zauna tana kallon yadda kowa yake kallonta, ita ba mamaki yau irin mafarkin da tayi kenan, zuciyarta cike da tsoro ta d'ago kai zata yi magana, ta ga an juye abin da yake cikin tukunyar nan, sun hada da kai da kafar dan mutum, kayan cikin dan adam, gudan jariri, a cikin mahaifarshi. Sai mace da ciki. Bata san lokacin da ta sake komawa wani sumar ba. Domin ta masifar razana, haka ya kuma daka tsalle akanta, ta bude idanunta. Sannan ya ce mata , "kin zata zaki samu nasarar rayuwa ne da tsoro? Ko ance miki shiga wancan kasungurmin dajin da kika yi wani abin mamaki ne? Can ba zai tab'a miki aiki dawamamme ba, nan kuwa zamu miki aiki dawamamme. Ki ajiye a ranki, babu gaggawa babu shakkar wani zai lalata miki shiri, da kanki zaki sarrafa shi yadda kike so ba tare da wani ya saka wasu sun miki ba. Maza ga D'a a cikin mahaifarshi ki dauka, ki cinye kada ki rage min ko kashi ne ki cinye. "
Duk yadda take son yin musu, ta kasa domin tsintar kanta tayi da rarrafawa har gaban tiren ta saka hannu tana ci, bibiyu har bata san yadda akayi take durawa ba. Sai da ta gama cinyewa tass, har ta riga kowa komawa gefe, domin jin wani irin abu yana bin jikinta, juyi take a wurin har sai da ta rikide zuwa farar mage, ta d'ago kai tana gurnani. Murmushi Mamanta tayi tana me rikidewa magen, amma bakakiririn.
Doro suka yiwa juna, kafin suka fara sunsuna juna. Sannan suka koma mutanensu, da matukar gajiya Gimbi ta zube jikin Mamanta. "Shugaba aiki yayi kyau, ya batun mijinta?"
"Babu wanda iya isa kama mata shi, sai ita. Domin kuwa mutum ne me rikon addini yana da yawan ibada. Ita tasan lokacin da zata kama shi, ai mace ce ita idan ta sake ya kubuce mata ba zata tab'a nasara ba."
"Shugaba taya zata samu mace me cikin?" Kura mata ido yayi kafin ya ce mata. "Me kika gaya mata kafin kizo da ita? Haka zata bi, mu mayyu muna da tarbiyya da iya mu'amala da kowa. Sannan ki gaya mata, ba kowani kurwa zata kawo min ba, ga tukunyarta can, zan tura mata gidanta. Sannan wanan karamin madubin ta ajiye tunda ta daurawa ranta son yawo."
"An gama!" Basu watse ba, sai da suka ji garin yayi wani irin sanyi, sannan masu d'ana tarko, masu mika bukatarsu suna mikawa, kafin suka watse. Maman Gimbi kuwa, ɗaukar yarta tayi suka nufi takalminsu, suka bar dajin a guje. Tunda bukata ta biya me kuma rage mata.
★★
Jajja.
A bisa al'adar Malam, kafin ya kwanta sai yayi karatu kafin ya kwanta. Kuma koda kuwa barci ne ba zai tab'a yi ba, sai yayi wannan karatun. Yau girkin Hajiya Lami ce. Tunda ta ga yana karatu ta wuce dakinshi ta kwanta. Tunda goshin asuba zata koma daki. Yana cikin karatun barci me karfi ya fara fisgarshi. A wurin ya kwanta, barci me nauyi yayi gaba da shi.
Midnight.
