wanda ya Sanya ta dena ji na wucin gadi,nuna ta ya yi da hannun sa idon shi na fidda ruwan masifa,
"Wannan da ki ke gani rayuwa ta ce, ban yarda ba Fure, ban amince ba ki wulaqanta ta, idan ki ka kuskura ki ka sake yi mata kallon da bai gamshe ni ba, sunan ki Matacciya, in na kashe ki ba abinda zai faru, dama iyayen ki basu San ko kina raye ko kina a mace ba,rayuwar ki bata da wani amfani a waje na, ita kuma idan na rasa ta zan shiga damuwa da tashin hankali,dan haka ki kiyaye... Balira ! Balira"
Cikin sauri Balira da ke Jin duk abinda ya ke faruwa ta fito daga d'akin ta na zuwa ta taya Fure kama Jiddah zasu shiga da ita d'akin da akai mata masaukin, suna yin kusa da d'akin Balira ta yi dabara ta karb'i Jiddah daga hannun Fure ta ce Mata zata qarasa da ita, cikin bacin Rai Fure ta kalli Balira ta ce,
"Oho Miki"
Ta wuce dakin su, ta na zuwa ta fad'a katifar ta ta dinga rizgar kukan baqin ciki, Ina ajin ta yake Maza a jama'ar Abuja da ke son ta haka ta dinga wulaqanta su, ita ce yau namiji ke mari akan wata kucaka illiterate? Ina ilimin ta ya tafi? Masters fa gare ta amma ta tsaya biye wa zuciya take son d'an ta'adda,d'an ta'addan ma da ya sace ta, d'an ta'addan ma mara ilimin arabiyya da boko irin Muido,hawayen ta ta share sannan ta hau tuno kyan fuskar shi,
"Tabbas kyan shi ne ya rud'e ni, kyan shi ne ya gigita zuciya ta ba komai ba, mutumin da ko a d'an aikin gidan mu bai kamata ya zo ba saboda rashin ilimi da wayewar zamani amma Wai ni Furairah shi nake so Kuma shi nake qauna Sannan shi yake wulaqanta ni? lallai soyayya bata yi min adalci ba"
Balira da ta gama gyara Jiddah ta bata abinci mai rai da lafiya ta qi ci, se ta qulle mata nama ta aje mata ruwa ta rufe wajen ta bar ta a nan dan kuwa iya taimakon da za ta iya bata kenan, ita kuwa Jiddah se ta ci gaba da kuka da addu'ar Allah ya fitar da ita daga wannan qangin wahala da tashin hankali Kar itama ta mutu a wulaqance.
Balira na shiga d'akin su ta tarda Fure na jimanta soyayyar da ta tsinci kanta ta na wa Muido, murmushi ta yi ta zauna sannan ta ce,
"Allah ya kyauta, shi so ba ruwan shi, baya shawara balle a yanke hukuncin inda zai shiga, makaho ne domin baya kallon sura kafin ya shiga zuciyar da ya zab'a,sannan kurmar ne baya ji balle ya gane yare ko qabila ko halayyar mutumin da ya yi niyyar yi wa nutso a zuciya, dan haka ni ban tab'a ganin laifin ki ba Dan kina son Wanda ki ka fi matsayi da muqami a rayuwa, sannan ni Kai na ina ga saboda makantar da so yake da ita ne ya sa har yanzu be hango tawa zuciyar ba, wataqila da ya dasa min mummunar gubar soyayyar Gorko Muido a tawa zuciyar, ki Kara hakuri ki Kuma cire girman Kai da qiyayyar da ki ke nuna wa mutane, wataqila hakan ne kawai zai sa ki zauna da kowa lafiya."
Dikkan kalaman Balira na shiga kunne da zuciyar Fure, amma girman Kai da Isa da jin ta fi kowa su ba ajinta bane ya sa ta buga tsaki ta banka wa Balira harara sannan ta ce,
"Dalla matsa village girl kawai, what do you know about love? Mtswww illiterate kawai"
"Oho dai koma me zaki ce ke ki ka sani ke ki ka iya wannan yaren kin ga ke zai wa ciwo dan ban san me ki ka ce ba, anan wajen bokon ki ba zata maki amfanin komai ba, dan da zata maki da ta fitar da ke da baki auri d'an ta'adda ba,aikin banza kina fama da shegen qaton goshi ki na wa mutane isar banza"
Tashi Balira ta yi daga zaunen da take ta bar dakin gaba d'aya ta koma wajen sauran matan yaran Muido suka dasa sabuwar hirar zagin Fure dan dama yawancin su suna Jin haushin yanda take mu'amalantar su a wajen, ita kuwa Fure wata iriyar sabuwar tsanar Jiddah ce ta d'arsu a zuciyar ta da matsanancin kishi, ji take kamar ta je kafin kowa ya dawo ta kashe Jiddah kowa ya huta.
