bud'e naka saboda rashin godiyar Allah, idan Kuma ba haka ba za ka dena aiki anan sannan na sa a rufe asibitin ka na can d'in shashasha"
Ba tare da likitan ya gane me magana ba, ya miqe tsaye dan tattara ya nashi ya nashi ya kama gaban shi ya koma Kamba, dan da Jin muryar Mai maganar ba qaramin mutum bane, to wanne munafikin ne ya sanar da shi Yana da asibiti a birnin kebbi? Idan ya gano ko waye se zaman garin Kamba ya Masa wahala.
Major na nan tsaye ya kasa zama Dan dama zama na Mata ne tsayuwa se zaratan Maza, a haka Abbah da su Ummah suka iso asibitin Wanda ita kan ta Ummah se da aka bata magani saboda Jinin ta da ya yi bala'in hawa sannan sugar d'in ta ya yi low ta jima rabon ta da abinci,se Kuma aka bata gado ta kwanta saboda ta samu hutu.
Ran Major idan ya Kai million ya b'aci da yanda ya ga take taken Abbah, dan haka cikin bacin rai ya ce,
"Abbah dan Allah minti d'aya ina da magana da Kai a waje"
Zaro Ido Abbah ya fara sannan ya ce,
"Iyyee? Ka na son gani na? Ina zuwa to bari Ummahn tasu ta yi bacci ka ga an ce ta na buqatar hutu"
"Abbah muje na ce Ina son magana da Kai !"
Ba yanda Abbah ya iya haka ya bi bayan Major zuwa waje zungui zungui kamar kazar da kwai ya fashe wa a ciki........
*Su Abbah manyan qasa..... I love your comment mutanen kwarai masu albarka...kwantiniyo kwamentin and I promise to kwantiniyo typing more pages for you in shaa Allah*
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 16:
Major Muhammad Labbo bai zauna ba, be Kuma huta ba har sai da ya tabbatar da an shigar da qarar su Muido babbar kotun garin Abuja,duk Wanda ya gan shi zai tabbatar da ya ga jarumin soja, tsayayyen soja, domin kuwa Major Muhammad Labbo be saka komai a gaban shi ba da ya wuce taimaka wa qasar shi ko da shi zai raunata,ya Sha karb'ar harbi a jikin shi se ya yi kamar ba zai rayu ba sai Kuma qudirar Allah ya tada shi,ya ci gaba da gwagwarmaya, shi kan shi ya San wannan karon bayan yi wa qasar shi hidima, samun tsaro da kwanciyar hankalin Jiddahn shi ya qara tunzura zuciyar shi, duk da matsalolin da aka so a samu da tsaikon da aka so a samu na gurfanar da Muido a gaban kuliya Wanda ya kasa gane daga Ina wannan kariyar da ake so a bawa Muido take fitowa, be karaya ba ya na nan ya jajirce se da komai ya tabbata, kuma ya yi alqawarin bibiyar qarar har qarshen ta,gefe daya Kuma Yana nan Yana jinyar hannun sa da harsashi ya wa illa,sauran Yaran shi Wasu na asibiti Wasu na Bakin aiki.
Matar Major Muhammad Labbo mai suna Sakeenatu wadda Jiddah da sauran qannen Major ke Kira da Aunty Sakee ta bada gudummawa wajen qarfafa wa Major guiwa tare da nuna masa Kar ya gajiya domin ko babu Jiddah akwai sauran al'ummar musulmai da ke buqatar kariya daga ire iren mutane kamar su Muido.
Be samu ya koma Kamba ba se da ya yi wata d'aya da sati biyu, ranar da ya shirya zai tafi ya sa Aunty Sakee a gaba ta had'a kaya har da nata da na Yara,dan ya San idan ba haka ya yi Mata ba zata kawo masa wani uzirin Dan Kar ta je garin mahaifan nashi da ya kula Bata qaunar zuwa.
Game da Jin ya lafiyar Jiddah take kuwa kullum sai ya kira Sama da sau uku ya ji ya take, wane ci gaba aka samu,me ake da buqata, Balqis kuwa bata b'ata lokaci wajen sanar da shi duk wani abu da ta San zai so ya sani d'in, Dan ita kan ta ta matsu Yah Jiddahn ta ta samu lafiya.
