Allah ya nuna min ranar da za ki
ware ki bar shirme."
"Ya ya Iya? Ina son dama in yi mata aiken dambun kaza ga
shi nan jiya na sa aka yi mata, kin ga tun da kin zo in za ki tafi
sai ki tafi muku da shi."
"To an gode ummi," Amra ta fada sannan suka shiga hirar
yaushe gamo. Can Amra ta nunfasa, "Ummi ni kam kin san
zan fara IT?"
"E Abbanku ya sanar da ni komai an tura ki gurinsu ko?"
Amra ta kalle ta, "Ummi da ma ya sanar da ke?"
Ummin tata ta kalle ta, "Ya fada min gurinsu aka tura ki."
31
AKWAI KURA
Cikin dabara ta fara bugun cikin uwar tata don sanin ko ta san
aikin da ya ba ta amma Zainabu ta ki ta nuna ta gane me diyar
tata take nufi. Karshe Amra ta shagwabe fuska.
Ummi ni da nake karantar "Business management and
Administration' me ya hada ni da IT a ofishin yaki da
fasakwauri?"
"Ka ji shirme," in ji Ummin tata, "ai tun da kika ga sun kai ki
wajen akwai alakar ke nan. Ke dai ki yi aikinki da fahimta,
insha'Allahu za ki gama attachment lafiya kin ji Amratun babanta."
Amra ta share kwallar da ta taru a cikin idanunta, "Na gode
Ummi, addu'arki nake nema don da ita nake cimma dukkan
nasarar rayuwata."
Wuni guda ta yi wa Ummin tata sai yamma lis! Kafin ta yi
sallama da uwar tata. 'Yan biyu suna kewar ta. Direba ya dawo da ita gida.
***
Karfe takwas na safiya ta gama shirinta cikin local Doctoress; riga dabam dankwali dabam zaninta na zama gida wanda ya sha ruwa shi ta yi amfani da shi da kanta daren jiya ta yi lumbushen kitse wa kanta guda uku, hoda ta bakaken mata ta
sanya a fuskarta don ragewa kanta fari, ta dauki zumbulelen
hijabi da ya ji jiki na Iya wanda ita kanta Iyan ta mai da shi tsumma, nikabi ta sanya ta daura a fuskarta. Iya na bayan gida
ta daga murya, "Granny na tafi ni ba zan jira ki fito ba kada in makara."
Gyaran murya Iyan ta yi alamun ta ji abin da aka ce da ita...
32
AKWAI KURA
Direct kwatancen da ta ji an yi jiya shi ta yi amfani da shi. Minti kadan ya kawo ta inda take so bayan ta sallami mai a- daidaita-sahu. Da karfin gwiwa ta nufi bakin gate din shiga gidan. Masu gadi ne a jere sun kai mutum uku zaune kan
benci suna shan iska. Da sallama a bakinta cikin ladabin da ta
kirkire shi wanda ita kanta ba ta san tana da shi ba ta yi musu sallama.
Daya daga cikinsu ya ciro naira hamsin, "Ga sadaka baiwar Allah."
Amra ta sunkuyar da kai kasa tare da kara sassauta murya, "Ba almajira ba ce, don Allah ku taimake ni Hajiyar gidan na zo gani."
Kallo suka bi ta da shi duka a tunaninsu mai bara ce take nema
sadaka, sai suka ga sabanin haka. Kallon taro uku sisi daya
daga cikinsu ya yi mata, ganin shi ba ta isa ta ce za ta yi
magana da Hajiya ba.
Tuni dabara ta fado ranta ta ce; Ni bakuwa ce 'yar uwar
Alhaji ce kuma daga Kano."
Fuska suka dan sassauta. Dayan ya kuma yin magana, "Kai 'yan Kanon nan sun cika son banza, kullum kwa nan duniya
sai an samu mai zuwa neman taimako." Amra ta kuma
sunkuyar da kai ita dai burinta su barta ta shiga. A 6angaren
zuciyarta kuwa tsinewa maigadin take yi sai ka ce gidan ubanshi.
