ba
ku amma ku bar min yarona, lafiya ba ta ishe shi ba," ta fada
tana shesshekar kuka. Daddy dake kwance duk addu'ar da ta
zo ranshi yake karantawa.
***
Gudun ceton rai take yi kamar za ta tashi sama, ban da
bambancin halitta ta mace da na namiji ba za ka taba cewa
wannan mace ce ke zuba uban gudu akan mashin ba. Sai da ta
yi tafiya mai nisa inda ta tabbatar ta yi musu nisa kafin ta dan
rage gudu. Anas ta kira yana dauka ta ce masa, "Kana ina?" ya
ce; "Ga ni hanyar gida," "Yawwa ka same ni yanzu a gida,
yanzu fa!" ta ce cikin karaji. "Beb I hope babu matsala?" "Ka
zo din please," ta kashe wayar har ta kama hanyar gida ta sake
tunani wayar ta kuma cirewa ta kira shi, "Mu hadu a Gamji
gate," "Ok," ya kuma fada. Amrah ta canza akalar mashin
din ta dauki hanyar Gamji gate a kusan tare suka iso ita da
Anas domin tana tsayuwa ta hango motarshi. Da sauri ta sauka
daga kan mashin din ta fada gaban motarshi. Nikabin ta cire ta
ajiye tare da hijabin ta hau sauke numfashin gajiya. Anas ya bi
ta da kallo yana murmushi, "Beb, Beb, ba ki gajiya fa yau
kuma me ya faru?" "Ruwa!" ta ce mishi. Anas ya miko.mata
sauran ruwan da ya sha a gora. Amrah ta karba ta shanye tas!
sannan ta yi ajiyar zuciya. "Dear mashin din nan yau ya gama
aikinsa a san yadda za a yi da shi." Anas ya kalle ta fuskarshi
90
AKWAI KURA
cike da son jin dalili ta ci gaba da magana, "na san an dauki
mumber na mashin din a kowanne lokaci jami'an tsaro za su
iya neman shi. Anas ya shafa gemunsa, "Yau ita ce karo na
farko da na ga tsoro a fuskarki Beb, me kika aikata?" Amrah
ta hada girar sama da ta kasa, "Ka san dai ba zan yi kisan kai
ba ko?" Ya yi dariya, "Ni ma ban ce ba kawai ina son sanin
me kika yi ne don in san ta yadda zan bullowa al'amarin."
Amrah ta sanya hannu cikin aljihunta ta mika masa bindiga,
"Na gode sosai da ba ni taimako cikin kowanne hali," Anas ya
yi tsai da ido a kanta, "Beb me ya sa har yau in na yi miki
tambaya sai ki canza tambayar da wata? Hm! Ka ba ni lokaci
ni da kaina zan sanar da kai komai, bayan na gama cinma
nufina." "Ok mu je in sauke ki a gida, mashin din ki bar shi a
nan duk wanda ya dauke shi rayuwarshi na cike da tambayan
'yan sanda, mu je kawai bar shi gurin tun da ya gama aiki,
neman kai ake da shi yanzu." Amrah ta yi dariya "Dadina da
kai akwai saurin gano mafita, mu je ka sauke ni gida ina son
canza kaya in koma gun aikina." "Kuma?" Anas ya kuma
fada, "lallai zan auri jaruma ba irin matan zamani ba masu son
jiki ko girki ba su iya ba.
***
Tun da ta dawo gidan ta fahimci ba su dawo ba, hankalinta ya
kwanta, kicin ta wuce kamar daga asibiti take ta fara aikin
abincin dare. Ta kai minti ashirin da fara aikin kafin ta fara jin hayaniya.