Major Muhammad Labbo ne da iyalan shi a jirgin sama idanun sa lumshe ya na tunanin shin a yaya zai ga Jiddah? Sanar wa aka fara akan kowa ya d'aura belt d'in mazaunin shi,hankalin shi na can duniyar tunanin Jiddah ya ji hannun Sakeenatu a qugun shi ta na qoqarin d'aura Masa belt d'in,suna had'a idanu ta yi murmushi sannan ta ce,
"Kar ka damu soja na, she is fine, even if she is not fine now she will be fine, na tabbata 100% za ta samu lafiya, Allah ba zai bar ta ta yi ta Shan wahala ba, ok? Ka kwantar da hankalin ka please we all need you, alive and healthy"
Murmushi ya yi Mai sauti, sannan ya kama fuskar ta ya sumbaci bakin ta, daga baya ya jingina da kujera ya furta,
"Subhanalladhi sakkharalana hadha wama kunna lahu muqurinina wa inna ila rabbina lamunqaliboon,"
Sakeenatu da yara Suma addu'a suka yi, sannan yaran suka hau kallo a tabs din su, hannun Sakeenatu Major ya kama sannan ya ce,
"Ki yi hakuri Mata ta da abubuwan da suke faruwa, na sani suna Sosa ran ki,amma Ina roqon Allah ya kara maki hakuri da ni ya yaye maki mummunan kishi ya sa ki so Jiddah itama ta so ki duk sanda wannan al'amarin ya tabbata ku zauna lafiya"
"Ameeen ya Allah Soja na, kar ka damu da ni ka San wace iriyar rayuwa na yi a baya, amma hakan be dame ka ba, ka San su wanene ahali na, Kuma ka aure ni a haka Dan haka na koyi darasin rayuwa kala kala, ba zan tab'a matsa maka ba akan abinda ka ke so"
Murmushi major ya yi sannan ya ce,
"Baki da wata matsala a rayuwa Sakeenah, Ina son ki ke kin sani Ina Kuma qaunar ki ba zan tab'a dena son ki ba ko Mata dubu zan aura a duniya ke ce ta farkon su,Allah ya yi maki albarka"
"Ameeen ya Allah, ka ga irin addu'o'in nan da ka ke yi min da kulawar da ka ke bani da tausayi na da ka ke ji, su ke qara Sanya min natsuwa domin ko ba komai na San nima Ina da babban matsayi a wajen ka, ko da ka fi son Jiddah akai na nima ka na so na"
"Ina son ki mata ta, Ina son ki sosai a cikin zuciya ta da ruhi na"
Kwantar da kan ta ta yi a kafad'ar shi, tare da matse hannun ta cikin nashi, tabbas ta sani ya fi son Jiddah akan ta, amma Kuma yanda yake nuna mata soyayya da jaddada mata kalmar Yana son ta suna mantar da ita kishin Jiddah da ke damun zuciyar ta, sannan abu na gaba da ke Hana zuciyar ta tsanar Jiddah, Jiddah yarinya ce kyakkyawa baqa, Mai natsuwa da rashin qiwa, duk sanda Jiddah ta je masu hutu ita ke komai a gidan, ita daga chatting se yawon shopping da Yara da qawaye, da an ji sabon abu ya fito an tafi siyo wa, hatta da abincin miji Jiddah ke had'a wa ta Kuma kula da Yara, ta tabbata idan aka auri Jiddah ita kam hutu ne ya zo mata, yawo kuwa da ake hana ta saboda Yara zata samu sauqin sa.
Ba jima wa jirgin su ya sauka a sokoto,suna Isa motoci biyu suka je d'aukan su Dan Kai su garin Kamba, major riqe da hannun Sakeenah,yaran su na riqe da hannun kowannen su abun gwanin burgewa, tafe suke suna hira har suka Isa bakin mota suka fad'a, suna shiga aka saka kayan su a bayan mota sai suka d'auki hanyar Kamba.
