Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 12
kafurci ne, sun manta da cewa idan suka mace a haka wuta za su je, sun manta da cewar Allah da kan shi ya haramta wa kan shi zalunci sannan ya hana wa bayin sa aikata zalunci. Su na Isa bakin titi suka samu waje suka tsaya daga nesa suke hango motoci na tafe,K'wan da suka siyo na musamman dan tsaida motar da ta yi gardama suka d'auka,Wasu daga yaran Muido suka tasamma bakin titin, suna zuwa suka samu motar farko da ke zuwa a cikin motoci sama da biyar da suka hango, suka watsa mata kwai a gaban motar, nan take driver ya hau wiping gaban glass d'in shi, hakan na faruwa kuwa se ya dena ganin gaban sa, dole ta sanya shi cin burki, ihu su Muido suka Sanya sannan suka fito daga inda suka tsaya, suka tsaida sauran motocin da ke tahowa ta hanyar saita tayar mota su sakar mata harbi, gudun Kar su bud'e masu wuta kuwa dole driver ya tsaya, Wasu motocin ma tun kan su iso direbobin ke sauka su gudu su bar fasinjoji. Motar su Major Muhammad Labbo na can baya wanda gaba d'aya motocin bakwai baqin gilasai suke da shi, haka nan Muido ya ji ya na so su yi sauri su yi clearing wadannan motocin da ke gaban su su karasa can wajen motar su Major, su kuwa su Major suna ciki sun gama zama ready duk wani kaya da zai protecting din su sun Sanya sun saita bindigogin su jiran umarni kawai suke su tasamma yaran Muido, a zaman da suke na jiran umarni Major Muhammad Labbo ya d'aga hannayen shi Sama ya na addu'ar samun nasara(wannan koyarwar Goggon sa ce wadda a kullum take nuna masa samun nasarar shi na faruwa ne ta dalilin addu'a ba Wai qarfin shi ko dabarar sa ba, Dan haka ya Dage a duk sanda zai tunkari wani aikin ya dinga addu'a), suna kammala wa kuwa umarni ya samu na afka wa yaran Muido, nan take Babu b'ata lokaci suka bud'e motocin su cikin sand'a suka dinga bin jikin sauran motocin tare da nuna wa mitane su yi shiru Kar su nuna alamar da za ta Sanya su Muido gane akwai hukuma a wajen. Basu miqe daga duqen da suke ba sai da suka Isa daf da su Muido ya zamana sun kusan yi masu qawanya (zagaye su/zobe shi ne qawanya) sannan suka miqe tsaye tare da sakin wuta. Nan da nan waje ya koma filin daga, mutane na ganin haka suka hau shiga motocin su suna gudu Wasu da qafafun su suke arta su yi daji, su Muido sun jima su na qoqarin kare kan su, amma inaaa ba su samu nasara ba, an kashe da dama daga cikin su,an raunata Wasu irin mummunan raunin da sai dai ta Allah kawai, Wasu daga yaran Major ma biyu sun mutu an jinya ta mutum hud'u, shi kan shi major an harbe shi a hannu amma da alama ba wani shiga ciki ya yi ba naman hannun sa ta tab'a. Major da Muido ne aka tsaya ana kallon kallo, bayan yaran Major sun damqo shi an daure shi za a wurga bayan mota, cikin murmushin gefen baki Muido ya kalle shi sannan ya ce, "Sojan Jiddahna, amma fa ka shammace ni,a yanda na tsane ka na ke qin ka ci gaba da numfashi a duniya da na San ka na wajen nan lallai da na yi Shirin da da mun yi arangama se dai ka Ji ka a lahira" Murmushi kawai major ya yi kamar ba zai magana ba, tuna wa da halin da Jiddah ke ciki ta dalilin wannan azzalumin ya Sanya shi Kai wa Muido wani irin naushi Mai shegen zafi se da bakin Muido ya fashe jini ya yi tsartuwa, sannan ya ce, "Dama Kai ne la'anannen da ka d'auke min Mata? (Ya na fad'in matar shi Muido ya d'aga kai ya kafe shi da wani mugun kallo) To ka sani ba zan huta ba har se an