Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels AKWALKURAPRINCESS SAYYADA TAHEER (Mrs FaisalZakaril AKWAI KURA MABUDI adam Amrah wannan hotunan da kike gani su "M ne wadanda aiki ya zo kansu, ga sauran takardu tare da bayanai akan zargin da ake yi musu na baki six months kacal! Ki fito mana da hujjar tabba tar da laifinsu ko rashinsa kafin in sallame ki da takardar shaidar IT dinki. Aikin naki ne ke kadai sai dai kofa a bude take duk lokacin da kike bukatar taimakonmu. Daga karshe ina gargadin ki da ki bi abin a hankali!" Bai saurari amsarta ba ya yi mata alama da hannu, "fice min daga office." Amrah ta sauke gwauron numfashi tare da tarkata takardun tare da hotunan ta fice daga office din. Masu keke napep sun kai biyar suna tsayawa a gabanta. "Hajiya tafiya ne?" Amma ko daya Amrah ba ta san ma suna yi ba, gabadaya hankalinta ba ya tare da su ko kaďan. Tunaninta da zuciyarta sun yi nisa wajen barin jikinta, kunnenta ba ya jin komai sai 5 AKWAI KURA kalmar six months kacal na ba ki ki fito min da hujja kafin in ba ki takardar shaidar IT dinki. Gabadaya kalma daya take maimaitawa a wane dalili ni ba ma'akaciyar bincike ba amma za a ba ni aikin da zan iya rasa rayuwata? For what reason? Ta sake maimaitawa da karfi ta furzar da hucin bacin rai daga bakinta. Yau na tabba tar uban su Amla kashe ni yake son yi kwa nana bai kare ba. "Tsinanne!" ta furta da karfi tamkar ta zare. "Hajiya tafiya ne?" mai keke napep dan ana ce da yake ta bin ta ba ta sani bay a maimaita maganar da ya yi mata a karo na babu adadi shi ne ya dawo da ita cikin hankalinta. Amrah ta hadiye busasshen miyau ta ce; "Oya! Mando za ka kai ni dai-dai Neco Junction." "Kudinki dari biyar Hajiya." "Muje kawai," ita ce amsar da ta iya ba shi. *** Da gudu ta shigo gidan tana kwala kira, "Granny! Granny! Fito yau an ba ni takardar ajalina kafin kwa nana ya kare, to billahil'azim ubansu Amla ya taro match domin kuwa akwai kura. Tabbas dole in shirya 'yan wasa kafin ranar buga final." Tsohuwar ta kama baki, "Oh! Ni Hafsatu yau kuma me ya hada ku da baban naku Amrah?" Turo baki ta yi ta ce, "Ni ubana yana Aljanna Insha'Allah, wannan kam har aba da ba zai haife ni ba Granny ki duba dan mahaukaciya wai ni ce zan kamo masa criminals.' 6 AKWAI KURA Tsohuwar ta kama baki ta maimaita kalmar, "Kirimino! Me wannan kalmar take nufi kuma 'yar nan?" Amrah ta fashe da kukan shagwaba, "Haba Granny yaushe za ki waye ne? Criminals fa na ce miki ba Kirimino ba, da Hausa ana nufin masu laifi ke nan fa Granny, Ni wallahi so nake yi ma in yi sauri in gama karatun nan in yi kudi in kai ki kasashen waje ki waye," ta jawo jakarta ta bude fayil ta ciro ta yage takardar. Hotuna ne suka zubo kasa sun fi dari tare da takardu na sauran bayanai kan masu laifin. Ido tsahuwar ya ware bayan ta gama kallon hotunan ta dauki daya daga cikin hotunan ta ce; "Wadannan masu jajayen fuskar kuma daga ina? Na shiga uku yau na ga zuriyyar Annabi Yusufa a wajen kyau da sauri. Amrah da ranta yake 6ace ta fizge hoton tana kokarin mayar da su ma'adanarsu, manyan idanunta ta zaro tana kare ma wanda ke jiki kallo. Tabbas kyau kam Granny ba ta yi karya ba akwai wajen young man din nan, a zuciyarta ta ce halan zuri'ar Annabi Yusuf din ne? Daya bayan daya ta bi hotunan da kallo tare da nazari akan halittarsu, mata san samari ne akalla ba za su wuce shekaru Talatin da uku a duniya ba, kyawawa ajin karshe kowannanensu