ta shi a dole dan gayu.
Gaisuwa suka yi irin tasu kafin daga baya su isar da saqon Allah Reni, nan take Hanafi ya ce,
"A gaskiya ba zamu ba da ita ba ba tare da an bada kud'in fansar ta ba, wannan umarni ne daga shugaban Gorko Muido, Dan haka ku koma da bawan Allahn nan duk sanda ya had'o kan million ashirin sai ya karbi Yar shi,"
"Mu kuma mun zo maku da umarni daga Allah Reni ya ce a bada ita a million d'aya a yau ba sai gobe ba"
"Ina million d'ayan?"
Nan fa Abbah ya hau zare Ido, dan ko nera hamsin bashi da su a aljihun sa, gyaran murya ya yi ya hau bayani,
"To yanzu tunda mun samu sauqi Ina neman alfarma a yi min lamuni zan yi waya gida se a Saida wata kadarar tawa se a aiko da kud'in,kun ga ni ban San abubuwan za su zo da sauqi Kuma da sauri haka ba"
"To kun dai ji se ya shirya kud'in dan haka se ku koma har se an kawo kud'in za a d'auke ta, harkar nan fa kun San yanda ake yin ta be kamata Kuna yi mana haka ba"
"Dan Allah ku taimaka min in gan ta ko sau d'aya ne kafin na kawo kud'in,"
Jinkiri Hanafi ya yi ya na nazari, can dai ya ce su bi shi, gidan Muido suka je suna zuwa aka fito da Jiddah, Abbah na ganin yanda Jiddah ta koma, sai ya susuce ya hau sambatu,
"Jiddodon Ummah ke ce kuwa? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, Jiddah me ya same ki haka? "
Jiddah kuwa tsabar kuka ta kasa cewa komai qoqari take ta isa gaban Abbah, amma an hana ta, nan take yaran Allah Reni suka fiddo makaman su da ya fi na yaran Muido, suka saita yaran Muido,Balira ce ta fito dan ganin me yake faruwa ta na ganin za a tafi da Jiddah se murna ta kama ta, ta hau hamdala da fatan Allah ya Basu Sa'ar kub'utar da Jiddah.
"Hanafi hakuri za ku yi mu Kai wa Allah Reni yarinyar nan ya ajiye maku ita har a kawo kud'in fansar ta,mu bamu Isa mu koma masa babu ita ba ka San halin shi, idan muka koma ba ita da mu da ku dika kowa zai d'and'ana azabar shi ba zai kyale mu ba kun sani"
"Haka zalika idan kuka tafi da ita muma zamu d'and'ana azabar Gorko Muido dan haka dole ku yi hakuri har a kawo kud'in fansar ta"
Nan da nan hayaniya ta kaure a tsakanin su, se yaran Allah Reni suka kasu Kashi biyu, Wasu uka sace Jiddah suka tasa qeyar Abbah da ke a matuqar tsorace Kar a kashe shi be cika burin rayuwar shi ba,nan suka nufi kogi dan su gudu Wasu suka tsaya dan hana a bi bayan su, duk yanda suka so abun Kar ya Kai su da zubar da jini hakan bata samu ba, dan kuwa bayan tafiyar su Jiddah ba jimawa fad'a ya kaure, nan take suka dinga yin shi babu kama hannun yaro.
Su Jiddah kuwa na Isa suka hau jiragen ruwa suka fara tafiya, sun yi nisa suna tafiya suka ga Wasu jiragen sun biyo su, ana ta haske su da torch light me hasken gaske, wuta suka qara ba wa nasu jiragen, duk yanda yaran Muido suka so su kama su Jiddah haka suka kasa, suna Isa bakin teku suka hau motocin su suka nausa cikin gari,haka suka rabu da yaran Muido suna masu albishir da ko bajima ko ba dad'e za su waiwayi su Jiddah dan ba su cika alqawari ba.
A gidan Allah Reni aka ajiye Jiddah da Abbah, tunda suka sauka Abbah ya yi waya gida ya ce gobe a Sanya motar shi a kasuwa, sannan Ummah ta had'a duk kud'in da ya rage Mata a aiko Masa ta account d'in sa,gashi ga Jiddah an ce ba za a bada ita ba sai an bada million d'aya.
