faman kiransu ya ke a waya yau in ya kira
wannan, gobe sai ya kira wancan har dai Dad ya gaji ya
ce da Mum "Wannan yaron Bashir na san fa abinda ya ke
yiwa yawan waya, so ya ek matarsa ta koma, saboda
haka a wannan satin za ta tafi". Mum ta ce "Ni ma ina da
niyyar gaya maka haka, ai gara ta koma gidan ai ta
zaunu". Ya ce "Yauwa ai gara ta koma yanzu me za'a
shirya mata na komawa?" ta ce "Ba abinda zata tafi da
shi sai dai a tura musu kudi a banki kawai". Ya ce "to
shikenan".
Kwana uku da wannan maganar sai kawai suka fara
hadawa sameera kayan ta, don kashe gari za ta wuce,
haka ko aka yi da ranar ta zo, suka sa ta a jirgi sai
nigeria. Bashir na gida a zaune bai fita ko ina ba, ya ji
sallamar Sameera cikin mamaki ya ce "Yaushe kika zo?"
Ta ce "Saukar kenan". ya ce "Wa ye ya dauko ki daga
airport?" Ta ce "Motar haya na hawo". Ya ce "To me ya
sa ba ki yo min waya ba?" Ta ce "To ai ban san uzurin da
ke gabanka ba shi yasa ya ce karka kara yin irin
wannan". "Ai ko ni baki yo min ba sai kijewa su Abba
dasu Abban gidan su Maryam". Ta ce "To ni dai wallahi
93
Kwadayı barijana'- Amina Abdalalu Sharada
ban kıra kowa". Ya ce "To ya su Mum da Uncle?" T се
"Suna nan lafiya, ka san kuwa Dad ne ya ce lallai in ta
ho". Ya ce "Ai ya kyauta kına can kin barni da kewarkı"
Ta ce "Dama ai saida na ayyana" Ya ce "Yanzu ke da
basu ce ki taho ba, ba zaki taho ba kenan ko?" Ta y
murmushi "Haba Bashir mahaifa fa aka ce ma?" Ya ce
"A'a lallai, ai ko baki fađa ba na sani".
Tayi murmushi "Ashe na mance na bar dan tasi da
kaya a mota, zo muje ka taya ni daukowa". Ya ce "Au
ina mai gadi, baya nan ne?" Ta ce "Ban ganshi ba". Ya
ce "To muje Haruna mai wanki na san shi ya na nan don
yanzun nan ya gama guga".
Nan dai duk ta yi wa su Hajiya Jamila waya ta
komo da su Hajiya Rukayya, wato mahaifiyar Bashir
kenan, sannan shi kuma ya sanarwa su Abbansu, nan dai
suka yi ta bugowa sunai mata sannu da zuwa, kuma ta yie
wa can gidan nasu waya cewa ta sauka lafiya, ta samu
kowa lafiya.
Bayan kamar wata guda da dawowar Sameera
Maryam ta yo waya cewa ita ma ga ta nan zuwa, nan aka
yi ta shirin taryar ta, cikin doki da murna.
Kwana biyu kuwa da yin wannan naganar sai ga
shi ta yo waya cewa ta iso, ta kuma bukaci Abba ya aika
a dauko ta, dai-dai misalin hudu na yamma Abba yа
amsa mata da to.
Lokacin na cika da kansa ya tafi daukota ya ko yi
sa'a saukarsu ke nan taan hango shi ta rugo da gudu tana
murnar ganinsa, ya amshi jinjirin ya rungume ya na
faman murna har dai wani lokaci sannan ya dauki kayan
nasu ya sanya a boot suka taho gida suna ta faman murna
da farin ciki.
94
C
Kwadayı bari jana'- Amina Abdullahu Sharada
Suna zuwa gidan fa su Hajıya Jamila da su Halima
aka dinga murna, Halıma ta ce "Miko min yaron in
ganshı, kin san ni banje suna ba". Ta mika mata shi,
karbar shi ke da wuya sai gaban Halıma ya yanke ya fadi, ta ko zubawa yaron nan ido kirr ta na tunanin gano
da wa suka yi kama, ta dai san mai irin fuskar nan amma
ta manta, sai can ta tuno lallai wannan jinjiri suna mata kama da tsohon saurayinta Jamil wanda ya yi mata cikı
ya kore ta ya barta da kajaga, ta ce a ranta "Allah mai iko, ji bi dan nan sai kace sun hada iri da Jamil, ko da yake uwar ma tana kaam da Jamil din, to amrna kamannin sun fi bayyana ga yaron, wannan abin mamaki
da yawa yake, lallai in kana dã rai babu abin da ba zaka gani ba, dubi dai yadda yaron nan ya debo kamanin wani banza can bare".