Duk hayaniyar dake faruwa a gidan tana jin su ita dai tana
kicin tana ci gaba da aikinta ko alama ba ta nuna ta san wani
abu na faruwa a gidan ba. Grace ce ta shigo kicin din cikin
damuwa ta sanar da Amrah abin da yake faruwa da oga a
hanyar dawowa gida daga asibiti. Amrah ta zare ido ita ma
cikin damuwa tare da addu'ar Allah ya tsare na gaba. "Maman
Affan, Maman Affan," Mommy ta kwala mata kira daga side
91
AKWAI KURA
na Saleem. Da sauri ta rage gas din don kada abincinta ya kone
ta haura saman Saleem din. Har kasa ta tsuguna ta gai da
Mommy tare da yi mata Allah ya kyauta akan abin da ta samu
labarin ya faru yanzu. Mommy ta shafa kanta "Ashe ke kin
riga kin dawo gida, Mera ta fada min Alhamdulillahi Allah ya
tsare ki,ba rabon za ki ga tashin hankali." Amrah ta yi dan
murmushi ta mai da hankalinta kan Saleem din dake zaune
kasan kafet yana shan lipton karamin cup cike da girmamawa
cikin muryarta mai zaki ta ce da shi, "Oga jarumi, Allah ya
kiyaye na gaba Allah ya kuma tona asirin mugu a duk inda
yake." Ba ga Saleem kadai ba hatta Maheer sai da ya juyo
daga kujerar da yake kwance ya kalle ta tare da amsawa,
"Amin amin Thanks," Saleem ya furta a hankali. Amrah ta
dube shi da mamaki a kan fuskarta da ma akwai abin da zai
sassauto da zuciyar wannan mugun? Ta yi murmushi a ranta
lafiya uwar jiki wato ciwo ya fara dawowa da shi saiti.
Mommy ta katse mata tunani, "Ki kara abinci kin ga gidan
namu yau akwai baki kuma ki dan yi wa Saleem pepesup na
kaza mai dan yaji ki soya masa arish yanzu please." "No
Mommy dambun kaza nake sha'awar ci irin wanda kike yi
mana shi nake bukata." Mommy ta rike haßa, "Son wannan
bakin da muke yi 'yan Allah kyauta ina ni ina wani shiga
kicin?" "Mommy ba komai bara in yi masa, na iya." Amrah ta
fada. "Yauwa 'yar albarka je ki ki yi masa kada ki makara ki yi
magana wa Mera na falona ta dan taya ki wani abin kada
aikinki ya kai ki dare." "Ba komai Mommy zan iya," ta kuma
fada. "Shikenan agogo sarkin aiki je ki kada ki makara."
Amrah ta mike don barin falon. Ga mamakinta Saleem bai ce
a'a ba kamar yadda ya saba ba ya cin abincinta Maza an ji jiki
ta fada a ranta kafin ta bar musu falon. Mommy ta mike ita ma,
"Bari in je in dan samu ruwan zafi in watsa ko zai rage min
gajiya." Maheer ya hau tsokanar ta, "Mommynmu ki kwanta
92
AKWAI KURA
ki yi baccin gajiya ki rabu da wannan tuzurun yanzu kam ai
muna gida babu abin da zai taba miki shi," Mommy ta yi dariya, "Ai tuzuruan dukkanku ne, ni dai Allah ya nuna min
ranar aurenku." Saleem ya ce; "Amin! Mommy na gode miki
ai shi ma matsayinmu daya." Fitar Mommy ke da wuya
Maheer ya sauko kasa, "Abokina alamu sun nuna ita ce ko?"
Saleem ya rike gashin kanshi, "wa ke nan?" "Mai mulkin
ranka ita ce yau ma ta kuma taimakon mu." "Yes she is." "Ba
muguwa ba ce," Maheer ya fada. Saleem ya kada kai, "ban
san ta a cikin layinsu ba tun last time bare dis time da ta zamo
ita ce silar kauce kaddararmu," ya tsai da idonshi kan Maheer,
"abokina ina zan gan ta? Lallai ina son in san wace ce ita."
Maheer ya dafa kafadar Saleem, cooldown za mu nemo ta duk
inda take a fadin kasar nan jikina na bani kuna tare always,"
Saleem ya kada ido alamun tambaya. Maheer ya gyada kai, "I
mean ita ma kana cikin rayuwarta akwai lokaci abokina kawai
mu ci gaba da addu'a." Maheer ya canza maganar, "wannan
wadda ta fita wacece ita?" "Oh! 'Yar aikina ce." "Very
beautiful gaskiya ta yi ba karya ba don akwai Babyna ba da na
zago ta nan." Saleem ya yamutsa fuska, "Kun cika son mata,
ai sai ka je in ba ka da M." Maheer ya yi dariya, "Mata ai abin
so ne in ban so mata ba maza zan so?" Saleem ya kauda kai
tare da lumshe ido alamun bacci, "lets sleep."
