Daga haka ta saka kai ta fice daga cikin dakin, tana wakarta.
Dafe goshinsa yayi, dole ya hana Nazneen magana, domin aljanun da suke tare da ita, sun bude mata kunne da idanunta. Yana tsoron kada haka yasa ta rasa mijin aure.
Haka yayi ta shirin maida ta bauchi, yana ji kamar bai kyauta ba. Shi da gidanshi amma bai da ikon kawo kowa ƙarƙashinsa, haka yasa bai kuma bin ta kan Haulatu da Yaranta ba.
Kamar yadda Nazneen din ta fada, haka ya faru Dayyiba da kanta, ta ce su hakura da juna. Bai yi mamaki ba sai ma godiyar da yayiwa Allah. Kwana biyu tsakanin ya dawo da Nazneen bauchi, bayan ya tsaya ya gama mata kome, shi da Tahir da yake son gani yarinyar ta cigaba. An sakata a Urban college, da drivern da zai na kaita. Duk wani abin bukata sai da ya ajiye mata.
Budar bakin Innayo ta ce mishi.
"Ban yarda ka sake kashe mata kudi haka ba, ai nima ina da hakki akanka."
Shiru yayi bai ce kome ba, Nazneen tana wurin Malam, amma tana jinsu kowa a gidan tana jin maganarshi. Murmushi tayi.
Haka tasha fura a wurin malam, tana gama sha ya ciro mata kunshin kilishi. Ta fara ci tana lumshe idanunta. "Baba Malam, wannan namar kullum ana ajiye min."
"In sha Allah, amaryata."
"Kace Innayo ta min wanka da ruwan barkono kenan."
"A'a waye ya gaya miki."
"Eh tana da mugun kishi, da son kanta tana son kowa ya zama."
"Shiiiii! Kul na kuma jin kin fadi haka. Ya kamata muyi wani abu akan aljanin da yake tare dake."
"Meye yayi maka?"
"Saboda ya bude miki, idanu da baki kina fadar magana."
"Ai har da kunne, daga nan ina jin goma tana zagin Innayo."
Maza yayi ya toshe mata baki.
"Bana ce ban da magana ba."
D'ago kai tayi tana faɗin. "Kace Baba Malam"
Hawaye ne ya zubo mata, tana kallonshi sannan ta sunkuyar da kanta. "Maganar zata saka a tsaneki, dole na tsaya miki da rokon Allah, ya baƙi lafiya."
Gyada kai tayi, tana wasa da bakin rigarta. "Ba na miki faɗa don bana sonki ba ne, a'a maganar ce bata da amfani kinji."
"Tow kuwa Baba Malam, Innayo tana ƙoƙarin raba ni da Papa, ni kuma ba zan yarda ba." Ta faɗa idanunta suka fara juyawa.
"Kenan ba zaka rabu da yarinyar nan ba?" Malam ya daka mata tsawa, D'ago kai tayi tana dariya, idanunta yana wani irin juyawa ta ce.
"Muhammad Sani Malami, ce maka akayi zamu barta? Ai muna kan umarnin mu sauyin ƙaddara ba zai rab'a mu ba."
"Kai wani irin mushuriki ne?" Dariya Nazneen ta saka tana kallon Malam. "Ba zamu rabu da ita ba."
"Zaku rabu da ita!" Inji Malam. Tabe baki tayi tana kauda kanta.
"Ku fita kafin na fara kona ku."
"Babu inda zamu je, domin muna tare da ita matuƙar aka ce za a tab'ata sai mun bayyana, kuma ka ja kunnen matarka ko kuma daga yau mu fara takun saka da ita."
Shiru suka yi, ta fara hamma kafin ta kwanta a wurin.
Barci me nauyi yayi gaba da ita, shigowar Babanta Malam ya zuba mishi idanu, ganin yadda idanunshi suka kad'a jajjur.
A hankali ya zauna yana sakin murmushin yake, ya cewa Malam.
"Mamana tayi barci ne?"
"Me Uwarka ta kitsa maka?" Shiru yayi yana jin babu dad'i.
"Kasan ba zaka iya rike ta ba, ka saka ni baka ita? Kasan sai abin da Uwarka ta gaya maka na barka da yarinyar da ta nace zata zauna a wurinka akan mahaifiyarta?"
