wa su mahafiyar Muido fyad'e suka d'auke su kamar kayan wanki suka wurga su cikin bukkar su, sannan suka banka ma wajen wuta, ihu suka dinga yi suna wa kawunan su kirari, kafin daga bisani su Kora sauran awaki,tumaki da shanun na su Muido har ma da jakunan da aka d'ora wa kaya suka yi gaba.
Da misalin tara da kwata na safiya sai ga Muido nan ya nufato ruggar su da shanayen su da ke da ciki guda goma Sha tara, Yana tafe ya na murmushi Dan ya San yanda zai lallab'a Mahaifin nasa Kar ya Masa fad'a,haka nan ya ji gaban shi na faduwa bai San dalili ba, azama ya sa ya ci gaba da nufatar garin nasu Wanda tun daga nesa ya fara hango baqin hayaqi da mugun qaurin da ke tashi, wata iriyar faduwar gaba ce ta same shi, nan take ya bar shanun ya Isa rugar tasu a guje kamar mahaukaci sabon kamu, banda kwala wa mahaifan shi da qannen shi Kira ba abinda yake yi.
Ihun mutane da neman taimakon su kawai ke tashi ko ta Ina, gefe d'aya Kuma Mai gari ne da fadawan sa ke bi suna ganin barnar da manoman suka yi wa rugar tasu suna Allah wadai da abinda aka yi musu tare da cin alwashin daukar fansa.
Muido na Isa bukkar su abokan shi da suka zo ganin abinda ya faru suka tare shi, Dan kuwa har a wannan lokacin wuta na nan na cin bukkar tasu,makiyayan ba su wani jima da barin wajen ba.
'Me ya samu Innar mu? Ina Baffana da qanne na? Ku sake ni na je na ga qanwata tana tsoron wuta bata son ta ga wuta na ci hankalin ta na tashi, Ina Innah ta ta na da hawan jini ba ta son zafin wuta, ku matsa na je na gan su, wayyoo Allah Baffah am ka yi hakuri ka yafe min abinda na yi ba zan sake qin Jin maganar ka ba, na zaci har na je na dawo baka dawo daga masallaci ba shi yasa na je ba wa chanun da ke da ciki ruwa, Baffah ka tashi ka fad'a min Ina Innah da Addah petel suke Ina Sa'ade Ina sauran qanne na suke ne? Wai ba me bani amsa ne?'
Gaba d'aya Muido ya fita a hayyacin shi, sannan ya ba wa mutane da yawa a wajen tausayi duba da yanda kowa ya San shaquwar da ke tsakanin ahalin, Wasu sai taya shi kuka suke, Wasu Kuma na ganin shi a matsayin ragon namiji Wasu sun fi shi shiga bala'i amma ba su yi kukan da yake yi ba, me zai sa ya dinga abu kamar ba namiji ba?
'Muido am ka yi hakuri, taso Mahaifin ka ya riga ya rasu ba zai iya yi maka magana ba, mahafiyar ka da qannen ka Mata kuwa makiyayan nan Wanda suka zo da makamai cikin Shirin qungiyar sa Kai sun kashe su bayan sun yi masu fyad'e,Muido qannen ka Maza kuwa sun yi masu yankan rago duba can...'
Ganin Muido ya zube a qasa a sume ne ya Sanya farin bafulatanin da ke ta bashi mugun labarin nan yin shiru ya na salati, matasa biyu ne suka d'auke Muido aka Kai shi gidan mai gari,Dan kuwa ba shi da kowa ba shi da komai, ba Kuma Wanda ya bi bayan shanun da ya dawo da su balle su zama abinda ya mallaka a rayuwa bayan rasuwar ahalin shi.
Kwanan Muido takwas be San inda kan shi yake ba, se an kwantar se an tayar, daidai da ruwa in an bashi baya wuce masa, ikon Allah ne kawai ya raya Muido har ya cika kwana goma a kwance Yana jinya, a Kwana na Sha d'aya ne ya samu farfad'o wa,da ihun Kiran sunan 'yan uwan shi ya farka tare kalamai na tuhuma da cin alwashi.
