fashe da kuka tare da dannawa
Amrah harara, "Mayya ki fita a zuciyar Mommyna, Mommyna
ba ta taba yi min masifa ba sai a kanki, wannann dalilin ya sa
na tsane ki," fu! Ta bar falon tana kuka. Amrah da ranta ya yi
bala'in 6aci ji take yi ina ma a waje suke ta nunawa Zahra ita
ma fa ba tayar baya ba ce, ta hadiyi wani yawu mai daci tare
da hadiye fushinta, kafadarta Mommy ta dafa, "Ki yi hakuri
Maman Affan, yarinta da rashin hankali ke damun ta, wate
rana na yi imanin da kanta za ta ba ki hakuri bayan ta gane kurenta." Amrah ta yi murmushi dan kwantarwa Mommy da
hankali. Tabbas Allah shi ke cire rayayye a cikin mamaci
67
AKWAI KURA
kamar yadda yake cire matacce a cikin mai rai akwai kauna
mai zafi na Amrah dake ratsa zuciyar Mommy, haka ita ma
Amrah take son Mommy da a halinta saboda karamci da take
nuna mata. Agogo ta kuma.kalla, "Zan wuce Mommy ina da
uziri kada dare ya yi." Mommy ta shafa kanta, "A gai da gida
Amrahtu ki gai da goggon taki."
***
Bayan sallar Asuba kamar yadda ya saba kullum cikin shirinsa
na training ya fito, jugging na gudu yau ta gabas ya mike
sabanin arewa da ya ke bi kullum. Hakan kawai ya tsinci
kanshi da son mikewa gabas. Hanyar ta GRA shafe take babu
mutane kasancewar anguwa ce da ake rayuwar shiru ba sosai
za ka ga mutane suna hayaniya ba kamar cikin gari. Saleem ya
ci gaba da sassarfa hanyar da ya bi shiru ba ka jin komai sai
kukan tsuntsaye sai kalilan jefi-jefin mutane da yake shigewa
a kan titi. Sanye yake da riga ja mai gajeren hannu irin ta 'yan
kwallo wato Arsenal sai wandonta ita ma kamfanin Arsenal
sai facing cap mahadin rigar wanda ya kara masa kyau
kasancewar su kalar ja. Da ka gan shi ka ga kakkarfan namiji
mai cikar zati da siffar jarumta, ga wanda bai san shi ba zai
dauka irin Turawan nan ne ko Larabawa don kowanne ka
sanya shi cikinsu tuni zai saje da shi. Cikin gudunshi mai
dauke da sassarfa yake jiyo kamar karar bindiga, hannunsa ya
shafa cikin aljihunshi amma sai ya ji wayam babu bindiga, tuni
ya tuno ashe ya bar ta cikin aljihun kayan da ya cire jiya na
training, cike da karfin guiwa ya ci gaba da bin hanyar da yake
jin harbin, a lokacin ne ya kara jin karar harbin sosai, yana
dukan kunnuwanshi. Gudun nashi ya karawa kaimi don son
iske inda yake jin harbin, babu tsoro ko kadan a zuciyarshi ya
yi imanin in har hukuma ce shikenan sai ya yi tafiyarshi haka
in barayi ne ya kudura a ranshi yau fa sai dai shi ko su. Mafi
rinjayen zuciyarshi ta ba shi farayi ne don a hanyar gurin sam
babu office na hukuma ko gurin training na hukuma a gurin
68
AKWAI KURA
bare ya ce su ke koyar da yaransu harbi. Daga nesa ya hangosu kowa rike da bindiga, mace da namiji, ya gane macen
ce ta siffan halittar ta dake da bambanci da na namijin, cikin su biyun kowa fuskarshi rufe take ta mask sanye suke da riga da
wando iri daya mai tambarin arsenal jajaye kamar na jikinshi. Saleem jarumi cikin sanda ya fara lallabawa don cafke daya daga cikinsu, burinshi ya rike bindigar daya, ya san tabbas ya gama da su. Daga inda ya boye yake hango su, namijin ya rike hannun macen da alama ita yake koyawa harbi. Tas! Tas! Tas! Kake ji, ta saki harsashin bindigar sama sannan ya saki hannunta tare da umurtar ta ita ma ta yi, inda ya yi cikin