"Malam ya zan yi? Shi yasa naso da Uwarta tana nan, zata fi sakewa."
"Kasan Allah, wannan yarinyar akwai babban lamari akanta. Kada ka biyewa mahaifiyarka ku shiga hakkinta. Yanzu haka sun ce ba zasu kyale duk wanda ya tab'ata ba. Har yau na kasa gano bakin zaren dalilin samuwarsu a tare da ita ba. Abu daya na sani aljanin yana da alaka da irin aljanun da ake bautawa.
Na so, nayi dogon binciken akansu sai na fara sai abin ya lalace. Duk wanda ya rab'eta matukar mutumin kirki ne, Allah yana yalwata shi da kare shi, idan kuma ka nufe da sharrin zai koma kanka, zan gayawa mahaifiyarka da mutanen gidan nan, duk da nasan bai zama dole su yarda da ba. Amma idan suka ga wani abu a kan idanunsu zasu nutsu.
Ba fata nake ba, amma ban tab'a ganin aljani me mugun taurin kai irin Aljanin Nazneen ba."
"Malam ya zamuyi da ita? Bana son wannan laluran ya lalata mata gobenta." Ya faɗa cike da damuwa. Murmushi Malam yayi sannan ya ce masa. "Idan aka yi hutu, kazo ka ɗauketa."
Haka ya bar gidan bayan ya bawa Malam kome ya gaya mishi yadda suka yi da Innayo, sannan ya wuce Gombe.
Sai dare ta farka, Malam ya kalli yadda take mika ya ce mata.
"Lokacin sallah ya wuce, kiyi sallah kizo muyi karatu."
"Tow;" ta nufi cikin gidan, a bakin kofar dakin Innayo ta ga akwatin kayanta, kamar ta fashe da kuka ta ce. "A ina zan kwanta tow?" Ta shiga kokarin daukar akwatinta. Dauka aka yi cak sama, juyawa tayi ta ganshi sanye da farar shirt.
"Ina zaki iya dauka kayan nan." Ta shiga falon Innayo da kayan. A fusace ta sallame addu'ar da take yi. Ta ce mishi.
"Bana son munafunci, ku fice min a daki."
"Babu inda zata, kin isa ki hanata zama ne bayan kin rabata da ubanta." Inji Malam ya faɗa yana shigowa cikin falon, haɗe rai tayi tana hararanta.
"Shiga wancan dakin, ka ajiye kayan a dakin can, daga yau nan ne dakinta."
"Ban gane ba? Kana nufin daki za a bata?"
"Kiyi a hankali, shaidanun da suke kanta sai sun shayar dake mamaki zaki gane abin da nake nufi."
Daga nan ya fita tsakar gida, ya tara su yana musu nasiha tare da gaya musu muhimmanci azkar na safe da marece,
Ayatul kursiyyu
Suratul iqlas (kulhuwallahu)
Falaqi da nasi,,,, kafa uku uku,,,
Ko su kadai ka karanta sun isheka kariya,,, idan Kuma ka ita sauran addu'o'in da akeyi saika Kara dasu. Ga wasu daga ciki :
اَمْسَيْنَا وَاَمْسَى الْمُلْكُ لِلَّهِ وَالْحَمْدُ لِلَّهِ، لَا إِلَهَ إِلَّّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، رَبِّ أَسْأَلُكَ خَيْرَ مَا فِيْ هَذه اللَّيْلَةِ وَخَيْرَ مَا بَعْدَها، وَأَعُوْذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِي هَذَه اللَّيْلَةِ وَشَرِّ مَا بَعْدَها، رَبِّ أَعُوْذُ بِكَ مِنَ الْكَسَلِ، وَسُوءِ الْكِبَرِ، رَبِّ أَعُوْذُ بِكَ مِنْ عَذَابٍ فِيْ النَّارِ وَعَذَابٍ فِيْ الْقَبْرِ
Transliteration:'Amsaynaa wa'amsal-mulku lillaahi walhamdu lillaahi, laa 'ilaaha 'illallaahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu wa Huwa 'alaa kulli shay'in Qadeer. Rabbi 'as'aluka khayra maa fee hatheehil-layla wa khayra maa ba'daha wa 'a'oothu bika min sharri maa fee hatheehil-layla wa sharri maa ba'daha, Rabbi 'a'oothu bika minal-kasali, wa soo'il-kibari, Rabbi 'a'oothu bika min 'athaabin fin-naari wa 'athaabin fil-qabri.