Haka kuwa aka yi da safe Sudais ya dinga cigiyar Wanda zai sayi motar Abbah, da kyar ya samu wani tsohon driver ya ce zai siya, amma ba kud'i hanu ba za a samu dubu d'ari biyu kacal saura se daga baya, haka Sudais ya karbi wannan kud'in Ummah ta had'a dubu d'ari uku suka aika wa Abbah, Abbah na kuka ya je gaban Allah Reni ya kwanta ya na roqon shi akan ya taimaka Masa iya abinda yake da su kenan, ganin yanda Abbah ke ba shi girma dukda cewar ya haife shi ne ya Sanya Allah Reni amincewa zai karb'i dubu d'ari ukun,nan take Abbah ya Masa transfer Allah Reni ya sallame shi tare da bashi tabbacin ya kula da 'yar shi dan tunda yaran Muido suka ce za su waiwaye su to fa tsugunne bata qare masu ba.
Bayan tafiyar su Jiddah gida shi kan shi Allah Reni ya yi mamakin yanda ya sadaukar da rayuwar yaran shi dan taimakon ta Jiddah ba tare da ya San ta ba ko wata alaqa ta had'a su ba, (ni kuwa na ce ba bu bawan da zai shiga wani hali na damuwa ya yi addu'ar Rabbi inni magalubun fantasir face Allah ya kawo Masa mafita a rayuwar shi )
Gidan su Jiddah ya cika da dangi da maqota dan ganin ta inda Jiddah za ta bullo, sannan a wanne yanayi zata dawo, masu taya Ummah murna kuwa da farin ciki na gaskiya Suma ba a bar su a baya ba
Bangaren Ummah kuwa yanda zuciyar ta ke bugawa da zullumi da tsoro abun ba a cewa komai, gefe d'aya Kuma farin ciki da murnar bayyanar Jiddah sun hana ta sukuni, Balqis har da yin wanka ta Sanya kaya masu kyau Dan tarbar qawar ta Kuma yayar ta sannan aminiyar ta, Ihsaan kuwa ya share d'akin su ya gyara jakar kayan Jiddah kamar ta na nan, abinci aka dafa kala uku dika Wanda Jiddah ke matuqar so, se zob'o da aka yi saboda ta na son Shan zob'o.
Mom ta zo da Abdunnasir, a ranar ta shirya sanar da Major me ke faruwa Abdunnasir ya bata shawarar ta jinkirta har a ga dawowar Jiddah lafiya, Ummah ta ji dad'in ganin yayyen ta Mata da qannen ta tare da matan yayun ta Maza, se ta ji cewar ashe ba ita kadai ce ke cikin damuwar rashin Jiddah ba, ranar se ta zama kamar wani biki ake na musamman a unguwar dika, se barka ake yi wa juna. (Amfanin kasancewa yaron kirki a unguwa kenan ko mutumin kirki sanda duk wani abu ya same ka se a had'u a jajanta, Idan na farin ciki ya same ka se a had'u a taya ka murna)
Da yamma lisss su Abbah suka iso, ya so akwai inda zai tsaya Jiddah ta yi wanka ta sauya mugayen kayan da ke jikin ta da ko a tsumma suka zo ba za a iya amfani da su ba se dai a yaddar.
A lokacin da suka Isa gida mutane duk sun ragu,dangi ne na kusa ana ta jiran dawowar su, mota Abbah ya kawo har qofar gidan shi tana tsaya wa ya bude ya fita ya zagaya wajen Jiddah ya fito da ita ya yi wuf ya fad'a gida da ita,ba zato ba tsammani Ummah na tsaye bakin rijiya ta na wanke hannun ta da ta gama kwashe gawayin da akai girki ta ga shigar Abbah da wata baiwar Allah siririya kamar skeleton, rigar jikin ta kamar a nannad'e ta a cikin ta, kan nan kamar na mahaukatan da sukai shekara ba wanki, Jikin Jiddah ne ya fara rawa, saboda ganin Ummahn ta, hawaye ne ke zuba mata wani na bin wani,qafafun ta se kyarma suke da sauri Abbah ya damqe kafad'un ta da kyau ya jingina ta da jikin Sa, cikin rawar murya Ummah ta nuna Jiddah ta ce,
"Jiddahhh?? Jiddah na ce haka? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un,Jiddah ke ce ki ka koma haka?"
