wani
ciwon".
Ya yi shiru yana tunani, sannan ya ce "Eh, to
hakan ma kinyi dai-dai to amma kin san me ya kawo
ni?" Ta ce "A'a". Ya ce "Zuwa nayi in maida ke
dakinki". Ji tayi kamar ta rungume shi don murna, ta
ce "To shikenan na gode, Allah ya Kara kauna". Ya
ce "Amin". Sannan ya kalleta yayi murmushi
"Yanzu me kike da bukata?" Ta yi murmushi ta
sunkuyar da kanta ta ce "Ka ga Yalwa ba lafiya,
tabin hankali ne ya same ta ga tsufa babu mai kula
da ita".
Ya ce "Yanzu tana ina?" Ta ce "Ta na can
gidan mai magni". Ya ce "Ai wannan shirme ne can,
da wannan ai Gwauron Dutse za a kaita, amma kun
kaita can gidan bokaye? Yanzu dai ki fara komawar
tukunna, in yaso ma san abinda za a yi". Ta ce "То,
yanzu in na tafi waye zai kula da Baba, gidan babu
kowa?" Ya ce "Ina Lawan?" Ta ce "Ai Lawan shi ne
ya mutu". Ya ce "Au ina Auwalu?" Ta ce "Ya fice
shi da baya son zama a gida?" Ya ce "To shi kenan,
na ji yanzu dai zan barki nan zuwa sati in an sami
wanda zai zauna shi kenan..."
Sallamar Auwalu ya jiyo, ya ce "Au to ga ma
Auwalu nan, bara ya zo sai mu ji in zai zauna".
Auwalu na shigowa ya yi kiransa ya amsa ya zo ya
132
Kwadayı barıjana!- Amina Abdullahı Sharada
gaishe shi, bayan sun gama gaisuwa ne sai Alhaji ya
ce "Dama ina son ganinka, wai shin Auwal sai
yaushe zaka nutsu ka yi hankali ne? Ka ga fa iyayen
nan naka sai ka yi biyayya gare su zaka sami
rahamar Allah, yanzu abin da nake so da kai shi ne
ka zauna a wurin Baba ka daina yawon kana kula
dashi, in don abin da zaku ci ne, zan dinga kawo
muku". Ya ce "To shi kenan Alhaji, mun gide, ya cе "Yauwa, kuma in har Baba ta sami lafiya zan
daukeka zuwa can aksuwar mu ka dinga tayani
ciniki". Cikin murna ya ce "To Alhaji na gode Allah
ya saka da alheri". Ya ce "Amin". Ita ma Halima ta
yi ta godiya.
Bayan Halima ta koma gidanta da kamar sati
aka kai Yalwa asibitin mahaukata, cikin ikon Allah
tana samun magani da kulawa har aka samu ta saitu,
wato ta koma cikin hankalinta. Cikin ikon Allah
kuma aka sallamo su suka komo gida ta warke ras, ta
tambayi wa ya biya aka kaita asibiti, aka sanar mata,
nan da nan sai hawaye, ta ce "A gaskiya komai ma
ya sameni ni na jawa kaina, yaran nan tun farko ni ce
ban basu cikakkiyar tarbiya ta gari ba, shi yasa suka
kasance fandararu, daga yanzu ina rokon duk wata
UWA da ta tsaya ta kula da tarbiyar yaranta, don
gudun fadawa halin da nawa suka fada, domin ance
ka so naka duniya ta ki shi, ka ki shi duniya ta so
shi, to wai kin ba ana nufin ka nuna masa kiyayya ba
ne, a'a ana nufin kar ka so shi tsananin son da zai
133
Kwadayibari jana'- Anuna Abdullahı Sharada
hanaka ka tarbiyantar da shi, ka dinga biye masa
yana tabargazar da yaga dama, shi yaro rakumi ne
sai da akala, sannan kuma ka bi da shi ta hanya
madaidaiciya in ka kama akalar bayan nan kuma mu
iyaye don Allah a rage KWADAYI da son abin
duniya, ga shi tun farko shegen KWADAYINA ne
ya janyo min har na fada cikin wannan mummunan
halin. Sai dai ina rokon Allah ya yafe min abinda na
yi tsakanina da shi, amma tsakanina da yarana sai
dai kash na makaro da har suka mutu ban roke su
gafara ba, domin ni ce silar su ta shiga wannan
mummunar hanya, amma ina mai tubarwa Allah
mahaliccin kowa da komai ya yafe min, ke ma Halima ki yafe min".
