ya zo fa amma bana
mutuwa na aure dan aradun Allah wannan gaye ya tafi da ni."
Amrah ta fizgo wayar a hannun besty tare da fadin, "Mu ga
wane mai sa'a ne ya sace zuciyar bestyna?" Karaf! Idonta ya
sauka a kanshi, gayen ya hadu, sanye yake da bakin wandon
jins tare da farar riga mai dogon hannu yana tsaye rike da
56
AKWAI KURA
makullin mota, murmushi dauke a fuskarshi. 'Tabbas na san
wannan fuskar,' Amrah ta fada a zuciyarta. Zahra ta ce; "Ya dai bestyna ko bai miki ba ne? Kin san duk kaunar da nake yi mishi in bai yi miki ba ai dole in kora shi gaba." Amrah ta kirkiro murmushi tare da rungume bestyn tata sosai, "Ya yi min bestyna ga shi kyakkywa kai congrat bestyna, mu ma Allah ya mai da mu madadinku." Zahra ta 6ata rai, "Ai ke kam kin riga ni samu besty, ko kin manta da Ya Anas?" Amrah ta ce; "Haba bestyna wai irin kunyar nan." Zahra ta daka mata duka, "yau kuma ina ganin sabon salo." Wayar ta kuma karba, Ba ni in kare ma angonmu kallo sosai." Zahra ta mika mata wayar, "Ai na tura miki hotonshi a facebook da whatssap tun da na ga ba ki hauba shi ya sa na je gida amma na taras baki
nan besty ai kin san ba zan yi saurayi ba tare da na sanar da ke ba." "Ayya sory bestyna dan wani uzuri ne ya fitar da ni kin
san na fara IT." "Wow! very fantastic ki ce saura kadan besty
ta yi bankwana da school, kai congrat ki ce Yaya Anas ya fara shirin aure, Besty ina suka tura ki attachment?" shiru ta yi don ba ta da amsar ba ta a nan din. Kir! Wayar Zahra ta yi Kara. Hamdala Amrah ta yi a ranta. Zahra cikin zakuwa ta dauki wayar, "Bebyna albishir," a daya bangaren ya ba ta amsa, "Goro fari kal!" "Ga bestyna ta zo." "Kai ina gai da bestynmu babyna I miss you," ya ce da Zahra yayin da Zahra ta shagala tana hira da babyn nata. Amrah ta ciro wayarta dake jaka, data ta ta bude tuni sakonni suka fara shigowa ciki.
Ba ta tsaya bude na kowa ba sai na bestyn nata, hotonshi ne ya bayyana kala wajen shida. Tuni Amrah ta dago inda ta san shi; 'Maheer' shi ne Amrah ta fada a ranta, ta yaya hakan zai faru,
mugu azzalumi, shiine ne bestyna ta haukace akan son shi? No ina
ga kama ce ta yi yawa ba shi ba ne.' Zahra dake kwance kan kafet tana wayarta tuni ta shagala da soyyaya, idonta kulle tana
amsar sawon soyayyarshi ta waya. Amrah ta kalle ta, "Lallai bestyna ta yi nisa domin in ba ta yi karya ba iyakar rayuwarsu
57
AKWAI KURA
ba za ta ce ga kanar da wani saurayi ya dauke hankalinta irin
wannan ba, da alama bestyn ta manta akwai aminiyar tata a
dakin saboda soyayya. Ai kuwa juyowar da Zahra za ta yi
suka yi ido hudu da Amrah, ta daga mata hannu biyu alaman
ban hakuri. Ita ko Amrah ta daga mata kai alamar babu
damuwa. "Besty ga wayar ku gaisa," Zahra ta fada tare da
sanya wayar a kunnrn Amrah. Karamar ajiyar zuciya Amrah ta
sauwe tare da yi masa sallama cikin muryarta mai dadin
sauraro. Cikin wasa ya ce da ita, "Bestynmu yau dai sai da
muryar bestyn matata saura inga bestyn matata da ido." Kamar
yana kallon ta ta daga gira, "Haka ne gaskiya ni ma sai da na ji
dadin jin taka muryar angonmu. Ina fatan za ka rike bestyna
hannu bibbiyu, daga kanmu babu kari ka san muna da kishi ni
da bestyna." Ya yi dariya, "Daga kanku kallo ya kare, ni dai
ina so a kula da ni ehe!" Amrah ta katse masa hirar don ta ga
alamar shi ma dan caftan ne, ta ce da shi, "Sunana Amrah
Ammat what of you?" "Maheer Jabir Saraki," ya ba ta amsa.