yanke maka hukuncin kisa, idan hukuma Bata kashe ka ba ni zan kashe ka da hannu na" "Ai Kuma ka makara major, ka na ganin ba da hannun hukumar mike abinda muka ga dama ba a qasar har mu Kai qarfi muka gawurta haka? Na baka nan da Wasu 'yan satittika zan fito, Kuma zan dauki Jiddah na, wannan karon ko tana so ko bata so sai na aure ta, se dai ka mutu" Da qarfi Major ya sa hannu ya fizgi Muido da kan shi ya wurga shi bayan motar shi sannan su sani suka kama wadanda suka yi saura da ba su fi mutum biyar ba suka danna a mota suka ja sai garin Abuja, so suke komai dare su Isa garin na Abuja. Tafe suke Major na bada sanarwar suna buqatar backup na rundunar soja kafin nan kafin su Isa Abuja saboda Shirin ta kwana, ya na gama wayar ya Sanya idanun sa da kyau a kan kwalta saboda yanda yake Jin ya samu wata gagarumar nasarar da ko manyan ayyukan da ya yi wa qasar shi be tab'a irin wannan ba .......... [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 17: Gyaran murya ta yi tare da bud'e baki zata yi magana Balqis ta yi sallama ta shiga d'akin, rintse idanu Jiddah ta yi bata ji dad'i ba da Balqis ta katse ta wajen furta wa Yah Major sirrin zuciyar ta ba, a hankali ta bud'e idanun ta ta d'ora akan fuskar Yah Major da Balqis da ke mata magana, "Ki na ji kuwa? Na ce bari na je Goggo na na Kira na na ci abincin ta mai dad'in nan da nai kewa, ko Zaki raka ni mu ci tare?" Da sauri Jiddah ta noqe kafad'ar ta alamar ah ah, suna haka Aunty Sakee ta shiga ta zauna gefen Jiddah, idanun ta sun kad'a sun yi jawur saboda kukan da ta yi a lokacin da Ummah na bata labarin abinda ya samu Jiddah, ganin Jiddahn da ramar da ta yi se ya sake karya zuciyar ta, Major na fita ta kama hannayen Jiddah sannan ta ce, "Na samu labarin abinda ya same ki a wajen Ummah Allah ya kiyaye gaba ya wulaqanta Wanda ya yi maki wannan abun, Allah ya saka maki Jiddah, kalli yanda ki ka koma? Rayuwar nan gaba d'aya ta lalace zamani ya zo qarshe, jarabawowi kala kala suna ta samun bayin Allah, sannu Jiddah" "Yauwa Aunty, Ina Yara na,na yi kewar su," "Su na can sun bi Abdunnasir gidan Mom, sun so shigowa sanda daddy su na nan na ce su bari in sun dawo se su zo su gaida ki, sannu Jiddahn Ummah kin ga rayuwa kema" "Hummm" Shine kawai abinda Jiddah ta iya fad'a, cikin share hawaye Aunty Sakee ta ce, "Allah ya jiqan Addah Sophy, haka muka sha wahalar rayuwa har mutuwa ta riske ta, ba zan taba manta wannan mummunar ranar ba a rayuwa ta, gashi yanzu dad'i ya zo bata raye, yau labarin ki ya sa na ji kewar Addah Sophy ta kama ni fiye da kullum" "Allah ya jiqan ta Aunty, ki kara hakuri mahakurci mawadaci watarana sai labari, Allah ya jiqan magabatan mu ya qara wa iyayen mu da ke raye lafiya da imani" "Ameeen Jiddah, bari na je wajen su Ummah na bar ki ki huta, dan Allah ki dinga cin abinci, an ce min har yanzu baki yawan cin abinci ko akwai abinda baki sanar da su Ummah bane, idan akwai abinda ke damun ki ki fito ki fad'a Kar ki bar damuwa ta yi ta cin zuciyar ki, irin haka ne ake kamuwa da mugun ciwon nan na depression" "In shaa Allah zan dinga ci, ba wata matsala" "To shikenan bari na je" "Na gode Auntyna" Sakeenatu na fita, Jiddah ta hau tunanin rayuwar su Sakeenah da 'yar uwar ta. Sakeenatu da 'yar uwar ta sun taso a cikin gata sosai saboda kasancewar Mahaifin su riqaqqen d'an boko Kuma Mai ra'ayin kasuwanci kafin ya zama d'an siyasa a garin Katsina,mutum ne shi mai riqo da