Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da Hajiya Goma su salwatar da ita ba. Sau uku suna barinta a masallaci, da farincikin su, suna bude dakin zasu isketa a saman gado tana barci. Haka ya sa Innayo hakura da abinda take, duk da ita kanta ba son ranta ba ne, amma tana kara jin tsanar yarinyar saboda bakin Hajiya Goma. Yau da zasu tafi masallaci, Nazneen ta rigasu fita, domin ban da kyara da hantara babu abinda yake had'asu. "Innayo dama naga kamar hankalinki yana tashi, me zai hana, mu ce Nazneen ta miki sata kinga nan dokarsu da tsananin." "Ban gane ba goma, kina nufin na mata sharrin sata? A'a duk kiyayyar da nakeq mata ba zan kashe ta ba, kuma ba zan mata sharri ba, abin da na sani na tsane ta. Ba don ba jinin Adamu ba ce a'a sai jinin da ta haɗa da arna, don haka bar zancen sata tayi min." Shiru goma tayi tana mamakin ashe, Innayo ta san me take yi, don haka ta ce mata. "Wai naga kina shiga damuwa ne, idan kika ganta, amma ya wuce ai." *** A can masallaci kuwa, Yankar jiki wata mata tayi da take gefen Nazneen. Dake yau juma'a, Sheikh Abdulrahman sudais yana hudubar juma'a. Juyawa Nazneen tayi ta nufeta, tana me tattabata, kafin ta isa wurin wata mata da take shige da fice na hukumar masallacin, tazo ta aka.kira aikatan lafiya suka tafi da matar. Komawa mazauninta tayi ya zauna, Hajja Marih da take kallon kome murmushi tayi sannan ta dawo wurin Nazneen da zama. "Sannu yarinya me halin manya." Murmushi tayi tana faɗin. "na gode hajiya, ina wuni?" "Lafiya lau, ko zaki kawo min ruwa na sha?" "Tow" ta fita can dai gata da ruwan zam-zam. Ta kawowa Hajja Marih. "Ke dawa kuka zo?" "Ni da kakata da kishiyarta, basu iso ba." Haka suka zauna shiru, har aka yi sallah juma'a, kusan tare da hajja Marih suka fito, a waje ta samu ganinsu Innayo, ta cewa Hajja Marih, "ga kakata can " Kusan tare suka isa wurin, Innayo ta zabgawa Nazneen harara. "ina kika shiga?" "Ayya tana cikin masallaci ne." "Hajiya kin san dan yau, baka shedan shi. Tun yaushe muna nan bamu ganta ba." Inji Hajiya Goma. Kallon Hajiya Goma tayi kamar zata yi kuka ta ce mata. "Hajiya Goma ban gane ba, na zauna jiranku kin ce min, na saka ku a gaba kamar Mayu ai kun san hanya, na tawo kin ce baki yarda da ina masallaci ba, Hajiya Goma ki daina shiga harkata. Idan ba haka ba wallahi ko." Ai kuwa ta wuce su ko sallama da Hajja Marih bata yi ba, "Baiwar Allah, muna tare da ita, a cikin masallaci. Sannan kuna kyautata zato ga kowa domin Allah zai iya jarabtar ka da abin da kake zargin wani. Yarinyar nan tana da hankali. Domin kuwa." Bata rufe baki ba, hukumar masallacin suka fito niman Nazneen, a ganta domin da taimakonta aka kai matar da ta fadi asibiti. Lokacin da larabawan suka zo Hajja Marih ta amsa musu, suka.yi ta labrace take gayawa musu ga kakaninta, sai kunya ta kama Innayo da Goma. Aka yi ta musu godiya, da fada musu ai jikar ta Mutuniyar kirki ce, Da rigima da fada, da tashin hankali aka gama umran, suka dawo Nigeria. Tunda suka dawo sau biyu Innayo tana rashin