***
Gaba dayansu suka mike daga kwancen da suke, dukkansu
suka rungume Saleem suna kuka don jin dadin arzikin da ya
auna a karo na biyu. A daidai lokacin ne jami'an tsaro suka iso
gurin Saleem ya daga musu hannu, "Ku je kawai ba mu
bukatar taimakonku," ya fada cikin fada, "ku je ba ma so
yanzu ku me za ku yi mana? Ashe da ma hakan kuke aiki a
banza kuke karbar salary ba ku san kan aikinku ba?" Gaba
dayansu hakuri suka shiga ba wa Saleem don sun san in har
bai huce ba to fa kowa zai shafi aikinsa. Bai saurare su ba illa
93
AKWAI KURA
waya da yake amsawa daya hannunsa rike da bindiga da suka Kwace a hannun farayin. Jiniya ce ta motar asibiti ta karaso gurin tare da rundunar motocin custom da na soja suka iso gurin cikin kamewa daya bayan daya suke sarawa Saleem, Ku kai su asibiti ina bukatar su samu lafiya, wannan ba aikin ku ba ne aikina ne da kaina in gano wa ya turo su, lallai zan
gano shi ko ma wane ne ko da yana cin kasa ne lallai ni Saleem Jarumi ni zan gama da shi da hannuna," ya yi
murmushin gefen baki. Maheer ya yi umurni a sanya su a mota,
Daddy na rike da hannun danshi gani yake kamar wani abu zai
kuma samun shi ji yake kamar ya maida Saleem ciki saboda
kulawa. Mommy da su Mera su dai kuka suke ta yi tare da
godiya ga Allah da ya tsare su duka.
A motar Maheer Daddy ya ja su Mommy da Aunty Mera su ko
Saleem a motar su ta wajen aiki suka karaso gida, su Maheer
da Ahmad tare da rundunar tashi dake take musu baya. Ahmad
ya fi kowa cikinsu damuwa kan abin da ya faru, "Abokina wa
ke son kashe ka? Mun shiga uku wa muka tarewa gaba yake
son gamawa da mu?" Maheer ya kalle shi, "Ai ba mu ake son
gamawa ba jarumi ake son kashewa, abokina ya ya kake
magana kamar ba jami"in tsaro ba, ni da kai wa ya taba mu? Ai
duk alamu a fili suke ya nuna JARUMI ake son kashewa. "Shi
dai Saleem kala bai ce da su ba illa numfashin 6acin rai dake
cirewa tare da kudura niyyar ko ma waye tabbas ya taro match.
***
A bakin gate na farkon shiga gidan nasu ya sallami duka
matakan tsaron Saleem ya juyo kan abokan nashi, Ku ma ku
je ku samu hutu." Ahmad ya ce; "Maheer mu je ka sauke ni
gida." Maheer ya ce; "Ka wuce da motar mi ina tare da
abokina mu je ai motar na ciki da ita Daddy ya dawo." Ahmad
94
も
AKWAI KURA
da hankalinshi ba ya jikinshi sai wutsil-wutsil yake da ido alamun damuwa. Saleem na hankalnce da shi ya sassauta
murya, "Abokina ai mun saba karon-battar karfe da abokan gaba wannan ba komai ba ne ka je gida kawai." Ahmad ya yi
murmushin yake, "Mu je in dauki motar." Da kafarsu suka
taka cikin sauran gate din har suka kawo gate na karshe da zai
sada su da cikin gidan, a farfajiyar gidan Daddy da Mommy da kowa na cikin gidan suka tarbe shi haka ma'aikatan gida har
masu gadi ko ina sai Allah ya kyauta suke yi masa. Shi dai
Saleem, "Na gode, na gode," ya ke ce da kowa. Sannan ya
wuce side nashi. Maheer na take masa baya tare da sauran 'yan
uwansa.