gaskiya da amana,shi d'in sanata ne Wanda mutanen garin su suka zab'a saboda gaskiyar shi da amanar shi da Kuma son taimaka wa mutane ba tare da mutanen sun riqe shi ba, matsawar zai San ka na da buqata Kuma ya na da ikon taimaka maka to fa zai taimaka. Mahaifin su mutum ne mai son iyalan shi matuqa gaya, wannan dalilin ne ya sa duk inda za shi da 'ya'yan shi mata biyu yake tafiya da matar shi, Addah Sophy ita ce babba, se qawar ta Sakeenatu, dika su biyun sun yi matuqar shaquwa da junan su da Kuma iyayen su, wani lokacin ma idan Mahaifin su zai yi doguwar tafiya kamar ta barin qasar tare suke yi har matar shi,ta zame masa kamar jakar shi saboda baya neman Matan banza, su kuwa yaran su basu yarda su ba wa masu aiki kula da tarbiyyar su ba, shi yasa duk inda za su je da yaran su suke tafiya, har Allah ya raya su suka Kai na Sanya wa a makaranta aka Sanya su,se yawan tafiye tafiyen nasu ya ragu saboda ba zai yu ana yawan yawo da Yara ba suna zuwa makaranta. Ana haka bayan su Sakeenatu da 'yar uwar ta sun girma, dan kuwa Addah Sophy ta gama secondary d'in ta ta shiga jami'a tana level 200, ita Kuma Sakeenatu ta na ajin qarshe a sakandire, a lokacin ne abokan siyasar Mahaifin su Sakeenatu suka ga ya matsa masu, ma'ana ya hana su sake wa su yi yanda suke so da arziqin kasa,ta bangare d'aya Kuma sun yi sun yi ya janye bincike da yake yi a kan rashin tsaro da ta'addanci da ke faruwa a garin shi na Katsina, se kawai suka had'a qarfi da qarfe suka qulla masa sharrin da sa hannun shi a shigo da makamai, duk wata shaida idan aka binciko wajen shi take nuni, duk yanda ya so ya kare kan shi ya kasa, a wannan lokacin ne ya had'u da Major Muhammad Labbo,ya yi iya qoqarin sa wajen taimaka wa Mahaifin Sakeenatu da shi da wani abokin sa Barr. Abdullah Darazau, basu huta ba har sai da suka wanke shi tsaf a kotu ya zamana an gane sharri aka yi masa. Ana haka wata ranar lahadi Major ya ziyarci Mahaifin Sakeenatu se aka aike ta ta Kai Masa ruwan Sha, tun daga wannan lokacin ta kamu da matsanancin son major,Wanda shi kuma Mahaifin ta a wani zuwan da Major ya sake yi ya Masa tayin auren Sophy har ya kira Masa ita sun gaisa, inda daga baya Major ya ce a bashi lokaci ya yi shawara da iyayen shi. Bayan tafiyar major a daren aka haura aka kashe Mahaifin su Sophy aka yi wa Sophy fyad'e, da ita da mahaifiyar tasu, suna gab da yi wa Sakeenatu fyad'e jami'an tsaro suka samu zuwa gidan, saboda Kiran su da maqota suka yi, nan dai suka gudu suka bar su cikin jini, wannan abun da ya faru ne ya Sanya kan mahaifiyar su Sakeenatu tab'uwa Wanda har yanzu bata da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa. Bayan arba'in d'in rasuwar Mahaifin su rayuwa ta fara gara wa su Sophy haka nan abokan siyasar Abbahn su za su zo su ce suna bin sa kud'i kimanin million kaza, ko ta duba Littafin da yake rubuta bashi ya ajiye saboda ta Allah idan ta kasance se ta ga ba wadannan kudad'en hasali ma shi ke bin su kud'i, duk yanda ta so ta hana su se sun San yanda suka yi suka tsorata ta ta bayar, ga lalurar asibiti suna kan yi ba fashi, saboda hauka tuburan mahaifiyar su ta yi a lokacin,ga makaranta suna zuwa,Wanda daga qarshe dole ta hakura saboda kula da mahaifiyar su. Har wannan lokacin major be koma ba, Sophy bata Kira shi ba har suka shiga wani mawuyacin hali, dangi duk aka guje su ba Mai taimaka masu, duk wad'anda Abbahn su ya taimaka wa a da sun guje