Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nishi da rike cikinta. Dole ya zare abin ya shiga tambyarta lafiya, ganin jinin da yake zuba, yasa shi mikewa jikin shi yana rawa, "Subhanalillahi! Bari na kawo miki kayanki muje asibiti." "A'a bari na shiga na gyara jikina " Shiga dakinta tayi, ta dauko abin kama kurwa, sannan ta fito tana wash-wash. Haka suka nufi asibiti, aka wuce da ita dakin yan haihuwa, ana shiga da ita. Aka shiga dubata domin yadda take zubda jini. Tana shiga taga yadda mata uku. Sai nurse din da take tsaye itama da tsohon ciki, a take ta kama kurwan nurse din, sannan ta kama na wata me ciki a wurin. Kafin ta kwanta ko minti goma ba ayi ba, aka kawo wata mai haihuwa. Yadda zaka san rashin imanin ya wuce yadda ake tsammani, haka Gimbi ta kama kurwan mai hannuwar nan, ta tura can kungiyarsu. Ana kaiwa ko minti ashirin ba ayi ba, matar da aka kawo ta fara wani irin girgiza da gigita, ga kan Yaro ya kunno kai. Amma ina ana ji ana gani haka aka fitar da gawar matar nan, babu ita babu cikin jikinta, don tsabar munafurci tana ganin matar ta mutu, itama ta fara wani irin jijjiga. Jini kuwa ya kara balle mata. Dakyar aka tsayar da jinin da yake zuba mata, sannan aka wuce da ita akai mata wankin ciki. Dama cikin ita kanta bata san tana da shi ba, sai da aka mata wannan aikin da zata kame shi da kyau, aka ce ta sadaukar da cikin jikinta, bayan ance ta kawo mata biyu sai gashi mata uku takai don rashin imani. Sai da aka fito da ita, tana kwance domin an yi mata alluran barci, bude idanu tayi a kungiyar ta ce musu. "Kada ku kashe su yadda za a fahimci wani abu, ku musu irin kisan da ba za a kawo wani abu a rai ba." "Kin gama naki! Saifullahi-Khalid ya zama naki, babu wanda ya isa shiga tsakaninku. Koma waye zai mutu domin babu saki babu yaji aurenku mutu karaba." "An gama ranka shi dade." Akan idanunta nurse din da ta karɓe ta, ta fita bayan ta gama aikin ranar ta tashi, tana fita ta shiga motar taxi. Basu bar bakin Asibitin ba, wata mota tazo da gudu ta murkushe taxi ɗin. Saura biyu, kallon ɗayar matar dodon yayi, ya cewa Gimbi. "Wannan a maida ta, domin Uban mijinta boka ne, itama wannan idan muka tab'ata, aikinki zai lalace." Dun haka, aka mai da sauran mata biyun. An ci mata biyu. Da cikin na Gimbi uku. Lokacin da ta farka asibitin, sake bakin zaninta tayi, kurwan mata biyu suka fita da sauri zuwa jikunansu. Lokacin da ta farka, Saifullahi-Khalid yana gefenta, sai sannu yake mata ta fara kuka kamar an mata mutuwa. Da aka gaya mata cewa tayi b'arin wata guda. "Sai ka gayawa danginka, nima Allah ya bani cikin ya fita." Shi dai rarrashinta yake da mata alƙawarin zai bata kyautar kuɗi. "Ban gane ba? Cikin nawa da na rasa zaka bani kudin don narasa shi ko murna kake don na rasa yarona?" "A'a Gimbiya ba haka nake nufi ba, amma kiyi hakuri." Yadda ta mai da al'amarin zai bata kudi sai ka dauka shi ya zubda mata cikin da gayya, nan kuwa bai san kome ba. kwananta daya aka sallame ta, niman hutu yayi suka bar kasar. Wannan ya kwantar da hankalinta. ★★ Abuja. Abuja tun Ummi tana saka idanu har ta daina saka rai da zuwan Saifullahi-Khalid, har ta hakura biki saura sati daya suka wuce Azare, amma wannan abin ya mata ciwo, babu labarin shi har aka daura auren. Nassif ya tsaya madadin Saifullahi-Khalid. Haka aka ɗauki amarya aka kaita gidan mijinta da yake cikin gidan iyayenshi. Babu wanda bai ji zafin abinda yayi