FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 18:
A qofar gida ya tarar da yaran baki d'aya riqe da Ummahn su da ke numfashi Sama sama, Jiddah na rakub'e jikin gini ta kafe fuskar Ummahn ta da kallo ko kiftawa bata yi,duk yanda Sudais ke mata magana ita da Balqis akan su koma cikin gida sun qi ji, a hanzarce Major ya bud'e motar shi ya isa gaban Sudais da Ihsaan da ke riqe da Ummahn,kama ta suka yi dikan su suka Sanya ta a mota, cikin bada umarni da tsare fuska Major ya ce,
"Ihsaan kama Jiddah ku shiga ciki kada ku sake ku fito ku rufe gidan,duk Wanda ya buga Indai ba Abbahn ku bane Kar ku bud'e"
"Toh Yah Major Allah ya ba wa Ummah lafiya,"
"Ameeen"
Jiddah babu bakin musu sai jikin bin Umarni, Dan haka ta na ji Ihsaan ya sa hannun shi a jikin ta ya taimaka mata suka koma gidan tare da rufe qofar gidan da sakata.
Daga asibitin Kamba aka tura su Ummah babban asibitin FMC(Federal medical center)na cikin garin birnin kebbi, likita ya duba ta sosai bayan an bata gado an daura Mata ruwa.
Major Muhammad Labbo ne zaune shi da Sudais a kujera a gaban likita ya na rattaba masu bayani game da ciwon Ummahn,
"Alhamdulillah an samu numfashin ta ya daidaita, amma a gaskiya zan fad'a maku ku had'a da addu'a domin kuwa sugar d'in ta ya yi tashin da ban tab'a ganin irin sa ba, ga Kuma Jinin ta da ya hau sosai Shima, Allah ya bata lafiya, yanzu zan rubuta alluran da za a qaro da Kuma magunguna, in shaa Allah muna saka ran ta samu sauqi nan kusa da izinin Allah"
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, mun gode likita, dan girman Allah ku yi iya qoqarin ku, za mu dage da addu'a Allah ya tashi kafad'un ta, na gode"
Sudais kam ba baki sai Ido, gaba d'aya ya rame ya yi zuru zuru, idan wani abu ya samu Ummahn su ya za su yi a rayuwar su? Ita ce uwar su ita ce uban su, basu da Wasu manyan abokai da suka wuce ta daga shi har qannen shi, ita ke basu shawarwari na rayuwa,ita ke masu nasiha, da ita suka bud'i idanu tun daga jariranta har girman su, yau ya za su yi idan wani abu ya same ta?"
Kuka ya fashe da shi suna Isa d'akin da Ummahn take, hannun ta ya kama ya hau sambatu,
"Ummah Dan Allah ki tashi, ki yi qoqari ki samu lafiya, ba zamu iya ci gaba da rayuwa ba idan wani abu ya same ki, Ummah ke ce komai namu a rayuwa, idan babu ke wa zai kula da mu?"
"Allah, Allah ne komai naku Sudais, habaa kar ka bani kunya mana kana magana kamar wani Ihsaan, be strong my brother, in shaa Allah za ta samu sauqi ok?"
Share wa Sudais hawaye major ya yi, kafin daga baya ya ce,
"Ka zauna bari na je na siyo magungunan na Kuma biya kudad'en da aka rubuta"
"To Yah Major Ubangi Allah ya saka maka da alkhairi mun gode"
Hararar wasa ya yi wa Sudais sannan ya ce,
"Kai tsaya ni ma Ummah ta ce ai ko ka manta ne? Ni ne d'anta na fari kafin Kai dan haka ka dena min godiya"
(Allah ka qara Mana zumunci a Koda yaushe mu na Jin yaran 'yan uwan mu kamar namu, saboda a rayuwa baka sani ba zaka mori yaran ka ko 'yan uwan ka ne za su more su? Idan baka koya wa yaran ka son'yan uwan ka ba to tabbas za su tashi cikin al'ummar da ke watsa zumunci na qarshen zamani, Wanda Allah baya son hakan, mu daure mu na qoqarin sada zumunci a tsakanin mu ko da kuwa ana korar mu saboda babu, ba ka da uziri ka ce Wai ana wulaqanta ka saboda suna da kud'i,gaishe su idan sun amsa sun samu Lada ka fi su Lada, idan basu amsa ba kana da lada Mai tarin yawa na sada zumunci, mu Kori shaidan mu bashi kunya a game da zumuntar mu, mu Gina rayuwar mu akan KYAKKYAWAR FAHIMTA)
Major Muhammad na tafe ya na waya da Mom da ta Kira shi dan ta ji ya jikin Ummahn se ga wayar Abbahn Jiddah na Kiran shi, sallama ya yi wa Mom ya amsa Kiran Abbahn,
"Ah ah Muna nan FMC daga can suka turo mu nan saboda jikin nata ya yi tsanani....Ok to Allah ya kawo ka lafiya"
Yana gama waya da Abbah se ya Kira Balqis ya ce ta had'a shi da Jiddah,sanar da shi ta yi tunda suka fita Jiddah ta yi alwala take ta sallah, murmushin Jin dad'i ya yi saboda irin wadannan halayen na Jiddah ke qara Masa son ta a cikin ran shi, cikin murmushi ya ce wa Balqis,
"Ki sanar da ita jikin Ummah da sauqi yanzu haka an saka mata ruwa numfashin ta ya zama daidai, wataqila ana iya sallamar mu ma gobe ko jibi"
"Da gaske Yah Major? Allah na zaci Ummahn mu mutuwa...."