gwanin kyau ne. Ido ta kurawa hoton da ya fi jan hankalinta wajen kyau. Fari ne tas! Kamar Balarabe, fuskarsa cike da annuri tare da saje mai kyau wanda ya karawa fuskar tasa kyau, ido ta kuma kurawa tabon goshinsa mai nuni da alamun sallah, ta danna wa hoton harara kamar yana kallon ta a fili sai ta ce. "Mugu ba shi da kama young millionaire ka taro match hope ka tanadi players?" *** 7 AKWAI KURA Zainab Amarah Ammat shi ne cikakken sunanta, 'ya daya tilo ga Malam Ahmad haifaffen garin Kaduna cikin karamar hukumar Igabi mazauna cikin Mamdo Kaduna. Malam Ahmad malamin makaranta ne a nan cikin Afaka yamma dake nan cikin Mando mutumin kirki ne mai wadatar zuci, cikakken Bahaushe gaba da bayansa a lokacin Malam Ahmad ya samu ilimi na NCE ba da jimawa ba ya fara aiki, cikin hukuncin Allah ya yi nasarar samun macen kirki Zainab. Ya auri Zainab 'yar jihar Borno, kabilar Shuwa Arab. Zainab aure ta zo Kaduna na 'yar kawunta da aka kawo Kaduna nan cikin unguwar Dosa, cikin ikon Allah Malam Ahmad na cikin abokan ango a nan suka hadu da Zainab har suka kulla soyayya cikin yardar Allah iyayenta suka amince suka ba ta zabin ranta duk da kowa ya sani Shuwa Arab ba su cika ba da 'ya'yansu ga bare ba musamma talaka amma iyayen Zainab da yake suna da Addini tuni suka amince da malam Ahmad. Zainab ba su samu matsalar hakan ba, an yi auren cikin aminci da kaunar juna. Malam Ahmad ya gyara gurin zama mai kyau a nan cikin gidansu kasancewar mahaifiyarsa kadai ke zaune da shi, mahaifinsa ya jima da rasuwa. Auren Zainab da wata sha daya kacal! Allah ya sauke ta lafiya ta haifo 'yarta mai kama da ita sak! Kamar an tsaga kara. Ma'auratan sun yi murna tare da godiyar Allah. Cikin rufin asiri daidai misali akayi sunan. Ranar suna yarinya ta ci sunan mahaifiyarta Zainab. Saboda kaunar Ahmad ga Zainab iyayen sun yi murnar kaunar da Sarakin nasu ke yi ma 'yarsu Zainab. Ita kanta Zainab ta yi farin cikin abin da mijin nata ya yi mata, kuma ya kara masa kima tare da kauna a zuciyarta. Ita kanta Iya Maman Malam Ahmad ta yi murna ga kaunar da dan nata ya nunawa matarsa. Zainab ita da kanta ta yi alkunya wa 'yarta da suna Amrah, a cewarta ita ma ta yi masa takwara don tun da ta san shi take kiran sa da Ammat saboda kunya irin tata. Zainab karama ta ci 8 1 3 AKWAI KURA gaba da girma, tun tana karamarta Allah ya zuba mata wayo ga son gayu sunan Granny da take kiran kakarta tun tana yarinya da shi ta budi baki don Abbanta shi ya koyar da ita hakan. Amrah tana girma kyawunta yana kara yawa, makwabta da yawa kowa na kaunar Amra ita ma Amran ba baya ba akwai son mutane sai dai tun tana karama yarinya ce masifaffiya ga rashin son raini, ko da yara ka nanu sa'anninta suke fada za ka ji tana fadin ba ta son raini. Malam Ammat yakan yi dariya ya ce; "Girmanki da kallo." Zainab ba ta sake haihuwa ba har Amra ta kai shekara uku tuni an sanya ta a makaranta, nan inda mahaifinta ke koyarwa; Model Primary and Secondary School Afaka Yamma, haka Islamiya ba a bar ta a baya ba. Amra na zuwa kuma tana fahimta sosai. Mahaifinta yana yi mata bita sosai a gida, wannan ya kara buda kwakwalwarta tuni ta gama makarantar raino (Nursery) ta fara Firamare tana aji hudu, har yanzu mahaifiyarta ba ta sake haihuwa ba wannan dalilin ya karawa Malam Ahmad kaunar 'yarshi tare da shagwaba ta, bangaren tarbiyya yana kokari don duk shagwabar Amra da son neman fadanta tana tsoron abin da zai taba ran