***
Karfe biyar da rabi na yamma ta kammala dukan girkin nata
har da dambun naman kadan ta gama, bayan ta kammala ne ta
raba gida biyu ta raba ta nemi tangaran mai kyau manyamanya ta zuba. Amrah da yawa ta dan yi shi saboda ta yi har
da Mommy da Aunty Mera. Daya daga cikin naman ta dauka da kanta ta yi sallama falon Saleem. Ga mamakinta Saleeem
na kwance na bacci, Maheer kaďai ke zaune yana kallo a
katuwar talabijin dake manne jikin bangon falon. Sallama ta
shiga dakin, sannu da hutawa ta yi masa kafin ta ajiye
dambun ta juya za ta fita, Maheer da ya kura mata ido ta baya
yana yaba kyan halittarta ya sanya baki, "Yanmata ya ya sunanki?" Amrah ta tsaya ba tare da ta juyo ba ta dan yi jim kadan sannan ta ce; "Zainab." Maheer ya ce; "Kai Zainabu Abu, tsohuwa ce ashe to mun gode da delicious."
kasancewar sunan kakar shi ce wadda ta haifi mamanshi, Zainabu. Amrah ta fita daga dakin tana murmushi tare da yaba saukin kanshi duk da bai san ta ba amma ya yi mata wasa,
a ranta ta ce; 'Alhmdulillah da ba su taba haduwa a gun besty
ba da yanzu asirinta ya tonu duk da bestyn ta kai mata shi sau biyu gidansu amma ko rana daya ba su taba samun ta a gida ba
95
AKWAI KURA
sai dai su gai da Granny. Amrah ta koma kicin da kanta ta
dauki daya tangaran din ta yi side din Mommy don kai mata
nata yayin da Grace ta fara kai abinci side na Mommy kamar
yadda yanzu take yi. Ba ta tsaya hira ba yau kasancewar a
gajiye take, ita kanta tana bukatar hutawa. Bayan ta gai da
Mommy ta tsuguna ta ajiye mata tangaran din. Mommy ta
washe baki tana yi mata sannu tare da yi mata godiya, "Maman
Affan ai da kin mika masa." Amrah ta ce; "Mommy wannan
naki ne na kai wa Oga nashi." Mommy ta rike baki tare da
jawo tangaran din ta bude. Kamshi ne ya cika falon. Da sauri
Mommy ta damki dambun ta kai bakinta tana kada kai alamar
gamsuwa tare da jinjinawa Amrah wajen kwarewa akan wani
irin girki, dambun ya yi dadi sosai har ya fi natan da take yi
musu dadi, a ranta ta ce, 'In ma son bai ci ba ai gaba ta kai ni
sai in hada duka in ci dadina.' Godiya Mommy ta shiga yi
mata tare da sanya mata albarka kamar kyauta ta kawo mata
Amrah ta sunkuyar da kai tana murmushi tare da jin dadin
addu'ar da Mommy ke yi mata, "Amin," ta ce tare da yi mata
sallama ta fice daga dakin, har ta fita sai ta dawo ta ba Mommy
sako a gaida Maman Affan in ta tashi daga baccin firgici tare
da yaronta Affan.
***
Amrah tana fita Maheer ya tashi da kanshi ya shiga karamin
kicin dake side na Saleem wanda yake dauke da 'yan
abubuwan amfani kamar cokali da dan fulet na dai bukata in
ta kama ba sai ka fita falo ba ya dauko karamin sosa na gilas
tare da karamin cokali na shan shayi five alive yadauko mai
sanyi a firjin kicin din sannan ya dawo falon. Dambun ya bude
tuni kamshin dambun ya karade falon, Maheer ya fara hadiyar
miyau, kut! Kut! Cikin zakuwa ya dibi dambun da dan dama
ya zuba a filet din sannan ya matsa da sauran gefe, kasa ya
sauko ya zauna a kan kafet ya fara cin dambun, 'Wai wai, dadi
ke nan,' ya fada a ranshi tare da ci gaba da cin dambun kamar
AKWAI KURA
mayunwaci yanaci yana gyada kai alaman dadi ya tafi da shi.
Sai da ya cinye tas! Kafin ya dauki lemon ya sha. Tangaran
din dambun ya kuma ja ya bude ya kara a filet din, wannann
karon a hankali yake ci yana jin dadin shi. Saleem ya bude ido
ya sauke shi kan Maheer. Murmushi suka yi wa juna duka.