'Sai na da'u ki fansa, ba zan yarda ba, se na rama abinda aka yi wa ahali na, me yasa ba a taimaka musu ba sun kub'uta daga hannun azzaluman Nan? Me yasa aka bari suka kashe min dangi na? Me yasa ahalin Mai gari da shanun shi da tumakin sa suke da rai ba Wanda ya mutu? Me yasa gamagarin mutane irin mu ne suka rasa rayukan su da dukiyoyin su? Me yasa? Me yasa? Me yasa?'
Kuka kawai yake yi ya na sambatu, duk yanda akai ya yi shiru ya kasa yin shirun....bud'e qofar cell d'in da aka yi ne ya Sanya Muido d'aga kan shi ya kalli sojan da ke tsaye ya na daka Masa tsawa.
"Ya ana ta Kiran sunan ka ka yi wa mutane shiru? Ko an fada maka nan ma dajin naku ne? Nan uban ka za mu ci ka mana iskanci qaramin dan Iska kawai, ka San za ka yi nadama me yasa ka fara, duk kukan ka se an kashe ka Kai ma kamar yanda ka kashe bayin Allah "
Murmushi Muido ya yi sannan ya sa tafukan hannayen shi ya share hawayen shi da yake Jin dumin su har a wannan lokacin, da Ido ya bi sojan har suka fita suka bar building din baki d'aya, a cikin motar da ake Kai masu laifi kotu a ciki aka Sanya Muido Wanda zuciyar shi ke cunkushe matuqa da tunanin silar kamashi, Jiddah ita ce silar komai,Jiddah ita ce rayuwar shi a yanzu ba Kuma zai huta ba har sai ya sake samun ta a karo na biyu, be gama daukar fansar abinda aka yi wa iyayen shi da qannen shi ba.
Ya sani ko ba jima ko ba dad'e wata ran zai mutu amma be shirya mutuwa a hannun hukuma ba ta hanyar yanke masa hukunci, dan haka nan take ya rintse Ido ya na fatan wani tsautsayi ya gilma a shari'ar a sake shi ya koma bakin aikin sa.
Muido be gama isar da fatan shi ba suka ji an daki motar su da wani irin qarfin da se da dikkan Wanda ke motar ya sauka daga mazaunin sa ya Fadi qas, Wasu Kuma suka yi gware da junan su.
A Saman babban titin da ke garin Abujan matasa sanye da kayan sojoji fuskar su daure da baqin kyalle suka tsaya,hannayen su Wasu irin mugayen makamai ne dangin bindigu kala kala,da muggan makamai wanda ko hauka mutum yake aka ce ya je wucewa ta wajen ba zai je ba zai gudu.
Cikin ruwan sanyi suka bud'e Muido suka Sanya shi cikin wata kyakkyawar mota baqa Mai bakin gilasai, motar ta cilla Saman titi da mugun gudu Wasu motoci guda biyu kalar ta na take masu baya.....
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 3:
Zaune yake luntsume a cikin kujerar had'ad'd'iyar motar da aka sace shi daga hannun hukuma se gudu drivern yake da alama inda za su je akwai nisa, lumshe kyawawan idanun shi ya yi tare da sauke sassanyar ajiyar zuciya, murmushi ne kwance a Saman fuskar shi mai cike da gashi duguzummm Wanda da gani ya jima Bai samu aski ba, yaran shi ne ke yi masa bayanin yanda Babban ogan su ya sa a had'a gadar zare dan a kub'utar da shi daga hannun hukuma, wayar da ake miqa Masa ya karba, cike da ladabi ya fara magana cikin harshen fullanci da hausa,
"Allah Saini barka da war haka......
