Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 12
Wanda ke tare da Kai ko da baya son ka, na tsani in bud'e Ido in kalle ka, na tsine wa ranar da na fara ganin ka a rayuwa ta, Ya Allah ka yi min sakayya akan wannan bawa naka, Ya Rabbi Inni magalubun fantasir,ya hayyu ya qayyum Inni magalubun fantasir,ya Rabbi inni magalubun fantasir..." Bakin ta bai gushe ba ya na fad'an wannan addu'ar har sai da Muido ya daka mata tsawa cikin Wasu irin hawaye masu tsananin zafi Wanda rabon da ya zubar da hawaye haka tun ranar da ya rasa iyayen shi da qannen shi, sai gashi yau soyayyar Jiddah ta Sanya shi zubar hawaye, cikin kuka da sarqewar murya Muido ya ce, "Ya Isa haka, ya Isa haka, Jiddah tinda na zama qasungurmin d'an ta'adda ban tab'a neman abu na rasa ba,ke tun iyaye na na da rayuwa komai nake so Ina samu, Jiddah na hakura da mallakar gangar jikin ki da zuciyar ki, Jiddah zan barki ki tafi, amma se na karbi kud'in fansar ki kamar yanda ake karb'ar kud'in fansar kowa, zai zame min abun kunya na sake ki ki tafi ba tare da na karb'i ko sisi ba, me mutane za su ce? Shahararren d'an ta'addan nan da ya gagara ya gawurta ya rasa soyayyar shi? Inaaa ba zai yu ba, Jiddah iyayen ki za su fanshi rayuwar ki da kud'ad'e masu yawa masu tsada,ba ruwa na da babun su, ke ce ki ka jawo musu" "Da ka Sanya iyaye na a cikin baqin ciki da tashin hankali a karo na biyu na roqe ka da ka kashe ni ka d'auki gawa ta ka Kai musu, dan Allah Kar ka Sanya iyaye na a qunci da wahala bayan quncin da suke ciki a yanzu, basu da irin kudad'en da kuke ambata wa bayin Allah su Baku, Kar ka zama sanadiyyar da zan rasa wani a cikin iyaye na saboda tashin hankali da damuwa" Ko sake waiwayar ta Muido bai yi ba ya fice ya bar gidan,a ran shi ya na fad'in, 'Dole na karb'i aikin da Allah reni ya yi min tayin shi kwanaki na qi saboda bana so na yi nesa da Jiddah,ba zan iya jure ganin abubuwan da za a yi mata ba' Duk Wanda ya gan shi a ranar ya San akwai wani gagarumin tashin hankalin da ke dawainiya da rayuwar Muido, Jiddah kuwa addu'ar Rabbi inni magalubun fantasir ta dinga maimaitawa ta na kuka, fatan ta Allah ya kawo Mata mafita a wannan lamarin. **************************** Bangaren su Abbah da Ummah ma ba a bar su a baya ba wajen yawaita addu'ar Allah ya bayyana Jiddah, 'yan sanda na can na ta bincike, Wanda Ummah ta Kira da aikin banza, ai sun San inda azzaluman suke zuwa ne ba za su yi ba, se a b'ige da zancen ana bincike,wannan dalilin ne ya sa basu sake koma wa wajen 'yan sandan ba, sai dai idan su suka neme su. Abbah na zaune ya zabga tagumi saboda rashin Jiddah, se ga Kira da sabuwar lamba ya shiga wayar shi, jiki babu laka ya jawo wayar daga aljihun sa ya amsa tare da Kara wayar a kunnen sa,kukan Jiddah ya ji gefe kuma ana daka mata tsawa ana fad'in, "Baza ki yi magana ba? Ki yi magana ki dena wannan shegen kukan" Cikin kuka Jiddah ta ce, "A...A...Abb..Abbbbaaahh" Tunda Abbahn su Jiddah ya fara Jin kukan ta ya tashi a guje ya shiga d'aki inda Ummah take zaune Saman abun sallah ta na addu'o'i, a handsfree ya saka wayar Dan haka a tare suka ji maganar Jiddahn, can Kuma sai suka ji wani mutumi na magana, "Ku ne iyayen yarinyar nan me kafirin taurin Kan tsiya ko?" Cikin sauri Iyayen Jiddah suka had'a Baki wajen fad'in, "Ehhh mu nee, Dan Allah Kar ku cutar mana da yarinya, Dan Allah ku taimaka ku dawo Mana da