suna
hira jefi-jefi har doya ta dahu. Amrah ta daka sakwara a turmi
ta ajiye a gefe. Grace ta kama baki, "Kin ci sunanki; agogo
sarkin aiki, yanzu har kin yi wannan aikin? Kuma na ga kin yi
an kai wa oga wannan." Amra ta ce; "Girki inda kayan wuta
ai mai saukine Mommyne na san dataso abincin saboda
masoyintane Grace tagyada kai shi ya sa ajiya ke sonki kinaba
ta irin wannan girkin Amrah ta yi dariya ngd Grace ai ita ma
tana sona dole insota, Amrah ta ji dadi data tuno akwai sauran miyan kowannane. Tadan dakata Grace dan Allah ko daki dan
sayamin katin waya wallahi namanta inada urgent kira kuma
babu na plashing awayara Bakomi Ai ko dan wannan girkin
danaci mai dadi naje miki Grace ta fada Amrah ta jawo jakanta
taba ta naira dubu, "Ungo ki sayo min Mtn na 700 ke ma ki
saya na canjin." Grace ta ji dadi tana godiya, ita dai Amrah burinta kada Grace ta fita don ba ta da matsalar kati, ita
wayarta sai dai wani katin ya taras da wani katin. Grace tana
fita Amrah ta je ta sanya key a kofar shigowa side din, da sauri
125
AKWAI KURA
ta zuba miya a fulas ta dauko basket ta jera kulas din guda
hudu.
A hankali cikin sanda kamar barauniya ta shigo cikin falon
nashi, sai da ta duba gabas ta duba kudu ba ta ga kowa sannan
ta ci gaba da shiga falon tana rike baki don kada a ji motsinta.
Tun shigowarta ya ga hasken inuwarta ta cikin labule. Cike da
mamaki yake kallon ta, daga bisani cikin hankalinshi ma ya
tashi ya boye a cikin labule tare da lekowa kadan-kadan don
ganin me za ta yi. "Alhmdulillah," ta fada a ranta ganin ba
kowa, a zatonta ba ya dakin, tana daga kicin ta ga sanda ya fita
abin da ba ta sani ba fitarsa ba da jimawa ba ya dawo dakin
nashi ta farauniyar kofar da babu wanda ya san da ita sai
Daddynshi kadai.
Dinning table ta wuce, abincinsa da aka jera ta nufa, miyar ta
dauka duka da kuskus din ta daga sakwarar da miyarsa ta
matsar da shi gefe. A hankali ta ciro basket cikin hijabinta ta
ciro wasu fulas exactly irin wannan ba su da bambanci ta ajiye
masa wani kuskus din da miya. Da sauri tare da sakwarar da
miya ta mayar da wadancan din cikin basket din har da ruwa
da lemo sai da ta kwashe ta fito da wasu ta canza. Gabas da
kudu ta kuma dubawa ba ta ji motsi ba, cikin sanda ta fito daga
falon nashi tana jin dadin nasarar aikin, babu wanda ya gan ta,
da sauri ta ajiye basket din a kicin ta zare key na kofar falon,
miyan ta zuba ruwa ta wanke tare da samun leda babba ta juye
abincin a ciki ta jefa a cikin katuwar jakarta. Abincin dare ta ci
gaba da hadawa tuni ta samu nutsuwa a cikin zuciyarta tana
daga kicin ta ji maganar Mommy na sallama ga su Meena,
"Hmm," Amrah ta ce tare da murmushin mugunta.
126
AKWAI KURA
Saleem ya fito a cikin labule gemunsa ya shafa yana
murmushin ganin duk abin da ta yi, wato a duniya yanzu kowa
ya dawo mugu. Masu aure boka, zawarawa boka, 'yanmata
boka, masu mulki boka, talaka boka, kai duniya ina za ki damu?
Ya godewa Allah da ya nuna masa wannan mummunan gani.