A kofar gida yake zaune, yana tsakiyar almajirai ana karatu, ya hango wata mace hannunta rike da yarinya, kallon yarinyar yake sosai amma duhu ya hana shi ganin fuskarta, balle na matar. Abin da ya iya fahimta kawai shi ne kan yarinyar inuwowi biyu baki da fari, har bakar inuwar tana son rinjayar farar inuwar, yadda matar take tafiya ba haka yarinyar take tafiya ba, kamar bata taka kasa, asalin tafiyar a iska take yi, a raunane yake kallonsu har suka iso kofar gidan. Matar ta mika mishi yarinyar tana kuka. Sautin kukan yarinyar da takeyi yaƙe jin shi har tsakiyar kanshi, ambaton sunan Allah yayi, wanda yayi sanadin bude idanunshi. Yana kallon inda yake kwance, dafe goshinsa yayi sannan ya mike, jikinshi a mace. Ya nufi dakinshi, ya sami Hajiya Lami tana barci don haka ban daki ya shiga yayi alola sannan ya fito ya gabatar da sallar nafilla tun tashinsa.
Bai yarda ya tashi ba, sai da ya kuma hada da salatul istahara, sannan ya nufi masallaci. Da yakinin Allah yana sane da kome. Kuma shi zai kawo mishi dauki. Bai da tsimi bai da dabara. Anan yayi sallah asuba har gari ya waye, suka fito aka fara karatu. Karfe bakwai da wani abu aka tashi saboda masu zuwa boko. Sannan ya shiga cikin gidan ya kwanta kafin tara yayi walaha, ya nufi fada.
Yana shiga cikin gidan, ya bi kowani daki yana gaishesu. Dakin Innayo ya fara shiga, sannan ya fita ya nufi dakin Goma, bayan sun gaisa ta ce mishi. "malam ina son zuwa jahun na duba yar Kanwata, dazu Jamila take gaya min tana asibiti batajin dad'i." "Allah ya bata lafiya, sai kin dawo."
"Amin!" Ya juya zai fita, ta ce mishi "Malam ban gaya maka ba." Juyawa yayi yana faɗin. "Ina jinki!"
"Wai dama Hadiza ce tace, na roka mata Baba karami ya tura mata wani abu, zata biya kuɗin makarantar yaranta ne?" Shiru yayi yana kallonta, kafin ya ce mata.
"Amma goma baki da tausayi, yaron nan yayi iya bakin ƙoƙarinshi wancan lokacin ya bata kudi ta kara jari, karewa a shagon shi take amsar kaya tana sayarwa, ta cinye kudin kuma ta koma ya bata, ai ya dace ki mata fada, ta adana na hannaunta gara ita aiki take, shi kuma kasuwanci ne da taimakon Yan uwanshi maza, ai Yaran suna da ubansu idan ba zai iya ba ya sakota zan rike ta da ita da yaranta. Ai ba gajiya nayi da riƙesu ba."
"Ka dai yi hakuri, a mishi magana ya taimaka domin nayi mishi magana ya ce zai duba, ban san wani irin dubawa zai yi ba." Ta faɗa tana saukar da kai, Ita fa Goma tana da saukin kai da iya biyayya matsalarta daya munafunci, wanda kowa yasan da haka, amma kuma dake mace ce da take iya kyautatawa yasa ake mata uzuri da halinta amma tabbas babu wanda bai gaji da ita ba, sannan tana da wani irin hali duk munafuncinta bata kaunar ka san halin da take ciki, balle kuma akan Yaranta tana da son taji na wani, amma ita ko ka kai kaska naci baka tab'a sanin halin da take ciki. A bisa tsarin Alhaji Adamu ko Abdullahi ya dace ta samu da zancen ko ta ce Malam ya musu magana amma kada wani yasan halin da take ciki yasa tayi gum su yi kominsu ita da Yaranta.
Sannan ta gefe guda, Jamilah tana karawa borno masu, domin itama ba ƙaramar makira ba ce. Don ma Allah ya taimaka Umma da Hajiya Lami, basu da sauki tass suke mata a gaban uban ko uwarsu.