"Bari a fada mata," na tsakiyan ya kuma fada, "ga waje zauna
ina zuwa," wayar telephone ya dauka dake makale ta cikin
gate din ya danna kira. Cikin second kadan aka dauka. Hajiya
cike da girMamawa kamar tana ganin shi ya gaishe ta sannan
ya fara isar da sakon, "Baki kika yi Hajiya... a gate... "E wai
ta ce daga dangin Alhaji ne... "To to ba matsala ga ta nan za a
33
AKWAI KURA
yi mata iso." sannan ya ajiye wayar ya leko kanshi ta gate,
"yarinya mu je."
Da sauri Amra ta ja bujen hijabinta ta bi bayanshi. Abin
Mamaki bayan sun fita wannan gate din wani gate ne a gaba su
ma da masu gadinshi. In takaita muku sai da suka wuce gate uku kafin ta kai ga shiga harabar gidan, kowacce gate ta fi ta bayanta kyau sannan kowacce gate masu gadi uku ke tsaron ta
a gate, a ta karshe ce ta ga sojoji ke tsaron ta. Gate din da ta fi kowacce kyau ke nan, a gefe katon fili ne inda ake ajiye motoci. Motoci ne sun fi talatin jere masu kyau kamar ba da kudi aka saya ba. A bangare daya mota guda hudu da ke gefe da direbobi a ciki, kowacce direba sanye yake da kayan aikinshi mai tambarin custom, da gani sun shiryawa fita a
kowacce jikin mota akwai mutum.biyu kowa na rike da bindiga a hannunshi alamar fita za su yi da mai gidan.
Tasbihi Amra take yi a zuciyarta na tsaruwar gidan. fadar kyau na gidan ma bata lokaci ne sai mu cika littafi guda ba mu
gama ba.
"Aljannar duniya," Amra ta fada a ranta. Ita dai bin maigadin
take bakinta dauke da addu'a. tafiyar minti shida ta kawo su
cikin falon. Kujera maigadin ya nuna mata, "Ki jira ta a nan za
ta sauko."
Kwas! Kwas! Ta ji alamun tafiya. Da sauri ta dago kanta dake
durkushe.
Ras! Ta ji gabanta ya fadi. Tuni ta fara jin kamar fitsari zai
kufce mata sakamakon hango ta da ta yi. Wata Baturiya ce
sanye da doguwar riga 'yar kanti mai kyau kanta bude babu
dankwali, gashinta har gadon bayanta, ko tamtama babu ita ce
maigidan, hannunta sakale a cikin nashi suna saukowa daga
saman bene da alamun fita zai yi don sanye yake da kayan aiki
wanda yake kara masa kyau.
34
AKWAI KURA
Cikin harshen Turanci suke maganarsu. Da sauri Amra ta aro
jarumta ta sanyawa zuciyarta. Turus! Ya ja ya tsaya fuskarshi cike da bacin rai.
"Mother wacce kazama ce wannan a gurin da zan yi break fast?"
"Cool down my dear bakuwa ce, mu je ka yi breakfast kada ka makara." Ta kwalawa 'yar aikinta kira, "Hajara.
Da gudu wadda aka kira da Hajara ta fito, har kasa ta durkusa, "Ga ni Hajiya.” “Ku je da wannan zan neme ta an jima mu je sweetheart ka ci break."
Ya yatsina fuska yana shafa ciki kamar ba zai yi magana ba ya
ce; “Am ok mother zan sha coffie, a office."
Sanin halin danta da kyama ya sa ta sumbace shi a goshi, take care my dear i love you."
Shi ma kis ya yi mata a goshi tare da furta I love you always
my deares."
***
Cike da farin cikin samun nasara ta dawo gida. Granny kanta
ta fahimci jikar tata farin ciki ne cike a ranta.
"A'a Zainabu an fita a sa'a an dawo kenan ga alamu ya nuna
bisa fuskarki," Iya ta fada.d
Dariya mai kara Amra ta yi wadda har sai da Iya ta rike baki, "Yo hala tsintuwar kudi kika yi? Irin wannan farin ciki haka."
