ba ta ga Granny ba cikin sauri ta gama
daura nikab ta dauki jakar da take sanya kayanta na canji in za
ta wuce aiki ta raba a kafadarta ta fita. Granny ta sauke ajiyar
zuciya bayan ta gane Amrah ce ba barayi ba. Da sauri ta koma dakinta, wayarta ta dauka ta ta danna alamomin da Amrah ta
nuna mata kan wayar na gane number wanda take son kira, ta
yi bugu daya ya dauka, don daga sallah ya fito cikin damuwa
ta gaya masa abin da idonta ya ga Amrah na yi. Alhaji Usman
ya yi dariya, "Kada ki damu Iya ina sane da duk abin da take yi
kuma na tabbatar miki hanyar dat a dauka hanya ce mai bullewa, shi ya sa nake tura mata kudi sosai cikin account nata
don tana buwatar su. Iya ki kwantar da Hankalinki kada ma ki
nuna mata kin gane, ki sanya mata ido kuma ki ci gaba da yi
mata addu'ar nasara babu shige da ficen da take yi wanda ban
sani ba. Amrah 'yata ce ba zan taba bari ta fada halaka ba,
aikinta na kyau kuma na tafiya daidai ki kara hakuri Iya."
"To to ai da na dauka 'yar fashi da makami ta dawo shi ya sa
na kira da Asubahin nan." Abban Amlah ya yi dariya, "Iya zan shigo gidan an jima, ki dai kwantar da hankalinki."
Ita ko Amrah da sauri ta dale mashin na Anas ya ja suka bar kofar gidan. ranar Anas ya fara koya mata mashin. Cikin
kwana uku Amrah ta kware a koyon mashin har tana iya kawo
su in da za su rabu tuni Amrah ta kware gun koyon harbi da
mashin har Anas ya sallame ta yanzu babu maganar fita koyo a
gunsu sai dai soyayyarsu da suk esha ta waya da ta gida don kusan kullum.in ta dawo daga aiki bayan sallar Isha'i Anas ya kan zo hira. Iya ba karamin jin dadi ta yi ba ganin Amrah ta kwantar da hankalinta sun daidaita kansu da Anas don ranta na kaunar yaron musamma da ta san shi din mutumin kirki ne iyayensa ma haka, haka Zahra ba karamin dadi ta ji ba da ta ga
79
AKWAI KURA
soyayya sai karfi ya sake kulluwa tsakanin bestyn nata da
Yayanta. Wannan ke nan.
***
Alhamdulillah yau kwanan Saleem bakwai cur a sibiti, jiki
yana samun sauwi sosai, kowanne lokaci Doctor zai iya ba shi
sallama. Kasancewar jikin ya fara sauki sosai shi ya sa
security suka dan yi sauki a gurinsa sai dai 'yan uwa da abokan
arziki kullum suna hanyar Kaduna duba Saleem, 'yan Kano ma
ba a bar su a baya ba sun yi mota guda katuwa sun zo gai da
Saleem cikinsu har da Meenah da Mamanta. A ranar sauran
'yan uwa suka koma, Meena kadai da Mamanta suka tsaya
kwana biyu kafin su koma. A bangaren Maman Meena asiri ne
kala-kala ta karbo daga gurin bokanta wasu a cikin abinci za a
sa wasu ko binnewa aka ce su yi a gun da Saleem zai taka da
wannan kudirin na son aiwatar da aikin bokan ya sa suka ki
bin abokan tafiyar tasu. Zaune suke kan kafet da aka shimfida
a waje saboda masu zuwa duba mara lafiyan. A cikin dakin
kuwa Saleem zaune a bakin gado shi da abokanshi Maheer da
Ahmad tare da security daya dake bakin kofa Maheer na zaune
daf da kafar Saleem yana yi masa magana cikin rada da alamar
ba ya so Ahmad ya ji tambayar da Maheer ke yi masa shi ya sa
ya kara matsowa kusa da shi, shi ko Saleem ya lula duniyar
tunani tun da abin ya faru kullum yake cikin yinsa infact ma
har mafarkin abin ya yi. Saleem ya yi tsai da hankalinshi yana
tuno kyawun gashinta tare da kyawun fatarta duk da bai gan ta
complete ba amma ba zai manta da laushin hannunta da ya rike
ba. Bugu da kari ba zai manta da original gashi da ya gan shi
kwance a gadon bayanta ba. Saleem.ya yi rayuwa cikin
Turawa ya san original gashi ya san attachment hakan ya sa
original fari ya san farin bleching, ido ya lumshe yana tuno
dadin laushin hannunta, 'Who are you?' ya yi tambayar kamar
tana ganin shi. Saleem ya lula duniyar tunani ya manta da
wadanda suke tare da shi, cikin tunaninshi ganin hoton komai
80
AKWAI KURA
yake a gabanshi kamar yanzu abin yake faruwa, 'uhun uhum
ko ma wace ce ke na yafe miki,' ya fada cikin murya mai sanyi.