kuskure da rashin kwarewa ta saita bindigar sama maimakon ta
harba sama sai ta harbi gefen da Saleem.yake. "Wash Allah
na!" ya fada cikin muryarshi mai sanyi, take karfi ya shige shi,
da gudu ya fito a maboyarshi ya tunkari inda mace da namijin
suke hannunsa daya rike da inda ta harbe shi tuni jini ya fara
bulbula a hannunshi, namijin ne ya fara ankarewa da saurayin
da ya dumfaro su, ai da gudu ya fauce daya bindigar dake
hannun macen ya ari na kare. Sam ita ba ta kula da abin da
yake faruwa ba, zatonta don ta yi mistake ne ya kwace. Cikin
murya mai karfi ya kwala mata kira, "Beb ki gudu mu je Beb
Beb yi sauri yi sauri mu gudu." Ina! Kafin ta ankare tuni
saurayin ya cim mata, rike ta ya yi sosai tana kokarin fusgewa,
ai tuni ta hada dukkan karfinta ga karfin tsoro ta danna ma
hannunshi inda ta harba cizo, karamar kara ya yi, bai san
lokacin da ya sake ta ba ta gudu, sai mask nata da ya samu
damar cirewa. Da gudu ta ari na kare yayin da gashin kanta da farin bayanta ya bayyana, ko kadan ba ta yi tunanin juyowa ba
don kada ya gane fuskarta, don ita tun ganin farko da ta yi
masa har ta yi yunkurin guduwa tuni ta gane shi. Da gudu sosai
ta cimma saurayin ya tada mashin hawa ta yi tuni ya ja mashin
din a guje suka bar wajen, sai da suka tabbatar sun yi masa
zarra kafin ya nemi gefen titi ya tsaya. "Beb ba mu da lokacin
magana ki tafi gida za mu yi waya kawai," "Ok," ta fada cikin
69
AKWAI KURA
sauke numfashin cin nasara. Jakarta ya ciro a jikin gaban
mashin din, "Karbi kada a yi ram da mu, kin ga gari ya fara
wayewa sosai." Ta kalli agogon hannunta karfe shida saura
minti daya. Saurayin ya ja mashin ya tafi. Tafiyarsa bai fi
minti guda ba mashin ya tsaya a gabanta, da alamun da ma ita
ya zo dauka. Cikin sauri ta haye mashin din, "Yi sauri kada in
makara." cikin sauri ya ta da mashin tare da sanya masa giya
mai karfi ya dauki hanya don kada su makara.
***
Jini ne sosai ke zuba a hannunshi, tuni jiri ya fara dibar shi
saboda zubar da jinin da ya yi duhu-duhu ya fara gani, amma
haka ya daure ya ci gaba da tafiya domin ya yi imanin in har ya
fadi a wannan gurin sai dai gawarshi don wannan jeji shi
kanshi da yake cikin anguwar bai taba sanin da shi ba sai yau
da tsautsayi ya kawo shi, ya jika labba cikin jarunta ya kuma
mikewa yana tafiya, burinshi daya shi ne ya fito inda zai samu
mutane domin neman taimakonsu ya yi tafiya mai nisa yayin
da jinin yake ci gaba da zuba a hannunshi. Dabara ce ta fado
ranshi na ya cire rigarshi ya daure hannun, saboda kada
jininshi ya kare a kasa. Numfashin wahala ya ja tare da sanya
gwiwarsa duka a kasa yana kokarin cire rigarshi da daya
hannun da babu ciwo. Wayarsa ya ji alama wanda dimuwa ya
sanya ya manta da ita tuni ya ji sanyi a ranshi, cikin dauriya ya
ciro wayar number Daddy nashi ya fara kira amma bai dauka
ba. 4 missed call ya yi masa still ba a dauka ba. Momminshi
ya kira, wayar Mommy a kashe hankalinsa ya ji ya kuma tashi
jijiyar hannunsa na masa tsa nanin ciwo saboda a nan harbin ya