ba, amma sai suka bishi da fatan shirya.... _KASUWA A KAI MIKI DOLE_ *Nesa tazo kusa, ko kun san Muzafa World collections. Sun zo muku da kayan zamani babu ruwanki da zuwa kasuwa. Yar uwa, kayanmu daya yake tankar da dubu. A rashin tayi akan bar raha, haka kuma bahaushe ya ce a rashin kira karen bebe ya b'ata. Tow ga dama ta same ku, domin kayanku ya tsinke a gindin kaba, kayanmu sun haɗa da Dubai Abayas, yan kunne da abin wuya, takalman Manya da Yara, lace masu kyau da inganci. Hajiya nesa da ake ce miki tazo kusa babu ruwanki da shan rana da kura, kayanki yazo inda kike! HAJIYA Abu me kyau ke sayar da kanshi* *08130269641* [11/19, 7:01 PM] Queen BeeBee: *NAAZNEEN* EXQUISITELY BEAUTIFUL #Mai_Dambu 'Top-Notch Season 3 بسم الله الرحمن الرحيم _Wannan shafin na kune na Team Gimbiya baby, Aka Gambi Matar Saifullahi-Khalid 😹🙄.kun san kanku kawayen Gimbi ne, kut da kut_ Chapter 14 Ita kanta Amarya daga haka ta fahimci irin mijin da ta aura, mijin da matarshi take juya lamarinsa. Tsoron da take ji kenan, tun farko sai da ta nunawa Mahaifiyarta ita tana tsoron kada ayi auren ta zama koma baya, uwar da ke mace ce da ta san akwai samuwar Allah, yasa tayi ta rarrashinta tana nuna mata girman biyayya domin itama biyayya take yi, bata da zabi da ya wuce tayiwa mahaifiyarta biyayya. Khalwat tayi hakuri ta rungume auren tunda har mahaifinta shima ya gaya mata, tayi biyayya domin shi na zai janye daga abin da ya saka ranshi ba, sannan da kunya Hajja Marih ta nime ya bada auren yarshi ga jikanta mafi soyuwa a ranta, shi yasa ya bita da addu'a. A can kuwa Gimbi sai yadda tayi da shi, gashi wani irin tsoronta yake ji, da baya iya mata magana sai abin da ta ce. Haka yasa take juya shi son ranta. Watansu daya da rabi da barin kasar, ya zuba mata idanu cikin tararradin abin da zai fito bakinta ya ce mata. "Ina son komawa bakin aikina, kin ga wata guda aka bani kada na yi wani abu su dakatar dani." Juya idanu tayi tana faɗin. "Baka yi kama da makaryaci ba, balle nace maka karya kake, amma taya zasu kore ka? Bayan sun san yadda suke amfani da kai. Saif gaya min gaskiya ko kana son zuwa cin sabon wuri ne?" Kamar munafiki haka ya sunkuyar da kanshi, jikinshi yana rawa. Domin yafi tsoronta da kome a duniya. "A'a wallahi ba haka ba ne." "Haka ne mana!" "A'a ki yarda da ni!" Yayi maganar kamar zai fashe da kuka. "Tow shi kenan." Daga haka ta bar zancen ta cigaba da abinda take, domin tasan matukar ta cigaba da magana zata zage shi ne, don haka ta share shi, har zuwa lokacin yana zaune a wurin kamar almajirinta. "Ai gara ka tashi ka tafi ka fara mana shiri ba, kada ka ce na hanaka zuwa wurin amaryarka." Bai ce mata kome ba, ya tashi yana barin dakin ta buga tsaki. Tana kananun magana. Domin ta tsani yayi batun komawa gida. ★★★ Malami Jajja. Tun ranar da Alhaji Adamu ya ɗauke yarshi suka bar gidan, ya kashe rabin tashin hankalin da yake faruwa tsakanin Innayo da Umma da Lami, domin kuwa zuwa yanzu ta masifar shiga hankalinta da zafin kishin da take yi, ba domin kome ba, sai abin kunyar da danta mafi soyuwa a ranta ya kwaso shi yasa take taka tsantsan da duk abin zai iya faruwa gudun kada a mata gori. Bayan sallah la'asar malam yana kofar gida, wurin masu karatu. Tsakar gidan babu kowa dai ita ɗaya tana wanke geron da aka surfa mata. Wayarta da take can daki tayi kara, mikewa tayi ta nufi dakin. Ɗaukar wayar tayi, ta kanga a kunnenta. "Innallilahi