Saleem ya kalli filet din gaban Maheer, tuni ya tuno da
mafarkin da ya gama yi yanzu nata akan ta kawo masa dambun
kaza. Abin ne yaba shi mamaki ganin da gaske dambun kaza
ne a gaban Maheer. Cikin dakiku kadan ya fara tariyo
mafarkin nashi.
Yau ma kamar kullum sanye take cikin riga da wando fuskarta
rufe da nikabi tare da babban hijabi ya rufe mata jiki har kasa
sai dai ko kadan shigar tata ba ta 6oyewa baiwar kyan jikin
nata ba kirar coca-cola shape. A hankali budurwar ta tako ta
zo har gabanshi ta tsaya. Fuskarta kunshe da nikabi, Saleem
ya yi murmushi alamar jin dadin ganin ta. Hijabinta ta bude ta
zo gabanshi ta ajiye masa kwanon dambun nama cikin
muryarta mai dadi ta ce masa, "Jarumina tashi ka ci abinci ba
ni son zamanka da yunwa ka ga wannan dambun kazar da
hannuna na yi maka na ga kana kaunar shi." Saleem ya riko
hannnunta yana murmushi "Thanks jarumata matar jaruma to
a dan bude min fuskar mana in gani, in ga kyakkyawar fuskar
matata ko?" ya daga mata gira tare da murza zara-zaran yatsun
hannunta masu kyau farare tas. Cikin dariyarta mai sauti ta
daga nikabin za ta bude fuskar tata ke nan sai karar talabijin da
Mahir ya kara ta tashi Saleem daga mafarkinshi mai dadi ba
tare da ya ga fuskar tata ba. "Mitsw," ya ja tsaki yana hararar
Maheer, "dan iska ka raba ni da abar kaunata ban ga
kyakkyawar fuskarta ba." Maheer ya hau yi masa dariyar shakiyanci, "Sorry abokina ban sani ba da na bar ka kun sha soyayya." A kasalance Saleem ya mike ya shiga bayi, wanka
yake yi zuciyarshi cike da nishadi tare da sauri-yana cikin dokin son cin dambun kazar. Bayan ya gama wankan, alwala
97
AKWAI KURA
ya dauro don lokacin Magriba ya gabato cikin shirinsa mai
kyau na hap jamfa blue mai aikin ruwan zuma ya fito daga ciki
hannunsa rike da kum yana taje gashin kanshi. Cikin nutsuwa
fuskarsa cike da nishadi ya jawo tangaran din dambun naman
kazar, yatsunsa uku ya sanya ya fara kai wa bakinsa. Ido ya
lumshe alamun dadin naman na ratsa kwanyarshi Maheer
dake zaune shi ma ya sauko ya sa hannunshi suna ci suna
shakiyancinsu tare da yaba dadin dambun kazar.
***
Karfe tara daidai ya faka matorsa a harabar asibitin cikin
kasaita da izza yake taka kasa kamar ba zai tafi ba hannunsa
daya still daure da bandeji, waya ya ciro ya kanga a kunnensa,
maganar minti biyu ya kashe wayar. Da sauri doctor din ya
karaso gurinsa, "Ranka ya dade barka da dare kai ne haka
yanzu? Ya ya jikin?" ya fada cikin tausaya. Saleem ya amsa,
"Da sauki mu je ko?" Likitan ya ce; "Bismillah ranka ya
dade." Ya shige gaba Saleem na biye da shi a baya. Daki mai
lamba 16 likitan ya nufa. Jimawa Saleem ya ce da shi. Likitan
ya dawo baya da sauri yana sunkuyar da kai alamar
girmamawa, "Je ka ka yi aikinka in na fito zan neme ka," "То
ranka ya dade," ya kuma fada tare da barin gurin. Saleem ya
yi jim na second daya sannan ya sanya kafarshi hanyar dakin.
A daidai kofar shiga security ne uku ke gadin dakin. Da sauri
suka kame alamar girmamawa ga Saleem tare da mika masa
gaisuwa, kamar ba zai amsa ba ya amsa gaisuwa tare da dosat
shiga sakin da sauri. Daya daga cikinsu ya bude masa kofa ya
shiga dakin. Gado ne guda biyu a dakin mai dauke da
katuwar talabijin manne a bango sai toilet shi ma guda biyu
kowa da nashi haka firji guda biyu ne a kusa da kowanne gado
tare da katuwar loka ta sanya abin ajiya cikinsu,da alama dakin
na musamma ne, gefen kowanne gado security ne daya rike da
bindiga. Shigowar Saleem gabadayansu suka kame tare da kai
98
AKWAI KURA
gaisuwa. Saleem ya kalle su, "Ku jira ni a waje ina fitowa." "Ok Sir."