lafiya, har lokacin azumi yayi, a lokacin Alhaji Abdullahi Malami ya zo hutu da iyalinsa. Akan idanunshi yaga yadda Innayo da Goma suka saka Nazneen a gaba, su mata a gaban jama'a, Duddiya su hana su barci. Don ma Malam ya kara kafe gidan. Alhaji Abdullahi da kanshi ya gayawa Umma zai tafi da Nazneen, ita kuma ya gayawa Malam, shima da ya gaji da halin Innayo ya ce su tafi da ita. Haka aka yi azumi, kayan sallah Nazneen da Babanta ya saya mata. Innayo ta hanata, ita kuwa ta kwashe na Innayo ta saka a rufin dakin Innayo. Wannan abin da yayiwa Innayo zafi, domin ana sallah jininta ya hau, Aunty Uwani da Aunty Hawwa'u, suka ce gaskiya Alhaji Adamu ya ɗauke yarshi zata kashe musu uwa. Wannan abun ya mishi ciwo ainun, ya gayawa Malam. "kada ka damu lokacin da zasu gane kuskurensu yana zuwa, yarinyar nan alkhairi ce. Amma ba kowa zai gane haka ba, Abdullahi ya ce zai tafi da ita gara ya nisantatta da nan " "Alhamdulillahi! Kafin ayi babban sallah zan nima mata visa n zaman can " Duk da Alhaji Abdullahi iyalinshi suna, New g.r.a. ita Nazneen bata san dukkan yaranshi ba, Tahir ya sani. Tahir yana da kanne, Anas, Amrah, Sadiq, sai Auta Naylah, karshen shekaran nan za ayi bikin Amrah, a can London din, wani dan Kano ne. Duk sauran jikokin Malam, suna son alaka da su Tahir, amma kishin kakaninsu yasa suke taya kakaninsu kishii. Naylah da take da mugun iyayi da gani-gani, ranar sallah. Da suka hadu da Nazneen sai da ta kasa boye mamakinta, domin har dakin Umma ta je ta ce mata. "Umma, yarinyar da ta shigo ita ce, yar Baban Abuja?" "Eh ita ce Nazneen Aisha." "Sai kace Barber doll. Tafi kowa kyau a gidan nan,. Ki ga dan kunnen da yake kunnenta diamond ne fa." "Eh nice na saya mata, zuwana Umra kema na saya maki, ita nata pink ne ke kuma purple." "Da gaske Umma!" "Da gaske ki tambayi Mamarki na bata ta baki." Kasa magana tayi, ta koma tana murmushi. "Umma da ita zamu koma London?" "Eh tare zaku koma, kiyi shiru da bakinki ki." Rufe baki tayi, daga nan ta fara cin masarta. Washi garin sallah ana dawowa kallo, gidan aka taru, Washi gari hawa kuma akayi wunin sallah, baki daya yaran gidansu haɗu, tunda Yaransu suka zo aka saka Nazneen a gaba, zagi hantara karshe dakin Malam ta nufa ta kwanta abinta. Sau biyu yana shigowa ya ganta tana barci, abincin gidan kuwa yadda aka zuba shi a cikin tukunyar ana izza wuta haka ya zauna babu al'amarin yasan ana izza wuta. Har wurin karfe biyu na rana ba a sauke abincin gidan ba. Hajiya umma ta nufi dakin Malam, Nazneen tana ta barci, tab'ata tayi tana faɗin. "tashi Nana A'ishah, zoki duba mana girkin nan yaki yi, sannan ki gaya min me ya same ki." "Zagina Mommy tayi,akan yan kunnena da Munayyah ta dauka zata saka na ce ta bani abina kada ta lalata min, shi ne suke ta dukana da zagina. Bayan malam ya hanani yin wani abu." "Ina yan kunne suke?" "Kin ga ta tsinka min sarka na." Daukar abin wuyar Umma tai, ita kadai tasan yadda take ji, "kiyi hakuri kinji!" malam ya fada a bakin kofar dakinshi. "Wata rana zasu so, su isa matsayin