tana yi masa tambayar gabas. Murmushi ya yi tare da
nuna mata gabas hadi da mikamata jallabiya dake kan gado. Ba ta ce komai ba ta karba ta rufe kanta ta ta da sallah
Magriba da Isha i duka ta yi. Tana sallamewa ko addu'a bai ba
ta damar yi ba ya kwashe da dariya ya kyalkyale kamar ya
zare. Amrah ta bi shi da ido tana mamakin me ya sa shi dariya,
fizgo ta ya yi tare da kama gashin kanta ya murde, Amrah ta yi
ihun azaba tana neman dauki. Ya bata rai kamar bai taba
dariya ba "Wace ce ke? Wa kike yi wa aiki?" Amrah ta yi
wiki-wiki da ido tana.shakar numfashi tare da cije azabar zafin
da take ji a kanta na rike mata gashin kai. Cikin tsawa yake
maganar, "mace ta yi kadan ta yaudare ni, tabbas ke din mai
kyau ce da za ki dauki hankalin duk wani tantiri amma ban da
ni, ko da na bar ki kika yi ibada saboda ni ma musulmi ne,
kuma ki sani Ahmad ni murucin kan dutse ne ban fito ba sai
da na shirya," ya nuna kansa, "zan iya fasa kanki da bindiga
yanzu in har ba ki sanar da ni wa ya turo ki ba," ya sanya
hannu cikin aljihunsa tare da ciro bindiga ya sanya a kanta
goshinta tare da saita kunamar bindigar, kiris yake jira ya tashi.
***
Cikin second daya kwakwalwatta ta ba ta amsar da ta ba shi
tare da cire tsoro, ido cikin ido ta kalle shi ta yi murmushi, "Za
ka samu amsarka matukar ka ninka min farashi fiye da nashi
wannan kana iya fasa kannawa don na san wanda ya turo ni in
ya gama da Saleem kai ma ba zai bar ka ba." ta yi dariya mai
sauti, "mutuncinka aljihunka, ni ba ni da mutumci akan kudi
duk wanda ya ninka farashina shi ne maigidana."
137
AKWAI KURA
Kamar soko haka ya sauke bindigar daga kanta yana
murmushi tare da matsowa daf da ita har suna gogar juna,
"Nawa ya biya ki?" Amrah ta kalle shi tare da kara matsowa
kamar za ta shiga jikinsa. Hannu ta dora a kan fuskarsa tana
shafawa, cikin muryarta mai dadi ta ce; "Miliyan biyar." A
zahirin gaskiya ita kanta bakinta ya yi mata zugal wajen fadin
kudin amma sai ta gimtse tana ci gaba da shafa fuskarshi. Tuni
ya fara daukar layi saboda jin dadin shafar da take yi masa.
Cikin sauri ya jawo ta jikinsa tare da kai fuskarshi daidai tata
yana shirin hada bakinsu. Amrah ta yi fari da ido tare da daga
masa hannu, "maganar farashi kuke ba na harka ba, ka nutsu ni
bana cikin Kananan karuwai, mai kwana da ni sai wanda ya
kai." Cikin bacin rai ya jawo ta da karfi ta fadi kasa tare da
taka kafarta daya yana murdawa, "Ni ba karamin mutum ba ne,
miliyan biyar din banza, na kara miki miliyan biyar.""Waye
shi?" Amrah ta kalleshi tana nazari, tuni ta ramfo gidan zancen.
Ba za ta taba mantawa ba lokacin da Abban Amlah ke fadin an
kama Alhaji da hodar iblis, daga karshe ya ce; "Saleem ne
maigidansu, hasalima shi ke shigo musu da hodar iblis din
kasancewarshi ma'aikaci a hukumar yaki da fasa-kwauri
saboda wannan dalilin hukumar DSS take zargin sa bisa ga
zargin aka wakilta bincike, Idonta a kanshi sai dai a zahiri
tariyo abin da ya faru take yi ita da Abban Amlah.
Amrah har ta juya za ta fita office din ta dawo, "Abban Amlah
waye shi?" ya kalle ta da alamun tambaya, "Wa ke nan?"
"Alhajin," ta fada tana kallon sa. "Ba ki bukatar sanin
sunanshi." "A wanne dalili?" ta fada tana yi masa kallon raini.
