a Kai jami'an tsaro gidan ku daga nan har sanda za a gan shi a kama shi, Kuma a duk sanda aka gan shi doka ta bada damar a harbe shi da shi da yaran nashi on sight"
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un"
Jiddah na fad'in haka ta saki wayar ta ta fad'a gado ta rushe da kuka,shin murna za ta yi masoyin ta ya kub'uta ko baqin ciki za ta yi ya zama free ba tare da an d'auki fansar kisan gillar da ya yi wa bayin Allah ba? Shin ko dai tsoro ya kamata ta ji ne tunda bata San da wacce ya dawo ba? Kamar fad'uwar aradu haka Sudanis ya afka d'akin,da sauri ya kama Jiddahn ya na jijjigawa, banda kuka ba abinda take yi, cikin tsananin tausayin ta ya ce,
"Yanzu Yah Major ya kira ni ya ce na duba masa ke, Jiddah ki kwantar da hankalin ki, da yardar Allah ba abinda zai same ki,muna nan tare da ke ba Wanda ya Isa ya sake d'auke ki, Allah ba zai ba su iko ba kin ji qanwa ta?"
Ba tare da ta tsaya da kukan nata ba ta daga masa Kai kawai, ta miqe ta shiga band'aki ta d'auro alwala, ta na buqatar Allah a lamarin ta, she is not Okay,her feelings is not normal, she is not supposed to feel this so much affection towards Muido,he is evil,he is a monster, makashi ne shi, mugu ne azzalumi ne, me yasa take son shi haka? Soyayyar ta yi yawa, ba ta son Jin haka a tattare da shi, dole ne ta roqi Allah sassauci.
Ganin zata tada sallah ne ya Sanya Sudais fita daga d'akin,ya na fita Major na Kiran shi, nan dai ya kwashe duk abinda ke faruwa ya sanar da shi, ajiyar zuciya Major ya yi sannan ya ce,
"Ka fad'a min me ya sa ba zan so yarinyar nan ba Sudais?"
Murmushi Sudais ya yi ya ce,
"Babu, muma Allah ya bamu ya taku"
"Ameeen qani na"
Hira suka d'an tab'a kafin Major ya ce,
"Ni fa Ina ganin ku tattara ku koma gidan mu da zama kamar shi ne zai fi tsaro, ko da jami'an tsaron sun zo hankali na ba zai kwanta ba, Jiddah na buqatar uwa a tattare da ita, nisan Jiddah da Mom ba zai samar mata kwanciyar hankalin da take da buqata ba ko me ka ce?"
"Wannan ma shawara ce, amma ka San kafiyar yarinyar nan, zan gwada yi mata magana zuwa gobe"
"To Allah ya Kai mu"
"Ameeen"
Suna gama magana ya tuna da ya Kai wankin machine d'in sa da Major ya cika masa kud'i ya siya, dan haka cikin hanzari ya leqa d'akin su ya ce,
"Ihsaan ka kula da gidan bari na je na karb'i machine d'ina na dawo"
Ba tare da ya ji an amsa shi ba ya yi gaba abun shi, Balqis na zaune ta na qunshe dariya ya wuce ta, ya na fad'in,
"Idan ya fito kun ta yin fad'an kaji, ahhh kaji tunda ba ku gajiya, ko meye abin dariya dan an ce ya kula da gida oho wàto kin raina shi ko? Ko kin qi ko kin so namiji yake dole shi zai kula da ke dik da kin girme shi ah toh"
Ya na gama fad'in haka ya bar gidan,ita Kuma ta ce,
"Yayan nan se a hankali ne watarana, be tabbatar da Ihsaan na gidan ba ko baya nan yake wannan surutun, Ihsaan ya jima da guduwa ball dan haka ka ba wa Balqis kula da gida har shi kan shi Ihsaan d'in dan in ya dawo se na ci qaniyar shi a gidan nan tsallan kwad'o zan saka shi na ce Yah Sudais ne ya ce ya yi kafin ya dawo"
Dariya ta fashe da ita ta wuce d'aki ta ajiye wayar ta a gefen gado, dan yanzu a d'akin Ummah suke kwana tunda Abbah ya yi fijo ya b'ace, ta na shiga band'aki wayar ta ta yi qara alamar saqo ya shiga, kamar Jiddah ba za ta tab'a ba, kawai se ta samu kan ta da son duba Wanda ya tura wa Balqis saqo, hannu ta Sanya ta ja wayar tare da kunna ta, No ta gani da ba a yi saving ba, cikin son ganin me saqon ya qunsa ta danna saqon ta fara karanta wa, nan da nan kuwa ta miqe cike da wani irin yanayi a tattare da ita hannun ta na rawa ta fita daga d'akin da gudu ta yi waje qafar ta babu ko takalmi daga ita sai hijabin Ummah na sallah da carbi a hannun ta, ta na fita qofar gida ta gan su riqe da mugayen makamai,idanun ta ne suka sauka akan wata bindiga qirar AK-47s ja da baya ta fara yi Suma su na bin ta cikin gidan ba su tsaya ba har sai da matashin da ke biye da ita ya manna ta da jikin gini, idanun su ne suka sarqe da na junan su, tsananin tsoro da fargaba, tare da kewar kwayar idon shi ce ta taru waje d'aya ta haifar mata da mummunar fad'uwar gaba,cikin wata iriyar murya ya furta,
"Sannu men be lorugu fottugo gido am" (sannun mu da sake haduwa masoyiya)........