wa inna ilaihi raji'u, Haulatu lafiya kike kuka?" Ta kira sunan matar jikinta a mace. "Inna tunda Babawuro ya kawo yarshi, yake min abin da yaso itama yarinyar sai yadda tayi a cikin gidan ba a kwabarta ba a hanata kome, Innayo a gaji ya zauna da Yarshi zan bar mishi gidan ni da Yarana." "A'a koda wasa, sai dai ita ta bar gidan ba dai ki bar gidan ba." "Tow ya zan yi? Gara na bar mishi gidan yayi yadda yake so. Tunda ita ce mutum." "In sha Allah baki bar gidan ba, ita ce zata bar gidan. Zan kira shi in sha Allah." Da haka ta ajiye wayar, tana jin kamar ta isa abuja tayi ta zabga musu rashin mutunci. Don haka ta shiga duba wurin kira, ta hango number, kiran layinshi tayi tana jin kamar ta shiga ta wayar ta mare shi. Domin Haulatu yar Yayanta ne, auren zumunta ne. "Assalamu alaikum, ina wuni Innayo?" "Bana bukatar gaisuwarka, idan har nice na haifeka da cikina da jikina, da jinina na umarceka da ka dawo da shegiyar yarinyar nan, idan kuma kana da uwar da ta fini sai ka zabi ni ko yarka." "Ayya Innayo an biya kuɗin makarantar tafa." "Nace kan dawo da ita, tazo tayi sale manga ko unguwar Borno!" "Shi kenan!" Ya fada yana me jiran ta kashe wayar. Ajiyar zuciya ta sauke ganin ta gama da karamin case idan yarinyar ta zo sai ta tabbatar da ta hana yarinyar sukuni, sai ta azabtar da ita kamar me. ---- A can Abuja kuwa, yana falonshi da Nazneen. Tana wasa da laptop ɗinshi, yake wayar."Innayo ta ce na ka mai dani ba?" Kallonta yayi, kwana arba'in da zuwanshi da ita, tun a can ake kiranshi ana mishi congrats na samu matsayi a hukumar lafiya ta kasa, kuma tun daga lokacin da ta ganshi ta gaya mishi zai samu karin mukami. "Papa kada ka damu, in sha Allah sai ka sha mamaki. Allah zai bude maka kofofin samu sama da yadda kake yanzu." Zama yayi a gabanta sannan ya ce mata. "Baki biya min karatun da muka yi ba?" Murmushi tayi tana faɗin. "Papa zan maka bayani dalla dalla! FARILLAN ALWALA GUDA BAKWAI NE. FARILLAN ALWALA GUDA 7 NEH: 1. Niyya 2. Wanke Fuska 3. Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu 4. Shafar kai 5. Wanke kafafuwa 6. Cuccudawa 7. Gaggautawa SUNNONIN ALWALA • Wanke hannaye zuwa wuyan hannu • Kurkure baki • Shaka ruwa • Fyacewa • Juyo da shafar kai • Shafar kunnuwa • Sabunta ruwa agaresu • Jeranta tsakanin farillah MUSTAHABBAN ALWALA • Yin bismillah • Goga asuwaki • Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye • Farawa daga goshi • Jeranta sunnoni • Qaranta ruwa a nisa gabobi • Gabatar da dama kafin hau. AKAN FASALIN ALWALA • Wanda ya manta da wata farilla daga gabobinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abunda ke bayanta, idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwar abun. • Idan kuma ya bar sunna, to saiya aikata ta ita kadai bazai sake sallah ba. • Wanda kuma ya mance lam'a sai ya wanke ta ita kadai da niyya, in kuma har yayi sallah by an faruwar hakan toh sai ya sake ta • Wanda ya tuna da kurkurar baki ko shaqa ruwa bayan ya rigaya ya fara wanke fuska, to bazai dawo gare su ba har sai ya gama alwalarsa, sannan sai yayi su • Tsettsefe 'yan yatsu hannuwa yana wajaba, an so a tsettsefe 'yan yatsun qafafuwa, tsefe gemu mara dubu yana wajaba acikin alwala, tsefe gemu yana wajaba acikin wanka koh da mai duhu neh. AKAN FASALIN ALWALA (2) • Babu yana halatta ga wanda bashi da alwala yayi sallah, koh dawafi, koh ya taba al qur'ani koda acikin gafakarsa neh, bada hannunsa ba