babu mai matsala da hakan, kowa ya amince da wannan auren, amma bata San me yasa ba, bata jin shi a zuciyar ta kamar yanda shi yake nuna Mata tsantsar soyayya da qauna, bata San me yasa ba a kullum tsoron shi, da tsoron aikin shi yake danne soyayyar shi a ran ta,gaba daya Jiddah ta riga ta Sanya wa ran ta aikin soja aikin mugaye ne, banda cin zalin mutane ba abinda suka iya, shi yasa duk yanda ta sake da shi suna hira da ya sauya fuska zata rikice ta fita hayyacin ta.
Amma da alama iyayen nasu basu bata zab'i ba, shi ne dai mijin da suka tsayar zata aura, ita ma kuma bata da ja ba ta da wani zab'i, fatan ta Allah ya sa hakan ya zama alkhairi a rayuwar su gaba d'aya, ta na nan kwance ta na tunani bacci mai dad'i ya yi awon gaba da ita, abinka da an gaji to, tun asuba da ta farka bata sake koma wa bacci ba saboda karatun jarabawar da suka yi wadda ita ce ta qarshe a wannan zangon na uku da suke ciki.
Ba tare da ta Sani ba, Muhammad Labbo ya shiga d'akin ya gama qare mata kallo sannan ya tafi gidan su bayan ya ba wa Ummah tsarabar da ya kawo masu,a harabar gidan nasu drivern shi ya yi parking motar da suka je da ita, nan da nan Mai gadin su da drivern gidan nasu suka hau kwasar gaisuwa,amsa wa ya yi cikin mutunta wa sannan ya shige cikin katafaren gidan nasu.
Mahaifiyar shi na zaune riqe da alqur'ani a hannun ta TV na kunne ta Kai makka ana karatu ta na bi, ba zato ba tsammani kawai ta ji sallamar shi, cikin zumudin son ganin gudan Jinin nata ta Kai qarshen aya sannan ta rufe qur'anin ta miqe tsaye ta na masa maraba, da sauri ya nufe ta ya rungume ta, itan ma rungume shi ta yi tare da shafa kan shi da ya Mata tsayi sosai a kafad'ar ta, sannan ya duqa daidai tsahon ta ya sumbaci goshin ta.
"Masha Allah... Junior yaushe ka zo? Dan na San se da ka bi gidan goggon ka ka cika cikin ka tafff sannan ka iso min nan"
Sosa qeyar shi ya yi sannan ya zauna a qasa inda kafarta take, ya d'auke qafafun ta dika ya dora a Saman cinyar shi ya na Mata tausa.
"Mom kamar kin sani, se da na je na ci danwake, na ci shinkafa da wake sannan na Sha wannan zob'on mai dad'i muka gaisa na taho, rabon da na ci abinci me yawan na yau tun kafin na tafi wani aiki Ibadan"
"Lallai ya kamata ka dinga cin abinci sosai, Ina yawan sanar da Kai ko ba a girka a gidan naka ba ka na siya a restaurant ka na ci kana qoshi, ko ka sa ana Kai maka har gida,bana son wani ciwon ya kama ka saboda yunwa, bani da matsala da matar ka ko ta Ina se ta wajen kula da cin ka da Shan ka,ba yanda ba a yi da ita ba dan ta gyara amma ta qi ta gwammace a mata kishiya da ta gyara,Allah ya kyauta"
"Ameeen Mom, na same ku lafiya? Ina Daddy da Abdunnasir?"
"Dazun nan suka fita d'aurin auren yaron abokin Dad d'in ku, wataqila ma ka gane shi, yaron nan da ke Saida motoci a sokoto?"
"Eh na gane shi Bilal ko? Masha Allah, Allah Basu zaman lafiya,Allah ya sa alkhairi, Mom ya jikin naki? In ce dai ki na kula da Shan magani ana Kuma kula da abinda ake ci?"