Tana cikin wannan tunanin ne Hajiya Jamila ta
kalleta ta ce mata "Ba dai ya auren da ke kika zuba masa
ido, kinga sirmin saurayi, to kin yi masa tsufa". Cikin
wasan ita ma ta ce "Nima bana so a kaiwa Hajiya Rukayya, ko Hajiya Husna su ne suka fi dacefwa da shisabuwar fata, mu kam mun tsufa".
Maryam ta ce "O har yanzu dai kuna nan da abin
nan naku?" Halima ta yi dariya ta ce "Maryam ke nan, ai
kin san ni da Auntyn tawa kamar abokan wasa".
"Au Aunty ina 'yan kannena da aka haifa bana
nan?" Halima ta ce "Wallahi dazun nan Bashir ya zo ya
kwashe su baki daya suka tafi gidansa wai su taya Sameera wuni".
"Ke ni ko ina Baba Abu din nan?" Ta ce "Tana nan
ai kafin ki koma ya kamata ki je ki gaishe su". Ta се
"Zani wallahi, har can gidan kuma na yi niyyar zuwa".
95
Kwadayı barijana!- Amuna Abdullalı Sharada
Ta ce "Aiko da kin kyauta, dama ko kanwata Asabe tana
gıdan ba lafiya sai mu tafi tare ki dubata". Ta ce "To
muje in an kwana biyu". Ta ce "To shi kenan, Allah ya
kaımu".
Tuni Hajiya Jamila ta shige daki ta barsu, don haka
sai Halima ta ce "Ki shiga mana ku gaam gaisawar
inyaso kya zo mu ci abinci". Ta ce "To". Ta shiga dakin
Hajiya Jamila.
Tana shiga Hajiya Jamila ta ce "Lallai Maryam na
yarda mai hali baya fasawa, wato har yau kina nan da
halin nan naki, to maye na tsayawa a wurin wannan
banzar har ma wani kina cewa zaki je gidansu wata Abu
can, to sai kin dawo sha-sha-sha, marar hankali". Nan da
nan Maryam ta zumburi baki "To in naje gidan laifi na
yi? Wai ni Mama me yasa kuke haka ne? Ni dai gaskiya
bana son ku dinga irin wannan......" "Kinga rufa min baki
kinji ko? Bana son wani surutu".
Halima ko na can tana ta al'ajabin abinda ta gani
dangane da kamannin wannan yaro har dai wani lokaci,
sannan ta táshi ta kawai Maryam abinci ta ci ta koshi,
sannan Maryam ta fito falo suka zauna suna hira har
wani lokaci. Nan Alhaji ya dawo ya same su shima ya
zauna ana ta faman hira da shi har sallar magruba, bayan
sun gama cin abincin dare ne Maryam ta koma inda aka
tanadar mata don ta sauka, wato dakinta na tun tana
budurwa, nan ta yi kwanciyarta da yaronta Saddik kusan
sha dayan dare agogon nan Nigeria, Faruk ya bugowa
Maryam waya, ta dauka bayan sun gaisa ya ce "Ina
Saddik?" Ta ce "Ga shi nan har ya yi bacci". Ya ce "Ai
na san yanzu dare ne". Ta ce "Wallahi kuwa ka ga ma
shirin kwanciya muke yi". Ya ce "Ni ko kinga shirin fita
96
Kwadayı barıjana'- Amına Abdullahu Sharada
ma ne ke y1, shi ne na ce bara in kira kı". Ta yi murmushi
ta ce "Wai dazun nan da na kira ka bayan na sauka kana
ina ne?" Ya ce "Ina can office din Dad akan maganar
fara aikina". Ta ce "lallai to Allah ya taimaka". Ya ce
"Amin, zan kira ki can bayan karfe biyu". Ta ce "To shi
kenan Allah ya kaimu, sai anjiman". Ya kashe wayar
sannan ta kwanta ta na mai godewa Allah da ya bata miji
mai tsananin sonta da gaskiya.