saidai idan *juzu'i* neh ga mai neman ilimi acikinsa. • Yaro a wajen taba al qur'ani kamar babba yake, amma laifin yana wuyan wanda ya bashi al qur'anin ya taba. • Wanda yayi sallah da gangan ba tare da alwala ba toh shi kafiri neh. Allah yakiya she mu." Duk wannan karatun tana yi, hankalinta yana wurin wasa. "Nazneen!" Kallonshi tayi tare da barin wasan. "Zan mai dake gida, amma zan dauka miki wanda zai na zuwa yana miki karatu, naso Tahir ne amma nasan Innayo ba zata yarda ba." "Babu kome Papa." Idanunshi ne ya cika da kwallar tausayinta. "Me yasa Jiddah taki zama da ni?" Murmushi tayi ta ce mishi. "Papa saboda ba zata samu soyayyarka ba." Ta faɗa tana gyara zamanta sannan ta ce mishi. "Papa Innayo bata sona, kuma kana tsammanin zata zo Nne ne? Ba zata sota ba ita ɗaya ba Yaran Innayo yan uwanka idan aka cire Baba Rufa'i sauran suna tare da Innayo, don haka ka daina tunanin Nne zata samu damar zama da kai." Tun da ya kawota gidan Allah ya shiga bud'a mishi ba iya da karin girma ba, har da budi ta hanyar kasuwancin da suke na haɗin gwiwa. Wani abu daya da bai sani ba, shi ne tunda ya kawo Nazneen gidan, Matar shi Haulatu hankalinta yayi mugun tashi, na farko zaren ba kalar yadin ba ne, Allah shi yayi halittar Yaranta da Nazneen, amma idan kace kyau da kwarjini Nazneen ta fi su. Tana da yara huɗu, Baba karami, sunan shi Muhammad Adamu Malami, suna kiran shi Baba karami yana da kusan shekarar goma sha takwas, Sai Munayyah wacce tafi Nazneen da shakara biyu, sai Yusrah wacce take da shekaru takwas, sai Adnan wanda shi ne kaɗai yayi welcoming din Nazneen tun kafin su iso Abuja aka gaya mata ai Nazneen ba yar Babawuro ba ce, sharri ne don ya auri Chioma shi ne ta kunso shegiya a waje ta kawo mishi. Da wannan itama ya gurbata Yaranta musamman Baba karami da Munayyah wacce take ganin kaf jikokin Malam babu wanda yake so kamar su, sai gashi zuwan Nazneen ta goge wannan mafarkin. Da farkon zuwanta, sun yi yunkurin mai da ita baiwa. Wato sakata aiki ita kuma dake tana son yan uwanta, kome suka ce mata tow take cewa, sai da tayi kusan sati biyu ta fahimci bafa don suna yan uwanta suke saka ta aiki ba, domin sun fara kiranta da wasu irin suna musamman idan suka yi baki, haka yasa ranar da ta cika sati Uku, Baba karami ya shigo cikin gidan, daga wurin wasan ball. Tana zaune ta saka tv a gaba tana kallon,. Shaun and the sheep, yana zuwa ya ce mata. "ke Bingo jeki dibo min abinci." Bata amsa mishi ba, ta cigaba da kallonta sake magana yayi ya ga da gaske bata kula shi ba, kawai ya taso ya kashe tv. "Don ubanki, tashi ki dibo min abinci" dama ire-iren iskancin da sukewa Mai aikinsu kenan, kuma uwarsu bata tsawata musu. Bata kalle shi ba ta kai hannunta gefe kamar zata kauda abu a gabanta, haka ta matsar da shi can gefe ta kafe shi a wurin, sannan ta nuna tv da yatsarta ta cigaba da kallonta. Jin motsin ana shigowa yasa ta dunkule hannunta, sake shi tayi ta cigaba da kallo, tsoro yasa shi zubewa akan gwiwarshi. Yana kallonta. Shigowar Munayyah da sport wear, ta ce mishi. "Tun dazu ka shigo baka koma ba?" Bude baki yayi zai yi magana, Nazneen tayi wani kyasta hannunta, tuni ya Hadiye maganar ya mike suka bar falorn. Munayyah tana mishi magana amma ina bai san tana magana ba, har suka fita kofar gidan. Zai nufi titin. Da gudu Adnan ya shigo cikin gidan yana faɗin. "Mommy kizo ga Yaya Baba zai tafi kan titi." Sake kyasta hannunta