babanta. Mutane da yawa cikin makarantar Afaka Yamma Malamai su ne suka ba wa Malam Ahmad shawarar canzawa Amra makaranta, a cewarsu in har ya kai ta makarantar kudi inda ya fi nan ilimi za ta hadu da wadanda suka fi ta ilimi, a take Malam Ahmad ya yi na'am da shawarar abokan aikinsa amma sai dai alba shin nashi ba zai dauki dawainiyar gida da na 'yarshi ba. Dalilin karatun Amra Malam.Ahmad ya fara buga-buga yana hadawa da aikin karfi don Amra ta samu ingantacciyar rayuwa. Cikin ikon Allah Amra ta samu nasarar cinye interview a makarantar sojoji wadda aka fi sani da Command Day Secondary School dake garin Kaduna. 9 AKWAI KURA Fara karatun Amra cikin sojoji da yaran sojoji ya kara mata rashin tsoro tare da karfin hali irin na sojoji, a nan ta yi kawaye yaran manya mafi yawa iyayensu kushoshi ne a gwamnati, kasancewar makaranta ce ta kudi ta 'ya'yan manya. Amrah mai farin jinin jama'a ce, da wuya ta zo guri ba a samu masu Kaunar ta ba sai dai kullum mahaifinta na yi mata fadan ta san irin kawayen da za ta jawo kuma kada ta yarda ta kai kanta inda Allah bai kai ta ba, wannan dalilin ya sa sai dai kawayen su bi ta ita ba ta zuwa gidan kowa. Aminiyarta daya tak ita ce Zahra Khasheem ita ma Zahran kadifirinsu ne ya zo daya. Granny kakarta ta sha fadin; "Amadu daman Zainabu yaya aka Kare da rashin tsoro bare ka kai ta cikin marasa tsoro. Allah dai ya kyauta ya shirya mana Zainabu." Yakan yi dariya ya ce; "Inna ai karatu ne, da zarar ta gama za ta bari a cikin command. Tabbas! Canjin makaranta ya kara mata mai da himma bilhakki da gaskiya, tuni Amra cikin Command ta kara samun guraye wadanda suka fi ta ilimi, ai tuni Amra ta sake hazaka tare da nacin karatu don fitar da mahaifinta kunya. Lokaci na tafiya karatu na kara zafi har Amra ta je ajin karshe a makarantar sojoji, a wannan lokacin ne ranar Litinin suna shirye-shiryen fara jarrabawa ta fita Malam Ahmad ya dauko ta a bayan mashin daga makaranta suna tafiya suna hirarsu. Dariya take tikawa sosai na maganar baban nata ta rufe fuska da tafin hannunta kamar tana kallon shi, tana bayan mashin shi ko yana tuki ta ce; "Kai Abba ni kam ba zan yi aure ba ina nan tare da kи". 10 *** AKWAI KURA BABI NA BIYU Kir! Kau! Motar ta shiga da su. "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un." mai motar ya fada da sauri ya ce da direban, Danladi yi parking." Kafin ka ce kwabo mutane sun cika wajen don ba su taimakon gaggawa, jini ya wanke titi sai ka ce an yanka rago sakamakon fashewa da kan Malam Ahmad ya yi saboda taka shi da tayar motar ta yi. Salati kawai mutanen suke yi ya yin da mai motar yake fadin, "Ku taimake ni mu kai shi asibiti ku taimake ni kada bawan Allah ya mutu a hannuna, kamar a mafarki Amrah ta mike a kwance da motar ta wurga ta can gefe ko kwarzani ba ta yi ba illa karamar suma da ta yi, tuni ta tariyo abin da ya faru da ita da Abban nata a hanyar dauko ta daga makaranta. Da gudu ta mike, wata mata na rike ta tana fadin, "Kwanta yarinya asibiti za a kai ku, kwanta kada ki kuma jin wani ciwon. Ina Amrah ta fusge hannunta, da gudu ta ratsa mutanen dake zagaye da Abbanta gabanta ne ya fadi ganin shi kwance kamar matacce a cikin jini, ta kurma kukan da sai da duk wadanda suke gurin suka dawo da hankalinsu kanta tare da yi mata kallon tausayi. Cikin kuka take jijjiga shi, "Abba ka tashi, ka tashi don Allah." Ba ta damu da jinin dake bulbula kanshi ta hanci da baki ba da