Kwanan Maryam uku ta fara zaga 'yan uwa da
abokan arziki kamar su gidan Alhaji Hassan gidan
Bashir, gidan su Hajiya Jamila ma anan gidan lyayen
Hajiya Jamila, gidan su Baba Abu, har gidan su Yalwa ta
je, sannan ta komo gida, tana mai mamakin ganin
gidansu Yalwa da yadda gidan ya lalace ba don komai ba
sai don rashin tarbiya, wato baki dayan gidan ya zama
tamkar gidan taron garken dabbobi kowa da tambelen da
yake yi, da niyyar kwana ta je, amma a daddafe ta yi awa
daya a gidan ta komo gida.
Bayan ta dawo ne Halima ta yi ta fargaba don karta
fadawa Hajiya Jamila abinda ta gano a gidan ta bar mata
abin giri, hakika Maryam ta cika 'ya mai hankali domin
kuwa ko a fuska bata nunawa Hajiya Jamila ba, dama ta
tambaye ta komai yasa bata kwanan ba sai ta ce "Yaron n
yake mata rigima shi ne ta fasa kwana don kar ya hana su
bacci, ita ko Halima da Maryam ta shiga dakinta sai ta се
mata "Maryam kin ga gidan namu ko?" Ta ce "Na gani
Aunty, wannan gida naku ai ya rikice". Ta ce "Wallahi
shi yasa tun da na ganki na ce akwai dalili na san ba zaki
iya zama ba". Ta ce "Ina zan iya wannan tashin hankali
wai wanna Lawan din kaninki shi ne suke ta fada da
abokinsa sai ya sari abokin nasa ko a ka ne, shi ne ya
97
jang Ma Naunali Sarada
debo masa 'yan sanda, yanzu zancen da ake yı ya gudu
wai kuma sai suka kama dayan wato Auwalu wai shi ma
dama nemansa ake, ya yi wani laifi, ita kuma Asabe na
daki a kwance ba lafiya duk ta rame ta yi baki sosai,
Yalwa sai kuka take yi, wai an tsanar mata 'ya'ya an sa su
a gaba sai an ga bayansu".
Halima ta ce "Ai Yalwa ba zata taba barin halin ta
ba, ni ko naga sanda Yalwa zata gane wallahi yaron nan
zaman su a gaban Yalwa matsala ne, dama dai kawai can
aka kai su gidan horo aka bar su a can in sun nutsu a
komo da su". Maryam ta ce "Wai har tabar wiwi Auwal
yake sayarwa". Halima ta ce "Ai ya jima yana wannan
cnikin, sau nawa ana kama shi akan haka?" Maryam ta ce
"Wai yanzu babu wani abu da za a yi a kai ne?" Halima
ta ce "Me za a yi musu a kai wanda za su nutsu bayan
sun riga sun gama fandarewa? Dama-dama ma Auwalu
amma shi Lawan ai abin nasa ya yi nisa domin ya zama
sai kace wani gagarumin dan fashi in kin gan shi ma baki
son kara dubanshi". Maryam ta ce "Shi Auwalun da zai
sami wata sana'a ya dunga yi aiai da ya fi". Ta ce "Da da
abin bai yi girma haka ba, yana zuwa bakin titi wani
yana taimaka masa yana dan taya shi gyaran mashi yana
biyansa, to shi ma yanzu ya daina ya biyewa Lawan".