tayi, can a bakin titin hankalinsa ya dawo jikinshi. Da sauri wani mutum ya ture shi.daga tsakiyar titin. Ya fadi can gefe, Munayyah da take bakin get kasa motsi tayi wani irin bala'in tsoro ta kamata. Lokacin da Hajiya Haulatu ta fito daga cikin gidan ta same su a kofar gidan ana mishi fada. Sai rawa jikinshi yaƙe. "Mun gode sosai." Inji Hajiya Haulatu, sannan ta tura Yaranta suka shiga cikin gidan, Nazneen tana zaune a falon. "Ke little demon, baki san me ya faru ba ne kika zauna a wurin?" Inji Munayyah tana me kashe tv." "Na sani mana, zuwa yayi ya zane ni shine na koya mishi tarbiyyar da ya rasa." "Ke don ubanki har Tarbiyyar ce dake, yar karuwa." "Mommy ki daina zagin mahaifiyata, bata da laifi, idan akwai mai laifi Papa ne, meye tayi miki?" Ta faɗa da mugun karfin da ya haddasa daukewar wutar lantarkin falon. "Idan da tana da ra'ayin zama da Papa, baki isa yin kome ba... _KASUWA A KAI MIKI DOLE_ *Nesa tazo kusa, ko kun san Muzafa World collections. Sun zo muku da kayan zamani babu ruwanki da zuwa kasuwa. Yar uwa, kayanmu daya yake tankar da dubu. A rashin tayi akan bar raha, haka kuma bahaushe ya ce a rashin kira karen bebe ya b'ata. Tow ga dama ta same ku, domin kayanku ya tsinke a gindin kaba, kayanmu sun haɗa da Dubai Abayas, yan kunne da abin wuya, takalman Manya da Yara, lace masu kyau da inganci. Hajiya nesa da ake ce miki tazo kusa babu ruwanki da shan rana da kura, kayanki yazo inda kike! HAJIYA Abu me kyau ke sayar da kanshi* *08130269641* [11/19, 7:01 PM] Queen BeeBee: *NAAZNEEN❤🔥* EXQUISITELY BEAUTIFUL #Mai_Dambu 'Top-Notch Season 3 بسم الله الرحمن الرحيم Chapter 15 Curewa wuri guda Hajiya Haulatu sukayi da yaranta, domin Nazneen ta zame musu abin tsoron, juyawa tayi ta nufi dakinsu. Duk yadda take sonsu haka take hakura da abin da suke mata, amma ba zata yarda su tab'a mata Nne ba. Alhaji Adamu yana wurin aiki, Hajiya Haulatu ta kira shi tana kuka, balbaleta yayi da fada, ganin ba zata yi magana ba ya kashe wayar, can ya kuma kiranta shi ne ta ce mishi. "Yarinyar nan da ka kawo." Bai gama ji ba, ya kashe wayar. Tasan zai zo shi yasa ta shirya haka, aikuwa minti arba'in ya kawo shi gidan, lokacin da ya zo ya gansu a falon. "Me ya faru?" Fashewa sukayi da kuka, ta ce mishi "meyasa kasan yarinyar nan ba mutum ba ce, ka kawo mana ita?" Sharce hawaye tayi ta cigaba da cewa. "Saura kiris, ta kashe Baba karami." Kallon karin bayani yayi mata a rude. "Kamar ya?" Ya cilla mata tambayar, yana kallon Baba karami da yake nad'e cikin bargo, "ban san me tayi mishi ba." "Papa...!" Ta kira sunan a shagwabe. Da dan sauri ya juyo yana kallonta har ta iso wurinshi, durkusawa yayi ya bude mata hannuwan shi. Shiga jikinshi tayi tana faɗin. "Kasan Momma ta hanani shigar mata kitchen, shi ne ya zo ya kashe min tv. Ni bani na mishi kome ba, Angel of guardians ne yayi switch ɗinsa." Sake rungumeta yayi yana shafa bayanta. Ya d'ago kai yayi yana faɗin. "Daga yau kada wani ya kuma takura mata, idan haka ya faru zan dauki mataki." Wannan abin ya b'ata musu rai, dama suna cike da haushin lokacin da aka kawota office din Alhaji Adamu an yi bikin kara mishi girma, kawai da ya tashi tafiya Nazneen ya dauka da Hajiya Haulatu, karshe Hajiya haulata ganin ba za a je da yaranta ba, tace ta fasa zuwa dole aka tafi tare dasu. Abin da ya musu ciwo har suka ji kamar da basu biyo Daddy ɗinsu ba, yadda yayi ta gabatar da Nazneen a gaban kowa