ya cika, wannan ya zo wannan ya tafi, a haka ne wasu bayin Allah suka zo suka yi sallama da Abbahn Jiddah, Abbahn Jiddah na fita ya Basu hannu suka gaisa, sannan suka samu waje suka tsaya kowa na kallon d'an uwan sa ana jiran Wanda zai fara magana, ganin sun yi shiru ne Abbah ya qura wa wani me kama da ustazai Ido a wajen, ajiyar zuciya Ustazun ya yi kafin ya ce,
"Wato ainihin mun zo ne wajen ka saboda mu samu mu yi maka bayani game da b'atan yarinyar ka, muna so mu sanar da Kai wani hasashe da mu ka zauna muka yi ni da abokai na, ka dai San ni malami ne a makarantar islamiyyar da ke layin nan, hakan ce ta bani damar sanin shige da ficen da yawa daga cikin mutanen unguwar nan, wato ainihin akwai wani bawan Allah da muka jima muna zargi a unguwar nan,bi ma'ana muna zargin shi da yin wata muguwar sana'a ta safarar mutane ko dai wani abu makamancin hakan, to a jiya muka tabbatar da hakan shi ne muka ga ya dace mu garzayo mu sanar da Kai ko zaka tsananta bincike har Allah ya sa ka dace,"
Cikin qosawa da dogon labarin Ustazun Abbah ya ce,
"Ta ya akai ku ka gane mutumin Dan safarar mutane ne? Sannan ya sunan shi? Ya kamannin sa yake?"
D'aya daga cikin mutanen ne ya gyara tsayuwar sa ya ce,
"Da farko dai gidan da bawan Allahn nan ya zauna da matan sa gida na ne, haya suka karba, dama tun da suka zo wannan yaron nawa ya ce shi fa be yarda da su ba Kar na basu haya, to sakamakon kud'in da ya bani suna da kauri se na ga be kamata na hana shi haya ba, Dan kuwa ba me bani wadannan kud'ad'e masu yawa a shekara,ba tare da na tsananta bincike ba na basu gida suka zauna, ga maqocin shi nan malam Rabe, ya ce gaskiya ya kan ji ihu da dare a gidan, to a zatan su ko dukan matan shi yake,se watarana da dare ya fito dan ya Masa nasiha a daren Kuma ya bashi hakuri, se ya ga mota baqa ta wuce baya hango cikin ta Amma gilmawar da za a yi ya ji kukan wata ta na fad'in su kyale ta ta koma gidan su,duk da haka be kawo komai ba sai ya dauka fad'a ne tsakanin mutumin da iyalan sa, bayan kwana biyu nan ma ya ga ana ta zuwa da motoci da tsakar dare ana shiga da Wasu abubuwa a manyan buhuna, gashi duk yanda ku ke da bawan Allahn nan baya bari a shiga masa gida, Maza ko Mata, saboda koda yaushe ya na nan, da ka je ka sallama zai ce shi baya son iyalan shi na hulda da kowa, ga Mai shago nan Shima zaka ji tashi shaidar"
Zufa dik ta gama jiqe Abbah, idan ya fahimta kidnapping 'yar shi aka yi kenan,
"Ni dai na San tsakanin Jiddah da bawan Allahn nan akwai wani abu, Ina nufin suna son junan su, saboda a gaban Ido na take tafiya makaranta da 'yan uwan ta, shi ma Kuma a gaban Ido na yake zama inda yake ganin su kullum in za su tafi makaranta, rannan anan suka gama maganganun su da Ido, har yake mata zanen zuciya da hannun shi, Jiddah ta ji kunya ta shiga gida da gudu,daga nan Kuma se soja ya zo suka tsaya suna hira a qofar gida, bawan Allahn nan Ina hango yanda ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda kishi,bayan soja ya tafi ya fito ya na hararar Jiddah wadda ta shige gida a cikin damuwa daga nan na ga ya fito qofar gidan ya na ta bige bigen waya ya na magana cikin fushi da bacin rai"
Kuka Abbah ya fashe da shi, sannan ya ce,
"Mai shago ka ci amanar zaman tare, ka ci amanar makwaftaka, Kai yanzu fisabillahi wannan abubuwan na faruwa Ina zuwa shagon nan, Sudais na zuwa ka kasa sanar da mu komai? Ka ci amanar zaman tare alqawari be ce haka ba, yanzu ni ta Ina zan kama neman Jiddah wadannan mutanen ko ta Ina zama suke, Ina na San inda zan kama neman ta yanzu?"
