Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ma ba a dauka ba, hankalinta ta ji ya fara tashi, "Lallai kam babu lafiya," ta fada a fili. Zahra ta kalle ta, "Aunty wane ne ba lafiya?" Mera ba ta kalle ta ba kanta na kan waya ta ce; "Maman Affan." Zahra ta daga kafada alaman ko a jikinta tare da tabe baki ba tare da ta ce komai ba. Ta jawo filet ta fara dibar abin da za ta ci na break fast. Mera zama ta yi tare da sake kiran number Amrah, har yanzu tana ringing ba a dauka ba. A haka Saleem ya shigo falon, tare suka shigo shi da Mommy dake saukowa saman benen dakinta cikin kulawa Mommy take tambayar shi jikinsa. Da sauki," ya ba ta amsa yana kokarin zama kan kujerar dinning table. Mommy ta kalli Zahra, "Je ki ki kira Goggonku da Meena su zo mu yi break fast." Mera ta fashe da dariya har tana rike ciki, "Mommy ai Goggo da gudawa ta kwana cikin dare Meena ta zo wai in akwai filajin in ba su Goggo jiya an ga fitinar da ba a taba ganin irinta ba ta kuma kwashewa da dariya, ita ma kanta Mommyn sai da ta dara ita da Zahra. Gogan kam Saleem sai tafe baki yake yi tare da kallon Zahra, "Ke ba ki iya gaisuwa ba ko?" Mera ta ce; "Ba mu iyan ba ai na san har da ni kake mutum an grime shi amma sai son girma." Saleem ya shagwabe fuska tare da kallon Mommy, "Mommy ina ce ni ne babba hakuri na fita na bari ta fara fitowa?" Mommy ta shafa kanshi, "Rabu da ita ai kai ne namiji kai din nan kai ne יי magajin duk gidan nan, bayan haka Ai arrijalu ya ba ka girma." Saleem ya harari Mera "Kin ji ko? To fa daga yau a gyara. Mera ta kwashe da dariya, "To yayana mun tashi lafiya ya ya jiki ya ya fargaba?" Saleem ya tabe baki, "Jiki da sauki ita 102 AKWAI KURA kuma fargaba kin gan ta a nan?" ya nuna kanshi yana jan Karamin tsaki. Zahra ta kuma fada, "Barka da safiya Bro J," ya amsa tare da tabe bakinshi, cup ya dauka ya hada shayi ya fara sha a hankali. Zahra ta mike ta je aiken Mommy, can ta dawo tana dariya, "Mommy wallahi dukkansu bacci suke hala jiya ba su yi ba? Da na tashi goggo a razane ta farka tana ihum don Allah kada a kashe ta." Dariya suka yi dukkansu har Saleem sai da ya dan dara. Ganin saukowar Goggon nasu tare da Meena ya sa suka hadiye dariyar tare da gai da ita. Cikin kunshe baki ta amsa tana yatsina kamar gidanta wai ita a dole kanwar maigida. Abincin kowa ya diba suka fara ci. Suna cin abincin babu mai magana cikinsu sai karar cokali da tauna kawai kake ji. Mera ta ajiye cokalin, "Mommy Maman Affan ba ta daga wayar ba har yanzu." Mommy ta ajiye cokalinta, "Allah ya sa lafiya, sai ki bari an jima ki kuma neman ta ko za a dauka ni ma na yi mata fibe miss called ba a dauka ba. "Wace ce Maman Affan?" Goggon nasu ta tambaya. Mera ta ce; "Ita ce mai aikin Saleem mai yi masa girki." "Oh da ma tana da da ne?" Meena ta yi tambayar. Mommy ta ce "A'a ni ke kiran ta da hakan saboda tana son Affan sosai shi ma yana son ta." "Sannu 'yar kalen dangi," Goggon tasu ta fada tana kallon Mommy. Saleem ya kalli goggon tashi yana cin magani, "Da Mommy kike magana fa ba da Mera ba." Ta Harare shi tare da kumbura fuska tana tauna. Mommy ta yi kamar ba da ita