"Ahhh alhamdulillah,ni yanzu manta wa nake Ina da sugar, alhamdulillah "
"To alhamdulillah Allah ya Kara lafiya ya sa kaffara"
"Ya kabaro min wadannan amaren masu kwacen miji? Suna lafiya ko?"
"Lafiya kalaou suke Mom, suna gaishe ki, sun bada tsaraba a kawo maki, se na huta zan Ciro maki ki ga abinda suka bayar a kawo maki"
"To shikenan Ina nan Ina jira, Allah ya sa ba qashi bane dan banda haqorin tauna wannan se su"
Dariya ya yi sosai sannan ya ce,
"Habaa Mom ai yanzu ba Wanda zai kalle ki ya ce kin aje qaton mutum kamar ni balle ki rasa hakorin cin qashi, to ba qashi bane, almond ne Mamin su ta sa na je da su shopping suka kwaso maki da sauran tarkace dai haka se kin gani"
"Allah ya musu albarka kamar sun San babu anan, na sa an je an duba min ya fi sau nawa amma babu"
"Ameeen ya Allah, Mom"
"Tashi ka je ka huta kafin su dawo wannan uban surutun ya hana ka hutawa"
Murmushi ya yi sannan ya sauke qafafun ta a hankali daga cinyar shi ya miqe tare da sumbatar hannun ta ya wuce sashen su shi da qanin nashi.
Yana shiga ya hau cire kayan shi, ba jima wa aka kwankwasa qofa drivern shi ya shigar Masa da kayan shi, sanan ya Sara Masa ya koma masaukin shi da aka aje shi, abinci ne mai aiki ta Kai Masa irin na zamani me rai da lafiya ,cikin ran shi ya ke ayyana.
'Ba dan Kar a ga rashin godiya ta ba da na koma gidan Goggon yallabai nima na cika ciki na da abincin gargajiya'
****************************
Tinda Yah Major ya tafi take zumbura baki, dan kuwa ko jakar da ya bawa Ummah ya ce tsarabar su ce Ummah ta qi bari su bud'e, a cewar ta sai sanda Balqis ta San ta yi laifi Kuma ta bada hakuri sannan za a bud'e jakar, ita kuwa gimbiya Jiddah ko a jikin ta, ta San dai tsarabar baza ta wuce kayan maqulashe ba se Kuma suturu da Auntyn nata ke bayarwa a kawo masu, se kuma turaruka da kayan kwalliya, idan kuwa su ne kayan kwalamar kawai take wa a ciki, amma sauran alhamdulillah har Wasu suke ba wa ma, Ummahn su ta tsare masu duk wani abu da budurwa zata nema saboda ta gujewa roqon samari, ko ta qetare raini a wajen sa'annin ta.
Ta sani Abbahn su ya na son su, dan kuwa a Koda yaushe ya na zama da su su yi hira sosai,Kuma ya basu labarai na ban dariya da jarumta, amma sisin shi ba za su ciyu ba a wajen kowa a cikin su, Ummahn su ce qarfin komai a gidan, ita ce cin su, Shan su, suturar su, Kai hatta kud'in makaranta da na haya ita ke biya,ta na sana'a sannan dangin ta suna da hali daidai misali,idan yau wannan be mata ba wancan zai mata, Dan kuwa suna zumunci a tsakanin su daidai gwargwado, a kullum ta na yawaita tunani akan ina Mahaifin su ke Kai kud'in shi? Dan kuwa ba talaka bane, balle a ce babu ce ta Sanya shi hana wa, sannan me ya sa kullum suke yawan fad'a da Ummahn su? Gashi yanzu har hawan jini gari Ummahn su saboda damuwa.
Gyara kwanciyar ta ta yi tare da sauke ajiyar zuciya, ta so ci gaba da zurfafa wa a tunanin ta ko zata gano wani abu ta ji murnar Balqis ta na fad'in.