Wannan yasa gidan ake zaune da karamin zaman lafiya, Bayan malam ya bar dakin Goma, Jamilah tana kallonshi. Ya shiga dakin Umma yana faɗin. "Sa'adatu!" Dake Umma mace ce me yawan jiki, wanda hakan ya haifar mata da ciwon kafa. Ta fito daga uwar dakinta, tana me zama a kujeran falonta. "Barka da asuba, Malam" "yawwa barka dai." Ya kalleta yana faɗin. "Kunyi waya da Alhaji kuwa?" "Mun yi dashi, yanzu ma haka ina niman Fatu ce. Ya ce min Attahiru zaizo bautar ƙasa watan nan, ina son naji kan zancen ne domin Manu yaki tsayawa muyi magana da shi."
Murmushin jin dadi yayi yana faɗin. "Taya zai yarda ku ji zancen a bakinshi yana uba guda? Kawai abin da ya kawo ni, shi ne a je a gyara wancan dakunan samarin tunda duk basu nan,. A saka mishi duk abinda yake bukata."
Kallonshi tayi tana faɗin.
"Malam ni kuwa ina son." Sai tayi shiru, sannan ta ce mishi. "Jiya nayi mafarkin zamu yi baƙi." Kura mata idanu yayi sannan ya gyara zamanshi. "Nima haka, sai dai ban san daga inda zasu zo ba."
Wayar hannunta ce tayi kara, ta kalla sannan ta ce mishi. "Yawwa ga fatun nan ma!" Mikewa yayi ya fita zuwa dakin Hajiya Lami. Yana shiga ta ajiye miishi abin karyawar shi tana faɗin. "Malam yau ba zaka fada bane?"
"Zan je." Ya faɗa yana cigaba da karyawa. Har ya gama tana zaune, ya ce mata. "Jiya mun fara magana kafin na dawo kinyi barci, shi yasa ban tashe ki ba." Gyara zama tayi, tare da tattara nutsuwarta ta zuba a kansa ta ce mishi. "Eh dama akan maganar, Kungiyarmu ta fowan ne nace na maka magana a kai, zasu shiga garuruwan azare, itas gadau, shira, gamawa, odubo, bulkacuwa." Kura mata idanu yayi ya ce mata. "a cikin kwana nawa?" Shiru tayi kafin ta ce mishi. "sati daya!" Shiru yayi, kafin ya ce mata. "Kina son zuwa ne?" Girgiza kai tayi tana faɗin. "Da suka zabe ni, sai da na gaya musu cewa, bani da tabbas a zuwa na kawai su zabi wasu."
"Allah ya dawo daku lafiya, ya tsare kunsa sharrin ƙarfe."
"Ka amince kenan?" Murmushi ya mata yana cewa. "Ai dole na" "a'a babu dole Malam, idan baka son zuwana, ai dama ban daurawa kaina ba."
Dariya yayi irin na manyan, suka tab'a hira kafin ta tafi dakinshi ta haɗa masa ruwan wanka.
★★
Gidansu Gimbi.
Har gari ya waye, Gimbi tana can dakinta kamar gawa, Uwarta kuwa tana sane da ita, ta cigaba da aikinta tare da hada kunun zak'inta, wanda ya ji had'in maita da siddabaru.
Gimbiya Baby Yusuf Bogoro.
Iyayenta sayawa ne, daga Bogoro local government. Gimbiya tana da yayu maza biyu mace daya, waɗanda suke uba daya.
Kabiru, Falalu, Saratu, sai ita Gimbi amma sauran ukun Uwarsu daban, domin Malam Yusuf ya muslunta da jimawa duk da kowa yasan yadda sayawa suke da mugun taurin kai da kafiya, haka yasa basu cika dogon sha'ani da kowa ba, sai kabilarsu da tsirarun hausawa ko fulani.