Bangaren su Muido kuwa ranar ya harbe mutane sun fi uku, saboda tsananin b'acin rai, har suka gama abinda za su yi na kiraye kirayen dangin mutanen da suka kwamushe be koma daidai ba,Wasu daga yaran shi kuwa sun shiga gari karbar kud'in fansa, daf Muido zai koma gida suka masa waya suka sanar da shi cewar sun karb'i kud'in, izini ya bayar da su Kai kud'in can wajen babban ogan su da dare zai zo a raba, sannan ya bada umarnin a d'auki mutanen da aka biya wa kud'in fansa a Kai su gari a watsar sannan idan an samu Wasu a kwaso in ba a samu ba a bari zuwa gobe su tare babban titi su kwashe ko mota biyu ne zuwa uku haka.
Kwanan Jiddah bakwai a wajen su Muido ya yi daidai da kwana shida da zuwan Abbah cikin garin Niger, ya yi bulayi ya yi bulayi har ya rasa inda zai saka ran sa, kud'in wajen sa sun qare kafff wajen siyan man mota da cin abinci da Wasu buqatun,da dare waje yake samu ya rufe kan shi a mota ya kwanta da safe ya miqe ya bazama neman Jiddah.
Ana haka wataranar laraba ciwon Ummah ya tashi, Mom din Major ta je duba ta tare da jajanta rashin Jiddah, sannan ta sanar da ita rashin lafiyar da Major ya dawo ya na yi, Dan kuwa ya na can kwance a asibiti a Abuja ana bashi special kulawa,se ta tarar da Ummah a wani irin mawuyacin hali, Dan haka ba ta jira komai ba ta sa Sudais ya saka ta a mota driver ya ja su sai asibiti.
Suna Isa aka shiga da ita ganin likita Dan Bata taimakon gaggawa Dan kuwa numfashin ta da kyar yake fita, cikin kuka da karyewar zuciya Sudais ya roqi Mom akan ta Kira Abbah ya dawo haka a ci gaba da yi wa Jiddah addu'a har Allah ya bayyana ta.
Mom hannu na rawa saboda tausayin ganin halin da jarumin yaro kamar Sudais yake ciki ta zaro wayar ta ta Kira Abbah, Kira ta dinga yi har sama da uku be d'auka ba, saboda ya bar wayar a mota ya je ana ta masa kwatancen inda zai sake nausa wa dan neman Jiddah, be samu amsa wayar ba se da ya koma mota ya zauna sannan Kiran ya sake shiga wayar shi, cikin mutuwar jiki ya yi amsa Kiran Kukan Sudais ne ya kid'ima shi ya ce,
"Hajiya lafiya dai ko? Me ke faruwa na ji Sudais na kuka? Me ya samu Ummahn su"
"Dan Allah ka dawo gida,ka dawo mu ci gaba da addu'a har Allah ya bayyana ta, Umman su na cikin matsanancin ciwo, yau dai Bata sanin ma wa yake kan ta,shekaran jiya suka tattara suka koma sabon gida ga aiki ga kuma yawan tunani Ina Jin shi ne ya dago Mata da hawan Jinin ta"
Kifa kan shi Abbah ya yi a jikin steering wheel ya hau sauke numfashi,ta Yaya zai koma gida ba Jiddah? To in be koma gida ba wani abu ya samu Ummahn Jiddah fa? Zai zamana ya rasa mutane biyu masu mahimmanci a rayuwar sa kenan? Ba uwar ba 'yar?
Kamar Wanda aka mintsina kawai se ya wuce tasha, Nan ya samu ya yi lodin mutane daga Niger zuwa kebbi Dan ya samu Wasu 'yan kud'i a hannun sa,Babu Bata lokaci kuwa mota na cika ya hau titi se garin kebbi, tafe yake ya na tunanin halin da iyalin sa suke ciki, anya ba abubuwan da yake aikata wa a boye bane suke bibiyar rayuwar shi tun kan burin shi ya cika???