su, qarshe ma qannen Abbahn su da kan su suka zauna suka yi rabon gadon zalunci gonar Abbahn suka siyar suka ce ta gadon su ce dama ya cinye,gida Kuma idan an raba su ma suna da gadon d'an uwan su,shagunan sa kuwa suka ce had'aka suka yi dan haka sai an raba da su. Haka aka gididdiba dukiyar Abbahn su aka basu nasu kason Wanda Sophy ta yi nazari sosai ta gane rayuwar nan idan baka da mahalli to fa kana cikin tashin hankali,duk kud'in ka idan haya ka ke se ka ga tawaya, dan ba zaka samu yanda ka ke so ba, Dan haka se ta had'a kud'in hannun ta ta sama masu qaramin gida, ta na ji ta na gani suka bar babban gidan su sauran kayan su se siyarwa sukai a wulaqance saboda qaramin gidan ba zai d'auka ba. Ita kad'ai ke kula da jinyar mahaifiyar su se Sakeenatu da ke taimaka mata, Dan tuni ta Dena zuwa makaranta ita ma, duk yanda ta yi wa qawaye da dangi bayanin ita ba a mata fyad'e ba sun qi ganewa kowa kallon 'yar Iska ake Mata. (Shin fyad'e Wai laifin waye ne? Laifin wanda aka yi wa ne ko Kuma wanda ya yi ne yake da laifi? Me yasa har yanzu mutanen mu an kasa ganewa ba a tausaya wa mutanen da aka yi wa fyad'e? Ba fa su suka Kai kan su ba, ba da son ran su bane fin qarfin su akai, amma haka za a sa wa mutum depression saboda an Masa fyad'e ba a bar shi ya ji da trauma d'in fyad'en ba se a qara wa mutum stress) Ganin tsana da tsangwamar sun yi yawa ne ya Sanya ta dena zuwa, gefe d'aya daidai da rana d'aya bata cire ran watarana za su sake haduwa da Major Muhammad ba. Bayan barin su unguwar kuwa da kwanaki Major ya dira a unguwar ya na neman su, saboda ya samu labarin abinda ya faru a qurarren lokaci, duk Wanda ya tambaya se ace Masa ba a San gidan da suka koma ba, mutanen da da Mahaifin su ya dinga taimaka wa sune suka juya masu baya. Haka Major ya gaji ya koma Kamba da qudirin watarana zai dawo neman su ko Kuma idan binciken da ya sa a Masa akan su ya samu zai dawo ya gan su. Ana haka watarana su Sakeenatu suka tashi gidan su ba komai na abinci, gashi duk sun sayar da valuable things da ke gidan gaba d'aya, ga mahaifiyar su na buqatar magani, Sakeenatu haka zata shiga bandaki da buta ta zauna ta yi ta kuka saboda ita tun dama acici ce bata wasa da abinci, Sophy ce ta miqe ta shiga ta yi wanka ta sauya kaya sannan ta kira Sakeenatu ta bata kula da mahaifiyar su ta ce zata je ta dawo. Ko da ta fita direct wajen aikin Mahaifin su ta nufa, ta na zuwa ta samu wani aminin Abbahn su ta Isa gaban shi ta durqusa ta gaida shi, sannan ta sanar da shi buqatun su, murmushi ya yi sannan ya ce, 'Taso 'yar albarka, muje office d'ina,ai ba zai gagara ba, yanda muke da Abbahn ku ai kin fi qarfin komai a waje na' Haka ta bi shi ta na murna dan kuwa ta San a yanda yake da kud'i zai iya daukan nauyin dawainiyar su har ma da ta Wasu be ji komai ba, su na Isa office din nashi se ta ga ya mayar da qofa ya saka key, sannan ya nufe ta ya na wani shu'umin murmushi, ya na zuwa sai ya sa hannun shi ya cafki mazaunin ta guda d'aya tare da Kai fuskar shi saitin kunnen ta ya ce, 'Na jima ina kwad'ayin wannan wajen, a kullum ku ka zo da Mahaifin ku sai na wuni tunanin mazaunan nan naki ta yanda ko gida na koma sunan ki ne a baki na, yau kin ga tunda ki na da buqatar kud'i ni Kuma Ina buqatar na huta da ke me zai hana mu yi wani abu?' Da qarfi ta samu dama ta kwace ta koma gefe ta na maida numfashi tare da zubar da hawaye, mamakin abinda yake faruwa da ita duk ya gama cika Mata ciki, yau ita ce aboki Kuma aminin Mahaifin ta ke neman ya lalata ta? 