kallon kar ta san
kar. "Saleem yawuce tunaninku na san waye shi, I know him
very well! Matukar muka yi sake dukkanmu zai gano mu kuma
in har ya gano mu tamu ta kare." Ya kallesu duka hudun, "Ina
mafita? Oga yarinyar nan na rantse tun da Duna ya ce bai san
ta ba na tabbatar bai san ta ba, mu ankare fa Oga watakila ita
ma wani take yi wa aiki saboda Saleem na da makiya fa Oga,
Duna ba zai taba cin amanarka ba in ya ci ai ta shafe mu duka,
mu ma ba za mu taba barin shi ba, ko ya ya Oga?" Duna ya
113
AKWAI KURA
furzar da iska daga bakinsa, "ba ni da alaka da ita billahillazi,
na fi zaton aljana ce don mace ta yi kadan ta yi wannan aikin,
mace ta kasa ta kora maza hudu, kai Oga Aljana ce aradu."
"Ko aljana ce za mu gama da ita, ya zamo lallai ku fara
farautar ranta a raye nake son ganin ta." Dukkansu suka amsa,
"An gama Oga amma ai ba mu san fuskar tata ba, ya zamo
dole mu fara ankarewa mu gano fuskar tata. Dayan ya ce;
"Haka ne Duna maganarka dutse mu ankare, na san tabbas tana biye da mu ya zamo dole karon gaba mu gane fuskarta don ko
ta kubuce mu yi farautar ranta da tushe, Oga maganar yaranmu
da suke gurin hukuma muna cikin talala, Oga a yi wani abu
fa." Ogan nasu ya yi murmushin bos, "Suna asibiti ya zama
dole kafin hukuma ta karbe su daga asibiti kai Duna da mai
malafa aikinku ne ku aika da su lahira, a halin yanzu ba na
bukatar su a raye tun da an riga da an san fuskokinsu ko da sun
tsere za a nemo su ko ina kuma neman su na nufin har da mu,
a daren nan nake son a yi aikin nan ku yi duk abin da ya dace
kan aikin, sako zai shigo wayoyinku." "Cau! Cau! Oga an
gama, za ka ji labari zuwa safiya," suka fada tare da shirin
barin gidan.
***
Kwananta hudu a asibiti jiki ya yi sauki sosai sai dai ta rame
sosai, da ka gan ta ka san ta yi ciwo sai farinta ya kara fitowa
sosai, hancin ya kuma tsini saboda ramarta. A yau ne kuma
Doctor ya ba ta sallama, Ummi da kanta ta zo daukar su a cikin
asibitin. Granny ta gama hada musu kayansu, duka 'yan uku
suka dauka suka yi mota da shi. Amrah ita ce karshen fitowa
daga dakin saboda ta tsaya ta wanke fuskarta, hijabinta ta
dauko daga saman gadon ta bude ta sanya, a ranta tana
mamakin yadda binciken Granny ya kai har ta ga wannan hijabin ta dauko saboda ranar da ta yi karon-battar-karfe da
shegun ta dawo gida a birkice kuma tana sauri ta canza kaya
114
AKWAI KURA
don ta koma gidan aikinta, in ba ta manta ba hijabin ita kanta
ba ta san inda ta jefa shi ba ta yi sauri ta canza kaya, Anas ya
mai da ita gurin aiki kuma babu niyyar sake amfani da hijabin
a ranta saboda tsaro. Sai ga shi Granny da ta je dauko mata
kaya tana asibiti ta dauko da hijabin a ciki. Kai Granny akwai
bincike ta fada a ranta, tare da fitowa a dakin don ta iske su
Ummi a mota. Da sauri 'yan uku suka rungume ta suna tsalle,
"Aunty gidanmu za mu je ko? Ba gidan Granny ba." Ta shafa
kansu, "Mu je 'yan ukun Mommy kada ku ka da ni kun ga bani
da karfi," ta janye su, "mu je mota." Karaf! juyowa da za ta yi
suka hada ido ko a cikin bacci ta farka ba za ta manta da
fuskarshi ba. Kallon -kallo suke yi wa juna tuni ya ramfo
zancen tare da gaskata zuciyarshi na tabbas ita ce, saboda ita
kanta kallon tsarguwa ta yi masa. Bugu da kari hijabin nan
tabbas da shi ta zo. Da sauri Amrah ta ja ‘yan uku har tana
shirin faduwa. "Hasken gilmawar kemara ya haska fuskarta,
alamu na an dauke ta a hoto. Da sauri ckin kidima ta shiga
motar zuciyarta cike da damuwa. "Ummi mu wuce gidanki
kawai," ta faďa cikin kidima. Ummi ta washe baki don dadi
domin dazu kafin su fito sun yi sun yi da Amrah kan ta koma
gidan Ummin kafin ta dan gama samun karfin jikinta, amma
Amrah fur ta ki sai ga shi yanzu da kanta ta ce su wuce gidan
Ummin. Tuni 'yan uku suka yi ihun murna suka rungume ta.