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 9:
D'aki Balira ta koma dan tabbatar da cewa Muido bai farka ba saboda tsananin tsoron shi take ji itama, hukuncin Muido baya tsallake kan kowa sai dai idan ba a yi masa ba daidai ba, dan haka addu'a take ta yi Allah ya bata sa'a ta taimaka wa Jiddah ba tare da ya sani ba.
A can madafi kuwa matan nan dama abinci kala biyu suke yi, abincin Muido da iyalan shi, yaran shi da su matan yaran na shi,Wanda abincin su na alfarma ne ake masu Dan Jin dad'in su, abinci ne ake masu na irin mutumin da ya yi aikin wahala ya Sami halal d'in sa se ya ce bari ya ci Mai dad'i dan barje gumin sa,sai Kuma abincin jama'ar Annabi da suke kamo wa,shi kuma abincin mutanen da suke kwamusowa abinci ne mara kyan gani a Ido Kuma mara dad'i a baki, dan wani lokacin ana sane ake dafa jellop rice ba Maggi daga gishiri sai tattasai busasshe, ruwa kuwa na kogin garin suke ba wa mutane, su Kuma ruwan Leda suke sha Gorko Muido kuwa ruwan roba yake Sha.
Suna kammala abincin suka Kai na iyalin Muido da shi kan shi Muido'n d'aki da Ido suka yi wa Balira alama ta kuwa miqe ta fita kamar ba wajen su za ta je ba, Fure ce ta yi tsaki dan ita haka d'abi'ar ta take da kowa ma bata shiri har shi kan shi Muido'n da take mutuwar so,abinci ta ja ta hau zubawa abun ta hankali kwance.
Balira na zuwa ta d'auki plate d'in da aka zuba wa Jiddah soyayyan dankalin turawa da kwai se soyayyan nama shayi aka had'a Mata a cup karami se ruwan Leda guda d'aya,a hanzarce Balira ta ke sauri Dan Isa inda Jiddah take, ta na zuwa ta bud'e qofar da aka maqala wa kwad'o ba tare da an datse ba,ganin Jiddah ta yi jingine a jikin ginin wajen, idanun ta duk sun kumbura sun yi jawur, Jiddah kuwa Jin idanun nata take kamar ba nata ba, wani irin yaji da zogi suke yi mata ko gani bata yi sosai se dai dishi dishi.
Cikin yin qasa da murya Balira ta durqusa a bakin qofar ta ce wa Jiddah.
"Jiddah daure ki tashi ki ci abincin nan kafin Gorko Muido ya farka"
Wani irin kallo Jiddah ta bi Balira da shi, Wanda ya Sanya Balirar Jin nauyin sake had'a idanu da Jiddah, cikin dasasshiyar murya Jiddah ta ce,
"Ba ruwan ki da ci na ko Sha na,ki je ki ci gaba da faranta wa mijin ki ta hanyar shiga gidan mutane ki gane sirrin su ki je ki sanar da shi shi Kuma ya sace su ya Kai su inda ya ga dama ko ya kashe su ko ya azabtar da su"
Idanun Balira sun taru da kwalla dan kuwa ita kan ta tunda Muido ya ce ta je gidan su Jiddahn ta Kuma je ta ga yanda suke gudanar da rayuwa a gidan su gwanin sha'awa, sannan ta gane Jiddah yarinyar kirki ce se ta ji bata so ya sace Jiddahn, ba yanda za ta yi ne, da ta na da yanda za ta yi Kar hakan ta faru da tun a baya ta San yanda ta yi ta hana faruwar hakan, cikin rauni ta ce wa Jiddah,
"Ki gafarce ni Jiddah ni Kai na ba a son raina nake rayuwa a qarqashin ikon sa ba, an fi qarfin Mahaifi na ne, abinda baki sani ba shine hatta da abincin da za mu ci sai sun bamu izinin me za mu noma a gonakin mu, sannan se sun karbi haraji a kowacce gona da aka yi shuka cikin ta, hatta da 'yan kasuwa a garin Nan basu tsira ba,duk abinda ka ke siyar wa suna da kamasho a ciki, Mai garin garin nan kan shi se yanda akai da shi wato Mahaifi na, ba shi da katabus a karagar mulkin sa, ya na iya zartar da hukunci Gorko Muido ko shugaban Gorko Muido d'in su hukunta shi shi kan shi saboda be nemi shawarar su ba, dan da dare kuka shi go ne amma da Zaki ga kowacce