Miyetti masin Allah Saini Allah wadi barka, se mun iso"
Abinda ya fad'a kenan ya miqa wa Wanda ya bashi wayar da farko, sannan ya Kara lumewa cikin kujerar tare da lumshe idanun shi kamar mai son ya yi bacci, nan kuwa ba bacci yake ba tunanin ta ne fall cikin zuciyar shi.
"Jiddah"
Shi ne sunan da ya furta a hankali, Wanda idan ba mutum ya natsu ba ma ba zai ji me ya ce ba da kyau.
"Se na cika alqawari na akan ki hankali na zai kwanta, idan da fari an yi min fin karfi wannan karon ban dawo da Wasa ba, ba zan tab'a barin ki ba, sai na mallake ki, sai kin zama tawa ni kad'ai,saboda ke nake ci gaba da rayuwa a yanzu,"
Waiwaye.......
Tafe take cikin uniform d'in ta na makarantar boko se tsiyayar da zufa take, sakamakon zafin da ake bugawa a garin na Kamba dake a qaramar hukumar Dandi,Rana ce ta kwalle sosai kamar zata tafasa kwakwalwar d'an Adam, tasbihi kawai take ga Allah saboda idan ba Allah ba ba mai gudanar da wannan lamari, ga rana, ga zafin da ake zabgawa Kuma dan Adam ya ci gaba da rayuwa be narke ba ko ya qone.
Murmushi ta yi da ta yi wannan tunanin, har ta na ayyana,
'Wai wa ya ga Jiddah Black ta qone, ko ta narke ta zama kitse'
Ledar hannun ta da ta yo cefane ta qara damqe wa tare da sake rataya jakar makarantar ta a kafad'ar ta ta dama, cikin sauri take taku dan son Isa gida da wuri ta watsa ruwa, qanwar ta ce ta yanko daga wata kwanar da ke gaban ta ta na dariya,itama Jiddahn dariyar ta yi sannan ta ce,
"A gaskiya Iska na wahalar da mai kayan Kara,ko dake bahaushe ya ce sa Kai ya fi aikin bauta ciwo,yanzu dai gashi takun da ki ka wuce ni da shi kad'an ne,ga uban sauri ki na ta zabga wa dan Kar na wuce ki,amma kin qi ki dena wahalar da kan ki a banza"
"Oho dai na riga ki isowa gida woooo"
Da gudu Balqis ta fad'a cikin gidan nasu saboda ganin Jiddah ta kusan riga ta shiga ciki, cikin raha da walwala suka karasa cikin gidan nasu na haya Wanda yake da dakuna biyu kacal ba kitchen ba parlour se tsakar gida mai fad'i da bandaki biyu.
A gefen tabarmar da mahaifiyar su da suke Kira da Ummah ke zaune Suma suka zauna suna maida numfashi,da sauri suka cire hijaban su suna gaishe ta cike da girmama wa,domin kuwa Jiddah da 'yan uwan ta sun samu cikakkiyar tarbiyyar Islama wajen mahaifiyar su.
"Lafiya qlou 'yan albarkan Umman su,an dawo kenan, ya jarabawar to?"
"Eh Ummah mun dawo jarabawa Kuma alhamdulillah"
"Da kyau, Allah ya muku albarka ya bada sakamako mai kyau mai albarka,Jiddah ya naga kayan miyan yau kamar da yawa?"
"Eh Ummah ba laifi yau ya mana arha gaskiya,bari na je na watsa ruwa zafi nake ji sosai"
"To ya kamata kam maida hankali ki yi sauri kafin Ihsaan ya dawo ya kama maku masifar ya deb'o ruwa Kuna sheqarwa a banza gashi yamma ta gabato a yi a zo a dauraye plates d'in anjima"
Balqis ce ta ce,
"Aiko dai, wannan yaro shi fa Jin sa yake kamar shi ne Yayan mu, ko Yah Sudais baya mana iko da Isa da mallakan da yaron nan yake mana a gidan nan, son girma kamar gyambo, da shi ne Yayan mu da mun shiga uku"
Dariya suka yi har Jiddah da ke cire dogon wandon ta ta ja zani Saman igiyar shanya ta daura zuwa qirjin ta sannan ta cire rigar ta ta rataya ta a igiyar, bokiti ta dauka ta zuba ruwa rabin shi sannan ta d'auki kwandon wanka zata shiga band'aki.