Cikin sauri ya dauki duka plask din ya bi hanyar baya dan
zubar da abincin. Cak! Ya tsaya don maganar da zuciyansa ke
fada masa, 'anya muguwa ce? In da muguwa ce ita ce ta dafa
abincin ai da tun a gurin girkin za ta idda nufinta ba sai ta bari
an jera cikin bangaren nashi ta biyo sawu ba. A matsayinsa na
jami'in bincike shi ya fi cancanta ya gane mai laifi. A hankali
yajuya da abincin ya koma falon shi. Kan dinning table din ya
mayar yana wasu-wasi a zuciyarsa, tuni zuciyarsa ta yarda da
shawarar da ta ba shi na cin abincin domin in ma sihiri aka yi
ai ya jima yana cin girkin nata yanzu kam ya yi imani duk
kudurin da aka yi ya wanzu a kanshi, sai dai daya zuciyar na
tunatar da shi bai taba cin abinci babu bismillah ko tare da
addu'a ba. A zuciyarsa bisa ga mafi rinjaye ya ji ya gamsu da
maganar zuciyarsa ya ci abincin, Addu’a tana canza kaddara.
Abincin ya bude, kamshin girkin ya bugi hancinsa tuni ya ji
yana kaunar cin abincin duk da lokacin cin nashi bai yi ba, ya
dauko filet da kansa, bai jira mai zuba mishi ba ya zuba a filet
tare da sanya cokali ya yi bismillah tare da yakinin Allah zai
kare shi akan komai, ya fara cin abincin yana ci yana lumshe
ido saboda dadin girkin.
***
Dariya sosai take kyalkyalawa har tana rike ciki, "Kai bestyna kai bestyna, wallahi ke muguwa ce yanzu tsakani da Allah ki
rasa wacce shiga za ki yi sai wannan, haba bestyna shopping fa
za mu je kuma da babyna, haba bestyna ai sai ki ba da ni a
gaban arna," ta ci gaba da fada, "gaskiya ba zai yiwu ba sai
127
AKWAI KURA
ka ce matar malam ko liman ni kam ban taba ganin ki da katon
hijabi har kasa ba bare nikabi," ta ci gaba da tsula dariyarta,
"amma ko ba komai yau kin sa ni nishadi mai yawa." Amrah
ta dokawa Zahra harara, "To sai dai in ba zan je ba, ni yau
shigar da na ga damar yi ke nan, ai ba kullum ake kwana a
gado ba, yau shigar ustazai nake son yi," ta bata rai alamar
babu wasa. Zahra ita ma bata rai ta yi tana kwalawa Ummi kira.
Ummi dake kicin ta fito da sauri hannunta rike da ludayin miya.
Besty ta hau buga kafa, "Ummi don Allah ki ga shigar da
Bestyna ta yi, haba Ummi ai sai ta ba ni kunya a gun Babyna."
Ummi ta kalli 'yar tata tana kama baki, "Ikon Allah kuma
shigar ta yi miki kyau, ai da ma shigar da ya dace ku dinga yi
ke nan amma saboda zamani kullum ba ku da abin fita sai
mayafi." Amrah ta washe baki daga fushinta a zatonta Ummi
za ta goyi bayan Zahra sai ta ga saßanin haka. "Kai Ummi,"
Zahra ta fada tana buga kafarta. Ummi ta yi murmushi,
"Amrahn Abbanta ba a yi hakan ba tun da fitar ta musamma ce
cire hijabin sai ki nemi abaya ki sa tun da ita ma shiga ce ta
mutumci kin ga sai ku yi anko da bestyn taki." Zahra ta washe
baki, "Yauwa Umminmu Allah ya biya." Amrah ta koma daki
ba don ta so ba ta nemi abaya ta sanya tare da daukar
dankwalin abayar ta yi rolling bayan ta gama shirin ta dauki
nikabin ta kuma rufe fuskarta ta fito falon tana kunkuni. Zahra
ta kwashe da dariya, "Ko ke fa ai kin fi kyau a hakan amma fa
abin zai fi kawo kyau in kin dan cire nikabin. "Wallahi sai dai
kada in je," Amrah ta fada tana shirin komawa daki. Da sauri
Zahra ta riko ta tana dariyar mugunta ita ma Amrah dariyar ta
fara tare da kaiwa bestyn tata duka.
