yi ta kasa tashi daga
gaban malamin nata tsabar damuwa, domin ta san wannan
sharrin Alhaji Usman ne, in ban da sharri ita da karatunta
dabam me ya hada ta dawani IT ofishin security? Rokon
malamin nata ta shiga yi kan ya taimake ta ya canza mata
musamma da ta bude takardar ta tabba tar ofishin uban su
Amlah aka kai ta, kamar yadda take yi masa inkiya.
Cikin kasala ta bar masa ofis din nashi saboda damuwa. Tana
fita kai tsaye mashin ta hau ta ce da shi ya kai ta ofishin su
Abban Amlah, a ganinta tana bukatar sanin dalilin da ya sa aka
kawo ta gurinshi kuma a bakinshi take son ji, a ganinta Litinin
ta yi nisa da har za ta jita ta fara zuwa kamar yadda ta gani a
jikin takardar. Ai ko tana zuwa gare shi da rashin kunyarta a
nan ta yi karon battar karfe da shi inda ya ba ta aikin da ya
sanya ta a cikin garari, bai ba ta fuskar da har za ta iya mayar
masa da raddi ba ya kore ta. To fa ga Amrah ga Babanta da
sannanu za mu ji dalilin da ya sa ya kai ta wannan ofishi.
***
Karfe daya daidai am karar alarm ya buga. Amra ta yi salati
tare da mikewa duk da ba wani bacci ne mai yawa ta yi ba don
ta kai sha biyu na daren ba ta yi bacci ba tana bincike kan
takardun aikin da aka ba ta. Tana cikin binciken ne a nan bacci
barawo ya dauke ta kwance akan takardun. Bandaki ta shiga ta
dauro alwala sannan ta gaba tar da sallah raka'a hudu,
hannunta ya kai minti ashirin a sama tana rokon Allah gafara
ga mahaifanta tare da sauran bukatunta na rayuwa, ba ta
sallame addu'a ba har sai da ta roki Allah nasarar aikin da za ta
18
AKWAI KURA
fara tare da kariyarsa cikin hatsarin aikin. Idar da sallarta ke da
wuya ta jawo wayarta kirar infinix ta hau bude sakonnin da
aka turo mata na whatssap, wani tsaki ta yi sannan ta yi
murmushi, agogo ta kuma dubawa; karfe biyu na dare amma
ga online din yadda ta zama kamar rana don abokai ne da yawa
maza da mata wadanda ba sa baccin dare sai daren ya raba
sabod chating.
Mts! Ta kuma jan tsaki, "Shegun friends Allah ma dai ya sa
suna sallar nafila duka akan lokaci waya ba ta dauke hankulan
nasu ba. Group nasu na makaranta ta shiga tana danna voice.
"Ni kun cika min kunne kowa ya ware ya yi bacci."
Ai ko tuni aka yi mata ca da korafi.
Zahra Kasheem kawai ke kare ta, "E gaskiya ne, tun da dare ne
ya dace yanzu kam kowa ya kwanta."
Amra ta ce, "Rabu da su kawata ai makulli zan nema in rufe
gidan in ga wani shegen da zai kuma budewa, kun ga ba ni da
lokacin surutu goos night," ta sauka tare da danna wayar don
ta kashe ta. Gabadaya takardun gabanta ta kuma jawowa tana
nazari.
***
Saleem sunanshi mai matakin mataimakin Konturola Janaral
(Assistant Controller General) a Custom. Saleem haifaffen
Kano ce mahaifinsa dan cikin unguwar Tarauni ne ya yin da
mahaifiyarsa ta kasance Baturiya 'yar kasar Cairo. Mahaifinsa
shahararren dan kasuwa ne wanda ake ji da shi a Nigeria;
Alhaji Hamza; in za a lissafo masu gidan rana wato kudi
tabbas za a sanya shi matsayin na uku ko na huďu a cikin masu
19
AKWAI KURA
kudinmu na nan Arewa, matarshi daya tak! Mahaifiyar Saleem
Hanna daga ita bai sake aure ba, yaransu uku akwai yayar
Saleem Mera sai Saleem kafin auta Zara. Tun fil'azal Hanna
Musulma ce mai Addini cikin Turawa shi ya sa Alhaji Hamza
ya yarda da auren ta don tabba tarwa ita din macen kwarai ce.