Halima cikin kuka ta ce "Ba komai Yalwa na
yafe miki". Та се "Тo, Malam kaima ka yafe min".
Ya ce "Ba komai Yalwa mu yafi juna, kuma Allah
ya yafe mana". Sannan ta cewa Halima "Tashi ki
koma dakin mijinki, ki yi zamanki kar ki saba masa, ki kasance mai biyayya da hakuri". Alhaji ya ce "Ai Halima macen aure ce domin
tana da duk abinda kika zano". Ta çe "Yauwa Allah
ya yi miki albarka, kai kuma Auwal ka sami sana'ar yi domin zama babu sana'a ita ke janyo lalacewar tarbiyya". Alhaji ya ce "Ai tare zamu dinga zuwa kasuwa yana tayani ciniki". Ai nan da nan sai murna ta yi ta sa masa albarka, sannan ta ce "To ni yanzu zan dinga kula da Malam don haka kar kiyi komai ni
134
Kwadayı bariLana'. Amina Abdullahı Sharada
ma ina bukatar samun lada, don in dan ciccika na da
da ba a tsaya an samu ba". Suka yi dariya baki
dayansu, sannan kowa ya watse.
Yanzu dai gida ya yi dadi, hankalin kowa a
kwance, Halima ana gidanta tana zamanta lafiya,
babu wani tsangwama ko kyara, domin babu
ruwanta da Hajiya Jamila, ko ta yi mata ma bata
kulawa, sai ta dauke kai domin ta ji fadan mijinta da
İyayenta.
***
Tana zaune a falonta ita da Hajiya Jamila sai ga
yaro ya shigo ya ce "Halima wai ki zo inji Jamil".
Nan da nan gabanta ya fadi, hankalinta ya tashi, ta
ce "Yau na shiga uku, wai me yasa Jamil yake min
irin wannan ne? Bari inje in gayawa Alhaji kawai".
Ta mike ta nufi dakin Alhaji.
Hajiya Jamila ta kalleta ta tabe baki, ta ce "Kya
san ta dai da shegen munafurci sai ta je ta gama
masha'arta sannan ki dawo kina mazurai, in ya biyo
ki gida ki rude, ai da can ma sirinki zai toni wato kin
je kin yiwa Alhaji asiri ya komo da ke, zaki koma
kan harkar ki?" Duk wannan maganganun a zuci ta
ke yinsu, don haka Halima bata san da su ba.
"Alhaji ka ji wai Jamil ne ya komo yana kirana,
ni dai na shiga uku Alhaji ya zan yi?" Sai hawaye
shar a fuskarta. Alhaji ya ce "Yana ina?" Tа се
"Yana can waje". Ya ce "Yi zamanki kyaleshi na
135
Kwadayı barıjana'- Amına Abdullahı Sharada
karbi rigimar a hannuna, bara in fita". Nan da nan
ranta ya yi mata sanyi dama tsoro ta ke kar ya sake
korarta.
Yana fita falo Hajiya Jamila ta ce "Yanzu
Alhaji fita zaka yi, bayan ta gama iskancewarta,
sannan zaka fita ka yo me? Ai a daukeka kaima
marar mutuncin?"
"Kin ga babu abinda ya shafe ki da wannan
maganar, ni ba na son shisshigi kin ji ko?" Nan fa
ranta ya 6aci, ta fara maganganu amma ko kallonta
bai yi ba, ya ficce.
Zuwa ya yi ya tsaya a wajen Jamilu ya cẽ masa
"Ina son muyi maganar fahimta da kai, ka ga
wannan maganar bata yara ba ce, ka je ka turo
mahaifinka, da shi za a yi wannan maganar ka ji ko?
Domin ni bana so ka dinga zuwa kana sallama da
matata, in baka turo shi ba, to ni zanje". Ya ce "Zan
turo shi, amma wallahi koma me za a yi sai an bani
'ya ta". Ya ce "Eh, na ji amma ka turo shin. "Wawan
banza a ina 'yar taka ta ke za a baka, wa ya san inda
ta ke? Kai in banda ma sha-sha-sha har ka zo ka ce
wani kana son 'yarka to a wurin wa? Kar in kara
ganinka daga yau, maza ka bace min daga nan, in ba
haka ba wallahi zan sa a kama min kai". Ya ce "Na ji
zan bar maka kofar gidanka, to amma wallahi sai
Halima ta fito min da 'ya ta". Ya ce "Oho dai". Ya
juya ya koma gida yana fada.