ya bata mata jikin uniform ta rungume shi tana jijjiga shi amma ina, bai san me take fada ba sakamakon numfashinsa dake fita sama-sama da alamun ran na shirin barin jikinshi "Yan yi mata ki yi masa kalmar shahada, ‘yan yi mata daure," 11 AKWAI KURA su ne abin da mafi yawan mutanen dake tsaye gurin ke fadawa Amrah, ta tsinci zuciyarta da bin umurninsu bakinta ta kafa a kunnensa dake fidda jini. "Abbana," ta hau maimaita masa kalmar shahada, "La ilaha illallahu Muhammadur Rasulullahi," shi take maimaitawa. Cikin ikon Allah kamar an fusgeshi ya fara karbar kalmar. Karanto kalmar shahada yake yi tare da sauke numfashin wahala. Amrah na yi yana amsawa da kyar saboda jikkata cikin dakiku kalilan jikinshi ya sake, duk da ba ta san mutuwa ba yau kam ta yi imanin ta gan ta tsirararta ya dauke mata Abbanta. Amrah ta kurma ihu da gudu ta rike wuyan Alhajin tana kuka tana dukan kirjinshi, "Ka dawo min da Abbana, wayyo na shiga uku ka dawo min da Abbana in har Abbana ya mutu sai na kashe ka sai na kashe ka, sai na kashe kaina wayyo Abbana." Karfi ne take da shi kamar doki ga karfin tashin hankali mutane sun kai biyar suna bambare ta daga jikin mutumin amma sun kasa cire ta daga jikinsa. Lu! Ta yanki jiki ta fadi. "Subhanallah!" Alhajin ya fada. Cak ya dauke ta ba tare da ya saurari maganganun mutane kan gawar ba ya jefa ta a mota, fadi yake, "Ku taimake ni waya iya mota ga makulli a ceci rayuwar baiwar Allahn nan kada hakkin rai biyu ya bi ni." Direbanshi dake gefe cikin jimamin aika-aikar da ya yi ya mika hannu, "Kawo Maigida bari mu je." 12 AKWAI KURA Sam ya manta tare yake da direba, shi ji yake yi ma shi ne ya buge su ba direba ba. Ya mika masa makullin. "A'a Alhaji ai wannan makullin dakinka ne, ga na mota a aljihuna." "Yauwa ku je Shehu ku je, akwai kudi a mota zan kira wayarka." Da taimakon mutane aka dauki wayar Malam Ahmad da ta tarwatse a gefe aka hada, a nan aka samu kiran karshe nasa. Bayan sunyi magana da mutumin ya yi musu kwatancen gidanshi, tashin hankalin da ba a sa masa rana, Iya da Zainabu na zaune sai gani suka yi ana shigo musu da gawa. Fadin tashin hankalin da wannan iyali suka shiga na da yawa. Ita kanta Zainab mahaifiyar Amrah sumanta biyu. Iya Granny ita ce ta yi karfin halin neman sauran 'yan'uwa ta waya, tuni suka hallara aka yi wa Malam Ahmad sutura tare da kai shi gidanshi na gaskiya. Shi ma Alhajin da ya buge su tare da shi aka yi komai, da ganin shi kun san yana cikin tashin hankali. Ita ko Amra sai da ta kwana uku a asibiti tana ihu kamar ta zare, da taimakon Allah da na 'yan uwa da suke lallashin ta ta fara samun nutsuwa Alhaji shi yake komai na game da asibitin tare da sauran duk abin da za su bukata, ga Amra ta matsu a sallame ta ta koma gida ba don ta warke ba sai saboda kukan da take ita za ta dawo gida wannan dalilin ya sa ranar kwana biyar likita ya ba ta sallama tare da sauran magungunan da za ta sha, Amra ta tsani ta bude ido ta ga Alhji in ta daga kai ta kalli Alhaji babu abin da takeji illa tsana da bakin ciki a zuciyarta ba don shi ba da yanzu tana rayuwa mai dadi da Abbanta. Amrah tuni ta dauki alhakin mutuwar Abbanta ta dora akan wannan Alhaji, gare ta hakuri ya yi kadan ya hana ta kukan rashin mahaifinta sai dai zuciyar musulunci. Ba ta ci ba ta sha sai umminta ta zare mata ido. Karshe Granny 13 AKWAI KURA Almajiran kusa da gidansu ta ba wa sadaka suka yi ta sauke mata Kur'ani, tare da yi mata