shi da kyau cike da takaici ya ce. "Amma kai daga dan Iska babu biyunka? Anan zaka ishe mutane da Allah ya ce Annabi ya ce, dan iska kazo da girmanka kana narkewa kamar jinjiri? Goggo kyale wannan gardin lafiyarshi lau fa, aure yaƙe son a mishi."
Yatsina fuska tayi, ta ce mishi.
"Kai dai da baka san ciwo ba, amma yaron da babu ruwanshi yana fama da ciwo bai gayawa kowa ba, ai abin tashin hankali ne. Sannu kaji, Shamsiyah dariyar me kike yi ne? Ce mishi sannu mana!"
Kunshe dariyarta tayi tana kallon d'a da Uwa, dama ai an saba. Domin ita Umminsu matukar kana son ganin rikicewarta, tow kace Saifullahi-Khalid bai da lafiya, kai ko ciwo kake kana suma kana farfaɗowa abu ɗaya Umminsu zata ce, ka fiya ragwanta sannan ita bata ga ciwon da ake ta tashin hankalin baka da lafiya ba, shi yasa duk wanda bai da lafiya. Yake kokarin boyewa, domin yanzu Hajiya Samiha zata ce ba ciwo ba ne, son a kashe kudi asibiti ne kawai. Amma Saifullahi-Khalid yana cewa bai da lafiya.
Kaf mutanen Egpyt sai an gaya musu bai da lafiya, sannan an kira mutanen Azare a gaya musu Saifullahi-Khalid bai da lafiya. Tow har likitan da yake asibitin sai Ummi tace bai da imani,. Yana yiwa yaro karami mugunta.
Diban porridge din take tana bashi, yana sha yana narke mata, ta tab'a goshinsa ya kai sau goma. Kamar ta cire ciwon a jikinshi ta daurawa kanta, domin tasan bai da lafiya, kuma tunda ya ce bai da lafiya da gaske bai da lafiya ne.
A hankali ta mika mishi ruwa, daidai shigowar Alhaji Mansur Katagum da Likitan iyalinshi.
Mikewa tayi tana faɗin.
"Yawwa ka ganshi nan, bai da lafiya."
"Samiha!" Alhaji Mansur ya riko hannunta, kallonshi tayi, sannan ya nuna mata wuri ta zauna. "Bar shi yayi aikinshi." "Amm Anur haka." Rufe mata baki yayi, sannan ya ce mata.
"Kiyi hakuri!"
Bude yar box din da yazo da shi likitan yayi, ya shiga tambayar shi mek damunshi yana bashi amsa, har ya gama sannan ya koma ya debi jininshi ya, kalli Saifullahi-Khalid ya ce masa.
"Zan saka maka ruwa, sannan idan da hali ko muje asibiti ne sai a maka hoton kirjinka da yake ciwon."
"Anur ka ji kwantar da shi za ayi, kun dauka ciwon Habibi na wasa ne."
"Dr kuje da shi, Nassif ku tafi gamu nan zuwa."
Haka kuwa suka tafi, Ummi ta fi kowa rikicewa, wasa-wasa sai da aka kwantar da shi a gadon asibiti. An bincika kirjinshi babu kome, amma fa yana jin jiki domin asirin ba karamin shiga jikinshi yayi ba.
Haka suka cigaba da jinyarshi tsawon kwanaki goma sha huɗu, sannan aka sallame shi.
A hankali sauki da sauyi yayi ta samu shi, duk da asirin yana tab'a shi sai dai karfin Ibadarshi, yasa bai cinye shi baki daya ba..
★
Gimbi.
Ganin babu nasara, ta cire ranta da zuwa bikin su Sadiya Badar, amma Haka Amina Nuhu Giyad'e ta matsa mata, aka fara hidimar bikin da ita, karewa ana daura auren a gwallaga, suka nufi Abuja a can za ayi bikin sosai.....