Amra ta rungume Iya, "Ai wannana tsintuwar ta fi kudi domin
shi abin da na samo kudi ba ya saya, Granny nasara na fara
35
AKWAI KURA
samu kan aikina kin ga nasara ai kudi ba ya saya Allah ke ba
da shi ko?"
Iya ta gyada kai hadi da wangale baki, "Zainabu ai in har jinin
Amaduna ne a jikinki to kin daura da nasara ke nan har aba da
sha Allahu.'
Amra ta kuma rungumo Iya da karfinta tana ihun murna, "A'a
shika ni kada ki karasa ni gara ke da sauranki a karfi shika ni
na ce."
"Iya me kika dafa mana ne a gidan?" tana magana tana shiga
dakinta don rage kayan jikinta.
"Awara yau na yi mana 'yar nan da yake yau Zahra'u ta zo ba
ki nan, da yake akwai lokaci shi ya sa muka gama da wuri don
ma an yi mata waya ta yi baki gida da kin dawo kin tarar da
ita."
"Ayya wallahi kuma na sha'afa ina sauri na bar wayata gida,
yanzu haka na san na sha kira kafin ta zo."
"I haka ta fada sai da ta zo ne ta tarar da wayar taki ashe kasan
ďaki kika bar ta." "Ayya! Bari in samu nutsuwa zan kira ta,
kai amma sai da dadi da aka yi mana awara. Granny bari in
dan watsa ruwa in yi sallah sai in zo in kwashi gara, yauwa
mun yi waya da Habu ina hanya in ya zo ki ce ya jira ni."
"To." Iya ta ce da ita.
Wanka ta fara yi sannan ta daura doguwar riga ta yi sallah,
bayan ta idar walDoctorop ta bude, kaya mai sauki ta ciro;
wando tiri-kwata da 'yar shimi ta sanya don garin akwai rana
Allah ma ya sa Kaduna akwai wutar Nepa sosai musamma
Mando, sannan ta yi dakin Granny. Filet ta samu ta zubo
awara tare da miyar jajjage ta bude karamin firji dake falon
36
AKWAI KURA
Granny ta dauko ruwa mai sanyi tare da zoßo wanda kusan koyaushe ba a raba ta da hadawa ta sanya a firji don tana kaunar zobo sosai da kunun aya. Cikin nutsuwa ta fara cin abincinta hannunta daya rike da cup tana shan zobo, a haka Habu ya yi sallama ya shigo.
Habu dan gida ne a gurinta shi ne mai mashin din da yake kai
ta school har ta kai shekarar karshe, a wata Ummi ke biyan shi. Habu saurayi ne a mawwabtansu yake gida uku tsakaninsu shi
ma Habin yana buga-buga tare da yin okada yana biyan kudin makaranta shi ma yana shekarar karshe ke nan a diploma akwai shakuwa sosai tsakanin Amra da Habu kasancewar
yakan shigo gidan nasu duk lokacin da yake free su sha hira, a
takaice Habu ba bako ba ne gare ta hatta Grannyn tata. Habu ya nemi guri ya zauna idonshi gar akan Amra, a ranshi yana yaba kyan halitta nata inda sabo ya saba ganinta cikin irin
wannan Doctoress. Ita ko Amra ko a jikinta dankwalin kanta
kawai ta kunce ta dan yafa akan kirjinta don rufe dukiyar fulaninta da ta dan fito ta saman shiminta.
Ta daka masa harara, "To maye bar kallo na kada ka cinye ni."
Habu ya yi dariya, "Ai da ni maye ne da ke zan fara cinyewa."
Amra ta yi tsaki, "Habu ka sani daga gobe nake so za ka fara
kai ni GRA karfe biyar da rabi ta yi maka a nan, na san ka da
wasa to ba ni son African time."
Habu da Iya suka hada baki."Biyar da rabi fa!"
"E haka na ce ko ba za ka iya ba in nemi wani?"
Habu ya ce; Na mene ne da tsa nani? Ai ko karfe ukun dare
kika ce zan zo ai girmanki ne gimbiya."
37
AKWAI KURA
"Oho! Ka ji dai da shi ni tashi ka je ka bar ni in sha iska kiran
da na yi maka ke nan, za ka ji alert zuwa in an jima in na samu
nutsuwa."