same shi. Saleem ya ciza baki shi kansa ya san matsala ta jijiya
yana bukatar emergency. Tuno da hakan ya sa shi kuma tashi
ko Allah zai sa ya fito inda zai cimma mutane domin ya yi
imani komai zai iya faruwa da shi, a karo na uku cikin sauri ya
lalubo number Auntynshi, bugu daya ta dauka. "Ka ga jarumin
jarimai yau an yi mafarkina ne?" cikin nishin wahala ya ce da
70
AKWAI KURA
ita, "Zan mutu zan mutu," a firgice ta mike daga kan gadon,
"Kana ina Bro?" "Wallahi ba ni gida ina tare da Abban Affan...wash!" ya katse mata maganar, "Mommy. Mommy
nake son ji." Dif! Wayar ta katse, tuni ta bi layin da kira ta yi.masa 6 missed call amma ba ta dauka ba hakan ya sa ita ma
ta kira Daddy amma bai dauka ba ta kuma kiran wayar Mommyn a kashe, tuni ta fashe da kuka. Abban Affan dake
wanka da gudu ya fito daure da towel ya rike ta yana tambayarta lafiya amma sai kuka take, "Bro bro!" "Me ya
samu da shi?" da kyar ta sanar da shi me ke faruwa. Cikin
sauri ya dauki jallabiya ya sanya, "mu je gidan." A hanya suna tafiya tana kuka, tuno da Amrah da ta yi ya sa ta dauki wayarta
ta hau kiran Amrah don ta san in har Amrah na lafiya to fa ta
zo aikinta gidansu, ai ko cikin sa'a Amrah na gaban Mommy
suna gaisawa cikin sauri ta ce, "Maman Affan kai wa Mommy
wayar." "Ina gabanta Aunty ga ta nan," Amrah ta mikawa Mommy wayar Mommy ta karba da kuka Mera ta sanar da Mommy abin da ya faru Mommy cikin sauri ta kashe wayar
maimakon ta dauko nata dake kashe tuni ta fara sanya number
Saleem a cikin wayar Amrah ringin biyu ba a dauka ba,
Saleem dake cikin wani hali saboda azaba duk jarumtarshi yau
kam ta kare ya gama sadaukarwa yau kam tashi ta kare. Yana
ganin wayar tashi na kara number babu suna amma ba shi da
ikon dauka saboda azaba, da kyar ya samu ya daga wayar,
nishi kawai yake saukewa. muryar Mommy da ya ji ya sanya
ya fashe da wata wahalalliyar kuka, "Mommyna zan mutu,
please ki yafe ni." Mommy a rude take fadin, "Kana ina son?"
amma ya kasa ba ta amsa, "please son yi kokari daure ka tabbatar min da sunanka da Daddynku yake fada 'JARUMI'
daure ka yi min wannan alfarmae." Idonsa ya sauke akan
gidan ruwan cikin duru-duru da idonsa yake masa ya samu
damar hada haruffan, "Gidan ruwan FAISAL Eksal Table
water." Dif! Numfashinsa ya dauke.
71
AKWAI KURA
A rude Mommy ta yi dakin Daddy. Tsabar rudewa Amrah na
tambayar ta lafiya lafiya, ina, ta yi gaba a rude ta shiga tashin
Daddy dake bacci tana kuka, "Daddy son son," A firgice ya
tashi a mafarkin da ya ke yi na Saleem din yana neman
taimako babu wanda ya taimake shi. "Me ya samu son?" ya
fada yana rike ta. "Mu je Daddy mu je," take fada. Da sauri ya
biyo ta zuwa kasa. Amrah da Zahra dake tsaye suna rude
Mommy ta karbi hijabin jikin Amrah, "Mu je Daddy." "Muje
ina?" "Son yana gidan ruwan Faisal eksal table water."Cikin
rudewa Daddy ya ce, "Mu je kada dana ya rasa ranshi, mu je,
na gan shi a mafarki cikin jini." Tare suka fito dukkansu har
da Amrah cikin damuwa ba ka jin komai sai kukan Mommy da
na Zahra, ita kanta Amrah sai da ta zubar da hawayen tausayin
wannan family. Daddy da kanshi ya shiga direbin side.