[11/19, 7:01 PM] Queen BeeBee: *NAAZNEEN❤🔥 *
EXQUISITELY BEAUTIFUL
#Mai_Dambu
'Top-Notch
Season 3
بسم الله الرحمن الرحيم
Bikin a unguwar Maitama ake yi, kusan ma za a ce, makotansu Saifullahi-Khalid ne, wanda yake kwance har lokacin bai koma aiki ba. A hankali Auta ya turo kofar dakin Saifullahi-Khalid din da ya zurawa tv idanu.
"Ya Saif!"
Juyawa yayi ya kalle shi, sannan ya mai da kan Tv gabanshi. "Dama Ummi ce tace na gaya maka, ko zaka zo ka amso mata sako ne?"
Ware idanu yayi, kamar zasu fado kasa, dama gashi manya manya, wanda suka kawata zankad'ed'iyar fuskarshi. "Sakon me?"
"Nima haka ta ce min!"
"Ok!" Ya ce tare da miƙewa ya nufi dakinshi, daura jallabiya yayi a saman kayan jikinshi. Wayarshi ce tayi haske, dauka yayi ya ga Masallacin da yake musu karatun sati-sati ne suke kiran shi. A hankali ya kashe kiran ya kira su, "Assalamu alaikam, Barka dai Imam!" Aka faɗa a can,"Amin wa'alaikamun Salam,Yawwa barka dai!" Ya bada amsa.
"Mun jika shiru ne, shi ne muka ce bari mu kira ka."
"Allah sarki, babu komai in sha Allah ina nan zuwa."
"Ubangiji ya kawo lafiya, ya kuma baka lafiya."
"Amin Ya Allah."
Daga haka ya kashe wayar, duk wani abin da ya shafi Ibadarshi, an raunana su. Allah ya taimaka ne ma yake kokarin yin wani abu, dan ba karamin abu aka mishi ba. Yana gamawa ya fita, tare da nufar part din Ummi. Bayan ya shiga ya same ta zaune tana rarrashin Auta, Basmah tana jinsu.
"Ummi da kin bar ni na kwad'a mishi marin ne ma!"
"Babana don Allah ka kai shi, ya amso cake ɗinshi." Kallon Auta yayi sannan ya mika hannunsa yana riko na auta, ranshi baya son ya fita, amma kuma baya jin zai ce a'a a fitar.
A hankali suka bar gidan, zuwa waje yana jan motar yana kallon hanyar. "A ina...?" Bai karasa tambayar ba idanunshi ya sauka a kan Gimbi da take tsaye da wasu yan mata, tana dariya. Sanye Da Kayan biki. Kanshi ne ya dauki wani irin bala'in kara, dakyar ya cire idanunshi akan ta, ya cigaba da tafiyar. Wani irin azazzalar da zuciyarshi take masa yasa shi dole ya koma gefen titin unguwar yayi parking. Zufa ke karyo mishi kamar an tsoma shi cikin mangyada aka ciro shi.
Kifa kanshi yayi da sitiyerin motar, "Ya Saif!" D'ago kai yayi ya kalli Hashim. "Baka da lafiya ko?" Girgiza kai yayi, sannan ya ce masa. "Ina zuwa!" Ba musu ya cire sit belt din, ya fita daga cikin motar ya nufi inda ya ga yan matan nan, suna tsaye. Koda ya je wurin babu Gimbi babu alamarta.
Haka ya gama nimanta bai ganta ba, sannan ya juya wurin motarsu, suka bar wurin. Dakyar ya kai auta ya amso cake din, suna dawowa ya hangota tana sauka daga mota, da sauri yayi parking. Ya fito tsabar sauri ma, wata mota kamar zata kwashe shi. Haka ya tsallaka yana me shan gabanta yana haki.
"Baiwar Allah!" A dan razane tayi baya, tana nuna shi, sannan ta nuna kanta. "Ni?"
"Ke! Please muje ga mota ta can!" Juyawa tayi ya ga motar, kafin ta girgiza kai tana kokarin barin wurin. "Please ina son magana dake, idan babu hali bani number wayarki."