A Cairo suka fara zama don a can suka haifi duka yaransu, sai
bayan wasu shekaru ne suka tarkata ya nasu ya nasu suka dawo
Nigeria.
Alhaji Hamza na da zumunci, mutum ne mai kyautatawa
iyalansa har ma da duk wanda yake bukatar taimako daga
family nasu har da makwabta. Ko da suka dawo Nigeria Kanon
suka fara zama cikin GRA daga baya ne Hanna ta kawo ziyara
Kaduna a nan ta yi sha'awar garin. Alhaji Hamza duk state din
nan na Nigeria babu inda ba shi da gida, ganin matarsa ta nuna
sha'awar Kaduna ya sa ya dawo da zaman nan, kasuwanci
kuwa sai kara gaba yake yi (duk dukiyar da aka cire hakkin
Allah ai gaba take yi kullum). Mera ta yi aure yanzu hakan
yaranta biyu tana Lagos da mijinta. Saleem bai dawo Nigeria
ba sai da ya kammala karatunsa a Cairo a matakin karatu ya
gama PHD kafin ya dawo Nigeria. Dawowarsa babu jimawa ya
fara aiki da hukumar custom, mahaifinshi ya so ya yi
kasuwanci amma sam ya ki don ya fi sha'awar aikin custom
tun da kuruciyanshi. Fara aikinsa ke da wuya ya samu ci gaba
sosai saboda gaskiya da rikon amana, shekaranshi bakwai ya
samu ci gaban da wanda ya shekara sha biyar cikin aikin bai
samu ba. Da yawa mutane suna ha'inci ne akan aikinsu don cin
hanci shi ko kudi gidansu an tara, in zai yi zamansa babu aiki
akwai dukiyar da za ta ishe shi rayuwa, yana aiki ne saboda
sha'awa.
Saleem fari ne tas! Kamar mahaifiyarsa Hanna ya yin da Mera
baka ce kamar mahaifinsu, haka Zara ita ma baka ce sak! Mera
sai dai sunada kyawunsu na bugawa a jarida amma Saleem bai
baro komai ga Hanna magaifiyarsu ba, da yawa mutane ba su
20
AKWAI KURA
daukar shi matsayin Bahaushe saboda kamarshi da Turawa,
sau da yawa in mutane sun ji ya yi Hausa sukan sha Mamaki,
zatonsu ya ya aka yi Bature ya iya Hausa, ga Saleem ya fi kaunar harshensa na Hausa fiye da English ga shi kuma kasancewar bai tashi ckin Hausawan ba in yana maka Hausan
za ku ci dariya amma a hakan yake yin abinsa in hakan ta kama.
Mahir da Ahmad abokan Saleem ne na aiki a nan gidan custom
suka hadu suka kulla abota amma in ka gan su a tare yasda
suka shaku sai ka dauka abokai ne tun yarinta.
Mahir da ne ga wani Basarake a nan cikin Kaduna suna da
rufin asiri, haka Ahmad shi ma da ne ga wani atta jirin mutum.
A takaice kowa na da rufin asiri daidai gwargwado, sai dai
Saleem ya dare su nesa ba kusa ba, ko a ofis shi din nesa yake
da su in don matsayi ne da ba su yi abota ba cikin wadannan
abokai kowa gwani ne wajen kyau ga ji da kai da da wasa da
naira. Abban su Amlah da saninshi ya je har makarantar su
Amrah ya roki alfarmar a turo ta IT gurinsu domin burinshi ya
ba da Amrah wannan bincike kamar yadda ya yi imanin
binciken mace kadai za ta iya domin sun tura maza biyu daga
cikin ma'aikatansu amma har yau babu labarinsu, wannan yake
tabba tar musu cewa ma'aikatan nasu sun mutu wajen aikin. A
zahiri aikin akwai hadari amma alkhairi ne ga duk wanda ya
samo amsoshin case din, don gwamnatin tarayya ta yi
alkawari tare da hukumar DSS cewa akwai kyauta mai tsoka
gami da kujera mai girma da za a bai wa wanda ya yi wannan
aikin. Lokacin da suka yi taro da manyansa kan aikin, Amrah
kadai ta fado masa a rai, haka kawai ya ji a jikinshi jaruntar
yarinyar za ta iya ya yi imanin mace ce mai kamar maza shi ya
sa ba tare da Amrah ta sani ba ya je har gida ya sanar da Iya
tare da Zainabu suka je don ita ya fara sanarwa. Da fari Iya
tsoro ya hana ta yarda gani take yi kada Amrah ta rasa ranta
kuma ita kadai ce take gani ta ji dadi tun da babu mahaifinta
amma da Abban su Amlah ya yi mata bayani hadi da roko ba
21
AKWAI KURA
don Iya ta so ba ta amince, daga karshe ya roki alfarmar kada
ma ta nunawa 'yar rigiman nashi ta sani, a nan Zainab ta ba da
shwarar sanya fuskar Bos ga diyar tata don kada ta tsinka shi
gaban yara a ofis kuma ta hakan ne zai yi mata kowane umarni
ta bi don ta yi imanin Amrah zuma ce shanta sai da wuta.