"To Hajiyata," Habu ya fada.
Karamin tsaki ta ja, "Kana iya tafiya ka wani sa ni a gaba da
kallo sai ka ce ba ka san ni ba."
Ya shafa gemunsa yana dariya, "Ai ke kullum makerin kyau
sake kera miki halitta yake yi."
Shi dai Amra tana burge shi yana son masifarta da rigimarta
sau da yawa yana son tsokanarta don ta yi masa masifa ya ci
dariya, ina ma shi wani mai arziki ne tabbas da ya fito an fafata
da shi wajen neman auren Amra. Sai dai shi kanshi ya san
wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa.
"Iya bari na je tun da an kore ni."
"A'a dawo Habubakar ka zauna mu yi hirarmu rabu da
Zainabu."
"Na dawo wani lokacin Iya yanzu akwai in da nake son zuwa."
***
Ranta in ya yi dubu ya baci, wannan wane irin mutum ne ma
canza kala? Ranar ta gan shi yana hada hannu da almajirai da
shigarsu ta fi tata kazanta, bai wulakanta su ba, a halin yanzu
ta gama sakankancewa ranta cewa abin da ake zargin shi zai
aikata tun da ta lura shi din hawainiya ne mai canza kala.
Hajara mai aiki tana gai da ita sam ba ta ji ba hankalinta ya
38
AKWAI KURA
lula duniyar tunani, mai aikin ta kuma shigowa hannunta dauke da tire mai dauke da kofin shayi sai filet mai cike da wainar kwai tare da buredi da ruwan faro mai sanyi kasancewar safiya ce.
"Baiwar Allah ga karin kumallo, na san kin yi sammako ba ki karya ba sai ki hanzarta kafin Hajiyan ta neme ki."
Boyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, ba don ta so ba ta dauki
ruwan ba ta tsaya zubawa a kofi ba ta sanya bakinta ta fara
kwankwada, sai da ta sha fiye da rabin ruwan kafin ta ajiye
goran, yadda ranta yake, bace ruwan kawai take bukata
saboda samun sanyin zuciya.
'Alhmdulillah,' ta fada a ranta lokacin da ta tabbatar da
nutsuwarta ta dawo, zaman banza na minti sha biyu Hajaran ta
kuma zuwa, "Baiwar Allah ki ci abinci mu je ga Hajiya mu je
Hajiya na son ganin ki."
Amra ta yi murmushi, "A'a a koshe nake mu je in ga Hajiya
shi ne damuwata."
Tare suka fita a dakin zuwa ga Hajiyar, abin Mamaki falon da
suka shiga dazu ba shi aka kai ta ba an kuma kai ta ne wani
falon da ya fi wannan dan karen kyau. 'Hm! Masu kudi suna
jin dadinsu,' ta fada a ranta. Har kasa Amra ta tsugunna ta
gaida Hajiya cikin sakin fuska.
Hajiyar ta amsa sannan ta kuma sunkuyar da kai. Hajiyan ta
katse mata tunani ta hanyar tambayar ta, "Sai dai ban gane ki
ba cikin dangin namu akwai yawa, ke kina ta wane bangare ne
a cikin 'yan uwan?" ta fada tana murmushi.
Amra ta kuma sauke kai alamun ladabi, "Hajiya ni bakuwa ce
ba daga cikin family nake ba na san masu gadi ba bari na za su
yi in zo gare ki ba shi ya sa na ce hakan."
39
AKWAI KURA
Hajiyar ta daga kai alamar gamsuwa musamma da ta san tsarin
shiga gidan matukar ba don gidan ba ko dan uwana ne sai ya
nemi izini a gate an sanar da su kafin ko waye ya kai ga
shigowa.