اللَّهُمَّ بِكَ أَمْسَـينا ، وَبِكَ أَصْبَحْنَا ، وَبِكَ نَحْيَا، وَبِكَ نَمُوتُ، وَإِلَيْكَ المصير
Transliteration: Allaahumma bika 'amsaynaa, wa bika 'asbahnaa, wa bika nahyaa, wa bika namootu wa 'ilaykal-maseer
اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لَّا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَأَبُوءُ بِذَنْبِي فَاغْفِر لِي فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَن
اللَّهُمَّ عَافِـني فِي بَدَنِي، اللَّهُمَّ عَافِـنِي فِي سَمْعِي، اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَصَرِي، لَا إِلَهَ إلاَّ أَنْتَ. اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُبِكَ مِنَ الْكُفْر، وَالفَقْرِ، وَأَعُوذُبِكَ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ ، لَا إلَهَ إلاَّ أَنْتَ3*
حَسْبِيَ اللَّهُ لَآ إِلَهَ إِلَّا هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَهُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ7×
Transliteration: Hasbiyallaahu laa 'ilaaha 'illaa Huwa 'alayhi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-'Arshil-'Adheem.×7
بِسْمِ اللَّهِ الَّذِي لَا يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الَْأرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ3×
Transliteration: Bismillaahil-lathee laa yadhurru ma'as-mihi shay'un fil-'ardhi wa laa fis-samaa'i wa Huwas-Samee 'ul- 'Aleem.×3
رَضِيتُ باللَّهِ رَبًّا، وَبِالْإِسْلَامِ دِيناً، وَبِمُحَمَّدٍ صَلَى اللَّهُ عَلِيهِ وَسَلَّمَ نَبِيَّاً3×
Transliteration: Radheetu billaahi Rabban, wa bil-'Islaami deenan, wa bi-Muhammadin (sallallaahu 'alayhi wa sallama) Nabiyyan.
×3
سُبْحَانَ اللَّهِ وَبِحَمْدِهِ
Transliteration: Subhaanallaahi wa bihamdihi.(100times)
لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِير
أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ
Transliteration: 'A'oothu bikalimaatil-laahit-taammaati min sharri maa khalaqa. (3times)
اللَّهُمَّ صَلِّ وَسَلَّمْ عَلَى نَبِيِّنَا مُحَمَّدٍ
Transliteration: Allahumma salli wa sallim 'alaa nabiyyinaa Muhammadin (10 times)
"Kada ku sake kuyi wasa da addu'a. Domin kuwa shaidanun da suke jikin Nazneen, suna iya zame mana fitina. Idan kuna son zaman lafiya, kada wani ya nufi cutar da ita. Sannan Addu'a ya zame mana jiki kamar kullum.....
_KASUWA A KAI MIKI DOLE_
*Nesa tazo kusa, ko kun san Muzafa World collections. Sun zo muku da kayan zamani babu ruwanki da zuwa kasuwa. Yar uwa, kayanmu daya yake tankar da dubu. A rashin tayi akan bar raha, haka kuma bahaushe ya ce a rashin kira karen bebe ya b'ata. Tow ga dama ta same ku, domin kayanku ya tsinke a gindin kaba, kayanmu sun haɗa da Dubai Abayas, yan kunne da abin wuya, takalman Manya da Yara, lace masu kyau da inganci. Hajiya nesa da ake ce miki tazo kusa babu ruwanki da shan rana da kura, kayanki yazo inda kike! HAJIYA Abu me kyau ke sayar da kanshi*
*08130269641*
[11/19, 7:01 PM] Queen BeeBee: *NAAZNEEN❤🔥*
EXQUISITELY BEAUTIFUL
#Mai_Dambu
'Top-Notch
Season 3
بسم الله الرحمن الرحيم
Chapter-16
Duk nasihar da Malam yayi, wai ko za a dace a kiyaye. A'a Innayo gani take kamar da gangan yake fadar kome, da daurewa karya gindi. Bayan ya wuce dakin Umma Goma ta shigo falon Innayo. Cikin tsannanin munafunci, ta zauna tana jimamin lamarin kafin ta ce mata.