***
Zahra na gaba kusa da Babynta suna shan hirar soyayya. jefijefi Amrah ke sanya baki saboda Zahra ta dame ta da son sanya
ta a cikin hirar tasu, shi ma Maheer sai tsokanar ta yake yi yana
cewa da ita, "Hala angon naki ustaz ne? irin wannan shiga
128
AKWAI KURA
haka." "Baby ke ma irin shigar za ki na yi in za ki fita don ba
zan yarda a rinka kalle min kyakkyawar fuskar matata ba."
Zahra ta yi dariyar jin dadi, "Kai baby ita ma fa yau ne ban san
munafuncin da ya sanya ta sa ba." Amrah ta amsa "E din ai
dai bai taba gani na da wata shigar ba don haka makircinki ba
zai yi tasiri ba, angon mu wallahi ka sanya mata doka daga yau
kada ta fita sai da hijabi da nikabi." Zahra ta juyo bayan mota
ta jefi Amrah da jakarta, "Zan rama ne wallahi bara in je gida
in hada ki da Yaya Anas, tun da haka ne za ki fara sanya
nikabin na dole don yau kam munafunci ne ehe."
Shakiyanci suke yi wa junansu har suka isa super market din.
Tare suka shiga dukkansu uku. Maheer na gaba Zahra da
Besty na bin sa sai ka ce 'yan biyu sun yi kyau cikin abaya.
Basket na rike a hannun Maheer Zahra tana zabar abin da take
so, amma Amrah ba ta dauki komai ba. Zahra ganin ba za ta
dauka ba shi ya sa ta fara daukar komai bibbiyu. Kaya sosai
Zahra take dauka Amrah tana ta hararar ta kan ta bari hakan,
amma Zahra ba ta gane ba sai kara loda kaya take yi. Cikin
dabara Amrah ta matso kunnrn bestyn ta sanar da ita ta bar
dibar kayan haka. Maheer dake gefe ya ce; "A'a bar matata ta
zabi son ranta." Ganin bestyn ta ci gaba da dibar kayan
Amrah ta matsa gefe, duk kunya ta ishe ta daga karshe ma sai ta matsa layin tedis ta daga nikabinta tare da saita kemarar
wayarta ta fara daukar kanta a hoto. Zahra dake can gefe tana
daukar kaya da sauri ta bar daukar kayan, ana son hoto ke nan,
ta matso ta rungume bestyn nata ta baya. Tuni Amrah ta ci gaba da daukar su a hoto suna dariya, "Ai da ma saboda ke na yi na san ba ki ganin hoto ki bari musamman a irin wannan gurin." Sun dauki hotuna sun fi kala hamsin, wani su turo baki
wani su yi dariya, styles kala-kala Maheer na rike da basket
yana kallon su ta baya suna daukar hoto, sun ma manta da shi
cikin dariya shi ma ya matso ta bayansu yana dariya, "A dauka
129
AKWAI KURA
da ni na ga abin wariya ne." Amrah da ta ji kunya ta matsa
gefe tare da sauke nikabinta, "bara in yi muku angonmu.
"Yauwa bestynmu da kin kyauta." Maheer ya matsa jikin
besty. Amrah ta ci gaba da daukar su hoto sai da ta yii musu
kala takwas different colour kafin suka je gurin biyan kudi.
Maheer ya mika musu ATM (katin cirar kudi) su cire tare da
kara waya a kunnensa ya matsa gefe yana amsa kira. Zahra ta
kuma daga nikabin Amrah, "Bestyna bari in yi mana hoto a
nan gurin, ya yi min kyau." Zahra ta yi musu kala biyu suna
dariya, ita ce kalmar da kunnenta ya ji ke nan da sauri ta kalli
inda ta ji maganar, ido hudu suka yi kallon minti daya ta yi
masa ta sauke nikabin da sauri duk da ba ta san mutumin ba ba
ta kuma taba ganinsa ba amma jikinta ya ba ta da ita yake
duba. Cikin sauri ta duba gefenta, Zahra ta yi wajen Maheer
dake ansa waya. Amrah ta karaso gurinsu, "Mu je ko?"