Muryar Balqis ce ta katse ta daga shiga bandakin ta d'auki wani d'an qaramin dutse ta jefa mata,
"Oho dai be same ni baaa, an fad'a wankan baki asarar ruwa ko ya yi ma kamar be yi baaa"
"Alhamdulillah gwanda ni baqa ce ba qaton goshi gare ni ba,baqin nan da ki ke gani kasashen turai kashe masa kud'i suke ki ji ana black beauty, yanzu nan da zan samu Yan kwabbai yarinya gani na ma se kin nemi appointment"
Dariya Ummah da Balqis suka kwashe da ita, sannan suka furta,
"Appointment d'in gaske,"
Wankan ta ta shige bakin ta d'auke da addu'ar shiga bandaki, domin kuwa Ummah ta nuna masu mahimmancin shiga bandaki da addu'a ba da waqa ko hira ba,ta ce masu, bandaki matattara ne na aljanu masu bala'in taurin Kai da nacin tsiya,gwanda mutum ya samu aljanu a wani wajen da ya samo a bandaki, Dan kuwa kafiya ne da su da wahalar jinya. (Allah ya Mana tsari da su...Allahumma inni a'udhubika minal khubsi wal khaba'is..idan an fito a ce Ghufranak)
Jiddah na wanka ta ji muryar Mahaifin su da suke Kira da Abbah ya dawo, cike da zumudin son ganin shi take sauri Dan ta gama ta fita, muryar Balqis duk ta karad'e gidan da shewa da murna, cikin sauri ta daura zanin ta tare da yarfe soson wankan ta mayar cikin kwandon ta d'auki bokitin ta bud'e qofar bandakin ta fita bakin ta d'auke da addu'ar fita daga bandaki.
"Abbahhh sannu da zuwa"
Shine abinda ta fara cewa,mutumin da ta Kira da Abbah kuwa juyawa ya yi ya kalli gudan Jinin nashi da yake matukar kauna, ya ce,
"Jiddahn Abbah kema sannu da dawowa daga makaranta,ya jarabawar da fatan an rubuta abun kirki kamar yanda aka Saba ko?"
"Eh Abbah alhamdulillah ba wahala ma sosai yanda na zata,"
"To alhamdulillah Allah ya taimaka, daga wannan jarabawar Kuma se ta fita daga sakandire a fad'a jami'a ko aure"
Jiddah na Jin kalmar aure se ta kwasa da gudu ta yi dakin su, shi kuwa Abbahn ta me zai yi Banda dariya, Balqis ma dariyar ta Sanya sannan ta ce,
"Ai gwanda ki zo ki yi auren ki bani waje na sakata na Wala duk kin ishen dama"
"Ranar auren Jiddah ranar Auren Balqis kenan da yardar Allah"
"Kaiii Abbahhhh"
"Keee Balqisssss"
Tashi ta yi ta na zumbura Baki ta da'u bokitin wankan da Jiddah ta yasar ta gudu daki, ta na tafe ta na mitar ita ta yi yarinta ba ta son aure yanzu, Ummah na zaune kamar wadda aka dasa fuskar ta d'auke da busasshen murmushin da duk Wanda ya gani ya San ba har zuciya take yin sa ba,Balqis na shiga wanka Abbahn su ya zauna kusa da Ummah ya ce,
"To ya Ina abinci na?"