take ba ta ci gaba da cin abincinta suna hirarsu da Mera. Mommy da Mera kadai ke jajanta rashin zuwan Amrah yayin da Zahra ke cin abincinta a hankali kwance. Saleem ya mike tare da barin gurin falon na Mommy ya zauna kan kafet tare da jawo Laptop dinsa dake ajiye kan kafet din ya fara dannawa. Can ya daga kai, "Ke wai ba za ki koma school ba ne?" Zahra ta yi wiki-wiki da ido, "Zan koma gobe insha Allah." "Yau za ki koma," ya fada tare da nuna ta da yatsa, "kada in fita daga 103 AKWAI KURA gidan nan in dawo in same ki ranki zai 6aci." Zahra ta amsa, "To Bro J." Mera ta yi dariya, "Wato kura ma ta san gidan mai babbar sanda." *** Cikin dare zazzabi ne mai zafi ya rufe ta tare da ciwon kai mai tsanani har ba ta iya daga kanta, tsoronta daya kada fa ta mutu cikin dare, kuka ta fashe da shi mai tsuma rai kafin ta yi karfin hali, a daddafe ta yi rarrafe ta kai kofar dakin Granny. Cikin muryar wahala take kiran, "Granny bude min kofa." Granny da ko cikin bacci muryar jikar tata ba za ta bace mata ba da sauri ta diro daga kan gado, kofar ta kama ta zare sakata, duk da kofar akwai key akwai sakata ita kam Granny ba ta amfani da key, a cewarta ba ta san shi ba, tun haihuwarta sakata ta sani. Amrah ta rike goshi, "Wash Allah! Granny za ki karasa ni." Granny ta rike ta, "Sannu Zainabuna ai ban san kina jikin kofar har haka ba." Amrah ta ci gaba da kukanta, "Granny zan mutu, kaina, wayyo Granny zazzabi." Granny cikin kidima ta rike Amrah tana yi mata sannu tare da taimaka mata suka shiga dakin Grannyn. Magani ta duba na ciwon kai da na zazzabi ta ba wa jikar tata tare da rufe ta da bargo saboda karkarwar zazzabi da Amrah ke yi." Daren ranar ba su yi bacci ba dukkansu biyu. Amrah zafin ciwo, Granny tausayin jikar tata. Sannu kuwa har ta gaji da yi wa Amrah. Sai karfe biyar saura na Asubahi kafin zazzabin ya fara saukar mata, ciwon kan ma ba laifi ta fara jin dadin kan nata, tuni bacci mai karfi ya dauke ta. Granny ta yi hamdala tare da kallon tausayi wa jikar tata Zainabu, tana da lafiya sosai takan jima ba ta yi cíwo ba amma fa in ta tashi yin ciwon takan yi mai zafi. Granny ta fada a cikin ranta, ita kam ba ta koma bacci ba bandaki ta shiga ta dauro alwala ta komo falo ta ta da sallar nafila ta raka'a tainil fajri kamar yadda ta saba kafin a kira Assalatu. 104 AKWAI KURA Bayan sallar Asuba Amrah baccinta take ta yi, Granny ba ta taba ta ba saboda bacci ana so mara lafiya ya yi shi, a cikin bacci ake samun sauki, gari ya fara haske karar wayar Granny ta hau kadawa. Da sauri ta fito daga kicin tare da danna kore ta kara akan kunnenta, "A'a Zainabu da safiyar nan?" Ummi ta ce; "Wallahi Iya da ku na tashi a raina in cedai duk kuna lafiya?" Iya ta ce; "Lafiya ba lafiya ba, wallahi Zainabu ita cе babu lafiya kwana muka yi ba mu yi bacci ba." "Assha! Assha!" Ummi ta ce, "wallahi mafarkin ta na yi, da ita na tashi a raina shi ya sa na kira da wuri ashe rashin lafiyar tata ce Allah ya nuna min a mafarki." "Ayya haka ne uwa da da ai sai Allah." In ji Iya, "ki kwantar da hankalinki Zainabu da sauki bacci ma take." "To Iya bari in shirya yara school zan