Maryam ta kawar da kai gefe ta ce "Ai ina ga shi yanzu
in aka janyo shi aka bashi jari zai nutsu?" Ta ce "To kila
in anyi sa'a zai zauna, to amma wa kike gani zai iya bashi
jarin?" Ta ce "Ga Abbana ki gaya masa mana". Ta ce
"A'a ni ba zan fadawa Abbanki wannan magana ba
domin kuwa ba irin taimakon da ba ya yi mana in na
gaya masa zai zama kamar rashin godiyar Allah ne"
Maryam ta ce "Shi kenan sai yadda ta yiyu kawai, amma
98
Kwadavi harmal
Kwadayı bar jana'- Anuna Abdullahı Sharada
ya kamata ayi wani abu akan lamarin nan"
Yau satin Maryam uku da zuwa yaronta ya kara
wayo sosai domin ya shiga wata na uku kenan, kamannin
kam da Jamil sai kara fitowa suke yi, Ilalima tana
mamakin wannan abu, to amma bata nuna ba sai ta boye
abin a ranta domin bata son kowa ya san halin da take
ciki, ita ko maganar Jamilun ma bata sonta, sau da yawa
dai ti kan tunano 'yar da ta haifa ta tafi ta barta, wani
lokacin ta kan yi tunanin ko 'yar na nan da rai? Wani
lokaci kuma sai ta tunano ko ta mutu oho, amma dai ita
sai a yanzu take ganin ta yi farar dabara da ta bar 'yar
domin da suna tare Alhaji Usaini ba zai aure ta ba da
yanzu suna gidan Yalwa suna cin bakin ciki tare ga shi
yanzu asirinta a rufe, ga yaranta mijinta yaan kaunar ta,
ga shi suna zaune abinsu da shi lafiya lau ba ya son
laifinta yana taimakawa 'yan uwanta da iyayenta, yana
kaunar yaranta kamar ya hadiye su, duk wani makircin Hajiya Jamila in ta kulla shi ba ya tasiri a kan sa, to
yanzu wanda ya ke cikin wannan zaman lafiyar da
kwanciyar hankali me zai dame shi? Gara kawai ta kara
kwantar da hankalinta ta yi zamanta cikin rufin asiri,
dama irin fadan da Baba Abu take mata ke nan a ko da
yaushe domin ta zauna lafiya a gidan mijinta, shi yasa
ma duk abinda Hajiya Jamila zaat yi mata bata kulata
domin bata son batawa mijinta rai suna zamansu lafiya.
Watan Maryam guda da 'yan kwanaki sai Alhaji ya
ce ta shirya domin ta koma gida, ai tama jima haka ta
shırya aka hada mata sha tara na arziki, ta koma gidan
mijinta wato can Jamus. A lokacin shi kuma Faruk ya
fara aiki a wani asibiti mai zaman kansa da aka bude.
Tana komawa gida ya nuna matukar farin cikinsa daam
99
Kwadayı barıjana'- Amina Abdullahu Sharada
ya damu da rashin dawowarta, kunya ce ta sa shi kasa
magana kun san Faruk akwai kunya kamar ba dan turawa
ba, ko da yake ruwa biyu ne shi yasa.
Kwanci tashi cikin Sameera na kara girma har ya
kai wata tara kowa na murna da wannan ciki domin shi
ma bashir zai sami dan kansa su maman Bashir da su
Hajiya Jamila sai faman shirye-shiryen taryar haihuwa
ake yi, kowa sai faman dokin zuwan ranar ake yi, domin
a wannan lokaci ne aka sa shi ma Ibrahim ya fidda matar
da zai aura domin sun ce ba zai auri jar fata ba, gara ya
dawo nan ya yi auransa har ma Alhaji Usaini da Alhaji
Hassan sun gama karfi wuri guda sun kera masa wani
kyakkyawan gida, shi Alhaji Hassan ya ce akwai wata
'yar amininsa mai suna Alhaji Ashiru zai bashi ita, domin
yarinyar ta na da hankali. Tun da ya ga yarinyar ya ji
yaan ma Ibrahim sha'awarta, to Ibrahim din ma ya yi
na'am domin an kai musu dankareren hoton ta sun gani,
saura gani da ido kuma.
Sameera na kwance a falo kusan sha daya na dare
da tsohon cikinta tana jiran dawowar Bashir, shiru tun da
Alhaji ya ce ya zo sa tafi unguwa shiru ba su komo ba,
can sai ta mike don ta koma cikin daki, ai ko ikewar nan
da zata yi kamar an tsira mata ciwo, nan ta cije baki ta
fara murkususu, tana kiran Allah har wani lokaci, cikin
hukuncin Allah bashir na jeho kafa falon ta dan ma na
fitowa. Da gudu ya karaso gami da tallafeta ya nai mata
sannu akan tsananin mamaki domin shi dai lafiya ya
barta ba ko alamar ciwo ba don yanayi da za a iya gani
na nuna alamun an sah wuya ba, za a iya cewa kamar a
sadaka ta sami dan, to fuskarta ce zata nuna alamar
wuyar da ta sha kafin dan ya zo duniya.
