kada
iska mai sanyi a farfajiyar gidan. Cikin nutsuwa yake tafiya ya
dumfaro inda Amra ta buya a karo na biyu wayarsa ce ta kuma
yin kara kamar ba zai daga ba ya kara a kunnenshi autan
Mommy a daya bangaren ta ce; "Morning Bro J." "Morning
autan Mommy how studies?" "Fine bro," ta shagwabe fuska
kamar za ta yi kuka tamkar yana ganin ta, "Bro J Mommy ta ki
bari in shigo weekend please ka sa ta bar ni two weekend ban
zo ba I missed all of them," "Ok ki shirya direba zai zo." Ta
yi ihun murna a waya, "That is why I am always proud of
you." Da sauri ya cire wayar a kunnenshi don kada ta fasa
mishi kunne. A rayuwarsa sam ba ya son hayaniya bare kara
ya tsani kara sam. Ita kanta kanwar tashi baki ta rike don ta
san tabbas ta tabo Bro shi ya sa ba ta jira mitanshi ba ta kashe
wayar tana dariya ta san yanzu sai ya fasa barin ta zuwa
weekeend saboda ta yi laifi. "Mts!" ya ja tsaki tare da sanya
dayan hannunsa cikin aljihu, "Mata ba su da hankali, ihu,
shouting always kamar ba su girma..." har ya juya zai wuce ya
dawo da baya. Tuni Amra ta daskare a boye, gabanta ya shiga
faduwa zatonta ya gan ta ne, tuni ta fara karanto duk addu'ar
da ta zo bakinta amma ga Mamakinta sai ta ga ya daga hannu
ya cire nunannen mangwaro dake bishiya wanda ya yi jajajur!
Ido ta daga ta kalli bishiyar bishiya ce irin ta gidan gona masu
'ya'ya masu kyau da dadi wanda bishiyar jere suke ras! da
'ya'ya wanda yawan 'ya'yan har da yawa reshensu ya sauko
kasa, ko ita da ke tsugune a boye hannnunta zai iya ciro wasu
45
AKWAI KURA
dake lilo jikin reshensu. "Wash!" ta fada a hankali sakamakon
taka mata 'yan yatsu da ya yi azabar zafi ne ya ziyarci ranta
tuni ta fara tsiyayar hawaye shi ko ko a jikinshi mangwaron
yake juyawa yana cilla shi sama yana cafewa, ba ta san lokacin
da azaba ya sanya ta ji fitsari yana tsiyaya a jikinta ba.
***
Amra ta mike rike da hannu tana.hura masa iska, tare da bin
bayanshi da kallo, harara ta danna masa tana turo baki, baki ta
bude tana Mamakin shi yana gudu yana sassarfa kamar a
mafarki ya yi tsalle ya fada cikin ruwan swimming fool dake
farfajiyar filin hutawar. Tuni ya fara iyo sai ka ce kifi, abin
burgewa ita kanta ya ba ta sha'awa, har ta sai da ranta inda ta
iya ruwa to fa tabbas wata rana sai ta dana ko da hakan na
nufin karya dokar gidan. A ranta godiya take yi wa Allah da
ya raba su lafiya ba tare da ya gan ta ba. Tabbas inda ya gan ta
ba ta shirya amsar kare kan ta ba, ba ta da hujjar dalilin kawo
ta gurin domin ba ya daga hanyar da aka lamincewa 'yan aiki
su je a gidan. Guri ne na motsa jiki ga 'yan gidan kadai tare da
shan iska. Ranta in ya yi dubu sai da ya baci, jikinta ta kalla
yadda wandonta ya baci ta tsakiya da fitsari. Iyakar
rayuwarta ba za ta iya tuno yaushe ne ta yi fitsari a jikinta ba
sai ga shi da girmanta azaba ya sa ta yi babu shiri. Saukinta
daya iyakarsa wandonta bai taßa rigar ba bare ya shafi hijabin
jikinta, tuni ta kuduri aniyar barin hijabin don shi ne kadai
rufin asirinta kafin ta bushe. Gudu-gudu ta doshi hanyar da za
ta sada ta da 6angaren aikinta, agogon kicin ta kalla karfe,
karfe bakwai na safe daidai, ita ko yanzu me za ta dafa masa?