Wani banzan kallo ta mishi sama da kasa, sannan ta ce mishi. "Ni matar aure ce!"
Wani bala'in dauke wuta yayi, "please ki saka mijinki ya sake ki, wallahi ina kaunarki."
"Malam bani hanya!"
"Please ki saurare ni!"
"Ok bani number ka, idan na samu lokaci zan kira ka." Hadiye yawu yayi ya karanto mata numbershi, rab'a gefenshi tayi bata ce mishi cikanka ba. Kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha, farinciki da walwalar shi lokaci guda suka dawo, ya koma cikin motar ya zauna, yana sauke ajiyar zuciya. Sannan suka bar kofar gidan, yadda bai yiwa auta magana ba, shima Hashim bai bi ta kanshi ba, koda suka isa gida kowa ya wuce nashi hanyar ne, tunda ya iso gida ya saka wayar ya gaba yana gani, kafin ya rasa me ke yake mishi dad'i. Sai da ta kai yaƙi daukar kiran kowa gani yake zata kira shi.
Gimbi.
Tsabar farinciki, kamar tayi ta ihu ita ɗaya sai murna take, take ta kira Siyamah da Linah ta fesa musu, ai dama sun gaya mata, ita ce dai bata yarda ba. Amma sun san aikin ba Allah, karya kace bai maka ba. Don haka suka bata shawara ta wana shi kafin ta yarda su sake haduwa. Haka kuwa akayi, duk da bata so ba. Haka taki kiranshi.
Tashin hankalin da Saifullahi-Khalid ya shiga kamar ya zauce, domin yadda yaga rana haka yake ganin dare, gashi duk tambayar da za a mishi bai tab'a cewa ga abin da yake damun shi, a bangaren Gimbi itama tana jin babu dad'i, sannan tana yawan nazarin matuƙar ta bar abuja basu hadu ba, tayi sake reshe kama ganye kenan fa, da ita da asara duk ɗaya ne.
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin ba zata iya barin garin abuja basu hadu ba don haka ta gyara kwanciyarta. Tare da lumshe idanunta, gobe za a gama bikin daga nan kowa zai kama gabanshi, "Baki yi barci ba ne?" Inji Amina Nuhu Giyad'e.
Sai da ta tabe baki,wanda haka ya zame mata jiki, ta ce mata. "Eh wallahi." "Gobe za a gama bikin, gaskiya ba zan iya komawa Bauchi a gobe ba, sai jibi zan dan zaga cikin gari nayi wani kamu." Kallon Amina Nuhu Giyad'e tayi tana imagine yadda take wani iyayi zaka rantse da Allah irin kyawawan ne, amma take wani salo. "Tow ko na bi yarima a sha kid'a ne?"
"Me zai hana?" Suka kwashe da dariya, har wurin asuba, basu tashi sallah ba sai da gari ya waye suka tashi, dake Gimbi bata damu da sallah ba, cewa tayi tana off. Cigaba da barci tayi sai da Amina ta tashe ta, tayi wanka suka fita.
Suna fita daga gidan bikin ta hango Saifullahi-Khalid tsaye, domin tun safe ya bar gidansu yazo ya tsaya a kofar gidan. Tana ganin shi ta tsallako titin. Juyawa tayi tana kallon Amina Nuhu Giyad'e, da ta shiga rud'ani.
"Nayi ta jiranki tun jiya."
"Oh sorry, na mance da kai ne!" Kallonta yayi kafin ya sauke numfashi ya ce mata. "ina ta jiran ko zaki kira, amma kice kin manta da ni."
Cikin tsiwa ta ce mishi.
"Hala ka ajiye ni, gadinka ne ko? Kaga don na tuna ka ne yasa nazo wurinka sai an jima."
"Please ki tsaya, ko suna na, zaki tambaya ai?" Yayi maganar cikin sigar rarrashi.
"Ok meye sunanka?"