***
Ta ja gwauron numfashi bayan ta gama karanta historyn
Saleem da mukarrabansa, a karo na biyu ta kuma. daukar
wayarta ta kunna datar ta bude ta yi log in a facebook, abu
daya ya zo zuciyarta shi ne; duba assitant controller ko yana
facebook, full name dinsa ta yi searching kamar yadda ta gani
a jikin takardun Saleem Hamza jarumi. Ba a fi dakika hamsin
ba ta yi nasarar samo shi, bincike ta fara yi a cikin profile nashi
tuni ta shiga hotuna.
Masha'Allah,' ta fada a ranta don ganin baiwar halitta da
Allah ya yi masa daya bayan daya take kallon hotunan, wani
cikin kayan aiki ya yi kyau sosai shi da family nashi a kasan
hoton an rubuta my everything tabbas ko tambaya babu ganin
kyakkyawar mace rungume da hannun Saleem a kirjinta shi ya
tabba tar mata wannan ita ce mahaifiyarshi, a gefe kuwa ga
kanwarsa da Daddynsu cikin farin ciki da katon cake a
gabanshi an yi ado da fulawa da kyandir alamun daya cikinsu
ke birthday. Da hanzari ta ci gaba da duba sauran rubutun
kasan inda aka yi rubutu da manyan haruffa da kai haka
JARUMI is +1 da alama hoton bai jima da yin birthday din ba.
Da sauri-sauri don sanin yaushe ne ya yi wannan postin, ai
kuwa ta yi sa'ar ganin date din; 30 first watan Oktoba, duk da
bai da misalin karfe hudu na yamma hakan yana nufin an haife
22
AKWAI KURA
shi ranar 31 ga watan October ke nan. Ta daga kai sama, "Yes
haka ne." comments na mutane ta ci gaba da gani daya bayan
daya, mutane sun kai dubu uku likes kuwa sun fi hakan, ba su
gajiya ba suna yi masa wishes birthday, age wt Grace sir sir
sir ita ce kalmar da ta fi yawa a cikin comments din, a
maimakon ya bi daya bayan daya wajen reply a'a is rightita ce
kalmar da ya rubuta a kasan ya yin da mutanen suka kuma yin
ca wajen yabawa da nuna kauna a gare shi.
Amra ta ja tsaki, "Kai kwadayi ya yi yawa a duniya kun wani
damu kanku wajen nuna masa kauna shi ko ba shi da lokacin
amsarku kai wannan da gani dan zafin kai ne girman kan banza
kawai."
Friends nashi ta so shiga ko za ta samu evidence a nan amma
ina ya kulle friends na shi babu halin gani ba ta gajiya ba ta ci
gaba da duba sauran hotunan da ya sa tana duba comments na
mutane a kasan. A wani hoto ne da ya sa yana sanye da kayan
Hausawa farar kaftan da malum-malum ya yi rubutu a kasan
kamar haka; Kanawan Dabo ko da me ka zo an fi ka. Ya yi
kyau kamar sabon ango. Amra ta ci gaba da kallon hoton, ya yi
kyau sosai, a ranta ta ce; "Shi ko wannane cikin kaya kyau
yake?"