Ita ko Granny cewa ta yi, "Zainabu sarkin iko yanzu zuciyar
taki ta yarda ke nan, to Allah dai ya shiryeki uwar iya yi.”
Amrah kala ba ta ce da su ba don ta lula duniyar tunani da
neman mafita, ya zamo dole ta tserar da rayuwar
Grannynta .domin ta yi imanin ko ma su wane ne suna biye da
ita kuma in har ta yarda ta je gidan Granny, to fa ita kanta Grannyn na cikin hatsari shi ya sa ta yi wannan dabarar ta
zuwa gidan Ummi, ko ba komai gidan Ummin akwai tsaro
sannan Abban Amlah shi ya dace ya fuskanci matsalar ba
innocentmutum ba kamar Granny. Ummi da Grannyn sai hira
suke tare da yara. Amrah ba ta san suna yi ba, ganin za su
115
AKWAI KURA
dame ta da son ta shiga maganar ne ya sanya ta lumshe ido
kamar tana baccim daga nan tufka da warwara take yi.
***
Ta shirya tsab cikin abaya mai kyau wadda Ummi ta fita jiya
ta yi mata shopping, kasancewar babu kayanta a gidan Ummin
wadanda ta zo da su daga asibiti ba su da yawa. Abayar ta yi
mata kyau sosai kasancewarta doguwar mace ce fara tas!
Wayar Habu ta shigo wayarta, da sauri ta dauka, "Yauwa jira
ni bakin gate ga ni nan fitowa," da sauri ta fito daga falo ganin
gurin akwai duru-duru alamun garin bai waye duka ba ya
sanya ta dan ajiye short note wa Ummi kasancewar ta fita
gurin IT. Da sauri ta fita gate, masu gadi na yi mata sannu ta
wuce su. Habu ta samu bakin gate ta dale mashin nashi suka
tafi suna tafiya suna hira jefi-jefi. Tafiyar mintuna tara ta
kawo su kofar gidan. Bayan ta sallami Habu ta sanya kai cikin
gidan. Cikin sa'a ta samu kofar a bude gudun kada lokaci ya
kure kicin ta shiga ta fara shirya abinci, tuni kamshin girkinta
ya fara cika gidan. Saleem na kwance a dakinsa ya ji kamshin
girki. Mamaki nen ya kama shi ya san dai kwana biyu ba ya nan
amma ai tun kafin ya tafi ya san mai aikinsa ba ta zuwa,
Mommy ke yi musu girki duka gidan. Laptop dinsa ya rufe
tare da tashi, labule ya daga daga sama yana hango kicin din
amma bai ga kowa ba, hakan ya sa ya saki labulen tare da
tunanin ko kamshin girkin Mommy ne ya buso har nashi side
din. Amrah cikin lokaci kadan ta gama duk abin da take yi,
direct side na Mommy ta nufa don ta yi kewar Mommy sosai
tare da Maman Affan. Mommy da saukowarta ke nan daga
sama tana tsaye a kicin tana shirin fara hada break fast, a ranta
tana mamakin baccin da ya dauke ta har ta makara ba ta fito ba sai yanzu. Amrah ta yi sallama falon, kamar a mafarki
Mommy ta ji sallamar Amrah, da sauri ta ajiye tukunya ta fito,
tsananin dadin ganin ta da Mommy ta yi da gudu-gudu ta karaso ta rungume Amrah, ita ma Amrah cikin jin kunya ta
116
AKWAI KURA
rungume Mommyn zuciyoyinsu cike da farin cikin ganin juna.