Wata tsawa mai matuqar gigitarwa Balqis ta ji an sakar mata, da sauri ta saki wayar qasa tare da juya wa bayan ta, Jiddah ta gani ta na maida numfashi da sauri da sauri, idanun ta sun kad'a sun yi jawur, gefe daya kuwa Major kan shi ya Sha mamaki da Jin tsawar da Jiddah ta katsa wa Balqis,dama ta na da energy d'in yin wannan tsawar? Cikin b'acin rai Jiddah ta ce wa Balqis.
"Idan ki ka sake Kiran mutuwa a gidan nan se na babballaki shashasha kawai, ke baki iya addu'a bane se mugun fata?"
Duk da cewar ba a yanayi na jin dad'i ake ba be hana Ihsaan darawa ba, cikin dariya ya ce,
"Balqis d'in fa ba rake bace ba, ba Kuma Kara bace mutum ce Yar lukuta me tsokoki a jika ke yanzu Yah Jiddah aka ce ki balla yatsan ta ma ta Ina Zaki fara balle ki babballa ta?"
Dariya suka kwashe da ita shi da Balqis Jiddah kuwa ta yi tsaki ta koma ta zauna ta na ci gaba da tasbihi a ran ta, Major kuwa na Jin sun maida abun Wasa se ya kashe wayar shi ya gama abinda zai ya koma wajen Ummah da Sudais.
Abbah dai be tashi zuwa asibiti ba sai washegari da rana, sanda ya zo ya samu Ummah ta farfad'o har ta na iya magana,sai dai duk wanda ya ganta zai tabbatar da ta na Jin jiki, bayan ya gaisa da Major Muhammad da d'an shi Sudais se ya samu waje ya zauna a kujerar da ke jikin gadon ya na sake tambayar su yanayin jikin nata major Muhammad na bashi amsa, cikin jimami ya kalli Ummah ya ce,
"Allah ya baki lafiya Ummahn su, Allah ya tashi kafad'un ki"
Murmushi ta yi mai ciwo, sannan ta yi nuni da hannun ta akan ya matsa ta na son magana da shi, cikin zumud'i ya ja kujerar shi ya Kai kan shi saitin fuskar ta,cikin muryar marasa lafiyar da ke jin jiki Ummah ta ce,
"Abbahn su Ina neman alfarma a wajen ka...Dan Allah...Dan Allah ba dan ni ba...ka taimaka..ka kula da yaran nan...wannan ciwon ya na tsorata ni...bana Jin zan rayu da Yaran nan rayuwa mai tsaho kamar yanda na ke so....a baya baka d'auki nauyin mu ba a matsayin mu na....Wanda Allah...ya d'ora maka nauyin namu a kan ka...a yanzu Ina neman alfarma ka kular min da Yara na kar ka bari su wulaqanta..ka na so ka yi kud'i ka yi arziqi ko ta halin yaya....na maka nasiha amma ka ki ji..ba zan bika mu yi arziqin da a lahira zai zame mana talauci ba....dan haka Ina maka nasiha da ka ji tsoron Allah...ka tabbatar da Jiddah ta auri Junior....ga Sudais nan idan ya samu mata ka taimaka masa ya yi aure..ka kular min da Balqis da Ihsaan kar ka bari su yi kukan rashi na...ka min wannan alfarmar Idan baka kula da ni a sanda nake raye ba..ka kula da yara na bayan mutuwa ta"
"Ke yanzu da ki ke maganar mutuwa wa ya ce maki mutuwa Zaki? Jinya ce kowa na yi Zaki tashi ki ci gaba da aikin alkhairi da ki ka Saba kin ji? Allah ya baki lafiya"
Tabbas jikin Abbah da Sudais da ke Jin su sun yi sanyi,Major Muhammad kuwa na can wajen ya na yi wa Dad d'in shi kwatancen inda suke,isar Dad d'akin ya yi daidai da jijjigar da Ummah ta fara yi,da gudu Sudais da majo suka fita Kiran likita, Dad na Isa gaban Ummah sai ya tsaya ya kama hannun ta ya na karanta mata kalmar shahada, Abbah ne ya ce masa,
"Kai wa ya ce maka mutuwa za ta yi? Gashi can an tafi Kiran likita"
Dad bai amsa shi ba har se da ya ji Ummah na ta maimaita kalmar shahada, hannun ta da ke cikin na Dad ne ya sake, jijjigar ta tsaya cakk, idanun Ummah na kallon Sama jikin ta ya miqe sambal, Dad na ganin haka hawaye masu zafi suka wanke masa fuska,hannun shi na rawa ya rufe mata idanun ta da ke kallon Sama.