Tsayuwar minti biyu bai ce da kowa kala ba a cikinsu, kallon
su yake yi cike da nazarin su haka su ma suka tsura masa ido
cike da rashin tsoro. Saleem ya karasa jikin gadon, daya daga
cikinsu kafarsa daya ya dora a kan gadon yana yi masa kallo
cike da izza, "Jarumi za ku kashe ko? Tabbas jarumi zai mutu
amma in kwanansa ya kare amma ba a hannun kananan ‘yan
iska irinku ba, wa ya turo ku?" ya furta tambayar cikin karaji.
"Oga ba wanda ya turo mu,"1," wanda ke daya gadon ya fada.
Saleem ya kai masa mari mai cike da kara, "Don ubanka kai na
tambaya na ce kai na tambaya dan ubanka?" ya shako wuyan
rigarshi, "kai karamin dan iska ne tun da har yanzu ka da
kashin wani kake 'yan uku naira goma Becareful," ya fada
tare da cakumo wuyan wanda ya fara tambaya, "kada ka bata
min lokaci answer me, wa ya turo ku?" "Oga mu muka turo
kanmu," ya fada cikin nuna rashin tsoro. Saleem ya shako
wuyansa ya kai masa 6arin makauniya, "wane ne kai da ka yi
yunkurin kashe ni? Wane ne kai, ko ubanka? Kai duk
zuri'arku sun yi kadan a biya fansar raina da ku, za ku sanar da
ni wa ya aiko ku ko sai na sanya bindiga na tarwatsa daya
kafar taku?" ya fada cike da murya mai karfi."Ko kashe mu za
ka yi oga ba za mu fada ba, kowa ya tuba don wuya babu lada
ai akwai amana." Saleem ya yi murmushin gefen baki, "Za ku
fada daga karshe kuma in kashe ku sai dai bakin naku na
rashin kunya shi zai fada," ya sanya hannunsa a aljihu ya ciro
bindiga yana kada ta, bai ce kala da su ba ya juya zai fita. Sai
da ya kai bakin kofar ya kuma juyowa, tas! Tas! Tas! ya
sakarwa kowa bindiga a daya kafar, dakin ne ya dauki kara
tare da karae shegun biyu na azaba, "Za mu fada, za mu fada.
Saleem ya sanya kanshi ya bar dakin yana huci.
99
AKWAI KURA
Sintiri yake ta yi a dakin ya kasa samun nutsuwa, hankalinsa in
ya yi dubu ya tashi bai taba jin tsoro muraran irin na yau ba
yadda ya ga safiya haka ya ga dare bai runtsa ba. Mafita kawai
yake nema, ya daga kai ya kalli agogon dake manne a dakin
nashi, karfe uku daidai na dare. Ko alamu babu na bacci a
cikin idon nashi sai damuwa. "Saleem kai wanne irin shaidani
ne, komai na sanya a gaba sai ka yi kokarin ka lalata shi? Ba
zan bar ka ba Saleem ba zan bar ka ba. raina fansa ne a kanka
ba zan taba barin ka ba har sai na ga bayanka, yadda kake son
ka ga bayana ni ne nan sai na ga bayanka dan shegiya," ya
fada da karfi kamar Saleem din yana jin shi. Matarshi ce ta
shigo falon da gudu da alamar daga bacci ta farka, maganar
Alhaji da karfi ita ta ta da ta daga bacci, "Alhaji lafiya me ya
faru?" ta karaso ta rike hannunsa, "Raina fansa ne a kan shi,"
ya kuma fada yana kallon ta. "Wane ne shi? Ba dai Saleem
ba?" "Akwai wani bayan shi ne wannan karon ba zan taва
asarar kayana ba ya kuma rike kayana saboda dazu na samu
labarin hakan ina bacci aka tashe ni aka sanar da ni." ya fesar
da iska mai zafi daga bakinshi wannan karon na daura niyyar
sai na kai shi kasa ba zan bar Saleem ba, Matar tashi tahau
shafa kanshi, "Wannan an yi dan tsinanniya yo in ba a shigo da
irin wadannan kayan ba yaushe za mu samu kuzi a cikin kasar
nan Nigeria? Ai rayuwar yanzu sai da hakan shuwagannin sun
zame cinye duka daga su sai 'ya'yansu, in ban da ta hanyar
shigo da hodar iblis ba za su taba ba mu kudinsu ba, yo na ga
ba sata kake yi ba sana'a ce kuma ai in har gaskiyar ce me ya
sa ba za a kama har da masu shan ta ba sai kai da
kasuwancinka kake yi?" mitsw ta ja babban tsaki tana shafa
kanshi cikin sigar lallashi. Ya yi lum a jikinta ya samu dan san
yin zuciya. "Na rantse ni da Saleem sai dai mu yi mutuwar
kasko."