unguwa ko layi akwai mutane da kayan soji da makamai, to yaran Gorko Muido ne da kuma Wasu qungiyoyin, idan suka ga dama suna iya zuwa su kwace wa mutum shanun sa da dabobin sa Kuma dole ya hakura dan ba yanda zai yi, kuma ba hukumar da za ta karba wa mutum haqqin sa su ne hukumar, da wannan bayanin nawa nake fatan Zaki gane abinda na yi maki tursasa ni aka yi dan Allah ki samu ki cinye ki bani kwanon na mayar saboda ki samu qarfi a jikin ki,tunda ya ce Zaki Sha wahala to fa tabbas Zaki Sha wahalar Indai ba kin aminta da qudirin sa bane"
Kallon abincin Jiddah ta yi, amma gaba d'aya ta rasa ta Ina ma zata iya d'aukan wani abu ta Sanya a cikin ta, ko irin yunwar nan da ke tasowa mutumin da ya jima be ci abinci ba ya ga abincin Jiddah bata ji ba, lura da hakan ne ya Sanya Balira daukan dankalin ta Kai bakin Jiddah, kamar ba zata bud'e bakin ba, can dai ta bud'e Baliran ta sa Mata dankalin, Balira bata bar wajen ba se da ta tabbata Jiddah ta ci iya cin ta ta Kora shayin, sannan ta bar Mata ledar ruwan pure water'n ta tafi da sauri, a hanya ta had'u da Sadi ya bi ta da kallon tuhuma, yaqe ta yi ta ce,
"Qani na daga Ina haka?"
"Aunty Balira ai ke zan tambaya daga Ina haka?"
"Auuu abun haka ne ma? In tambaye ka ka maido min da tambayar Kai na, lallai qanin Nan nawa ka girma da yawa, ko dake jiya ai na ji ana cewa ka ci gasar Gorko Muido ya ce zai baka Mata, to Ina fatan dai ka zab'i me kyau a cikin su ko?"
Nan take Sadi ya washe baki ya hau bata labarin yarinyar da ya ga ta fi kwanta Masa a rai, tafe suke har suka Isa inda ake ajiye kayan wanke wanke ta ajiye sannan suka tsaya suna ci gaba da magana da Sadi, cikin zuciyar ta kuwa gode wa Allah take da ta shashantar da shi be gane abinda ta aikata ba balle ya sanar da uban gidan sa da yake wa tsananin biyayya.
Muido ne ya fito cikin shigar shi ta kayan sojoji idan ya na garin Mariga, kallon Balira ya yi wadda ta yi sakk kamar ba abinda ta aikata, durqusawa ta yi ta gaida shi ya amsa tare da fad'in,
"Ban gan ki ba wajen cin abinci ashe ki na nan Kuna ta surutu ke da qanin ki"
"Iyyy ai na ci ni se dai na qara, na ga kana bacci baka tashi ba shi yasa na d'iba na ci"
"To da kyau, yarinyar can ta ci abinci kuwa?"
Da sauri Balira ta ce,
"Eh ta ci na ga sun Kai Mata, se dai bata ci wani abun kirki ba"
"To da kyau ai a qalla ta ci"
"Hakane"
Wuce ta ya yi itama ta bar wajen ta koma d'aki tare da gode wa Allah da ba Wanda ya gane me ta yi, direct inda aka ajiye Jiddah Muido ya nufa, ya na zuwa ya gan ta zaune kan ta jingine da gini, wani irin tausayin ta ne ya kama shi Wanda rabon da ya ji irin hakan har ya manta, bud'e qofar ya yi da kyau yanda zai gan ta da kyau, Jiddah kuwa kafin ya bud'e ta yi sauri ta boye pure water'n da Balira ta bata a bayan ta, ta sake Jan rigar ta ta rufe qirjin ta da kyau,gyaran murya Muido ya yi kafin ya ce,
"Abar qaunar Muido kin tashi lafiya? Allah dai ya sa kin sauya ra'ayin ki, kin shirya zaman aure da ni?"
Harara ta banka Masa, sannan ta buga dogon tsaki,Muido ne ya gyara tsugunnon da ya yi a gaban d'an qaramin d'akin da take ciki sannan ya saki murmushi ya sake cewa,
"Tsiwar nan taki ta na burge ni,taso ki fito ki ga yanda muke gudanar da aikin mu, kin San kowanne ma'aikaci da safe ya na shirya wa ya tafi office d'in shi, to nima na gama hutu na a unguwar ku na dawo bakin aiki"
"Aikin shiga wutar? Ka je dai ka yi abun ka ba inda zani"
"Ki na da zab'i ne dama?"