Shiru suka yi mutanen nan, mai shago kuwa se hakuri yake bayarwa,tare da fad'in,
"Malam ka yi min aikin gafara, ka San yanzu ba kowanne iyaye ke son a shiga lamarin yaran su ba, se yanzu a ce maka d'an baqin ciki ko dan sa Ido ko mahassadi da dai sauran ire iren sunayen nan,in shaa Allahu za a gan ta malam"
"Wai ni yanzu ba wannan ba ma, wa ya San sunan tsinannen? Ku bani sunan matsiyacin" In ji Abbah da ya fusata ya ki kallon fuskokin su, Dan gaba d'aya sun bashi haushi, ta ya ya saboda son abun duniya za ka bada haya a unguwa ga Wanda baka yi bincike ka San wanene shi ba? (Su Abbah ke Jin haushi Dan an bada haya ga wanda ba a bincika ba, Ina ce shima akan son kud'i har kauce hanya yake son yi?) Gefe daya kuma haushin Mai shago ya Hana shi sukuni,ace ya na Dan unguwa a gaban idon shi wani ya dinga nuna wa 'yar shi soyayya amma ya qi sanar da kowa, har da shi fa aka Sha alawar engagement din Jiddahn da yayanta,amma shine ya na ji ya na gani wani ya sace wa Yar sa zuciya kuma be magana ba a matsayin shi na dan unguwa.
Muhawara ya ji suna yi a game da sunan bawan Allahn nan asalin, wani ya ce sunan shi irin na Fulani ne saboda dama bafulatani ne, da kyar aka samu Wanda ya tuna sunan shi, nan take kuwa wani Dan tsamurmurin mutum a cikin su ya ce,
"Yauwaa malam sule na tuna sunan shi, sunan shi Muido, tabbas sunan kenan, Dan kuwa akwai watarana Ina zaune bayan layin gidan shi bawali ya kama ni na jingine zan yi bawali se na ji ya na waya ya na fad'in, 'Muido ke magana da wa nake magana?' to daga nan ban sake Jin me yake cewa ba saboda ya tashi ya shiga gida"
"Ah ah malam Usaini ba fa Muido sunan shi ba, ce mana ya yi sunan shi Shehu Usumanu"
"To duk yanda akai karya yake ba sunan ba kenan,"
Bayin Allahn nan na ta surutai Abbah ya zagaye su ya shige gida, kaya ya d'iba kala biyu, sannan ya nemi ko Ummah na da 'yan kud'in da zata iya bashi ya na so ya nausa neman Jiddah tinda hukuma ta gaza.
"Abbahn su idan ka tafi ka San inda za ka je ne? Sannan na ce a sanar da yaron nan Junior ka ki,baka ganin a matsayin sa na soja akwai gudummawar da zai bamu, ban San me yasa Kai da Yaya kuka hana a sanar da shi ba"
"Ba Zaki gane ba ne Ummahn su,yanzu a wannan zamanin da ake ciki duk budurwar da kidnappers suka d'auka idan ta dawo ganin bazawara ake Mata, Dan kuwa sun riga sun gama da ita, so ki ke ya sani ya guje ta?"
Cikin sauri Ummah ta ce,
"Sanin kan ku ne Junior ba haka yake ba, ba zai tab'a yi wa Jiddah haka ba, sannan ba na wa yarinya ta fatan wani dan Iska ya kusance ta, in shaa Allah yanda suka sace ta haka za ta dawo lafiya,sannan Abbahn su me zai hana ka sanar da 'yan sanda wannan abun da ka sani se su bincika"
"Da suna son binciken da sun zo sun tambayi 'yan unguwar har su samu wannan bayanan da kan su in ya so se su d'ora daga inda ya dace, kin ga Ina Bata lokaci bari na tafi"
Ummah ce ta miqe tsaye da sauri sannan ta ce,
"Abbahn su Ina zaka je? Ba fa ka San takamaimai inda zaka je ba"
"Allah zai nuna min waje bani hanya"
Haka ya fice ba dan Ummah ta so ba, tsaye ya ga mutanen nan suna ci gaba da tattauna wa, har zai wuce su se ya tsaya ya ce masu,
"Na gode da wannan information da kuka kawo min,ni yanzu zan tafi neman Jiddah se yanda Kuma Allah ya yi da ni"
"Malam yanzu Kai Ina ka nufa to?"