Tabbas hasashenta ya tabbata dama ta yi hakan ne don
tabbatar da shi din ne, kuma ya sanar da ita hakan da kanshi,
"Nice to meet you,'," ta ce da shi tare da zare wayar a kunnanta
ta mikawa bestynta. Zahra ta karba, "Babyna mu yi waya an
jima zan ji da bestyna kada ta yi fushi." Maheer ba don ya so
ba, "Ok babyna Kadunaa ki manta in ta tafi call me back, you
know I miss you always," "Yes my love me too," sannan ta
kashe wayar, bandaki ta shiga don ragewa kanta ruwa, bayan
ta sanar da Amrah. Tafiyar Zahra ke da wuya Amrah a karo na
biyu ta kuma bude datar wayarta don ya rage mata kadaici
kafin Zahra ta dawo, data ta bude tuni sakonni suka fara
shigowa daga wahtssap wasu daga messenger, don duba sawon
friends a nan ta ga an yi accept na friend request nata da ta tura,
sai ta ga an yi mata offline message da account na Zahra
Hamza sai ita ma ta ba ta amsa tare da rubuta mata thanks so
much my sis for accept me as friend Daya bayan daya take bin
sakonnin tana ba su amsa, wasu kuma ta sa alamun dariya ko
58
AKWAI KURA
kuka. Besty Zahra ta katse mata danna wayar tata, "Gayen ya yi miki? Don ban hango farin ciki a fuskarki ba kamar yadda na saba gani in har abu ya yi miki dadi I know you bestyna more than u think." Amrah ta rike baki, "Wacce mace ce za ta samu wannan gayen ta ce bai yi ba? Ai ko hassada za ka yi ka san gayen ya yi, yes ya yi min bestyna." "To in ya yi miki me ya sa kika zama so silen?" Tuni ta yarda da amsan da bestyn ta ba ta fa, "Wallahi gajiya na debo, kuma fa haka ne gaskiya ne don na ga alama tun da jikin neman ruwa na tarar da ke. Zahra ta kara matsowa kuwa da bestyn tata tana fada mata yadda aka yi ta san gayen wato sun hadu ne a Super market sun je shopping da Mama amma saboda ta burge shi ta tafi da imanin shi a gaban Mama ya zo ya kwashi gaisuwa sannan ya roki Mama alfarmar magana da ita. Mama ta amince, "Ke bestyna wallahi gayen ya iya soyayya, ai Mama tana matsawa ya ce da ni ya ga matar aure, shi tun da yake bai taßa ganin matar da ya ji lokaci daya ya kamu da son ta ba irina. hm besty kin san tun da muka shiga shagon na yi arba da gayen sai da ya burge ni sai da na ce ina ma ya ce yana so na, sai ga shi Allah ya dora ni
a kanshi da kansa ya ce na yi mishi. "Tun da ya yi miki ni ma ya yi min bestyna Allah ya sa rabon ki ne mu sha biki ranar zan debo shoki." suka tafa tare da ihun jin dadi. Sun jima suna hirar Maheer tare da soyayyar da Zahra take sha a gun shi. Sai bayan sallar La'asar kafin Amrah ta yi sallama da besty ta rako ta har gate sai da ta ga tashin mai keke napep sannan ta shigo gida suna dagawa juna hannu.