leko an jima in ta tashi, a gaishe ta da jiki." "Za ta ji," iya ta ce tare da kashe wayar ta koma kicin don hada musu abin karin kumallo. Bakwai da rabi Amrah ta yi salati tare da bude idonta, cak! idonta ya tsaya a kan Umminta dake zaune kusa da ita tare da Granny dake zaune tana karin kumallo. Amrah ta yi murmushi sai don dadin jikinta tare da dadin ganin mahaifiyar tata. "Sannu." duka suka yi mata ta amsa tana kokarin mikewa. Ummin ta dan taimaka mata ta zauna. Ummi ban yi sallah ba," ta fada cikin kasala don ko ina sai ciwo yake mata sai dai zazzabin da ciwon kan amma alhamdulillahi da sauki. Da taimakon Ummi ta yi alwala ta dawo kan sallaya ta ta ta da sallah, a zaune ta yi sallar kasancewar tana jin dan jiri. Kunun koko tare da soyayyen dankalin turawa Granny ta ajiye mata a gabanta, "Daure Zainabu ki ci uwar taki ke take jira ki farka ta kai ki asibiti." Amrah ta yatsina fuska tare da zumburo baki, "Ummi na warke fa ba sai mun je asibiti ba." "Kaniyarki Zainabu," Iya ta yi mata dakuwa, "ai ko a dauke sai kunje 105 AKWAI KURA asibitin nan kin san irin kwanan tashin hankalin da na yi jiya ne? Yo ba zan lamunta ba tun wuri ki ci abin kari, ki shirya ta kai ki asibiti don ban san daren yau ba gara ku je." "Rabu da ita Iya za ta je," Ummin ta kalleta cikin kulawa akan fuskarta, "daure ki ci sai mu je ko? Na san alluran ce ba ki so ba zan bari su yi miki allura ba." Amrah ta gyada kai tare da fara cin dankalin tana kurbar kokon kadan, ta ji ta fara jin amai kamar zai dawo mata. Granny ta rike ta tana yi mata sannu, "Tashi ku tafi don gulma kina fama da kanki amma ki ce ba za ki je asibiti ba to ba zan lamunta ba, tashi ku je." "Ummi zafi jikina bari in dan watsa ruwa." Granny ta bude baki tana kallon ta, "Kya ji da gulmarki, in ce alwalar ma da kyar kika iya mu je in cude miki baya sai ki karasa wankan Amrah ta danna wa iya harara, "ban sa ki ba zan iya da kaina haka kawai ki kalle min jiki." Granny ta rike baki, "yo wanne dare ne jemage bai gani ba? Ai sai na mutuwarsa in ce da nike yi miki wankan magulmaciya kawai. *** Bayan likita ya duba ta ya tabbatar musu da zai rike ta na kwana biyu saboda ya auna jininta ya ga alamar ya dan hau, ga kuma zazzabin ya sauka ya dawo. A take ya sanya aka ba su daki tare da sanya nurse ta debi jinin Amrah don yi mata test. Ummi ta kalli 'yarta cikin tausayawa tare da kauna, "Mecе се damuwarki Amrah, da har zai daga jininki sama?" ta fada tana kallon Amrah. Ita dai Amrah na kwance gadon likita tana jin ciwonta yayin da take kallon mahaifiyar tata da duk hankalinta ya tashi. Amrah ta kago murmushi, Ummi kwantar da hankalinki ba ni da damuwa ciwo ne kawai sai rashin hutu shi kuma.na san zai wuce da zarar na gama IT." Ummi ta matso kusa da Amrah ta rike hannunta tana murzawa, "Amrah in roke ki arzikin wani abu?" Amrah ta daga kai alamar E, Ummi ta kuma rike daya hannun nata tana shafa inda aka soka allura don dibar jini, "Don Allah ki kwantar min da hankalinki sanin 106 AKWAI KURA kanki ne ba ni da kamar ki sai na kasa da ke, Amrah na rasa mahaifinki ba don na so ba har yau ban fita daga kukar rashin