Miqewa ya yi tsaye cikin murya Mai kaushi ya ce,
"Ki fito yanzu"
Da Jin yanda muryar Muido ta fito Jiddah ta San ba wasa, dan haka ba dan ta so ba kan dole ta ja jiki ta fita daga d'akin,ta na fita ta miqe tsaye se ta ji qasusuwan jikin ta na wata qara gaba d'aya jikin ta ya Mata tsami, bin shi ta yi a baya kamar raqumi da akala har suka fita daga gidan.
Tafiya suka yi Mai d'an nisa kafin su Isa wani daji wajen duk ciyawa anan ne ta ga mutane kala kala, abun tausayi, Jiddah bata San hawaye na kwaranya a idanun ta ba se da ta ji gishirin su a bakin ta, bakin ta na rawa ta nuna mutanen da ke kwance cikin sanyin ruwan daminar ga ciyawa da ta fito Wanda da gani akwai Wasu halittun masu cizo a wajen, ashe ta na ganin an azabtar da ita ba ta sani ba a waje Mai kyau ta kwana? Cikin rawar murya ta ce,
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un,wadannan mutanen anan suka kwana?"
Muido ne ya tsaya da tafiyar da yake zuwa wata kujerar roba ya dawo baya daidai inda Jiddah take ya duqar da kan shi daidai kunnen ta ya ce,
"Cewa za ki yi anan suke kwana? Ba anan suka kwana ba, ke ma ki na gab da fara kwana da su idan ba Zaki bi abinda nake so ba"
Shiru Jiddah ta yi saboda wani irin tsoro da ya ziyarce ta, ta ya za ta iya fara kwana anan dajin? A Ina zata kwanta? Idan maciji ko kunama suka cije ta fa? Idan akwai wani mugun abun a cikin wajen fa?
Abincin da suke ci ta kalla, wata iriyar cab'abb'iyar shinkafa ce, ko ruwan Sha babu,ci suke kuwa hannu baka hannu kwarya kamar Wanda suka yi shekaru basu ci komai ba, kuka Jiddah take ta na fad'in,
"Ya Allah ka kub'utar da mu daga wannan qangin rayuwa da muka fad'a, Allah Kai Mai tausayin bayin ka ne ka tausaya Mana"
Zama Muido ya yi a kujerar shi ya na bin su da kallo d'aya bayan d'aya, idanun shi ya sauke akan wata Mata fara tasss ta Sha leshi , da alama leshin ya na da tsananin tsada,hannun ta ya Sha baqin lalle da ja, nuni ya yi da a miqo ta, a gaban wani qaton mutum aka ajiye ta, cikin muzurai mutumin ya ce wa matar,
"Bamu lambar mijin ki ko wani naki"
Jikin ta na rawa ta Kira No mijin ta shi kuma ya na loda wa a waya, ta na gamawa ya sa ta miqewa tsaye sannan ya danna Kiran, wayar na ta ringing ba a d'auka ba, kallon ta qaton mutumin ya yi ya ce,
"Idan na sake kira bai d'auka ba se na kashe ki"
Cikin kuka matar nan ta hau addu'ar Allah ya sa mijin nata ya d'auki Kiran da ake masa, ai kuwa ana sake Kira sai gashi ya d'auka tare da yin sallama, matar na Jin muryar mijin ta se ta fashe da kuka, cikin tsananin tashin hankali mijin ta ya hau Kiran sunan ta,
"Nafeesatuna ke ce? Nafee Ina ki ka shiga muke ta neman ki? Babu inda ba mu je ba saboda neman ki, Nafeesah Dan Allah ki dawo gida yaran ki na tsananin kewar ki, Nafeesah ina kewar ki bana iya bacci bana iya cin abinci saboda rashin ki, naf...."
"Kai dallah malami rufe wa mutane baki, Wai Kai romiyo ko? To me zai hana ka biya Wasu 'yan kud'ad'e se a Sako maka Nafeen taka,in kuma ba zaka iya fansar rayuwar ta da million hamsin ba se kawai mu aikata lahira Kai ma se ka bi ta Kai da Yaran nata se ku had'e a can ko?"