Mommy da ta fada ciki suka fice a rude kamar za su taka masu
gadin a first gate, a guje suka fita. Agate na karshe ne suka
cimma motar su Mera. Mera ta fito tana magana, ina, Daddy
ya cinna hancin motar kan titi, ita ma Mera da mijinta da sauri
suka rufawa Daddy baya. Bai sha wuyar gano inda gidan
ruwan yake ba kasancewar Daddy ya san unguwar sosai tuni
ya gane gidan ruwan da ake nufi. Cikin minti bakwai ya kawo
su wajen gidan ruwan amma wayam babu Saleem. Cikin gidan
ruwan suka shiga nan ma babu Saleem sai ma'aikatan gidan
ruwan; mutum biyu dake shirin aiki da alamar yanzu su ma
suka zo. Cikin damuwa Daddy ya tambayesu ko sun ga Saleem
amma suka ce ba su ga kowa ba. Da sauri suka fito daga gidan
ruwan. "La! Mommy kalli can kamar mutum ne kwance." Da
sauri Daddy ya ta da kafa don cumma gurin da Mera ta nuna,
ai ko a rude ya rike shi, "Son son wa ya yi maka wannan aikin?
Inna lillahi wa'inna ilaihir rajiun!" yake maimaitawa. Mommy
da Mera sai kuka suke yi Daddy tsabar ya rude ya rasa yadda
zai yi da Saleem dake kwance illa fadi yake, "Son wa ya yi
72
AKWAI KURA
maka hakan?" tuni hawaye suka fara sauka daga fuskarshi na tausayin dan nashi. Abban Affan ne ya ankarar da shi da,
"Daddy mu je Asibiti." Daddy ya manta da maganar asibiti.
Da sauri suka ciccibi Saleem suka sanya shi a motar Daddy.
Abban Affan ne ya ja motar don kai Saleem asibiti, domin ba
zai bar Daddy ya yi dirabin cikin wannan halin ba. Mera ba ta
motar mijinta suka rufa musu baya zuwa asibiti, "Ibrahim mu je 44 hospital," Daddy ya ce da Abban Affan.
***
Hankalinta ya tashi sam ba da niyya ta harbe shi ba ita da take
bincike a kanshi ta ya ya za ta kai masa hari. "No," ta furta a
fili.hasali ma ba ta san yana wajen ba, ita kanta ba karamin
mamaki ta yi lokacin da idonta ya sauka a kanshi. Ta razana
sosai lokacin da ta ankare shi ne tsautsayin mistake nata ya hau kanshi. Amrah ta dan muskuta a katifarta ta kalli hannunta da harbin ya kwace ta yi dan murmushi, "My hand wato akan makiyinka ka fara kwarewa a koyon harbi!" Amrah ta tsayar a ranta da za a ba ta bindiga karo na biyu don koyo tabbas za ta harba cikin kwarewa. Don yau fitarsu ta dauki haske sosai musamma da ta yi mistake a nan ta gane harbin sosai. Mommy ce ta fado mata a rai tare da Maman Affan ganin irin tashin hankalin da suka shiga saboda Saleem. Tuni tausayinsu ya cika mata zuciya musamma da ta tuno yadda Mommy take kuka faruwar abin sam ranta bai yi mata dadi ba ganin masu nuna mata kauna suna cikin damuwa kuma
duk ita ce sila, wayarta dake kara ita ce ta katse mata tunaninta cikin kasala ta danna kore, “Anas ina ka shiga? Kira
nawa ba ka dauka ba?" Anas ya ce; "Yi hakuri Beb wallahi ba
na nutse ne saboda abin da muka aikata don tsoron kada a ce
wanda kika harba ya gane mu, tsorona daya aikina da abin da
zan taras na hukunci. Beb da ma na fada miki aikin fa akwai
hatsari. Ina son ki da yawa Beb ta inda bana hango matsalar da
za ki sanya ni a ciki." Amrah ta karba, "Haba Anas sai ka ce
73
AKWAI KURA
kai din ba hukuma ba? Waye zai ga bindiga a hannunka ya
tuhume ka? Ai ko ni da nake mace ban karaya irin taka ba,
please ka kwantar da hankalinka kada ka karya min zuciya
daga ni har kai babu abin da muke yin shi cikin son zuciya aiki
ya zo mana da hakan." Anas bai sare da rashin tsoron Amrah
ba sai yau, mace mai kamar maza ya fada a zuciyarshi. Wani
abin mamaki Amrah ta ki sanar da shi dalilanta na son ya koya
mata harbi, abu daya ta sanar da shi shi ne in lokacin ya yi za
ta sanar da shi dalilinta. "Hello kana ji na?" muryarta ta dawo
da shi cikin hankalinshi. Beb amma kin san wanda. kika harba
kuwa?" ya jefo mata wannan tambaya. " A'a ban sani ba kai
ka san shi ne?" ta fada don son jin amsar da zai ba ta.