***
Tun daga ranar da suka samu matsala da Saleem.ba ta sake ganinshi ba hakan bai sa ta bar shirya masa dukkan kalolin abincin da yake so ba, ita dai ba ta da tabbacin Saleem din ke cin abincin ko zubarwa ake yi, aikinta dai ba ta fasa ba kamar yadda Mommy ta yi mata umurni ta ci gaba kama daga abincin safiyar har na rana da yamma duk tana yin su. A cikin wannan
59
AKWAI KURA
lokacin ne Mera ta zo gidan ita da yaranta Affan da Afnan,
Mera tana da.kirki sosai don ranar farko da ta zo har side na
Kanin nata ta zo. Amrah na kicin tana girkin rana sai gani ta yi
mace ta yi mata sallama cikin girmamawa. Amrah ta gaishe ta
ita ma, a cikin sakin fuska ta amsa gaisuwar Amrah, "Bari in
duba bro," ta ce da Amrah. "A fito lafiya Aunty," Amrah ta ba
ta amsa. Affan ne ya hau mikawa Amrah hannu alamar yana so
ta dauke shi. Yaro ne dabai wuce shekara daya da rabi ba.
Mera ta rike baki, "Ikon Allah kin ga fa ba ya yarda da kowa
daga ni sai Afnan sai Abbanshi ko Nanny tashi ba ya zuwa gun
ta sai ta yi lullubi. Amrah ta mika hannu, "Kawo shi Aunty."
"A'a kina aiki rabu da fitinar Affan," "Aunty kawo shi don
Allah," Amrah ta fada. Mera ta mika mata shi, "to ni bara in je
in ga bro in ya ki sai ki miko min shi ko." "To aunty," ta ba ta
amsa. Wasa ta fara yi wa Affan tana tsilla shi sama, Affan sai
kyalkyala dariya yake yi kamar ya san ta tun fil azal .Amrah da
Kaunar yaron ya shiga ranta tuni ta ware tana yi masa wasa,
dariya take yi ita ma.kamar yadda yaron yake yi tana yi tana
aikinta. Can Affan ya fara lumshe ido alamar yana son bacci,
"To fa," Amrah ta fada, "ni dai ba zan iya zuwa dakin wancan
mara mutuncin ba. Dankwalinta dake daure a kanta samanshi
hula ne na aiki shi ta cire, tuni tulin gashin kanta ya watsu a
gadon bayanta, hular ta dauka ta mayar saman gashin kanta,
duk da haka bai rufe gashin ba, suna zube a gadon bayanta,
Affan ta sanya a bayanta ta dauki dankwalin ta goya shi da shi
sannan ta ci gaba da aikinta. Affan kuwa sai don ya samu
balance ya ci gaba da baccinshi, aikinta take yi tana wakar
kuch kuch hota hai cikin muryarta mai zaki kamar ita ta yi wa
kanta. A haka tare suka sauko daga sama ita da Saleem, suna
tafe suna kyalkyalar dariya, da alama hirar ta yi musu dadi.
Mera kamshin girki ne ya cika mata hanci tuni yawunta ya
tsinke, "Bro mu hade dakin Mommyn ni bara in karbi Affan a
kicin." "Mitsw," ya ja tsaki, "mata ba ku da hankali yaron naki
za ki bai wa mai aiki a kicin? Ba ki gudun ta kona miki shi?"
60
AKWAI KURA
Mera ta ce; "Kai Bro Allah zai tsare wallahi shi ne daga ganin
mai aikinka ya fara rikici shi ya sa na ba ta shi." "Oho miki,"
ya yi hanyar fita. Mera ta kama hanyar kicin. Turus! Ta yi
tana kallon gashi dake zube a kafadar Amrah kamar 'yar India.
Mamaki ta kuma yi ganin Affan goye a bayanta yana baccі
hanka linshi kwance, a gefe kamshin girkin ke kuma tafiya da
imanin ta. Maman Affan Mera ta fada, "A'a Aunty kin fito?
Sannu da dawowa ki yi hakuri wallahi ban ji zuwanki ba, ba
komai amma me ake girkawa bro ne? Ni ma fa yau zan yi
masa kwadayi. Amrah ta jawo fulas guda biyu a gefe, "Ga shi
Aunty da ma na zuba wa yarona Affan na san zai iya ci." Mera
ta shigo kicin din, ai ko har da Mommynsa wannan za mu ci ya
ishe mu, kai na yi godiya sosai." "Maman Affan ba komai."