Kuka kawai Ummah take ba qaqqauta wa, Jiddahn ma kuka take, Balqis kuwa na zuwa bata damu da dattin da Jiddah ta yi ba ta kama ta ta rungume ta ta qi sakin ta, Dan ta kula ta na sakin ta zata fad'i,Ihsaan kuwa kasa zuwa inda Jiddah take ya yi, ya na can nesa ya na kallon ta ya na ta rizgar kukan, hatta da Sudais da Abdunnasir se da suka zubar da hawaye.
"To tsayuwar ta Isa haka, a d'ora ruwan zafi a wanke ta, a bata abinci ta ci a barta ta huta,"
"Kwarai maganar Baban Sudais gaskiya ne, ke Ummahn Jiddah ai hamdala Zaki yi tunda ta dawo da ran ta, se a duqufa nema mata lafiya,kama ta Maza Balqis ki yi bandaki da ita ruwa kam an riga an tafasa shi, se dai in an juye wannan a qara saka wani dan kuwa wanka uku ma sun yi kad'an"
In ji cewar Mom da ke share hawaye.
Nan da nan yayar Ummahn Jiddah ta kama ta suka yi bandaki
aka dasa kujera aka zaunar da Jiddah, ganin busasshen Jinin al'ada a jikin kayan Jiddah ya sake Sanya ta kuka duk jarumtar ta, wato haka mutane suke wulaqanta idan an kama su musamman Mata.
Ta na yi wa Jiddah wanka ta na kuka Jiddah ma kuka, se za ta miqar da ita dan wanke Mata mazaunan ta da suka yamushe kamar Leda se ta ga Jiddah na duqa wa ta na abu kamar me tsoron Kar ta bige kan ta da wani abun,ba komai ya jawo haka ba sai Jin ta da take kamar a wannan quntataccen d'akin da bata iya miqe kafa ko tashi tsaye, tuna wa da kalar zaman da ta yi a wajen nan ne ya Sanya kukan ta tsananta, kwakwalwar ta se ta sake tuno Mata sanda za su bar garin bata ga Muido ba Ina ya je? Me ya same shi bayan ta sanar da shi bata son shi bata qaunar shi?
Ta na tsaka da tunanin nan ta ji an sake Sab'a mata sabulu, se da aka wanke Jiddah wajen sau bakwai sannan Innar ta ta duba gaban ta, ta tabbata ba abinda ya same ta, hamdala ta dinga yi ta na Kuma wa, sannan ta ga Jinin ya tsaya se ta sa wa Jiddah ruwa Mai kyau ta ce ta yi wankan tsarki idan ba za ta iya ba ta yi mata,cikin murya Mai rauni, muryar da ta gaji da kuka da kewar iyaye da dangi ta kalli innar ta ta ce,
"Innah ta na gode Allah ya saka maki da alkhairi ya maki tukuici da aljannah, Innah baki ji yanda na ji dad'in jiki na ba Allah ya wanke maki zunuban ki, Innah ban zaci zan sake rayuwa a cikin ku ba, ban zaci zan sake ganin Ummah na ba da kowa da kowa, na zaci ko ba su min komai na cutar wa ba za su kashe ni idan na qi yarda da abinda yake so, lallai duk Wanda ya dogara da Allah zai isar Masa, na gode Innah na gode,"
Da gudu Innar Jiddah ta bar bandakin ta na kuka sosai saboda tausayin Jiddahn, ganin haka se ya tsinka zuciyar Ummah ta hau tunanin shikenan, rayuwar Jiddah ta lalace, shikenan sun lalata Mata yarinya, dan kuwa ta sanar da Yayar tata ta duba Mata Jiddah ko an lalata ta,tunanin da ya had'u ya wa Ummah yawa ne ya Sanya ta Jin Jiri na kama ta, tafiya ta yi luuu zata fad'i Allah ya bata sa'a akwai gado a gefen da take se ta dake ta zauna a hankali, idanun ta ta ke Jin sun mata nauyi kamar bata gani da su sosai, Kiran qanwar ta ta hau yi me bi Mata a hankali ta na fad'in,
"Shikenan Salmai sun b'ata min yarinya sun lalata ta, shikenan maganar auren ta da d'an uwan ta ta lalace na shiga uku Salmai sun lalata min yarinya"
Cikin rashin fahimta Innah Salmai ta ce,
"Ban gane me ki ke nufi ba fa Ummahn Jiddah?"
"Salmai kalli Yaya ta fito ta na kuka da dikkan alama ta ga abinda nake gudu, na shiga uku Salmai sun gama lalata min yarinya yanzu wa zai aure ta a haka?"
