Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 12
shaqaqqiyar muryar da ta Sha kuka ko na ce take kan yin kuka ta amsa da, "To Ummah se kin dawo" Sudais ne ya d'an had'e gira ya ce, "Me akai mata? Na ji kamar kuka take ko?" "Hahhaaa eh mana, kukan soyayya ne Yayan ku ya koma Abuja d'azu" Murmushi ya yi Shima sannan suka sa Kai suka bar gidan, haka Jiddah ta wuni ranar ba walwala a tattare da ita, dan ko da Balqis ta dawo ma ta na ji ana mata fad'an daukar wayar da tai qala bata ce mata ba saboda bata da kuzari, a wanne hali mystery man yake? Shin ya tsane ta kenan saboda ya gan ta da wani? 'Yah Major d'in ne wani? Yaushe ki ka koma haka ne Jiddah? Akan Wanda baki sani ba ki ke neman saka kan ki a masifa, so ki ke ki yi disappointing iyayen ki? Sun riga sun maki miji tun kan ki San kan ki, me yasa Zaki yi qoqarin tura wani a rayuwar ki?' Da sauri ta tashi zaune ta amsa Kiran da Ummah ke yi mata a tsakar gida. "Jiddah baki Jin iskar da ake yi ne ku zo ku taya ni kwashe kayayyakin nan a shigar ciki, hadarin da gaske ya taso ba da Wasa ba" Suna tsaka da kwashe kayayyakin su ne aka fara yayyafi, a daidai lokacin da Abbahn su ya dawo dan kuwa sun jiyo karar motar shi da ba me hawa a cikin su, daga shi sai shi. Bude masa qofa Sudais ya yi sannan ya kwashe shimfid'ar shi shima ya Kai d'akin su Jiddah, dan dama idan ana ruwa dika waje d'aya suke had'e wa a kwana, irin wannan rayuwar ce ta Sanya Ummah dagewa da sana'a kala kala dan ta sai masu gida su huta da yawon haya,tun da ta kula Abbah ba mijin da za a had'u a rufa wa Kai asiri bane, gashi Allah na gab da cika mata burin ta, dan kuwa har ta sai gidan a d'azu da suka fita,an ba da kud'in an basu takardu da makullin gidan, jira take Abbahn ya dawo ta sanar da shi sannan su saka ranar komawa. Balqis ce ta ce, "Gashi se Iska ake da ruwan sama amma ba a d'auke wuta ba," "Iyyy alhamdulillah, mu je dakin su Ummah mu yi kallo" "Na kwana biyu ban kallo ba hankali kwance dama, da za ai kallo Yah Jiddah zata ce, Ihsaan jarabawar faaaaa" Ihsan ya qarasa maganar shi ya na kwaikwayon Jiddah, dariya suka yi, Jiddah kuwa banda yaqe ba abinda take yi, dan haka se kawai ta bi su kamar raqumi da akala. Su na shiga d'akin ruwan Saman na kecewa, nan take suka nemi waje suka zauna suna kallon Sunnah TV Dan kuwa Ummah ta ce ba za a sauya tasha ba, duk haushi ya kama su, su ZEE CINEMA suka so gani, "Ku gama tura bakin ku ba me sauya min tasha Wanda ba zai gani ba ya tafi daki" Shiru suka yi suka samu waje suka zauna, Abbah ne ya gama cinye abincin shi ya saki gyatsa, Ummah ta kalle shi cikin baqin ciki ta Kau da Kai, kallon Jiddah ya yi wadda ta zuba wa TV kallo ba tare da ta qifta ba ya ce, "Ke Jiddo je ki dafo min shayi" Da sauri suka kalle shi dikan su, Ummah na so ta yi magana Dan ta hana amma bata so ta koya wa yaran ta muguwar d'abi'a se ta ce, "Bari na je na had'a maka ai mantawa na yi," "Ni ba ke na aika ba, Jiddah je ki dafo min shayi, ki min irin dahuwar nan me goruba ta fi dad'i" "To Abbah" Ba tare da tunanin komai ba ta fita ta fad'a kitchen da gudu ta ja risho zata kunna kawai se ta ga haske Mai qarfi ya haske ganin ta daga nan bata sake sanin inda kan ta yake ba......................... *Assalamualaikum mutanen kwarai masu albarka anan free pages suka qare, ku biyo ni ta wannan No 09031416423 Dan Jin shin me ya samu Jiddah? Tsakanin Major Muhammad Labbo da Mystery man waye zai mallaki Jiddah, ?menene alakar Jiddah da Muido? Shin Muido na samun nasarar MALLAKAR Jiddah kuwa kamar yanda ya yi wa kan shi alqawari? Shin Hukuma na.yin nasara akan su Muido kuwa? Ku biyo ni Dan Jin yanda zata kaya.....