Saleem da kamshin girkin ya cika masa ciki tuni ya fara jin
miyansa na tsinkewa tare da wata yunwa da ta taso masa
Karshe kasa jurewa ya yi ya fito don zuwa side na Mommy don
ya cika cikinsa da daddadan girkin da kamshinsa ya cika masa
hanci. Turus! Ya tsaya yana kallon Mommyn tashi rungume da
ita. Mommy ta kai minti biyu tana rungume da Amrah ba ta
sake ta ba kafin ta sake ta hadi da rike hannunta duka biyu.
"Maman Affan," ta fada tana kare mata kallo yadda ta yi
tsananin kyau cikin abayar, "masha'Allah," ta fada a ranta,
akwai kyau Allah ya yi halitta ko ita da take Baturiya ba ta isa
ta kai Maman Affan kyau ba. Mommy ta kuma rungume don
dadi tare da kaunar yarinyar tabbas jininta yana yawo a jinin
jikinta. Ita ma Amrah dadi ne tare da kunyar Mommyn da ya
kamata a rayuwarta ba ta taba ganin mace mai karamci irin na
Mommy ba ba wanda zai gan su tare ya ce ita din 'yar aiki ce
saboda babu kyama ko kadan a gun Mommy sai zallar kauna
da karamci. Saleem ta yi masa kyau sosai cikin abayar a
rayuwarsa yana son abaya a jikin mace musamman doguwar
mace abaya na daukar jikinta ya ci gaba da kare mata kallo,
babu makusa a jikinta sai madarar kyau da kwarjini, ya
tambayi zuciyarsa ina ta samu wannan abayar? Tabbas ya san
karamar abaya ya san babbar abaya don yana sayowa
Mommynsa kasancewar ita ma masoyiyar abaya ce. Tana da
kyau ya yi imanin sai dakinta abaya ce babba mai tsada
wannan in ta samu gyara ai ta fi karfin talaka, matar manya ce,
ya runtse ido yana tuno Doctoream girl nashi tuni ya ji kaunar
nashi babyn na ratsa jikinsa tare da burin kasancewa da ita, hm!
Zai so ya gan ta cikin abaya ya yi imanin za ta yi kyau sosai
fiye da 'yar aikin tashi. "I love you Angela ya fada cikin
muryarshi mai sanyi," bai san lokacin da murmushi ya kufce a
kan fuskarshi ba don dadin farin cikin da ya gani a fuskar
mahaifiyarsa. Mommy ta kuma'cire ta daga jikinta tana kallon
ta, "Maman Affan ko ba ki fada ba kin yi jinya don ga rama ta
117
AKWAI KURA
nuna a fuskarki." Amrah ta yi dan murmushi, "Sosai Mommy
kwanana hudu a gadon likita." Mommy ta kama baki, "Ayya!
Sannu 'yar kirki sannu kin ji I hope jikin da sauki yanzu?"
"Alhamdulillahi Mommy na ware sai godiyar Allah."
"Masha' Allah sannu Maman Affan." "Mommy ina Aunty?"
"Auntyn taki ta wuce tare da danki Affan." Amrah ta ji babu
dadi sosai a ranta har sai da fuskarta ta nuna Mommy ta dafa
kafadarta, "Yi hakuri Maman Affan ita kanta Auntyn taki da
kyar ta bi mijinta saboda rashin samun ki a waya ba ki kuma
zo ba ki yi hakuri sai dai ku yi waya, mu je ki zauna, bari in
hada break fast saboda Daddy kada in makara zauna ina zuwa
kafin mu yi hira." Amrah ta ce; "Mommy ai na gama komai
na side na Oga jarumi." Saleem dake gefe ya ji gabansa ya
fadi jin ta furta sunan Jarumi, bai taba jin dadin sunan a bakin
wani irinta ba, ko Daddu nashi da ya sanya masa sunan tun
yarinta bai taba jin dadin sunan a bakinshi irin nata ba,
Mommy ta zare ido, "Sannu Maman Affan, agogo sarkin aiki
ki ce yau za mu ci delicious da muka kwana biyu muna kewar
shi, kai sannu Maman Affan."