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 19:
A qofar gidan su Jiddah ambulance d'in ta tsaya, mutanen da ke tsaye a wajen unguwar ana ta da hada-hada tare da hira sai ganin mota suka yi ta tsaya, da damar mutan unguwar dama sun San da cewar Ummahn su Jiddah bata da lafiya ta na asibiti, kusan kowa tsaya wa ya yi ya ga me zai faru,basu bud'e kofar ba kamar yanda Major ya roqa har sai da motar shi ta iso d'auke da Abbah da Sudais motar Dad na take masa baya.
Qarasowar su ke da wuya aka bud'e ambulance, kafin a fito da ita a shiga da ita Major da Dad sun shiga gidan, a zaune suka tarar da yaran Ihsaan da Balqis na cin abinci , Jiddah na zaune Ido kulle ta na motsa bakin ta da dikkan alama tasbihi take ga Allah, sallama su Dad suka yi masu, cikin sauri yaran suka tashi gaba d'ayan su har Jiddah da ke Jin kan ta kamar ba daidai ba, kwalla ce ke qoqarin saukar wa Major muhammad tsabar tausayin yaran da ya ji ya na tsarga Masa, ganin ya kasa magana ne ya Sanya Dad d'in shi yin gyaran murya ya ce,
"To....ammm...Kuna ji ba, ku yi hakuri,kun San rayuwar nan da ni da ku kowa lokacin sa yake jira ko? Kuma duk Wanda ya mutu ya na mai son gamuwa da Allah Allah na farin ciki da maraba da shi ko? To Ina so ku sa a ran ku Ummahn ku ta...."
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, shikenan Ummahn mu ta rasu, hasbunallahu wa ni'imal wakeel, ya Allah ka jiqan ta ka yi mata rahama ka sa aljannah ce makomar ta da dikkan musulmi"
In ji cewar Jiddah da jikin ta ya ke wata iriyar rawa had'e da karkarwa, a daidai wannan lokacin aka shigo da gawar Ummah d'auke a zanin gadon asibitin fari,Abbah na biye ya na ta barza kuka,duk yanda Sudais yake bashi hakuri Sam ya qi ji,Balqis da Ihsaan kuwa da gudu suka tsallake abincin suka yi kan gawar Ummah, cikin kuka suka durqusa su na qoqarin bud'e fuskar ta, su na yin Ido biyu da fuskar ta suka sake rushe wa da kuka, Jiddah kuwa har a wannan lokacin ta rasa a Ina take, kan ta sai juya mata yake yi ta na Jin Jiri na kwasar ta, fad'uwa ta tafi zata yi major ya riqe ta da hannu d'aya sannan ya rungume ta tsamm a jikin shi, ta na Jin an rungume ta sai ta saki wani siririn kuka mai matuqar cin rai,shi kan shi se da hawaye masu zafi suka zubar masa ya tabbata zai qare rayuwar shi ne ya na kewar Goggon shi Mai qaunar shi,ga Kuma tausayin Jiddahn shi da ke ragargazar zuciyar shi,ana haka kafin minti talatin ya cika yayun Ummah da qannen ta tare da matan yayun ta na kusa duk sun hallara, se Wasu daga cikin dangi da yaran su, maqota ma ba a magana har da maqotan ta na tsohon gidan su, dama ba wani nisa ne sosai a tsakanin su ba.