da nuna ita yarshi ce mai daraja. Ga kyau ga nutsuwa, Munayyah tana kallon wannan kayan bakincikin ta cewa Uwarta. "ina ji kamar na kasheta!" Rike ta uwar tayi tana girgiza mata kai. Ire-iren waɗannan abin yasa suka tsaneta, gashi babu halin a tab'ata Aljanunta zasu dauki mataki akanka. ....... Kallonshi tayi sannan ta ce mishi. "Ni ba zan koma Bauchi ba, i change my mind." Ware idanu yayi yana faɗin. "Me?" "Ba zanje bauchi ba!" "Saboda me?" "Allah bani zuwa bauchi, zan gayawa Malam." Ta faɗa tana dariya, jan hancinta yayi yana faɗin. "Zaki hada ni da kawarki." "Ba zan koma Bauchi ba.". "Ki koma na miki alqawarin kai ki London, idan kika gama primary school." Murmushi tayi, tana faɗin. "Papa da gaske?" "In sha Allah, da gaske." Tsalle ta fara yi, tana jin wani irin dad'i. "Zaki bauchi?" "Eh zani." Ya gama yanke hukuncin kaita can, domin yasan Innayo ba zata tab'a barin, yayi abin da ya dace ba, sannan idan tana nan abuja ba zai taba samun zaman lafiya ba, don haka ya saka a ranshi kafin ya tafi da ita bauchi, zai tattauna da Abdullahi domin ta haka zai nisanta Yarshi daga fitinar yan uwanshi da Matarshi da Mahaifiyarshi. A duk lokacin da ya kalli yarinyar, sabon soyayyar mahaifiyarta yake kara cika mishi zuciya, yana ji kamar ya dauke yarshi ya boye ta. Bai auri Chioma domin yana sonta ba, abu biyu ya ja hankalinshi, kyanta da laluranta. Tunda ya mata jinya na tsawon kwanaki goma, shi kenan Yarinyar ta makale mishi. A duk lokacin da ya tuna da haka, addu'a yake Allah ya tsare mishi Yarinyar shi kada ta faɗa irin rayuwar da Uwarta tayi. Mikewa yayi ya nufi dakinshi. Yana zaune Hajiya haulatu ta shigo, tana murmushi. "Daddy ka dawo ne?" "Eh na dawo." Shiru tayi kafin ta ce mishi. "Batun zuwan mu Dubai da Yara baka ce kome ba." Kallonta yayi na wasu lokuta kafin ya ce mata. "Na soke zuwan ne, dama domin Nazneen zan biya. Yanzu kuwa na fasa." "Amma!" "Dakata min, kin san dai nace na fasa ko kuma bani da niyyar kuje. Tunda kin zabi haka. Ba damuwa ina ganin zaku koma Bauchi ke da yaran suyi karatun a can. " "Bauchi!" Ta faɗa tana mikewa, "eh bauchi, ko ba daga can kuka dawo nan ba?" "Amma karatunsu fa?" "Akwai makarantu a can." Daga haka ya ajiye maganar bai kuma tanka mata ba, fita tayi fuuuu, ya kira Malam ya gaya mishi, shima dake yana bala'in tausayinta tare da soyayyarta, haka yasa ya bawa Adamun goyan bayan, sannan ya gaya masa cewa zuwa duk wata ya kama shi kenan. Sosa kai yayi yana faɗin. "Eh malam, amma ina son na kara aure ne." Shiru Malam yayi kafin ya ce masa. "Tow Allah ya tabbatar da alkhairi, amma kasan yana da kyau ka nime yar mutunci ko?" "Eh malam, yar Dass ce tana aiki a nan bauchi babban asibiti. Yar gidan Alhaji Nuhu Dass ce." "Masha Allah, shi kenan." Da haka suka ajiye maganar, za a tafi nima mishi auren, kanshi a sunkuye. Bai san zuwan ba, sai dai kamar kiftawa da Bismillah, ya ga kamar wani bakin mutum a kanshi, a dan tsorace ya D'ago kai yana fadin. "Kin bani tsoro." "Papa! Kana son auren Dayyiba ko? Ita ai tafi Momma mugun nufi, gara ka hakura da ita. Kayi maneji da Momma. Amma Dayyiba shaidaniya ce fitinaniyar mace, idan ka aureta zaku sha wahala ne." "Ya aka yi kika san sunanta?" "Ina jin kana gayawa Baba Malam zaka kara aure, sannan a kaina kake son ka maida Momma bauchi ko? Kyaleta ta zauna da kai a nan, ita kuma wancan matar da kanta zata kiraka gobe ta ce ta fasa aurenka "

Chapter 8 of 12