Bai ce mata kala ba ganin ya raina mata hankali ya sanya cikin
fushi ta kama hanyar barin office din, kamar daga sama ta
tsinci muryarsa na fadin, "Alhaji Musa Dancanji." Amrah ta
138
AKWAI KURA
yi dariya bayan ta gama tariyo abin da ya faru ita da mijn
Ummi.. a hankali tamatso kusa da shi bakinta ya kai daidai
kunnensa ta furta, "Pay me my money first before I offer you what you want from me."
***
Ta kira wayarta ya fi sau sha uku ba ta dauka ba, daga karshe
ma sai aka kashe wayar. Da fari hankalinta bai tashi ba ta yi
zaton ko sun wuce gidan su Zahra ne amma bayan an yi sallar
Isha'i sai ga shi Zahran ta kira ta a waya Kan cewa ta bai wa
Bestyn nata wayar saboda ta kira bestyn wayar ba ta shiga,
Ummi tsaye take saura kadan ta fadi saboda jin maganar da
Zahra ta fada a waya, salati ta saka tana sallamewa Zahra ta ce;
"Ummi lafiya me ya faru?" "Na shiga uku," ita ce kalmar da
Ummin ta fada, "Zahra Amrah ba ta dawo gidan nan ba a ina
kuka rabu?" cikin tashin hankali Zahra ta fashe da kuka a
waya, "Ummi wallahi kin ji abin da ya faru tiryan-tiryan ta
sanar da Ummin yadda suka yi a Super market. Ummi ta dan ja
ajiyar zuciya, "Ina kyautata zato ko ta wuce gidansu bari in
kira Iyan in ji," ta fada tare da kashe wayar tata, lambar Iya ta
nema cikin sauri ta fara kira sai dai kash! An fada mata wayar
Iyan na kashe. Kuka Ummi ta fashe da shi tana fyace majina.
"Amrah ina kika shiga, Amat ban rike amanar gudan jininka ba
yau in Amrah ta rasa ranta tabbas sakacina ne," ta fada tana
kuka sosai. Da sauri 'yan uku da ke falonsuna kallo suka taso,
"Ummi wa ya saka ki kuka? Abba ne ya dake ki? Yi shiru
Mammynmu za mu rama miki in mun girma." Ummi ta jawo
su jikinta ta kuma fashewa da kuka mai kara, su ma 'yan ukun
kwamciya suka yi a jikinta suna kuka, cikinsu babu mai
lallashin wani. Wayar tata ta kuma dauka ta kira Abban su
Amlah da ya dauka ta fashe da kuka mai tsuma rai, "Zan je gidan Iya," Abban su Amlah ya ce; "Lafiya?" Ummi ta ci gaba da kuka ta kasa magana. "Ummin 'yan uku kada ki fita ko ina
139
AKWAI KURA
ban yarda ki yi tuki ba, gani nan zuwa gidan nan ba da jimawa
ba," ya fada tare da kashe wayar
...
"Me ya faru?" uwargidansa ta fada tana kallon sa a tsorace
don ta ji dukkan wayar da suka yi da Ummin, 'Yan uku danna
handsfree suka yi kasancewar akwai kyakkyawar alaka
tsakaninsa da matan nashi. Alhaji Usman ya ce, "Ban sani ba
Hajiya, don Allah ki yi min..." ta daga masa hannu, "Ba ka
bukatar tambaya ta izini don sai da komai maza tashi na yafe
maka, daren yau in ka je ka kwana sannan kada ka manta ko
me ye ya faru don Allah ka sanar da ni ko ta hanyar sako don
in samu nutsuwa in yi bacci." Alhaji Usman ya shafa kan
matarsa, "Allah ya yi miki albarka." "Amin!" ta fada tana
kokarin mika masa key na mota. Jallabiya ya sanya ya bar
gidan zuciyarsa cike da damuwa ta rashin sanin me ke damun
Ummin.'yan uku. Tafiyar minti ashirin da bakwai ta kawo shi
gidan kasancewar akwai 'yar rata sosai tsakaninsu. Maigadi ya
wangale masa gate ya wuce cikin sauri ya rufe motar ko
sauraron gaisuwar maigadi bai yi ba ya sanya kansa cikin
gidan. Maigadi kansa ya yi mamakin ganin maigidan nasa don
yana hankalc e yau ba kwanan amarya ba ne. "Allah ya sa
lafiya," ya fada tare da rufe gate.