100
Kwadayı harijana'- Amuna \bdullahı Sharada
Waya Bashir ya dauko ya fara kıran su lajiya Rukayya cewa Sameera ta haihu, sannan ya sake bugawa
su lajiya Jamila ya kuma buga can Jamus wato gidan
iyayen Sameera, ai nan da nan sai murna, cikin daren nan kowa ya dinga murna kamar anan aka yi haihuwar a
cikin daren su Ilajiya suka isa suka gyara jaririn sannan suka gyara mata gidan ta tsaf, sannan kuma ita kanta bayan sun gama komai suka bar su da jaririnsu suka tafi gida.
Kashe gari kuwa jama'a aka cika gidan tamkar
ranar ake suna, da yake abinka da 'yan dangi ga shi kuma
auren zumunci ne, kuma wasu ma domin su zo su ga irin haduwar da za ayi a sunan suka zo, haka dai aka dai aka yi ta zowa, tare da burin zuwan ranar sunan.
***
M
asu karatu kar fa ku manta da labarin Jamilu
wanda ya yiwa Ha;lima ciki tun shekarun baya da suka wuce akalla za a sami kimanin shekaru goma sha takwas da 'yan foriyar watanni.
Jamilu ne zaune ya hada kai da gwiwa cikin dumbin takaicin abinda ke damunsa, ba ko wani abu
bane ya dame shi ba, sai matsalar rashin haihuwa, akallah ya yi auren mata dai-dai har biyar amma duk ya sake su saboda sun ki zama babu yarinyar da zata yarda ta zauna babu da, idan ma ta amince da an fan samu shckara biyu ko uku sai ta bijire ta ce ya saketa ita ba
zata zauna da shi ba, domin in sunje likita ya auna su sai
ace matsalar daga gare shi ne, ga dai dukiyar Allah ya bashi, abin ba a magana, amma abu daay
101
ya rage masa
Kwadayı han jana Anuna Abdullam Sharada
an dadi, ahın nan kuwa shi ne rashın magaji domin shi
ma yana so ya ga 'yan dugwai-dugwai a gabansa, to
amma babu hali. Na san zaku ce ai ko Jamilu na
haihuwa, domin ai shtya yiwa Halima cíi, to hakika a
wannan lokacin yaan haihuwa abinda ya faru shi ne.
Tun ranar da Yalwa ta kai karar Jamilu gidansu
wurin mahaifinsa Alhaji Ali in baku manta ba shi Alhaji
Alın ya tura shi waje domin ci gaba da karatunsa zuwa
mataki na biyu, ma'ana digirinsa na biyu, kuma zai yi ne
a bangaren harkar kasuwanci domin shi ya zaba, kuma
ya ke so ya yi Alhaji Ali ya shirya masa komai don ganin
ya tafi kuma ya shaida masa cewa ba zali dawo yanzu ba
sai bayan wasu 'yan shekaru, kafin lokacin kowa ya
gama rurumar zancen ya yi wa wata 'ya ciki, abin ya
wuce don haka sati daya da yin wannan hatsaniya
tsakanin Yalwa da Alhaji Ali sai ya tura shi can kasar
Amurka ya ce kuma kar ma ya sake ya komo musu sai
bayan wasu lokutta ko ince shekaru, haka ko aka yi
domın tun da ya tafi bai komo a sai dai ya buďe kan
iskanci a kasar kasancewar an sakar masa kudi sosai wai
don ya ji dadin zama, sai ya zama shi ne shugaban 'yan
iska a can, saboda gidan sa ma ya koma tamkar dandalin
karuwa, kuma wani abu da yake yi basa kula yarinyar da
la riga ta fandare sai dai wacce take da mutunci ko а
yaudare ta da kudi ko kuma kyau, domin na gaya muku
Jamilu kyakkyawa ne sosai domin yanayin kyansa yana
yin kyan jarumin līlm din indiya shi yasa 'yan mata da
dama suke rudewa akansa, to haka ya bude babin iskanci
shi da masu hallaya irin tashi suka gama kai.