Babu b'ata lokaci aka yi mata wanka aka gyara ta, Jiddah kuwa tunda ta samu hankalin ta ya dawo jikin ta ta nemi a Kai ta ta yi alwala, ta na yin alwala se ta samu waje a can quryar d'akin Ummahn ta kafa nafila ta na roqa wa Ummahn ta rahamar Allah da gafarar shi,tun ta na iya yi a tsaye har ya Kai bata iya tashi se ta koma yin sallar a zaune, har aka Kai Ummahn bata sake ganin ta ba, a cewar ta, yi wa Ummahn addu'a shi ne ya fi mahimmanci,ta ba wa kowa mamaki yanda ta yi saurin karb'ar qaddara, ko Balqis da ta ki shiru ta na ta kuka Jiddahn ce ta kira ta daki ta yi ta mata nasiha kafin daga baya ta yi hakuri ta rage kukan nata, a nan d'akin itama ta samu waje ta kwanta ta na tsiyayar da hawaye, cikin ran ta Kuma ta na wa Ummah addu'a.
Haka akai ta karb'ar ta'aziyyah daga wajen mutane kala kala, saboda Ummahn Mai jama'a ce musamman da yake ta na sana'ar abinci daga unguwanni kala kala zuwa ake manya da qananan mutane duk an sassanta.
Duk tsayin kwanakin nan Jiddah ta qi sakin jiki ta ci abinci se dai ruwan shayi ko koko/kunu su kad'ai take iya Sha har akai kwana tara da rasuwar Ummah, Aunty Sakee ta yi iya yin ta ta Sanya Jiddah ta ci abinci amma ta kasa Dan haka cikin b'acin rai ta ce
"Tunda ni kin raina ni bari na kira maki Yayan naku wataqila idan ya sa ki ci dole kin ci, kin gan ki kuwa Jiddah? Kin ga yanda ki ka koma? Anya Jiddah babu abinda yake damun ki bayan damuwar rashin Ummah? Jiddah ki fito ki yi magana idan baki fad'a ba ba Wanda ya sani, dan Allah save your self, say something anything voice out what is troubling your heart, idan baki fad'a ba ba yanda za mu yi mu taimaka maki"
Aunty Sakee na Jin Jiddah a ran ta kamar qanwar da bata da ita, se take Jin son Jiddah a ran ta kamar yanda Adda Sophy ke nuna Mata soyayya a lokacin da take raye bata d'auki Jiddah a matsayin kishiya ko wadda zata aure Mata miji ba, she is willing to share her husband with Jiddah da zuciya d'aya,cikin zubar da hawayen tausayin Jiddah ta d'auki wayar ta zata Kira Major se suka ji muryar shi ya na gaisa wa da mutane a parlour,ta tabbata daga nan wajen su zai leqo dan haka se ta mai da wayar ta aljihun rigar atampar ta ta na kallon yanda Jiddah ke wani irin kuka mai matuqar ban tausayi.
"Assalamualaikum in shigo?"
Major da ke tsaye a bakin qofar riqe da labulen d'akin ya nemi izini, cikin shaqaqqiyar muryar Aunty Sakee ta ce,
"Wa'alaikumussalam, Bismillah shigo, dama neman ka nake"
Ya na shiga idanun sa suka sauka akan Jiddah da ta sake qanjame wa ta rame ainun,ga Kuma kuka Mai matuqar tab'a zuciya ta na yi,da sauri ya Isa gaban ta ya durqusa,nan take kuwa shaid'an ya mintsini zuciyar Aunty Sakee, wani irin ciwo ta ji a ran ta ganin yanda gwarzon mijin ta yake a durqushe gaban Yar mitsitsiyar yarinya jikin Sa har wani rawa yake kamar an buga gujen yaqi,cikin sauri ta Kau da kan ta ta hau korar shaid'an,cikin ran ta take fad'in,
'A'udhubillahi minasshaidhanirrajeem'
Ta fad'i haka ya fi sau biyar kafin ta ji sunan ta da qarfi a bakin major ya na fad'in,
"Sakeenatu !! Ki na ji na kuwa? I said what is wrong with her? Yau ma bata ci abincin bane?"
Cikin in Ina ta ce,
"So..sooryy ban ji ba...ban ji ka bane...bata ci abincin ba, shi yasa ma zan kira ka se na ji muryar ka a parlour"
"Ya salam Jiddah please eat something,ko kad'an ne, taso tashi zaune maza tashi ki ci abinci zama da yunwa zai maki illa"
Ganin yanda shaid'an ya dage sai ya Sanya wa Sakeenatu wani mugun tunani da Jin zafin abinda ke faruwa sai ta yi dabara ta ce,"
"Yauwa tunda ka shigo bari na je na ba wa Yara abinci, Ina ga basu karya ba Suma"
"Ok ki je d'in ba komai, I will take care of her, thank you for everything love,Allah ya maki albarka, I love you wifey"
Wannan kalaman nashi sun sauke mata kaso mai tsoka na kishin da ya taso mata a rai,se ta koma Jin kunyar kan ta da Kuma zargin tabbas idan bata dage da addu'a ba shaid'an zai yi nasara akan ta watarana.