A tare suka shiga d'akin su Uku, Major Muhammad, Sudais da likita,direct wajen Ummah suka nufa Major na fad'in,
"Dan Allah yi sauri ka duba mana ita, ko akwai maganin da zan qaro ne?"
Dad ne ya riqe hannun sa ya ce,
"Son se dai mu yi hakuri, domin Allahn da ya bamu ita ya karb'i abarshi,ba dan ya na ganin bama son ta ba, ah ah se dan shi ya fi mu son ta, ya na so ta je ta huta daga wannan duniyar mai rikici da tashin hankali, Sudais zo nan samu waje ka zauna ka yi ta mata addu'a,Kar ka manta da ilimin ka da kowa ya San ka da shi,Kai ne magajin limamin makka, ka yi aiki da addinin ka kar ka yi aiki da zuciyar ka,ba zan hana ka zubar da hawaye ba, amma kar ka yi kuka ko aiki irin na jahilan farko idan sun rasa wani nasu"
Wani irin numfashi Sudais da Major suke fidda wa na tashin hankali,gefe d'aya Kuma Abbah ne tsugunne kamar danqauyen da ya je gona zagayawa, gaba d'aya kan shi ya kulle, shin da gaske uwar yaran shi ce ta rasu ko dai wata ake magana?
Kafin su Dad su farga su San me ake Abbah ya zabga wani irin ihu ya sa kuka mai qarfi tare da fad'in,
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un,ke mutuwa! ke mutuwa ! yanzu kin raba soyayya da qaunar da aka zuba shekaru ana gina wa? Kai likita sake duba ta shi wannan be San komai ba dan aikin jinya ba bangaren shi bane balle ya San ta mutu ko ta na raye"
Cikin sigar lallashi Dad ya kama hannun Abbah, amma ya fisge ya na roqon a sake duba masa ita, be yarda ya bar likita ya fita ba se da aka sake duba masa ita ya tabbata bata raye sannan ya yarda ta rasu, kuka ya dinga yi ya na Kiran ,
"Allah ya jiqan ki mata ta mai biyayya marufin asiri na, uwar Yara na, yanzu wa zai ci gaba da kula da mu yanda ki ke yi?"
Cikin daure fuskar Dad yace,
"Dan Allah tashi mana meye haka? Ka dai San irin kukan nan bai da kyau a musulunci ko?"
"Kai ni rufen baki ka rabu da ni saboda ba taka matar bace ta mutu? Wayyyoo Allah na na shiga uku na lalace uwar yara na ta mutu mun zama marayu da ni da su"
Ganin Yana tara masu mutane ne ya Sanya kowa kyale shi,aka hau gyara ummah za a maida ta Kamba a ambulance, Major kuwa ba abinda yake tunani da ya wuce Jiddah ya ya zata ji idan ta samu wannan mummunan labarin na rasuwar Ummahn ta????