"Da Wai zamfara zani ko Katsina na bincika ko Allah zai sa a dace"
Mai shago ne ya ce,
"Ah ahhhh Ina ga fa wannan bawan Allah ba ta nan yake ba, Dan kuwa na ji ya na yawan maganar garin Niger state Ina kyautata tsammanin ta can yake"
"To bayin Allah salamu alaikum"
Kallon Abbah suka dinga yi suna tunanin Anya be zare ba? Idan ya tafi Niger wajen wa zashi ya ce ya zo neman 'Yar shi? Ta ya zai gano su? Anya batan yarinyar be tab'a kwakwalwar shi ba?
A qafa Abbah ya nausa hanya, tun suna hango shi bar suka dena hango shi, be tsaya ko Ina ba sai tashar birnin kebbi, wadda daga nan zai hau motar zuwa Niger state.
Balqis ce riqe da wayar Jiddah da ke ta ringin, tinda Jiddah ta tafi ake kiran wayar da wata lamba kamar ba ta Nigeria ba,amma a yanzu sunan da ta gani an rubuta ne ya Sanya jikin ta rawa kamar mazari, hannu ta sa dan amsa wayar zuciyar ta na rawa da tunani kala kala......
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 8:
Cikin murya mai kaushi tare da sakin hannun ta Muido ya ce wa Jiddah,
"Je ki zauna a can, gobe war haka kin zama mallaki na ke ma, gasu nan, waccan da ki ke gani ita ce uwar gida, sunan ta Fure, 'ya ce a wajen wani hamshaqin d'an kasuwa, wani informer na da ke cikin garin Kaduna ya sanar dani Mahaifin ta hamshaqin Mai kud'i ne in aka kama ta zai saki nera ga ta nan da kud'in uban ta muka Gina nan Kuma muka hana shi ita,wannan Kuma 'yar Mai garin nan Mariga ne,kyan ta da natsuwar ta ne suka ja ra'ayi na na sa liman ya aura min ita, Jiddah tunda nake ban tab'a son mace ba da sunan soyayya ba se dai ta burge ni, a kan ki na San menene so,na San ya ake ji idan ana Jin so irin na soyayya tsakanin mace da namiji, Jiddah bana qaunar safiya ta yi ban yi tozali da kyakkyawar fuskar ki ba,bana gajiya da kallon ki,a duk sanda nake kallon ki kyawun ki karuwa yake a ido na,tun daga ranar da na gane Ina son ki na ji ba zan iya barin ki ba tare da na aure ki ba,shine dalilin da ya sa na Sanya maki masu tsaron lafiyar ki ba tare da ke kin sani ba,duk Inda Zaki je akwai masu gane min duk abinda ki ke yi, da fari na so na sace ki saboda dangin mahaifiyar ki da Mahaifin ki suna da kud'i ko da ku baku da shi,akwai zumunci Mai qarfi a tsakanin ku ba za su tab'a barin ki ba sai sun biya kud'in fansa, Jiddah a yanzu na sauya ra'ayi na game da kab'ar kud'in fansa akan ki, auren ki shi ne fansar ki,Dan haka ki shirya gobe za a daura mana aure, sai dai ke ba kamar sauran Mata na ki ke ba, na yi maki alqawarin ba zan tab'a kusantar ki ba har sai kin aminta da ni da kan ki"
"Ai kuwa ranar da zan aminta da Kai ba zata tab'a zuwa ba har abada ni Jiddah da na aminta da dan ta'adda azalumi irin ka gwanda na mace ban yi aure ba, da ka duba ka ga dangin namu na da kud'i baka hango Ina da Wanda zan aura ba a cikin dangin?,ni Jiddah a yanzu a kaf duniyar nan bani da Wanda na tsana nake qi Sama da Kai,a baya na yi zaton Kai mutumin kirki ne, yanayin shigar ka da gemun ka ya yi kama da na mutanen kirki, na yi tunanin na sanar da iyaye na ba zan iya auren Yaya na ba da suka zab'a min saboda soyayyar mutumin da bai San Ina yi ba,ashe Kai din mayaudari ne , d'an ta'adda ne, azzalumi ne, me kashe mutane ne,ashe Kai ba alkhairi a tattare da Kai, to Ina neman tsarin Allah akan ka Ina roqon Allah da ya kare ni daga sharrin ka, ni Jiddah na tsane ka, na tsane ka, na tsane ka, ba na son ganin ka, ka taimaka min ka maida ni gidan iyaye na, Ummah na Bata da lafiya Kar wani abu ya same ta Dan Allah"