Maheer dake kusa da shi duk maganar zucin da yake yi babu
kalmar da bai ji ba, cikin kwarewa akan soyayya, tuni ya ramfo
zancen abokin nashi kuma maigidanshi. Maheer ya dan
dungure mishi kafa, "Jarumi how far?" ya fada yana mai
daga masa gira. Saleem ya yatsina fuska cikin kasala ya ce da
shi, "Normal." Ahmad dake can gefe a zatonshi magana
Saleem din yake yi da Maheer shi ne suke boye masa don kada
ya ji, tuni ya ji ranshi ya baci haushi da takaicin Saleem da
Maheer ya kama shi, cikin siyasa irin tashi ya danne fushinshi,
"Guys bari in amsa waya." Maheer ne ya amsa, "No problem
abokina." Fitar Ahmad ke da wuya Maheer ya yi gyaran
murya, 'Wace ce ita?" Saleem.ya kalle shi da dara-daran
idanunshi masu kyau, "Wa ke nan?" Shi ma ya yi mishi
tambaya. Maheer ya ce da shi, "Wadda ta hana maka zuciya
sakat wadda ka yafe mata laifin nata." Saleem ya zare ido don
mamakin maganarshi ta zuci ya fito fili bai da masaniya. Gira
maheer ya kuma dagawa alamun ina sauraronka.
***
A badini gaskiya Maheer makusanci ne a gun Saleem amma
su kadai suka bar wa kansu sani amma a zahiri in ka ga
Saleem da Ahmad za ka yi zaton sun fi amintuwa, amma ga Saleem ya bar wa kansa wannan sirrin, sau da yawa yakan yi shearing secret nashi shi da Maheeer kuma Maheer din na ba
shi shawara wadda in ya bi yake ganin dacewarta. "Ina son ta duk da ita ce silar kawo ni gadon Doctor." Cikin murmushi
Maheer ya dafa kafadarsa, "tabbatarwa kawai nake son ji
amma maganaar soyayya na gan ta a kwayar idonka, but wace
ce iţa?" "I don't know her," ya kuma fada cikin murya mai sanyi da ta yi kasa sosai. wayarshi dake gefenshi ya dauka, masssge ya shiga cikin rubutunshi mai tsari, komai da ya faru tsakaninsu ya rubuta ya yi send wayar Maheer. Sannan ya yi
81
AKWAI KURA
delete na wayarshi. Karar sako ya ji ya shigo wayar tasa
kamar bai san komai ba ya dauki wayar ya bude sakon, delete
ya yi bayan ya gama karantawa kamar babu abin da yafaru
dukkansu kowa ya yi shiru, "Time prayer ya yi warfe hudu,
mu je mu yi sallah." Saleem.ya ce da Maheer tare suka fita
cikin dakin har yanzu hannun Saleem, nade da bandeji.
Jikinshi kuwa bakar jallabiya ce da ta kara ma hasken fatarshi
haske tare da sajewa kamar Balarabe. A waje suka hadu da
Ahmad yana waya yana ganin su ya washe baki, "Madalla
abokina gate well soon."