'Baba ban gane me ka ke Shirin aikata wa ba, Kar ka tozartar da amana da amincin da ke tsakanin ka da Abbah na, ka ji tsoron Allah ka taimake mu domin Allah, ni fa 'yar ka ce,' 'Ni ban haife ki ba, Kar kuma ki sake kira na da Baba,ki ban gishiri na baki manda, abinda ma 'yan ta'adda sun gama da wajen taimaka maki zan yi? Ke bari ki ji dika mutanen wajen nan da ki ke gani kwad'ayin ku suke, kowa dannewa yake dube ki fa ki ga komai ya ji' 'Hasbunallahu wa ni'imal wakeel' Da sauri ta nufi hanyar fita,kafin ya iso ta samu nasarar bud'e wa ta bar ma'aikatar ta na kuka sosai, gida ta wuce da qafa jikin ta har rawa yake saboda yunwa, ta na zuwa se ta tarar da Sakeenatu a sume Mahaifiyar su na Saman kan ta ta na kuka ta na dariya, idan ta yi kuka ta yi kuka ta rungume Sakeenatu se Kuma ta fashe da dariya ta tafa hannaye. Da gudu Sophy ta deb'o ruwa ta yayyafa wa Sakeenatu, ta na bud'e Ido ta hau Kiran sunan Sophy ta na ta taimaka mata da abinci yunwa zata kashe ta, Jin haka ne ya Sanya Sophy shiga maqota ta na kuka akan su taimaka masu ga halin da suke ciki, se kowa ya hau mitar sun gaji da ciyar da su, idan zata fita ta kama sana'a ta je ta kama Suma jalauta rayuwa suke, aron d'ari biyu ta yi a wajen wata maqociyar su da ke basu hakuri saboda ita ma ba wani abun kirki ne da su ba balle su taimaka masu,a guje ta nufi bakin titi ta tsaida machine ta haye ya maida ita ma'aikatar Mahaifin su, ta na zuwa ta fad'a office d'in abokin Mahaifin su ta na kuka take roqon shi da ya yi duk abinda zai da ita ya bata kud'i ta na buqatar kud'in, murmushi ya yi kamar ba zai kula ta ba se ya ce, 'Matso nan to mana, ko ni zan zo?' Da sauri ta Isa gare shi jiki na rawa ,nan take a office din shi ya biya buqatar shi da marainiya yarinyar Kuma aboki aminin sa, kud'i bandir d'in dubu dubu ya wurga Mata sannan ya ce, 'Idan ki na son Sama da haka gobe ki shirya ki raka ni wani waje har million d'aya se na baki' Ta na kuka ta d'auki kud'in ta bar office d'in,abinci ta fara siya masu sannan ta wuce gidan, ranar dai sun yi kwana ba yunwa ba qishirwa, ta ba da dubu d'aya a mayar wa da maqociyar su, tun daga ranar Sophy ta zama abokiyar holewar abokan aikin Mahaifin ta da ma wasu mazan da ke da kwad'ayi, a haka take samu su ci abinci ta biya kud'in maganin mahaifiyar su Sakeenatu ta zana jarabawar waec da neco, har ta samu dai daga qarshe ta amince wa wani babban d'an siyasa Shima ya yi amfani da ita ta baya ya bata kud'i masu yawa da alqawarin Kai mahaifiyar ta asibitin mahaukata na Abuja dan a bata cikakkiyar kulawa, haka kuwa aka yi, tafiyar mahaifiyar su asibitin mahaukata ke da wuya major Muhammad Labbo ya dira a garin Katsina ya na neman su Sophy again, wannan karon direct ma'aikatar Mahaifin su ya nufa Wanda da shawarar Mom ya yi hakan, ya na zuwa ya zarce office d'in abokin Mahaifin su Sophy, babban abinda ya bashi mamaki bai wuce jin an rufe qofar ta ciki ba, ya jima ya na kwankwasawa kafin aka bud'e ya na shiga idanun sa suka sauka akan na Sophy da ke qarasa gyara kayan ta, ba sai an fada wa mutum abinda ya faru a wajen ba Major ya gane, dan haka da sauri ya fita ya bar office d'in da niyyar ya bar su kenan har abada,ganin irin kallon da Major ya yi wa Sophy ne ya sa jikin ta yin sanyi ta bi shi da gudu ta na roqon shi da ya tsaya ya saurare ta ko na minti