* *Sanarwa* *Ba zan karbi kud'in Novel ba sai ya zama complete,saboda halin yau(idan mune yau ba mu ne gobe ba Allah ne ya San gawar fari), Dan haka ku yi min hakuri har na kammala, duk sanda ya zama complete zan sanar da ku. na gode* [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 7: Hannun ta ta ji an dafe cikin sauri ta d'aga kai suka yi Ido biyu da Ihsaan Wanda idanun sa suke a kumbure saboda kukan rashin Yah Jiddah, cikin dasasshiyar murya ya ce, "Ke Wai ba an ce Kar a sanar da shi me ke faruwa ba saboda yanayin aikin da ya tafi yi?" "Ai tunda ka ga ya kira da No shi ta Nigeria ya dawo qasar ka bari na sanar da shi halin da ake ciki ko zai taimaka mana" "Ki bari har Abbah ya dawo ko a bamu izinin sanar da shi, ke dai duk rashin ji na kin fi ni se ki dinga kafewa akan abu kamar namiji" Harara Balqis ta banka Masa sannan ta ce, "Ko abinda ya fi namiji ba in baka kiyaye ni ba se na b'arar maka da haqora" Ummah ce ta fito daga band'aki idanun nan nata jawur, kallon su ta yi ta kad'a Kai sannan ta kama hanya zata shige d'akin ta, bakin ta na furta, "Allah ya shirya ku, muna cikin wannan mawuyacin halin amma ku kun ga ta yin fad'a, a zato na b'atan Jiddah zai zame maku darasi," Jikin su ne ya yi sanyi, Balqis ta zabga tagumi nan da nan hawaye ya fara zuba mata, kallon Ihsaan ta yi ta miqa masa wayar Jiddahn Dan ta tabbata idan har Yah Major zai ci gaba da kira to fa za ta dauka ta sanar da shi komai. Karba ya yi ya latse wayar gaba d'aya ya kashe ta sannan ya shiga d'akin Ummah cikin kwanukan da take ajiye kud'i ya saka wayar ya bar gidan gaba d'aya. ********************** Tafe suke cikin wani irin surquqin daji ba gida gaba ba gida baya, motar nan ba abinda take da ya wuce tashi Sama sannan ta dawo ta daki qasa,gaba d'aya Jiddah da sauran matan da ke cikin motar sun jiqata, tun suna Kuka har suka danganta suka dena kukan,wani irin mawuyacin numfashi kawai suke fitar wa, Muido ne ya kula da yanda jikin Jiddah ya sake kamar ta Suma,gaba daya ya juya ya hau jijjiga ta, gani ya yi baya iya riqo ta da kyau sakamakon shi ya na zaune ne a gefen driver,cikin tsawa ya bada umarnin a tsaya,wani wawan burki motar ta ci ta tada qura sannan ta tsaya a tsakiyar dokar dajin, yamma ce sakaliya rana ta dakko fad'uwa wajen ya d'auki wani irin yanayi Mai dad'i saboda ruwan da aka tafka tun daren jiyan,gashi har a wannan lokacin akwai alamun hadari wataqila a sake yin wani ruwan Saman, fita Muido ya yi cikin hanzari sannan ya bud'e bayan motar ya fitar da Jiddah daga ciki,sannan ya d'auki ruwan robar da yake Sha ya watsa Mata a jikin ta,nan take ta ja wata ajiyar zuciya mai qarfin gaske sannan ta bud'e idanun ta a Saman fuskar kyakkyawan bafulatanin da a baya take mutuwar son ya furta mata kalmar so, wata iriyar zabura ta yi ta na waige waige Dan ganin inda suke, ta na ganin su a daji ta ji wata iriyar juwa ta deb'e ta ta na qoqarin sake faduwa sumammiya, "Ta tabbata kenan sace ni ka yi? Me na yi maka? Me na yi maka mummuna da na cancanci haka a gare ka? Ka San kuwa yanda zuciya ta ta baka babban matsayi a cikin ta?" Kafin Jiddah ta sake yin wata maganar Muido ya zabga wani uban ihuuu ya ja baya ya daga bindiga Sama se zabga harbi yake, drivern shi da ke tuki ma se washe baki yake saboda ganin