ita" "A banza ma zamu dawo maku da ita kenan, to bari ka ji, tunda ta qi yarda ta auri Gorko Muido ta kafe ta nace Bata son shi mu ma ba za mu d'aga Mata qafa ba ba za mu yi maku da sauqi ba,Dan haka duk abinda ka ke ka tabbata baka saka hukuma a cikin lamarin nan ba, ba Wai Dan muna tsoron ta ba, ah ah kawai bama son harkar b'ata lokaci ka gane? Ka had'a kan million ashirin Muna nan zamu sake Kiran ka mu sanar maka inda zaka Kai ka d'auki 'yar ka" "Ranka ya dad'e...ranka..." Qarar tsinkewar wayar ce ta Sanya Ummah zube wa a qasa ta na fitar da wani irin wahalallen numfashi, Abbah kuwa bai tsaya b'ata lokaci ba ya Sanya takalmin sa ya bar gidan, be zame ko ina ba sai tasha, cike da tashin hankali ya samu motar da za ta je Niger ya haye, ganin irin damuwa da tashin hankalin da yake ciki ne ya Sanya yaron motar tambayar shi ina za shi dan kar ya shiga wrong mota, "Wajen masu kidnapping za ku Kai ni su bani 'ya ta Jiddah,sun d'auke min yarinya wata da watanni, yau sun Kira na Kai kud'i su bani 'ya ta ni Kuma bani da ko sisi, dan Allah ku Kai ni wajen su na roqe su su bani yarinya ta," Ganin yanda hankalin shi yake a tashe ne ya Sanya ba Wanda ya tambaye shi kud'in mota, har mota ta cika suka d'auki hanyar garin Niger, sanda suka Isa dare ya yi sosai, shagon Mai Saida indomie da shayi ya samu ya rakube ya na tunanin inda zai fara neman Jiddah. Mai shayi na kula da Abbah zaune a rakube har kowa ya tashi ya tafi shi Yana Nan, qarshe dai Shima tafiyar ya yi ba tare da ya yi wa Abbahn magana ba,washegari da safe Abbah ya bazama cikin gari duk Wanda ya gani a hanya sai ya nuna hoton Jiddah dake a wayar shi ya na tambayar ko akwai Wanda ya gan ta? Haka zai qaraci yawon sa dare ya yi ya samu wajen Mai shayin Nan ya sake bajewa ya kwanta. Ranar da ya cika kwana takwas ne Mai shayin Nan ya gaji da ganin shi a wajen Wanda ya tabbatar da a wajen shayin sa Abbahn ke kwana,Dan haka sai da kowa ya tafi Mai shayi ya Isa wajen Abbah ya Masa sallama, amsawa Abbah ya yi tare da miqa wa Mai shayi hannu suka gaisa, can se Mai shayi ya ce da Abbah, "Bawan Allah Wai me yake faruwa ne? Ina yawan ganin ka a Nan da dikkan alamu anan ka ke kwana, me ya kawo ka garin Nan?" Cikin jimami Abbah ya ce, " 'Ya ta na zo nema,ni mutumin kamba ne, yau kusan wata uku kenan da aka sace mana yarinyar mu budurwa har cikin gida, to na ji labarin Wanda suka sace ta sun yo ta Nan, shine na shigo gari nake neman ta" "Ikon Allah," Jujjuya wa Mai shayi ya yi irin na mutanen da za su yi gulma ba su son wani ya ji,sannan ya rage murya, "Ka na ji ba, akwai wani shugaban masu kidnapping a Nan garin Wanda shi ba boyayye bane, ka tashi mu je yanzu na raka ka ka Kai Masa kukan ka wataqila idan Allah ya so ka sai ya taimaka maka,amma fa za ka kashe kud'i" "Dan Allah ka taimaka min kamar yanda Allah ya taimake ka," Nan take kuwa Mai shayi ya janyo machine din sa ya haye ya ce Abbah ya hau su tafi, Nan da Nan kuwa ya haye machine suka kama hanya,tafiya suke, tafiya suke kamar za a bar gari,sai da suka yi tafiya Mai nisa sannan suka Isa wani katafaren gida Mai babban gate, tun daga hanya za ka ga mutane riqe da manyan makamai har bakin gate d'in gidan, su na Isa Mai shayi ya sauka ya gaisa da Wasu, Nan take Abbah ya gane da alama Mai shayin Nan aikin shayin nasa da biyu,ba yanda za ai ya zo wajen Nan Kai tsaye ba tare da ya San ya