"Ke tashi karon ga har da waya an ka siyo miki, gashi nan a kwalin Wai ya rubuta 'My Queen Jiddah' zamu faso gari muma bana, kawo na bude maki WhatsApp da Snapchat mu dinga hotuna"
"Kaiii subhanallahi Balqis Allah ubangiji ya shirya ki"
"Me Kuma na yi? Daga abun arziqi?"
"Ihun me ake neee a gidannn...kutiri Yah Jiddah wa ya qarar da ruwan drum din nan? na rantse da...."
Da sauri Jiddah ta fita tsakar gida ta tari numfashin qanin nasu, ta ce,
"Kar ka rantse masoyi, ni ce na yi wanka, na yi wanke wanke sannan na wanke mana uniforms d'in mu har da naka duba can ka gani"
D'aga kai ya yi ya ga gaba d'aya uniforms d'in shi biyu a wanke har da gajerun wandunan shi da vests, se handkerchief d'in shi guda d'aya kamar rai, murmushi ya yi sannan ya ce,
"Auuu Ashe ke ce, ai na zaci Yah Balqis ce in ce Yasin se an biya ni"
Cikin rashin mutunci Balqis ta bude labulen d'akin ta ce,
"Iyyy Balqis qaramar katangar ka me dad'in tsallaka ba, to nima na yi wanka da ruwan se ka sa na biya ka Ubana"
"Ban yafe ba tom Wanda ki ka d'iba "
A guje ta bi shi suka hau zagaye gidan, ta na fad'in in ta kama shi se ta masa shegen duka, ba wanda ya kula su dan kuwa in ba gajiya suka yi ba ba za su bari ba.
D'aki Jiddah ta koma ta ga yanda Balqis ta kasafta tsarabar kowa da nashi, se ta kwashi nata ta nufi dakin Ummah dan kuwa akwai maganar da take so su yi Mai mahimmanci..........
*Read*
*Share*
*Comment*
*Thank you*
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 5:
A zaune ta tadda Ummah ta na qirga kud'ad'e masu yawa ta na murmushi, itan ma murmushi ta yi ta na cewa,
"Da dikkan alama komai ya yi daidai Hajiya Ummah, Umara ce ko Hajji?"
"Allah ya kira mu 'yar nan ba Dan halin mu ba, sai Dan rahamar sa da kyautar sa"
"Ameeen ya Allah Ummah"
"Uhumm Ina Jin ki, wace magana ce a bakin ki?"
Da Jin haka sai Jiddah ta daburce ta kasa furta komai,jikin ta ya yi sanyi qalou, da wanne Ido za ta kalli mahaifiyar ta ta ce bata son auren d'an Yayan ta akwai wanda yake burge zuciyar ta? Akwai Wanda take ganin zata iya rayuwar aure da shi za ta ji dad'in zama da shi Sama da d'an d'an uwan ta? Gaskiya idan ta yi wa Ummah haka za ta Sanya ta a bakin ciki mai yawa, ita Kuma har abada bata fatan ta sa iyayen ta a qunci, fatan ta ta zamo yarinya mai biyayya a koda yaushe,sannan ta wani fannin bata tab'a Jin qiyayyar Yah Major ba, kawai dai bata Jin soyayyar shi a ran ta kamar yanda take Jin qaunar wannan bawan Allah da ko sunan shi bata sani ba, sannan ta ya zata fara ture alqawarin shekaru ta kawo uzirin soyayyar da ba a ma fara ta ba, gashi bata da tabbacin shi wannan bawan Allah son ta yake ko Kuma burge shi kawai take.
"Kin yi shiru, ko akwai matsala ne?"
Kud'in gaban ta ta ture gefe saboda ta samu damar bawa d'iyar ta cikakken lokaci da hankalin ta.
"Ammm Ummah dama cewa na yi, Yah Major ya kawo min waya kin gani kuwa? Ki na ganin ya kamata na riqe wayar ba mu yi aure ba?"