shi ba please ki taimake ni ki kwantar da hankalinki kada ki bari in rasa ki." Ta fada tana share hawayen da ya zubo mata. Amrah ta girgiza mata kai, "I promise you, zan kula Ummina ba ni da wata damuwa bayan aikin gabana," Amrah ta tuno gwagwarmayar da suka sha ita da Anas da wadda ta sha jiya ta yi murmushi, ai ko jikin karfe gare ta dole ta kai ga kwanciya a gadon likita a fili kuma ta ci gaba da murmushi don faranta ran Umminta, "Ina son ki Ummina," ta rufe ido tana dariya kasakasa. Ummin ta shafa kanta, "Ina son ki Amrahn Abbanta." Amrah ta fara lumshe ido alamar bacci saboda allurar baccin da aka yi mata. Ummi ta kwantar da ita tare da gyara mata kwanciya, tuni Amrah ta yi bacci. Waya Ummi ta ciro cikin jakarta ta kira mijinta tare da fada masa sunan asibitin da Amrah take. Allah ya kyauta ya yi mata tare da sanar da ita cewa ga shi nan zuwa, Granny ta kuma kira ta sanar da ita an kwantar da su tare da sanar da ita asibitin da suke. Granny ta fashe da kuka a waya, "Allah sarki Zainabuna ashe jikin na damun ta amma ta daure Allah sarki 'yar marainiyata ga ni nan zuwa me za a zo muku da shi?" Ummi ta ce; "In kin zo zan koma gida zan taho da komai na bukata." "To shikenan ‘yan nan gani nan zuwa yanzu." Abban Amlah shi ne ya fara zuwa sibitin ya kira Ummi a waya ta fada masa dakin da suke kwance, bai jima da zuwa ba ita ma Granny ta zo dukkansu kowa hankalinshi na tashe na damuwar ciwon Amrah. Granny kuwa kukan ta ci gaba da yi tana tausayin Amrah. Ummi da Abban Amlah sai hakuri suke ba ta, Ummi ta mike. "Iya ki zauna bari in je gida in dan hado abin bukata." "To 'yan nan a dawo lafiya." Abban Amlah ya сe; "Bari in zo in kai ki." ta ce; "Ai da motata na zo." "E bari in kai ki sai in dawo dake ba sai kin je da taki motar ba." 107 AKWAI KURA A hanya suna tafiya Ummi tana share hawaye, "Abban Amlah aikin nan anya bai fi karfin Amrah ba? Jininta fa likita ya ce ya hau duk da Amrah tana boye min damuwarta kuma ta ce min ba komai don hankalina ya kwanta to amma ai ni ba yarinya ba ce I know aikin nan ne yake caza mata kwakwalwa Abban Amlah," ta fada tana zub da hawaye. Abban Amlah ya nemi gefen hanya ya yi fakin tare da dafa kafadar matarshi, "Na gode wa Allah da har kika gane aikin ne ya sanya jinin nata ya hau, to kin ga ai Alhamdulillah mun san da dalili, da a ce ba ta da damuwa ta samu kanta cikin wannann halin shi ne dukkanmu ba za mu nutsu ba, ki kwantar da hankalinki Ummin 'yan uku ba zan taba cutar da Amrah da son raina ba sai bisa kuskure kuma na ba ta aikin nan don na san za ta iya. Still na san aikin zai samo mata daukaka irin wadda kowanne uba zai yi alfahari da 'yarsa, Amrah ta fada min maganar da na ji dadinta na kuma daura aniyar taimakonta duk da ta fada min maganar a sigar rashin kunya ne amma ni na dauki mai amfani cikin maganar." Ummi ta kalle shi tare da son karin bayani, Abban Amlah ya daga mata gira, "Yes ta ce da ni na ba ta aiki don in kashe ta saboda ba ni son ta to ita kuma ta yi min alkawarin za ta yi aikin don cika burin mahaifinta na son ta yi karatu mai yawa ta zamo abar alfahari ga duniya bakidaya don hakan