Amra ta ci gaba, “Hajiya aiki na zo nema ko Allah zai sa in yi
dace in samu, mahaifina ya rasu, tare da Yayar Babana nake
zaune cikin Amando, tsa nanin rayuwa ya sa na yanke
shawarar neman aiki don rufa mana asiri ni da Goggona shi ne
na zo da kokon barata ko zan dace, don Allah ki taimaka
Hajiya," ta fada cike da alamun tausayi a fuskarta. Ta kai
minti biyar, tana kallon Amra daga bisani Hajiyar ta ja
numfashi, "Ba mu bukatar 'yán aiki a gidan nan yarinya a
kowanne bamgare 'yan aiki namu uku ne kuma sun cika, а
halin yanzu ba mu bukatar kari sai dai in za ki ajiye lambar
wayarki lokacin da bukatar hakan ta kama sai a neme ki," ta
jawo wata loka dake gefenta, bandir na naira dubu dari cas! Ta
mikawa Amra, "ga shi ki rike muku ke da Goggon taki."
Amra ta fashe da kuka don wannan damar ita kadai ce take ji a
ranta za ta yi aikinta cikin sauki kuma ta yi imanin ta kufce
mata shikenan. Kuka take yi kamar an yi mata mutuwa tana
rokon Hajiya. "Yau da kika ba ni Hajiya gobe wa zai ba ni? Ni
kam na fi son aikin wanda na tabbatar kowanne wata muna da
mafaka ni da Goggona." Cikin tausayi ta daga mata hannu,
"Ya isa! Ya isa yarinya, kin yi karatun boko?" Da sauri Amra
ta ce, "E Hajiya." "Wanne mataki kika tsaya a boko?"
Cikin in ina ta ce, "NCE." don ba ta shirya da fada mata
gaskiyar matakin karatun ba saboda tsaro.
Bangaren Saleem kadai yake neman 'yan aiki saboda daya
daga cikin masu aikinshi ta je ganin gida mahaifiyarta babu
lafiya kuma da alamun za ta dauki lokaci sai sadda jikin ya yi
sauki," ta kalli Amrah tana nazari, 'anya Saleem zai amince da
40
AKWAI KURA
ita in ta dauke ta aiki ganin dazu yadda ya yi mata ba tare da
sanin ita wace ce ba?' tausayi da karamci irin na Hajiya shi ya
sa ta yi shahada ta ce da Amrah, "Saleem ba ya cin abincin gida Nigeria sai lokacin da ya yi sha'awa kina ganin za ki iya?"
Amrah ta kuma daga kai don tabbatarwa. "Ok zan ba ki dama
ki jarraba, akwai time table da za a ba ki ki dinga amfani da
shi wajen aiwatar da abincinshi na kowacce rana sannan akwai
computer wato system da za a baki don karar da ke ilimin
abincinshi maybe wata rana ya bukaci abincin Canis, kin ga
tun da kin yi karatun boko sai ki duba Google, yanzu haka
akwai 'yan aikinshi biyu za ku haďu gobe zan sa su kara miki
haske kan ubangidan nasu don gujewa faruwar kuskure sai dai
duk degree gare su daga mai yi masa gyaran daki mai yi masa
abinci har ma mai savin nashi in zai ci abinci." Amrah ta
gyada kai alamun tana fahimta, "Na gode sosai Mommy Allah
ya kara girma." farin ciki ne ya lullube Mommy wanda har sai
da ta murmusa, hakika yarinyar ta shiga ranta musamma yanzu
da ta kira ta da Mommy, a zahirin gaskiya ita kadai ce cikin
ma'aikan ta fara kiran ta da Mommy sauran sai dai su ce
Hajiya, "To Amratu sai a yi hakuri da son don shi din jakar
magina ne sai ya so ake hawanshi. "To," Amrah ta kuma cewa.
"To shikenan za ki iya tafiya gobe za ki fara aiki kuma kada ki
manta karfe shida na safe ta yi miki a gidan nan. Amrah ta
furta a fili, "Shida?" tana kallon Mommy idonta cike da tsoro.
Mommy ta shafa kanta, "E Amratu aikin ne akwai yawa kuma
mutumin naku karfe takwas yake break fast kin ga dole sai
shida din shi ne za ki gama da wuri in ko za ki dinga kwana ba
damuwa sai a baki masauki a sashin 'yan aiki." Amrah ta ce,
"A'a Mommy zan yi kokarin ganin ina zuwa haka din.'
"Yawwa yarinyar kirki Allah ya yi taimako in kin zo goben za
ki samu uniform na ki a gurin Grace tare da sauran bayani."