*Ya Allah ka jiqan magabatan mu ka yi masu rahama ka qara Mana hakurin rashin su*
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 20:
Abinda ya faru da Abbah kuwa shine, a yunqurin sa na zama wani hamshaqin mai kud'i ne ya had'u da maqoci mai irin halin shi ya had'a da wani boka,bokan ya umarce shi da ya yi Wasu sacrifices Kuma ya gabatar da komai yanda aka ce,dan haka boka ya bashi Wasu 'yan kwanaki ya ce ya je ya jira shi zai neme shi,haka kuwa aka yi, Abbah ya dawo gida ana ci gaba da jimamin mutuwar Ummah, kwatsam watarana ya na zaune a tsakar gida ya na Shan Iska bokan shi ya yi masa waya, ya ce ya je, cikin hanzari babu b'ata lokaci ya shirya ya tafi.
Ya na Isa boka ya d'auki wata qatuwar jaka ya ba wa Abbah ya ce masa,
"Duba nan ka gani, gasu nan kud'i ne a cikin ta fall amma fa na bogi, daga nan zuwa kwana uku za su zama na gaske amma se ka Sanya hakuri,suna komawa na gaske se ka d'auka ka Kai banki ajiya a nan ne ko da sun dawo jabun su Kai dai babu ruwan ka, kud'i ka Kai banki Kuma dole kud'i zaka Zara idan ka tashi"
"Yanzu ran boka ya dad'e dole se nan da kwana ukun ba za a iya Kai wa yau ba?"
"Eh ba a son garaje a wannan aikin ka bari se kwana uku sun cika se ka Kai ajiya banki"
"To shikenan boka na gode, Allah ya kaimu kwana ukun,"
Haka Abbah ya gama sallama da boka ya d'auki jaka, ya na zuwa gida ya wuce d'akin su direct ya boye jaka, tunda Abbah ya dawo da jakar nan ya duba ta ya fi a qirga, bini bini ya leqa se ya ga kud'i suna nan amma fake ne ba su koma na gaske ba.
Bayan kwana biyu Abbah ya gaji da jira, kawai ya d'auki jaka ya yi birnin kebbi dan ajiyar kud'i a banki, ko da ya Isa ya samu mutane ana ta hada hada kowa ka gani cikin sauri yake kasancewar ranar juma'a ce ba wani jimawa ake a banki ba, waje Abbah ya samu ya na ta zare idanu,ma'aikatan yawanci sun tafi sallah,Abbah kuwa se kalle kalle yake, to abun ka da mara gaskiya, ganin irin jakar da ya zo da ita ne aka Kira manyan wajen aka Kai shi wani d'aki inda za a qirga kud'in kafin a ajiye masa su, ana shiga cikin d'akin aka bashi wasu takardu dan ya cike sunan shi kawai ya rubuta aka bud'e jaka za a fara qirga kud'in nan take suka gane fake money ne, ba tare da sun nuna masa sun gane ba suka fita dan zuwa Kiran securities, jikin Abbah ya bashi cewar sun gano shi, dan haka suna fita sun bada baya suna bayanin halin da ake ciki Abbah ya sud'ad'a ya shige 'yar qofar nan irin ta banki me qara, se qarar ma'aikatan wajen suka ji suna juyawa su ka ga Abbah ya afka ya fece, da gudu suka hau bada umarnin a tare shi, amma ina wani irin gudu gare shi kamar mota gashi ya samu ba mutane a waje an tattafi sallah, ya na fita ya tsallaka titi ya tsaida mai kabu kabu, ya ce ya Kai shi tasha shi ba ma a birnin kebbi ko Kamba ze kwana ba ma.
Yana zuwa ya tarar da mota na lodin sokoto ya afka, sauran cikon mutum biyu ya ce a ja a tafi zai biya, nan take ya zaro kud'i ya bayar driver ya sallami Yan tasha ya tada mota suka kama hanya,hankalin Abbah be kwanta ba se da ya ga sun bar garin kebbi sannan ya sauke ajiyar zuciya mai qarfi tare da fad'in,
"Lallai yau na Sha da kyar"
Ba Wanda ya ji me ya ce balle a zargi mutumin kirki ne shi ko na banza, suna Isa sokoto ya samu wani qaramin hotel ya kwana washegari ya wuce Kano,a cikin babban birnin Kano ya sauka a wata unguwa da ake kira da Rimin keb'e, ya bar marayun 'ya'yan shi da shiga damuwa da tashin hankali.
*Cigaban labari*
Muido ne zaune cikin mutane a katafaren gidan da aka yi masa maboya suna ta shagali da murnar dawowar sa, se wasanni suke kala kala ga kayan maye ana ta Sha ana ciye ciye da lashe lashe,waje dai se kace ana wani biki,gaba daya zaune yake a wajen kawai, amma hankalin shi da zuciyar shi basa tare da kowa na wajen, tunanin sa ya yi nisa kwarai, Ina zai ga Jiddah?