takan wani abu ba. Sun jima tsaye kafin a musu iso su shiga, kamar Abbah zai kife haka yake tafiya cikin sauri,su na shiga aka shigar da su wani parlour na alfarma, Abbah na nan zaune ya na jiran ya ga wani dattijo a matsayin shugaba a gidan, kawai sai suka ga wani matashi da ba zai wuce sa'an Sudais d'in shi ba ya fito sanye da wata danyar shadda ya samu waje ya zauna ya na wani murmushi kamar mutumin kirki. "Ah malam Idi Kai ne kazo? An samu wani bayani ne?" "Ah ah ran ka ya dad'e, wani bawan Allah ne ke neman taimakon ka,ni Kuma na San ka akwai taimaka wa bayin Allah shi ne na ce masa akwai wani oga na zan Kai ka wajen shi in shaa Allahu ko kana samun biyan buqatar ka" Wanda aka Kira da Oga ne ya ji kan shi ya Masa wani gingirim ya na bala'in so a yabe shi, Dan shi wannan kidnapping da raping da sayar da mugayen makamai da kwayoyi da yake a cewar shi ya na yi ne saboda taimakon al'umma, (kwakwalwa ta tab'u) Dan haka cikin wata Isa da Jin shi wani Mai share wa al'umma hawayen su ne ya kalli Abbah ya ce, "Uhumm ina Jin ka wanne taimako zan maka?" Abbah zama ya yi ya ba wa Matashin Nan labarin zuwan su Muido garin Kamba da yanda ya fara son Jiddah har ya samu nasarar sace ta, murmushi matashin ya yi sannan ya ce, "Wannan aikin Muido ne, yaro na ne ai, akwai wani aiki da na aike shi can garin naku, be samu yin nasara a aikin ba wato shine har ya iya fad'a wa soyayya, lallai na maka alqawarin yarinyar ka zata dawo gare ka Nan ba da jima wa ba, yanzu haka akwai wani aiki da na aike shi da jimawa ya qi zuwa se kwanan nan kawai Ina zaune ya yi min waya ya karb zai je aikin, yanzu haka baya gari Muido na da tsananin taurin Kai, Dan haka kafin ya dawo zan karbo maku yarinyar ku, amma fa dole zaka bada wani abu,Dan duk yanda zan so taimakon ku Kuma sai kun taimaki kan ku, ko ba gaskiya ba?" Cikin sauri Idi ya ce, "Kwarai da gaske ran ka ya Dade ai dama na San da ya kawo kukan sa Nan za a share Masa hawayen shi" Zube wa Abbah ya yi a qasa ya na zuba godiya da addu'ar, "Allah ya kare ku ranka ya dad'e daga sharrin gwamnati da Yan sa Ido" Dariya matashin ya kece da ita sannan ya ce, "Amin Baba, lallai ka na ji da wannan 'yar taka mu gan ta in kana da hoton ta" Da sauri Abbah ya lalubo hoton Jiddah a waya ya nuna wa Matashin, ko da ya ga Jiddah sai da ya sake riqe wayar da kyau, sannan ya ce, "Lallai dole Muido ya sato ta,kar ka damu za a dawo maka da ita ka tabbata ka had'a ko da million d'aya ne,na maka alqawarin zan aika da jirgin ruwa a dakko ta ka wuce da ita gida" Godiya Abbah ya yi sosai, sannan suka bashi wajen kwana a wajen, waje ya raka Mai Shayi sannan ya sake masa godiya ya koma ciki, ji yake kamar gari ya waye ya gan shi gashi ga Jiddah. A cikin daren matashin Nan ya bada Umarnin aje garin Mariga a dakko Masa Jiddah, Babu b'ata lokaci kuwa Abbah da ke kwance ya tashi aka shirya se Bakin teku,jiragen ruwa suka shiga suka nausa se garin su Muido Dan zuwa dakko Jiddah..... [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 11: Da misalin 11:38pm Abbah ya Isa Kamba,direct asibiti ya nufa inda aka sanar da shi matar shi na kwance,tunda ya je ya gan ta hankalin shi yake a tashe, ya tabbata rashin Jiddah ne ya sa jikin ta shiga wannan yanayin, "Allah ka tsine wa shegen da ya sace min yarinya, Allah ka hana shi rahamar ka, Allah ka tozartashi ka sa ya yi mutuwar wulaqanci, Allah