Har ta juya za ta tafii tat dan juyo, "Ba ki tambayi salary ba
41
AKWAI KURA
Amratu." Amrah ta rufe ido, "Mommy ni ko nawa ne ina
godiya." Mommy ta yi dariya, "All right salarinki dubu dari
duk wata I hope ya yi miki?" Ta zaro ido tare da rike baki,
"Mommy ina godiya Allah ya kara girma.
***
Kwanaki uku ke nan da fara aikinta gidan Alhaji Hamza, a
cikin kwana ukun nan ta fahimci tsarin gidan da yawa ta
hanyar abokiyar aikinta Grace, Amra ba ta samu matsala ba ko
kadan wajen shirya masa girki saboda ita din dama gwana се
a wajen hada delicious kama daga na gida Nigeria har da na
Kasar ketare musamma da ta samu kayan aiki kama daga kan
na'ura mai sarrafa dukkan abin da take so, har ta abin bukatar
hada duk kalar abincin da ta gani cikin timetable nashi akwai
komai cikin store dake manne da kicin din, kichin din kawai
abin kallo ne iya kalle-kallenta ba ta taba ganin irin tsarin
kichin nashi ba ko a film, lallai kudi na shan kuka cikin
wannan gida.
Grace ita ce ke shirya table ba musulma ba ce haka Amira ita
ce mai gyaran dakin nashi, ka'ida ce cikin ma'aikatan uku
daya bay a shiga cikin aikin daya, mai gyaran daki ba ta da
ikon komai sai gyara daki ta fita haka mai girki ba ta da ikon
hada mishi table kamar yadda mai hada table ba ta da ikon
sanya hannu cikin harkar kicin, ita dai aikinta a gama ta
aiwatar da hada mishi abin da yake bukatar ya ci. A cikin
aikin Amra babu night kasancewar karfe biyar na yamma ta
gama aikin haka mai gyaran daki ba ta daga cikin masu night
amma mai ba shi abinci zaune take tare da sauran 'yan aikin da
suke kwana a cikin 6angaren 'yan aiki, tun da da ta fara aiki
shida saura Habu ke sauke ta ba ta taba latti ba hakan ya burge
Hajiya don ta san na daya daga cikin dalilan da Saleem yake
korar 'yan aiki, kafin zuwan Amra gidan Saleem ya kori 'yan
aiki fiye da shirin saboda lattin zuwa, a tsarimshi komai nashi
42
AKWAI KURA
da lokacin da yake son a yi masa shi ya sa ma ko jikin time
table akwai time din da za ki gama kowanne abincin ranar don
shi Saleem mutum ne.mai amfani da lokaci, da zarar time na
cin abincinsa ya yi ko yana office zai turo direba yadauka dan
baya wasa da cikinshi san baya jure yunwa duKadunaa abincin
bawani cinta yake sosaima amma dadaran lokaci ya yi baya
wasa da cikinsa. Cikin kwana ukun nan da ta yi ba su taba
haduwa da Saleem ba ka'ida ce in har ka gama naka aikin ba
ka da sauran amfani da har za ka zauna bangarenshi sai in har
wacce duty nata ne ita kadai ke da ikon zama bangaren Saleem.
Sam bai ga bambacin da ya samu kan abincinshi da na
ma'aikaciyarshi da take yi mishi a da ba wannan ya sa ya yi
zaton ko ta dawo ne, don kwana biyar da suka wuce Mommy
ke ciyar da shi don yana da labarin rashin mai girkin nashi ta
bakin mahaifiyarshi illa ma dadi da ya ga abincin ya kara. Ita
ko Mommy ganin Saleem bai yi complain kan girki ba ya sa ba
ta yi imishi maganar canjin mai aiki ba ta ja bakinta ta yi shiru.