Takardar time table ta kalla baki ta rike, Na shiga uku." Ko
ita aljana ce ba za ta gama hada wannan kalar girki har kala
biyar zuwa karfe takwas ba, tuni ta yi na'am da abin da
zuciyarta ta ba ta shawara. Cikin minti arba'in ta gama hada
kala uku daga ci kin abincin, jakarta ta jawo ta jero fulas na
kosanta da kunun gyada wanda ta yi asubancin yin shi saboda
46
AKWAI KURA
Granny, ita ma ta zuba nata kamar yadda ta saba zuwa da abin
karinta kullum, filet ta kuma daukowa ta raba kosan biyu ta
zuba masa rabi ta jawo karamin plaks ta zuba masa kunun
gyada, kadan ta ragewa kanta a daidai lokacin agogon kicin ya
yi kararrawa, karfe takwas daidai ko second uku bai kara ba
Grace ta shigo kicin din a gurguje ta gai da Amra cikin
harshen turanci. Kasancewar Amran za ta girmewa Grace din
da shekara akalla biyu. Babban tire ta jawo ta jera duk abincin
break fast da Amra ta kammala, "My sister let me finish my duty i will be back to you," Grace ta fada .Amra ta yi mata
alamu da hannu don ta kasa magana saboda jin dadin kununta. Grace na kaunar Amra saboda Amra ta iya turanci, wannan ya
sa take Mamaki, a zatonta Hausawa ba su dagewa su iya Englsh haka, musamma a cikin talakawa kamar Amra. Wannan
dalili ya sa take son hira da Amra don tana burge ta. Saurisauri Grace ta fice don fara nata aikin. Amra ta jawo sauran
indomie da ta dafa ta ragewa kanta don ta san kosai da kunun
da ta rage ba zai ishe ta ba, ita ma Amran ba baya ba ce wajen
kwasar girki. Hankali kwance ta ci gaba da cin abincinta sai da
ta yi nak da koshi kafin ta mike, saukowa ta yi zuwa falon
dake farkon shigowa side din, ta shiga bandaki wandonta ta
cire iyakar inda ya baci ta wanke tas! Sannan ta mayar da shi jikinta don ba za ta iya jiran har sai ya bushe babu sutura a
jikinta ba.
"House girl! House girl!" ta ji muryarshi na fada cikin fada.
Da sauri ta fito don komawa kicin. Kicibis suka yi karo da ita,
kallon-kallo suke yi wa juna, sanye take da riga da siket wanda
ya dame ta ita da tsirara daya suke, bayanta gashin doki ne kwance ya zubo kafadarta, cingam ne a bakinta tana taunawa
tuni suka gane juna ido cikin ido suka kalli juna.
Meena ta kalli Amra cike da isgilanci, "Ke mahaukaciya daga
ina? Lallai yau zan nuna miki shayi ruwa ne ba ya rike ciki."
47
AKWAI KURA
Tuni dabara ta fado ranta, Amra ta rike baki, "Baiwar Allah
me ya faru? Don Allah ki yi hakuri ban gan ki ba ne."
Meena ta hankade ta, "Don uwarki kina nufin ki ce ba ki gane
ni ba? To kin yi min rashin kunya a motar haya kin ci bulus
amma yau gidanmu kika zo, zan koya miki hankali."
Da sauri ya sauko yana mai kiran, "House girl," cikin
turancinshi mai dadi. Da gudu Grace ta sauko gabanshi ta
durkusa, "Sir am sorry am sorry," ta ci gaba da maimaitawa
don ko ba a fada ba ta san laifi ta yi.
Saleem ya daka mata tsawa, "Don ubanki kin taba ganin na ci
akara?"
Ba Graceba har ita Meena da Amra sai da suka tsorata.
"I ask you, kin taba ganin na ci akara as break fast kayan
tusa?"
Grace ta hau kada karwa, kun san yare da tsoro, "Sir am not
the one," ma'ana ba ni ba ce. Hannuwa hada tare da nuna
masa Amra dake zube a kasa sakamakon ture ta da Meena ta yi.