ka ba wa Mata ta lafiya" Anan Abbah ya kwana Sudais ya wuce gida dan ya kula da qannen shi, washegari da safe se ga Kiran Yah Major ta wayar Sudais, bayan ya d'auka sun gaisa ne Sudais ke tambayar shi, "Ya jikin naka? Na ji jiya Mom ta ce baka ji dad'i ba, sannan yanzu ma a muryar ka na ji alamun rashin lafiya,dama sojoji na ciwo ne" Ya dan saka wasa dan Kar Major ya gano akwai matsala, "Lallai ma yaron nan, wato soja ba mutum bane ko? Shi kenan kar mu yi ciwo se a ce soja ne Kai fa ba ka Jin zafi, to mu ma mutane ne muna ciwo,muna mutuwa muna komai kamar kowa, Ina amaryar ta? Yau dai kam Kar Wanda ya ce min ba zan samu yin magana da ita ba" "Kashhhh ai kuwa ka makara, amaryar nan taka tsada ne da ita boye maka take, maybe ko dan an ce duk sanda ka zo za a d'aura auren ku ne shi yasa take maka wasan buya,ba su jima da tafiya asibiti ba Kai wa Ummah abinci, jikin ta ne ya motsa can ta kwana wajen Ummahn" Major ne ya yi qoqarin tashi ya zauna saboda Jin masoyiyar goggon shi ba lafiya, "Subhanallah yaushe ciwon nata ya tashi?" "Jiya ne," "Allah ya Bata lafiya ya sa kaffara,amma to me yasa Jiddah ta kashe wayar ta?" "Ni na Karba na ajiye saboda wannan yarinyar Balqis, duk yanda aka so a nuna Mata Kar ta na daukan wayar nan bata ji bata gani kullum se ta d'auka qawayen banza kala kala gasu nan ta yi a wayar shine na Karbe" "Ka yi daidaii idan na zo zan San ya za a yi da wannan rashin Jin maganar na Balqis" Suna gama waya Sudais se ya juya ya ga Balqis a bayan shi ta na sharb'en kuka, cikin rashin gane kukan na meye ya ke tambayar ta da, "Ke lafiya? Me akai maki?" "Yaya ba Kai ne ba, ka had'a ni da Yah Major gashi Nan Yana za a San ya za ai da rashin ji na, ka sani fa Ubana zai ci hankalin sa kwance" Dariya Ihsaan ya Sanya Sudais d'in ma se ya yi murmushi sannan ya ce, "Habaa autar Mata, Kar ki damu, ai idan ya zo zai ji meye asalin dalili so you don't have to worry yourself" Tunawa da Jiddah se ya Sanya jikin su mutuwa, addu'ar Allah ya bayyana masu ita cikin aminci suka yi sannan Sudais ya d'auki abincin asibiti ya wuce shi da Ihsaan wajen duba Ummahn tasu, saqon gaisuwa Balqis ta bayar sannan ta koma cikin gidan ta rufe ta shige d'aki ta rufe,dan tun da aka sace Jiddah take Jin tsoron ta kasance ita d'aya. ************************** A cikin watanni biyu da sace Jiddah rayuwa ta yi wa mata tsanani a wajen su Muido, dan kuwa har tunani take anya dama ya tab'a son ta ma kuwa? Ta tabbata idan da da akwai soyayya wannan wahalar da yake bata da azabar da ake guma mata ba zai yuwu ba, masoyi ba ya cutar da masoyin sa. Zaune take a takure kamar Koda yaushe, ta yi baqi ta rame ta yi duhu sosai fiye da asalin kalar ta, gashin kan ta me tsaho da cika duk ya cukuikiye waje d'aya, rabon ta da wanka tun wankan da ta yi a ranar da ta zo, gashi ta cika wata biyu a hannun su Muido yanzu,wajen ya zame Mata kurkukun asali, tun ya na fita da ita dajin da suke zaluntar mutane har ya daina saboda lokuta da dama idan ta je ta ga yanda ake yi wa bayin Allah to fa ta rikice kenan da koke koken watarana har da Suma. Tsakanin Jiddah da Muido an rasa wa ya fi sauqin Kai, saboda shi ya kafe se da amincewar ta zai aure ta,ita Kuma ta kafe ba zata tab'a auren d'an ta'adda ba. Idanun ta ta bud'e da kyar tare da Sanya hannun ta na dama ta na kare hasken ranar da ke haske Mata idanu, Balira ce tsugunne