"Yanzu haka zaki cigaba da zuba idanu?" Kallon Goma tayi sannan tayi kwafa tana faɗin. "Idan ban zuba idanu ba, me zan yi? Ai babu yadda na iya da Babawuro ne da ya kwaso min bala'i cikin zuri'ata. Amma tabbas wannan abin ba karamin abin dariya ba ne domin nasan Sa'a da Lami suna can suna min dariya."
Girgiza kai Goma tayi cikin kwarewa a harkan munafunci, ta ce.
"Ni dai yanzu ki san yadda zaki yi domin kuwa." Kallon kofar tayi sannan ta yi kasa da muryanta ta ce. "Na gaya miki, ki tashi tsaye yadda yarinyar zata bukaci a maida ta wurin Uwarta."
"Tow me zan yi?"
"Me kuwa zaki?" Goma ta kuma tambayar Innayo, kafin tayi kwafa ta ce mata. "Tambaya kike? Bayan a bangarenki take, ai watan cin uwanta ne ya tsaya."
"Ke tab'a ni da arziki, kina nufin na hanata sakat." Inji Innayo,
"kwarai kuwa, ai dama ce ta samu dole mu hanata shakar iskar yanci." Inji Goma, gyara zama Innayo tayi, domin wani lokaci a gaban Goma Innayo wawuya ce. "Na tab'a baki da arziki, ina jinki."
Gyara zama Goma tayi, ta shiga tsara Innayo, kada ku manta ita fa Goma ba zata tab'a barin Innayo ta san halin da take ciki, amma ita Innayo duk abin da ya same ta, bata da masoyayi sama da Goma, bata da me kaunarta sama da Goma, kaf duniya babu me mata alkhairin Goma.
A yadda suke hiran nan, Nazneen tana bakin kofar tana jinsu. Dole yau da dauki mataki akan Goma. Bata musu magana ba, don dama abin yana kusa a hankali ta wuce ba tare da sun san da wucewarta ba, domin bata yi tafiyar yadda zaka san cewa mutum ce ba, tayi tafiyar ne akan yatsun kafarta. Tana shiga dakin ta tsaya cak a kan iska. Idanunta a rufe rub, fuskarta a murtuke kamar an gaya mata sakon mutuwa, tana dakin tana jin su Hajiya Goma da Innayo.
Duk yadda ta kai ga kaunar Innayo, domin tana yawan jin Papa yana gaya mata, Innayo she's a great Mother. Bude idanunta tayi da ya koma koriya shar sai wani irin wuta da yake ci a cikin idanun.
Kofar dakin ne ya rufe kanshi, ta juya tana kallon kofar. Wasu murtukakkun kadangaru ne, wasu da gashinsu kamar bayan bushiya, wasu kuma kamar kwalabiya. Zama tayi akan iska tana me tankwashe kafarta. Murmushi tayi musu tana faɗin. "Auta me ya dace muyiwa, Hajiya Goma?" Juyi yayi yana tsalle, da muryanshi a shake ya ce mata.
"Amanda..... Au Nazneen kawai ta goya ni sai nayi barci rabona da barci, tun kafin a haife ki."
"Dan karami, me zamu yi mata?" Ta tambaye, wani dan karamin kadangare, girgiza yayi sai gashi ya koma bakinkirin ya ce mata, "Yau shekara tara rabona da ayi min wanka, tun zamanin haihuwarki."
"Kato kai fa?" Shima wani katon kadangaren ne, har da gemunshi.
"Ina laifin ina son a saka min, duddiya dariya, rabonta da dariya tun kafin a haife ki."
"Dan siriri kai fa?" Ta tambayi wani dantsigigin kadangare, dariya yayi ta ce mata. "Bayana nake son a sosa min."
"Yau a dakin Goma zamu yi hiran dare, tunda ta hana goɗiyar mu sakat, itama.haka zamu hanata sakat."
"Mun gode!"
Suka fada, suna rawa domin damar da suke nima kenan ga duk wanda ya tab'a Nazneen.