Mahaifiyarsu Kabiru rasuwa tayi, wanda kafin rasuwarta taji labarin mijinta yana niman budurwa, wanda bata so ba amma sanin mijinta ba zai tab'a rabuwa da ita ba, yasa ta kwantar da hankalinta, wata shekarar da akayi kirsimeti, aka kawo musu abinci daga bayan gida su, sannan dan aiken yake gaya mata cewa, budurwan mijinta ne, yasa taji haushi ta ce maza ya maida mata abincin, ba za a karba ba. Ai kuwa sai ga Wasube wato maman Gimbi, suka tawo da kawarta balla, suka tawo akayi ta faɗa kaca-kaca, cikin fushi ta dauki murfin tukunya ta buga mata a goshi. "Kina buga min murfin tukunya!" "An buga miki, me zaki yi?" "Babu" daga haka ta fita, bayan anyi rabo da kyar, ita Wasube a tunaninta Malam Yusuf zai ɗauki mataki ne a kan matarshi, sai ta ga ma ya daina kulata. Haka ya fusata ta har ta kai da ta kama kurwan Mamansu Kabiru , bata mata kamun wasa ba, domin tana kamata ta murde wuyarta, ta kashe. Anyi haka da sati daya ranar new year, tace ga garinku. Ko sati Uku ba tayi da rasuwa ba, sai maganar aurenshi da Wasube.
Abin ya mugun bawa Yaranshi haushi, wanda ya kai suka bar gidan suka koma wurin kakansu da yake Kafin tafawa. Ita kuma Wasube rabo ya kawota domin ana auren sai cikin gimbiya Baby. suke kiranta da Gimbi. Duk inda ake niman namiji Malam Yusuf ya kai, domin yana aiki da IDC. Duk da shi karamin Ma'aikici ne, amma yana iya kokarin shi, saboda ko su Kabiru ma yana musu aike.....
[11/19, 7:01 PM] Queen BeeBee: *NAAZNEEN❤🔥*
EXQUISITELY BEAUTIFUL
#Mai_Dambu
بسم الله الرحمن الرحيم
Chapter-5
Saifullahi-Khalid
Yayi kokarin kula da Yaranshi, amma Wasube sai da ta shiga ta fita ta raba shi da Yaranshi sannan hankalinta ya kwanta. Sannan ta cigaba da baza mulkinta daga ita sai Yarta. Wasube sunan ta musulunta ne amma muguwar mace ce da bata yarda da kowa ba sai kanta da Yarta, wacce Allah ya yanka mata ita da arha, Gimbi tana da kyau domin bakar mace ce me kyau da haiba, tana da wani irin nutsuwa da mugun naci, duk abinda take so tana nimanshi ne idanu a rufe, tun tana shekara goma a duniya ta fahimci Uwarta Mayya ce, amma bata taɓa sha'awar zama mayya ba.
Gashi sai Allah ya daurawa Uwar sonta da bin duk abinda takeso kamar me, domin duk abinda take so uwar na mata. Duk da aikin Malam Yusuf Bogoro, amma zaka sha mamaki yadda Wasube take juya kudi kamar wata matar Attajiri. Ga wata bakar dabi'a ta ta na zuwa kasuwar kauye sayan dawar kunun zak'i. Duk da kuwa an san dawa take sayowa amma ita fa ba dawar bace, kurwan mutane take kamawa ta kai a juye mata dawa, kuma abin mamaki yadda kununta yake karewa duk sati. Musamman ranar Laraba da Alhamis ranar kasuwar mararaba da kasuwar Dass, babban j5 ake cikawa da manyan kuloli ana kaiwa kasuwar, ta sayo dawa ta kai musu kunun zak'in.
Ranar juma'a kuwa, kasuwar cikin garin Bauchi da ake ci na C&C, shima anan tattara kurwan mutane take tana sayar musu da kunun, ranar lahadi kasuwar durum, duk yadda kake tsammanin Wasube ta wuce tunanin me tunani, lokacin da Gimbi take aji uku na secondry school, wani yaro ya kamata yayi mata duka, domin tayi rashin kunya, abin da ya janyo haka shi ne tayi kwalliya kuma ta makara, ya ce ta goge taki, shine fa ya zane ta sosai. Ai juyawa tayi ta koma gida tana kuka, koda uwar ta ganta ta ga bulalar yadda ya mata burtutu. Sai da ranta ya b'aci. Don haka ranar juma'a taje makarantar da Gimbi don sai da tayi kwana uku a gida babu lafiya, daga nesa uwar ta tambaye ta Yaron. Nuna mata shi tayi.