Dan guntun tsaki Umman ta yi ta na murmushi,
"Har kin sa hawan jini na ya kusan tashi, ai na zaci cewa za ki kin fasa auren shi, baki ji yanda hankali na ya tashi ba, Jiddah auren Junior alkhairi ne a gare ki ke da 'yan uwan ki,ko bayan rai na Ina fatan za ki zama mai biyayya a gare mu domin samun ingantacciyar rayuwa a nan gaba, maganar riqe wayar da junior ya sai maki ai kema kin San ba wata matsala, ko ba komai d'ana ne shi fa? Yayan ki ne zai iya sai maki waya ko ba maganar aure a tsakanin ku, ballantana akwai maganar aure, ki ka sani ko kewar ki yake Yana so ya dinga Jin muryar ki idan baya nan?"
Cike da Jin matsananciyar kunya Jiddah ta miqe zata bar d'akin tre da fad'in
"Kaiii Ummahhhh"
Dariya Ummahn ta yi ta sake Jan kud'in ta gaban ta ta na lissafi, d'akin su Jiddah ta koma ta kwanta bayan ta Sanya wayar da ke kashe a caji, bata sake tab'a wayar ba har se da suka yi sallar isha'i, lokacin Sudais ya shiga gidan ta dakko ta nuna masa, albarka ya Sanya wa wayar ya Kuma gargad'e ta da Kar ta kuskura ya kama ta tana wani shashanci da wayar, ya had'a har da Balqis saboda ya San yanzu qarfin riqe wayar zai koma hannun ta ne.
Bayan sun ci abincin dare kowa ya kwanta, Sudais ya shiga d'akin mahaifiyar tashi da ke zaune zaman jiran shi, nan suka tattauna akan gagarumin abinda suke qulla wa ba tare da sanin kowa ba a gidan, suna tsaka da maganar suka jiyo dawowar Mahaifin su, a lokacin qarfe goma sha d'aya na dare ta gota, sallama Sudais ya musu sannan ya wuce soro inda yake kunna maganin sauro ya saka tabarma da zannuwa ya rufa ya yi baccin sa da pillow.
Balqis, Jiddah da Ihsaan kuwa a d'aki d'aya suke kwana, shi yasa kullum idan ya na yi masu rashin kunya Balqis ke cewa,
'Dole ka rai na mu tunda ka ga wajen kwanan mu yaro'
'Da da gado da katifa a wajen kwanan naku da ban raina ku ba, ku na fama da wata tsohuwar katifa tun ta auren Ummah ai dole raini ya shiga tsakani'
A duk sanda ya fad'i haka da kyar ake raba su dambe shi da Balqis,watarana Kuma idan bata Jin fad'an se ta kyale shi su yi ta cacar Baki.
Washegari tun asuba Jiddah ta farka ta yi sallah ta yi azkar d'in safe sannan ta fara taya Ummahn nasu d'ora abincin sayar wa Wanda a ciki suke cin na safe da rana,tunda Abbah ba bayarwa yake ba Shima anan ake debar masa.
Da sauri take yin komai kamar wadda ke tsoron Kar ta makara a makaranta, Balqis ce ta ce,
"Wai ke Yah Jiddah saurin me ki ke? Ba an gama jarabawa ba? Kin ce ba Zaki sake zuwa ba se ranar hutu to saurin na meye?"
"Ban sani ba uwar surutu, da sassafen nan Zaki ishen da magana,ki yi sauri ki gama na raka ku hanya"
Nan take Balqis ta gane me yayar ta ta ke nufi da raka su hanya, ta na so ta ga mystery man d'in ta ne,dariya ta fara ta na waqa tare da zura wandon makarantar ta a qafar ta ta dama.
"Soyayya ce ta had'a mu..."
"Bismillahr kenan Zaki saka kayan? Ke Wai me yasa ba Kya Jin magana ne Balqis?"