Haka suka zauna a dakin, har dare aka kawo abinci.
"Dan karami jeka duba an kawo mana abincin mu ne?"
"Tow!" A hankali ya ratsa bangon, ya biyo yana kallon yadda Innayo, yake kwashe rabin abincin ga wani matashin saurayin da yake falon, har da naman ta kwashe mishi, da sauri ya koma dakin yana tsaki.
"Uwar dakina me yasa baki son , mu hukunta kakarki?" Bude lumsashen idanunta tai tana kankance girmansu, sannan ta ce musu.
"Papa zai yi fushi." Ta sauko da kafarta kasa, sannan ta nufo bakin kofar falon.
Bude kofar suka yi, ta fita tana me kallon. Ammar dan gidan Aunty Uwani Babba, da yake ta cin abincin hankalinshi kwance. Kayan da Papa ya saya mata na makaranta Innayo ta Turo mishi akan ya kaiwa yan uwanshi. "Kayan makaranta na ne, idan kina son zaman lafiya ki bar min kayana. Idan kuma kina son ranki ya sosu ya gwada fita da kayan nan daga falorn nan, ku gani." Ta wuce ta fita waje, dakin Malam ta wuce, yana tare da Hajiya Lami, Sallama tayi. "Amaryanmu shigo." Inji Hajiya Lami.
Shiga falon tayi ta samu Malam yana cin abinci, kallonta yayi ya ce mata. "Yau ma bata baki ba?" "A'a nice nace ba zanci ba."
"Akan me?" Malam ya tambaye, yatsuna fuska tayi ta ce mishi. "Domin na ga ka ajiye min fura da nama." Kallon Hajiya Lami yayi, ita kanta mamaki take. A ka'idar malam magariba yana yi, babu me shiga mishi falo sai Matanshi, a cikin jikokin shi ya fi shiri da Tahir, amma wani ikon Allah tsakanin Tahir da falon Malam rana. Idan dare yayi sai dai shi ya fito ta bada abin da yake bukata, amma tun zuwan Nazneen aka fahimci soyayyar da yakewa Mahaifinta, ya tattara ya koma kan yar domin ba karya yana son Nazneen.
"Bata wancan kunshin." Janyo kayan tayi ta mika mata. "Malam ina kishi fa." Murmushi Nazneen tayi, tana faɗin. "Hajiyana, keda Umma Allah zai yalwata muku yadda baku zata ba."
"Uwar surutu, wuce."
"A'a Malam, kishi kake min ne?"
"Kyale shi, Hajiya Uncle Jamal ya biya Miki Umra. Keda Umma."
"Ke Indo;" malam ya kira sunan da bata so, fita tayi daga dakin tana zata koma dakinsu. Ta juyo tana kallon Malam ta ce mishi. "Uwargidanka, kuma tare zamu tafi da ita domin, Papa zai biya mana har da Uwar gulma" tayi ta fitarta.
"Hadiza karya Aljanunta suke fa."
"Eh koda karya suke, sai muyi ta mata addu'a. Amma yarinyar kyakkyawar mace ce za ayi."
Girgiza kai yayi yana faɗin. "Ina tason ba rabata da aljanun da suke tare da ita."
"Malam ayi a hankali."
Koda ta isa falorn Innayo, zama tayi tana kallon Ammar da ya saka kayan a gabanshi ya kasa daukar ko daya ya fita da shi..
Tana shan fura tana tura nama, tunda ta ga har lokacin bai bar falon ba, tasan ba zai iya daukar kayan ba, a hankali ta gama shan fura, ta kwashe kayanta akan idanun Innayo ta wuce da shi dakinta. Kuma aka rasa me mata magana domin kamar an batar musu da basirarsu ce.
Tunda ta kwashe kayan, sai lokacin Innayo hankalinta ya dawo jikinta, ya kalli wurin da ba shi kayan yaƙe babu kome.
"Ke zo nan"
Rufe kofar akayi, "Innayo kin ga babu kayan ta dauka kenan?" "Maza shiga ka zane min ita yar banza."