"Saifullahi-Khalid, ko kai kowannensu zaki iya kira zan amsa, ya sunan Gimbiyartawa."
Wani fari tayi da idanu, sannan ta ce mishi.
"Ai ka canki sunan, da kanka."
"Hmm! Gimbiya?" Ya kuma tambayata,
Gyada kai tayi tana lumshe idanunta.
"Gimbi kizo muje, kafin ya tafi ya bar mu." Inji Amina Nuhu Giyad'e.
Gabatar da ita Gimbi tayi, tana gaya mishi.
"Gimbi?" Ya tambaye ta, gyada kai tayi tana faɗin. "Gimbiya Baby Yusuf Bogoro!"
"Oh! Dukkan mun yan Bauchi kenan!"
Gyada kai Amina Nuhu Giyad'e tai, tana girmama a ina Gimbi ta samo Balarabe haka. "Kawarmu gashi bamu gama magana ba zaki dauke min ita, Ya kenan?"
"Tow ai sai na tafi na barku tare."
Gyada kai yayi yana faɗin. "Kin kyauta!"
Tafiya tayi ta barsu a wurin, a ranta tana jin wani irin mamaki. Shima daukar Gimbi yayi suka fita, idan da ace can baya ne, Gimbi bata isa tsayawa a gefenshi ba, amma dake al'amarin ba daya ba ne, yanzu kan sai yadda tayi da shi, haka suka fita tun safe, sai la'asar suka dawo,dake unguwar kowa harkan gabanshi yake..
Sosai suka samu kusanci da juna, wanda ta kai kamar ba zasu rabu ba, bayan an gama budar kai, aka sallame su. Sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta, dakyar suka samu inda zasu kwana, amma a daren Saifullahi-Khalid sai da ya fito ya same ta, suka tafi yawo.
Saifullahi-Khalid mutumin kirki ne, bai san wannan irin rayuwar ba, ba don kome ba sai don gidansu da familynshi.
Tun lokacin da Gimbi ta samu Saif a hannaunta, ta kara haukata shi, a kasa da sati Uku aka shiga nima mishi aurenta, a lokacin Yayunshi mata da yan uwan Babanshi maza da mata sunki auren, amma ina ya kafe, wacce ta kawo karshen rikicin Hajja Marih ita ta tsaya aka yi auren babu yadda suka iya, amma daga yanayin Familyn Maman Gimbi suka tabbatar babu mutanen kwarai, kuma basu da kome da zasu iya bikinsu na mutanen katagum.
A bangaren Babanta kuwa, cewa yayi ya mata miji, abin da ya haifar musu tashin hankali da Maman Gimbi da Babanta akayi ta kai ruwa. Wanda daga karshe honorable da kanshi ya zo yace ya fasa auren Gimbi, don dole haka ta saka Saifullahi-Khalid a gaba da jifa, wanda yaƙe jin kamar ana zuke jinin jikinshi. Yadda ya d'aga hankalin lallai a nima mishi aurenta. Hajja Marih ta fara shan jinin jikinta. Bata cika shiga sha'aninsu ba, amma a wannan tak'in da kanta ta tafi har Abuja, kallonshi kawai tayi na wani lokaci kafin ta ce mishi.
"Malam Alhaji, yaushe kika zama haka? Akan me zaka zama haka? Anya kana addu'a kuwa? Baka addu'a nasan da kana addu'a da ba zaka rikice akan mace haka ba, don haka kuwa daga gobe juma'a zamu fara da ikon Allah, duk me nimanka da sharri zai koma kanshi. Munyi imani da Allah da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, albarkacin alqur'ani sai mun ga bayan masu niman ganin bayanka."
Shi dai bai ce mata kome, dattijuwar nan bata yi kasa a gwiwa ba, ana maganar aurenshi a gefe guda. Ana saukar Alqur'ani.
A cikin sati daya, al'amarin auren gimbi ya fara tangal - tangal. Domin har an saka rana an gama kome maganar aure kamar an shuka dusa, babu shiri ta wuce kaltungo. Kura mata idanu ba Allah yayi, ganin yadda take kuka wiwi.