Shi ko Jamil yana komawa gida, sai kawai ya
136
Kwadayi ban jana!- Amuna Abdullahı Sharadа
tafi gidansu wajen mahaifinsa Alhaji Ali, yana kuka,
wallahi shi fa sai an bashi 'yar sa, ran Alhaji Ali ya
yi mummunan baci, ya ce "Wai kai Jamilu ko ka
fara shaye-shaye ne? In ba ka fara shaye-shaye ba to
me ya kawo haka?" Ya ce "Ai Alhaji Usaini ma ya
ce ka je". Ya ce "Kar ka kara sa ni a cikin zancen
banza marar tushe ka ji ko? Ko ni ma irin ka ne
mutumin banza? Ba inda zan je duk abinda za su yi
maka su yi maka".
Nan ma ran Jamil ya kara baci, ya ce "Daddy
wallahi ni na san ba zan taba samun haihuwa ba,
domin ina da matsala babba, don haka nake son a
samo inda ta kai yarinyar da ta haifa, ko Allah zai sa
in samu". Alhaji Ali ya ce "Ta ya ya za'a iya samun
yarinyar da aka 'yar sama da shekara sha takwas? Ai
kai ma ka san ba za a samu ba, to amma akwai wani
abu guda da nake tunani, hanya daya za a bi in an
bita to kila a dace, hanyar dayar nan ko ita ce a
tambayi ita Halima a ji a ina ta yar da yarinyar in ta
fada sai aje gidan renon yara kafin nan za a yi
kokarin jin mecece shaidar ita Halima, a lokacin da
ta yar da jaririyar, in ta fada inda rabo sai ka ga an
samu".
Cikin tsananin murna ya ce "To ai kuma mijin
Haliman ba zai amince inyi magana da ita ba, sai dai
ku kuje". Ya ce "Na ji zan je wurin shi Alhajin inji".
Ya ce "Yauwa Dad, to yaushe za ka?" Ya ce "A'a
tunda na ce zanje ai zanje, yau zan ji bakin naci, ga
137
Kwadayı ban jang'- Amına Abdullahı Sharada
shi nan duk ka bi ka rame ka kanjame tamkar wani
mai wata cutar daban, haka kawai ka sanya kanka
cikin tashin hankali, haihuwa ba ta Allah ba ce?" Yà
ce "A gaskiya ni Dad sai sun bani 'ya ta". Ya ce
"Shikenan sai ka yi ta yi, amma ina ji maka tsoron
wannan iskancin da ka ke yi, duk ranar da aka се
babu raina babu mai raga maka, domin a yanzu in
kayi ana ganin idona, kuma ka ga kai kadai na
haifa". Cikin kunan rai ya mike, bai ma tsaya ya
saurari fadan da ake masa ba, ya fice abinsa, uban
yana ganin ya tashi a fusace sai kawai ya mike ya
nufi hanyar fita shima.
Yana zuwa dai-dai lokacin da ya dauki motarsa
sai ya dakatar da shi, ya ce masa bayan ya tsaya "Ка
jira ni in fito sai muje". Nan da nan, cikin murna ya
tsaya ya jira uban har ya gama shiryawa, sannan
suka rankaya sai gidan Alhaji Usaini.
Suna zuwa suka sa ayi sallama da shi, jim
kadan ya fito yana fitowa ya yi arba da Alhaji Ali,
cikin mamaki ya karaso gami da cewa "Alhaji yau
kai ne a gidan namu?" Ya ce shi ma cikin mamaki
"Dama gidanka ne nan?" Ya ce "Gidana ne Alhaji ku
shigo mana". Suka bi bayansa ya jagabance su har
kayataccen falon saukar baki, suka zauna yayin da
ya umarci akawo musu dan abin motsa baki, nan da
nan aka wadata su da kayan marmari mai kyau.