Ta turo baki kamar yana kallon ta, "To ni ina ruwana da wani
kyansa kyan dan maciji mugu kawai ni din nan zan yi sanadin
da za a yi ram da kai.
Comments na hoton ta bi shi ma don duba kowa irin na shi
yabawar ga Sir din, shi ko wannan karan ko darajar dubawa ba
su samu ba. A wani comment ne da ta ga an yi magana ya yi reply, ai kuwa da sauri ta duba wanene mai sa'ar nan da ya ba shi amsa sai ta ga ashe mace ce. Comment din dariya ta yi hahaha sai rubutun da ya biyo baya Young millonia Baturen
Kanawa lolz..... U luk like gorgeous my bro. A ya yin da shi
23
AKWAI KURA
kuma rubuta mata Autan Mommy bulala biyar tukuicinki. Ba
ta yi wani rubutu ba illa sanya fuskar kuka da ta yi shi ko bai
kuma magana ba. Amra shiga profile nata ta yi, Zahra Hamza
ta gani rubuce wannan kanwarshi ce zuciyarta ya ce to amma
ga Mamakinta me ya sa ita babu kalmar jarumi jikin sunanta,
ko dai sunan kanwarshi gare ta shi ya sa ta ce broda, adding
nata Amra ta yi sannan ta kashe data. Bacci ne cike a idonta a
wajen ta kuma kwanciya tuni baccin ya dauke ta.
Asuba ta gari Miss Amra.
***
"Granny na fito Zainabu kin shirya sai kuma ki yi."
"Ina fada miki ba ni son sunan nan in ba za ki kira ni Amra ta
ba to ki ce Zainab. Haba Granny ke kullum ba ki wayewa
yanzu in da a gaban kawayena ne da kin kwabsa min ba ki ji
ba ke ina kiran ki da sunan 'yan gayu Granny."
Iya ta ci gaba da tauna goronta,"Yo ai ni gara ki kira ni
Hafsatuna da wani gurani wa ya sani ma ko sunan takalmi kika
ba ni."
"Hahahaha," Amra ta sheke da dariya har tana tsugunawa, "ni
kin ga tafiyata Granny kar kisa in makara."
"To Allah ya tsare hanya a gaida min Zainabin da angwayena
da kishi ya.
Kasancewar yau Asabar weekend ne tun daren jiya ta daura aniyar zuwa har gida ta cimma shi ta san tabbas yana gida in
ma ba ta same shi a gidan ba ta daura niyyar bin shi har gidan
dayan matar tasa. A hankali take tafiya cikin shigarta mai
kamala abaya ta sanya ta yi rollin da maya fin Amra ma'abociyar doguwar riga ce domin ta fi kaunarta fiye da
24
AKWAI KURA
sauran kaya, bugu da kari abayar ba karamin kyau take yi
mata ba kasancewarta fara tas kuma.doguwa sau da yawa in ta
sanya abaya ita kanta ta fi samun nutsuwa in tana tafiya a kafa.
Ta yi tattaki har ta kai ga Neco junction inda ake hawa mota.
Motar na tsaye kwandastoci suna neman fasinja a bayan motar
'yammatane guda biyu suke zaune suna hirarsu kafin motar ta
cika a kaisu inda za su je, kujerar baya kwandastan ya dagawa
Amra, "Hajiya shiga ku cika uku/"
A bayan bayan ta yi matsuguni wa kanta 'yan yi matan biyu ta
yi wa sallama amma babu wanda ya amsa mata hakan ya yi
mata ciwo amma sai ta danne, su ko 'yan yi matan kallo daya
suka mata tuni hassada ta cika ransu na ganin kyawu da
tsantsar kamala da Allah ya ba ta. Zaman Amra kusa da su sai
suka gan su so local a gurin haskenta da kwarjininta ya cika
masu ido wannan ya sa suka kasa boye bakin cikinsu ta hanyar
kin amsa sallamar da ta yi musu. Ita ma wayarta ta ciro ta ci
gaba da danne-dannenta, a haka har motar ta cika aka dauki
hanya. A zahiri danna waya take amma a badini hankalinta na
kan 'yan yi matan nan biyu don sauraron hirarsu da suke yi.