Bayan ya koma ya yi sallama kamar yanzu ya shigo side din,
"Son ka tashi." "Yes Mommy yunwa," ya fada yana shafa ciki.
Mommy ta rungume shi a jikinta, "Alhamdulillah ka yi sa'a
Maman Affan ta gama, ni kam ai yau makara na yi yanzu na
tashi, oya zauna dinnig bari in sanya a jera ka farayi kafin in
taso Daddynku." "Hajara," Mommy ta kwala mata kira. Da
sauri ta shigo, "yauwa je ki side na Son, Grace ta zo ta jera
abinci fada mata na kicin na Son," "To Hajiya," Hajara ta
fada ta yi waje. Mommy ta haura sama," Maman Affan ina
zuwa plaese.'
118
AKWAI KURA
Kamar ba za ta yi maganaba ta dan daga murya, "Oga J ina
kwana?" wani farin ciki ya tsinci kansa a ciki amma sai ya dan
tabe baki kamar bai gan ta ba, "Lafiya lau," shi kadai ya ce ya
yi shiru ita ma ba ta kuma bi ta kansa ba ta koma mazauninta
tana tunanin mafita kan matsalarta.
***
Kasa zama ta yi a falon ita da Saleem, ta mike a hankali ta zo
ta wuce ta gefensa. Da wutsiyar ido ya kalleta ya ci gaba da cin
abincinsa. Bayan gidan ta nufa wajen shakatawa hakan ta ji
tana kaunar zan zaga gidan bayan side na Saleem ta mike iska
na hura ta don dadin yanayin zuciyarta kunshe da tunani tana
kan tufka da warwara don neman mafita. Da fari ta dauki abin
Karami sai yanzu ta tabbatar abin babba ne. Tabbas akwai kura,
ta fada a ranta.
Da sauri ta ja tunga ta tsaya tare da dan labewa jikin katanga
daga nesa tana kare musu kallo, wayarta ta saita ta fara bidiyo.
Rami suka tona mai zurfi dukkansu suna hakin wahala kafin
Maman tata ta ciro wani kunshi daga cikin rigar nononta,
layoyi ta ciro manya-manya suka zuba a ramin, cikin sauri
suka mai da kasar suka rufe tare da daukar babban tiles dake
gefe suka mayar a gurin kamar babu wani abin da ya faru a
gurin. Ganin sun tunkaro wajen ta za su wuce da sauri ta yi
sauri ta dauke numfashi tare da labewa jikin katangar. Dariya
suke kyalkyatawa ta cin nasara suna tafawa ka ce abokai ne ba
uwa da 'yarta ba, sun wuce ta da kadan ta fito a ma6oyarta
tana murmushi, ikon Allah me ke faruwa? Duk wani tuggu da
aka hada masa sai na gani. Amrah ta buga kanta, what is
wrong why me? Allah masani. Ta ba wa kanta amsa. Cikin
sauri ta karasa gurin, abin mamaki ban da a gabanta suka binne
babu wata alama da za ta nuna maka cewan an daga tiles an yi
wani siddabaru a gurin. Cikin zafi-zafi ta fara waigen inda za
ta samu abin tono. Kicin ta koma da sauri ta dauko wuka tana
119
AKWAI KURA
waigen bayanta kada wani ya gan ta. Tono ta fara tana tsinewa
wannan mata da 'yarta marasa Imani. Amrah ta yi imanin
asirin ba na kowa Ba ne sai na Saleem don shi ne take da
labarin Meena na son ya aure ta. Tono sosai ta yi kafin ta ciro
Katunkatun layoyin guda uku, da sauri ta dauko su ta rufe
ramin, tare da mai da tiles din in da ta gan shi. Da sauri ta boye
layun a cikin gashin kanta ko tsoron ya yi mata illa ba ta yi ba
ita dai burinta su boyu kuma cikin gashinta shi ne zai buya don
babu jaka bare ta sa kuma babu inda za su boyu ba a gani ba
sai tulin gashin kanta.
Cikin sauri ta koma side na Saleem, kicin ta shiga tana sauke
numfashin cin nàsara tare da amakin rashin imani na mutanen
yanzu, wai a ce akan duniya ka cuci dan uwanka na jini!