da kike Allah ya daukaka ki, na hanaki mu'amala da aljanun ne don kada su zama rauninki. Jeki tura musu wutar." "Tow." Tashi tayi, ta fito ta samu kowa yayi cirko-cirko a tsakar gidan, anan ta mamakin yadda abincin yaki nuna, tana zuwa ta bude tukunyar ta saka.hannunta biyu ta wanke su tassa, sannan tukunyar ta hau tafasa. Ta wuce abinta tana jin kowa nacewa. "Tab na ba zanci abincin nan ba." "Duk wanda yaga ya ci abinci a wani wuri, tow gidanshi ne, amma tabbas babu me saka ni asara." Haka kuwa aka kwashe duk suka ci abincin haka, ban da Nazneen da Umma ta bata dambu da cake. Haka aka yi wunin sallah babu wnada yaji dadinshi.. Bayan sallah da kwanaki visa din Nazneen din ya fito. ★ Mutanen Istanbul, ranar da suka shiga kasar ranar Khawlat ta fara rashin lafiya. Da farko Saif ya zata ai normal, sai da suka kwashe sati biyu, ciwo ya saka yar mutane a gaba. Don dole suka nufi asibiti. Inda suka kwashe sati biyu a can, kafin suka dawo, kasancewar azumi ya gabato, haka Gimbi ta hana a maida ita gida, haka take jinya, Gimbi ke mata kome, har aka gama azumi. A lokacin jinyar yaci ƙarfinta. Wata juma'a, sai ga Ummi da Maman Khawlat, domin hankalinta yaki kwanciya, suka zo, lokacin da suka iso gidan Gimbi bata nan, Saif suka samu Don sun zo da Nassif ne shi ya gayawa Saif gasu a hanya. Lokacin da suka ga Khawlat, karfin zuciya ne irin na Uwa yasa bata zubda kwalla ba, amma ta karaya da Yarta, ai basu kwana a Lagos ba, sai bauchi. Domin Uwar na ganinta tace jinyar ba ta Asibiti ba ce, ga cikin da ya fito, das a ramamen jikanta. ★★ Sati biyu saura ayi Layya, Alhaji Abdullahi suka juya London, da Nazneen wacce abin yazowa Innayo bazata, sai da ta sami Malam da maganar ya mata wankin babban bargo. Sannan ta yi shiru. ★★★ A can Azare kuwa tunda aka dawo da Khawlat, ake maganin gargajiya da na Islamic, jinya ake amma jikin yana kara rikicewa, a ranar da gimbiya tazo Azare, kuka wiwi take, itama Khawlat kuka take, cike da kaunar Gimbi. Domin babu abinda zata ce mata, irin halaccin da Gimbi ta mata, satin Gimbi biyu, ta koma, bayan komawarta ne, Khawlat bakinta ya bude. Take bawa mahaifiyarta labarin yadda Gimbi ta mata alkhairi da kula da ita, kusan zuciyar Uwa, take ta manta da wani abu a ranta, tayi ya yiwa Gimbi addu'a. Bayan babban sallah da sati Uku, Gimbi tazo, a lokacin Jikin yayi sauki. Haka ta je gidansu Khawlat, suka sha hira, babu wanda Gimbi bata burge shi ba, Sai Nassif domin gani yake kamar fuska uku gare ta, satin ta daya, ta juyo zuwa lagos. Bayan tafiyarta da kwana biyar, jini ya tsinkewa Khawlat, aka nufi FMC Azare, yadda aka shiga da ita dakin, emergency........ Alhamdulillahi anan na kawo karshen FREE page's. K'ak'ara ƙaƙa, Khawlat zata mutu ko zata rayu?....... Labarin zai cigaba da zuwa muku.... Arewabooks da Whatsp. _NAAZNEEN, GENERAL NASIR ZAKI, BINTUN BATUL TOP-NOTCH TEAMS NA KUDI NE! BAKI DAYA UKUN 1300 NE_ BIYU=₦900 DAYA=₦500 CHAT ME IDAN KUNA BUKATA: 08130269641 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 12 of 12