Ummi ta janye 'yan ukun da suka yi bacci a jikinta a hankali,
ta daga su tare da kiran mai aikinsu ta kai kowa gurin
kwanciyarsa. Daga ita har 'yan ukun babu wanda ya samu
damar cin abincin daren da ta dafa, ta ji karar motar Abban
Amlah. Da gudu ta fito bakin kofa daga nesa ya gan ta, cikin
sauri ta karasa gare shi tare da fadawa jikinsa. Kuka ta kuma
fashewa da shi mai cin rai, "Abban Amlah in har Amrah ta rasa
ranta kan aikin nan ba zan taba yafewa kaina ba tabbas da
140
AKWAI KURA
sanina gudan jinina ta salwance wallahi ko tantama ba ni yi
mata nan nan za su iya sace min yarinya koyaushe.' Abban;yan uku ya rungume ta yana bubbuga bayanta alamar
lallashi, rungume a jikinsa har suka karasa dakinsu na bacci.
"Me ya faru? Wa ya fada miki Amrahn ta bata?' Cikin kuka ta
zayyana masa abin da ya faru. Shi kansa Alhaji Usman
hankalinsa ya tashi tuni ya fara jin zazzabi na son rufe shi, "Yo
ai in har hasashen Ummin 'yan uku ya kasance to babu wanda
zai kai shi shiga damuwa don shi ne silar komai. Cikin dauriya
da jarumta ya 6oye damuwarsa, "Haba Ummin 'yan uku
Amrah ba ta bata ba na san tana gidansu, in kin lura ai ma ta yi
kokari, yaushe Amrah ta taba zuwar miki kwana? Amma
zuwanta kusan sati guda fa ta yi miki please ki yi hakuri da
safe za mu je gidan Iya na san dota tana can," ya fada tare da
kara sassauta murya alamar rarrashi. Ummi ta kwanta a jikinsa
tana sauke ajiyar zuciya alamar ta ci kuka. Can ta ji ta samu
nutsuwa da kanta ta shiga bandaki ta yi wanka tare da dauro
alwala ta zo ta yi sallahr nafila kafin ta dawo gadon ta kwanta
jikin mijinta. Ya yi murmushi yana mata kallon kauna, "Ba ni
two minute in turawa yayarki sako." Ummi ta boye fuska don
kunyar kwacen kwana da ta yi wa yayar tata. Bayan ya tura ne
ya rungumo matar tasa suka kwanta tuni bacci ya dauke su
zuciyar kowa cike da tunani.
***
Tare suke da Mommy a falo suna hira wayar shi ce ta yi kara
ya kara a kunnensa.
"What?" ya fada tare da mikewa, "ga ni nan zuwa," ya fada
tare da kashe wayar. Mommy ta kalle shi, "Son lafiya?"
Saleem ya kama hanyar fita, "Mommy bari in dawo za mu yi magana." Mommy ta sha gabansa tare da sakawa kofar falon
key, "Wallahi son babu in da za ka je har sai ka sanar da ni me
ke faruwa." Saleem ya kalle ta yana shafa gemu, "Mom lafiya
141
AKWAI KURA
fa, please," ya fada cikin sanyin murya. "Son yadda na ga
hankalinka a tashe ba hauka nake ba da zan bar ka ka fita kuma
a cikin dare, ka duba fa karfe tara na dare, Daddy Daddy! Ta
kwala kira. Daddyn nasu dake sama da sauri ya sauk,o jin
kiran matar tashi. Hannunta rike da na Saleem ta tare kofa ba
zai fita ba. "Lafiya jarumin Daddy?" mahaifin nashi ya fada
tare da kama hannun dan nashi. Mommy ta fashe da kuka tare
da fadawa Daddy abin da ya faru. Saleem ya sanya hannu yana
share hawayen Mommy. Kuka Mommyn Saleem ta saka. "A’a
ni ba zan iya jure ganin hawayen sweettheart ba mu je in zauna
tun da fita ce ba ki so in yi." Mommy ta gyada kai tare da
kamo dan nata, "Zauna son, tsorona Allah tsorona mutane
musamma da yanzu suka sa min kai a gaba ba ka ci musu ba
ba ka sha musu ba. Saleem ya ce, "Addu'arku ita nake bukata,
Mommy zamana ba shi zai hana makiya bi na ba sai dai ita
addu'a tana canza kaddara musamma ta iyaye."