"Assitant controller na custom ne," ya fada cike da sanyin
murya. "To sai me?" Amrah ta fada, "ka ga Anas ni kada ka ka
sa in karaya abin da ya wuce ya wuce matukar muka ce za mu
dinga tuna abin da yawuce na barna ko bakin ciki lallai
hakarmu ba za ta cimma ruwa ba." "Ok," ya fada cike da
karfin gwiwa. Kiran da ya yi mata ya yi mata ne cike da
damuwa amma abin mamaki tuni Amrah ta sanya shi ya manta
da damuwar illa karfin gwiwa da nishadi da yake ji sai don
dadin muryarta. Ba su ajiye wayar ba har sai da suka canza
location na fitar Asubahin gobe, gare su babu abin da za a fasa
tsakanin mutuwa da hisabi.
***
A sume suka iso da shi asibitin, Saleem bai san wanda yake
kanshi ba. Da sauri Nurse suka tura shi kan gadon marasa
lafiya. A rude Daddyn nashi ya fito yana hawayen kada ya rasa
danshi, tuni ya manta da shi din waye a gari. Tuni Doctors sun
rufu a kan Saleem don ceton ranshi, kasancewar tuni sun farga
da waye mara lafiyar, matsayinsa bugu da kari Daddynsa shi
ma babban mutum.ne a Nigeria. Gaba daya Daddy da
Mommy sai sintiri suke sun kasa zama. Haka Mera sai kuka
take yi mijinta na rarrashin ta. Daddy da Mommy kowa na
74
AKWAI KURA
cikin damuwa babu mai rarrashin wani a cikinsu. Bayan share
tsawon awa daya da rabi likitocin suka fara fitowa da sauri. Daddy ya fara tambayar su lafiyar danshi. "Mu hadu a office," daya daga cikin doctors din ya ce, da alamar shi ne babban
cikinsu dukkansu Daddy da mommy suka rufawa likita baya, Mera kadai aka bari a tsaye ita da mijinta. "Bismillah," Doctor
ya nunawa Mommy da Daddy kujeru biyu dake office din. "Doctor I hope dana zai tashi?" Doctor ya share gumi, "Ка kwantar da hankalinka insha'Allahu he gonna br alright, jini ne ya zuba sosai a jikinshi kasancewar harbin kan jijiya aka yi masa, Alhamdulillah Allah mai yadda ya so yau kwana biyu ke nan Saleem din ya zo nan asibitin aka dibi jininshi kamar yadda ya saba ba da kyauta time to time a baiwa mabukata, kun ga Allah cikin ikonshi ba mu yi amfani da jinin ba da rabon wannann karon tanadin jinin ya yi wa kanshi." Daddy ya share hawayen da ya zubo masa sai don dadin abin da dan nashi yake yi na alkairi ba tare da ya sani ba. "Masha Allah," dukkansu suka fada shi da Mommy, alkhairi danko ne ga shi Allah ya nuna mana ishara akan son! Allah ya karawa Annabi daraja Sallallahu alaihi wasallama,” "Amin," suka hada baki wajen fada. Doctor ya ci gaba da yi musu bayani, " mun yi
nasarar cire masa harsashin, Allah ya tsare ma an kawoshi
asibiti cikin lokaci don gurin bai kame ba lallai an auna arziki, harbi a irin wannan gurin shi ne yake sanyawa hannun mutum ya nakasa, kuma in ya zo da karar kwana ma tuni ake rasa rai saboda hanyar nan jini yake gudana, nan da nan jinin yake tsiyayewa.” “Alhmdulillahi mun godewa Allah," Mommy ta fada. Daddy ya ce; "Doctor yanzu babu damuwa ko?" "Babu damuwa Alhaji duk wani taimako an gama yi masa insha'Allah farkawarsa zai tashi da sauki sai mu ci gaba da addu'ar hakan." "Muna iya ganin shi?" Daddy ya сe; "E mu je ba matsala." A
tare suka fito, Doctor ya yi musu jagora har dakin da aka kwantar da Saleem. Daki ne na musamma da ake warewa
manya, Saleem na kwance yana baccin wahala, a hakan
75
AKWAI KURA
dukkansu suka shigo dakin cikinsu har da Mera da mijinta.