Bakar mai nuna ta fi dayar jin kai ita ce ke maganar, "Ni fa
Yasira in zan mutu wajen nemo hanyar mallakar Saleem
billahil azeem ba zan gajiya ba ko da zan tafi tsirara sai na
same shi na ga alamar Umma tana sanya to ni kam na kusa in
fara neman mafita da kaina."
Wadda aka kira da Yasira ta ce, "Mina na sha fada miki ki
kwantar da hankalinki dan uwanki ne fa, hasalima ai
mahaifinshi shi ne madaurin aurenki dan kanin babanki ne ai
taki ta zo gidan sauki ko Saleem ya so ko ya ki ke ce matarsa.
Yasira ta daga hannu ta dunkule, "Allah ya ja zamanin
uwargidan jarumi."
Amra da ke gefe tuni ta ramfo zancen, wai da ma maganar
Saleem jarumi ake yi? Wato ba hukumar fasakwauri kadai ke
25
AKWAI KURA
neman sa ba har da 'yan yi mata ana fafatawa da shi tuni tsanar
shi ya dira a zuciyarta, ita ba ta son mai neman mata ko kadan
wannan dalilin ya sa duk nacin samarin dake bin ta ba ta kula
kowa, burinta karatunta don t acikawa mahaifinta dake kabari
burinsa, har yau har gobe ba ta ba wa wani saurayi fuskar da
zai shige mata ba, Granny ta yi mitar ta yi nacin amma sau
dubu in saurayi zai ai ko ta zo a waje to korar dan aike take yi,
karshe Granny gajiya ta yi ta sanya mata ido a cewarta in ta yi
bandaro za ta kai hotonta masallaci. "mitsw!" Amra ta ja
tsaki, "babu kunya babu tsoron Allah mota ta haya ba ta
ubanku ba kuna hirar jahilci."
"Kan uba!" 'yan yi matan biyu suka hada baki wajen furtawa,
"Yau sai mun ci uwarki a motar nan shegiya mai farin bilicin."
"Oh! Da ma hassadar farin nawa kuke yi ke nan shi ya sa da
na yi muku sallama ba ku amsa ba to ko makaho ya shafa ya ji
ya san ni din fentin Allah ce.':." Kokawa ce ta so ta kaure
tsakaninsu, fasinja dake motar tuni hankalinsu ya kai kansu,
hakuri suka shiga ba su amma 'yan yi matan nan sun ki bari, a
cewarsu sai sun ci uwar Amra. Daya mai jin kan ta jawo
wuyar rigar Amra, "Sai na ci..."
Tas! Amra ta kwada mata mari, "Sake ni uwata ta fi karfin ki
ci ta sai dai ki ci taki uwar."
Kokawa ce ta kaure sosai a motar haya.
Da sauri direban motar ya tsaya, "A'a ku rufa min asiri kada ku
jawo min hatsari a hanya maza Danladi ba wa kowa kudinta ta
kama gabanta ba zan iya da fadan tika-tikan 'yan yi mata ba."
"A'a direba su dai wadannan masu rashin arzikin su fita ita
kuma wannan ai ba ta da laifi dama tun shigowata motar nan
hankalina na kansu ina jin hirar rashin arzikin da suke yi,
26
AKWAI KURA
hakurinta suka kure kuma ta yi min daidai da ta more 'yan banza," wata 'yar dattijuwa dake kujeran ta fada.
Daya daga cikin 'yan yi matan ta murguda baki, "Mu dai ba 'yan banza ba ne da iyayenmu ehe!"
Ungo naki," dattijuwar ta fada tare da mata dunkulo.
Daya daga cikin fasinjan ne ya ce; "Direba ka yi hakuri ai dukkanmu mun kusa isowa inda za mu je, daure ka sauke mu
in ya so kowa ya kama gabansa," ya juyo gare su, "yan yi
mata duka ku yi hakuri ba girmanku ba ne fada a titi. Ke 'yar fara dawo nan ki zauna ni bari in koma mazauninki direba mu
je don Allah, sauri nake," ya mike tare da ba wa Amrah
mazauninsa.