Ido ya zaro yana kallonta, "Is that you again?” Amrah ba ta ce
da shi komai ba illa ido ta zuba mishi hadi da murguda masa
baki. Saleem ya dumfaro ta, "Don ubanki ni ki ke yi wa murgude-murgide? Ni sa'anki ne?" Kau! Kau! Kake ji ya
dauke ta da mari. Haba Meena ba ta san lokacin da ta tuma
tsallen.murna ba hadi da yi wa Amrah gwaliyo. Ita ko Grace
kada karwa ta fara yi a gun tasai daran nata saukan marin,
Amrah da azaban zafi ya sanyata kurma wani gigiceccen karan
ihu dagudu Daddy da Mommy suka yi rige rigen shigowa
falon.
48
Page 18
AKWAI KURA
Aguje sukashigo falon masifa Saleem ya ci gaba da yi inda
yake shiga ba nan yake fita ba." Yauwa mother wa ya kawo
wannan kazamar yarinyar gidan nan da har ta samu damar yi
min girki da kazamin hannuta in ci? Don uwarta yau za ta bar
gidan nan wannan ba ta kai ta yi girki in ci ba." Mommy ta kai
duban ta ga Amra dake durkushe ta dunkune kanta cikin hijabi
tana kuka cikin Mamaki take duban Amra, "Amratu ina kichin
Doctoress naki? Me ya sa kika bari son ya ganki cikin wannan
dattin Doctoress I know matukar zai gan ki hakan za a samu
matsala." Amra ba ta ce kala da Mommy ba illa kukan takaici
da ta ci gaba da yi, wato su yaran masu kudi ba su laifi ko? A
buge ka a hanaka kuka. Saleem ya daka mata tsawa, Fice min
a falo I hate you!" Amra ta aara sautin kukanta a zuciyarta
tsinewa Abban su Amla take yi da ya sanya ta kawo kanta
inda ake cin zarafinta. "wallah ban da dalili yau da ta nuna
masa ta fi tsohuwar mota lalata, take farin ciki da jin dadi
marar misaltuwa ya wanke zuciyarta. Meena yau Saleem ya
biya ta yau da tana da tukwicin da za ta ba Saleem tabbas da ta
ba shi. Daddy da bai san wainar da ake toyawa ba ya kasa
cewa komai. Mommy ce ta shiga yi masa bayanin Amra a
matsayin mai aikinda ta maye gurbin Iyabo kafin ta dawo daga garinsu. Daddy ya dagawa Saleem hannu tare da shan mur,
"Wato son ba ka jin Magana ko? Ina gargadin ka koyaushe kan wulakanci, shin ni mahaifinka ka taba taras da ni ina dukan daya daga cikin 'yan aikin gidan nan? To kada in ji kada in sake gani ban lamunta ba kuma a wannan karon na rantse da Allah ba zan lamunce da korar 'yar aiki ba ka ji na fada maka
kada in ji kada in gani." Daddy ya kalle ta, "Yarinya ki yi hakuri tashi ki share hawayenki maza je ki ci gaba da aikinki,"
49
AKWAI KURA
Daddyn Saleem ya fada yana buga kafa, "Enough enough son,
rantsuwa na yi ba za ka sa ni in yi kaffara ba. Allah kenan!" Fu!