halin da shugaban shi ya shiga na farin ciki da murna, a wajen su idan suna cikin farin ciki ko baqin ciki da harbe harben bindiga suke expressing kan su. Wani irin kallon tsana da qiyayya Jiddah ta wurga wa Muido, ganin irin kallon da take masa ne ya sanya shi yin saurin Sanya ta a gaban mota shi ya koma baya ya zauna da sauran matan da ke baya, "Ja mu je D'an Gumel tun kafin ra'ayin Mata ya sauya akan 'yan Maza su yi b'arna, ka San mata ba su da tabbas" Da gudu Wanda aka Kira da D'an Gumel ya ja mota suka ci gaba da nausawa daji Jiddah kuwa ji take kamar ta bud'e marfin motar ta fita idan ma mutuwa ne gwanda ta mace da dai ta zauna a hannun wadannan azzaluman. Kamar Dan Gumel ya gane me take Shirin yi cikin sauri ya danna lock ya rufe qofar, kuka ta fashe da shi Mai tsananin cin Rai, sannan ta ce, "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, la'ilaha illa'anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,ya Allah ka shiga lamuran mu" A bakin wani tafkeken ruwa suka tsaya, mutane ta gani riqe da manyan makaman da tunda take a duniya bata tab'a ganin irin su ba, jikin su ne ya hau rawa ita da sauran matan da suke wajen, motar su na gama tsayawa matasa da dattijan da ke riqe da mugayen makaman nan suka hau ihu suna kabbara suna sakin harbi, d'aya daga cikin matasan ne Wanda ba zai wuce yaro d'an shekara Sha takwas ba ya zo gaban Muido ya cake Yana Masa kirari, ya na gama wa ya ce, "Wacece Babbar yayar tawa a cikin wadannan?" Muido ne ya bada umarnin a kunce masu qafafun su a bar hannayen su a d'aure,nan take kuwa aka cika umarnin shi. Jiragen ruwa suka dinga shiga masu tuqawa na tuqa su,ana tsaka da tafiya ne Muido ya kalli matashin nan Mai suna Sadi ya ce, "Sadi mu yi wani wasa mana," Sadi na Jin haka jikin Sa ya yi sanyi kalau, domin ba kowanne wasan Muido bane abun so, ko ka  rasa wani sashen na jikin ka, ko ka rasa ran ka dika, abu Mafi qaranci shine ka kwana kukan azabar da zai maka, gashi idan ya ce za ai Wasa ba ka Isa ka ce ah ah ba, dole ne se an yi ,iya shekaru biyun da ya yi da Muido ba zai tab'a iya fad'in tsayayyen halin Muido ba, ya dai San shi mutum ne da ke kula da yaran shi, amma hakan baya hana shi yin mugun wasan da zai hallaka wani daga cikin su,har a wannan lokacin be gama gane gaba ko bayan Muido ba,saboda shi d'in quli quli ne bashi da gaba bashi da baya,yanzu ya na iya nuna maka tausayi,anjima ya kashe ka, su bakwai ne a qungiyar tasu Wanda ba garin su d'aya da Muido ba a yawon kidnapping d'in mutane suka had'u, sauran kuwa duk daga gari d'aya suke da Muido,lokacin da ya tashi kafa dabar shi sai ya tattara dika mutanen da aka kashe wa iyaye da 'yan uwa, suka je garin manoman nan suka masu kisan gilla kisan wulaqanci kamar yanda suka yi wa nasu iyayen, duk yanda Muido ya so ya yi wa Mata fyad'e kasawa ya yi,shine abu mafi Muni da aka yi wa Addah petel din shi, Dan haka a cikin qungiyar su ba maganar fyad'e se dai idan mace ta yi maka ka aure ta ko tana so ko bata so ku ci gaba da rayuwa a wajen,dan haka cikin rawar murya Sadi ya ce, "Toh me gida a buga shi kawai" "Da kyau Sadi, fad'uwar gaba asarar namiji....to yanzu ga mata nan a gaban ka, idan ka zab'i Babbar yayar ka a cikin su to zan baka dama ka zab'i mace d'aya a cikin wadannan Kai ma, zai zamana ka na da mata kaima ta kan ka" Cike da fargaba Sadi ke kallon Muido ya na son ya ji idan ya kasa fa? "Idan ka kasa zaben ta a qasa da minti biyar zan wurga ka cikin ruwan nan, ba