"Ni zan aure ta a haka"......
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 14:
Hankalin kowa se ya tattara ya koma kan mai magana a bakin qofar shiga parlour, qarasa shiga ya yi da sallama ya zauna a gefen Mom d'in shi, Innah Salmai ce ta fara gaishe shi dan gujewa ci gaba da maganar, da sauri Major Muhammad Labbo ya duqar da Kai ya hau gaishe su tare da yi masu jajen abinda ya faru da Jiddahn shi Wanda ba Wanda ya damu ya sanar da shi.
Cike da mamakin ya akai ya San me ke faruwa kowa ke kallon shi, kafin ya bud'e baki ya yi magana Innah ta shigo da Jiddah nade da zani baka ganin komai a jikin ta da ya wuce fata da qashi, se tulin gashin kan ta da ya Sha wanki yake digar da ruwa, manyan idanun ta sun yi zuru zuru tare da yin wani kwarmi me zurfi a Saman su,salati da tasbihi ga Allah kawai major yake yi ya kasa cewa komai sannan ya kasa d'auke idanun sa akan Jiddah da ta ke jin ta muzanta, kunya take ji matuqa bata so ya ganta a wannan yanayi ba, hawaye kawai take wanda ita da kan ta ta na mamakin yanda hawaye suka kasa yanke Mata iya tsahon wannan lokacin.
D'aki Innah ta shige da ita duba da yanda Jiddahn ke ta qoqarin tafiya amma ta kasa d'aga kafar tata ba tare da an taimaka mata ba, suna shiga ciki Major ya sadda kan shi qasa, tare da kulle idanun sa da yake Jin kamar an watsa masa yaji, jijiyoyin kan sa kuwa sun fito da kyau kamar jijiyoyin bishiya, hannun shi biyu ya had'e ya matse waje d'aya.
"A Ina aka samo ta?"
Shine abinda suka ji ya furta cikin wata iriyar muryar da basu tab'a ji ya yi magana da ita ba,nan take Mom ta shiga maganar saboda yanda ta ga ran Maza ya b'aci,
"A can Niger aka samo ta, Abbahn su ne ya San waje,"
"And all this while ba Wanda ya yi tunanin ya sanar da ni me ke faruwa, ko da ba ni zan auri Jiddah ba qanwata ce fa, Mom, Goggo qanwata ce fa Jiddah,shin ko dai ni ne ba d'an ku ba shi yasa ba a sanar da ni me ke faruwa da ita ba?"
Ganin yanda yake magana kamar ya tara yaran shi ne ya Sanya Mom had'e fuska ta ce,
"To yanzu ba gashi ka sani ba? Sanar da Kai meke faruwa a halin da ka shiga ai ba shi da amfani, se ya Kara maka damuwa, sannan ga ayyukan da ka gama akwai stress a tattare da Kai, tunda ka sani yanzu ai shikenan,"
Balqis na Jin ana neman a tona Mata asiri se ta lallab'a ta baro cikin d'akin Ummahn ta koma nasu na 'yammata Wanda ita d'aya ta ke amfani da shi saboda rashin Jiddah, ajiyar zuciya ta yi tare da dafe qirji ta ce,
"Na shiga uku,Allah ya sa kar Yah Major ya tona min asiri ya kira suna na, gani na yi an ce yau zata dawo shi yasa tun daren jiya na sanar da shi, yau Kuma ya hawo jirgi ya iso, ba shikenan ba magana ta qare? Su manyan nan se su yi ta kacancana zance salon kawai a kama bawa da laifi"
"Ke Kuma maganar me ki ke yi ke kad'ai? Ki na zaune kamar magen da ta saci kifi se uwar zufa ki ke ga fan a kunne?"
"Zufar qaniyar ka nake, na ce zufar qaniyar ka nake, Ihsaan ka fita a Ido na na rufe,"
"Ohhh na gane, ke ce munahikar da ta fad'a wa Yah Major Yah Jiddah za ta dawo yau ko? To ai da kyau gashi can ana had'a yanda za a baki jikin ki, gobe ma idan gulma sana'a ce ki saka jari me girma kin ga ribar ta fi yawa"
Cike da tsoro Balqis ta miqe tsaye ta na zaro indo ta maqale wayar Jiddah da ta sato take amfani da ita, boye wa ta yi cikin pillow ta zari mayafin ta za ta bar gidan har se tarzoma ta lafa ta dawo, karaf suka had'e da Yah Major da Sudais a tsakar gida Major na qara jaddada rashin Jin dad'in sa da ba a sanar da shi abinda ke faruwa ba,da sauri ta yi baya ta lab'e bayan qofar d'akin su ta na hango su ta tsabar qofar.