Cikin matsanancin kuka ta qarasa maganar ta tare da durqushewa a gaban shi ta kama kafar shi ta na masa magiya,Muido kuwa nan take duk had'uwar da suke yi ta fara gilma Masa a kwayar idon sa, murmushin ta da kunyar ta tare da tsananin kyan da Allah ya Mata sun yi masa, bayan iyayen sa da qannen shi be tab'a son wata halitta ba Sama da Jiddah, Dan haka Jin kalaman ta yake kamar saukar ruwan zafi a Saman fatar da ke cikin Sahara a tsananin zafin bazara,cikin matsanancin fushi ya fizge ta ya wurga ta tsakar gidan, ya bi ta da kafar shi ya take cinyar ta sannan ya durqusa a saitin fuskar ta, idanun shi da suka Sha kwalli suka rine suka yi jawur suke fidda wani ruwan masifa ya kafa Mata sannan ya nuna ta da yatsa kafin ya nuna kan shi, cikin baqin ciki da kunar rai ya ce Mata,
"Ni? Ni mace zata kalla ta ce wa bata so na Ido cikin Ido? Lallai Jiddah kin yi kuskure, Jiddah se kin yi danasanin wadannan kalaman naki, zan gana maki azabar da da kan ki Zaki kawo kan ki ki ce kin amince Zaki aure ni, zan gana maki azabar da Zaki manta da Wai iyayen ki sun zab'a maki Wanda Zaki aura, zan gana maki azabar da sai kin zo da kan ki kina rokon na aure ki Jiddah"
Cikin kuka da kafiya da taurin kan da bata tab'a sanin ta na da shi ba ta kalle shi hawaye na zuba idanun ta sun kad'a sun yi jawur ta ce,
"Har abada ba zaka ga wannan ranar ba, a yau na tsine wa ranar da na fara ganin ka a rayuwa ta, na yi Allah wadai da ranar da na fara Jin qaunar ka a rai na,Ina maka albishir nima ko da zaka dinga yankar naman jiki na ka na cin shi d'anye ne ba zan tab'a amince wa auren ka ba,Kuma shi Wanda ka ke cewa zan manta da shi ka San ko wanene? Zai iya zagaya duniyar nan domin nema na,Ina tausaya maka a duk sanda za ku yi Ido biyu da Yah Major, Ina tausaya wa rayuwar ka maqasqanciya a hannun Wanda zan aura"
Kalaman ta ba qara tunzura zuciyar Muido suka yi ba, wato akwai soja a gidan su Jiddah ya aka yi be sani ba? Lallai zai yi maganin informers d'in shi sun manta da abu Mai mahimmanci da ya kamata su sanar da shi,kallon ta ya yi ya na taune kumatun sa ta ciki ya ce,
"Haka ki ka ce Jiddah?"
"Haka na ce Muido, bana son ka bana son Mai son ka, bana qaunar Wanda yake qaunar ka Allah ya yi min maganin ka ya shiga tsakani na da Kai da...."
Wani gigitaccen Mari ya zuba wa kuncin ta sai da ta ga gilmawar wuta blue da green can Kuma ta ga wani duhu dundum kamar ta dena gani ga wat qara tsiiiii ta na ji a cikin kunne da kwanyar ta.
A hankali ganin ta ya fara dawo wa, bata tsinci kan ta a ko ina ba sai a wani d'aki Mai duhu qarami a matuqar quntace, ta yanda hatta da qafafun ta ba yanda za ai ta iya miqe su se dai ta zauna, idan ta miqe tsaye ma kan ta na tabo Saman ginin, dakin ba window qofar Mai kauri ce, se wani Dan qaramin window ta can Saman qofar, qofar dai ta fi kama da a kira ta da marfin wani window'n.
Kuka Mai tsanani Jiddah ta fashe da shi, ta rasa inda zata saka kan ta ta ji dad'i,a wanne hali iyayen ta suke? Ya Ummanta take ji game da b'atan nata? Shin ciwon ta ya tashi? Ta Sha magani? Abbah na nan dan supporting din Ummah a wannan yanayin ko ya na can inda su kan su ba su San Ina yake zuwa ba?