To matsalar da yake samu, sai ya kasance duk
yarinyar da ya kusanta sai ta sami ciki, ayi ta kai ruwa
Kwadayı barıjana'- Amuna Abdullahu Sharada
rana, wasu da dama sun salwanta sakamakon cıkın da
suke samu ta hanyarsa haka ne ya sa shi sauya dabara,
saı yaje ya sa aka yi masa allurar da take kashe masa
kwaikawaycn haihuwarsa baki daya domin a wannan
lokacı duniya na rudinsa gani yake shi haihuwar ma bata
da wani amfani a tare da shi.
Ya jima yana faman tafka shadancinsa kafin daga
bisani abin ya komo kunnen Alhaji Ali, kun san daam
ance zancen duniya baya buya, don haka nan da nan sai
ga shi da kansa ya zo ya tusa dansa a gaab ya koma da
shi gida domin ya ma bincika ba wani karatu da yake yi
sai tsiya da yake tsulawa kala-kala, don haka sai Alhaji
Ali ya ce lallai ne in sun koma gida ya sami mace a yi
masa aure, shi ne zai fi zaman lafiya, haka ko aka yi yana
komawa gida sai ga shi Alhajin yana ta kawo masa 'yan
mata daga bangaren abokansa, amma yana ki sai can dai
ya amsa daya, wato wata 'yar abokin Alhajin mai suna
Zahra ya ce yana so, domin yarinyar ta hadu, kuma aka
yi sa'a tana sonsa, to shi ne ma har aka yi auren bayan
uban ya kera masa gida suka zauna a ciki, aka yi biki
cikin jin dadi aka watse, zama ya mike har kusan shekara
biyu sannan suka fara tunanin samun haihuwa, wato ita
ce ta ma damu shi ba ruwansa da ya samu da, ganin ta
damu ainun sai ya je ya sanar da mahaifinsa, shi kuma ya
ce to aje asibiti domin a tantance waye ba ya haihuwar,
shi dai mahaifin nasa ya san cewa dansa ba shi da wata
matsala don haka sai kawai ya ce suje a duba su aga
waye mai matsalar, shi kuma bai san zai ce haka ba don
haka bashi da zabi sai ya bi umarnin mahaitinsa haka ya
dauketa suka je aka bincike su, nan da nan aka gano
cewar Jamil ne baya haihuwa sakamakon mutuwar
103
KwadayıIiri jana' Amna Abdullahı Sturasdа
kwayayen hathuwarsa baki daya, an Zahra taan jin abinda
aka ce ta ce ba zata zauna da shi ba, Iallai ya sake ta,
ganin zata tona masa asiri a wurin mahaifinsa sai kawai
ya sauwake mata. Mahailinsa na jin ya saketa sai ya rufe
shi da fada, shi ko ya ce ni likita ne yace bata haihuwa,
shi ne shi kuma ya saketa,ya ce "Ai baka saketa ba sai
ka auro wata ka hada su". Ya ce "Ai rashin kunya zata yi
masa shi ne yaga ya dace ya hakura da ita, nan dai
mahaılinsa ya yi ta yi masa fada har wani lokaci. ba har
Tun da ya saki Zahra bai kara maganar aure
sai da mahaifinsa ya matsa masa domin ya dawo da
shashancinsa sabo dal, nan dai ya takura masa har ya
sake yiń wani auren, nan ma suka sake samun kusan
shekaru biyu sai nan ma rashin haihuwar ya dami
yarinyar mai suna Aisha, ta yi iya kokarinta akan ya je
asıbitı ya ki, har dai ta haji ita taje likita ya tabbatar mata
da lafiyarta lau bata da wata matsala game da haihuwa,
nan ma abin ya dame shi da ya ji bayanin da ta zo da shi,
ga shi kuma yana kaunar Aisha fiye da Zahra, haka ya ci
gaba da lallabata ya nai mata nasihar Allah ne bai basu
ba har suka kai kimanin shekaru hudu, sannan dai Aisha
tura ta kai bango son da ya fi a aranta, sai kawai ta ce ita
ya sauwake mata ta je ta yi aurenta a wani wurin ko zata
haihu, nan dai babu yadda zai yi sai ya saketa, uban fa ya
same shi ya yi ta fada akan abinda yake yi, har ya ce "Ba
ka gado ni ba, domin ni tunda na ke ban taba kara aure
ba bare saki, gara ma kawai in daina shiga maganar
aurenka don ni zaka dinga baiwa kunya".