Daddy ya karasa jikin gadon na kwance yana bacci hannunsa
daya sanye da jini ana yi masa karin jini. Daddy ya rike daya
hannunsa da babu komai. "Allah sarki son, yau daya
fuskarshi ta yi fayau alamar babu wadataccen jini a jikinshi,
da gani ka san yana shan wuya." Daddy addu'a ya shiga
tofawa dan nashi. Mommy ma yadda Daddy ya yi ita ma
hakan ta yi ta tsaya kusa da kanshi tana shafawa tana tofa masa
addu'a tana tsiyayar hawayen tausayin dan nata. "Allah sarki
son Allah ya saka maka ko waye ya yi maka wannan
abin," .Mera kuwa kuka take yi wanda babu kara saboda kada
ta ta da kanin nata a bacci. Ranar dai babu wanda ya yi
yunkurin barin asibiti, burin kowa Saleem ya farka su ga ya ya
lafiyarshi, haka 'yan gida ma suna ta waya kan suna son zuwa
amma Daddy ya hana ya ce su bari ya farka sai karfe goman
dare kafin Mommy da Mera suka dawo gida yayin da suka bar
Daddy da Affan Affan a asibitin duk da ba a bukatar mai jinya
kasancewar babban asibiti ne na kudi komai suna da mai yi
musu amma haka Daddy ya ce babu inda zai je har sai ya ga
tashin dansa.
***
Washegari tuni labari ya baza cikin zuriya har ma da garin
Kaduna duk inda ka zaga maganar daya ce take rushing an
harbi Assistan controlla tuni jita-jita ta baza ko ina wasu su ce
makiya ne suka harbe shi wasu su ce Gwamnati ke son kashe
shi saboda an ga ya fara sanya ci gaban al'umma an ga yana
da gaskiya. Maganganu kowa da albarkacin bakinshi. Shi ko
Saleem tun da ya farka daga suman wahala bai ce kala ga
kowa ba ta kanshi yake duk da tarin tambayoyin da yake sha
daga Dad nashi Mommynshi kai har ma da hukumar'yan sanda
dana Custom wanda tun samun labarin faruwar abin suka yi wa
Asibitin 44 kawanya, su ma hukumar sojoji ba a bar su a baya
ba kasancewart asibitin na 44 asibiti ne private na sojojin Land
76
AKWAI KURA
Army. Tuni suka ba da gudummawarsu ga Assistan controlla
na security ko ina ka bi a cikin asibitin jami'an sojoji ne dana custom, hatta bakin kofar na Saleem security kyakkyawan
matakann tsaro aka sa. Babban shugabansu na custom ya
sanya tsaron lafiyarshi tare da alwawarin ko waye ya yi
wannan aika-aikar ga yaronshi zai dauki mataki mai tsauri akai. Ganin hukumar tasu ta dauki mataki da kanta ya sanya Daddy
ya bar nashi daukar matakin sai dai sosai ya kara burin
taimakon al'umma don ya ga ribar taimako akan gudan jininsa Saleem.