Bayan sun kammala Alhaji Ali ya dubi Alhaji
Usaini ya ce "Alhaji wannan rigimammen dan naka
138
6
Kwadayı barıjana'- Amina Abdullahı Sharada
ne ya jajibo ni, wai akan wata maganar banza tasa
marar tushe bare asali, dama abin da ya kawo ni duk
da ban san cewa gidanka ne ba ma, to in mun zo in
gaya maka cewa ka yi mana wata alfarma mai
dakinka ta fada maka inda ta yar da jaririyar sai mu
je can gidan renon yara mu sanar musu, da ranar da
kwanan watan in ma akwai wata shaida sai mu
tambaya ka ga shi kenan in su suka tsinta sai su
bamu, in ma babu sai ya hakura, in ma ta mutu shi
kenan, ka ga kowa ya huta, amma wannan alalafa ta
Jamilu ta ishe ni kamar wani karamin yaro".
Alhaji Usaini ya ce "Ai ba komai, bara ma inyi
kiranta ta fada muku da bakinta". Ya mike ya shiga
ciki.
Yana shiga Alhaji Ali ya dubi Jamil ya сe
"Amma Jamil ka ji kunya yau, domin Alhaji Usaini
mutum ne duk da cewa na girme masa, muna
mutunci abokin harkar kasuwanci na ne, don haka
ban so abinda ya faru ya zamo a gidan sa ba ne....".
Yana rufe baki sai ga Halima da Alhaji Usaini
sun fito, Halima na janye da hannun 'yar ta Zainab,
tana zuwa ta durkusa ta gaida Alhaji Ali, sannan
Alhaji Usaini ya bata umarnin ta fadi inda ta ajiye
yar da kuma in akwai wata shaida ta fada.
Nan take Halima ta fara zayyana musu yadda ta
haihu a wurin, sannan kuma ta nade jaririya da bakin
mayafınta da ma wurin da ta haihun duk ta shaida
musu, bata rage komai ba, sai dai ta mance kwanan
R0
Kwadayı bari jana'- Amuna Abdullahu Sharada
watan amma bata mance raanr ba.
Cikin tsananin mamaki Alhaji Usaini ya mike
tsaye ya ce "Alhaji ai yarinyar ma tana hannunmu, ai
mu muka tsinci yarinyar!"
Ba Halima ba, hatta Jamilu da Alhaji Ali sai da
suka razana, cikin tsananin mamaki suka ce "Kamar
ya ya Alhaji?" Ya ce "Bari in yi kiran Hajiya Jamila,
za ku tabbatar da wannan maganar". Yana rufe baki
sai ya shiga cikin gida da sauri.
Jim kadan sai ga su da Hajiya jamila, bayan ta
zauna suka gaisa sannan Alhaji Usaini ya ce mata
"Ko mayafin nan baki da muka taba tsintar yarinya
da shi, yana nan?" Ta ce "Yana nan a kasan
akwatina". Ya ce "To maza dauko shi". Та се "То".
Ta tashi cikin sauri ta dauko mayafin, a kulle cikin
bakar leda, ta mikawa Alhaji Usaini. Ya karbi
mayafin ya nunawa Halima, ya ce "Halima ko kin
gane wannan mayafin ne?" Cikin rawar jiki ta mike
la ce "Wannan ai mayafina ne wanda na rufo
jaririyar da shi".
Suna jin haka, suka yi kabbara baki daya, cikin
mamaki Alhaji ya ce "lallai komai nufin Allah ne,
Halima Maryam 'yar ki ce". Ta ce "Wacce Maryam
din?" Ya ce "Maryam tawa ta Jamus'. nan da nan
cikin firgita ta dafe kirji ta ce "Ya ta Alhaji?" Ya ce
"Kwarai kuwa 'yar ki ce, domin kuwa ita na tsinta a
cikin wannan bakin mayafin ranar sha biyu ga watan
uku 12/3/1991".
1440
C
Cikin doki Jamil ya ce "yanzu ina yarinyar?"
Alhaji Usaini ya ce "Tana can gidan mijinta a Jamus
har ma ta haihu". Alhaji Ali ya ce "To yanzu ya
zamu yi kenan?" Alhaji Usaini ya ce "Waya zamu yi
musu lallai su zo domin wannan lamari abu ne ba
karami ba, tunda ita yarinyar har yau bata san cewa
ba mu muka haifeta ba, ka ga kuma kafin mu saitata
ta gane komai sai anyi da gaske". Ya ce "Haka ne
yanzu dai zamu kyale komai sai in sun zo din ayi
mana magana". Ya ce "Shi kenan ba komai". Har
sun tashi Jamilu ya ce "Ko akwai hoto yarinyar a
hannunku?" Ya ce "Hotuna kai, har ma da wadanda
ta ke 'yar karama, har ma da wanda ta ke jaririya duk
akwai". Suka ce "To idan da hali a ba mu wasu daga
ciki".