Dariya ta qunshe dan ta gane wannan fad'an har da haushin an gano ta ne,dan haka da qarfi ta furta,
"Bismillahi alladhi la'ilaha'illahuwa, shi kenan? Gashi Nan na yi addu'ar zan iya ci gaba da waqa ta?"(ana so kafin mutum ya cire kayan shi ya yi wannan addu'ar duba da cewa ba mu kad'ai bane a duk inda muke akwai aljanu akwai mala'iku, Allah ya kare mu daga sharrin shaidanun aljanu)
"Can ta matse maki"
Waqe waqen ta ta ci gaba da yi na soyayya Wanda suka ba wa Ummah mamaki dan Balqis ba ma'abociyar soyayya bace balle ta ce ko ita ce ta motsa, ba Wanda ya sake kula ta har suka kammala Shirin su Jiddah ta riqe Mata jakar ta suka fita Ummah na fad'in,
"Jiddah Kar fa ki jima, Junior na nan tafe cin abincin safe kin sani ko? Sannan ki biya ki siyo ganyen shayi daga nan zo karb'i har na manta ma, ki had'a da sugar"
"To Ummah"
Koma wa ta yi ta karb'i kud'in suka fita, suna tafe Jiddah na gyara hijabin ta tare da sauya tafiya, haka kawai take Jin wani farin ciki a ran ta zata ga mystery man d'in ta, kullum da safe take had'uwa da shi, da rana zuwa yamma Kuma ba ta ganin shi, ta ta'allaqa hakan da maybe ya na zuwa aiki ne ko kasuwa.
Ba su yi nisa ba kuwa suka tsinkayo shi zaune a dandamalin da yake zama na qofar gidan shi,bakin shi riqe da aswaki ya na gogawa, fuskar shi cike da dogon gemu mai matuqar kyau,idanun nan masu tafiya da Jiddah sun Sha kwalli se lumshe su yake yi,ya na ware su a Saman fuskar Jiddah, hannun shi riqe da wata had'ad'd'iyar waya ta zamani ya na waya.
Ta gaban shi suka wuce Jiddah na Jin yanda yake bin ta da kallo,duk da ta na Jin ta kamar zata fad'i hakan be hana ta Jin dad'in kallon da yake mata ba, kalmar da ta ji ya ambata ne ta Sanya ta waiga wa ta kalle shi,
"Ku kawo su amma da dare"
Da sauri ta juya ganin sun had'a Ido ya kashe Mata Ido guda d'aya, nan take ta ji ta kamar za ta narke a wajen, da kyar ta iya miqa wa Balqis jakar ta da ke rataye a kafad'ar ta, bankwana suka wa juna Balqis ta wuce makaranta ita Kuma Jiddah ta wuce shago dan siyan abinda aka aike ta.
Ta na tsaye ta miqa kud'in ganyen shayi da sugar ta ji iskar da take shaqa ta sauya da wani qamshi da Kuma wani qauri qauri, da sauri ta juya suka had'a Ido da mutumin da take kwana take tashi da tunanin shi,
'Wai wannan bawan Allah shi d'in waye?' ta ayyana a zuciyar ta da ke tsallen murnar ganin shi.
Kasa janye idanun su suka yi daga kallon junan su, banda murmushi ba abinda suke sakar wa junan su, Jiddah ta tabbata idan bawan Allahn nan be mata magana ba nan kusa to kuwa zata yi masa, saboda ya had'u ya yi mata kwarai, a yanzu da suka tsaya daf da daf se ta ji duk duniya ba da Wanda za ta iya zaman aure ba da shi ba, da qarfi ta ji an ce,
"Ke Hauwa'u ga kayan ki"
Da sauri ta d'auke kan ta daga kallon ingarman namijin da ke gaban ta ta sa hannu ta karb'i ledar hannun mai shagon ta na masa godiya ta bar wajen da sauri.