Maheer ya danna mata hararar wasa, "A'a ni ma ina son yin
shoppping ga tsohuwa don na kwana biyu ban yi mata ba."
***
Waya ta kara a kunnenta kamar mai amsa kira, cikin dabara ta
fita daga super market din hannu ta sanya ta tsayar da mai adaidaita-sahu, tun kafin ya tsaya cikin sauri ta fada cikin Keke
napep. Mai keke napep ya zabura da gudu kamar zai tashi
sama, ta cikin mirrow ta kalli fuskar mai a-daidaita-sahun
cikin razana ta dafe kirji, "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un,"
ta fada tana zare ido, "Malam tsaya tsaya a nan zan sauka,
amma ko kallon ta bai yi ba illa wuta da ya karawa babur din
tare da mike hanya sambal inda zai sada ka da hanyar barin
garin Kaduna. Amrah da ta gama rudewa tuni ta fara karanto
duk addu'ar da ta zo bakinta. Karar wayarta da ta karade adaidaita-sahun ya sanya mai keke napep din ya dan rage gudu
tare da matsawa gefen hanya ya tsaya. Bindiga ya sanya mata a
goshinta tare da mika mata hannu, "Ba ni wayar." Amrah
cikin karfin hali ta daure ta furta kalmar, "Ba zan bayar ba."
130
AKWAI KURA
Tas! Ya tsinka mata mari, "ba ni na ce ko in keta miki haddi in
fasa kwanyar kanki." Jin zai keta mata haddi ya sanya ta ba
shi wayar tana kau da kai tare da dafe inda ya mare ta. Wayar
ya kashe ya jefa a aljihunsa tare da saita ta da bindiga, "Mu je." Keke napep din ta koma shi kuma ya shiga gefenta yana
muzurai kamar zai cinye ta. Wayarsa ya ciro ya kira wani layi,
"An gama Oga a rayen aka same ta, cau! Cau! Sai oga, an
gama, ya kashe wayar tare da kunna tabarsa ya fara zuka tare
da busawa Amrah hayakin a kan fuskarta. Amrah ta fara tari da
yunkurin amai don ita a rayuwarta ta tsani warin taba bare
wiwi. "Bushiya kada ki yi min amai a mota billahillazi... ke ya
dai na ga alamun so kike ki sha tabar ko kina busawa ne? Yo
matan yanzu ai ku ma jajayen wuya ne." Ba ta ankara ba ta ji
ya riko ta tare da kama bakinta ya busa mata hayakin. Wani
karfi ne da jarumta suka zo mata ta wanke fuskarsa da mari
tana tsartas da miyau, fuska ya shafa yana dariya mai karfi, "Ni
kika mara? Lallai yau kafin Oga ya kasheki sai na yi yagayaga dake," ya kuma riko ta yana kokarin cire mata riga.
Amrah tana turjewa. Kokawa sosai suke yi karfin ba daya ba
har ya kai ta kasa, rigarta a baya ya fara kokarin cirewa amma
ya kasa, dankwalin ya cire tare da nikabin yana lashe baki,
כי" Yau zan ci bulus da gani kyawun naki daga fuska har ciki ne,
ya kuma tunkarar ta gadan-gadan yana kokarin cire mata
abayan. Da sauri motar tasu ta karaso gurin dukansu uku suka
fito daga motar. "Mai malafa yadai? Rabu da bushiyar nan wai
ni ne za ta mara akan fuskata shi ya sa nake son nuna mata ba a
marina a zauna lafiya, amma tun da kun zo ai shikenan sai mu
yi yaga-yaga da ita kafin mu kai wa Og ko ya ya?" gabadaya
suka bushe da dariya, "Hakan za a yi."
***
"Ba mu yi hakan da Oga ba mu je da ita ai Ogan kanshi na san
ba zai ga wannan dadi ya bari ba mu je da ita gurinshi in ya so
in ya ci ya ba mu ragowar aha, jawo kekenmu bari mu ja ta a
131
AKWAI KURA
mota, ke dalla tashi mu je shiga mota kada ki bata mana
Jokaci." Amrah ta kalle su da idonta da ya yi ja saboda bacin
ran abin da wancan ya yi mata, "Sai dai ku ja gawata amma ni
da kaina babu shegen da ya isa in bi shi 'yan iska kawai
wadanda iyayensu suka tsine musu albarka." "Hahha!" suka
kwashe da dariya, "Ba ki yi karya ba bushiya amma ba za ki
gane hakan ba sai mun keta miki haddi, Duna dauko ta don
uwarta." Amrah ta turje ba za ta bi su ba kamar 'yar baby.