Tunawa ta yi da bata yi sallah ba, rabon ta da sallah tun isha'in da ta yi jiya kafin Muido ya sace ta,dan haka zama ta yi ta tankwashe qafar ta ta kabbara sallah, duk sujjadar da ta yi se ta koka wa Allah akan halin da take ciki.
Jiddah bata daina sallah ba har sai da ta rama kaff salolin da ke kan ta har ta qara da nafila, dan a ganin ta ba ta da abinda za ta yi da ya wuce sallar da roqon Allah ya fitar da ita daga wannan qangin.
Muido kuwa ranar ya Sha giya kalar shawuwar da be tab'a irin ta ba, duk abinda ya shiga gaban shi ciki yake da shi, gaba d'aya gidan kowa ya shiga taitayin sa, daidai da masu walimar dawowar shi ba Wanda ya sake zuwa yankar naman rago balle ya sa a bakin shi, Muido na zaune ya kira D'an Gumel, a kunne ya rad'a Masa magana shi kuwa ya gyad'a Kai cikin girmamawa ya gyara zaman bindigar shi ya nufi d'akin da aka ajiye Jiddah, ya na zuwa ya tadda ita ta na sallah,se ya koma ya sanar da Muido, murmushi ya yi sannan ya ce,
"Jeka"
D'an Gumel tafiya ya yi bakin kofar gidan inda sauran mutanen Muido suke, ga magana a bakin kowa ba damar a furta ta dan haka kowa tsaye yake ya na jiran abinda zai je ya zo.
Muido kuwa na nan zaune yanda ya ga rana haka ya ga dare, cikin ran shi ya ke ayyana,
'shin Wai menene so? Ina so yake ne na dakko shi na yayyanka shi gutsi gutsi na kunna wuta na zuba Masa fetur na qone shi? Me yasa so ya rasa zuciyar da zai kama sai irin zuciya ta? Bana son na samu rauni a rayuwa ta, ba na so na zama Mai rauni,soyayya rauni ne, soyayya wahala ce, bana son soyayya '
Tun Yana fad'a a ran shi se ga kalmar
"Ba na son soyayya "
Ta na fita a bakin Muido, gaba d'aya ya birkice ya fita a hayyacin sa kamar wani majinyaci.
Jan jikin Sa ya yi har zuwa qofar d'akin da aka kulle Jiddah ya kwanta a qasa warwas ya na surutai,gabb da Kiran sallahr asuba bacci ya d'auke shi.
Jiddah na Jin sanda ya kwanta ya na surutai, banda kuka ba abinda take yi, tabbas soyayya bata yi Mata adalci ba, da ta San wanene Muido da bata bari ta kamu da son shi ba, duk da tsana da qiyayyar shi da take ji a ran ta, wani bangaren na ranta ya na son shi, ya na son ganin kyakkyawar fuskar shi, shin Ina so yake ne? ashe mummunar fahimta ta yi wa Muido ba mutumin kirki bane ? ashe da ta nutsu ta tsaya ta masa KYAKKYAWAR FAHIMTA da Bata kamu da soyayyar Wanda bai dace da rayuwar ta ba?
Jiddah taimama ta yi da qasar wajen sannan ta tayi sallar ta ta asuba,ta na nan jingine da gini ta hau rera karatun qur'ani,bacci Sam ya qi kama ta,duk yanda ta so ta rintsa ko zata farka ta gan ta a gidan su, a Saman tsohuwar katifar ta da samun tabbacin mummunan mafarki ta yi abun ya gagara, muryar ta ce ta tada Muido daga baccin da ya fara, shiru ya yi daga kwancen ya na sauraron ta kafin daga baya ya tashi ya shige d'akin shi ya kwanta.
Fure da ke Jin tsananin kishin Jiddah ce ta yi tsaki ta bar masa sashen nata da aka kewaye da labule ta bar d'akin gaba d'aya.
Balira kuwa tagumi ta zabga ta na matuqar tausaya wa Jiddah,dan kuwa ta shiga gidan su sau biyu siyan abinci da umarnin Muido duk dan ta Kai Masa rahoton rayuwar Jiddah, ta San gidan su Jiddah ba Wasu hamshaqan masu kud'i bane, amma tabbas akwai kwanciyar hankali da soyayyar juna a tsakanin ahalin,yanzu ya Ummahn ta zata ji? A wanne hali take?