Kallon mamaki ta bi shi da shi da takaici be kawo ba amma ya fi kowa tambayar Ina abincin sa, ta bud'e baki za ta yi magana ta ji sallamar yarinya karama hannun ta d'auke da Kwanuka,
"Wa'alaikumussalam, Fadila shigo"
"Hajiya ce ta ce In an yi danwake a zuba mata na d'ari da hamsin, se a sa mata wake da miya na d'ari da hamsin Lantana zata zo ta d'auka an jima"
"To Fadilan Hajiya ga wake can na ta dahuwa danwake kuwa rana na yin sanyi za a fara ki gaishe min da ita ko?"
"Tom"
Miqa wa Ummah dankwalin ta yarinyar ta yi, Ummah kuwa ta kunce d'aurin da ke jiki ta zare kud'in ciki sannan ta daura wa yarinyar dankwalin ta sannan ta sallame ta, Ummah Bata samu damar magana da Abbah ba saboda Yara masu zuwa kawo kud'in danwake da wake da Kuma shinkafa da wake,se zob'o da kunun zaqi.
Abincin shi ta Kai Masa dakin su ta ajiye masa tare da furta,
"Allah ya shirya min Kai Abbahn Sudais"
"Ameeen Umman Jiddah"
Cikin baqin cikin da da shi take kwana take tashi ta watsa masa harara ta bar dakin, shi kuwa ko a jikin Sa, haka ya ja kwanon sa ya hau cin lafiyayyar shinkafa da wake da salad da soyayyan kifi, gefe Kuma ga zob'o na raba saboda sanyi, Bismillah ya yi ya fara cin abincin sa, ya na yi ya na danna wayar shi qirar Iphone,magana yake ta wasu kudade ta WhatsApp da abokin shi,ya na tsaka da maida voice note ya ji motsi da sauri ya sake shi ya tafi ba tare da ya qarasa maganar da zai yi ba, cikin nuna alamar rashin gaskiya ya hau zare Ido ya na fad'in,
"Ke Umman su meye haka? Se kawai ki fad'o d'aki ba sallama ba magana? Haba wannan ai be dace ba me ki ke koyar da Yara kenan?"
Dariya ta yi tare da tafa hannayen ta ta ce,
"Allah mai iko, wa'azi Kuma ka koma? Da kyau, to ai alhamdulillah duk Wanda ya San Yara na ya San suna da tarbiyya ba jahilai bane ba Kuma 'yan Iska a cikin su alhamdulillah,ka na can kana maganar kudad'en da ba naka ba na yi sallama baka amsa ba, Kai baka Jin kunya ko Kabeeru? Baka Jin kunyar Allah ko? ba dai ba za ka sauya halin ka ba? Ka ci gaba, Allah ya hore wa kowa arizi mai albarka,ka ci kud'in ka Kai kad'ai, mu ma mu ci namu mu kadai ba shi kenan ba"
Kame kame ya fara saboda ya tabbata ta ji maganar da yake yi kenan, can daga baya Kuma ya ce,
"Ke fa matsala ne da ke, na ce maki ki zo mu samu a had'a Kai a rufa wa juna asiri, mu fad'a hanyar nan gaba d'ayan mu se a fi samun kud'i kin ga gidan da za a siya ma se a siyi babba wadatacce na zamani,Amma kud'in da ki ka tara na tabbata be fi a sai irin gida me daki uku ko hudu ba,amma idan ki ka yarda se ki ga kud'i na ta zuwa mana da kyau ga shi zamu sakata mu Wala mu faso gari mu yi bankwana da talauci"
"Allah ubangiji ya tsare ni da cin kud'in haram kud'in tsafi ko damfara, Allah ya bani iko na ci gaba da neman halal d'ina na ci gaba da ciyar da iyali na har da Kai tunda ka kashe zuciyar ka, Kuma mugunta ta sa kana da shi ba zaka yi mana komai ba se dai ni na yi,iya sana'ar da Allah ya baka ta halal ta ishe mu Jin dad'in duniya Kai har wani ma ya mora ya ji dad'i amma ka ki ka sauke nauyin da Allah ne ya dora maka, ka barni da wahala se dai ka shiga wannan shadda ka Sanya wancan yadi mai tsada,ba komai ba Wai Ina complain bane, zan iya,zan iya kula da ku dika, ai Yara nawa ne ba na wani ba, ba laifi Dan na ci da su na tufatar da su na Kuma Sama masu mahalli Dan su kauce gori da wulaqancin masu gidan haya."