A can garin Kamba kuwa Jiddah ta dawo gida ana ci gaba da kula da ita, har a wannan lokacin Bata gama dawowa daidai ba, ga rama saboda Bata cin abinci da kyau se Ummah ta zauna ta Bata, sun kasa gane tunanin da ke cin ta take qara qarmashe wa kamar wata takarda,duk tambayar duniya Ummah da Balqis tare da Sudais sun yi mata akan dalilin yawan tunanin da take yi ta kasa magana, qarshe ma idan aka matsa Mata se ta kama kuka ta na fad'in,
"Kaico na, kaicon zuciya ta, Ummah Dan Allah ki dinga yi min addu'a Allah ya sauqaqa min wannan rayuwar da nake ciki"
Ummah kuwa ta kasa samun kwanciyar hankali itama saboda rashin kwanciyar hankalin Jiddah, a haka suke rayuwa kowa ka gani fuskar shi babu wata walwala kamar a baya,Abbah kuwa har wata qiba ya d'an yi abun shi, shi a bangaren shi hankalin sa kwance yake ba abinda ke damun sa.
Sanin cewa Major a gidan zai sauka ya fara cin abinci ne ya Sanya Ummah shiga kitchen ta yi Masa lafiyayyen abincin duk da ya fi so,ta hada Masa zob'o da kunun aya Mai dad'i, tare da lemon kankana, se lemon tsamiya,gaba d'aya suna fridge sun yi sanyi sosai jiran Baki kawai suke, ta na tunanin yanda zata ga jikokin ta Dan kuwa ta jima rabon ta da su.
Jiddah ce ta fito daga wankan da aka matsa Mata dole sai ta yi,Wanda ba Dan haka ba niyyar ta ta yi zaman ta a d'aki, Bata son ganin kowa Bata son yi wa kowa magana, she always wants to be alone in a dark room doing nothing.
Shafa mai Balqis ta uzzira Mata ta yi, se kawai ta fashe da kuka ta yi wurgi da man ya fad'i qasa har ya na zubewa, zanin ta ta daura ta yi kwanciyar ta,ta takure waje d'aya se ka rantse ba kowa a wajen,qashin hips d'in ta kawai zaka hango tunda ta na da hips sosai ramar da ta yi ne ya Sanya suka zube se qashi kawai.
Gashin ta da Balqis ta gyara Mata ta yi mata parking na zaune das a Saman kan ta ta baya ya cika ya yi fusss, fuskar ta ta yi fayauu gwanin ban tausayi domin kuwa har qashin kumatun ta ana hangowa,ita kan ta ta tabbatar da ta rame Wanda ba Dan ta San ba abinda Muido ya yi Mata ba se ta rantse cutar qanjamau ce ta qanjame ta.
Tuna wa da shi da ta yi ne ya Sanya hawaye zuba a idanun ta, da sauri ta Sanya hannun ta a saitin zuciyar ta ta na fidda wani irin numfashi,a hankali take fad'in,
"Wayyoo Allah zuciya ta, wayyoo Ummah na, zuciya ta Baki yi min adalci ba, na kamu da son mutumin da ya cutar da ni, ya cutar da iyaye na da duk wani masoyi na, na kamu da son wanda Babu Allah a ran shi, ba arabi ba boko, na kamu da son wanda ya d'auki kashe mutane a matsayin sana'a, Muido baya Jin cewar shi ba a kan daidai yake ba balle a taimaka Masa ya fita daga wannan mummunar harkar, ya zan yi ne? Allah ka kawo min mafita Kar na had'iyi zuciya na mace, a wanne hali yake a yanzu? Me yake yi? Ina zan...."
Da gudu Balqis ta fad'a d'akin ta afka Saman katifar tasu ta na fad'in,
"Sun iso Yah Jiddah, sun qaraso, Baki ga yanda Yah Major ya rame ba Shima, amma fa ya yi kyau, Aunty Sakee da yaran ma duk sun yi kyau Masha Allah, tashi ki saka kaya Dan Allah ba Dan ni ba, ki aje fushin ki a gefe Dan dai ba Wanda ya San me ke damun ki tunda kin qi fad'a "
Wata uwar harara Jiddah ta sakar wa Balqis Wanda hakan ba qaramin dariya ya Sanya Balqis ba, cikin dariya ta ce,
"Yah Jiddah zan Baki shawara kar ki sake irin hararar nan, Dan se ki tsorata bawa, kin ga idon ki kuwa? Gullisuwa sunan wani abu, can ciki ya yi rami kamar a zuba ruwa a ciki ya zauna, tashi Dan Allah saka kaya, kin San zai shigo Kuma haramun ne ya gan ki a haka ko?"
Jin cewa haramun ne ya gan ta a haka ya Sanya Jiddah karbar rigar da ta yi mata yawa, ta Sanya sannan ta yafa mayafi siriri a Saman gashin kan ta kafin ta had'e shi da gashin ta ta d'aure.