Ajiyar zuciya ta sauke Mai qarfi sannan ta miqe, mata ne guda biyu ke girki a gidan, Kuma Mata ne ga 'yan ta'addan da ke a qarqashin Muido ,su na can sun yi nisa a hidimar girka abincin safe Dan mutanen gidan, Balira ta leqa inda suke girkin ta yi umarnin idan an gama a zuba wa Jiddah abinci a bata za ta Kai Mata da kan ta.
Kallon juna suka yi cikin sauri, da alamar tsoro a fuskokin su,itan ma kallon su ta yi da tuhumar me yasa suke kallon ta haka.
"Gorko Muido ya ce Kar a sake a ba wa baqin da ya kawo jiya abinci yau se ya bada izini da kan shi"
"Dama ban ce baqin da ya kawo za ku ba wa ba, Jiddah na ce ku zuba wa ita ta musamman ce a wajen shi, ko Kuna so wani abu ya same ta saboda kun yi girki a gidan nan kun hana ta?"
Gaba d'aya matan biyu rud'e wa suka yi, ya za su yi? Umarnin Mai gida Muido za su bi ko Kuma umarnin matar Mai gidan nasu Wanda yake tattare da qamshin gaskiya a ciki?.......
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 10:
D'aga Jiddah Muido ya yi tsaye ya na so su had'a Ido, amma ta kasa tsayawa da kyau tsabar kukan da take yi, jikin ta se rawa ya ke zufa na karyo Mata, ganin halin da ta shiga saboda kawai an ce za a sake harbin tsohuwar nan ya b'ata ran Muido, idan ta zama matar shi haka za ta dinga wannan rashin jarumtar? Su Fure duk ba haka suke ba, jaruman Mata ne su, Basu tab'a kisa ba ko ji wa wani rauni, amma dukkanin su ba wadda take Jin irin wannan tsoron da jiddah ke ji,hasali ma Fure kan taimaka Masa da fassara Masa turanci idan sun kama qabilun da ba su iya Hausa ba se turanci,cikin fushi ya zaro bindigar shi ya saita tsohuwar nan ya sakar Mata harbi a kan ta, nan take ta baje ko shura wa bata sake yi ba, cikin tsananin bacin rai ya fizgi hannun Jiddah da tai mutuwar tsaye bakin ta bud'e Ido kamar zai fad'o qasa ta na so ta gasgata abinda ya faru a kan idanun ta, Yana gama juyar da ita idanun ta suka sauka a kan baiwar Allah'n nan kwance shame shame cikin jini, wata iriyar qara Jiddah ta saki ta fad'i a wajen a sume, ashar Muido ya saki ya hau masifa ya na zage zagen hali irin na Jiddah, D'an Gumel ne ya tsaya a gaban sa, cikin nuna alamar girmamawa ya ce,
"Gorko Muido ka yi hakuri, ka bata lokaci watarana ba zata yi hakan ba, da ta Saba ganin irin wadannan abubuwan shikenan za su zame Mata jiki"
Sauke ajiyar zuciya Muido ya yi tare da tsirtar da yawu sannan ya kira Sadi, da gudu ya Isa gaban Muido ya tsaya hannun shi riqe da bindiga,
"D'auke ta a machine a maida ta gida,"
Sadi ne ya tsaya ya na tunanin tab'a Jiddah Kar ya yi laifi, murmushin mugunta Muido'n ya sake sannan ya ce,
"Lallai Sadi kana son rayuwar nan taka da yawa, wataqila Kuma Allah na so mu zauna da Kai ne rayuwa mai tsaho a tare,"
Sosa qeya Sadi ya yi, ya na murmushi, Muido ne ya d'auki Jiddah da kan shi ya d'ora ta a machine ya hau Shima ya wuce gida da ita, ya na zuwa ya kwala wa Fure Kira, ko da ta zo ta ga Jiddah kwance a hannun Muido se ta buga tsaki zata koma ciki, wata iriyar tsawa ya buga mata,se ta dawo da baya ta na qunquni,
"Ki Kama ta ki Kai ta d'akin ta, a bata ruwa da abinci idan ta farka,"
"Toh"
Shine abinda ta ce ta kama Jiddah ta na janta kamar ba mutum ta kama ba, wani gigitaccen Mari Muido ya sauke Mata me lafiya a kuncin ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 12