"Maganar auren ya fara lalacewa, a taimaka min ayi wani abu."
Kallon madubin kogon yayi, ya nuna da isgar hannunshi ya ce.
"Wannan shi ne ko?"
"Eh!"
Tashi yayi ya dauko wasu tantabaru bakaken wuluk ya ce mata. "Wadannan sune bakakkrn tantabarun soyayya, idan har suka mutu soyayyarki zai mutu, a zuciyarshi. Idan suka rayu har da yayyafa, babu me raba ki da Saif sai mutuwa."
Haka yayi ta tsafe su har sai da ya jika su da tsafi, sannan ya bata tare da cewa. "Ki tabbatar da kin saka a cikin gidanku, kina zuwa gida ki kira shi, ki watsa musu wannan ruwan bayan kin kira shi. Aure kuwa na gaya miki, ranar juma'a za a daura aurenki da shi."
Haka ta ajiye mishi abin da ta kawo mishi, sannan ta bar ramin, tana tabbatar da babu Allah.
Da wannan ta baro garin, tana shigowa gidan tayi abinda ya ce mata, ai kuwa a daren sai ga kiran Saif. Babu kakkautawa itama tayi biris shi, kada kuce baya kula da addu'a ne a'a jarabawar shi ce Gimbi.
Washi gari kuwa kamar mahaukaci haka ya zama a cikin gidan, don dole suka tawo Bauchi nima mishi auren ranar Laraba, suka kwana Alhamis.
Ranar juma'a aka shaida aurensu, duk da a ɓangaren iyayenshi basu so aurenta, amma babu yadda suka iya, tunda shi yaji ya gani yana sonta. Sai da aka yi auren hankalinsa ya dawo jikinshi. A hankali kome ya juye tare da kazamta, domin dai Ummin ta hana shi tafiya da ita, don haka suka saka idanu akanta, sannan yan uwanshi kiri-kiri suka tsaneta. Musamman da suka lura da cewa dan uwansu sai yadda tayi da shi.
Bata da ikon shiga cikinsu, sai kyara da tsangwama, a gefe guda tana da kawayenta da suke mata kaiwa da komowa. Wannan yasa baki daya bata yi wasa wurin rike wuyarshi ba.
Yanzu shekararsu bakwai kenan, sannan ya ɗauke ta zuwa lagos, akan Gimbi Saifullahi-Khalid ya rabu da kowa abin tausayi har uwar da ta haife shi.
Kowani gefe kuwa kokuwar ya dawo da shi tsaginsa yake, a wannan lokacin Aunty Mariya ta shirya mishi zancen aure ne, domin yana yawan kiranta, ita ɗaya ce bata rabu da shi ba, akan Gimbi sai da ta daki Basmah saboda sun yi faɗa da Gimbi.
Itama kuma Gimbi fadar da suka yi tayi alƙawarin ajiye Basmah a wuri guda, mijin da zata aura yayi hatsari wanda shirin Gimbi ne, sannan ta bakantata a idanun masu niman aurenta. ....
[11/19, 7:01 PM] Queen BeeBee: *NAAZNEEN❤🔥 *
EXQUISITELY BEAUTIFUL
#Mai_Dambu
'Top-Notch
Season 3
بسم الله الرحمن الرحيم
Yadda take juya Saif ya kazanta, hakan yasa baki daya kome na rayuwarshi ya koma hannunta, a halin yanzu babu wanda yake mu'amala da shi sai Aunty Mariya itama don yasan bata cikin masu zagar mishi mata ne, shi yasa yake dan sassauto da fushinsa akanta. A watan nin baya har Lagos Ummi taje, wani abin tausayi yadda ta isa gidan haka Gimbi ta hana a barta ta shiga, har Saif din ya dawo aiki. Ya same ta a kofar gidanshi tsaye. Fitowa yayi ya bude mata kofar motar shi jikinshi a matuƙar sanyayye.