Ta na fita kuwa Major ya ja Jiddah jikin shi ya Debi abinci kad'an a plate ya zuba har da nama, ya had'a mata tea da kyau, ya zauna daf da ita ya d'ebi abincin kad'an a spoon, cikin bada umarni ya ce Mata,
"Haaaa,Maza bud'e baki ki ci"
Idanun ta na zubar da hawaye ta bud'e bakin ta ta karba, bakin ta kuwa se rawa yake, a haka major ya dinga bata abincin ta na ci har se da ta qoshi sannan ya ajiye ya bata tea din da take ta kwalaficin ya bata a bar abincin, ta na Sha kuwa wata gyatsa ta danno Kai, murmushi suka yi a tare ta sunne Kai a hijabi, cikin salo da sigar tsokana ya maimaita irin gyatsar da ta yi,sannan ya yi amfani da salon muryar ta ya ce
"Kaiii Yah Majorna na gode da zan cuci Kai naaaa"
Murmushi ta sake yi mai sauti sannan ta kauda Kai gefe ta ce,
"Na gode"
"Your welcome, uhumm dama abinda ya shigo da ni Ina so na sanar da ku gobe ni zan koma Abuja idan Sakeenatu ta shirya tafiya se mu wuce idan ta na so ta qara kwanaki zan bar maki ita anan, Ina so wannan shiga kotun da za a yi akan azzaluman 'yan ta'addan nan a yi shi da ni,har na ma yi booking flight idan Allah ya Kai mu gobe zan wuce,in za su bi ni Kuma se Suma na musu yau d'in gobe mu wuce tare"
Gaba d'aya jikin Jiddah ya mutu, shin wanne hukunci za a yanke wa Muido ? ba tare da ta San ta ma tambaya ba ta ce,
"Yanzu Yah Major kana ganin wanne irin hukunci za a yanke musu?"
"Ai Jiddah idan da ta ni ne da a dajin da muka gan su zan kashe shi shi da yaran sa, saboda basu da amfani a al'umma,amma yanzu na San duk idan aka gama se dai a ce a kashe su ta hanyar harbi ko rataya, na ga ma shari'ar ta d'auki lokaci se abu d'aya ake yi wata da watanni akwai Wasu tsirarun mutane da ke amfana da wannan rikicin da suke yi mana a qasa, ba a son a yanke masu hukunci Kuma da yardar Allah se an kashe su kowa ya huta"
"Yah Major kowacce halittar Allah mai amfani ce a doron kasa, me zai hana a yi qoqarin sa wa su shiryu su dena abinda suke yi idan yaso a basu sana'a a yi musu aure?"
Cikin gatse major ya ce,
"A basu sana'a a yi musu aure in sun shiryu? Ke Zaki auri irin su?"
"Me zai hana idan har za su shiryu d'in?"
Kallon kallo major da Jiddah suka hau yi wa Juna, shi ya na so ya hango iya gaskiyar ta a maganar ta, ita ma ta na so ta bashi damar hango gaskiyar tata a maganar tata, suna haka Balqis ta shiga riqe da cup d'in kunun gyad'a, sallama ta yi da qarfi ta ajiye cup d'in, sannan ta ce,
"Gashi in ji Aunty Sakee"
Zata fita Major ya ce Mata,
"Kira min Auntyn naku,"
Da sauri ta fita ta kira masa ita, ta na zuwa ya maimaita mata abinda ya sanar da Jiddah, nan take ta ce masa za su bi shi,saboda maganar gaskiya ta gaji da zama cikin mutane da yawa wannan ya shiga wannan ya fita, ga dangin su Major akwai yawa.
Su na nan zaune ya musu booking flight Suma suka ci gaba da magana da Sakeenatu amma hankalin sa na kan Jiddah da ta sakar masa magana tai shiru abun ta, Jiddah kuwa ta juya masu baya ta na share hawayen da ke zubar mata,Jin zuciyar ta take wani irin empty ba komai a cikin ta banda kad'aici, ga dai 'yan uwan ta ta ko wanne angle amma rashin Ummahn ta ya sa ta na Jin zuciyar ta kamar kango, gefe d'aya tunanin what if aka kashe Muido fa? Shikenan ita kuma haka zata qarasa rayuwar ta ta na dakon soyayyar d'an ta'adda?
Hadari ne ya taso, nan Aunty Sakee ta wa Jiddah sallama Abdunnasir zai zo ya maida su gidan Mom su fara shiri, hadarin nan ya jima ya na taso wa Sannan ya na bajewa ba tare da an yi ruwa ba, Wasu garuruwan ana ta musu ruwa amma kamar kowacce shekara Kebbi su ne karshe.