a gaban ta hannun ta riqe da abinci  ta kawo wa Jiddah,cikin murya Mai rauni ta ce, "Dan Allah Jiddah ki ci abincin nan Baki ga yanda ki ka rame ki ka yi baqi bane,ki taimaka ki ci abinci domin lafiyar ki" Wani busasshen murmushi jiddah ta yi sannan ta kalli Balira ta ce, "Na fad'a maki ba zan ci ba,na gwammaci na mutu da na ci gaba da rayuwa anan," "Jiddah me yasa ki ke da taurin Kai ne?" Wani irin kallo Jiddah ta bi Balira da shi, kallo ne na mamaki, kallo ne na tuhuma, "Ni ce me taurin Kai? Me na yi na taurin Kai? Da ace Baku dakko ni daga gidan iyaye na ba da ba Wanda ya San na ci ko ban ci ba, da tuni Ina tare da 'yan uwa na muna cin abinci Kwano D'aya da mahaifiyar mu, me yasa ku ka shiga rayuwa ta kuka tarwatsa min ita? Me yasa ba za ku bar ni na koma wajen iyaye na ba tunda ba kud'in fansa kuke nema ba? Tsakanin ni da ku waye me taurin Kai kenan?" Balira rasa abinda za ta ce ta yi, se kawai ta ajiye abincin da ruwa ta bar wajen, Jiddah kuwa watso su ta yi waje tun kafin Balira ta rufe qofar sun riga ta miqewa tsaye,cikin takaici ta d'aga kai ta kalli Jiddah, kad'a Kai kawai ta yi ta rufe wajen ta tafi ta na ayyana, 'Shi taurin Kai, ita taurin Kai, Allah ka kawo Mana qarshen wannan lamari' Ta na shiga d'akin ta tadda Muido sai Kai wa da komowa ya ke hannun shi riqe da tabar wiwi ya na zuqa, gefen katifa kuwa Fure ce ta zabga uban tagumi, a zuciyar ta ta na roqon Allah ya sa watarana Muido ya yi Mata Koda rabin son da yake wa Jiddah ne,ya nace Jiddah yake so ita Kuma Bata son shi, gashi ita da take mutuwar son shi ba ta tata yake ba,cikin zaquwa da zumud'i ya kalli Balira ya ce, "Ta ci abincin kuwa?" Jiki a sanyaye Balira ta ce, "Gorko Muido am ta qi cin abincin, na rasa yanda zan yi da ita, ta ce ka rabu da ita ta..." Marin da ya sauke Mata ne ya sa ta kasa qarasa maganar da ke bakin ta,cikin zubar hawaye tare da dafe kuncin ta ta d'aga kai ta na kallon idanun Muido da suka rine suka yi jajawur, kasa furta komai ta yi, saboda yanda ta ga bakin sa na motsi alamar zai ci gaba da magana da ita, "Idan na sake Jin kin furta kalmar rabuwa tsakani na da Jiddah se na kashe ki,zan kashe ki Balira na kashe banza na koma na dakko qanwar ki na aure ta na ci gaba da zama da ita,kin ji ko Baki ji ba?" Kasa furta ko da kalma d'aya Balira ta yi, Kai kawai take gyada Masa alamar saqon ka ya shige ni, "Da kyau, yanzu ki koma duk yanda za ki yi ban damu ba ki sa ta ci abinci ta Sha ruwa ba zai yu ace ta zauna da yunwa na tsahon kwanaki haka ba, se ta iya mutuwa" "Gorko..." "Ki je ki yi abinda na saka ki bana son musu !" A guje ta bar d'akin ta sake d'iban abinci ta yi wajen Jiddah da shi, ta na zuwa ta bud'e qofar idanun ta na zubar da hawaye masu mugun zafi gefen kuncin ta da ya Sha Mari har ya kumbura, ga shatin manyan yatsun Muido a farar fatar ta rad'o rad'o,ita ba dukan da ya Mata bane damuwar ta, Dan kuwa ba yau ta fara Shan Mari da dukan sa ba, babban abinda ya tsaya Mata a rai shine cewa da ya yi zai kashe ta ya dakko qanwar ta ya aura, shikenan in haka ta faru Mahaifin ta ko mahaifiyar ta wani a cikin su sai ya kamu da mummunan ciwon da zai zama ajalin sa, ba Dan komai ba sai Dan a yanzu haka da take hannun Muido iyayen ta basu Dena fatan ta koma gare su ba, to ina ga ya kashe ta ya da'u qanwar ta Kuma? Ba tare da Balira ta ce komai ba ta ga Jiddah ta ja abincin gaban ta ta