Kamar jira yake kuwa ta na gama wa ya na doka sallama, Jiddah kuwa ji ta yi zuciyar ta ta buga da karfi, tausayin kan ta da shi kan shi Yayan nata take ji, kwallar ta ta mayar Sannan ta amsa sallamar shi tare da yi masa izinin shiga.
Balqis na ganin ya shiga se ta fita ta na washe baki,zama ya yi a qasa a gefen katifar tasu inda ya ga Jiddah na zaune,sallama ya sake yi mata ta amsa kan ta a qasa, ta kasa bari su had'a idanu, ji take yi kamar da ya kalle ta zai gane menene a zuciyar ta, Dan haka sai ta gwammace ta yi wasa da yatsun ta sama da ta kalli cikin idanun sa.
"Jiddahty ya jikin naki?"
'Humm Yah major kenan Wai Jiddahty' ta fad'a a ran ta, a zahiri Kuma sai ta ce,
"Alhamdulillah da sauqi, da fatan kun sauka lafiya "
"Alhamdulillah Jiddahty,amma ya na ga kin rame har yanzu ba ki da wani Kumari, ko dai abinda ki ke son ci ne Babu? Bari na aika a kawo maki duk abinda ki ke so, sanar da ni me da me ki ke da sha'awar ci?"
Da sauri Jiddah ta daga kan ta suka yi Ido biyu da idanun major,kafe shi ta yi da Ido ta na so ta gano aibun shi, ta kasa ganin wani abu da ya sa Bata Jin soyayyar shi irin ta soyayyar saurayi da budurwa sai dai ta 'yan uwantaka,murmushi ta yi a ran ta ta ayyana,
'Laifin ka d'aya ka yi kama da ni ni kuma na gaji da ganin Kai na a madubi'
Major ya ji dad'in ganin murmushin ta Dan haka sai ya sake matsawa kusa da ita murya can qasa ya ce,
"Jiddahhtyy sanar Dani me ki ke so?"
Kallon shi ta yi Ido cikin Ido ta ce...............
*Me ku ke tunanin zata sanar da Major ta na so?*
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 15:
Kafe shi ya yi da Ido bayan ya tambaye shi a Ina suka samo Jiddah a karo na biyu, cikin daburcewa Abbah ya ce,
"Ka na ji ba, ni dai a gani na a bar bala'i ya yi bacci,tunda Allah ya kub'utar Mana da ita da ran ta, mu bi su da Allah ya Isa kawai,mu maida hankali akan nema Mata lafiya,mutanen nan yanda na gan su cikin kayan yaqi da tashin hankali da bala'i da masifa Allah ya gwadan Annabi,ba na so wata alaqa ta sake had'a mu har abada"
"Ba za a bar su ba ! dole ne su karb'i hukunci daidai da abinda suka aikata,tsoron me ka ke ji? Kar ka manta fa Kai uba ne, na tabbata akwai Wasu yaran da ma magidanta wanda suka bar iyalan su ba cin yau balle na gobe a hannun su, na tabbata wannan kashe kashen da ake ta yi na ba gaira babu dalili a daji da saka hannun su, me ka ke tunani watarana ko ni ko Kai wani ya fad'a a kwatankwacin wannan hali? Kai da kan ka ka ce sun ce za su waiwayi Jiddah d'azu da muna hira, kana nufin mu zauna mu nad'e hannu har sai sun dawo kenan?"
"Ah ah ba haka nake nufi ba, kar ka kai ni inda Allah be Kai ni ba yaro, Ina nufin kafin su waiwaye mu ka aure ta ka wuce da ita can Abuja, ka ga ko sun zo ba se su d'auki uwar su ba tunda sun aje ta wajen mu?"