Wannan abu akwai ciwo, jin ta fara jin yunwa ya sa ta tashi ta
nemi indomie guda daya ta dafa tare da hada shayi ta ci sannan
ta dora abincin rana tana girki tana tunanin mafita.
***
Kwananta uku a gidan Umminta ba ta yi maganar za ta koma
gida ba. Umminta ta ji dadi sosai ganin 'yar tata ta fara
saukowa ne daga kiyayyar da take yi wa mijin uwa. Haka
Alhaji Usman ya yi murna sosai na ganin Amrah gidanshi har
sai da ya kasa 6oye farin cikinsa ta hanyar sanar da Ummin
tata ya ce da ita, "Allah ya sa dota ta sauko ne da kuwa zan fi
kowa murna" Ummin tata ta yi murmushi, "Amrah rikici,
wallahi Abban Amlah ina mamakin hali irin na Amrah ka ga
akan kishi babu abin da ta bar mahaifinta haka jajircewa kan
abin da tasa a gaba kamar mahaifinta, dalilin jajircewansa ya
sanya Amrah ta samu gurbin shiga makarantar sojoji saboda a
lokacin ko kadan ba shi da arzikin sanya ta a makaranta, infact
ma albashinsa ya kasa, amma saboda shi mutum ne mai
jajircewa kan niyyarsa sai da Amrah ta samu gurbin shiga
makarantar. Bayan shigarta da karfinsa ya yi neman kudi don
120
E
ב
5
AKWAI KURA
tanadin kudin makaranta, kuma cikin ikon Allah kafin lokacin
biya ya tanadi kudin sai dai a kai makaranta. Ahmad yana da
kokari musamman akan diyarshi. Sai dai Allah cikin ikonsa
bai nufa zai ji moriyar karatunta ba.," Ummi ta fada tana mai
zub da hawaye. Alhaji Usman ya jawo ta jikinsa cikin
tausayawa yana shafa bayanta alamun lallashi, "Allah ya jikan
sa da rahma ko da ban san Ahmad ba sai dai a baki mai karfi,
amma shi din mutumin kwarai ne wanda kowacce mata za ta
yi alfahari da shi kowadanne 'ya'ya za su yi alfahari da shi ki yafe min Zainab ki yafe min na san ba za ki ta6a mantawa da
ni ne sanadin Ahmad ba kamar yadda wannan dalilin ya hana gudan jininki kusantar ki saboda jin zafina ganin ni ne sila,"
ya fada fuskarsa cike da damuwa. "Is okey Abban Amlah ko kadan ba ni zargin ka ai kowanne rai akwai adadin kwanansa a
duniya akwai kuma silar shi, ko babu kai Ahmad ba zai wuce adadin kwanansa a duniya ba,” ta shafa kansa tana murmushi, "Abban Amlah wai me ya sa ba ka kishi da Ahmad? Wallahi wani lokaci sai shauki na rabuwa ya kama ni na aikata wani abin akan marigayin sai in na farga inji kunya ta kama ni har abada ba zan daina yi maka godiya ba bayan rasuwar Ahmad kai ne mutumin da babu kamarsa a guna, ka dauki amanata
sannan ka dauki amanar tsohuwarmu wadda ko Ahmad ba zai yi mata abin da ya fi hakan ba, tarin godiya mai yawa Abban 'yan uku. Allah ya jikan mahaifa," ta fada tana sunne kai a
kirjinsa. Ya yi karamar dariya tare da shafa gashin kanta, "Ai ni ba na kishi da matacce don haka filfree."
Abin da ba su sani ba zamanta a nan gidan Ummin nata akwai dalili; da fari ta tsorata ranar da ta dawo daga asibiti amma daga baya ta samu nutsuwa tare da shirin tunkarar kowaccе kaddara in ta zo mata, tsoronta daya Granny, hakan ya şa ta kaucewa duk abin da zai hada alakarta da ita don tseratar da
rayuwar Granny ga masu farautar tata. Tana da sanin tabbas
121
AKWAI KURA
ko ta Grannyn za su iya samun damar cimma burinsu. Ga
aikinta ba ta fasa zuwa ba, duk wayewar garin Allah Habu zai
zo ya dauke ta, biyar da rabi zai dawo ya mai da ita gida.