Nan da nan Alhaji Usaini ya umarci Hajiya
Jamila ta kawo. Ita ko Halima mamaki ne ya hanata
magana, sai tunani take kala-kala, har kowa ya fashe
bata tashi ba, ita ma ta koma ciki ta samu Alhaji a
falonsa yana zaune yana tunanin wannan lamari, ta
sami wuri ta zauna ta ce "Alhaji dama ashe yarinyar
nan Maryam 'ya ta ce?" Ya ce "Yar ki ce mana". Ta
ce "To yanzu ya za ayi ta amince cewar ni ce
mahaifiyarta?" Ya ce "A to nima yanzu abinda nake
tunani kenan, amma ina ganin kamar zata amince sai
dai yadda zamu tunkareta da maganar ne abin
tunani". Ta ce "Ba ka ce zaka yi musu waya ba?" Ya
ce "Waya yanzu ko zan buga musu". Ta ce "To ai in
141
sun zo sai ayi maganar a gaban kowa". Ya ce "Dama
abinda nake so kenan,yanzu kira min Hajiya jamila"
Ta сe "Тo". Ta tashi ta nufi dakin ta.
Ta sameta ta hada kai da gwiwa tana ta faman
kuka, karam ranta zai fita, cikin sanyin jiki ta nufi
inda ta ke ta ce "Hajiya ki yi hakuri dama wannan
abu dole sai an yi hakuri, wai ki zo inji Alhaji". Ва
magana ta mike ta bi bayanta, suna zuwa ya dubi
fuskar Hajiya Jamila ya san cewa kuka take sai ya
fara bata hakuri, gami da nasiha, sannan ya zauna ya
warware mata abinda ya faru har Maryam ta kasance
'yar Jamilu da Halima, sannan ya dora da cewa
"Wannan abu kaddara ne don haka ki kwantar da
hankalinki, insha Allahu komai zai zama kamar bai
taba faruwa ba". Anan Halima ta yi ma Hajiya
Jamila alkawarin Zainab in har aka gama wannan
rikita-rikitar, zata bata ita har auranta, nan da nan
Hjiya Jamila ta dan saki ranta, dama sun saba a
tafiyar da Halima ta yi ta barta.
Yau dai gidan Alhaji Usaini cike yake kaf da
baki, wato su Alhaji Gambo da Alhaji Hassan, can
kuma gefe daya Alhaji Ali ne da Jamil, nan kuma
Baba ne da Yalwa da Baba Abu, can kuma Bashir ne
da Faruk, sai kuma su Hajiya Jamila da Maryam da
Halima suna zaune, domin tattaunawa akan abinda
yake faruwa wwanda ya janyo kiran wannan mitin
na gaggawa, domin a san yadda za a 6ullowa
lamarin.
142
C
Kwadayı harijana Amuna Ahdullabu Sharada
Alhaji Usaini ne ya fara jawabi kamar haka:
"Jama'a 'yan uwa da abokan arziki, assalamu
alaikum". Bayan sun amsa sallamar ya ci gaba da
cewa "Walo abinda ya tara mu baki daya anan, shi
ne akan wata 'yar matsala da ta taso, matsalar kuwa
ita ce, shi wancan yaron Jamil shi ya dinga zuwa nan
aeman 'yarsa a hannun Halima wanda zuwansa na
farko sai da ya yı sanadin na dan bata hutu ta je gida,
saboda, bacin ran abında ta yi min, to bayan na huce na
komo da ita sai ya kuma ci gaba da zuwa har dai na aike
shi ya turo min mahaifinsa domin wannan maganar sai
da manya Bayan ya zo ne na ga ma ashe na san shi,
muna matukar mutunci da shi, to a wannan zuwan da
suka da shi ne muka gano cewa ai Maryam 'yar Jamılu
ce, domin mun gane a inda muka tsince ta anan uwarta la
haifeta ta barta, wato Halima, kuma har shaidar
mayafinta duk ga su don haka na tara ku anan domin mu
warware wannan lamari cıkin maslaha ba atre ad zuciya
ta sosu ba".
Har ya gama bayaninsa, Maryam bata san inda aka
dosa ba, domina zatonta ba ita Maryam din ake nufi ba,
don haka ta zunguri laruk cikin rada ta ce masa "Faruk
mu me ye namu a ciki aka kira mu?" Ya ce "Ke dai ki
kasa kunne ki ji komai". Ta ce "To".