Washegari kuwa Major ya zo ya yi wa su Jiddah sallama tare da kyautar kud'i sannan ya yi masu alqawarin zai dinga dawowa akai akai ya na ganin su, godiya suka Masa shi da aunty Sakee suka wuce sokoto jirgin su zai tashi Sha biyu na rana.
Jiddah kuwa bayan tafiyar su se ta ji dama ace sun mata tayin bin su da ba abinda zai hana ta bi su, ko ba komai idan za a je kotun ta bi shi ta ga Muido, haka nan take Jin ta na son ta sake Sanya idon ta cikin kwayar idanun sa me sanye da kwalli, idanun da ke d'auke da dogayen lashes da gira cikakkiya baqa qirin.
Da sauri ta kauda tunanin Muido a ran ta, ta hango irin baqar wahalar da ta ci a hannun su, da yanda yake kashe mutane ba alamar nadama, hango d'akin da ya ajiye ta a matsayin fursuna ta yi, nan da nan jikin ta ya fara rawa,kuka ta fashe da shi, tare da fad'in,
"Kaico na ni Jiddah wannan wace iriyar rayuwa nake ciki? Allah ka fitar da ni ka yi min zab'in alkhairi ka sauqaqa wa zuciya ta nauyin da ke cikin ta"
*************************
Rayuwa babu Ummah a gidan rayuwa ce makauniya wadda babu haske a cikin ta, rayuwa ce mai cike da qunci da rad'ad'i tare da kad'aici amma a haka su Jiddah suke ta turawa,sun so su dena yin sana'ar Ummah ta danwake se Kuma Jiddah ta ga a kullum mutane na zuwa nema, dan haka se take taya Balqis suke ci gaba da yi, idan aka dasa mata kujera ta na daga zaune take komai, har yanzu bata qaunar cin abinci, se dai ta na yawan Shan kunu da shayi,sune suka taimaka mata ta d'an farfad'o,ramar nan da ta yi da har in ka na kallon ta zaka zaci ba mutum bace, yanzu babu ita, se dai bata dawo normal yanda take ba tun asali.
Tunda major ya tafi ya na masu aike akai akai, sannan ya riqe wuta saboda yanda ya kula ana neman murd'e shari'ar mutanen da ga shaida ga komai sun tabbatar da su y'an ta'adda ne, amma saboda komai a Nigeria se an masa munafurci ana neman a bar su su tafi free, ba tare da hukunci ba,idan Kuma ya samu lokaci haka zai Kira ta a sabuwar wayar da ya sa Sudais ya siyo mata mai kyau da tsada su yi ta hira, Wanda hirar tasu ta fi shafar case d'in su Muido, a duk sanda ya dakko mata zancen soyayya se dai kawai ta yi murmushi ta ce masa.
'Allah ya zab'a mana abinda ya fi zama alkhairi Yah Major'
Shi kuwa yakan amsa mata da,
'In shaa Allahu mu alkhairi junan mu ne Jiddah, mu yi qoqari mu cika wa Ummah burin ta, a gaba na take barin wasiyyar Abbah ya tabbatar auren Jiddah da Junior ya d'auru,'
Idan ya fad'i haka bata iya sake fad'ar komai, da gaske har ran ta ta bar wa Allah komai, idan Major ne mijin ta tana fatan Allah ya basu zaman lafiya, idan Kuma ita d'in rabon Muido ce ta na fatan Allah ya shirya shi ya aure ta su zauna lafiya.
Wataranar juma'a da safe su Jiddah sun tashi daga bacci, suka ji shiru Abbah bai fito sallah ba, se suka yi zaton ko har ya wuce masallaci, se kawai suka tafi gabatar da tasu sallar, abu kamar wasa yau ne za su ga Abbah gobe ne za su ga Abbah shiru, Abbah ya tasamma sati guda ba labarin sa ba bayanin sa, gaba d'aya hankalin yaran ya tashi, se suka bazama gidan Mom dan su sanar da ita abinda yake faruwa, da za a tafi se da aka Sha fama da Jiddah dan ta zauna a gida tunda an hana ta fita tun da abun kidnapping d'in ta ya faru, amma firrr ta qi yarda se da suka tafi da ita.
Labari fa ya baza gari ana neman Abbahn Jiddah, an duba ko wace kwana da lungu da saqon garin Kamba ba a ga Abbah ba, ba a ga Wanda ya ji labarin ya ga Wanda ya ga Abbah ba, Jama'a Ina Abbah ya tafi???????
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 12