Ji ta yi an ce,
"Baiwar Allah kin Yar da wannan"
Da sauri ta juya saboda yanda amon muryar shi ya ratsa kowacce jijiya a jikin ta, hannun shi ta kalla ta ga ba komai sai alamar heart da ya zana da hannayen nasa biyu,murmushi ta yi mai sauti ta kwasa da gudu ta yi hanyar gida, shi ma murmushi ya yi na gefen baki ya bi bayan ta da kallo har ta shige gidan su.
A tsakar gida ta ajiye ledar ba tare da ta kula da Wanda yake zaune a tabarmar a tsakar gidan ba ta fad'a d'akin su ta kwanta a katifar su ta na ta Jin dad'i da zabga uban murmushi Wanda za a iya Kiran shi da dariyar farin ciki.
Ummah ce ta bi bayan ta cikin hanzari, ta na shiga ta ga yanayin Jiddahn se ta tsaya saroro ta na kallon ta,
"Jiddah lafiya ki ke kuwa? Me ke damun ki? Wannan ba kalar tarbiyyar ki bane, ba halin ki bane, Junior ne fa a tsakar gida amma baki tsaya ki ka gaishe shi ba balle ki tsaya ku d'an yi hira kin tashi kin afko d'aki kamar baki da lafiyar kwakwalwa ko kin yi gamo."
Cikin murmushi ta miqe tare da ba wa Ummahn tasu hakuri sannan ta koma tsakar gidan ta gaishe da Major Muhammad Labbo, Wanda gaba d'aya ran shi a dagule yake, meke faruwa da jiddahn shi ne?
"Yah Major baka amsa min ba Ina gaishe ka, ko fushi ka yi? Ka yi hakuri to ba zan sake ba"
"To ai laifin naki ne ma da yawa, Ina wayar ki?"
Nan take ta tuna da sabuwar wayar ta, tun jiya da ta sa a caji a kashe har ta gama cajin bata kunna ba ta cire ta ajiye,goshi ta dafa ta shiga d'akin su da gudu Dan dakko wayar, se dai duk duban da zata yi wa wayar bata gan ta ba, hankalin ta ne ya tashi dan kuwa ta tabbata a jakar kayan ta ta saka ta to Ina ta shiga tunda ba qafa gare ta ba?
Ummah ta Kira ta sanar da ita me ke faruwa,nan da nan Ummah ta yi murmushin baqin ciki ta ce,
"Balqis ce ta dauka ta tafi da ita makaranta a yi wa qawaye papa, mu je Kar ki damu"
Su na fita Ummah bata boye wa Major me ya faru ba se suka hau jajanta halayyar Balqis suna mata fatan shiriya, kafin daga baya ta ba wa Major waje shi da masoyiyar tashi.
Hira suka fara sama sama inda Major ke matuqar Jin dad'in hirar, ta bangaren Jiddah kuwa hankalin ta na waje daidai inda ta bar bawan Allahn nan d'auke da hoton zuciya da ya zana da hannun shi.
Murmushi kawai take zabga wa Wanda yake matuqar yi wa Major kyau da Sanya shi nishad'i ji yake kamar Kar ya koma sai an daura masu aure, ya d'auke ta ya koma da ita abun shi, matsalar kawai an riga an yanke hukuncin shi zai aure ta bayan ta zana jarabawar ta ta qarshe amma.