Ya fita ya bar musu falon. Da karfi ya fada akan kujera yana
sauwe numfashi. Daddynshi bai taba yanke masa hukuncin da
ya ji zafinshi ba irin na yau, numfarfashi ya ke ta saukewa sai
kace mai asma. Mommy ta jawo shi jikinta tana shafa gashin
kansa cikin rarrashi, "Son yau ka bata ran mahaifinka maza ka
je in ya huce ka ba shi hakuri, haba son Amratu yarinya ce mai
kyau kuma mai tsabta zamana a a Nigeria more than twelve
years ban taba ganin yarinyar da ganin farko na fara jin ta a
raina ba irin wannan yarinya please son kai ma don ka tsane ta
ne na tabbatar da za ka gane abin da nake fada maka." "Mother
ni ni a canza min ita." "A'a son mahaifinka ya yi rantsuwa
kada ka sa ya yi kaffara ka ji," ta ci gaba da shafa gashin
kanshi hadi da rarrashin sa domin ita kanta ta ji dadin
hukuncin da Daddyn nashi ya yanke don har zuciyarta tana
Kaunar Amra musamma ranar farko da Amran ta yi girkin da
ya girgiza Mommyn, tabbas ta yi Mamakin kwarewar Amra
kan girki, bugu da kari yarinyar sam ba ta shiga harkar kowa
cikin ma'aikatan gidan, ta lura da ita in har ta gama aiki littafin
addu'o'i take budewa tana karatu. "Mother to a canza ta a girki
na." "Son ka bar maganar zan yi magana da ita wajen kara
tsabta na san matsalarka ke nan.
***
Da sallama ta shigo office din sakatariya ce zaune akan
kujerarta. Bayan sun gaisa ta nemi a yi mata iso gurin oganta.
"Ok bari na sanar da shi a ce mishi wace ce?" "Amrah
Ammat" ta ba ta amsa. "Ok," wayar telephone ta jawo hadi da
danna wasu lambobi, "Oga ka yi bakuwa..." "Amrah Amat ta
ce sunanta." "Lallai ina da babbar bakuwa, ki ce ta shigo."
Sakatariyan ta ajiye wayar ta yi umurni ga Amrah "Bismillah
Madam ya ce ki shiga." Har ta wuce za ta shiga Sakatariyar ta
kuma cewa, "Ji mana Madam." Amra ta tsaya. "Da alamar
50
AKWAI KURA
kina da muhimmanci a gun Oga ko?” Amrah ta faſa da alamun tambaya, "Yes Madam," ta kuma fada. "Oga ya yi baki sun zo fiye da biyar amma bai ba su damar ganin shi ba sai ke, kodayake kin kai kowanne mutum ya yi miki iznin ganin shi
ko waye shi." Amrah ta yi murmushi, Na gode sister you are welcome," ta ce da ita. Ba ta yi jinkiri ba wajen cusa kanta
cikin office din. Baki ya kama, "Lallai ina da babbar bakuwa,
Amrah ashe rai kan ga rai? Da gaske ke din ce, ai na dauka
wata ce ke son yi min basaja da sunanki.” Amrah ta yi karamkr dariya, "Ai ni kaďai ce mai wannan sunan a duk fadin
Kaduna." "Really," mutumin ya fada, "ai ko hakan ne fa ba ki yi karya ba ke din dai ke ce babu wata Amrah mai kyau
kamarki a Kaduna." Ta yi fari da ido, “Kai Anas ba ka rabo da zolaya." Ya kura mata ido, “Amrah ba zan gaji da fada miki
kina da kyau ba kamar yadda ba zan gaji da fada miki kalmar
ina son ki ba," ya marairaice fuska. “Amrah ba ta so na ban
san laifina ba why? Amrah don Allah ki fidda ni mijinki na
aure." Amrah ta yi dariya, "Anas ba a raba ka da wasa na sha
fada maka ba zan taba yaudarar ka ba ni ban shirya aure ba har
sai na cikawa Abbana burinshi na son in samu ilimi mai
inganci inda zan dogara da kaina Anas ni kadai ce kwallin kwal ga.mahaifina kuma burina in samu ilimi mai inganci shi
ne kusan kalmar second to the last na mahaifina a duniya, don
haka insha Allah zan cika burnish, zan nemi ilimi na addini da
na zamani da dukkan karfina," ta share siririn hawayen da ya
zubo mata a cikin idonta wanda ya zame mata dabi'a matukar
za ta tuno da Abbanta sai ta zubar da hawayen damuwa. Anas
ya kalle ta cikin tausayawa, "Maganarki gaskiya ce Amrah shi
ya sa nake kaunar ki don ke kaifi daya ce ba ki karya kan farin
cikin wasu amma ina rokon ki Amrah ni din nan Anas na yi
miki alkawarin zan jira ki har sai burin naki ya cika, kin yi
alkawarin in na jira ki za ki aure ni?" "Alkawari da ciwo Anas,
ba zan yi ba don alkawari kaya ne sai dai ina mai yi maka
albishir in har ni din matarka ce zan aure ka amma dai ka sani
51
AKWAI KURA
ban yi alkawari ba, ai matar mutum kabarinshi." Anas ya
gyada kai tare da nuna gamsuwa, "Allah ya sa ke din rabona
ce." Amin," ta furta a fili. Tare suka yi dariya, ga Anas dadi
ne ya ziyarci zuciyarshi, ita ko Amrah yadda ya marairaice ya
ba ta dariya.