Kamar Alhaji Usaini ya san abinda ake nufi, don
haka sai ya ce "Maryam ina so ki tuna cewa imanin
mutum baya cika sai ya yarda da abubuwa guda shidda,
su ne a turance a ke kira Sid Aticle of path, cikinsu kuwa
har da imanı da kaddara mai kyau da marar kyau, don
haka in har ka yi imani da wannan to ka zamo mai
143
Kwadayı bari jana'-Amına Ahdullahı Sharada
cikakken imani, abında nake so da ke kuma nake so ki
fahimta shi ne, ina so in sanar da ke abinda baki sani ba.
ban san yadda zakı dauki abin in kin ji ba, to amma in
kinyi hakuri kuma in kinyi imani da kaddara mai kyau da
marar kyau, to abin zai zamo miki mai sauki".
Tuni Maryam ta gano abinda ya ke nufi, tun bai
karasa bayaninsa ba, ta ce "Abba na riga na fahimci
abinda ka ke so ka ſaďa min, kana nufin ni ba 'yarka ba
ce kenan ko?". Ya yi murmushin karfin hali, domin bai
san ma abinda zai ce mata ba, ai abinda nauyi ya ce mata
eh, ta ce "Ko ba a bani anısa ba ni na gaen domin ina da
hankalina, ni yanzu so nake a nuna min waye mahaifin
nawa kuma ta wacce hanya aka same ni?"
Cikin sanyin jiki Alhaji Usaini ya nuna Jamil, ya ce
"Ga mahaifinki nan Maryam, kuma ko ma ta wacce
hanya aka same ki, ni ba zan iya fada miki da bakina ba,
shi ya fada miki". Ba wanda bai zubawa Jamil ido ba,
kuma nan take suka fahimci lallai shi ne mahaifin
Maryam, domin suna kama, kuma ga zahii babu abinda
ya raba su da dan Maryam din, wato Saddik.
Jamil cikin sanyin jiki ya ke maganar kamar haka
"Maryam ki yi hakuri kamar yadda Alhaji ya fada miki,
komai mukaddari ne, ba sai na fayyace miki komai ba, za
ki gane don haka ki yi hakuri ni ne mahaifinki, kuma
bani da kowa sai ke kadai na mallaka, don haka ki yi min
afuwa Maryam, a lokacin da haka ta faru babu mai
wadataccen hankali a cikinmu, saboda haka ki yi
hakuri".
Hankalin Maryam ya yi mummunan tashi, fuskarta
ta yi duhu, ranta ya baci, ta yi wata iri nan da nan sai
hawaye ya fara zubo mata.
144
Kwadayi barijana!- Amuna Abdullalu Sharada
Cikin kuka ta ce "Abba ba komai ne ya dame ni
ba illa yanzu na san makiyina, kowa ma ya sani, to
amma ya Faruk zai dauke ni domin na san abinda ya
sa Alhajin su Bashir ya ki aure na da Bashir kenan,
amma a wancan lokacin ban gane ba, to amma a
yanzu ya ya batun aurena da Faruk zai ci gaba da
zama da ni a wannan halin ko kuwa shi ma zai guje
ni ne? Abinda ya sa na yi wannan tambayar na san
wannan shi ne mahaifina, ma'ana na amince, to
amma ai ba a wurinsa zan zauna ba tunda na yi aure,
ina wurin mijina. To amma ban sani ba ko shi mijin
nawa zai amince ya zauna da ni bisa wannan hali na
kasancewata ba 'yar halak ba?" Tana gama wannan
magana Faruk ya cafe da cewa "Maryam ai tun kina
aririyarki na jima da sanin matsayinki, dukkanmu
habu wanda bai san matsayinki ba, tun ma kina (
jaririya don haka kar ma ki kuma sako wannan
maganar ta wuce har abada, domin ni da ke mai raba
mu sai dai mutuwa, sai dai in ke kika ki ni?"