***
A halin yanzu ta gama kwarewa kan harbi ta sanya a ranta in
za a fita filin daga na yaki da ita tabbas za ta iya fafatawa da
arna a fagen yaki in har da bindiga ne wannan ya sa ta zuba
makudan kudi ta mallaki bindiga tata ta kanta ta hanyar Anas. Shi kan shi Anas lamarin na Amrah ya daina ba shi tsoro da
mamaki sai burgewa gare shi, ko a tarihi ko a films bai taba cin karo da labarin mace kamar Amra ba. Kusan koyaushe suna
tare wajen koyon harbi hakan ya kara musu kusanci sosai ita da Anas, a baya ba ta jin burbushin soyayyar Anas a ranta.
amma saboda kusancinsu na yanzu da yadda yake ta sadaukar
da ranshi kan faranta mata rai, wadannan dalilan ya sa ta fara jin soyayyar Anas na huda jijiyoyin jikinta, Abu kamar wasa har ta fara baiyana masa hakan a fili. Tirkashi! Ga Anas nan da nan ya fahimci ya fara samun fada a gun Amrah, ba karamin farin ciki ya yi ba na samun sauyi gun Amrah imfact
ma har ya fara jin shi kam wannan aiki da ya hada su gaba ta kai shi wai gobarar Titi a Jos. Kiriniya irin ta Amrah tare da saurin kwarewarta kan abin da ta sanya ranta tuni ta koyi mashin gun Anas. Ranar da ta fara maganr koyon mashin Anas ke tuka su ita kuma tana bayanshi za su dawo inda yake
sauke ta kullum daga gurin koyon harbi ta ce da shi ya ba ta ta kai su gida. Kamar da wasa Anas ya ce; "Ai ba ki iya ba."
77
AKWAI KURA
Amrah ta ce; "Ai ina kallon yadda kake control hands naka don
haka na fara ramfo zancen." Anas ya yi dariya "Ko ni dake ba
amfani da mashin nake yi ba mota ya sakalta ni yanzu da kika
sanya ni amfani da mashin ranar farko da na hau sai da na yi
kamar zan fadi." Cikin shagwaba ta ce; "Ni dai ka ba ni."
"Ni a su wa in hana matata mashin? Bara in faka gefen titi."
Ya faka, "zo ki hau Beb," ya sauka ya ba ta gurin zamansa.
Ga mamakin Anas sai gani ya yi Amrah ta fara jan su, sai dai
rashin kwarewa. "Beb tsaya gobe in mun fita zan koya miki
sosai sai dai lokacin namu babu yawa kin ga minti talatin
garemu 5am 25 muke fitowa mu tashi shida saura 5 minute
lokacin ya yi mana kadan gaskiya, ko za mu bari mu gama da
daya?" "A'a duka za mu yi shi." Anas ya ce; "To Beb sai
abin da kika ce, ni kin san bawanki ne kawai umurni za ki yi
min ki ga aiki da cikawa." Amrah ta harareshi, "Kai bawan
Allah ne, ehe ba nawa ba, amma me zai hana mu fara fitowa 5
am da minti 20 tun da karfe 5: am da minti 15 ake sallar Asuba
ka ga sai mu raba lokacin biyu ma mashin da harbi tun da
yanzu ai na kware ba ni da matsala, kawai muna fita ne don
kara basira ko?" "An gama Beb hakan za a yi.
Washegari tana idar da sallar Asuba ta tsuke cikin kayanta na
training kamar yadda ta saba in za ta fita. Anas ya zo da ma shi
ya dauke ta. Granny dake dakinta wanda ba ta taba sanin
wainar da ake toyawa ba zatonta Amrah na fita wajen aiki ne
kamar yadda ta sanar da ita fara aikinta gidansu Saleem kan
son bincikenta da Abban Amlah ya ba ta, sau da yawa tun da ta
fara fita biyar da rabi na Asuba ta dauka sauri ne yake hana
Amrah yi mata sallama bare ta karya kumallo, yau kam
asirinta ya tonu ta gama shirinta ta dame ke nan tana shirin fita
fuskarta 6oye da mask wanda farayi ke sanyawa tana kokarin
daura nikab ta kuma 6oyewa fuskar Granny ta dumfari dakin
don tashin Amrah ta yi sallah kasancewar ita Grannyn ta
makara zatonta Amrah ba ta tashi ba. Kicifis! Ta yi arba da
78
AKWAI KURA
idon Amrah dake cikin mask, da sauri ta koma baya cikin tsoro
a zatonta barayi ne suka shigo, ko da wasa ba ta dauka Amrah
ba ce. Ita ko Amrah da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 12