Wanda aka kira da Duna ya dauko ta tare da jefa ta a bayan
mota saura biyun suka shiga bayan mota dauke da bindiga a
goshinta yayin da dayan ya shiga gurin direban ya ja ya bar
gurin.
"Bestyna bestyna," ta ci gaba da kwala mata kira, daga karshe
ta fara kiran Amrah, "Amrah ina kika boye fito mu je amma
shiru kake ji a cikin super market din. Da sauri ta karasa gurin
masu karbar kudi, "Don Allah ba ku ga wadda muka zo da ita
ba?" suka ce ba su gan ta ba. Zahra ta ci gaba da shiga cikin
super market din tana neman Bestynta daga karshe wani
saurayi ne da ya zo da babynshi shopping ya ce da Zahra,
"Yanmata in fa wadda kuka zo tare da ita ne na ga fitarta tun
dazu ta shiga a-daidaita-sahu. Zahra ta sauke ajiyar zuciya,
"Bestyna "yar rigima wato gida ta wuce ta bar ni, ai ko ni ma
yanzu gida zan wuce don na ga Magriba ta gabat,o gobe ta biyo ni gida ta karbi sakonta." Cikin yanga ta fito daga super
market din a mota ta cimma Maheer na zaman jiran su yana ganinta ya yi murmushi, "Matata na gan ki ke daya ina bestyn tamu?" Zahra ta yi far da ido, "Ka ga wai gida ta wuce ba ta
sanar da mu ba yanzu wani ya fada min ya ce kan idonshi ta shiga a-daidaita." Maheer ya ce; "Ayya mu ne masu laifi mun 6ata mata lokaci har ta gaji ta tafi please a ba wa bestynmu hakuri." Zahra ta ce; "Ai ko da alamun fushi ta yi bari in kira sai ka ba ta hakurin da kanka." Maheer ya ta da mota tare da
132
AKWAI KURA
fita daga Super market din. Zahra ta yi kira wajen sau biyu amma ba a dauka ba daga bisani aka kashe wayar. Zahra ta yi dariya, "Baby ai ko fushin ta yi ka ga ta kashe wayarta." "Ayya bestymu ta yi hakuri gobe ma je har gida mu yi lallashi.
***
Firgigit! Ya bude idonsa gabansa ne ya fadi, "Alhamdulillah," י
ya fada ganin mafarki yake yi ba gaske ba ne. Mamaki ya yi
na ganin bacci ya dauke shi zaune yaushe rabon da haka ta kasance har ya manta ya runtse idonshi yana tariyo mafarkin nashi, "Help me help me," take fada tana gudu, gashin kanta watse a kan fuskarta baki da hancinta jini ne yana zuba kafafunta duk sun fashe da kwalba saboda gudu. Mutane hudu
na bin ta da gudu. Saleem ya fara kwala mata kira yana cewa, "Ga ni jarumata daure ki karaso gare ni daure ki bayyana min
kanki ban gan ki ba maganarki nake ji ban gan kiba jarumata. Taimake ni kada ki bari mu rabu ba mu yi aure ba kada ki bari
su raba mu ba ki haifo min 'ya'yana dake jikinki ba." Kamar walkiya ta fado a gabanshi tana nishin wahala, gashin kanta
rufe da fuskarta; da gudu masu bin ta suka karaso. Saleem ya yi kukan kura ya make daya tare da kai wa dayan naushi. Ta baya dayan ya zo, Saleem bai ankara ba ya dora masa itace a
kai. Tuni Saleem.ya yi lu! Zai fadi dafe da kai. Hannunta duka suke ja ita ko tana ihu tana kiran jaruminta, Saleem ya fara lumshe ido saboda azaba yayin da mutanen suka janye ta da karfi suna tafiya da ita. Cikin ihu ta fizge ta koma kan Saleem dake kwance cikin muryar kuka take fadin, "Ga ni jarumina raina fansa ne a gare ka." Saleem ya yi murmushi tare da
sanya hannunsa daya ya shafa fuskarta tare da tattara gashin kanta. Fuskarta ta bayyana cikin murmushin jin dadi ya ce; "Jarumata ashe kina tare da ni lallai zan ba ki punishment na wahal da jaruminki," tare da rungume ta a jikinsa yana sauke ajiyar numfashi. mutanen uku su ne suka kuma zuwa da karfi suka janye ta daga jikinsa yana ihu tana ihu. Da sauri ya farka,
133
AKWAI KURA
kiran sallar Magriba da akayi a masallacin gidansu shi ya
farkar da shi daga mafarkin da yake yi.