Wani matashi ne ya zo wajen shi ya duqar da kan shi saitin kunnen shi ya yi masa rad'a a kunnen shi sannan ya tsaya ya na jiran amsar uban gidan nashi, gani suka yi Muido ya miqe tsaye cikin tsananin farin ciki da murna, rawa ya fara yi Shima tare da mutanen da ke ta rawa ya na rawa ya Suri kwalbar giya Shima ya balle marfin ya kafa Kai ya hau kwankwad'a be aje ba se da ya shanye kwalbar tasss, wani irin ihuuu ya zuba ya hau yi wa kan sa kirari da yaren fuslatanci ya na wata jinjina da hannun sa ya na abu kamar Wanda zai fita filin daga.
Nan take mutanen nasu suka ci gaba da taya shi murna ba tare da sun San farin cikin da yake yi ba, yana gama kod'a kan shi ya wuce cikin gidan, direct band'aki ya nema, ya na shiga ya banko qofar dole na tsaya a waje dan na jira shi ya hito tunda dai bana afka ba ko?
Ina nan tsaye na ga kyakkyawan matashin ya fito, ya Sha wanka se dai matsalar kaya masu datti ya sake maida wa a jikin shi, idanun nan sun sha kwalli rambad'ad'au, gemun shi sai kyalli yake, ya rage gashin bakin da ya taru ya rufe masa bakin sa, se fuskar nan ta fito ta asalin Fulanin daji, parlour ya je ya tsaya ya na kallon kan shi a jikin glass d'in da ke bangon wajen, be jima da zuwa wajen ba ya ji takun qasaita da izza, ya na juya wa suka yi Ido hud'u da Allah Reni, murmushi suka sakar wa junan su, Muido ya Isa gaban shi ya Kai gaisuwa irin tasu ta 'yan daba, godiya Allah Reni ya yi sannan ya samu waje ya zauna a d'aya daga cikin kujerun masu matuqar kyau da tsada, nuni ya yi wa Muido da ya zauna, nan take ya samu waje ya zauna a kujerar da ke kallon ta Allah Reni, Allah Reni da Ido ya yi wa masu take masa baya alamar su basu waje, babu bata lokaci kuwa suka tafi waje ya rage daga Muido sai Allah Reni, gyaran murya Allah Reni ya yi sannan ya ce,
"A gaskiya Muido da mun rasa ka da mun tafka babbar asara, irin qoqarin ka da jajircewar ka ce ta sa shugabannin wannan qungiya take alfahari da kai, sannan muka so mu murd'e shari'ar da ake yi akan ka amma abun ya ci tura saboda wannan shegen sojan, da Wasu daga cikin hukumomin da ke son ganin bayan mu,wannan plan na sace ka ya zo ne daga manyan mu dan a ganin su idan aka rasa ka an yi babbar asara,tonuwar asirin ka tonuwar asirin mu ne baki d'aya, dad'in dad'awa Kai jajirtacce ne,nima Kuma na shaida hakan, dan haka Ina fata dawowar ka ta zama dawowar mayunwacin Zaki cikin namun daji,"
Muido ne ya kalli Allah Reni Wanda a girme shi muido ya girme shi sosai, amma a muqami Muido ne a qasa da Allah Reni, cikin murmushi ya ce,
"Ina godiya da wannan yabon da na samu Allah Saini am,ni yanzu bani da babban burin da ya wuce a bani dama na je na d'auki kadara ta da na bari, daga haka zan b'ace ba mai sake gani na sai dai aiki na,idan aka ban wannan dama zan yi matuqar farin ciki"
Fuska Allah Reni ya d'an had'e, cikin b'ata fuska ya ce,
"Kai yanzu ba zaka hakura da wannan yarinyar ba? Ga mata nan farare tasss kyawawa da suka fi ta kyau da komai amma ka nace ka kafe sai ita?"