***
"Dad waya Dakta ya yi min wai yaran nan an same su a mace."
"What?" Daddy ya fada tare da mikewa, "ba dai wadanda aka
kama masu son kashe min kai ba.""Su mana." Dad ya ce
"Subhanallah!" Mommy ta kuma fashewa da kuka, "Ka gani
ko. Daddy wato masu farautar ran son ba su daddara ba, har
yau suna kan bakansu tun da ga shi sun bi wanda ake bincike
sun kashe, wayyo ni Allahna," ta fada tana shesshekar kuka.
Saleem ya kwanta a jikinta cikin shagwaba yana rarrashin ta,
"Is okey is so right ba mai kashe miki ni sai kwana na ya kare
insha'Allah ba zan mutu ba sai kin ga matar son dinki tare da
'yan dugui-dugui dina." Ya matso kusa da kunnen Daddy ya
yi masa rada. Dariya suka fashe da ita dukkansu har da
Mommyn. Saleem ya shagwabe fuska, "Bari in je in kwanta
tun da katoto da ni an hana ni fita no problem Mommyn
Saleem, gobe na je in bibiyi case din." "E je ka kwanta goben
142
AKWAI KURA
ido na ganin ido sai ka je.." Saleem ya fita yana jin dadin
kaunar da family nashi suke yi masa.
***
Account no ya fada yana kokarin ciro wayarsa daga aljihu.
Amrah ta yi fari da ido, "Wayata," ta fada. "Don tabbtr da alert
ba ki bukatar waya a nan." "Ina bukata,"ta fada, ya zamo dole
in ga alert, ganin sa kadai ne amfanin wayar a gare ni." Bai ce
mata komai ba ya kara waya a kunne, "Ku zo mata da
wayarta," ya fada, bai saurari amsar ba ya kashe wayarsa.
Daya daga cikin yaran nashi ya shigo falon a buge kamar zai
fadi tare da mika masa wayar. Da ido ya nuna masa alamar ya
ba ta. Hannu ta sa ta karfa tare da kunna wayar. "Tell me your
account no." ya fada yana kare mata kallo tare da lashe baki,
Ta kada kafada alamat babu tsoro. "Account nawa sun fi goma
saboda tsaro, bari in duba wanda ya dace," ta fada tana danna
wayar. Message ta shiga a hankali ta fara karanta masa
account no nata wanda yake haddace a kanta yayin da cikin
dabara ta hau kan sunansa ta yi masa rubutu An samu matsala
but Ummina kada su sani don't reply aika masa ta yi tare da
gogewa yayin da ta kai karshen fada masa account no da
account bank da account name. Tana gama fada masa ta mika
masa wayar kamar ba ta yi komai ba, sako ne ya shigo wayar, da sauri Amrah ta mika hannu za ta karbi wayar amma sai ya daka.mata tsawa tare da bude sakon. Cikin sauri ya tunkaro ta gadan-gadan. Amrah da ta tsure tuni ta fara ja da baya idonta
zare tana jiran me zai faru da ita.
143
AKWAI KURA
Masha'Allah na godewa Allh da Ya bani ikon gama littafi na
daya, a nan na kawo karshen labari na daya. Ku saurare ni
cikin littafi na biyu nan ba da jimawa ba don cigaban labarin.
Tabbas 'Akwai Kura'yanzu aka fara.
Taku har kullum.
Sayyada Taheer.
08100044786
Ba zan rufe littafin nan ba, har sai na yi miki fatan alkhairi uwa
mafí uba ko da uban sarki ne; Hajiya Khadija Musa Bukur.
Allah Ya ja kwana Hajiyata, Allah Ya ba ki aljanna ba tare da
hisabi ba, Amin.
Ina Kaunar ki Mamata.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 12