in sani in ma kashe ta nake son yi ko ta mutu ba za ta yi bakin ciki ba ta mutu wajen cika burin mahaifinta mai son ta kuma in ta mutu za ta je ta same shi a can kiyama ya san ta sadaukar da komai nata saboda cika burinshi. Ummi ta share hawayenta tare da jinjina kai don maganar 'yar tata ta shiga jikinta "Wallahi wallahi wallahi ba ni na haifi Amrah ba amma ma dauke ta kamar 'yar cikina kuma burinta ya burge ni, ina son karfin gwiwarta da kowanne ya ya za su yi 108 AKWAI KURA koyi da ita wajen cika burin mahaifansu mai kyau irin nata ina mai tabbatar miki da iyaye da yawa sun samu albarkar 'ya'yansu ko da bayan ransu, Ummin 'yan uku ki yi min afuwa na san za ki yi alfahari da 'yarki bayan burinmu ya cika na san nata burin na hanyar cika kada kashin aikinmu don haka ki ci gaba da yi mata addu'a 'yarki ba za ta rasa ranta akan aikin ba karshen ta alkhairi ne kin ji uwar 'yan ukuna." Ummi ta rufe fuska tana dariya tare da gamsuwa da duk maganar da mijin nata ya fada tuni ta ware ta fara dariya tare da godiya ga Allah da ya ba ta mijin marainiya a kasan ranta tana addu'ar cin nasara ga Amrah tare da fatan Allah ya ba ta lafiya mai amfani kuma mai dorewa. *** Kwananta biyu a asibiti tana jinya kulawa take samu sosai daga Doctor, mahaifiyarta tare da sauran 'yan uwanta. Alhamdulillah lafiya ta samu sosai ga Amrah. Duk hankalinta na ga gidan aikinta, ta san tabbas masoyanta kamar Mommy da Aunty Mera suna kewar ta ita ma tana kewar su, musamma danta Affan. Wayarta dake gida take tunanin a dauko don ta sanar da bestynta ta san da ta sani da ta tazo amma sai Umminta ta ce ga tata wayar kowa take son kira ta kira kasancewar Number besty kadai ke kanta, Zahra ta kira ta fada mata ba ta da lafiya tana gadon likita cikin damuwa. Zahra ta ce ga ta nan zuwa yanzu. Ta so kiran Aunty Mera ta sanar da su rashin lafiyarta sai dai babu number Aunty Mera a kanta Bai fi awa daya da yin wayar ba Bestyn nata suka iso ita da Anas hankalinsu a tashe. Anas ya ce ya kira wayarta ba a dauka ba karshe ta daina shiga alamar an kashe wayar. Amrah ta dan harare shi, "Ka cinye min chargy da kira ai sai ka biya ni chargyna." Anas ya bi ta da kallon kauna, "Ai da kin san hankalina inda ya tashi cikin kwana biyun nan da kin tausaya min zuwana gidanku sau uku na rufe ashe ke da Grannyn kuna 109 AKWAI KURA nan kuna shan jinya, kai sannu Beb sannu Allah ya sa kaffara ne har kin rame wallahi." Ummi ta yi waje don tana surukutaka da Anas kasancewar Amrah 'yar fari ne gare ta ita, ko Granny ta biye masa sai tsokanan juna suke yi ita da Anas. "Ga waya bestyna Bebyna zai gaishe ki," Zahra ta sanyawa Amrah waya a kunne. Amrah ta karba tana mai amsa gaisuwarshi tare da ba ta hakuri kan cewar in ya dawo gari zai zo ya gaishe ta yanzu don wani aiki ya kai shi Abuja shi da oganshi. Amrah ta ji dadi a ranta da ba ya gari. "Ba komai," ta ce da shi sannan suka yi sallama ta mikawa Zahra wayar. Mommy tun safe suke kiran Amrah ba a dauka ba. Har dare ba a dauka ba, hankalinsu ya kuma tashi tuni Mommy ta yi da na sanin rashin sanin gidan su Amrah hakan ya sa ta kudura a ranta in har