Ai kuwa Malam Ammar, ya mike tare da ɗaukar wayar radio record, yanufi dakin da kofar yake garkame, dakyar ya bude dakin, koda ya tura kanshi dakin, ji yayi an fisgo shi cikin dakin, sai gashi a wani kasungurmin daji. Juyawa yayi a mugun tsorace zai fita ina babu hanya.
"Wato kai ne mara kunya ko? Tow yau zaka sha mamaki" ga duhun da dajin yayi, wanda ya haifar mishi da tsoron bala'in da zai tadda, sannan be me magana ba, jin muryan kawai yake, bai san yadda aka yi ya juya ba, ya dai hango wasu diyoyin birai. Sun had'e kansu wuri guda, kasar wata bishiya mai matukar tsoratarwa, wuta na tashi a tsakiyar su.
"Kai zo nan!" Aka faɗa daga wurin biran.
Juyawa yayi ya kuma kallon gefe da gefe bai ga mai magana ba, aka sake magana bai motsa ba. Sai ji yayi an fisge shi kamar za a fyad'a shi da kasa.
Wani irin ihu ya saka idanunshi a rufe, mahaukaciyar dariyar da yaji, ya cika dajin wanda ya haɗa da janshi da ake yi a kasa, yana ihu.
------ Dakin Hajiya Goma.
Tunda ta idar da sallah, take jin wani irin barci. A can ƙasar ranta tana jin itama zata kwaso jikokinta guda biyu. Tunda Umma da Innayo, sun kwaso nasu zata saka a kawo mata Sailuba yar wajen Hadiza, da Nazeefa diyar Aminu wacce ita ce sa'ar Nazneen.
Tunda ga Tahir da Nazneen a gidan, kuma sai morar Malam suke baya ta kowa sai su. Anan ta cigaba da gyangyadi domin ko addu'a bata yi ba, ta soma gyangyadi domin Allah ya zuba mata gyangyadi kamar me, duk me gyangyadi yasan yadda yake da masifar dadi, balle nata tana kulla sharri ya same ta. "Goma!" Aka buge kafarta.
"Hmmm!" Ta amsa cikin barci.
"Tashi munzo miki hira ne."
Idanu tayi tana kallon dakin babu kowa, bata san lokacin da ta yi mika ba, sai ango wata katurwa kwad'uwa, ta kai girman karamin bokitin fanti.
"Goma gata nan, so nake tayi dariya, rabonta da dariya sun bayan haihuwar Nazneen."
"Kululu" cikinta ya bada sauti.
Tana son yin magana amma ina, sakar mata dundu aka yi a tsakiyar baya. "Goma ni kuma ki sosa min bayana."
Fashewa da kuka tayi, tana hada hannunta wuri guda.
"Fa yau sai kin goya ni!"
Tashi tayi zata gudu, sai ka fitsari shaaaaaaaaaa.
Ai kuwa dan karami, ya daka tsalle ya haura bayanta, a wurin ta yanki jiki ta fadi.
Dariya suka saka, suna faɗin .
"Sai aukin munafunci, ba karfin zuciya, kato turo Yaron nan, ko gobe ake ce ya tab'a Nazneen ba zai kuma ba. Ita kuma goma a tashe ta a mata kashedin babu ita babu."
"A'a babu kashedi, ina son nayi ta wasa da ita, domin ta sani yin murmushi, da ta sake fitsarin tsoro."
★
Saif.
Kusan satinsu biyu da dawowa, amma har yau Gimbi bata bashi damar zuwa Abuja ba. Idan ka ganshi zaka dauka jinya yake saboda rashin nutsuwa, sannan a bangaren Ibada, bai da raunin imani. Amma da Allah ya haɗa shi da shu'umar mace, bai san me yake ciki ba.
Tagumi yayi ya zubawa computer din gabanshi idanu. Yana tunani kamar kansa zai juya. Turo kofar aka yi ya d'ago kai, idanu biyu yayi da Nassif. "Taso muje!"