Aunty Maman Affan ta ce; "Wannan suma sai ka ce daga
Hindu kike," Amrah ta rufe fuska, "Wace ni Aunty? Hanyar
Hindu ma ban san ta ba, in tambaye ki Maman Affan." Mera ta
ce; "E tambaye ni." "Aunty mene ne yarenki?" Amrah ta yi far
da ido fullo-fullo shuwa-shuwa." No wonder," Mera ta ce,
יי" Ki ce daga tsatson kyau kike masha'Allah Allah ya yi halitta.'
Amrah ta kuma rufe ido, "Aunty ni kunya nake ji." "A'a
gaskiya ce dole in fada," ta katse ta. "Aunty mu je in kai miki
Affan side din Mommy kada kaya su yi miki yawa ga abinci."
"To na yi godiya sosai Maman Affan." Amrah ta ce" "Aunty
kina sa ni jin kunya kamarki ki ce min hakan Aunty, ki ce
Amrah don Allah," 'ta fada tana langwaße kai. Mera ta kuma
washe baki, "Sunan naki mai kyau ne na ji dadin haduwa da
ke Maman Affan, kuma ni ba zan ce Amrah ba daga yau
sunanki a guna Maman Affan." Fulas din duka biyu ta dauka
tana gaba Amrah na biye da ita da goyon Affan. A hakan suka
shiga babban falon Mommy. Ba kowa a falon sai Mommy
dake kwance tana kallon tashar Saudi Arabia. Da sallama suka
shigo. Mommy ta mike, "Sannu da aiki Amratu ga aiki ga
goyo." "Ba komai Mommy." Mera ta ce; "Mommy kin san boy"
na ganin ta ya mika mata hannu da na ki ba da shi saboda na
61
AKWAI KURA
ga tana aiki shi ne ta dage sai da na ba ta." Mommy ta ce;
"Ayya ai Amratu akwai hankali ina jin dadin aikinta sosai." Ita
dai Amrah ba ta ce komai ba durwusawa ta yi har kasa ta gai
da Mommy tare da sunce goyon Affan ta shinfida shi a kan
kujera. Sosai Mommy ta yi mamakin ganin tulin gashin dake
bayan Amrah har sai da ta kasa hakuri ta ce; "Amratu zo nan
ina yaba hankalinki, me ya hada ki da gashin doki?" Amrah ta
yi narai-narai da ido kamar za ta yi kuka, "Mommy ban sa
gashin doki ba," ta cire hular kanta tuni sauran wadanda suka
boye a hular suka zubo, "Kalli Mommy ban yi kari ba." Daga
Mommy har Mera kallon mamaki suke yi wa gashin Amrah
don ko Mommyn da take Baturiya gashin Amrah ya fi nata
tsawo ga cika. "Mommy ina son ta wallahi don Allah ki ba ni
ita in tafi da ita Lagos." "A'a ba zan ba ki ba tana tare da ni
mutu-ka-raba takalmin kaza,” in ji Mommy. Dariya suka yi
dukkansu kafin Amrah ta yi musu sallama ta koma bakin
aikinta.