***
"Gaskiya Maman Affan zan yi fushi dake saboda Allah Bro
satinshi guda a kwance asibiti amma ba ki taßa tunanin zuwa
ki duba shi ba?" Gaskiya yau kam za mu yi fada in ba ki je ba
don ina zaton any moment yau zai samu sallama, kin ga yau
Juma'a yadda Bro ya takura ya dawo gida na san ba zai bari
har Monday ba na san shi sarai in ya nace akan abu." Amrah
ta rufe fuska, "Aunty ki yi hakuri tsoro nake kada na je ya yi
min masifa." Mera ta jawo ta jikinta cikin sigar lallashi, "In
haka ne kina da gaskiya amma ki daure ki je, ai gasuwar maras
lafiya akwai lada sosai ko da ya yi miki masifa kin samu
ladanshi bare ma na san ba zai yi mikiba shi da ba shi da lafiya
ai babu maganar masifa." "To Aunty zan je, wanne asibiti ne?
kuma wanne daki zan tambaya?" "A'a tun da kin gama girkin
rana bari mu tafi tare in ya so sai direba ya dawo dake da wuri
ki dora na dare, maza je ki cire wannan kayan na jikinki."
"Aunty ai ba ni da wasu kaya a nan gidan." "Oh na manta
amma mu je Zahra ta ba ki nata ki sa ai na san za su yi miki tun
da girman naku kusan daya ne. ne." "Aunty," Amrah ta fada tana
murda hannu, "ki bar shi." "A'a dole za ki canza kaya don
kada mu je a raina min ke," Mera ta kuma fada. "To Aunty ki
ba ni katon hijab din na da na ga kina sallah zai rufe min ko
82
AKWAI KURA
ina." "Kin fison hakan?" Amrah ta gyada kai. 'To ina zuwa.' Daki ta koma kafin ta dawo hannunta dauke da sabon hijabi fil
a cikin ledarshi, "Ungo sanya wannan na sanya a dinko min su
ne saboda ya min kyau sosai kuma na ga design nasu su ake ya
yi a nan Arewa, kin san mu Lagos dake ba amfani aka cika yi
da shi ba ba mu cika samun masu kyau a can ba shi ya sa in na
zo Arewa nake sayen su da dan dama saboda ina son su sosai."
Amrah ta karba tare da godiya, ta ware shi a leda ta sanya. Kai
tabarkallah! masha Allah Mera ta fada kin yi kyau sosai
Maman Affan kamar don ke aka yi su, maza mu je kada mu
makara bari in dauko yaronki a gun Mommy."
Mera na tukin mota Amrah na zaune a gefenta Affan zaune
akan cinyarta suna tafiya suna hira kamar wasu aminai har
suka iso asibitin. Meenah da Mamanta tare da wasu baki biyi
da suka zo gai da Saleem na zaune kan darduma.suna shan iska
Mera da Amra suka karaso, hark kasa Mera ta tsuguna ta gai
da Goggon nata ita ma Amrah har kasan ta tsuguna ta gai da
Maman Meena, ta amsa fuska ba yabo babu fallasa ita ko
Meena tun fitowarsu a mota da ta kyalla ido ta ga Amrah take
bin ta da harara, Amrah ta gani amma ta kauda kai don gai da
maras lafiya ta zo ba za ta so wani rikici ya hada su ba. Tare
suka shiga dakin da Saleem.yake kwance har da Meena da
Mamanta. Saleem da shigowarsa ke nan daga masallaci, daya bayan daya suka kuma yi masa ya ya jiki, ya amsa cikin sakin
fuska. Amrah da tun shigowarsu dakin ta nemi dungu ta бoye gaisuwar ma a cikin rububi ta gai da shi ya amsa mata ba tare
da ya gane ko wace ce ba. Affan dake hannunta shi ne ya fara
mikawa hannu, "Unkul," yake fada cikin gwalantunsa na yara.
