Baba".
Ya yi murmushi ya ce "Ai ya zama dole domin in
hannunka ya rube babu yadda zaka yi ka yanke ka yar,
saboda haka ke ma Allah ya sa miki albarka". Та се
"Amin Baba, ai ni yanzu sai dai addu'a domin ni tawa
kuma ta kare". Ya ce "Wai me ya same ki?" Ta ce "wani
ciwo ne da ni wanda ake dauka ta hanyar yawon banza,
79
ku
na
Li
za
ya
ku
ba
K
ra
ta
la
A
g
..
Kwadayı harijana'- Amina Abdullahu Sharada
ko mijı ya daukowa matarsa ko mata ta daukowa mijinta
shi ne na samu, to na san wannan ciwon ba warkewa
zanyi ba shi yasa na ce tawa ta kare! Ka ga shima Alhaji
Rabi'u da ya san ina da ciwon ai ya gudu ya fasa auran
nawa". Ya ce "To aynzu ya za'ayi ke nan?" Ta ce "sai
hakuri, sai kuma jiran lokaci". Ya ce "To Allah ya yi
mana da kyau". Ta ce "Amin". Sannan ya ci gaba da yı
ma ta fada akan maganar kar ta sake yiwa Yalwa rashin
kunya domin mahaifiyarta ce, ya kamata ace ta dauki
mahaifiyarta da muhimmanci, ta ce "Na ji Baba insha
Allahu na amince". Ya ce "Shikenan na ji tashi ki je,
Allah ya kyauta". Ta ce "Amin".
d
ti
k
C
S
***
A
l'amarin Bashir da Sameera kuwa yanzu
soyayya ta yi nisa, har ma sun zama tamkar
dama can sun saba da junansu, yanzu dai Samecra an
samu abinda ake so don kuwa Bashir ya gama mutuwa
akanta, ko gida ya je su na magana ba shi da wata
magana sai ta Sameera, ran iyayensu ya yi matukar dadi
sosai.
Yau ma Bashir ne ya dauki Sameera zuwa can
gidan Alhaji Usaini ta gaishe shi, sannan ya kai ta can
gidansu wurin Hajiya Rukayya, bayan sun isa ne aka
tarbe su da murna Hajiya Jamila na cewa "A'a yau
Amare ne a gidan namu?" Ta yi murmushi ta ce "Mama
ya na ganki ke kadai? Ina Aunty Halima?" Ta ce "Ta na
ciki yanzu za ta fito, ai Abban na ku ma yau ya na gida".
Suka zauna bayan sun gaisa, ta ke cewa da su
"Yaushe za ku koma gida ne?" Bashir ya ce "Anjima
80
Kwadayı bar jana'- Anuna Abdullaht Sharada
kadan zamu tafi gidansu Mamata don ta gaishe su"
Ilajiya Jamila ta ce "laba dai ka barta anan mana mu
gama gaisawa wajen gobe kuma ta je can gidan na ku?"
Ya yi murmushı sannan ya ce "Shikenan Mama ga
ta nan da dare na zo in dauke ta, fita zanyi". Ta ce
"Yauwa ko kai fa? Ai gara ka kyaleta ka ga sa gaisa ma
da Abban ku sosai, ya ce "To shikenan, ni zan koma". Та
ce "To sai ka komo". Ya mike zai fita, Sameera ta mike
don ta raak shi wajen motarsa. Suna zuwa ya dubeta ya
ce "An samu abinda ake so yawo ba?" Ta yi dariya "Ai
ni dama cewa ka yi in kwana haka na ke so". Ya се "А
haba dai kwana? Ni kuma fa?" Ta ce "Kayi kwanciyarka
a gida ko tsoro ka ke ji?" Ya ce "Tsoro kai". Ta ce "То
me zai sameka?" Ya ce "Ba abinda ba zai sameni ba,
komai ma samuna zai yi" Ta yi murmushi "Ilaba dai yau
dayan?" Ya ce "Ashe kin gane?" Ta yi murmushi sannan
ya ce "Ni na tafi sai daren?" Tа се "То а dawo lafiya,
Allah ya kiyaye min kai". Ya ce "Amin". Ya na mai jin
dadin addu'ar da ta ke yi ma sa in dai zai fita.
Ita kuma ta koma ciki. Hajiya Jamila ta ce "Ilar ya
tafi?" ta ce "Eh ya tafi". Ta koma ta zauna jim kadan
Halima da ke rike da Zainab a hannu da Alhaji Usaini
suka fito, suna zuwa suka ga Sameera. Alhaji Usaini ya
ce "Sameera saukar yaushe?" ta durkusa ta ce "Uncle
yanzu muka zo". "Okey ina Bashir din?" T ace "Yanzu
ya fita ya ce zai komo ya dauke ni zuwa dare". Ya ce
"Allah Sarki ai kin jima ba ki zo maan ba". Та се
"Wallahi ba ya barina inje ko ina Abba". Ya ce "Ai ya
kyauta domin ni ma ba na son fitar, gara ya zama muturn
ya na killace wuri daya sai ya li, kinga ai gashi kinzo
mana a marmarcе".
81
Kwadayı barjana'- Anuna Abdullahu Sharada
Ta yı dariya sannan suka gaisa, ta karbı Zainab
gamı da tambayar ina su Auwal? Suka ce "Su Auwal
suna can makaranta ba a taso su ba tukunna" Nan dai
suka yi ta hira har wani lokaci, sannan Halima ta tashi
don dora musu abincin rana, ta komo suka ci gaba da
hıra
Yamma na yı Bashır ya dawo, da mısalın karfe
hudu, ya an shigowa su Hajiya Jamila suka ce "bashir har
ka yi me?" Ya ce "Har na dawo mu tafi gıda" Ta се
"Lallai Bashir ka zama dan kadafi wato kai baka amince
ta kai daren ba kenan?"
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 12