Anas Yayan Zahra Kashem ne Kawar Amrah tun da Anas ya
kyalla ido ya ga Amrah Allah ya dora masa kaunar ta, sai dai
ga Amrah sam babu burbudin soyayyar Anas a zuciyarta sai
dai tana yi mishi kara saboda babbar kawarta Zahra da kuma
Kaunar da Mommynsu ke yi mata. Amrah ta gyara zama tare
da tattaro dukkan nutsuwarta, "Anas taimakonka na zo nema
shi ya sa ban yi maka waya ba na zo da kaina, ka san an ce
zuwa da kai ya fi sako. Anas ya ce; "To fa fadi ki ga aiki da
cikawa ai babu abin da za ki nema in kasa yi miki sai dai in ba
ni da halinsa." "Sure," Amrah ta ce, "yes very sure my dear,"
Anas ya tabbatar mata. "Godiya dubu," ta ce sannan ta mike ta
je ga kofa. key da ta gani a jiki ta danna sannan ta dawo
maimaakon ta zauna sai ta matso kusa da Anas har suna jin
numfashin juna. Anas ya maida hankalinshi yana sauraron
bukatarta yayin da Amrah take yi masa magana kamar rada.
Ido ya zaro yana yi mata bayanin hatsarin aikin, Amrah ta ci
gaba da lallaba Anas tare da tuna mishi alkawarin da ya yi
mata na ko mene ne in har yana da shi zai yi mata. Anas ya
gyada kai. "Amrah duk duniya babu wanda zai sanya ni
wannan aikin in yi masa don kamar na ci amanar aikina ne da
na yi rntsuwa zan kiyaye amma zan yi miki saboda alkawari
za yi miki saboda kaunar ki da nake yi miki." Amrah ta
murmusa, "Da ma na san za ka yi Anas, don ba zan taba zuwa
da bukata ka yi reject ba matukar kana da ikon yi mini." Ta
hada hannuwanta biyu alamun godiya, jakarta ta bude ta ciro
takarda ta yi rubutu, "Zan wuce Anas sai mun yi waya, gidanku nake son wucewa kwana biyu ban ga Bestyna ba.
52
AKWAI KURA
"Kin kyauta sai mun yi waya,"Anas ba shi da karfin gwiwar
yi mata rakiya, kai kawai ya daga mata, "Fatan alkairi."
***
Wayar ta kanga kunnenta, "Bestyna kina gida?" A daya
Gangaren Zahra ta ce; "E Bestyna ina gida." "Ok ga ni a
hanyar gidan naku." Ihu Zahra ta fasa a waya, "Thanks
Bestyna wallahi I miss you so much."
Amrah ta kashe wayar tana dariya. Mai a-daidaita ta tsayar
don ya kai ta Malali gidan su Zahra, "Je ka kawai," ta ce da
shi saboda ta gan shi da alamar a buge yake. "Hajiya mu je
mana ai ko Kano kike so kin taras ya fada mata cikin muryarsu
ta 'yan shaye-shaye.
Ganin hadari ya fara haduwa ga shi titin babu abin hawa shi
ya sa ta yi kundumbalar shiga ba don ta so ba, ai ko mai adaidaita ya hau sharara gudu kamar zai tashi sama. Amrah
tun tana sharewa karshe ta ce; "Malam ka dan rage gudu
please haba Hajiya kin gan ni da rawani ne ko carbi? Eye!