Kamar dama jira yake, ya mike a hankali yabi bayan Nassif ɗin. Har wurin motar da ya kawo Nassif ɗin, suka shiga tare da barin Makarantar, suka nufi airport........ Nassif ka daukewa Gimbi mijinta 😡🤔🙄
_KASUWA A KAI MIKI DOLE_
*Nesa tazo kusa, ko kun san Muzafa World collections. Sun zo muku da kayan zamani babu ruwanki da zuwa kasuwa. Yar uwa, kayanmu daya yake tankar da dubu. A rashin tayi akan bar raha, haka kuma bahaushe ya ce a rashin kira karen bebe ya b'ata. Tow ga dama ta same ku, domin kayanku ya tsinke a gindin kaba, kayanmu sun haɗa da Dubai Abayas, yan kunne da abin wuya, takalman Manya da Yara, lace masu kyau da inganci. Hajiya nesa da ake ce miki tazo kusa babu ruwanki da shan rana da kura, kayanki yazo inda kike! HAJIYA Abu me kyau ke sayar da kanshi*
*08130269641*
[11/19, 7:01 PM] Queen BeeBee: *NAAZNEEN❤🔥*
EXQUISITELY BEAUTIFUL
#Mai_Dambu
'Top-Notch
Season 3
Chapter -17
Nassif bai ce mishi kome ba, haka suka bar garin Lagos. Ajiyar zuciya yake saukewa lokaci zuwa lokaci, har suka sauka a garin Abuja, Basmah tazo ta dauke su. Kallo daya tayiwa Saif ta dauke kai, domin har yau tana rike da abin a ranta. A hankali ya wuce gaban motar ya zauna, Nassif ya amshi key motar ita kuma ta shiga baya, karatun Alqur'ani aka saka a motar. Babu wanda yayi mishi magana har suka isa gidan. A falo ya same yan gidan har d su Aunty Mariya da Shamsiyah, kallonshi suke kamar sun samu sabon halitta.
"Alhamdulillahi, gashi nan na kawo miki shi Gwaggo." Hawaye ne ya zubo mata ta ce mishi. "Allah ya baka abin da kake nima!" Yar yake yayi ya ce mata. "Amin Ya Allah!" Kallon Saifullahi-Khalid suka yi da ya zauna kamar wanda yake jiran a bashi umarnin ya fara magana. Duk yadda suke son yayi magana shiru yayi yana kallonsu.
"Ba zaka yi magana ba Saif?" Aunty Mariya ta tambaye shi, muryanta yana rawa alamar zata yi kuka.
Sunkuyar da kai Ummi tayi, tana wani irin kuka domin babu wanda ya kawo a ranshi Saif zai zama haka. "Bani wayarka!" Babu musu ya ciro wayar ya mikawa Nassif. Bude wayar yayi ya shiga wurin kira, ya ga babu number kowa akan wurin kira, cantact ya shiga ya samu babu number kowa sai na Gimbi.
Kiranta Nassif yayi, wayar na ta ringing. Har ya tsinke, ya kuma kira bata dauka ba sai da a kira na uku. Ta dauka tana faɗin. "Meye ke kirana?"
"Ba shi ba ne." Shiru tayi kafin ta ce mishi. "Ina mai wayar?" Saka kiran yayi a hansakuwa. Murmushi tayi sannan ta ce mishi. "Ka cire a hand free, sannan ka ba shi wayar ko na kashe kiran."
Shiru yayi kafin ya ce mata.
"Idan na ki fa?"
"Ga ku gashi, Allah ya bada sa'a." Kashe wayar tayi, shiru shiru har Khalwat ta shigo ta kawowa Ummi abinci, kanshi a sunkuye.
"Nassif kira ka bata shi!" Inji Ummi, domin tana son ji daga bakin danta, she want hear him sweet voice, hawaye na zuba mata, cike wani tausayi mishi, ta kura mishi idanu. "Princess kiyi hakuri, tafiya ce ta kamani."
"Shi ne ka tafi baka gaya min ba? Shi ne ka bawa dan iskan mutumin can wayarka? Tow ka sani na baka sati daya kacal, ka gama ka dawo min na gaya maka, na baka izinin magana da kowa har da matar da suka aura maka, sai ka yi yadda kake so da ita na kuma nanata maka sati daya kacal na baka."
"Tow nagode Allah ya saka da alkhairi." Ya shiga mata godiya kamar tayi mishi abin arziki. Babu wanda ya iya magana har ya gama wayar ya kashe, kamar an cire mishi wani abu me nauyi, haka yaji kamar an zare mishi ya kalli Ummi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 12