rubutun dangana kafin aka samu kanta ta fara samun nutsuwa, kawarta Zahra Kasheem ita ma tana ba da tata gudummawar don samun nutsuwar Amra. Iyayen Zainabu sun zo daga Borno tare da su akayi zaman makoki, sai bayan sati guda suka koma, sun so su tafi da 'yarsu amma Iya ta hana ta ce su bar ta ta yi takaba a dakinta. Wannan ke nan. Alhaji Usman da matarsa su ma tare da su aka yi wannan zaman makoki har ta yaransa mata guda biyu Mariya da Rabi'a wadanda ba su wuce sa'annin Amrah ba su ma sun yi ta zarya wajen kawo abinci gidan mutuwar tare da sauran 'yan uwansa na kusa duk ya sanar da su mutuwar bawan Allahn da ya buge rai ya yi halinsa. A gurguje Amrah ta ki ta koma makaranta saboda mutuwar mahaifinta candyn da ba ta yi ba ke nan, karshe da taimakon Zahra Khashem kawarta aka samu aka biya kudin jarrabawar WAEC da NECO, malaman suka yi mata alfarman Zaran ta yi wa Amrah jarabawar Candy. Amrah hakan ta ci gaba da zaman jimamin rashin mahaifinta abin ya taba ta sosai kasancewar a gabanta abin ya faru. Alhaji Usman shi ya ci gaba da daukar nauyin gidan Malam Ahmad kasancewarsa mai abin hannu, koyaushe yakan yi musu aike, yana tausayawa Amrah sosai tare da Iya musamma Zainabu da ya yi sanadin mutuwar mijinta, wannan dalilin ya sa yake taimakon su sosai. Ta bangaren Amrah kuwa wannan abin da yake yi bai rage mata tsanar da take yi mishi ba ko daidai da kwayar zarra. Tun bai gane ba har ya gano tsa nanin tsanar da Amrah ke yi masa don babu ruwanta in ya zo gai da 14 AKWAI KURA lya ko gaida shi ba ta yi sai dai in har shi ne ya yi mata sannanu, a hakan ma tana hararar sa. Gare shi tausaya mata yake yi, don yarinya ce shi babba ne hankalinsu ba zai zo daya ba, kuma yana yi mata uzuri ya san yarinya ce duk abin da ta yi sam ba ya ganin laifinta. Lokaci zuwa lokaci in ya samu dama yakan zo har gida ya duba Iya don debe mata kewar danta. Wannan zuwan da yake yi a nan ya yaba da hankalin Zainabu bayan ta gama takaba ya bijirowa Iya da son auren Zainabu, har ga Allah Iya ta dauke shi da saboda kyautatawarshi gare su ba tare da bata lokaci ba ta yi maganar da Zainabu amma sam ta ki yarda shi ko bai bar naci ba. Da taimakon Iya da na sauran dangi har da na maidakinshi Hajiya Sadiya sai da ta zo har gida don neman alfarmar Zainab ta auri mijinta ita kam ba ta kishi da Zainab don ta yaba da halinta. Cikin dan lokaci kadan da suka san juna daga karshe Zainabu ta amince da auren Alhaji Usman. Nan fa Amrah ta ce sam ba ta amince ba, karshe ma ta ce ya kashe mahaifinta ne da gangan don ya auri umminta. Ni ko na ce ina ya san ta da zai kashe mata mijin nata? Tun da aka fi karfin Amrah kan auren umminta shikenan ta dauki tsa nanin tsana ta karawa Alhaji Usman. Iya Granny da Mamanta sun yi fadan har sun gaji amma taurin zuciya irin na Amrah ta ki bari. Akwai ranarda Iya ta fashe da kuka Alhaji ne ya turo musu da sako ciki har da na Amrah kan maganar makaranta cewa wacce makaranta take so kuma me take son karanta, amma Amrah ta ce a je a ce masa ba ta so in dai da kudinshi za ta yi karatu ba ta bukata. 