'Yan yi matan daya daga ciki ta funciko jaka za ta sauka dayar
ta jawo kunnaeta tare da rada mata su bari a je inda za a sauke
su in ya so su kama shegiya su lakkada mata na jaki. Ai ko
tuni ta gamsu da hujjar kawar tata, ba don ta so ba ta nemi guri
ta zauna. wayar ta ce ta yi kara ta kanga a kunnenta.
"Hello!" cikin harshen turanci take magana, "Nasir... Е
wallahi na iso mota ce ta lalace a hanya... E direba na ya je
gyara... mts ta ja tsaki,"motar haya na hau sai wari ke damu
na, ka san in ba a motar haya ba yaushe diyan talakawa za su
samu ganin ka a araha bare har su maka rashin kunya... a'a ba
sai ka zo ba kawai ka bari after sallar La'asar sai ka same ni a
cikin GRA gida mai lamba 12... gidan ai ba boyayye ba ne, in
ka ce gidan.... Ok ashe ka gane ma, no problem in ka iso sai ka
yi min waya zan fito," cikin gadara ta kashe wayar a dole ita
'yar GRA се.
***
27
AKWAI KURA
Cikin gadara ya fito daga cikin motar sanye yake cikin kayan
aikinshi na custom fuskarsa toshe da bakin gilashi wanda ake
kira da no respect ga dukkan alamu fuskanshi ta nuna babu
respect din abin Mamaki mutane na tsaye maimakon su ji
haushi illa yaba kwarjinin matashin jami'in custom din suke yi.
Cikin wannan hali boss nasu ya iso gurin, gaba daya fasinjan
dake cikin motar suka mai da hankali akan wanda ke tsaye
convoy jere da shi don ba wa idonsu abinci tare da ganin mai
zai aiwatar a wannan guri. A gefen hanya almajirai ne jere
reras suna bara maza da mata. Direct gare su ya karasa kamar
ba shi ba ya saki fuskarshi, murmushi mai kayatarwa ya
baiyana daya bayan daya ya dinga sanya hannu a aljihu yana
debo kudin da shi kanshi bai san adadinsu ba yana bai wa
almajiran sadaka abin ya burge mutanen dake tsaye matafiya
cikinsu har da gaba daya 'yan motar hayar, ita ma kanta Amra
abin ya burge ta sai dai a kasan zuciyarta tunani take ta ya ya
za a yi wannan matashi ya zamo mugu, bugu da kari aikinshi
aiki ne na masu kau da fasakwauri ta ya ya zai kasance daya
daga cikinsu? Tsayuwar minti biyar ya gama da almajiran
sannan ya juya don komawa mota. Da sauri daya daga cikin
'yan yi matan nan ta bude motar cikin gudu kamar ba budurwa
ba ta karasa gare shi "Yaya jarumi."
Cak! Ya tsaya shi bai tafi ba shi bai juyo ba.
Da sauri ta karaso gabanshi, "Motarmu ta lalace a hanya in
gida za ka je ka yi min lift."
Ko kallon ta bai kuma ba ya yi wa convoy nashi alamun su tafi.
budurwar na jin hakan ta yi saurin bin bayansu amma sai ya yi
mata alamun kada ta fara. Hannu ya sanya cikin aljihu ya ciro bandir na kudi bai saurare ta ba ya jefa mata akan fuskarta ya yi tafiyarsa, ya yin da convoy nashi suka rufa masa baya. Cikin
minti daya tak bat! Suka bace a kan titin. Dariya sosai mata
28
AKWAI KURA
san dake kan titin suka fashe da ita ganin ya tafi ya bar 'yar budurwar a tsaye, kunya tare da jin kamar kasa ta tsage ta buya
a ciki su ne suka hana ta komawa motar hayar. Cikin borin
kunya ta tsai da Keke napep da sauri kawar tata ta fito daga bus din ta fada a Keke napep din tuni suka bar gurin. Faruwar
wannan abin shi ne ya raba fadan Amra da wadannan 'yan yi mata.
***
A bakin gate suka hadu, tun daga nesa ya hango ta cikin gilashin mota, hakan ya sa ya umurci direbanshi ya yi parking.