za ka sake shiga rayuwar mu ba ka amince?" Cikin ran shi Sadi ke ayyana 'Ina da zab'i ne dama? Hankali tashe Sadi ke kallon su Jiddah ya na qoqarin gane wacece a cikin su,cikin Kasada kuwa Sadi ya yi nuni da macen da ke zaune daff da shi, gani ya yi Muido da D'an Gumel sun kalli juna, nan take jikin shi ya fara rawa,dariyar su da ya ji ce ta bashi tabbacin ya canka daidai dan haka ihu ya sa ya na wa Jiddah kirari, ita kuwa Jin kunnen ta take kamar ana zuba mata garwashin wuta saboda gaba d'aya haushin su da tsanar su take ji a cikin ran ta, ga wani irin kyankyamin su da take ji saboda Jiddah yarinya ce Mai tsananin tsafta. A haka suka Isa wani qauye da ake Kira Mariga,qauye ne na Fulani sosai, duk abinda ka ke so na Fulani akwai shi a garin,kindirmon no-no irin Me Mai din Nan,fura ,mafici,kwarya,kaji hatsi kowanne kala saboda akwai manoma sosai a garin, tabarmar kaba, kifi, da sauran su. Ta cikin kasuwanni su Jiddah suka dinga ratsawa wajen shiruuu saboda dare da ya shiga, tsilli tsilli ake ganin mutane, duk inda su Jiddah suka wuce se ta kula da yanda mutanen wajen ke ladabi ga Muido,tafe suke hannayen su a d'aure kamar su ne b'arayin har suka Isa wani gida Wanda daga yanayin yanda ruwan sama ya daki katangar ta yi wani layi layin baqi da ja zaka gane ginin qasa ne, madaidaicin gate d'in gidan aka bud'e su Muido suka shiga ciki, gidan se hada hada ake kamar rana saboda hasken fitilu da ke haska wa, gasasshen rago ne banqare se kwalaben giya da lemuka kala kala, cikin ranta Jiddah ke mamakin yanda mutanen nan suka samu saken da suke aikata abubuwan da suka ga dama a doron qasa hankalin su kwance,Wanda a yanzu sun zama ma kamar su ne hukumar dan kuwa su ake tsoro Sama da yanda ake Jin tsoron jami'an tsaro. A qasa suka zube saboda azabar gajiya, ba tare da Muido ya yi magana da kowa ba baya ga d'aga masu hannu da ya yi ya wuce wani d'aki,nan take d'aya daga cikin matan shi wadda ta San Jiddah ta fito daga dakin da Muido ya shiga ta nufi inda Jiddah ke yashe a qasa, ta San Jiddahn ne kuwa ta dalilin shiga gidan su siyan abinci, nan take ta kama Jiddah ta wuce da ita d'akin da Muido ya shiga, d'aki ne kantameme sosai an raba kowacce katifa da labulaye a tsakanin su, alamun kowa da bangaren ta kenan a cikin matan nasa biyu. Bandakin da ke cikin wajen matar ta tura Jiddah ta fita ta bar wajen, Jiddah na ganin ta a band'aki kawai sai ta durqusa a wajen ta hau kuka, kuka take kamar ranta zai fice daga jikin ta tsabar tashin hankali. "Wayyoo Allah na Allah ka fitar da mu daga wannan mummunan hali da muka shiga, wayyoo Ummah ta wayyoo Abbah na ku zo ku tafi da ni gida ba zan iya wannan rayuwar ba, Yah Major kana Ina ? Yah Sudais ka taimaka min, wayyoo qanwata aminiya ta Balqis, Dan uwana Ihsaan Dan Allah ku zo ku tafi da ni gida Ina tsananin kewar ku, ba zan iya rayuwa anan wajen ba, dabbobi ne ba mutane bane,makasa ne masu zubar da jini..." Kwankwasa qofa ta ji ana yi, da sauri ta tashi ta na qanqame jikin ta,tare da saurin matsewa a jikin qofa ta damqe bakin ta hawaye na zuba, "Ki yi sauri ki yi wanka ki zo Gorko Muido na jiran ki" 'Ya na jira na? In masa me ?baqin azzalumi macuci maha'inci munafuki me fuska biyu' Ba dan yanda Jiddah ke Jin jikin ta ba da ba wani wankan da za ta iya yi a wannan waje da take fatan ta bud'e idon ta ta gan ta a gidan iyayen ta. A gaggauce ta yi wanka tare da wanke kan ta, ba ta samu damar taje shi ba ta tattare shi a haka ta daure da