***
Meena 'ya ce a gun Alhaji Hamza domin Mamanta kanwa ce a
gunshi, uwarsu daya ubansu daya, akwai dafari akwai shakuwa
sosai tsakanin Saleem da Meena kasancewarta abokiyar
wasanshi ta musamma. Za su yi waya suna tsokanar juna duk
irin na abokan wasa amma daga baya sai Meena ta nuna ma
iyayensu soyayya suke da Saleem. Meena ta kamu da Kaunar
Saleem mai yawa a zuciyarta, shi ko Saleem kallo ba ta ishe
shi ba, tun da ya fahinci inda ta dosa shikenan ya fita harkarta
wasan ma ya daina da ita sai da 'yan uwanta maza, tuni ya
goge lambar tata a wayarshi in za ta kira sau dubu ba zai dauka
ba, daga karshe ma sai sanya number tata a black list. Meena
yarinya ce maras kunya mai girman kai na gaske saboda
kawunta na da kudi wato Daddyn Saleem kuma yana sake
musu sosai, ita da uwarta don har mota ya sayawa Meena mai
kyau ita ma kanwar tashi ya sai mata mota mai kyau, duk wasu
62
AKWAI KURA
bukatunsu in har sun fada zai dauki nauyin su. A girme Meena
za ta girmewa Amrah nesa ba kusa ba don ita
din ba yarinya ba ce, ta yi karatu har zuwa masters, a halin
yanzu tana aiki a gidan Radio Glop Fm Kano. Sau da yawa
weekend takan zo Kaduna gidan unkul din nata tare da kissa da
kisisina don ta dauke hankalin Saleem, sai dai ga Saleem kallo
ba ta ishe shi ba ban da gaisuwa ba ya yarda wani abu ya hada
su. Ummanta ta yi alkawarin ko Saleem ba ya son 'yarta
amma koda boka da Malam sai Meena ta auri Saleem. Da fari
Umman Meena Yayan nata ta yi wa maganar hada yaransu
aure sai ya ce da ita, in har yaran suna kaunar junansu zai fí
kowa murna, sai ta ce da shi Meena ta amince shi ma ya sa
Saleem ya amince. Alhaji Hamza ya yi dariya "Kada ki yi mata
dole don an daina wannan shirmen auren dolen, zan yi magana
da Saleem in ya amince." Ba don ta so ba ta ce, "To." Da
Alhaj Hamza ya kira dan nashi ya yi masa maganar auren
Meena a take Saleem ya ce bai amince ba shi ma Alhaji Hamza
ya sanar da kanwar tashi a bar maganar, Saleem ya ce bai
amince ba. Haba! Nan kanwar tashi ta hau sama tana masifa
daga karshe baram-baram suka rabu da yayan nata don ya ce
shi ba zai yi wa dansa namiji auren dole ba tun da shi ma
iyayenshi ba su yi masa auren dole ba. Hakan bai sa Meena ta
rabu da Saleem ba kullum tana hanyar boka da malaman
tsubbu ita da uwarta akan Saleem, abin da ba ta sani ba
Saleem tsaye yake kan addu'a, sam ba ya wasa da iba da duk
shagalarshi bai da wasa da hakkin Allah haka iyayenshi suna
yi masa addu'a sosai saboda hatsarin dake cikin aikinshi
wnnan ya sa koyaushe da zarar sun yi sihirinsu baya tasiri akan
Saleem da izinin Allah.
***
Sosai shakuwa ta shiga tsakanin Affan da Amrah, da zarar ta
zo aiki in har ta je gaida Mommy to fa Affan zai dafewa
63
AKWAI KURA
Amrah har sai ta dauke shi kuma ka'ida ne a gun Amrah in har
ta zo to fa sai ta fara gaida Mommy kafin ta je bangaren
Saleem, don fara aikinta a nan Affan zai dafe mata dole take
dauko shi su taho sashen Saleem. Tana aiki suna wasansu da
Affan, kun san an ce mai da wawa ne, tuni soyayyar Amrah ta
shiga zuciyar Mera, saboda kaunar danta da da take yi. Amrah
ta iya abinci sosai wannan dalilin ya sa kullum Mera ba ta cin
abincin kowa sai wanda Amrah ke shiryawa Saleem yayin da
Saleem.sau dubu za a yi girkin sam ba ya ci, falon Mommy
yake zuwa ya ci na Mommy. Abin da Saleem bai sani ba
abincin da Amrah ke yi shi Mommyn take sanya mai aikinta
zuwa ta jera akan dinning don ba za ta iya barin wannan abinci
mai dadi a yi asarar shi ba, ita kanta Mommyn ta san dadin
abincin sosai, hatta Daddy ya yi na'am da dadin girkin, sau da
yawa Saleem in ya ci girkin yakan yabawa Mommynshi kan
kokarinta na girki kasancewar ita ke yi wa mahaifinshi girki ba