"Alhaji Malam haka ka koma?" Abin ka da uwa, sunkuyar da kai yayi yana faɗin. "Ai aiki ne ya saka ni a gaba, bani da sukuni. " Bata kuma cewa cikanka ba. Haka suka shiga cikin gidan, duk da tana danne damuwarta. Amma yana parking Gimbi tana fitowa daga cikin gidan, rike kugu tayi ta ce mishi. "wallahi ba zata zauna min a gida ba, tun wuri ka san inda zata kwana!"
"Princess mahaifiyata ce, ki barta ta zauna gobe sai na maida ita."
"Chab dijam, a saka min wani abu a gidana, don an ga ka damu dani!"
Zai kuma magana ta d'aga mishi hannu, wallahi ka zab'a ko ita ko ni. Wani rawa jikinshi ya dauka, yana kallon Umminshi yana kallon Ummi, duk da Hausarta bai goge ba, amma jin wannan zantuttukar yasa ta juya zata fita. Ya riko hannunta.
"Don Allah kada ki tafi ki bar ni." Yadda yayi maganar yasa hawayen da take rikewa ya zubo mata, hannunta ta kai kanshi, tana shafa kwantaccen sumar kanshi, da ya sha gyara tana faɗin. "Babu inda zani na barka, ka kula da kiran Allah shi zai kula da amsa maka. Zan kira Nassef ya kai ni gidanshi."
"Muje na kai ki!"
"Babu inda xaka fa, wallahi na gaya maka." Ta fada tana bin ummi da kazamin kallo, "Tow naji bari na kira Nassef."
"Ka kira shi right now!" A hankali ya kasa da kanshi, ya lallubo wayarshi, ya kira Nassef. "friend don Allah zoka tafi da Ummi wurinka." Kashe wayar yayi yasan Nassef zai iya kashe shi da zungurerren ashar. "Oya mu shiga daga cikin gidan!" Daga haka ta tisa keyarshi, a gaban Mahaifiyarshi, suka bar compound din gidan. Bayan kamar minti ashirin sai ga Nassef, Ummi na ganin shi, ta fashe da kuka, ta kasa magana ma sai kuka. "Me ya faru?"
"Nassef mai dani Abuja, idan naga halin da Alhaji Malam ya shiga zuciyata zata buga."
"Me ya faru?" Bata iya gaya miishi ba, bude mata kofa yayi ta shiga, ya rufe sannan ya nufi wurin gate keeper din gidan ya tambaye shi, tass ya sanar mishi abinda ya faru. Shiru yayi sannan ya juya yana nad'e hannun rigarshi, sannan ya nufi cikin gidan, wani irin duka yayiwa kofar gidan, ya bude yana huci. A falo ya same Gimbi.
Dama ya tsane ta, from beginning. Sannan tunda ta auri Saifullahi-Khalid suke artabo da ita. Cikin matukar fushi ya nufi wurin kayan wuta, ya janyo wata zabgeggiyar wayar chaji, ya nufe ta. Kafin ta gudu ya zuba mata a cinyarta. Faduwa tayi a ƙasa tana fasa ihu.
"Don ubanki, iskancinki har ya tsallake kan kowa ya fad'i kan Uwarmu!"
Ihun Gimbi da yake ji ne, yasa shi fitowa daga shi dai towel ko kumfar jikinshi bai wanke ba.
"Wannan wani irin wawanci ne?" Ya tambayi Naseef, "yadda ka dauka haka ne, bani hanyar naci uban yarinyar nan, shegiya mummuna. Mara fasali!"
Rike bulalar yayi cikin jin haushi ya ce masa. "Bana son bura uba, kyale min matata."
"Kutumar ubanta, sake min bulala naci ubanta." Karewa faɗa ne ya shiga tsakaninsu, ita kan guduwa dakinta tayi, faɗa sosai, sai da Ummi ta shigo ta samu, Saifullahi-Khalid ya d'aga hannun zai kaiwa Nassef duka ta ce mishi.