band d'in da ta cire,sannan ta yi alwala,ta na yi ta na tuna yanda Ummahn ta ke gyara Mata kan ta saboda yawa da tsahon gashin ta na asalin hausawa Wanda aka fi sani da Virgin hair, hawayen ta tuni ya had'e da ruwan da ta wanke fuskar ta yayin da take alwalar, banda jan hanci da ajiyar zuciya ba abinda Jiddah ke yi,ta na tsaka da qoqarin maida kayan jikin ta ta ji an bud'e qofar an miqa Mata kaya, cikin sanyin jiki ta Sanya hannu ta karba, ta jima ta na tunanin shin ta Sanya ko kuwa? Qarshe dai haka ta Sanya doguwar rigar atampa da dankwalin irin me santsin nan dan qarami dan kuwa gaba d'aya gashin ta a bud'e yake ta bayan kan ta, a hankali ta fita ta shiga d'akin, zaune ta ga matan Muido su biyu Wanda a ciki ta gane d'aya ta tab'a zuwa gidan su siyan danwake sau biyun gaba d'ayan su idanu suka zuba mata, cikin matsanancin tashin hankali Jiddah ta bud'e qofar bandakin za ta koma ta ji an ja ta baya, kallon juna suka fara yi Ido cikin Ido Muido na Yaba halittar da Allah ya yi Mata, Jiddah na Jin tsananin tsana da qiyayyar fuskar da a baya take tsananin sanya ta farin ciki na taso Mata tun daga qasan zuciyar ta har Saman fuskar ta, kallon da yansa Muido shiga wani irin yanayin da ya maida wa Jiddah kallon tsanar da take masa zuwa kallon tashin hankali da tsoro....... [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 6: "Abbahn su dama yau Kai nake ta jira ka dawo ka ci abinci ka huta na yi maka albishir," Ummah ta fad'a ta na fad'ad'a murmushin ta, tare da kallon mijin na ta da shi ba ya da burin da ya wuce ya gina kan shi da rayuwar shi shi kad'ai, in ta yi wahala ta samo a cinye da shi,kallon ta ya yi ya na tsotso haqorin shi da yake Jin alamar maqalewar tsokar nama, "Uhumm wannan wanne irin albishiri ne da za a bani shi gaban Yara?" Ya fad'a ya na kashe Ido kamar wani saurayi. "Hummm to ai su ma albishir d'in ne a wajen su dan kuwa banda Sudais ba Wanda ya San maganar, zan so Jiddah na kusa zan sanar da ku, amma na tabbata ihun murnar yaran nan kad'ai ya Isa ya afko da ita d'akin nan yanzu,bari Kuma ku gani" "Dad'i na da ke Jan rai, to ki sanar da mu menene mana," "Wato Abbahn su Allah ya hore Mana samun gida, nan kasa da mu, bayan shekaru masu yawa da nake ta sana'o'i kala kala, saida icce ne, wankau ne Saida abinci Saida snaks da sauran su Allah ya hore da taro da sisi da ake samu na sai mana gida, idan da hali ma gobe gobe ko zuwa jibi sai mu koma, Nan kasa da mu ne ba nisa" Tun da Ummah ta fara magana su Balqis ke murna suna ihu da hamdala, Abbah kuwa washe baki ya yi ya na Sanya Mata albarka, shi dai ba zai yi ba, Amma idan ta yi se ya ji dad'i ya ji kamar shi ne ya sauke wani nauyi da ke kan shi. Shiru shiru basu ji Jiddah ta leqo ba dan Jin ihun murnar me ake ba, Ummah ce ta dafe qasa ta tashi da kyar saboda gajiya ta ce, "Bari na je na duba ta, ita d'in ma a gajiye take maybe ko bacci ya d'auke ta a kitchen d'in, dan in ba bacci ba wannan ihun Yaran Nan ke yi da tuni ta jiyo shi" "Ko Kuma qarar saukar ruwan Sama ya Hana ta jiyowa ba" In ji cewae Abbah da ya Haye gado ya kwanta. Ummah na fita ta d'auki ledar da suke yafawa idan ana ruwan sama ta yafa sannan ta shiga kitchen d'in,ganin tukunyar shayin da aka d'ora ta yi ta fad'i qasa da alama ruwan tukunyar ya jiqe rishon jagab,dankwalin Jiddah a yashe a qasa, fitowa ta yi da sauri ta na haska tsakar gidan tare da kiran sunan Jiddah bata ga kowa ba bata ga komai ba, sunan Jiddah ta tsananta Kira a