Murmushi Muido ya yi sannan ya ce,
"Ba zaka gane ba sai ranar da soyayya ta zab'e ka ta shiga rayuwar ka ta yi kane kane a lamuran ka, a sannan ne zaka gane a duk duniya ba abinda yake da kyau ko ya fi abinda ka ke so kyau, Jiddah ba wata yarinya bace ta daban, Jiddah yarinya ce ta musamman, kyan ta ya na d'aukan hankali, natsuwar ta da riqo da addinin ta na daban ne, Dan kuwa ban tab'a ganin Mai irin sa ba, gaba d'aya rayuwar ta na tuna min da Addah petel ne, Ina Jin ta kamar wata sarauniya a cikin mata, hummm ba zaka gane me nake ji ba, sai ranar da jarabawar soyayya ta afka maka"
"Allah ya tsare ni da wahala, Kai dai da ka d'ora wa kan ka se ka je ka yi ta fama, Kuma ba laifi na ga hoton yarinyar ba qarya ta yi,.... ammmm Ina so daga nan zuwa juma'a me zuwa a fara aiki, zan sanar da Kai sabon wajen da zaka koma, wannan karon bama son a sake ganin ka sai dai a yi ta ganin ayyukan ka, zaka zama aljani wato boyayye a idanun bil'adama, kuma sananne a fagen yaqi da wargaza masu zaman lafiyar su"
"An gama Allah Saini,duk abinda ka ce haka za a yi in dai zan samu biyan buqata ta nima"
"Na baka dama ka sama wa kan ka farin ciki"
Ya na gama fad'in haka ya miqe zai bar wajen, har ya kusan Kai wa bakin qofa ya juyo ya kalli Muido ya ce,
"Kar ka bari soyayya ta rinjaye ka ka Sab'a mana,idan haka ta kasance zaka gwammace baka sake ganin yarinyar nan ba a rayuwar ka a karo na biyu"
"Ba wannan maganar, Kai ma ka San wanene Gorko Muido"
"Da kyau"
Ya na sa Kai ya fice Muido ya fita waje ya samu sabbin yaran sa ya fara basu umarni..
*****************************
A Abuja kuwa banda neman inda su Muido suke ba abinda jami'an tsaro suke yi, Kama daga kan sojoji zuwa 'yan sanda da duk wata hukuma ta farin kaya, da fari an qi bada sanarwar guduwar su Muido saboda a ganin gwamnati abin kunya ne a ce an zo an kwamushe qasungurmin d'an ta'adda a garin Abuja,amma daga qarshe dole aka sanar da al'umma saboda tsaron lafiyar su idan sun gan shi ko sun ji labarin inda yake a sanar da gaggawa.
Major Muhammad Labbo da team d'in shi na d'aya daga cikin jami'an da ke neman Muido Ido rufe, Dan kuwa nasu neman ya zama personal, cikin matsananciyar damuwa ya d'auki waya ya kira Jiddah a sabuwar wayar da ya sa Sudais ya sai mata Mai tsada da kyawu,ringin d'aya biyu a na uku ta d'auka tare da doka sallama.
Major na Jin muryar ta se ya ji wata kasala ta kama shi, jikin shi ya mutu, bashi da buri a duniya Sama da ya ga ya mallaki Jiddah a matsayin matar auren shi, ta ya ma zai bar Muido ya ci gaba da rayuwa a tsakanin rayuwar matar da zai aura ? Cikin muryar ta Mai zaqi ta kashe shirun ta hanyar gaida shi tare da tambayar shi aiki da mutanen gida, a kasalance ya ce Mata,
"Lafiya qlou alhamdulillah Jiddahty,ki na lafiya?"
"Lafiya qlou Yah Major"
Gyaran murya ya yi ya d'an gyara zaman shi sannan ya ce Mata,
"Ammm ki na ji na ko? Ki Kara addu'o'i akan Wanda ki ke yi,Allah ya bamu nasara akan maqiyan mu, maqiyan kasar mu da maqiyan addinin Allah wato musulunci, sannan ki daure ki na yawan zama a cikin gida Kar ki dinga fita, sannan kar ki dinga zama ke kad'ai ki na yawan zaman cikin mutane kin ji ko? Wannan shaqiyyin ya samu ya yi escaping daga hannun hukuma ta hanyar kawo hari da mutanen da suka yi a yau da safe...."
Cikin wata iriyar muryar da na kasa gane shin ta murna ce ko ta tashin hankali Jiddah ta miqe tsaye ta na fad'in,
"Iyeee ka ce ya gudu? Ina yake to yanzu? In kuka kama shi me Zaku Masa?"
Da sauri Major ya tashi zaune da kyau daga kishingid'ar da ya yi ya ce,
"Jiddahty calm down, calm down mana, yanzu haka bamu San inda yake ba he can be anywhere shi yasa na ke sanar da ke saboda ki qara kula wa, na yi waya a yau
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 12