Kawai kira ni da Mai jarfa shi ya fi sauki." "Yau na dauko
ruwan dafa kaina," ta fada a ranta, "irin wadannan a hankali da
wayo ake bin su don a rabu lafiya.' wannan tunanin da ta yi shi
ya sa ta mai da hankalinta kan kallon titin da yake ta sharara
gudu tare da addu'ar sauka lafiya. Ai ko kamar an ce ta kalli
mirrow nashi ta yi gamon katar da bakar Jeep da take bin
bayansu. Ido ta tsurawa motar Allah ya ba ta sa'ar hango
mutane ta cikin glass, ta hango mutane uku a baya sai mutum
daya a gaba, wato direba, sai hura hayaki suke yi. Karaf!
Idonta ya haďu da na daya daga cikin mai shan tabar iblis din
gabanta ta ji ya fadi, in ba ta yi karya ba tun hawanta adaidaita sahun motar ke biye da ita. Cikin dabara da son
tabbatar da zarginta ta ce da mai adaidata, "Malam ka rage
gudu ina son amsa waya." "To Hajiya, hanzarta ki gama kada
53
AKWAI KURA
ruwan nan ya sauko kuma ba zan so ya taba ki ba in ya taba
babban yarinya ai mazan sai su fadi. Ita dai yana surutu amma
hankalinta na ga motar dake bayansu kuma abin da ya ba ta
Mamaki mai adaidaita na rage gudu maimakon motar ta zo ta
wuce su sai ita ma motar ta rage gudu kai kace tafiyar tasu
daya ce. 'Ok na ramfo zancen,' Amra ta fada a ranta. "Hajiya
kin gama wayar in kara gudu? Kin san mu matasa muna son
daukar irinku kyawawa don mu yi ta sharara gudu muna aloba
e yaya ne." Ita dai hankalinta na ga motar tare da nazarin
matakin da ya kamata ta dauka, tuni ta ji jarumta ta zo mata
tare da wata dabara ta ce da mai adaidaita, "Ai ko ka yi ta
sharara gudunka son ranka tare da yin aloba ai ni ma'abociyar
aloba ce shi ya sa duk bikina 'yan acaba da 'yan adaidaita ko
ba a gaiyace ni ba nake zuwa kawai don in sha aloba asaye.
Hahahaha!" Mai adaidaitan ya kece da dariya, "Ai kuwa
Hajiya yau kin shigo hannun gwani, tuni cikin hirar tasu ta
samo mafita, "Ai ko ni ma yau zan nuna maka ka dauko 'yar e
yaya ne din don haka sai ka yi try don ka ci gasar naira dubu
biyar da na saka maka." "Hahahah!" ya kuma kecewa da
dariya, "Ai ko Hajiya kan dubu biyar na daura niyyar cin gasar
ko da tayata za ta yi fata-fata don mu ba mu kariya in dai
wajen fidda kai kunya ne."." "Yawwa babban yaro," Amrah ta
ce, "ka ga Malali za ka kai ni cikin Ganbiya ko?" "E Hajiya
hakan kika fada," "To so nake da aloba ka yi ta keta gudu a
titin nan lungu loko da sako nake son yau a bi da ni ta inda za
mu isa inda za mu je da alobar nan zan kara yarda kai din na
yi ne, ka ga ni ma yau zan warwasa jinin jikina." "Hajiya na ci
kyautar nan an gama," ya fada. Tuni mai adaidaita ya sukwani
abin hawanshi sai keta gudu yake yi sai ya yi gaba kamar zai
mike sai ya ci burki ya canza hanya, ai ko mai motar ya ce da
wa Allah ya hada ni in ba ku ba, shi ma ya kara kaimi duk inda
mai adaidaita ya sanya kai shi ma zai ci burki ya bi, tuni masu
babura da motoci suka fara ba su hanya a tunaninsu 'yan biki
ne, aloban suke da gaske babu abin da kake ji sai kiiiiii kiiii!