ta dawo aiki za ta sanya ta zo har gida ta kai ta gidan nasu saboda gudun irin wannan ranar. Washegari ne Mera ta bi mijinta Lagos ba don ta so ba don ta so ta ki bin shi har sai ta ga Amrah sai dai a halin yanzu wayar Amrah ta daina shiga ta ya ya za ta ga Amrahn? Wannan dalilin ya sa Mommy ta lallaßa ta tare da yi mata alkawarin insha'Allah Amrah za ta neme ta very soon, ba don Mera ta so ba ta tarkata yanata-yanata ta bi Abban Affan Lagos tare da bar wa Amrah sakon kudi da kayan sawarta. Shi ma Saleem ranar ya wuce Abuja an neme shi kan wani aiki. Zahra da ma ta koma makaranta, tun jiya Saleem ya kada ta. Gidan ya yi shiru ga Mommy ba kowa sai ita da 'yan aiki, hakan ya sa da yamma ta dauki key na mota da kanta ta fita don shan iska, gidan ya yi mata kunci ba kowa sai Meena da Mamanta da suke side na baki. *** 110 AKWAI KURA "Granny wallahi kankana nake son sha, haka kawai nake sha'awar ta." "Zainabu in za ki sha yanzu sai in tsallaka titin nan in sayo miki ina ga akwai masu sai da wa.." Ummi ta ce; "A'a Iya bari in yi waya sai Abban Amlah in zai zo ya zo da ita." "A'a Zainabu ku bar shi ya dinga hutawa mana, komai sai shi ni kam kankana ba ta fi karfin arzikina ba bari in karbо mata." Amrah ta ce; "Kai Granny ai ni kam ki bar ce min Zainabu, yanzu ni da Ummi wa zai gane da shi kike yi tun da haka kike ce mana duka?" "Kinibabbiya kin ga tafiyata bari in nemo miki kankanar, mi ma ina kaunar kankana don abincin Ma'aikin Allah ne (Annabi Muhammadu Sallalahu alaihi wasallam)" Ummi ta ce; "Allah ya ba ki hakuri Iya." "To da hakurin ta mutu sadakar nawa kika bayar?" Zainabu ta sunkuyar da kai tana murmushi. Iya da Amrah sai Allah, su yi fada su shirya kamar ba dazu suka gama fadan da Amrah ba, fadan ya fara ne kan Amrah ta ce Iyan ta je gida ta huta saboda ta gaji, zaman asibiti babu dadi shi ne Iyan ta ce ba za ta je ba ko ubanki ne Ahmadu yadawo duniya bai isa ya sanya in bar ki in tafi gida ba. Amrah ta turo baki, "A'a wannan ai zagi na kika yi," ta fara share hawaye, "Abbana na kasa ana zagar min shi." Iya ta gutsiri goronta, "Munahuka dadin abin ni ce nan na haifi abina ba kishiyar uwa ba ce bare a yi min kadifiri kuma na fada babu inda zan je, kafata kafarki." Ummi ta yi murmushi, kaunar Iya da Amrah daga Allah ne. Ta sayo kankana da gudu ta hau titin za ta tsallaka tun daga nesa mai motar ta gan ta hakan ya sa ta rage gudu tare da cin burki, Iya ta rungume da kankana tana salati haka masu kankana da sauran mutane salati suka sanya Iya idonta rufe ta sai da ranta motar ta shiga da ita. Hamdala direbar ta yi da ta auna arziki, sannan ta fito daga motar. Iya da ta bude ido don jin shiru ya ratsa gurin, salatin mutane ya ragu sai hamdala da ake yi. Iya ta fara masifa, "Allah ya isa mana in ma asiri aka yi 111 AKWAI KURA mana, wato Amaduna ya mutu ta sanadin mota shi ne ni ma za ki kashe ni ta sanadin mota to wallahi ahir dinki ban fito ba sai da na yi salati ga Annabi sallalahu alaihi wasallama kuma sai da na yi duk kula'uzaina kafin in fito, shegiya mai farar fuska, na godewa Allah da na fita daga sharrin motarki." Matar ta Karaso