***
"Mommyn yara, yau tsohon hannu ya tashi ke nan gaskiya sai
da dadin sinasir din nan ga shi miyar ta yi suga kamar
mazakwai." Mommy ta yi dariya tana jin dadin yabawar
mijinta ba ta ce komai ba sai diban abincin take yi tana kaiwa
bakinta. Saleem dariya kasa-kasa yake yi yana kallon Mommy.
Sarai Mommy tana jin sa ta san so yake yi ya kwabsa mata
gun Daddyn nashi amma ta ki kallon shi, shi ma Saleem
cikinsa ya ci gaba da bawa abincin tare da tsananin jin dadin
abincin; Daddy ya kalle shi, "Jarumina fadi abin da ke ranka
na san da magana a bakinka dariyar nan akwai Magana."
Saleem ya kara kallon Mommy yana dariya mai sauti, "Dad
Abinci ya yi dadi," ya ci gaba da kai loma. Gabadaya suka yi
dariya har Mommyn sai da ta dara tana hararar Saleem. A tare
suka shigo falon suna mamakin dariyar me suke yi. "Ina
kwana?" ta gaida yayan nata tare da neman gurin zama, ita ma
Meena ta ce; "Daddy ina kwana?" tare da gai da Mommy.
Duk suka amsa. Ta nemi kujera kusa da Saleem ta zauna
cikin kisisina da yanga ta fara gai da Saleem. Cikin shan mur
ya amsa tare da ci gaba da cin abincinsa, abincin kowa ya ci
gaba da ci suna jin dadinsa, ita kanta Meena da Mamanta
abincin ya burge su sai dai hassada ta hana su furtawa. Daddy
ya katse musu shirun," Mommyn yara abinci fa ya yi don haka
kina da tukwici idan na dawo," Daddy ya mike tare da share
bakinsa da tishu. Mommy ta yi dariya don jin dadin yabawarta
ga mijinta, a gefen zuciyarta kuwa ta kuduri aniyar koyar irinsa
a gun Amrah tare da duk wani girkin da ba ta iya ba don
faranta ran mijinta.
122
AKWAI KURA
Daddy ya kalli kanwarsa Asama'u, "Kika ce gobe za ku wucе
ko?" ta gyada kai bakinta cike da funkasau, "Ba damuwa,
Daddy ya fada, "zan sa a shirya tsaraba sai ki je da shi a bawa
wadda ta dace kuma direba zai kai ku in na dawo zan gan ki
kafin in kwanta." "To," ta ta fada tana kurbar shayi. Meena ta
sunne kai, "Uncle mota nake son a canza min." Saleem da
Mommy babu wanda ya ce kala. Daddy ya yi dariya, "Kai
mata ku ba ku da damuwa sai son gaye yaushe ne na canza
miki Aminatu? Shikenan ba komai in na dawo ma yi magana."
Meena ta washe baki tana jin dadi, "Na gode Daddy." "Ba
komai," ya ce da ita. Mommy ta mike don yi wa mijinta rakiya.
Saleem ya tashi, "Dad a dawo lafiya, ni ma fita zan yi ina son
יי
in koma bakin aikina." Daddy ya yi murmushi, Jarumina
Allah ya tsare min kai a dawo lafiya kada dai a manta a kula da
addu'a tare da yin sadaka tana maganin masifa, abin da ya faru
a kanmu ya zamo mana ishara, ban da Allah ya kawo baiwar
Allahr nan da yanzu mun kwana biyu cikin kasa, Allah dai ya
yi mata albarka ya kare ta da ga sharrin masharranta, abin da ta
yi mana Allah ya yi mata irinshi I wish in gan ta da zan yi mata
kyautar da ban san yawanta ba." "Ai kuwa," Mommy ta fada.
Shi dai Saleem dariya ya yi an tabo masa inda yake yimasa
kaikayi rabin ransa. Side nashi ya wuce yana murmushin
kauna yayin da Mommy ta bi bayan mijinta.