Saleem ya ja ajiyar zuciya, 'Ikon Allah mafarki da 'yar
sukins"Jikinsa babu karfi ya mike daga kan kujerar, alwala ya
daura ya tafi masallaci bayan ya idar da sallah addu'a ya yi
sosai kan mafarkin da ya yi haka kawai yake ji a jikinsa babu
lafiya kamar wani abu yana shirin faruwa da shi.
Ihu take kurmawa a motar tare da bubbuga jikin glas na motar
da hannayenta duka biyu amma ko alamar mutane babu a
hanyar balle ta sanya ran ceto. Bugu da kari motar bakin gilas
gare ta wanda ba mai ganim na ciki illa na ciki dake iya ganin
na waje. Hegun ba wanda ya kula ta sai zukar hayaki suke yi
suna fesa mata tare da kyalkyala mata dariya. Amrah ta
hadiye kukanta ganin kukan ba shi da amfani don babu mai jin
ta illa wahal da kanta daketa yi wajen kukan Addua take yi
aduciyanta duk wanda ya zo mata tare da sauke ajiyar zuciya
tana rufe hanci don ba ta son warin hayakin, "Allah sai ya saka
min, shegu tsinannu wadanda Allah ya tsine musu shegu
'ya'yan karuwa, ta fada tare da tofar da yawun da ya cika
bakinta. "Kai maza! Yarinyar nan tana bukatar saiti ka tsaya
mu yanke mata kauna, haba maza sai ka ce ba mu ba yarinya
mace ta dinga zagin mu," faka mota kawai mu ba ta a jikinta."
"Maza ai mun kusa mu je, kaga Oga nata kira kada ya zuciya a
kuma ta ranar ni ko kudina nake zabari kawai mu je ya caske
mana manta da 'yar shegiya." Amrah da bakinta bai mutu ba
ta ce; "Ku ne 'ya'yan shegu, ga alama kun nuna ku shegu ne,
Allah ya tsinewa uwayenku da ubanku. Wutar Jahannama za
ku shiga," ta fada tana toshe hanci. gabadaya suka kyalkyale
da dariya, “Kai Bushiya ashe ke din ma ta yi ce." Dayan ya сe;
134
AKWAI KURA
"Yarinyar ta fara burge ni ba ta da tsoro." Oga kawai ya shigo da ita cikinmu don irinta mukeso." "Allah ya raba ni da shiga cikinku, ai Mamata ba ta ce je ki za ki gani ba da ganinku dikin shege aka yi aka haifoku."
***
Tafiya suka yi sosai a cikin dajin tafiyar da sai karfe tara na dare suka iso katuwar gate, da alama gidan shi kaďai ne a cikin jejin don ko da dare ne ba ta ga alamun akwai wani gida a gun ba saboda duhu da shirun gurin. Hon suka yi maigadin ya bude musu bakin gate din, duhu ne babu haske maimakon
motar ta tsaya a farfajiyar gidan a'a sai da ta kai har kofar shiga cikin falon sannan ta tsaya, haske ne sosai a gurin na
wuta da alamar generator ne. Gabadayansu suka fito kamar kaya suka haďa hannu suka ciccibeta tana mutsu-mutsu tana
fizgewa amma ta kasa kwacewa, ba su dire da ita ko ina ba sai
da suka kai ta wani katon falo kafin suka ajiye ta, makulli daya
daga cikinsu ya danna kafin suka dawo falon suna jiran Ogan.