"Idan har ka sake hannunka, ya tab'a min d'ana. Kaji da kyau na yafe mata kai ko gawata bana fatan ka zo kanta."
Sauke hannun yayi cikin fushi ya ce mata.
"Taya zai daki matar aure?"
"Saboda bata dace da mijin auren ba ne."
Ta riko hannun Nassef suka bar gidan, shi kuma sokon ya nufi kofar dakinta yayi ta bugawa. Taki budewa, yakira Nassef ya kai sau goma amma yaki dauka.
Yayi niyyar zaginshi ne, amma fir yaki dauka, sai wurin asuba Nassef ya tura mishi. *Idan kaso kazo ka ga halin da take ciki, domin jininta ya au an kwantar da ita.*
Jikinsa na rawa, ya saka kayan shi zai fita. Suka hadu da Gimbi bai gaya mata inda zai je ba, ya fito daga cikin gidan, ya nufi asibiti, dakyar Ummi ta mishi magana, shima sai da Nassif yayi ta rarrashinta, kafin ta ce mishi. "Zan kula ka, amma sai ka dawo da matarka, Abuja ta haka ne zan san abin da yake tafiya tunda duk karshen sati zaka zo na ganka!"
Ya amince, kuma yarda yasa Gimbi a gaba ta koma Abuja, a lokacin ta tafi har azare, ta gayawa mutanen gida. Shi kan Alhaji Mansur, gani yake kamar rashin hakurin Samiha ce, tana son Yaranta. Shi yasa take ganin kamar Gimbi ta rabata da Saif dinta.
Koda yake da Gimbi ta watsa mishi, rashin arzikin. Nan ya fahimci tabbas Saif ya dibo da zafi, haka yasa shima bai zauna akan dan nashi ba, wanda suka shiga nima masa aure, sai an gama maganar kome, daga baya auren ya watse.
Wannan lokacine baki daya, kowa ya mata caaa, akan auren da zai yi da wata coursin ɗin shi, yar wurin Hajiya Adamah Saifullahi katagum, wacce take itama Gwana ce, Sunanta Khalwata tana school of nursing Bauchi. Shine dalilin da yasa tayi fushi domin sun ce mata ko tsafi take da gudan mutum, sai yayi aure a wannan lokacin domin aure uku yana rejected din shi. Kuma babu uzuri ko dalili zai ce baya so. Dalilin da yasa ta bar abuja zuwa Bauchi kenan,
Wannan shi ne labarin Gimbi da Saifullahi-Khalid.
★★
Enugu.
Tunda suka dawo daga wurin Baba me magani, take kallon Amanda. Da dukkan zuciyarta take jin anya zata iya rabuwa da yarta..
"Nne!" Kallonta tai, a hankali ta isa gidan Yar. Buga mata kofar dakin aka yi, ta leka tana hango wanda yake buga kofar, da sauri ta bude kofar, ta rungume shi tana faɗin. "Obinna!" Rungume ta yayi yana buga bayanta.
"Sorry Chioma gani nan na dawo!" Riko hannunshi tayi suka shige dakin, "Obinna!" Ta kira sunanshi, "Yes Chioma!" Hawaye ne ya zubo mata, masu zafi da kunar zuciya. "Naje village aka ce min, kin jima da barin gida, Chioma ni da nace ki jira ni zan dawo. Sai ki bar gidan."
"Obinna sun yi kokarin kashe min Yarinyata, taya zan bar musu ita? Nima kada ka manta don ka tsaya zaka aure ni yasa Chef ya lamunce min nayi rayuwa cikin yanci."
Kallon yarinyar yayi duk da baya jin tsanarta, kamar yadda yake jin tsanar ubanta, sai dai yadda ya shirya rayuwarshi da Chioma baya jin zai dauki stepdaughter a gidanshi. Riko hannun Chioma yayi ya ce mata.
"Na samu aiki a can Canada, mu mai da Yarinyar nan, sai a daura
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 12