Major ya kula Abbah na da taurin Kai duk yanda zai yi ba zai sanar da shi wajen ba, se kawai ya tafi ba tare da ya sake ce masa komai ba, shago ya nema ya siyo wa Jiddah ruwan roba masu sanyi da lemuka masu kyau da sanyi, se abinda za ta ci idan ta farka, had'e da kayan marmari,duk wani magani da abinda aka rubuta major ne ya kula da biyan kud'in, ya na nan ya na sintiri tare da latse latsen wayar shi, se ga wani mutum nan gajere sosai kamar a kife da kwarya ga uban tumbi ya ci riga da wando irin na bature, se nishi yake zubawa, goshin nan dogo me tsini na ta nason maiqo, ga 'yar jakar shi a hannun sa da farar rigar likitoci sai stethoscope riqe a hannun da ya riqo jakar ta shi, direct wani office ya zira wa key zai bud'e Major da ke latsa waya ya na kallon sa ya tsaya da abinda yake ya ce,
"Nan za ka zo ka min bayanin dalilin da zai sa da ka bud'e asibiti ba za ka bari sai da weekends ka dinga zuwa ba kana neman kud'in,ka ga lokacin ka gama da aikin da gwamnati ta Sanya ka take biyan ka,"
Da sauri bawan Allahn nan ya juya su Kai Ido hud'u da major, daga qasa ya fara kallon shi har se da ya dire ganin shi a Saman fuskar major,tabbas wannan duk yanda akai babban mutum ne, to daga wace hukumar lafiyan ya zo? Cikin washe haqoran sa qanana Wanda suke farare tasss ya kalli Major ya ce,
"Ranka ya dad'e ai yanda ka ce haka ake yi, yau d'in an samu matsala ne my attention was needed there shi ne na tafi dama da niyyar ana kammala abinda ake a can a dawo Kuma, ehhhh, Bismillah Bismillah mu je office ka sha ruwa garin yau ana zafi"
"Kai gari ya wa zafi, ko na ce zai maka zafi a duk sanda makamancin hakan ya sake kasance wa, ka kalle ni da kyau, suna na Major Muhammad Labbo, Ina da hujjojin da za su Sanya ka ajiye aikin ka akan dole tunda Kai ka zab'i hakan"
"Dan girman Allah ranka ya dad'e ka taimaka min, irin haka ba zata sake faruwa ba Ina da iyali,ka yi hakuri ranka ya dad'e asibitin nan munafukai sun yi yawa, ban tab'a zaton dan yau kawai na je asibiti na saboda ceton rai har za a samu Wanda zai min gulma akai,"
"Sam Kar ka zargi kowa, ba wanda ya fad'i Wai ka je asibitin ka, na fad'a ne by experience Kuma se ya kasance haka ne, dan ni wata ma anan ce min tai ka tafi taron likitoci, mara lafiya na kawo ba likita a asibitin shi yasa na yi magana"
Major na gama fad'ar haka ya wuce ya na ci gaba da yi masa warning sannan ya bashi umarnin ya duba Jiddah da kyau, tafe yake tinqis tinqis ya na ta surutai, gashi dai ya na so ya sauke haushi akan wani a wajen ba dama, haka ya gama duba Jiddah aka d'ebi Jinin ta domin yin gwaje gwaje, Wanda wani ma se an je birnin kebbi dan ba su da kayan aikin yi a nan asibitin.
Haka Jiddah da Ummah suka kwana a asibitin a kwance suna jinyar jiki da zuciyar su, washegari Team din Major na iso wa suka d'auki hanyar Niger, duk wani bincike da samun information sun tsaya sun yi iyakar iyawar su, dan kuwa ba su bar garin ba sai da suka kwana hud'u.
A ranar da za su dawo ne suna ta shiri a hotel d'in da suka kama suka ji an kwankwasa qofa, se da suka dan yi jinkiri kafin nan yaron Major ya Isa bakin kofar dan ganin waye ya buga, d'aya daga cikin yaran Major ne ya bud'e Mai suna Sani, ko da ya leqa be ga kowa ba sai wani d'an qaramin box, duqawa ya yi ya d'auka jikin shi na bashi what if bomb ne a ciki fa?
Yana yin wannan tunanin se ya qi koma wa cikin d'akin ya bud'e a hankali, wata Yar takarda ya gani a ciki ita kadai, waiwaye ya yi sosai Bai ga kowa ba da zai zargin ko shi ya ajiye box d'in, d'aki ya koma ya je gaban Major ya bud'e akwatin ya nuna masa takardar da ke ciki, karba ya yi ya na sauraron bayanin Sani na cewar ya bud'e qofar ne ya gan shi a qasa be ga kowa ba.
Bud'e takardar ya yi ya ga ba abinda aka rubuta sai address, da sauri ya miqe ya qarasa Sanya kayan shi, wayar shi ya danna ya kira sauran abokan aikin sa dake a Wasu dakunan ya ce Maza su shirya su na da wajen zuwa.