***
a
Sun yi shirinsu tsab na tafiya Kano, sai dai aiken direba uku su
fito amma suka ce abincin rana suke jira kafin su wuce,
cewarsu ba a san da dawowarsu ba kada su bar nan ba su ci ba
su je can an ciye. Mommy ta gyada kai, "haka ne zancen,
tare da kwalawa 'yar aikinta kira ta ba ta sakon ta sanar wa
Amrah a kicin ta gama girki da wuri kuma ta dan kara da su
Goggo saboda za su wuce Kano, har Hajara ta juya za ta tafi
Mommy ta kuma kiran ta, "Ki fada mata yau Grace ta jerawa
Son a side nashi ban ga dalilin da ana biyan 'yar aiki a wata shi
123
AKWAI KURA
kuma ya ki ci a can ba sai a nan ni ma yau ina bukatar in ci
daga ni sai mijina," Mommy ta fada tana hawa sama. Haba
zuciyarsu duka ta yi dadi daga zuwansu Kaduna zuwa yau ba
su taba jin farin ciki irin na yau ba, tun zuwansu sun yi iyakar
yin tunanin ta inda za su ba wa Saleem magani ya ci a cikin
girki amma babu hanya, karshe har sun yanke shawarar tafiya
sai wani lokacin sai ga shi Mommy ta ba su mafita ba tare da ta
sani ba, kamar kawaye haka suka tafa suna jin dadi.
Tuni Amrah ta gama girki, mai aikin na Saleem Grace ta shigo
kicin ta dibi nashi ta fara jerawa dinning na Saleem a side
nashi. Ita ko Amrah da kanta ta dauki abincin baki don yau
Mommy ta sanar da ita ban da su Ta ci gaba da yin aikin
Saleem ita za ta yi nasu. Amrah ta shiga falon dauke da tiren
abinci ganin shigowarta da sauri Meena ta kara waya a
kunnenta kamar tana waya ta fita daga falon. Amrah ta ajiye
abincin kan kafet tare da gai da Goggon, amma ko kallo ba ta
ishe ta ba balallantan ta amsa. Amrah ta mike ta bar mata falon
don komawa kicin a daidai shiga side na Saleem din suka yi
karo da juna tana shirin fitowa, ba ta saurari Amrah ba tawuce
da sauri. Amrah ta bi ta da kallo tana nazarin me ya dauke
hankalinta. Ta kada kafada, "Oho mata." Yau hala 'yan
masifar ba su kusa ne.
***
Zaman minti talatin ta yi a kicin tana shirin hada abincin dare,
haka kawai ta ji zuciyarta bai yarda da Meena ba yau ta hango
rashin gaskiya a fuskarta bugu da kari masifar Meena ta yi
mamaki da suka yi karo kuma Amrah ita ce ba ta da gaskiya ta
buga ta amma Meenan ba ta dauki mataki ba. Amrah ta tsaya
da aikin da take yi, "Meena ta karbi fada ma na rashin gaskiya
bare na gaskiyarta kai akwai wata a kasa ta fada."
124
AKWAI KURA
Mikewa ta yi ta fita daga kicin din a falon suka yi karo da Grace. Amrah ta yi murmushi, "My Sis zo ki ci abinci." Grace
ta washe hakora don dadi, don sau biyu ke nan Amrah tana ba
ta girkin Oga mai dadi. Tare suka shiga kicin din Amrah ta
zuba mata nata da ta rage za ta ci nama zuku-zuku a cikin
miyar sakwaran da miyan kuskus din, duk da ranta na tsananin
Kaunar abincin, sai dai burinta ya fi abincin yawa. Grace ta
shagala tana cin abinci tana jin dadinsa cikin dabara Amrah ta
jefo mata tambaya, "My Sis ni kam yau kin ga Meena a cikin
sashin nan?" Grace da ta zuba kuskus a bakinta ta ce; "A'a
ban gan ta ba sai dai dazu fitarki ta zo ta shige side na Oga ba
ta jima ba ta fito ko Ogan ya fita I don't know." 'An zo gurin,
Amrah ta fada a ranta. Da sauri ta kunna daya gas din ta dora
ruwan kuskus, Grace na yi mata hirar abincin ya yi dadi ita ko hankalinta na kan girki. Cikin mintuna kadan ta sarrafa kuskus
ta maida tunkunya ta fere doya Grace tana cin girkinta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 12