fara ci, idanun ta na tsiyayar da hawayen da ta San ba za su taba tsaya wa ba in dai ba ganin ta ta yi a gaban iyayen ta ba. Murmushin yaqe Balira ta yi mata, ita kuwa Jiddah ta Kau da Kai ta na tura shinkafa da miyar da ko juya wa ba ta yi ba take d'iba ta na Kai wa bakin ta,naman ciki kuwa ko kallo be ishe ta balle ta ci, se da ta ci Rabi sannan ta Sha ruwa ta ture kwanon ta jingina da jikin gini, Balira na koma wa Muido ya ga alamar ta ci abincin se kawai ya hau godiya kamar ba shi ne ya gama Marin ta ba d'azu sannan daga bayan ya fice daga d'akin, ya na fita Balira ta zube a qasa ta hau kuka, Fure kuwa banda jan tsaki ba abinda take yi saboda haushin da ke cikin ran ta, ji take da zata samu shinkafar bera da zata Sanya wa Balira da jiddahn dika a abinci su ci su mace. A can daji inda suke gudanar da rashin imanin su Muido na tare da abokan shi tun na ruggar su suna hira yake Basu labarin yanda Jiddah ke wahal da zuciyar shi, cikin dariya d'aya daga cikin su da ake Kira da Jauro ya ce, "Gorko Muido fa Kai ka so haka take kasancewa da kai, ka duba ka ga dabar Me dawa su ko auren matan ma ba sa yi, kawai da ta maka ka ja ta ka kwanta da ita ko gaban mutane ko a d'aki,to amma Kai se ka ce se aure su muma Kuma ka sa Mana wannan dokar yanzu haka rannan Ina ganin aka kawo wata chika na so na d'an ehhh ka hana a banza aka kashe ta ban mora ba,sannan ta ya za a ce ma kana son yarinya qarama kamar wannan Wai ka jira izinin ta, Kai ba tsoron ta ka ke ba, Kai ba komai ba, ka bi yarinya ka taushe ka biya buqatar ka gobe ka qara har se ka dena Jin kwad'ayin ta sannan ka wurgar" "To ka ji in da aka samu matsala Jauro, Jiddah ba abinci bace da zan ci se na qoshi na ajiye ko na watsa wa kaji ko na watsar, Jiddah yarinya ce da zuciya ta ta kamu da so da qaunar ta, ba Wai sha'awa ba, da sha'awa ne da tun a unguwar su zan karbi abinda nake kwad'ayin na bar wa iyayen ta na dawo daji,aure Kuma da ka ke magana tun Ina ruggar mu ban San Zina ba, Ina ganin abokai na na wa Yara fyad'e ban tab'a ba Kai shaida ne, sannan ban yarda da nai ta yawo daga wajen wannan zuwa wajen waccan ba har na kwashi wani ciwon, Ina son nima yau ace an samu macen da nake so take so na, ina sha'awar hakan,ban dakko Jiddah ba sai da na tabbatar ta na so na, ban San me yasa yanzu ta sauya ra'ayin ta akai na ba" (Ka sace yarinya sannan ka ce baka San me yasa ta sauya ba to sanni me kan dankali) Hira suka dinga yi ana ba wa Muido shawara akan yanda zai haike wa Jiddah kawai ko da son ta ko ba son ta. Zuciyar Muido ta gama cika da maganganu akan ya samu Jiddah kawai ko tana so ko bata so ya kwanta da ita, Kuma tabbas zugar abokan shi ta yi tasiri kwarai a zuciyar shi, Dan haka da Shirin shi ya miqe Dan koma wa gida ya samu Jiddahn.................. [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 13: Ko da suka Isa tin daga bakin ruwa aka Kai wa yaran Muido su Hanafi sanarwar ga yaran Allah Reni nan sun shigo area din su, nan da nan kuwa yaran Allah Reni suka shiga gaba Abbah na biye suka ratsa ta kasuwa wajen shiruuuu saboda duhun dare ba kowa a kasuwar, su na Isa dajin da ake ajiye mutane suka nemi ganin Hanafi kasancewar sun San Muido baya Nan. Hanafi ne ya fito jikin Sa cike da kayan yaqi da wata shegiyar rigar sanyi irin ta mutanen China duk ta matse shi kasancewar sa qato,amma a haka ya tura

Chapter 7 of 12