Murmushi tayi sannan ta juya, tana me cire kurwanshi a jikinshi. Sannan ta juya tana faɗin. "Dan iska, gaka da nauyi kamar buhun sumiti!" Dama ba ta kama shi don ta bada shi ba, ta kama shine don ta rama abin da yayiwa Yarta. Aikuwa ta nufi kitchen ɗinta, ta daure shi a gefen murhu ta ajiye shi.
Yaron yana ganin Gimbi ya dauke kai, sakamakon sarawa da kanshi yayi, dakyar aka gama tsaron lattin da shi, ya koma aji ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Jikinshi a matukar gajiye. Yaron nan ya takura har aka tashi break. Bai fita ba, sai dai abokansa da suka kawo miishi abin break. Domin saurayi ne, lokacin da aka tashi yaron nan da kyar yaƙe takawa, har ya isa gida, tunda ya zube a kofar dakin Mamarsu bai kuma farkawa ba, sai la'asar.
---- lokacin da Gimbi ta dawo ta samu uwar ta gyara nama, dama tasan matukar taga Uwarta a gida kuma tana gyara nama, tasan ba ordinary nama ba ne, don haka da sauri ta isa gabanta ta ce mata. "Mamana ina cewa ba Namar sagir ba ne?" Dariya uwar tayi tana faɗin. "Ga dan banza can, na daure shi ai ba zai kuma damunki ba, sai ya shekara uku anan kafin na sake shi."
"A'a ni ba haka nake so ba, zaa ce don ya dake ni aka mishi haka, sannan idan aka gano ke mayya ce babu me ƙawance da ni, yayi kwanaki ki sake shi. Domin bana son ko fata tab'a mutane a kaina!'
Washe bakin Wasube tayi tana faɗin. "Chab! Kunga zuciyar Muslunci, shi kenan zan sake shi amma sai na wahalar da dan banza domin ba karamin wahala na sha wurin dauko shi ba." Ta faɗa tana hararan sagir da yake takure wuri guda, abin tausayi.
Haka don mugunta Wasube ta wura wuta, kurwanshi yayi ta azabtuwa da zafin wuta sai da ta ga ya kwanta a wurin baya numfashi, ta dauke shi zuwa wurin tukwanen kunun zak'inta, tayi ta kwana mishi ruwan randan kasa, me sanyi kalau.
Sannan ta daure shi, a wurin ta barshi. A can gidansu Sagir, ganin yadda yake suma iyayenshi suka nufi asibiti da shi, inda aka yi ta mishi karin ruwa da allurai, amma babu canji. Sai jikin shi ya dauki zafi na wasu awanin kafin kuma ya dauki sanyi kalau.
Haka Wasube tayi ta wahalar da Yaron nan, a makaranta Gimbi taji labarin halin da yake ciki, tana dawowa uwar zata fita, tsare mata hanya tayi, fuska babu wasa ta ce mata. "Muje ki sake mishi kurwanshi!" Yadda tayi maganar da karfi, yasa Wasube rufe mata baki, ta ce mata. "Bafa kashe shi zanyi ba, dukar da ya miki nake rama miki." Cikin kuka da hargagi ta ce mata. "Bana so! Ina da rayuwa da farinciki, idan aka san cewa nice silar kome, ya kike so nayi? Don Allah ki sake shi." Juyawa uwar tayi ta nufi gindin randar sanyi ta kunce shi.