Har bakin motar shi ta raka shi ta na masa Allah ya kiyaye hanya,
"Yah Major ka gaida Auntyna da yarana, ban zaci yau zaka koma ba da na yi masu kantun gana na soya masu gyad'a ka Kai masu,amma ba komai next time in shaa Allah za su samu wannan tsarabar na yi alqawari"
"Ko Kuma next time kin yi masu a can Abujan ba,"
Ya fad'a ya na sassauta muryar shi tare da kafe ta da idanuwan shi masu haske,duk Wanda ya kalli Jiddah da Major Muhammad zai San 'yan uwa ne, Dan kuwa hatta da kalar fatar su iri d'aya ne, manyan Ido kawai ya fi ta da dogon hanci, labb'an su iri d'aya ne duhun fatar su iri d'aya hatta yatsun hannayen su iri d'aya ne, kallon shi ta yi ta na murmushi ta ce,
"Yah Major ana jiran ka fa"
Kallon drivern shi ya yi ya ga ba ya kallon inda suke ma kwata kwata, murmushi ya yi sannan ya zaro kud'i a cikin aljihun shaddar da ya Sanya kalar coffee ya miqa Mata, qin karba ta yi zata gudu cikin gida ya yi saurin kama hannun ta ya Sanya mata kud'in sannan ya zare mata idanu, nan take fara'ar fuskar ta ta d'auke,dan kuwa shima wasa ya d'auke a fuskar shi, se da ya ga ta shiga taitayin ta sannan ya gyara riqon da ya wa hannun ta, ya riqe hannun kamar ya riqe kwai, cikin muryar Mai sanyi ya ce,
"My Queen ki yi hakuri zan koma da wuri, na so na d'an jima nima duba da cewa na jima ban zo ba, amma wani aiki ne ya taso jiya cikin dare aka Kira ni ana buqata ta a Abujan,ki kular min da kan ki, ki dinga barin waya a kunne, ita kuma wannan uwar rawar kan idan ta dawo zan kira ki had'a ni da ita,bata isa riqe waya ba da na sai mata kowa ya huta"
"To Yah Major Allah ya tsare,Allah ya bada sa'a da nasara, Ubangiji ya kare ku da kariyar shi ya baku nasara akan abokan gabar ku da abokan gabar qasar mu"
Ba karamin Jin dad'in addu'ar ta ya yi ba, ina ma a ce ta na a matsayin matar shi ta yi masa wannan addu'ar, da shi kadai ya San irin tukuicin da zai bata, amma ba komai Allah ya Kai damo ga harawa....
Da kyar Major Muhammad Labbo ya yi wa Jiddah sallama ya wuce, ta na nan tsaye ta na kallon wucewar motar su ta ga Mystery man d'in ta ya fito daga gate d'in gidan shi fuskar shi murtukkkk kamar hadari baqi a cikin duhun dare.
Gaban ta ne ya yanke ya fad'i, man da nan ta ji hankalin ta ya tashi,Kar dai ya ga duk abinda ya faru? Idan ya fasa furta mata kalmar so fa? Dan kuwa ta kula shi ma Yana Jin abinda take ji a ran ta game da shi,cikin sauri ta juya ta fad'a gidan su ta na furta.
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un,na shiga uku ni Jiddah, shi kenan labarin soyayya ta ya qare tun kafin ma ya fara"
Da kuka ta fad'a d'akin ta Wanda Ummah ta dauka na kewar Junior d'in ta ne, murmushi ta yi ta furta,
"Ohhh yaran zamani ko kunya babu"
Sudais ne ya shiga gidan bakin shi washe ya ce,
"Ummah Abbah ya fita?"
"Tabbb Kai ma ka sani ai, ya na gama karyawa ya fice,"
"Alhamdulillah ki shirya to mu je ki gani komai ya zama daidai an samu sak yanda ki ke so a qasa ma da kud'in da mu Kai hasashe"
"Dan Allah dai Sudais d'ina limamin makka mahaddacin sittin da hadisan Muslim da bukhari"
Dariya ya kece da ita, Dan kuwa ya na Jin dad'in kirarin da take masa,
"Ummah da gaske nake,a cikin unguwar nan ne ma Sako mayafi ki zo ki gane wa idanun ki komai"
Da sauri ta miqe ta zari mayafin ta dake Saman igiyar ta kwala wa Jiddah Kira ta ce,
"Jiddodon Umman ta taso ki fake kayan nan muje mu dawo yanzu da Yayan ku"
Cikin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 12