Saleem ya ji muryar Affan, "Sister ba ni yarona," ya fadawa Mera. Kir! Karar kida mai dadi ya kaure dakin. Ahmad ya
ciro waya a gaban aljihunshi, "Excuse me abokina," ya ce da
Saleem. Kai Saleem.ya daga masa da alamar ya fi gane
maganar kurame. Ahmad ya ratsa gefen Mera ya fita waje don
83
AKWAI KURA
ansa waya, "Ba za ki ba shi yaron nashi ba ne? Ai ko Mera da
ta haifeshi ba za ta hana Saleem karfar yaron nan ba bare ke
'yar aiki, son come here," Saleem ya fada, Amrah ta sauke
Affan. Da gudu ya je gurin unkul din nashi. Meena ba ta
daddara ba ta ce; "Kin wani tsaya mana nan sai ki yi waje nan 'yan gida ne ba 'yan aiki ba." Amrah ta kalle ta ta girgiza kai ba ta ce komai ba. Saleem da ya ji shiru ya ratsa dakin ga zatonshi ta fita ya dago kanshi. Cikin sa'a suka kalli juna
Amrah ba ta ce komai ba ta fice daga dakin. A karo na farko da
Saleem tausayinta ya darsu a zuciyarsa bai ce kala ba ya ci gaba da wasa ma Affan. Mera ce ita ma ta fita daga dakin don
ta je ta rarrashi Amrah, sanin halin kanwar babansu shi ya sa
duk wainar da aka toya ba ta sanya baki ba yanzu sai ta ce ta bi bayan bare. Shi ko Maheer bai san me ake ciki ba hankalinshi
nakan wayarshi yana chat da Zahra. Kwata-kwata bai ma san
tare Mera ta zo da bakuwa ba. Fitar Amrah daga dakin direct
hanyr motarsu ta nufa tana zuwa cikin sa'a ta ji ta a bude, tuni
ta fada kan kujera tana sauke numfashin 6acin rai. 'Don
uwarki an fada miki ni banza ce kamar yadda kullum kike
zagi na tsinanniya ki kiyayi ranar da za mu yi karon batta
dake,' ita kadai take maganar a fili ajiyar zuciya ta ci gaba da
saukewa, waya yake yi yana karkada wayar kafin ya mai da ta
kunnenshi da alamar network ke ba shi matsala, hakan ya sa
yake tafiya yana neman network, a daidai motar Mera ya fara
jin maganar garau na wanda yake wayar da shi alamu sun nuna
masa nan gurin akwai enough network. "Ina nan cikin asibitin
ba zan fita ba har sai na tabbatr an ba shi sallama ku zamo
ready zan yi kokari in ga mun tafi gidan nasu tare..."
"...yauwa zan yi maka sakon hanyar da muka bi..." "...E ku
harbe shi, hakan na ce ku harbe shi, ku tabbatar kun harbe shi a
inda ba zai yi rai ba a yanzu na gama yanke shawarar gara ya
bar duniya in huta shi ma dayan in ya yi wasa zan gama da shi
ba da jimawa ba. Da sauri ya kashe wayar tare da duba gabas
da kudu don tabbatar da babu wanda ya gan shi.
84
***
AKWAI KURA
A hankali ta sauke numfashinta wanda tun da ta fara jin maganar mutumin ta dauke shi tare da rufe bakinta da karfi
kada ya ji ta. Cikin sanda ta fito daga motar ido ta fara rabawa
dan neman wata hanyar bullewa don tsoron kada in ta bi
wadda suka shigo tsautsayi ya sa ya gan ta a halin yanzu ita kanta rayuwarta na cikin kwale-kwale don matukar ya san an ji
wayar tashi har ita din ma ba za ta tsira ba. Cikin bishiyoyin dake gurin parkinh din ta bi, ita kanta ba ta san inda za ta yi ta fita cikin asibitin ba. Wata mata ta gani tana shanya kayan
wanki da sauri ta karasa gurinta bayan ta yi mata sannu kafin
ta tambaye ta ko akwai wata kofar fita ban da waccan,
"Akwai," ta ce mata sannan ta fara yi mata kwatance. Da
sauri-sauri gudu-gudu ta bar wajen ta tunkari hanyar fitar, ta
kai minti biyar tsaye kan hanya ba ta samu abin hawa ba daga karshe ta fara takawa da kafarta, damuwarta daya wanne mataki za ta dauka kan wannan magana da ta ji? 'No,' ta fada