Sannan ta ce mata. "Shi kenan, na kunce shi." "Muje ki nuna min!" Haka suka nufi wurin, ta ga wani karamin tsuntsu, ya kasa tashi. Daukarshi tayi tana faɗin. "Don Allah dame haka yayi kama? Mamana mutum ne fa, kika mishi haka? Ya za ayi ta tashi."
"Ki cilla shi sama!" Kallon tsuntsun tayi tana kuka, domin duk rashin mutuncinta bata kai Uwarta ba, saima dai uwar da Allah ya daura mata soyayyar yar yasa take biye mata, sannan take kaunar yar kamar me, domin bata jin akwai abin da take so bayan Gimbi. Sai rayuwarta shi yasa take bin umarnin Yar, tunda ta sake Sagir yaron ya sha jinya sosai kafin yayi lafiya domin daga baya aka ji labarin ai mayyu suka kama shi..
Tun daga lokacin Gimbi bata kuma yin abin da zai saka wani a hatsari ba, domin tasan ko kuka tayi uwar sai ta bi diddigin kukan, balle kuma faɗa shi ne ta daina yarda tayi rigima da kowa asalima taki ƙawance da kowa don kada ta saka su cikin matsala. Shekaru sun ja ta gama secondry, kai tsaye ta samu Federal polytechnic Bauchi, inda take karantar Business Admistration, a wannan lokacin suka hadu da Siyamah da Linah yasaka Gimbi sake jin ita wata ce, domin suma Yan mata ne, na gararin rayuwa gashi basu jin magana domin ita dai Gimbi tana da kokarin yin abin da ya kawo ta , banbancinta dasu kenan, su kuma basa karatu sai bin maza da yawon shashanci.
Duk wannan abin da suke, ita kan bata taɓa yarda ta bawa namiji kanta, domin tun bata kai haka ba, Uwar ke gaya mata advantage na virgin ɗinta, shine sword din da zata yi Amfani da shi wurin mallakar abin da take so.
Haka yasa Gimbi ta ajiye aranta, ba zata bawa Kowa kanta ba, sai wanda take ganin ya dace da ita. Haka yasa baki daya take da mugun kamun kai da nutsuwa, idan ka cire kawayenta masu shegen rawan kai da niman suna.
Bayan ta gama diploma na farko, sannan ta shiga yin na biyu, shima ta gama ckin nasara, har ta tafi bautar ƙasa. Tana dawowa ta hadu da wani dan majalisar karamar hukumar Bogoro, sosai yake kashe mata kudi, har an fara maganar aure. Manyan sun shiga cikin maganar, Linah ta gayyace ta wani biki, a nan suka hadu da Saifullahi-Khalid Mansur Katagum, D'a ga Ambassador Mansur Saifullah katagum.
WAYE SHI...?
Kafin mahaifinshi ya zama jakadan Nigeria a masar, Tsohon shugaban Jami'ar Alkahira ne, sannan ya jagoranci wasu zabubbukan da aka yi a Nigeria, sannan wani abin mamaki, shine Ambassador Mansur Saifullah katagum ya auri yar kasar Egpyt Samiha Onsi Sawiri, wacce suke zaune a garin Abuja ita da Yaranta. Haka ya faru ne sakamakon can Alhaji Mansur Katagum yayi karatun degree dinshi na farko.
Sannan suka hadu, ita kuma ta fito Babban gida ne domin babu wanda bai san gidansu ba, Attajiran larabawan Egpyt ne masu tarin arzikin gado, Yayanta Omar Onsi Sawiris da kaninta Naguib Sawiris.
Familyn suna da karfi sosai, sannan sun bawa Alhaji Mansur Katagum auren yarsu ce, domin tana sonshi don suna da dabi'ar idan kana son abu ba zamu hanaka ba.