"Keee ya Isa haka ! bakaken maganganun sun Isa haka, ko baki ji ba ne?"
"Ni kuwa na ji ka, Allah ya shirya min Kai"
"Ke ma Allah ya ganar da ke"
"Ameeen Ina so Allah ya ci gaba da ganar da ni gaskiya"
"Mtssswww kan ki ake ji,"
Ba tare da ta sake kula shi ba ta fita wajen sana'ar ta, can ta tarar da Jiddah ta gama dauraye plates ta kife ta sake share wajen da suke girkin abincin sayarwar tasu a cikin gida.
"Ina wannan uwar son jikin take?" In ji Ummah.
"Ta na daki bacci take Wai kan ta na ciwo"
"Hummm idan ma baya yi za ta ce ya na ciwo Allah ya shirya min Balqis"
"Ameeen Ummah"
Ci gaba da taimaka wa mahaifiyar tasu ta yi suka yi ta cinikin abincin nasu.
Qamshin turaren shi ya riga sallamar shi Isa cikin gidan, lumsassun idanun ta masu kama da na wadda ke Jin bacci ta bud'e suka sauka a kan fuskar shi, cikin sauri ta Kau da Kai tare da miqewa za ta shiga cikin d'akin su.......
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 4:
"Ke zo nan, Ina Zaki je? Baki iya gaisuwa ba ne?"
A matuqar rikice Jiddah ta koma asalin wajen da take zaune ta hau in ina gaisuwar da ya yi ikirarin ko bata iya ba, se ya tabbata a yau ta kasa furta ta a Saman labb'an ta, zuciyar ta ce kawai ke ayyana gaisuwar amma bakin ta ya qi bata had'in Kai ta furta a Saman labb'an ta.
Ganin irin halin da ta shiga ne ya Sanya Major Muhammad Labbo sassauta d'aure fuskar da ya yi, ya Sanya kyakkyawa Kuma qayataccen murmushi a Saman fuskar shi wadda ta Sha aski Babu gashi ko d'aya, labb'an sa masu fad'i da tudu irin na Jiddahn ya mayar cikin bakin shi alamar qunshe dariya, cikin son yin dariya ya durqusa ya fara gaida Ummah da ke musu dariya shi da Jiddah.
"Lafiya qlou muke alhamdulillah soja ga wuta ga yaqi, yanzu ka ke tafe da yammar Nan? Ko sanar da zuwan ka ba ka yi ba amma, domin kuwa da na ji daga bakin Yaya dan ko d'azu shi da Abdunnasir sun zo gidan nan Yara suna makaranta, ka ga da zai sanar da ni ka na nan tafe"
"Ai kuwa dai wannan zuwan na bazata ne, aiki ya yi yawa na gaji da ganin masu laifi shine na ce bari na zo na ba wa idanu na abinci da mutanen kirki"
Ya na maganar idanun shi na kan fuskar Jiddah wadda ta sunkuyar da Kai qasa ta na Wasa da zoben azurfar da ke yatsanta na dama, Ummah ce ta d'auki kwandon gaban ta da ke d'auke da ragowar yankakken cabbage da lettuce,tumatur albasa da tattasai Wanda shi suke zuba wa a Saman danwake idan an siya, rufe wa ta yi sannan ta wuce ciki ta na Masa iso.