***
100
AKWAI KURA
Mommy da Daddy ke saukowa daga dakin Daddy a tare,
hannun Mommy rike da jakar Daddy suna hira, da alama fita
zai yi. Kai tsaye dinning table suka wuce don yin break fast
wayam babu komai. Mommy ta kwalawa 'yar aikinta kira,
"Hajara Hajara." Hajara ta fito da sauri tare da durkusawa har
kasa ta gaida Mommy sannan ta gai da Daddy. Mommy ta
kalle ta, "Yau lafiya ban ga break fast ba? Grace ba ta zo ba
ne?" "Ta zo Hajiya." "Ok kira min ita." A tare suka shigo da
Grace din ita ma Grace har kasa ta duka ta gai da Mommy da
Daddy. "Grace lafiya yau har muka sauko ba a jera break fast
ba? Maza ki yi sauri ki jera, Daddy zai fita yau da wuri."
Grace ta kuma dukawa cikin ladabi, "Mai girki yau ba ta zo
ba." Mommy ta kalli Grace da sauri, "Ba ta zo ba? Subhanallah
lallai Amrahtu babu lafiya don ba ta taßa kin zuwa aiki ba ku
je kawai zan neme ku, Daddy yarinyar nan ba lafiya jikina ya
bani hakan don akwai ta da hazaka." Daddy ya ce; "Ah to in
hakane sai a bincika a ji lafiyar tata, ina ce dai akwai wanda ya
san gidansu cikin yaran?" Mommy ta gyada kai alamar babu,
"Zauna Daddy bari in nema maka abin da za ka ci da sauri
kada ka makara." Daddy ya jawota jikinsa "Mommyn yara na
yafe miki yau kam na yi miki uzuri." Mommy ta kuma
kwanciya a kirjin mijin nata, "Bari in dauko maka sauran
dambun kaza sai in hada maka da 'yar juice mai sanyi ka yi
manage da shi." Murmushi Daddy ya yi, "Na gode abar
kaunata." Suka yi dariya duka.
Mommy da kanta ta shiga kicin ta hada break fast tare da
taimakon mai aikinta sai da ta kammala komai kafin ta ji
motsin Affan da Mamansa suna saukowa. Mera ta karasa
saukowa tare da gai da Mommy. "Lafiya lau," Mommy ta
amsa, "yauwa tun da kin sauko bari in shiga wanka ki karasa
shirya komai." "Mommy yau ina Maman Affan?" Mommy ta
yi jim, "Wallahi ba ta zo ba ko lafiya? Allah Masani." Mera ta
101
AKWAI KURA
zaro ido, "Ai kuwa ba lafiya ba Mommy don Maman Affan ba
ta da wasa kan aikinta amma bari a kira ta a waya a ji lafiya."
Mera ta kwalawa Zahra kira "Autan Mommy." Zahra ta amsa
tana saukowa daga dakinta, "koma ki dauko min wayata a kan
gado, don Allah ki yi sauri." Zahra ta juya dakin, ba ta jima ba
ta dawo da wayar rike a hannunta. Mera ta dubo number
Amrah ta danna kira har ta gama ringing ba a dauka ba, ba ta
daddara ba ta kuma danna kira still yanzu
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 12