ya cin na 'yan aiki, abin da ba su sani ba tun ranar da Mommy
ta ci girkin Amrah ta ji dadinshi tun ranar ta kudira a ranta duk
lokacin da ba ta jin aiki to fa Amrah za ta sa ta yi musu, sai
gashi Saleem ya ce ba zai sake cin girkin Amrah ba, a ranar ta
sanya mai aikinta ta canzawa Amrah timetable, na Saleem ta
ajiye nasu na gida tare da umurtar Amrah kan cewa a kara
girkin. Sarai ta san Saleem din, karshe ma ita zai dorawa
nauyin girkin nashi, ai ko sai ga shi yana cewa, zuwa cin girkin
nata ba tare da ya san wanda yake yin shi yake ci ba. Zahra
kanwar Saleem wato autan Mommy ta zo weekend sau biyu
bayan fara aikin Amrah a gidan sai dai ba su taba haduwa da
Amrah ba har sai zuwan Aunty Mera a nan da fari da ta ga
Amrah ta ji tana kaunar ta amma da ta ga inda Mommynta take
son Amrah hakan Aunty Mera ke son Amrah, tuni ta fara jin
haushin Amran wannan dalilin ya sa koyaushe suka hadu to fa
zagi ne da cin mutumci Zahra ke yi wa Amrah, ita ko Amrah
kallo bai ishe ta ba domin ta gano in ta ce fada za ta yi to fa
aikin da ya kawo ta gidan ba za ta aiwatar ba, shi ya sa ta aro
64
AKWAI KURA
hakurin da ba ta da ta shi ta sanyawa zuciyarta kafin adadinta
ya cika ta rantse daya bayan daya sai ta ci uban Zahra da duk
wanda ya ci mutumcinta wannan bashi ne sai ta biya.
***
Ran shi a bace tamkar an yi masa albishir da mutuwar
tsohuwarshi, huci yake yi yana masifa kamar wanda yake wa
masifar ya haife su, shegiya naira mai mai da tsoho yaro mai
mai da yaro babba, cikin karaji ya fara magana da murya sai ka
ce Bos, ba za ka ce matashin saurayin nan ba ne mai ji da naira
da izza ba, uwa uba ga kyau, "Hukuma ta yi kadan billahil
azim ba ta isa ba sun yi kadan su toshe mana hanyar cin abinci.
Wato ba su samu sa'a wancan karon ba da wadancan
ma'aikatan nasu ba, bai ankarar da su hatsarina ba shi ne suka
kuma turo wata. A wannan karon gunduwa-gunduwa zan yi da
dan aikensu sannan in tura musu gawar."
Ya kalli matashin dake gabansa a kalla matashin zai ba shi
shekara uku ya ci gaba da magana, "Duna yaushe ka fara
sanya wasa a cikin aikinka? Yaushe akayi hakan? Wato son
mata ba zai bari ka yi min aiki da kyau ba ko? Ta ya ya mace
za ta gagare ka? To wallahi na tabbatar da hadin bakinka kai
ma ba zan bar ka ba sai na yi daga-daga da kai," ya fada yana
zare ido. "Alhajin Allah ba za ka fadi ba sai a gadon baccinka
ka jima ka yi karko, ka ci dubu sai ceto, murucin kan dutse ba
ka fito ba sai da ka shirya babu wanda ya isa ya karya dokada
ka ya kwana lafiya, wallahi ta shammace ni ne, yarinyar da
alamar ita ma mace ce mai kamar maza ta bace mana bat! A
kan kwalta, maigida ka yi hakuri in kere na yawo zabo na
yawo za a hadu ne ai, Allah ya huci zuciyar Alhajin Allah,
Allah ya huci zuciyar maigida." "Dakata," ya daga masa
hannu yana huci, "sati daya tak na ba ka ka kawo min yarinyar
nan a raye ko a mace ba zan lamunci hakarsu ta cinma ruwaba
mazan ma ya suka kare balle mata lallai lallai ne a kawo min
65
AKWAI KURA
ita cikin sati guda." "Cau! Alhajin Allah an wuce gurin ka sa a
ranka ni Duna dan duniya na kawo maka yarinyar nan an gama
na rantse da sarkin dake busa numfashina sai na kawo ta
gabanka a mace ko a raye." Jin wannan magana ya sa
maigidan nasu ya dan saki fuska tare da murmushi, tuni
kyansa ya bayyana tare da kwarjininsa. "Duna na san za ka iya,
ka sani ranar da hakan ta faru akwai tukwici mai tsoka sai da
ranka ka tabbatar an yi abin cikin sirri, sannan ka ankare kada
a samu matsala ban yarda da matsala ba, matsala ba ta san ni
ba ni ban san ta ba." "An gama Maigida," ya kuma fada tare da
kada kada hannu alamun jinjina masa.