a ranta, 'ba zan taba bari ya mutu ba domin ba zan iya ganin
tashin hankalin da Mommy za ta shiga ba.' Mommy ta nuna mata kauna ko in ce tana kan nuna mata kauna, ban da Mommy iyakarta ba za ta so aikinta ya samu matsala ba ta riga ta ci alwashin tabbatarwa Abban Amlah ita din mace ce mai
kamar maza. Ayya Mommy kina nan nan da danki duniya
kuma tana son raba ku,' har yau ba za ta manta da tsananin tashin hankalin da Mommy ta shiga ba ranar da Saleem ya
samu matsala, ta yi imanin in har Saleem ya mutu ba ta cire kokonton Mommy ba za ta yi hauka ba saboda damuwa. Hankalin Amrah ya tashi ta rasa samun mafita, da sauri ta danna kiran number nashi ringinh uku ya dauka, "Beb kamar kin san ke na ke son kira, kashe wayar bari in kira ki," ya fada
yana shirin kashewa. Amrah ta katse shi cikin damuwa, "Wait Dear," cikin sauri ta sanar da shi abin da take so "Ok no problem Beb." Da sauri ta katse kiran saboda hango dan
85
AKWAI KURA
okada da ta yi zai wuce, hannu ta sa ta tsayar da mashin din,
ba ta tsaya ciniki ba ta hau, sai da suka fara tafiya ta fada masa
inda zai kai ta. Tafiyar minti sha bakwai ta kawo su kofar
gidansu, "Malam jira ni, bari in kawo maka kudinka," ba ta
jira amsarshi ba ta fada cikin gidan nasu. Shiru kake ji da
alamar Granny tana baccin rana. Amrah ta shiga daki da sauri
ta daukowa mai mashin kudinsa. Bayan ta dawo daga kai
masa kudin ta shiga sintiri a dakin ta yi nan ta dawo nan tana
neman mafita. Wayarta ce ta kuma kara alamar an turo sako.
Amma ba ta kula ba, murmushi ne ya bayyana a kan fuskarta
don samun mafita da ta yi. Da sauri ta bude Doctoress cikin
minti shida ta gama tsukewa a cikin riga da wando na jins.
Jakarta ta bude ta debi kudi ta kuma sanyawa cikin rigarta.
Amrah ta sha zanzaro kamar wata jami'ar tsar,o takalmi mai
igiya ta daura irin nata na gayu wanda duk farin kafarta a waje
suke, illa igiyoyin da ta dinga daurewa step by step suka jeru a
saman tsingililin kafarta kamar yadda wayayyun Turawa ke
sawa saboda takalmin na gayu ne sosai ya fi kyau da wando,
"Mitsw," ta ja tsaki, "Anas zai fata min lokaci." Da sauri ta
dauko wayarta don sake kiran shi a nan ne ta ga sakon Anas
yana sanar da ita dan aike na kofar gida. Nikabi kawai ta
dauka ta sanya kafin ta dauko katon hijabi ta rufe Doctoress
nata sai dai wandon bai rufe duka ba, kafar wandon na waje
wanda farin kafarta ya kara mata kyau cikin takalmin. Amrah
ta daga katifarta ta ciro bindiga sai da ta tabbatar ta gama
sanya harsashi ta zamo ready sannan ta sanya kai waje ko
kofar ba ta tsaya rufewa ba tun da Granny na gida. A waje ta
hadu da dan aiken Anas ya durkusa har kasa ya gaishe ta
sannan ya mika mata key na mashin, “Ga shi inji oga kuma ya
ce ki bude bayan but akwai sako," Amrah ta karba ta yi masa
godiya sannan ta mika mishi naira dubi biyu, "Ka yi na
mashin ka koma," "Na gode Hajiya," ya kuma dan russuna ya
karba da sauri ya ba ta mashin din ta yi masa giya a halin
yanzu babu lokaci mai yawa ta sanya a ranta tare da tsoron
86
AKWAI KURA
kada ta yi delay a samu matsala ba za ta yafewa kanta ba.
Matasan unguwa da kallo suka bi ta, wasu na cewa ta burge su
wasu na zagin ta. Amrah dai keyarta ta yi nisa ba ta ma san
suna yi ba.