"Yanzu ba dan yarinyar nan 'yar albarka ta sanar da ni ba Sudais da girman ka da hankalin ka ba za ka sanar da ni ba? Kuma kullum muna waya, ka Kira ka ji ya jiki na da sauran su"
"Ka yi hakuri Dad ne ya hana a sanar da Kai da Abbah to yanzu gashi dai redio Mai jini da b'argo ta sanar da Kai"
"Kwarai ta sanar da ni, ni yanzu ai punishment d'in da na ce zan bata ya juye ya koma alkhairi Dan kuwa ita za ta riqe wayar Jiddah ita kuma zan kawo Mata wata anjima Dan Ina so na yi magana da ita"
Wani tsalle Balqis da ke lab'e jikin qofa ta daka ta fita da gudu ta rungume Major Muhammad ta na masa godiya, Shima murmushi ya sa tare da shafar kan ta, sannan ya ce,
"Daga yau kin zama ji na da ido na a gidan nan duk abinda ake ciki ki dinga sanar da ni musamman Wanda ya kamata na sani"
Qamewa ta yi sannan ta ce,
"Yes sir, permission to carry on sir"
Dariya suka fashe da ita, sannan ta kwasa da gudu ta shiga d'akin da Jiddah ke ciki, zaune ta tadda ta an saka mata kaya se zame wa suke, nan da nan murnar ta ta koma ciki,tunda Jiddah ta dawo duk sanda zata gan ta duk rawar kan ta sauka take,manta wa ta yi da abinda ya shigo da ita ta zauna a qasa, daf da qafar Jiddah ta karb'i plate d'in da Innah ta zuba mata abinci zata fara bata, ta d'ebi kad'an a spoon ta Kai bakin Jiddah,kafe ta da Ido Jiddah ta yi, sannan a hankali ta d'ora hannun ta da ya zama qashi da fata a saman kan Balqis ta shafa har zuwa kumatun ta,cikin dakusasshiyar murya ta ce,
"Balqis ke ce? Ke ce Zaki bani abinci a Baki ba Balira ba?"
Gyara zaman ta ta yi ta na kare Sama kamar abu zai fad'o Mata a Kai, saboda yanda take ji kamar har a wannan lokacin ta na cikin quntataccen d'akin gidan Gorko Muido,cikin hawaye itama Balqis ta ce,
"Ni ce Balqis d'in ki uwar rigima Yah Jiddah, bud'e bakin ki ki ci abinci, daga baya se ki bani labarin wacece Balira"
Jimmm Jiddah ta yi kamar wadda kwakwalwar ta ke yanke wa ta na dawowa daidai,can Kuma se ta bud'e bakin Balqis ta hau zuba mata abincin, ci take ta na hawaye tabbas wannan Ummahn ta ce ta dafa, zamewa ta yi daga Saman gadon ta kafa goshin ta a qasa, ta na kuka Mai sauti tana fad'in,
"Alhamdulillah ya Rab
Alhamdulillah Ya Rab
Alhamdulillah Ya Rab
Hamdan katheeran ya Rahman, ya Allah ka qara wa Annabi daraja da wasila fil jannati,Allah na gode maka da ka amsa min addu'a ta a lokacin da na fi tsananin buqatar hakan, na gode maka Allah da ka sake had'a ni da ahali na"
Ta na kuka ta na addu'a Balqis kuwa tuni ta ajiye plate itama ta na kukan wiwi, Ummah da aka gama kwantar wa da hankali aka tabbatar Mata Jiddah is intact ba abinda ya same ta ce ta shigo dan Jiyo kukan yaran nata da ta yi, a duqe ta tadda Jiddah ta na sujjada ta na kuka ta na hira da ubangiji ta, itan ma goshin ta ta kafa a qasa ta na gode wa Allah, kamar a tare suka dago, Jiddah Balqis ta miqa wa hannu dan bata kula da shigar Ummah d'akin ba, cikin muryar kuka ta ce,
"Bilkisu ciyar da ni da abincin da Ummah na ta dafa, dama Ummah na ce zata bani da hannun ta da na fi Jin dad'i, Bilkisu na yi kewar ku, na zaci ba zan sake ganin ku ba, na zaci nima zai kashe ni kamar yanda ya dinga kashe mutane a gaba na duk dan na amince na aure shi, duk dan na zama jaruma Mai zuciyar kisan mutane ko Mai tattaurar zuciya idan an yi kisa a gaba na kar na damu, be yarda matar da yake so ta zama raguwa ba, be yarda..."