Suna kammala shiri suka fita daga hotel d'in sai bakin motocin su Wanda ke dankare da kayan aiki irin nasu na sojoji,da gudu suke Keta titunan garin Niger saboda suna son Isa kwatancen da aka yi musu a can garin zamfara da wuri, ba abinda Major ke yi sai addu'ar neman nasara akan abinda suka Sanya a gaba, ya na gama wa ya fara bada umarni da yanda za su tunkari inda za su je ta waya kowa na sauraren sa suna amsa shi, cikin kwarewa direbobin ke tuka su zuwa garin zamfara.
**************************
Bayan Muido ya bar gidan sa cikin qunci da tsananin damuwa tare da karyewar zuciya akan abinda masoyiyar shi abar qaunar shi Jiddah ta yi Masa, sai kawai ya fara bin duk wani aiki da Allah Reni ya Sanya shi yi ya na qi ya kammala su, babban abinda ya fi bashi farin ciki a wannan aiki be wuce yanda suke tare motocin bayin Allah ba su dinga dagargaza masu harbi ba tare da sun tsaya karbar ko taro a hannun su ba,se sun kashe su ne suke tsaya wa duba motocin ko da akwai abinda suke da buqata su d'auka, Wasu kuma motocin haka za su tsaida su su tasa keyar mutane zuwa daji, idan mutum ya gaji kafin a Isa Muido ya harbe shi ko ya sa a harbe shi, idan mutum ya tsaya tsoro da magiya sai Muido ya tuno yanda Jiddah ke Jin tsoro idan ta ga ya na kashe mutane se hakan ya b'ata masa rai ya hau harbi kamar an aiko shi, kullum cikin watsa kwaya yake dan kan shi ya d'auki caji ya manta da Jiddah amma inaaa, Jin son ta yake a cikin Jinin shi ya na Masa yawo, Jin son ta yake a cikin zuciyar shi ya zauna daram kamar a lokacin ya fara son ta.
Muido ya fara yi wa mata fyad'e dan ya huce takaicin qin yi wa Jiddah fyad'e da bai yi ba saboda soyayyar da yake nuna Mata, ya zama kazami wannan gayun da yake ya saka kwalli ya taje gemun nan kan nan ya Sha taza a kitse qarshen shi duk babu, iyakar shi labta kwalli kullum,rabon shi da wanka ma kuwa tun da suka baro garin Mariga, idan ka ga Muido ya yi wanka to ruwan sama akai ya dake shi amma ba dai shi ya watsa ba, ya maida rayuwar shi kamar ta mahaukacin Zaki dan kawai ya manta Jiddah a cikin ran shi.
Lokuta da dama idan tunanin ta ya ki barin zuciyar shi nausa wa yake daji ya yi ta tafiya shi kadai ba tare da ya San inda yake zuwa ba, haka zai ta kuka ya na zagin zuciyar shi mai rauni, ya na zagin soyayya tare da kiran bata yi masa adalci ba.
A yau Muido ya tashi da zuciyar mugunta kwarai, Kuma ya shirya tsafff dan satar mutanen da yake so ya kafa tarihi akai ba iya Nigeria ba so yake dika qasashen Africa su shaida Nigeria ba tsaro, so yake qasashen turai su shaida gwamnati ta gaza wajen ba wa mutanen Nigeria tsaro, sanye yake cikin kayan sanyin da a Koda yaushe suna jikin Sa, hatta da hannun sa ya saka irin safar nan ta hannu da sojoji ke saka wa, jikin shi sanye da makamai manya, idanun nan sun kada sun yi ja a lumshe tsabar d'ibar kwaya da ya yi, se wani lumshe wa suke suna dawowa daidai,ga kwalli nan rambad'ad'au ya zabga,gemun sa da baya samun gyara duk ya cika fuskar shi, haka ya dinga magana cikin yaren fulatanci ya na ba da umarnin a shirya a wuce wajen neman kud'i, Wanda Yana mamakin duk uban kud'in fansar da suke karba hannun mutane sun kasa yin arziqin da zai zame masu yanke talauci.
A machines suke Keta dajin su na wani ihu da kururuwa su a dole ga Marasa imani Wanda suka manta da Allah shi kad'ai ya cancanta ya d'auki ran bayin sa saboda shi ya halicce su, sun manta da cewa kashe mumini da gangan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 12