***
Da wuri ta gama aiki Karfe biyar daidai na yamma ta gama
shirin tafiya gida. Da sassarfa ta fara hawa saman benen
Mommy don yi mata bankwana saboda tana son ta biya Saloon
ta wanke gashinta, karo ta ji ta yi da wani abu har tana shirin
fadowa daga step na benen. Da sauri ta kama jikin karfen
benen, imagine kamshin shi ne ya ziyarci hancinta, ko ba a
fada mata ba ta san shi ne. Da sauri ta shiga nutsuwarta don
ganin da wa ta yi karo, "Am sorry," ta ce da shi. Yau 'yan
mutumcin suna kusa kala bai ce mata ba ya raba gefenta ya
wuce. 'Yau na sha da kyar,' ta fada a ranta tare da girgiza
kafada, ta haura sauran step din don shiga babban falon
Mommy. Zahra ke zaune jikin computer tana browsing. Da
sallama ta shigo dakin amma kamar da iska take magana.
Mommy dake cikin dakinta tana hutawa ta ji muryar Amrah na
kira, "Mommy zan wuce." Ta fito daga dakin "Maman Affan
wato saboda Affan sun je Kano kwana biyu shi ne aka daina yi
mana doguwar hira ko? To ai yau suna hanya, dan naki zai
kawo min ke hira har dakina." Amrah ta washe baki, "Ai ban
sani ba Mommy da na yi wa yarona shiri na musamman, ina
kewanshi Mommy ban da ina son zuwa wanke kaina da na jira
na tarbi dan gidana." Mommy ta yi dariya, "Ai ko shi ma yana
66
AKWAI KURA
kewar ki don jiya da muka yi video call yana ta kiriniya yana
kiran Maman Affan." Amrah ta yi dariya don tuno sunan da shi Affan din yake gaya mata; Maman Affan shi ma yake fada
kamar yadda ya ji Mommyn da Aunty ke fada, shi ya sa shi ma
a cikin gwalantinsa na yara har ya iya fadar Maman Affan. Mommy ta katse mata tunanin “Ayya ga shi cikin satin nan suke son wucewa Lagos, lallai Affan zai yi kewar Mamansa." Amrah ta kada kai alamar jimami, "Mommy ni ma zan yi kewar yarona." Zahra dake jin hirarsu a gefe ta ja dogon tsaki, "Kalan dangi kawai mutum babu dangin iya babu na Baba
amma yana shigewa uwata saboda kwadayin abin duniya." Kallo duka suka bi ta da shi. Mommy ta ce; “Ai Amrahtu 'yar
uwata ce tun da musulumci ya hada mu kuma ni na dauki
Amratu kamar 'yar da na haifa a cikina." "Kai Mommy,"
Zahra ta hau buga kafa, "Allah ya sauwake ki haifo wannan a
cikinki Mommy me za a yi da talaka? Ai tsakaninmu da talaka
sai dai a taimake shi kamar yadda ita ma taimakon ne ya hada
mu. Mommy ta sha mur, " Fatima zan saba miki wacce irin
magana ce ta marasa hankali eye? Yaushe kika dawo hakan ko
universty ce ta mai da dabi'arki hakan? To ki kiyaye ni zan
saba miki sosai, in ban da rashin hankali da mai kudi da talaka
ai duk daya suke a gurin Allah, wanda ya fi tsoron Allah shi ne
sama da wani, ki shiga hankalinki zan sa son ya tattaka min ke,
kin san shi sarai." Zahra ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 12