Nan da nan wuri ya dauki kabbara, sannan
Maryam ta ce "Shi kenan na gamsu kuma na san
Faruk kai masoyina ne". Alhaji Usaini ya ce "To ni
yanzu jamil magana ta gaskiya ba zan iya baka
Maryam a yanzu ba domin irin shakuwar ad na yi da
yarinyar nan, Allah ya sani". Hajiya jamila ma ta ce
"Ka ji Alhaji in ab don ni ba ya za ai yarinyar ta zo
wurinka? Ka manta artabun da muka yi kafin ka amince
a dauko ta?" Nan da nan ta shiga basu labari aka yi
145
Kwadayı barı jana Anuna dullahn Sharnda
ta dariya, sannan ta ce "Kuma kowa ya san ni na rike
Maryam ma'ana na rene ta nima kuma ba zan iya
rabuwa da ita ba har sai mai rabawa ta raba".
Jamil ya ce "Duk na ji wannan batu naku, tunda
dai kowa ya shaida Maryam 'ya ta ce kuma ga ta
hanyar da aka same ta, Maryam bata da gadona, to
amma na raba duk abinda na mallaka biyu na bata
don haka da shirina na zo, ga takardu nan zan sa
hannu, duk shedar sa hannu ga iyayenmu a zaune".
Nan ya fito da takarda, aka dinga rattaba hannu, duk
sai da ya raba dukiyarsa kaso biyu ya baiwa Maryam
sannan ya ce ta je ta ci gaba da zamanta a gidan
mijinta, sannan in ta zo nan sai a dinga tura mishi ita
yana ganinta, ya kara da cewa "Kuma a bani
adireshin gidan su na Jamus domin ni ma ina zuwa
can, sai in dinga ziyartarta in naje. Bayan haka kuma
Maryam uwa-uwa ce Halima ita ce mahaifiyarki,
wanda na yi imanin ba don an tilasta mata rabuwa da
ke ba, da babu yadda za a yi ta kyale ki. Maryam ki
yafe mana jefa ki wannan hali da muka yi, domin da
munyi aure sannan aka sameki da duk haka bata faru
ba, ni yanzu na fi kowa bakin cikin wannan abu,
domin a yanzu bani da da sai ke, kuma ke din ga
yadda ta kasance, hakan ya jefa ni a cikin dunbin
nadama domin da ace ban bi wannan hanyar ta
yaudara har aka same ki ba, da yanzu ke ma
halatacciyar 'ya ce, to amma ina kira ga sauran
mutaen masu hali irin nawa da su daina domin
146
Kwadayı barıjana', Amuna Abdullahı Sharada
gudun afkawa hali irin nawa. Na san Allah ya
jarabce ni da son da domin na samu kuma na
wulakanta, don haka jama'a ayi hattara a gujewa
shiga hanyar halaka, a gujewa shiga haramtacciyar
hanya".
Yalwa ta mike cikin kuka ta cc "Jamilu ba kai
kadai zaka yi wannan gargadin ba, har nima domin
duk abinda ya faru NI CE SILA, don ni na janyo
muku shiga wannan halin. Saboda son abin duniya
irin nawa, inda ace tun farko na tsawatar ai da haka
bai samu ba, to ina anin ana cika min baki da kudi,
sai ga shi na saki duk wata hanya ta tarbiyantar da
yarana KWADAYI YA JA NI! A sakamakon haka
ya ana biyu na rasa ta hanyar da bata adce ba, kunga
ko ince mai tsawatarwa maceya kamata inyi wa
nasihar su daina, domin gudun fadaya halin da ni
na tsinci kaina".
Alhaji Ali ya ce da Maryam "Maryam ni
Kakanki ne wanda ya haifi Mahaifinki, saboda haka
ina so ki yi hakuri da abinda ya faru, ni ma tawa
nasihar kenan".
Malam Usman ma ya gabatar da kansa ga
Maryam, sannan ya ce ta bi mijinta sau da kafa, kar
ta yarda ta saba masa, domin mai kaunarta ne, tun da
bai aureta ba sai da ya san halin da take ciki, kuma
bai taba nuna mata ba, in ba yau da ta ji ba. Nan dai
taro ya watse kowa na mamakin wannan abu. Malam
Usamn ya koma gida shi da Yalwa suma su Alhaji
147
Kwadayı han jana- Amuna Abdillaln Sharada
Ali suka koma shi da Jamil, Alhaji Gambo da Faruk
suka koma na su kasar.
Maryam ce zaune tana kallon yaronta Saddik
duk jikinta a sanyaye ta ce a ranta "Hakika Saddik
yana kama da mahaifina". Tana cikin wannan
tunanin ne Faruk ya shigo, ta dube shi ta ce "Faruk
ina
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 12