**
Amrah ta zaga hanya biyu da take tunanin su ne za su bi
saboda su ne hanyar ke da shiru babu hayaniya amma ba ta gan
su ba, a lokacin hankalinta ya gama tashi tuni ranta ya kuma
dugunzuma da 6acin rai ganin har ta kure duka hanyoyi ukun
ba ta gan su ba ya sa ta fara dawowa in da ta bari, bayan ta
kure shi ta hau daya hanyar don dawowa inda zai kuma sada ta
da asibitin. Abin mamaki hanyar shiru kamar an share babu
kowa, zafin rana ya boye kowa hatta checking point da ta zo
wucewa 'yan sanda ne biyu a gefen hanyar zaune a wata kasan
fulawa suna dan shan iska. Da gudu ta zo ta wuce gabansu ba
ta saurari izinin wucewa ba kamar yadda suke wuce su da
tafiyar minti sha biyu kamar a mafarki ta fara ganin motocinsu
daga nesa, in har idonta bai yi mata karya ba mutane ne
kwance akan gefen hanya. Saleem ta hango yana turjewa shi
da Maheer yayin da bindiga shida ke kansu ana jiran ta kwana
da alamar taurin kan Saleem shirye yake da kokawa da su duk
da kowa hannushi rike da bindiga. Amrah ta ji karfin guiwa ta
zo mata tare da wata jarumta. Da gudu ta karawa mashin din
wuta babu tsoro ko shakka ko kadan a ranta, gabadaya suka juyo gare ta, 6arayin don daukar mataki kafin ta iso gare su, abin mamaki sai ga ta a kasa ta fado daga kan mashin hijabinta ya ja ta. Da sauri ta cire kan hijabin a jikinta don gudun kada ya ba ta matsala, gashinta wanda ya sha gyara ya zubo a kafadunta ba ka ganin komai sai idonta dake foye cikin nikabi. hannunta duka biyu ta sanya cikin aljihunta ta ciro bindiga ji kake tas! Ta ta tas! Ta harba bindiga sama. Ba ta yi
wata-wata ba ta nunawa biyu daga cikinsu bindiga da alamun
su ne manya. cikin kakkausar murya ta fara Magana, "Hanya
87
AKWAI KURA
kadai za ku ba su su wuce in ko kun ki sai dai mu yi mutuwar
kasko da ku." Daga Saleem har Maheer cike da al'ajabi suke
kallon ta. Mace mai kamar maza duk suka fada a ransu.
Amrah ta kuma magana, "A shirye nake da na mutu kan
wadannan mutane," ta daga bindiga alamun harbawa, manyan
biyu da sauri Babban cikin su ya daga mata hannu alamun
saranda tare da daga muryarsa mai kaushi, "Guys ku ankare,"
ganin bindigar hannunta duka biyu sun fi nasu bala"i da gudu
suka juya don komawa ta inda suka fito. Saleem da Maheer
suka yi kukan kura suka rike mutum biyu cikin wadanda suka
sanya musu bindiga, tuni tasu jarumtar ta motsa, bindigar suka
fara kokarin kwacewa yayin da kowa cikinsu yake kokarin
sakin bindigar ya tashi ma dan uwanshi, su ko sauran hudun
tuni sun arce sun bar 'yan uwansu. Amrah ganin kamar kanda
suke kokawa da Saleem zai kai shi kasa saboda ciwon hannun
Saleem ya sa ya saita bindiga daidai kafafuwan duka biyun, ji
kake tas! Tas! Ta harbi kafafunsu, a tare suka kurma wata
kara mai firgitarwa. Da karar barayin da karar bindigar su ne
suka jawo hankulan 'yan sandan dake nesa da gurin da kuma
tsirarun gidajen mutanen dake kusa da gurin suka ankare
akwai damuwa, da sauri 'yan sandan na kusa da na nesa suka
tunkaro hanyar don ba da taimakon gaggawa zuwa inda suka ji
karar harbin. Amrah ta juya da sauri ta dale mashin dinta dake
gefe, farin kafarta ta saukar kasa ta dauko hijabinta da shi
kafin ta kara wuta wa mashin din cikin second uku ta баce a
gurin bat!