A jikin agogon falon ta kalla karfe goma saura na dare, take
tunanin gida ya fado mata yanzu Umminta da Granny suna
cikin wani hali hawaye ya fara zubo mata na tunanin family
nata. Dariya ta ji an.kyalkyale, "Kada ki karaya ‘yanmata ai ke din mace ce mai kamar maza tun da har kina iya fito na fito da
manyan tantirai, don haka kuka ba naki ba ne in kuka ne to ki
tanadi wayarki don ba ki ga komai ba.” Amrah ta danna musu
harara tare da yin tsuka, "Ba ku isa ku yi min abin da Allah bai yi min ba kuma iyaka dai ku ce za ku kashe ni ko?" ta tafa hannu, "sai me?" ai kowa zai mutu ubana ma ya mutu balle ni,
to a shirye nake da mutuwar, tsinannu." ta fada tana jujjuya
musu ido babu tsoro ko kadan a tare da ita.
***
135
AKWAI KURA
Tun da fara maganar tasu ya shigo falon kallo daya ya yi mata
ya ji ta tafi da imaninsa, "Wash!" ya fada yana lashe miyau, a
rayuwarsa yana son mace mai kyau iyakar rayuwarsa bai taba
ganin macen da ta hada abin da yake so a jikin mace irin ta ba.
Yarinyar ta yi masa ta tafi da imaninsa tabbas ya yaba da
karfin gwiwarta, ganin irin yadda take fito nafito da yaransa. A
daya banganren zuciyarsa ke gargadin sa kada ya bi ta kyau ya
kai kanshi inda zai yi da na sani, tuni ya yarda da gargadin da
zuciyarsa take yi masa, gyaran murya ya yi gabadayansu suka
juyo tare da mikewa, "Sai Oga, sai oga," tare da kada hannu
alamar gaisuwa. Ya daga musu hannu shi ma ya kada musu
alamun ya amsa cikin tafiyarsa a hankali ya karaso gare ta
Amrah sam ba ta ji tafiyar tashi ba sai jin hannun mutum ta yi
yana shafa mata gashi. Da sauri ta dago kanta tana kare masa
kallo tare da mamakin shi ne da ma? "Beautiful," ya fada yana
kara shafa fuskarta. Da sauri ta kauda kai tana hararar sa kasakasa da ido ya juyo ya kalle su, "Ku je ku huta zan neme ku an
jima." Gaba dayansu suka mike suna layi, kwaya ta bugar da
su a tare duka suka haurawa saman benen da alamun akwai
wasu dakuna a saman.
Hannunsa ta buge tare da daka masa harara tana yi masa
kallon raini. Dariya ta ba shi hadi da burgewa, hannunsa ya
fara tafawa yana jijjiga kai tare da daga mata dan yatsa alamar
jinjinawa, "Beauty ai in mari na kika yi ba zan ce miki komai
ba sai dai sambarka." Amrah ta tabe baki tana hamma alamar
yunwa ko in ce gajiya, "Malam ka nuna min inda zan yi alwala
in yi sallah," ta ce da shi. Ya kalle ta da gefen ido, "Ki ce
ustaziya ce da gaske, no wonder kullum fuskarki ke cikin
nikabi ashe kyau ake boye mana tare da ustazancin." Amrah ta
yi murmushin gefen baki "Ai ni duk tsiyata nakan sauke farilla
136
saboda
AKWAI KURA
tsaro," ta fada ckin sigar 'yan iska kamar tsohuwar
hannu a bariki. Bai ce komai ba hannu ya daga ya nuna mata, "Ga bandaki." Amrah ta mike tana tangadi kamar tana buge ta shiga bandakin. Ya bi ta da kallo yana hango tantiranci a cikin idonta. Alwala ta dauro ta fito a dakin, "Mu je," ya ce da ita. Har daki ya kai ta, sallaya na shinfide ta sallah Amrah ta kalle
shi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 12