Kuka ne ya sarke ta, ta na yi ta na tari, nan da nan Ummah ta rungume ta ta baya, tare da fashe wa da matsanancin kuka, ruwa Balqis ta deb'o ta Kai bakin Jiddah da ke tari da shaquwa a lokaci d'aya, kad'an ta karba ta kalli Ummah da ke hamdala ta na kuka ta ce,
"Ummah ki bani abinci na ci, Ummah Ina Jin yunwa, ba na ci bana Sha se ya daki Balira saboda tausayin ta se na ci kad'an, Ummah a wajen nake Kashi nake fitsari idan Jinin al'ada ta ya zo zan yi na gama ba tare da na yi wankan tsarki ba, Kuma dole na yi sallah idan ya d'auke,a haka nake taimama na yi sallah, Ummah na yi fatan na mutu Kar na rayu saboda na kasa jure azabar wajen nan....Ummah ji nake......"
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, Jiddah ! Jiddah ! Jiddah! Ke Jiddah ki bud'e idanun ki, kin tsira gaki a hannu na mahaifiyar ki, Jiddah ba abinda zai sake samun ki da yardar Allah se alkhairi, Jiddahhh, Balqis Kira min Abbahn ku da sauri"
Da gudu Balqis ta fita waje ba takalmi ba mayafi,a zaune ta ga Abbah a tabarma da major,idanun Abbah zuru zuru, ya na can Major ya tasa shi gaba da tambayar sunan wajen, da duk wani abu da ya sani, shi kuwa ya kafe ya nace ba zai gane wajen ba, in fact memory d'in shi ta fara goge wa da dikkan alamu asiri aka Masa baya gane komai, ganin Balqis cikin wannan tashin hankalin ne ya Sanya su miqe wa da gudu suna rige rigen tambayar ta me ke faruwa,cikin fidda numfashi ta ce,
"Abbah ! Yah Sudais Yah Jiddah ku yi sauri kar ta mutu Dan Allah,"
Ta qarasa maganar ta ta na rusa wani irin kuka, tunda ta Kira sunan Jiddah Major ya afka cikin gidan a guje,direct d'akin da ya ga an shige da ita ya nufa, kwance ya gan ta ta na wata jijjiga ta na qafewa Ummah na rungume da ita ta na kuka su Innah na taya ta, Mom ce kawai Mai qarfin halin deb'o ruwa ta hau zuba mata a jikin ta.
Hannu ya Sanya ya d'auki Jiddah a hannun sa kamar jinjira ya yi waje da ita,mota ya bud'e da key din hannun sa Sudais ya bud'e marfin motar ya Sanya ta ciki sannan ya zagaya ya shiga motar, be tsaya a ko ina ba se asibiti.
Su na isa nurse da ke da duty ta kalle su ta ce,
"Ni fa na gama duty na, sister d'in da zata Karb'e ni ta na hanya, likita Kuma ya yi tafiya birnin kebbi se da yamma zai dawo ana wani...."
"Shut the f**up stupid ! Ki Karbe ta ki mata duk wani abu da ya dace ta dawo hayyacin ta, ki yi saving wannan dogon bayanin naki bama son Jin,idan wani abu ya same ta se na d'aure dika dangin ki, ke kuwa yanzu zan harbe ki ba se anjima ba"
Tunda ya daka mata tsawa ta karb'i Jiddah a hannun sa, sauran bayanin a tafe ake zuba mata shi, jikin ta se rawa yake ta na da ta sanin abinda ta so aikatawa ba tare da ta San shi waye ba, waya ya yi wa babban yaron sa ya ce ya deb'o team d'in su su same shi a Kamba a yau ba se gobe ba komai dare su iso yau yau ASAP.
Duk wani abu da zata taimaka wa Jiddah da shi ta yi mata, numfashin Jiddah ya daidaita, sannan Major ya sa ta bashi No likitan, ta na ringing likita ya dauka Major ya ce masa,
"Na baka nan da awa uku ka iso asibitin da gwamnati ke biyan ka kud'i ka na can ka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 12