Nan ya yi ta baiwa uban hakuri har dai ya hakura
amma da sharadin kar ya sake aure, ya saki matar, to fa
nan ya ga babu sarki sai Allah domin ya zama lallai ya
104
Kwadayı barjana'- Amına Abdullahı Sharada
sanar da shi cewa matsalar nan fa tare da shi ne, ba wai
gamatan ba, to nan ne ya dan samı rangwame, to amma
fa uban bai san cewa shi ya saiwa kansa wannan matsalar
ba.
A takaice matansa hudu suna fita, sai a ta biyar
dince har yanzu dai ba a ji kansu ba, domin a yanzu haka
shekararsu ta daya kenan, da yin wannan sabon auren, da
haka zamu leka gidan nasu muga wacce wainar ake toyawa? Jamil ne zaune a katafaren falonsa ya kishingida
bisa wata kujera doguwa ta alfarma, yayin da idon sa
yake a lumshe daga shi sai babbar riga da gajeran wando, babbar rigar ta wata rantsatsiyar shadda ce, ruwan
madara ta sha aiki, ga wani shegen agogo a hannunsa
mai tsadar gaske, kallo daya zaka yi masa ka gaen shi
domin har yanzu kamanninsa yana nan da farar fatar da
komai, sai dai kiba da ya dan yi, sabanin lokacin da yake
saurayi siriri dogo, to yanzu ya yi dan jiki kuma ya aje
dogon saje da gashin baki siriri wanda ya kara masa kyau
sosai, yana nan a kwance sai ga Sakina ta fito wato
matarsa, sanye da doguwar riga kanta babu dankwali ita
ma dai doguwar ce, to amma ba can ba kuma irin
wankan tarwadan nan ce, ta zauna akujerar da ke kusa
da shi ta ce "Wai ya maganar zuwana gidan namu ne, ka
san fa matar Yayana ta haihu zanje ganin jaririya?" Ya ce
bayan ya bude idonsa ya kalleta "Kin faye son fita
wallahi, ba shekaran jiya kika je gidan ba ne?" Ta ce "to
ai na gaya maka haihuwa ta yi jiya". Tsaki ya yi gami da
juyawa ya fuskanci bangon kujerar ta mike ta shige cikin
daki ta dauko hijabi da jaka ta fito, ta suri makullin mota
ta dube shi "Sai na dawo". Ya ce "Ki gaishe su". Та се
105
Awaulayı baıjana Amuna Abdullahı Sharada
"to sa ji" Ta fice abınta yayın da ya juya ya zuba mata
ido har ta fice, ya tashı ya je ya kunna tıbi ya kamo da
remote a hannunsa yana canza tashoshin tauraron dan
adam, ko zai sami wacce ta dace da ganınsa. Can saı ya
gama danna-dannansa ya kamo M.B.C Action domin
ganın film din da suke yi, zai yi kyau, ya ko yi dacen
ganın wasu 'ya'yan turawa na wasan kwallo a waat
koriyar ciyawa su uku, can gefe kuma iyayen su ne ke
kallo su nai musu alkalancin wasan, sai abin ya burge shi
ya ce a ransa "Ina ma nima ina da 'ya'ya wallahi da zan
zamo mai saukin kai a cikin iyalina domin ina sha'awar
magidanci zaune cikin iyalinshi ana barkwanci".
Yau shi kadai ne tafe a motarsa yana Kokarin
komowa gida daga kasuwa, yayin da danja ta tsaida shi.
sai ko ga wani mai mota kirar jeep irin tasa sak! Ya yi
birki kusa da shi bayan motar wasu yara ne su biyu mace
daya suna ta faman hangen na waje, akwai dan duhu a
motar, amma zaka iya shaida na cikin motar. Jamilu ya
zuba musu ido har aka bada hannu, bai ankara ba,
zuciyarsa cike da shaukin son yara ya ce a
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 12