biyu ne. Da kyar Major ya tsaya ya saurari dika bayanan ta akan irin rayuwar da suka yi bayan rasuwar Mahaifin su da Kuma rayuwar da suke yi a wannan lokacin, Major Muhammad bai tab'a zaton zai zubar da hawaye ba akan tausayin wani saboda dakiyar sa, amma se ga shi ya na kuka saboda qarfin cin amanar da aka aikata, hakuri ya bata na saurin yanke Mata hukunci da ya yi sannan ya ce, 'Sophiyya na zo ne dan na amshi kyautar da Mahaifin ku ya yi min ta auren ki, Ina fatan kin shirya?' Cikin kuka Sophy ta ce, 'Me zaka yi da ragowar Maza? Me zaka yi da macen da ake amfani da ita ta gaba da bayan ta? Dan Allah ka nema wa kan ka da zuri'ar ka tsari da auren mace kama ta, Ina Mai neman alfarma a wajen ka, Dan girman Allah kar ka ce ah ah' Major na cikin tashin hankali dan haka ya amsa da cewar, 'In shaa Allah zan maki duk abinda ki ke so matsawar bai Sab'a wa Allah ba' 'Dan Allah Ina so ka auri Sakeenatu,yarinya ce nutsattsiya se 'yar shagwabar da ba a rasa ba, sannan Sakeenatu na mutuwar son ka dan kuwa ta Sha sanar da ni, ka taimaka min ko nauyi ya ragu a Kai na,' Da Jin haka major ya amince da bayanin ta sannan ya mata alqawarin zai gurfanar da wadanda suka cutar da su a kotu, cikin sauri ta katse shi ta ce, 'Babu buqata,mun bar su da Allah shine sarkin masu hukunci, ko me za a masu a duniya ba zan huce ba, ba zai biya abinda suka min ba,na fi so Allah da kan shi ya hukunta su' 'kin gama magana, yanzu muje na ga gidan naku ko?' Tun daga wannan lokacin Major yake zuwa yake Kuma basu taimako, amma dake an riga an lalata Sophy da bin Maza bata iya zama, se ta je an yi lalata da ita musamman ta baya in ba haka ba se tai ta Jin azaba a bayan ta, a haka har ta kamu da rashin lafiya Mai tsanani ta rasu. Major ya auri Sakeenatu ya Kuma sai wa mahaifiyar ta gida anan Abuja ya sa Mata masu aiki suna kula da ita ta ji sauqi se dai ba dika ba, har yanzu ta kan je ganin mahaifiyar ta ta raka ta karbar magani. Ajiyar zuciya Jiddah ta yi da ta gama wannan dogon tunanin sannan ta yi saurin kwanta wa ta rufe ido kamar mai bacci, leqa kan shi ya yi d'akin ya ga ta na bacci se ya yi masu sallama ya tafi gidan Mom tare da Sakeenatu. Bayan tafiyar su da magariba Ummah ta fito daga band'aki ta yanki jiki ta fad'i,dake Sudais na gida ya yi gudu ya d'aga ta da kyar ya maida ta daki, bakin ta ya karkace, harshe ya karye ba ta iya magana, Balqis kuka Ihsaan kuka Sudais d'in ma Jin shi yake kamar ya yi kukan. Jiddah ce ta ji kuka ya yi yawa ta lallab'a ta fito da taimakon dafe gini ta Isa d'akin Ummahn ta, ta na ganin halin da take ciki se itama ta zauna ta na hawaye,wayar Abbah suka dinga nema ta na ringing be d'aga ba, dan haka Balqis ba tare da shawara da kowa ba ta Kira Major, bugu d'aya kuwa ya d'auka tare da tambayar ta ko lafiya? Cikin kuka ta ce masa, "Yah Major Ummah ce, Ummah ce ta fad'i bakin ta ya karkace bata iya magana dan Allah ka zo ka taimaka mana" Major na Jin haka ya miqe tare da maida hular sa Saman kan shi ya d'auki makullin motar shi yana tafe ya na wa Mom da Sakeenatu bayani, Mom ce ta ce, "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, yanzu ace Ummahn Jiddah ta kasa cire damuwa a ran ta? Allah kar ka yi mana jarabawar da ba za mu iya dauka ba, yi Maza ka Kai ta asibiti" A guje Major ke Jan motar shi zuwa gidan su Jiddah....... *Longest chapter* [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR

Chapter 10 of 12