Mamaki yake karfin halin yarinyar, yarinya karama wai tana kishin ubanta, a hakan ma mutuwa ce ta raba, yo in mutuwar
aure ne hala sai ta Allah. A wani bangare kuwa addu'a ya yi
mata a cikin zuciyarsa, Allah ya sa ta yi dacen samun miji ita daya kwallin kwal! Don ya yi imanin wannan ta auri mai mata hm! Sai Allah.
Ta karaso jikin motar, murfin baya ba ta tsaya Alhaji Usman
ya ja gilashin ido cikin ido suka kalli juna, ganin ba ta da
niyyar gai da shi ya sa ya sha mur yadda ta yi tsaye kamar
sa'anta. Ya sha mur.
"Madam Amra ya ya dai?"
Ta cuno baki, "Barka Abban su Amla.
Ya sha mur, "Zai fi kyau ki canza min suna ko ban samu
darajar Abban ba, yanzu matsayin oganki nake."
Ta kuma cuno baki tana kunkuni, "Sir bindigata na zo karba"
ta ci gaba, "kun ba ni aiki mai hatsari sannan kun bar ni hannu
Rabbana, wato ni ma a kashe ni kamar yadda aka kashe min
uba ko?"
29
AKWAI KURA
Baki Alhaji Usman ya saki sai da ya dara kadan sannan ya ce;
"Bindiga kamar yaki? Ko an fada miki bindigar abar wasa ce?
Ko da yake a zafin kanki hala kin dauka rana daya ake fara
harbi ba tare da an horar da mutane ba?"
Amra ta kuma shan mur, "Yo in har su 'yan uwan aikin nawa
da aka ba wa suna rike da ita ai ni ma ya zamo dole a ba ni,
matakan aiki ciki har da bindiga sannan ina son in san halinshi
dan fasakwaurin saboda in san ta ina zan fara dakatar da shi."
Ya daga mata hannu, "Halinshi ni ma ba ni da masaniya akai,
a gurinki muke son mu sani. Abin da ya kamata a ce kin san
shi a garemu duk na cikin fayil da aka ba ki sannan bindiga
babu bukatar hakan a gare ki, hankali da tunani da rashin tsoro
sune makaman aikin naki oya wuce ki ba ni guri zan turo miki
da sako ta account naki."
Direban motar, Danladi baki ya saki yana kallon Alhaji da
'yar rigimarsa inda sabo ya saba ganin rikicinsu, tun yana jin
haushi har ya daina sai dai ido amma rigimar tasu ta yau ya ji
dadin yadda Alhajin ya fara takawa yarinyar burki. haka
kawai don kana auren uwar yarinya sai yarinya karama ta
rainaka? Yarinyar da ka haifi wadanda suka kere sa'anninta.
"Mu je Danladi," ya yi umurni wa direbanshi.
'Yan uku dake wasa a harabar gidan suka karaso da gudu,
"Oyoyo! Aunty oyoyo Aunty." Ta rungume Ahmad, "Babana
yau babu Islamiyya ne na gan ku a gida?" Yaran suka hada
baki wajen cewa, "Malaminmu ne ya rasu aka ba mu hutun
kwana biyu."
"Ok Ummi na nan?"
יי" E tana sama."
30
AKWAI KURA
"Mu je," ta rike hannunsu. Da ihu yaran suka riga ta isa falon
suna kwala kira. "Mommy Mommy ga Auntynmu Zainab wadda ta zamo babbar mace tuni ta rikide ta dawo."
Hajiya Zainab ta sauko daga sama hannunta rike da carbi, ta
idar da sallar walaha, "A'a Amratu yau ke ce tafe? Ashe yau
za a yi ruwa har da kankara."
Cikin jin nauyi tare da sinna kai na rashin gaskiya ita kanta
Amra ba za ta iya kiyasta rabonta da gidan mahaifiyar tata ba,
duk da kauna da nacin da 'yan uku suke yi mata tare da son
kasancewa da ita koyaushe. Ta zauna kan chanis kafet don
huta gajiya.
"Ummi karatu ne ya yi mana yawa tare da nutsuwa kin san an
ce aski in ya zo gaban goshi ya fi zafi."
Uwar ta harare ta, "Ka ji yarinya in haifi 'ya a cikina ta ce za ta
yi min wayo. Ni dai ina fatan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 12