"To Ummah gani nan zuwa"
A gaban Jiddah ya tsaya ya Dan duqa daidai fuskar ta yana ci gaba da kallon fuskar ta ya ce,
"Ina wuni? Da fatan na same ku lafiya? Ya exams? Kun gama ko da saura? Auntyn ki na ta damu na akan na Kai ki hutu Abuja yaran ki na kewar ki"
'Kaiii ya akai guy d'innan ya San Ina rubuta jarabawa?' ta ayyana a cikin zuciyar ta.
"Har yanzu Baki yarda na San komai game da ke ba ko? Tom aljanu na ne suka fad'a min"
Cikin sauri ta daga Kai ta kalle shi,sannan ta ce,
"Dama Maza su na yin aljanu ne Yah Major?"
"Kwarai da gaske mana, baki da labari? Ina zuwa na gama gaisawa da Ummah na zan zo na baki labari"
Cikin sauri da nuna alamar tsoro ta ce,
"Ah ah ni bana so, wa ya sani ma ko a wajen yi wa mutane mugunta ka samo su..."
Da sauri ta kulle bakin ta ta na zare fararen idanun ta ta na kallon shi, murmushi ya yi sannan ya wuce d'akin Ummah wadda ta gama had'a Masa abinci da abun Sha, Dan ta San ko gidan su ya je ba zai ci abinci ba sai ya zo wajen ta, a cewar shi idan ya zo gida ya na son ya samu sauyin abinci na gargajiya.
Bismillah ya yi kafin ya samu waje ya zauna, gaisa wa suka sake yi da Goggon tashi sannan ya wanke hannu da ruwan da ta aje Masa a roba, ya sake Bismillah ya fara cin abincin.
Kamar wadda aka wurga haka ta fad'a d'akin, ta na shiga kuwa ta zauna dafff da shi kamar zata shige masa jiki, cikin qara da murna ta ce,
"Yahhhh Majorrrrr ! Sannu da zuwa na gaji da baccin karyar, Yah Major na yi kewar ka ka jima baka zo ba,"
Cikin fad'a Ummah ta zari wayar charger da ke gefen gadon ta ta lafta wa Balqis da ke naniqe wa Muhammad Labbo a jiki ta na murnar ganin shi, saukar bulala a jikin ta ne ya Sanya ta tsanyara wata sabuwar qarar tare da rungume shi da kyau ta na kuka, cikin nuna alamar lallashi ya hau buga bayan ta, sannan ya ce,
"Habaa Ummahn mu ya Zaki min haka? Wannan fa ita ce ta qarfen idan ki ka mata tabo fa yanzu se dai a bar ni da jabu"
"Ka San iyashegen yarinyar nan fa Junior,Wai Dan iskanci Ashe idon ta biyu ta bar 'yar uwar ta da wanki da taimaka min wajen sana'a ita kenan ba za a more ta ba? Sanda Jiddah Bata nan fa? Ko dake ai kin ji Abban ku ya ce tare za a maku aure kin je gidan mijin ki Masa wannan iyashegen ya Zane ki"
"Ni ba me min aure da qananan shekaru na, dika dika fa shekarata Sha biyar ko ita Yah Jiddahn da a turai ne bata Isa aure ba nan Nan kudu ba sa aurar da 'yar Sha takwas balle turai,"
Baki Major ya sake ya na kallon Balqis ya na dariya, yarinyar na bashi dariya sosai, a Ina ta San ya ake yi a turai da kudu?
Jiddah kuwa da ke zaune ta na jiyo su ce ta banka wa qofar d'akin harara sannan a hankali ta ce,
"Ohhh wato ni ce ma jabu ko? Da kyau, za ka ga jabu kuwa ba sai na aure kan ba zaka kira ni da jabu?"
Tashi ta yi cikin b'ata fuska ta shige dakin su, amma kafin ma ta kwanta har ta manta da bacin ran da take, ta koma farin cikin sake ganin Yayan nasu, ita dai ta sani an ce shi zata aura, Kuma iyaye da matar shi kan ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 12