Muido ne da yaran shi suka fashe da dariyar maganar qaton mutumin da Muido ya kira da Najashi,
"Shege Najashi wato sun had'e a can ko?"
Wani irin yage haqora ya yi shi a dole dariya yake, fuskar nan kamar an shafa mata mai, se na so take da maiqo, ga Wasu uba uban Zane guda biyu a gefen kan shi manya, da sauri mijin baiwar Allah'n Nan da aka Kira da Nafeesah ya ce,
"Ranka ya dad'e million hamsin? Ni yanzu Ina zan samo million biyar ma balle hamsin? Dan Allah ku sassauta mana mu bada abinda muka tara a kawo"
"Baka shirya karbar matar ka ba da alama, nan da jibi idan baka kira ka sanar da mu kud'i sun samu ba, za mu kashe ta dan mu ba wani amfani da zata mana anan"
Kashe wayar suka yi, suka sake damqo wata Mata dattijuwa, Dan kuwa da gani matar za ta Kai shekara sittin ko hamsin da wani abu, da alama hutu ya zauna a jikin matar, se dai abun takaici sun harbe Mata qafa ko tafiya bata iya yi.
"Ke tsohuwa d'an ki har yau ya kasa had'a million talatin, ya ce a Masa rangwame an Masa rangwame Amma saboda baki da mahimmanci a wajen sa shine ya kasa biyan million talatin ko?"
Cikin tsananin azabar ciwo dattijuwa ta ce,
"Ba haka bane, bashi da shi ne, da ya na da shi ko nawa ku ka nema wajen Audu zai kawo maku,"
"Bari mu Kira shi mu ji, idan har be had'a Mana kan kud'in mu ba a yau za mu harbe d'aya qafar taki, gobe Kuma mu harbe ki gaba d'aya ki mutu Audu ya huta kema ki huta"
Cikin tsananin tashin hankali Jiddah ta hau rawar sanyi, dan kuwa Jin kalmar za a sake harbin wannan dattijuwa ya d'aga mata hankali, jikin ta na rawa ta Isa gaban Muido ta Sanya kuka tare da kifa kan ta a qafafun sa da suka yi dumu dumu da tab'o sannan ta ce.........
More comment more typing my beautiful fiful.
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 12:
Ko da ya Isa gida ya tarar da gidan ba mutane sosai duk yawanci matan sun tafi gona da mazajen su karb'ar kud'in haraji da suka Sanya wa bayin Allah,idan basu bada kud'i ba a loda wa machine kayan abinci Mata na zaune a bayan machine riqe da buhuna su dawo gida ko su wuce kasuwa su sayar wa da 'yan kasuwa,direct wajen da ya ajiye Jiddah ya nufa, zuciyar shi na qara kwad'ita Masa kusantar ta, bud'e d'akin ya yi tare da leqa kan shi, halin da ya tarar da Jiddah ne ya yi matuqar tsorata shi, da sauri ya miqa hannayen shi biyu ya tallabo ta,wani irin warin daud'a da warin wani abu da bai San ko menene ba yake ji na fita daga jikin ta,ya na fito da ita ya durqusa a gaban ta ya na kallon yanda ta koma qashi da rai,komai nata ya zagwanye ya rairaye ba wani abu da zaka kalla ya burge ka jikin ta,ga jini nan duk ya lalata Mata rigar jikin ta Wanda Muido ya rasa daga Ina Jinin ke fitowa,(tun zuwan ta idan ta na period ba Mai kula da ita, to Wanda ba a kula da rayuwar shi ba wa zai kula da wata al'adar shi?) neman sha'awar da yake ji akan ta ya yi ya rasa,tausayin ta ne mai tsanani ya mamaye zuciyar shi, Balira da Fure ya dinga kwala wa Kira amma shiru ba bu ko d'aya a cikin su, da sauri ya zube makaman jikin Sa a qasa ya nufi bakin rijiya zai ja ruwa Dan ya yi mata wanka, gani ya yi ta miqe ta na bin gini ta koma d'akin da ya dakko ta, sakin gugar ya yi ya bi ta zai sake fito da ita, nan take Jiddah ta dinga wani irin ihu da kururuwa kamar zata tsaga gidan, banda dukan hannayen shi da ke tab'a jikin ta ba abinda take yi, Muido kam har mamakin inda ta samu qarfin dukan shi yake, cikin kuka ya ji ta na fad'in,
"Na tsane ka, na tsani duk wani
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 12