kid'ime, ta na yada fitila bakin kofar fita ta ga warin takalmin Jiddah a kife a qasa se sarqar ta ta azurfa da ta tsinke a qasa,ga qofar gidan a wangale, ihu ta Sanya tare da zabga salati da qarfi ta nufi d'akin Abbah a guje ta na fad'in, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un Abbahn su an sace Jiddah ko Kuma wani mummunan abun ya same ta, Abbahn su ban ga Jiddah ba a dika gidan nan, se warin takalmin ta da dankwalin ta da sarqar ta, Abbahn su idan wani abu ya samu Jiddah mutuwa zan yi" Da kyar ta iya Kai qarshen maganar ta saboda yanda numfashin ta ke fita da kyar, a rud'e Abbah ya sauka daga gado ya taro Ummah da ke gaf da fad'uwa, "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un Sudais kama ta ka kwantar bari na je na duba Jiddahn ka kula min da mahaifiyar ku, kar ka bari komai ya same ta" "To Abbah" Balqis tuni ta fara kuka Dan Jin cewar ba a ga Yah Jiddah ba, Ihsaan kuwa ya daskare a zaune a inda yake dan kuwa mamaki yake Ina Jiddah zata tafi da aka neme ta aka rasa? Ita ba leda ba balle a ce wani ya d'auke ta, mutum ce fa ta ya za a nemi d'an mutum a rasa? A cikin daren nan, a Kuma cikin ruwan nan babu inda Abbah be duba ba amma ba Jiddah ba labarin Jiddah, Wasu daga mutanen unguwar sun taya shi neman ta kafin daga baya su Masa sallama su koma gidajen su. Tun Abbah na jurewa har ya samu dandamalin qofar gidan bawan Allahn da Jiddah ke mutuwar so ya zauna ya fashe da wani irin kuka Mai ban tausayi. "Laifi na ne Jiddah, laifi na ne, se da mahaifiyar ku ta ce na bari za ta dafa min na ce ah ah se ke, gashi nan yanzu abinda hakan ta jawo, Jiddah Ina ki ka je? Dan Allah ki dawo muna son ki mu na qaunar ki" Kuka kawai Abbah ya ke ya na sambatu, ba tare da ya ji qarar bud'e gate d'in da ke gaban shi ba ya ga wata baqar mota mai bakin gilasai ta fito daga cikin katafaren gidan da har yau bai San waye mamallakin gidan ba saboda rashin shiga shirgin mutane da Kuma rashin zama a gida da baya yi, ta gaban shi motar ta wuce a hankali ta cilla Saman hanyar da zata sada mutum da babban titin barin garin Kamba. Abbah na gama ganin gilmawar motar ya sake zabga tagumi ya na fad'in, "To yanzu ya zan yi na koma na ce wa Ummahn su ban ga Jiddah ba?" Aljihun sa ya laluba ya ji makullin motar shi na nan, kuma akwai kud'i a jikin Sa, qafar shi ba ko takalmi kawai ya koma gidan cikin sauri ya buga mota se police station. Ya na zuwa ya hau rattaba masu bayanin b'atan Jiddah, nan da nan kuwa suka d'auki bayanan shi aka bud'e file cikin gaggawa, d'aya daga cikin 'yan sandan ne ya kalli Abbah ya ce masa, "Baba ka kwantar da hankalin ka in shaa Allah za a gan ta, a yau mun samu case d'in b'atan 'yammata masu adadin shekarun 'yar ka Sama da biyar, dan haka muna zargin wadannan mutanen ne 'yan ta'adda suka sace su da yardar Allah zamu tsananta bincike yaran ku za su dawo" "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un,kana nufin maybe kidnapping Jiddah ta akai? To ni kuwa a kafff unguwar mu wa zai min wannan danyen aikin? Ya Allah ka bayyana min 'yata" Hakuri suka dinga ba wa Abbahn Jiddah kafin daga baya ya musu sallama ya buga mota ya koma gida. Ranar nan dai yanda mutanen gidan su Jiddah suka ga Rana haka Daren ya kasance masu a farke,Banda sallah da koke koken Ummah ba a Jin komai, ruwan Saman ya tsaya se yayyafi da ke sauka a hankali, a haka akai sallar asuba kowa zuciya ba dad'i,da safe kuwa se ga mutanen unguwa sun zo jaje, gida

Chapter 4 of 12