gaban Iya ta shiga ba ta hakuri tare da cewa Iya ta zo ta kai ta asibiti amma iya ta ce fur babu inda za ta je ta ci gaba da zagin mata tana turo dankwali gaban goshi. Karshe matar dariya ta fara yi don Iya ta burga ta sosai, tuni damuwar da ta fito da ita ta kau saboda wannan rigimammiyar tsohuwar, mutane sai hakuri suke wa da Iya. Sai da ta gama masifarta tsab! Sannan ta ce; "Je ki mai farar fuska na yafe miki amma fa ki dinga kula da hanya ran dan mutum daraja gare shi ba ran kiyashi ba ne, yo kin gan ni nan raina na da muhimmanci gun 'ya'yana musamman jikata Zainabu in har aka ce ba ni nan wannan yarinya mai shegen riko ba za ta yafe miki ba." Matar ta rike baki, Na godewa Allah da Ya tsare ban buge ki ba sannu Iya ki kara hakuri sannu, wallahi ban yi da nufi ba ki yi hakuri." Iya ta kama baki, "Ka ji siddabaru ina kika san sunana har da kira?" Matar ta yi dariya "Ayya Iya ai duk wata babba wadda ta kai munzalin shekarunki ba za ta rasa nasaba da iya ko inna ba ke dai je ki Allah ya kiyaye na gaba." Matar ta sanya hannu gaban motarta ta ciro jakarta, kudi dami biyu ta dauka ta mikawa Iya amma fur Iya ta ki karba, karshe shirin barin gurin take yi, "Kin ga kalla ga Almajirai nan ki ba su sadaka ni kam Usmanu da Zainabu sun wadata ni da komai sai dai in butulcewa Allah zan yi," ta kama baki, "Allah kuma ya tsare ni," ta bar mata kudin a hannunta. juyowa ta yi don bawa almajirai kamar yadda Iyan ta fada wadanda suka gewaye su sadakan kudin ta ba su tuni suka fara yi mata addu'a mai yawa tare da godiya. Bayan ta ba su ne ta juyo gurin Iyan don ta kai ta gida, hakika tsohuwar ta burge ta sosai za ta so ta san gidanta ko don comedynata sai dai Iyan ta 112 AKWAI KURA 6ace mata bat! Babu ko alamarta a gurin. Matar ta koma mota cike da nishadi tare da jin haushin rashin Iya a gurin. *** "Wace ce ita?" ya shako wuyansa yana damkar makogwaronsa kamar zai aika da shi lahira, "wace ce ita?" "Haba Oga, haba Oga gaskiya fa ko ta ware ko ta warwaraye sakar kasa wuya mu yi maganar hanyar da za ta bulle."Amma ina bai sake shi ba sai kokarin son aikawa da shi kiyama yake yi tare da fadar, "Wace ce ita?" Ganin yana kokarin kai shi lahira ne ya sanya ya sanya kafarsa da karfi ya kai masa duka a Kasanshi. Da sauri ya sakar masa wuya tare da rike kasanshi yana sauke numfashin wahala. Da sauri ya kuma tunkarar sa don ci gaba da shakar sa "A'a Oga na ce ka bari mu nemi hanyar bullewa ita fa hakallar nan ta shafi samu da rashi kamar yadda aka yi ram da biyu daga cikinmu su kuma su ce me? A raye ko a mace ba mu sani ba, kuma hakan bai hana mu ci gaba da sha'aninmu ba, don rashin su ba abin zai dakatar da mu a harkalla, haba Oga mafita ya dace a nema ba wai fada tsakaninmu ba. Sha ruwan sanyi Oga, sha ruwan Faro ka huce," ya mika masa gorar ruwa tare da mikawa dayan shi ma, duka suka karba suna sauke numfashi. Ogan kasa ya zauna yana sauke goran tare da sauke numfashin wahala tare da kara matse marainanshi, don dukan ya shige shi sosai, shi ma wanda aka shaken numfashin yake saukewa tare da kumbura irin na manyan 'yan daba yana kallon Ogan

Chapter 9 of 12