4 Kuka Iya ta fashe da shi domin wannan tsinka su da Amrah ta yi a gaban dan aike direba shi ne ya sa Iya kuka sosai. Umminta Zainabu ta dauki muciya ta bi ta da duka Amrah na kuka Zainabu na kuka ganin ummin tata tana kuka sosai tana 15 AKWAI KURA dukan ta ya sa Amrah ta saurara da nata kukan, don ta karanta addini ya yi mana magana da kakkausan harshe kan sanya iyaye kuka, musamma uwa. Cikin lallashi ta ba ta hakuri tare da alkawarin za ta yi karatun. "Ummi saboda mijinki kike duka na tun kafin a yi auren ko?" ta turo baki tana buga kafa. Sai tausayin Amrah ya kama Zainabin ta jawo ta jikinta tana lallashin ta tare da neman alfamar don Allah ta rage wannan kiyayyar ga Alhaji Usman, Malam Ahmad kwa nansa ne ya kare ko da yana kwance gida wannan ranar sai ya mutu ba zai kara kwana ba. Tsakanin 'ya da uwa uwa sai Allah tuni suka sasanta kansu sai ga shi dukkansu suna dariya. Zainabu ta ce; "Haba kamar kumbo kamar katanta wannan kishin na Amrah hali ne ta dauko irin na mahaifinta, bayan gama takabar Zainabu ba da jimawa ba aka daura aurenta da Alhaji Usman, sai bayan an daura auren ne suka gane ashe Alhaji Usman atta jiri ne na gaske kuma ma'aikaci babba ga hukumar nan ta sirri wato DSS mai matakin DG kuma babban dan kasuwa. Aurensu da ummin Amrah Zainabu ta kara samun ci gaban rayuwa arziki ya samu ga kwanciyar hankali, ita kanta Iya tana cin moriyar Zainabu da mijinta; sun zuba mata komai na jin dadin rayuwa a gidan nata sun gyara mata daki uku kowannane dauke da bandaki a ciki, na Amrah daya na Iya daya sai daya saboda baki. Ko Amrah in za ta cire kiyayyar Alhaji Usman ta tabba tar mahaifiyarta ta samu nutsuwa sosai kuma ta samu miji mai kaunar ta da gaske, zaman lafiya sosai suke yi da Hajiya Sadiya matarsa, haka yaranshi suna ba ta girma sosai. Gidan Zainabu dabam ya gina mata mai kyau ko a Turai ya hadu. 16 AKWAI KURA Da farkon auren ya so Amra ta koma gabansu ita da Iya amma Iyan ta ce ba za ta iya wannan abin kunyar ba sai dai Amrah ta koma, ita ko Amrah kallo ma bai ishe ta ba bare har ta tanka. Ikon Allah auren Zainabu da wata sha daya kacal ta haifowa Alhaji Usman 'ya'ya uku reras maza biyu mace daya inda ya yi kara ga Zainabu; namijin ya sa masa sunan Ahmad macen daya ya yi ma Iya takwara wato Hafsat suna kiranta da Amlah dayan kuma ya ci sunan nashi Baban wato Mahmood, Amir da Khalifa ake kiran su. Cikin shekara biyu Amrah ta gama difloma A Federal Poly Kaduna. Gamawarta ke da wuya ta fara HND a nan Poly din inda yanzu take shekarar karshe. Amrah makerin kyau ya gama kera mata halitta, Tabarakallah masha'Allah komai hassadarka in ka gan ta ka san ita din mai kyau ce, ga son gayu ga rigima, in ka ga suturar da take sanyawa sai ka ce diyar Gwamna. Umminta da mijinta sun wadata ta da komai da take bukata; sutura da kayan kwalliya ba sa karewa domin kafin wannan ya kare an kuma yi mata oda na wasu. Alhaji Usman ko me zai sayawa yaranshi tare yake oda da Amrah, haka asusunta duk wata kudin da yake ba wa yaranshi irinsa yake tura mata, hakan ya sa ta kara zama babbar yarinya tana fantamawarta yadda take so, sai dai babu shakuwa ko kadan tsakaninta da Rabi'a da Mariya yaranshi, domin a da suna kaunar ta amma tun da suka gane irin kiyayyar da ta nuna ga mahaifinsu tuni suka fara takun saka da ita, sau miliyan in za su hadu fada ke raba su, hakan ta sa Amrah ba ta cika zuwa gidan umminta ba saboda Mariya da Rabi'a na kaunar Zainabu kamar yadda ita ma take nuna musu kauna wanda su ma suke mata lakabi da Ummi. Kusan duk hutun karshen mako s gidanta suke yi tare da Ummin da kannansu 'yan uku. *** 17 AKWAI KURA Posting nasu ne ya fito na tafiya attacment wato IT, abin Mamaki sai ga shi an tura Amrah DSS office da sunan IT. Ranar da ta karbi takardan daskarewa ta

Chapter 1 of 12