54
AKWAI KURA
Ana lilo da Amrah a adaidaita sahu yayin da hankalinta rabi na ga keke napep da take riae da karafunansa tamkar ta fadi, rabi na ga mai bakar motar bayansu. Cikin ikon Allah 6at! Mai adaidaita ya yi zarra wa mai bakar motar. Ajiyar zuciya Amrah ta sauke bayan ta tabbatar sun yi masa layar zana, "Na gode maka babban yaro, ai ko yanzu ka bar aloba tabbas ka ci kudinka." "Ko Hajiya? To Allah dai ya biya." A ranta hamdala ta yi a fili kuma ta ce da shi, “Ashe ku ma ‘yan iskan kuna da rana?" "Haba Hajiya ai kare ma yana da rana bare dan mutum mai tunani, ko ya ya?" "Eh ai na ga alama," ta fada ita dai tana Allah Allah ta isa inda za ta je, har ga Allah ta tsorata da motar musamman yanzu da ta gama yarda ita din suke bi, to mw za su yi mata? Shi ne amsar da ba ta sani ba.
***
4
Da sauri ta shiga falon tana haki falo ne da aka ware saboda 'yan yi matan gidan falo ne babba mai dauke da kujeru set biyu da katuwar TV plazma sai katuwar firji mai dauke da
kayan sanyi a cikin falon. Dakunan bacci hudu ne, daya na Yayar Zahra Aunty A'isha sai daya na Zahra sai dayan na kannan Zahra, biyu kowa da nashi, direct firji ta nufa ta bude
ta dauko ruwa mai sanyi cikin zakuwa ta cire murfin gorar ta kafa kai ba ta sauke ba har sai da ta shanye gorar duka, a hakan
ma ba don ta koshi ba sai don kada ta yi amai. Tabbas da ta
kara robar ruwan daya saboda yadda take jin bushewar zuciyarta. Turus! Zahra ta yi cike da Mamakin ganin Amrah a
falon kuma a jikin firji don ko alama ba ta ji sallamar Bestyn tata ba bare ta san zuwanta don ko yanzu ta fito ne za ta ciro wayarta dake caji a falo ta kuma kiran Amrah ta ji lafiya har
yanzu ba ta iso ba, ai ko da gudu ta rungumo bestyn tata ta baya cike da jin dadin ganinta. Ita ma Amrah rungume ta ta yi
tana sauke ajiyar zuciya tare da farin cikin ganin junan su. Wannan dabi'ar su ne ko yanzu suka rabu suka kuma haduwa
an jima to fa za su yi ihun murna tare da rungume junansu don
55
AKWAI KURA
nuna jin dadi, wadannan aminai sam ba sa gajiya da juna. "Besty lafiya gudu kika yi? Irin wannan numfashi." Amrah ta
ce; No besty gajiya ce don ba daga gida nake ba mu je in gaida Mama kada mu zauna hira don tamu dake ba ta karewa."
"Kuma fa haka ne." in ji Zahra, "don akwai gulma, dama Allah Allah nake mu hadu." Tare suka shiga falon Mommyn bayan
ka shige side na yara sai na Mommy ita ma katon falo ne mai dauke da dakunan bacci uku wadanda aka tsara falon kamar a
Turai.
"A'a 'yan biyuna na kaina Sannu da zuwa bestyn besty."
Gabadaya suka yi dariya saboda tsokanar da Mama ta yi musu, "ya ya tsohuwa Iya mai ran karfe?" "Lafiyarta lau Mama, ta
ce a gaida ke." "Ina amsawa ni ma ina nan tafe zuwa gidan
naku don gai da ta cikin satin nan don na kwana biyu ban je
gidan naku ba." "Za ki jene Mama," Amrah ta fada.
Zahra ta mike, "Besty mu je akwai labari mai dadi."
Mama ta ce; "Tashi ku je can kwa ji da gulmarku in ta yi tsami
ma ji."
"A'a Mama ba mai jin kanmu ni da bestyna," Zahra ta fada.
"To a dai zo a debi abinci a ci kafin a je labarin." Amrah ta ce'
"A koshe nake Mama sai dai ko Bestyna." "Ni ma a koshe
nake." Tare suka mike don komawa dakin Zahra. Amrah tuni
ta ware daga damuwar da ta zo da ita. waya Zahra ta jawo
Gallery ta shiga ta fito da hotonsa. "Besty matso ki gani na yi
kamuwa, Allah besty ina ga lokacina
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 12