***
3
A sukwane take gudu ta matse giyar mashin burinta daya ta isa
kafin su bar asibitin. Cikin mintina tara ta iso asibitin, gate din
baya wadda ta fita dazu ta nan ta shiga. Security dake gate din
ba su da yawa kamar na bayą tana zuwa ta daga nikabinta.
Wannan dalilin ya sa ba ta sanya mask ba don gudun kada
jami'an tsaro su zarge ta, cikin turancinta mai dadi ta gai da
88
AKWAI KURA
jami'an tsaron, ai ko tuni ta cika musu ido ganin kyakkyawar
fuskarta suka ba ta katin wucewa tare da ba ta hanya "No oga
nan zan bar mashin dina, yanzu zan gai da maras lafiya in
fita," kun san maza da son mata nan da nan suka washe baki,
"Ba damuwa Hajiya a fito lafiya." Nikabin ta sauke ta wuce
cikin asibitin da sauri kasancewar fuskarta na rufe ya sa ta yi
hanyar dakin da Saleem ke kwance, "An sallame su," daya
daga cikin security ya fada mata. Cikin rudewa Amrah ta ce;
"Yaushe?" "Hajiya ga su can za su fita," ya nuna mata gate.
Da sauri ta bi motar da kallo, motoci uku ne a jere, biyun ta
gane motar Aunty Mera da ta Daddy, kasancewar motocin
gidan na da yawa ba za ta tantance wacce ce dayar ba. Da sauri
ta yi wa security din sallama. Cikin sauri sosai har tana
hadawa da gudu ta dawo gate din, "Na gode," ta ce da su
sannan ta mika musu kudi a dunkule da ta ciro cikin aljihun
wandonta. Haba nan da nan suka fara yi mata godiya, Amrah
ba ta saurari godiyarsu ba ta bar gurin a dari da sittin. Ba ta san
hanyar da suka bi ba kanta ya dauki caji ta rasa ta inda za ta bi
har ta ciro waya za ta kira Mera sai zuciyarta ta gargade ta da
kada ta yi hakan, da sauri ta bi hanyar dake da karancin abin
hawa ga mafi zatonta nan hanyar suka bi, don matukar suka bi
babbar hanya ta san hakar mugayen ba zai cinma ruwa ba. Kir!
Motar ta ci burki, tus! Tus! Tayoyin motocin biyu suka fashe.
Da sauri Maheer ya ci burki ya ja baya cikin ikon Allah motar
dake ciki kadai ba ta fashe ba, kamar kiftawar ido suka fito
daga maboyarsu. Jibga-jibgan mutane ne sun kai shida, hannun
kowa rike da bindiga. Da sauri suka kewaye motocin duka uku
cikin murya mai karfi aka ce da su, "Kada kowa ya motsa in
wani ya motsa zan aika shi lahira, kowa ya kwanta." Mommy
dake motar Daddy tuni ita da Daddy a rude suka fito daga
motar, suna fita suka kwanta a kasa, Mera wadda tsurewa ya sa
ta fitsari a jikinta iyakar rayuwarta ba ta taba ganin tashin
hankali irin na yau ba. Meena da Mamanta sai kuka suke yi
suna fadar sun shiga uku, su ma tuni sun kwanta a kasa.
89
AKWAI KURA
Saleem da Maheer suna zaune gaban motar, Maheer da Ahmad
na baya zaune shi da Affan akan cinyarshi da sauri ya sauke
Affan ya fito shi ma ya kwanta. Saleem da Mahcer babu
wanda ya yi yunkurin fita daga cikinsu, "Jarumi ya fita mana
Kananan 'yan iska," ya fada da ido ya tambaya Maheer ko
akwai bindiga a jikinshi. Maheer ya yi masa alama da babu
"Wato ku hamshakai ba za ku fito ba ko? Na rantse da sarkin
da ke busa numfashina zan sa bindiga in harbe kwakwalwarku.
"Son," Mommy ta fada tana kwance, "don Allah ka taimake ni
ka fito, don Allah kada ku taba min da ko me kuke so zan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 12