Anyi bikin aure tare da wanta Omar Onsi Sawiris, wani ikon Allah kusan a tare suka haifi Yaransu lokaci guda. d'an Samiha ya ci sunan kakansa. Saifullahi-Khalid haka kakansa ta wurin Uwa tace a kira shi da sunayen biyu. Shi kuma ɗan Omar aka saka miishi Nassef Omer Sewiris, a tare suka taso kome nasu ɗaya.
Don haka duk inda daya ya wurga kafa daya yana wurin, Saifullahi-Khalid yana aiki a lagos, a jami'ar Lagos, inda yake koyar da Islamic Science, kuma yana kasuwancin tsakanin kasashen turai. Da nan Egpyt ɗin. Kuma har lokacin bai yi aure ba, Saifullahi-Khalid yana da kanne mata biyu da namiji ɗaya, sannan kafin Mahaifiyarshi Mahaifinsu yayi aure matar ta rasu, ta bar Yara mata biyu.
Suma kuma suna auren manyan mutane, Saifullahi-Khalid dan shekaru talatin da takwas a duniya, yana cikin manyan Malaman Addinin musulunci sosai, domin yana jagorantar tafsir duk shekara a nan Azare central Mosqus.
Ya biyo mata biyu,
Aunty Mariya, Shamsiyah, sai kanenshi, Jasrah da Basmah, sai karaminsu Autansu Hashim.
A duniya family nan, suna son junansu. Domin Samiha ta koya musu tausayin juna.
Aunty Mariya tana auren Sarkin Fulanin Gombe, Dr Bashir Buba Yero da Yaranta guda uku, maza biyu mace daya. Afif da Arif, sai Sharifah. Tana da kishiyoyi itama.
Sai Shamsiyah tana auren Babban accountant general Alhaji Musa Muhmud Shira, na shugaban kasa domin mahaifinsa sune manyan mukararaban gwamnatin Nijeriya, suna can Abuja da Yaranta hudu, namiji ɗaya Mata uku, Ummu Kulsum, Aymanah, Amatullah. Sai Muhmud.
Jasrah tana auren Dan Sarkin Adamawa, babban sojan ruwa, suna zaune a lagos Yarta daya, Basmah tana bautar ƙasa domin basu aure sai sun kammala bautar kasarsu, amma an kai tambayar aurenta da kome bikin ya rage, zata auri Dan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Dr Hassan yame, yan Bauchi ne fulanin Yame ne.
Rayuwarsu kafin haduwar Gimbi da Saifullahi-Khalid, yana zaune cikin yanci da salama.
A dawo labari.
Tunda Gimbi ta ganshi, ta kuma ji yadda MC yake fadar matsayinshi yasa kara kwadaita mata sai ta nime shi, sai da aka bashi damar bude taro da addu'a, ya mike Nassef ya mike zai bishi. Juyawa yayi ya ce mishi. "Koma ka zauna!" Tab'e baki yayi ya koma ya zauna yana kallon shi. Koda ya isa wurin da zai bude taron da addu'a. Sai da yayi addu'a, jin muryanshi kawai Gimbi ta ji baki daya hankalinta ya bar jikinta. Kamar tayi hakuri, karshe tashi tayi ta bar hall ɗin, zuciyarta tana wani bugawa kamar zata faso kirjinta. Tana tsaye har suka gama abin da za su suka fito, tana kallonshi, wani irin azazzalar tsiya zuciyarta take mata, bata san lokacin da ta fito ba, daga inda take tsaye ta iso har inda suke. "Please ko zaku rage min hanya?" Dake a zaranda hotel aka yi taron, babu wanda ya kalli inda take balle ta saka ran zata samu damar shiga motarsu. Haka suka shiga zasu tashi motar, Saifullahi-Khalid din ya sauke glass zai magana Nassef da bai ɗaukar renin hankalin ya ce mata.
"Maybe fitowa zamu yi mu dauke ki ko?" Jin haka yasa ta nufi motar da sauri ta shiga, tana sauke ajiyar zuciya cikin harshen larabci ya ce mishi.
"Me yasa baka da hakuri? "
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 12