Yau weekend da karfe shida daidai Habu ya sauke ta a bakin
gate ta cire hijabi har kasa tuni uniform na shaidar ma'aikatan
gidan ya baiyana a jikinta, riga ce da wando sai hula da ta tara
gashin kanta a ciki, babu kwalliya a fuskarta ko kadan, hakan
bai hana baiwar kyau da Allah ya yi mata baiyana ba, kafarta
takalmi ne toms wanda duk cikin gidan aka ba ta tare da
uniform. Kasancewar an yi ruwan sama daren jiya garin ya yi
sanyi shiru kake ji kamar babu kowa a gidan, iska ce ta fara
kada ta tuni ta fara jin sanyi ya fara ratsa ta, hakan ya sa ta yi
kundumbalan ciro hijabinta a jaka ta sanya a jikinta. Yau ita ce karon farko da ta fara karya dokar aikinta domin ka'ida ne
babu maganar hijabi in har kana cikin ma'aikatan gidan
musamma ta bangaren girki. Ta kwankwasa kofa. Daya daga cikin masu gadin ne ya bude mata gate, ba ta saurare shi ba ta yi shigewarta ciki. Idi maigadi yana mitar ta wuce ba ta gai da shi ba arnma kala ba ta ce da shi ba ta yi tafiyarta ya ja tsaki, "Wannan yarinya zan koya mata hankali wato tun da ta ga ta
43
AKWAI KURA
zamo ‘yar gida take rashin kunya wa mutane ko darajar
gaisuwa ba mu da shi a gun ta, hegiya don ta ga tana da ky
ne, dube ta kamar ba ita ce ta zo nan busu-busu da ita ha.
kamar an ciro ta a bakin kare wato yanzu ta fara wayewa ko.
zan yi maganin ki ne."
***
Cak! Ta tsaya tana kallon shi, sanye yake da wando iya gwiwa
tare da farar riga mai katon hoton zaki a kirji, hannunsa biyu
dafe da karfe yayin da kafafuwansa biyu suke daure a kan
karfe yana press up ita kanta tsawuyarta a gurin ta kai minti
biyu cikin minti biyun nan ta kirga adadin press up da ya yi
dari da uku amma bai gaji ba yana ci gaba da yi yayin da zufa
ke ta bulbula daga fuskarshi, duk da sanyi dake hurawa.
Saleem alamun kamar mutun da jikinshi ya ba shi ya sa ya dan
dakata da press up din ya daga kai don tabbatarwa, ai ko da
sauri Amra ta buya a bayan fulawa.
"Mts! Ya ja karamin tsaki sannan ya ci gaba da motsa jikinshi.
Amra na 6oye a bayan fulawa time to time tana duba agogon
hannunta, ajiyar zuciya ta sauke kai na jawowa kaina da na yi
wucewata da ya fi min, yanzu ba ni da tabbacin mutumin nan
zai tashi yanzu a gurin nan bare in samu damar wucewa. Ido
ta zaro, "Na shiga million," ta furta a hankali. Shida da rabi
agogon hannunta ya nuna, awa daya kadai ya rage mata ta
gama hada break fast kamar yadda ta saba kafin mai savin
nashi ta zo ita ta gama da na aikin, "wayyo ni Amra," ta fada,
"mutum ba dan aiki ba an mai da shi dan aiki karfi da yaji
kamar wata mara gata, anya Abbana da kana da rai ba wanda
zai auri Ummi bare har ya mai da ni baiwa," ta share kwallar
da ta tarar mata a ido, "ko da nake.makarantar sojoji ban yi
wannan aikin wahalar ba," a karo na biyu kai ta kuma lekowa
da kanta don ganin ya gama ko yana kai. Ai ko cikin sa'a ta yi
dace ya juya bayansa yana waya. A hankali ta lalla6o cikin
44
AKWAI KURA
sanda tana tafiya dab da za ta wuce ne ta ji iska ya huro mata
Kalmar da ya sa ta tsayuwa babu shiri, "friend kayan nan su
zamo ready, cikin dare nake so su iso, ka yi iyakar yin ka don
ganin sun iso tsakiyar dare," ya dan saurara da alamun wanda
ke wayar ke ba shi amsa, "Ok no problem, ka tabbatar sun iso
lafiya ba a samu matsala ba...," "ok no problem in ya iso
yarana za su tare shi saboda... will talk later friend."
Da sauri Amra ta buya a bayan bishiyar mangwaro dake
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 12